falon tareda mami,sauqa sukayi downstairs suka bar Mamin
Zama sukayi anan falon nafisa na turo baki ita a dole abunda Mami ta sa suyi bai mata dadi ba, Na'ima ta kasa shiru tana murmushi dan yanayin nafisan dariya ma yabata tace "Nafee it's just ziyara fa, what's the harm in that? Beside, ba kince yayun Abba bane sudin" Nafisa ta bata rai tace "Eh..amma Mami ce take taqurawa sai munje alhalin su ba wani zuwa gidan nan suke ba,
tunda muka dawo kinga yaran gidan sunzo gaisheta ne?.." Na'ima batace komai, Nafisa ta cigaba " har gwara ma su yaya Adam da anty Fatima sai dan dama dama husna, Amma 'ya'yan anty da mummy fa bawanda yake zuwa gaishe da Mami" Na'ima da bawai saninsu tayi ba, tanadai jin labarin su wani lokaci a bakin nafisan, tace "yaran anty sune twins da Salman da za'ayi bikin nata ko?"
Ganin na'ima ba wani saninsu tayi ba yasa nafisan cewa "Kinga yaya Ahmad,wanda sukazo rannan to shine babba a gidan baba, forget it bari na miki dalla dalla, su Abba su hudu iyayensu suka haifa that is Babba sai Abba sannan Daddy and last dinsu Anty Amnah, to gidan baba yanada mata biyu da mamma sannan anty, yaran mamma sune yaya Ahmad,Anty Fatima,Husna sannan hafsa saikuma yaran anty wanda Salma itace fari sannan twins safiyya da sumayya" Na'ima ta gyada kai alamun fahimta at the same time idanun Ahmad neh suka fado mata arai tayi stiff tana tuna yanda yake kallonta dazu.
Nafisa ta cigaba "sai gidan Daddy kuma, kinga yaya Adam shine babba wanda shi mahaifiyarsa ta rasu so practically he was raised by mamma tareda yaya Ahmad, Mummy ce Matar Daddyn ita kadai, ita kuma yaranta akwai anty murja,anty ummi sannan Laila ce autarsu, to anty Amnah kam kinsanta ai" Na'ima ta gyada kai tace "Nagane" nafisa tace "Mami itadai kayi ta zuwa gaishesu kamar wa'enda akayiwa mutuwa" Na'ima tayi murmushi tace "to ai 'yan'uwankune nafisa, yazama dole" Nafisa tace "ni ba gidan Baba bane banason zuwa, gidan Daddy ne, mummyn ce ba sauqi a lamarinta" yar dariya Na'ima tayi tace "kijiki sai kace wata sa'arki" Dariya itama nafisan tayi tace "bazaki gane bane"
Abba ne ya shigo tareda samarin gidan dawowansu daga masallaci kenan su na'ima suka gaishesu, nan kowa ya nufi dinning don yin dinner Mami ta sauqo itama, Na'ima ce tayi serving dinsu, don tun farkon zuwanta gidan Mami kan sata itama tayi serving a table din so that she could feel at home, hakan yazame musu al'ada ko ita ko nafisa sune servers in an zauna cin abinci, Abubakar ne ya bubbude flask din ganin babu tuwo yace "anty yau ba'ayi mutuminki tuwo ba" Na'ima data koma ta zauna tayi murmushi tace "Abu tsokala ko" Abba yana fara'a yace "tuwo abunso ne ai Abu" Abubakar yace "inaaa, Abba munfi gane yaren shinkafah" akayi dariya gaba daya.
Bayan sun gama cin abinci aka koma main falon ana hira, su na'ima suka tattare kwanikan suka wankesu a kitchen sannan suka koma falon aka cigaba da hiran dasu, Al'adan gidan ne yawanci dare ana zama ayi hira in ba dai ranan da Abba ya gaji ba ko kuma yanada wani muhimmin uzuri ba, Morning ne dai ba'a cika haduwa ba dan kowa yanada lokacin tashinsa, so breakfast ma kowa da lokacin yin nasa.
Washegari...
Na'ima ta fito daga wanka ta zauna kan stool nan gaban madubi, cire hulan wankan nata tayi tafara taje gashinta da ya kasance mai santsi da laushi, har wani curls yakeyi gashin nata tsabar laushi. Taje gashin take while tana kallon kanta cikin madubin, idonta ne yakai kan bakin wani tabo a gefen kafadanta gashinta ya dan rufeshi, ta qurawa gurin ido acikin mirror takai hannu tana tattare gashinta daya sauqa kafadunta har zuwa bayanta, wani babban tabo ne ya bayyana sosai a gurin mai kama da yanka anyi dinki, takai hannu ta shafa kanshi tana tuna dalilin Jin ciwon,komai yana dawo mata cikin brain dinta kamar yanzu glass din da aka jefon ya yanketa a wajen, idanunta ne suka ciko da hawaye takai hannu ta sharesu still wasu ma suka sake gangarowa,
Tana cikin share idonta Mami ta shigo dakin, Na'ima tayi saurin kauda kanta gefe tana goge idanun nata, qarasowa Mami tayi ta dafata tace "Na'ima" juyowa na'iman tayi tacigaba da share hawayenta , Mami tayi shiru tana kallonta sai kuma ta kama hannunta ta jata suka zauna bakin gado, cikin kwantar da murya Mami tace "Na'ima fadamin meke damunki?" Muryan na'ima na dan rawa tace "babu komai Mami" shiru Mamin tayi tana kallonta sai kuma ta sake cewa "Kinason komawa wajensu ne?" da sauri na'ima ta jijjaga kai tace "A'a Mami" sai kuma ga wasu hawayen, Mami ta dan rungumota tana shafa dogon gashinta tace "it's okay dear, it's alright..... everything is going to be fine kinji" na'ima dake jikin Mamin ta gyada kanta, mami tacigaba "I won't let things be repeated again in sha Allah, we will do anything to protect you,ki kwantar da hankalinki kiyi karatun ki kinji, this is your home too..talk to me duk lokacin da kike buqatan someone to talk to" na'ima ta dago daga jikin Mami tana gyada kanta mami tace "Now wipe those tears, you had so much ahead to live for in sha Allah, stop wasting your tears kinji" na'ima ta sake gyada kanta tace "toh mami" Mami tace "in bakyason fitan ma kiyi zamanki ki huta" tayi murmushi tace "A'a Mami zanje"
Mami ta shafa kanta tace "toh tashi ki shirya" miqewa na'ima tayi ta nufi wardrobe dinta Mami ta bita da kallo zuciyanta na karyewa ta miqe ta fita daga dakin
Na'ima na cikin saka kayanta nafisa ta shigo all set tace "har yanzu wai baki shirya ba?" Na'ima ta kalleta tace "gashi fa inayi" nafee ta zauna kan gadon tana kunna wayanta, bayan na'ima ta gama saka kayan ta fara neman veil din da zata yafa jikin light blue doguwar rigan jikinta na atamfa dayasha beadwork, ta bincika bata samu wanda ya dace ba acikin jerin veils dinta na cikin wardrobe din sai kawai ta jawo babban box dinta data dawo dashi daga England tafara bincikawa aciki, idon nafisa ne yakai kan wayar na'iman dake cikin kayan, ta miqa hannu ta dauka tace "Bobo ni lafiyanki kuwa da bazakiyi amfani da wayarki ba" na'ima dake abun gabanta tace "nafee to wa zan kira?" Shiru nafisan tayi saikuma tace "to aiba kira kadai akeyi da wayaba akwai abubuwa da dama" Na'ima na rufe box din tace "duk inayinsu da ipad plus laptop dina ai" bayan ta mayar da box din ma'ajiyansa ta qaraso ta karbi wayar nata dake hannun nafisan ta jawo bedside drawer ta jefa nafisa na binta da kallo.
Sun fito zasu tafi nafisa ta jefawa na'iman key tace "kiyi driving dinmu yau kema" na'ima tayi dariya tace "kinfa sani hannuna bai gama fadawa ba" nafisa data bude side din mai zaman banza tace "ai sai kinayin a hankali zaki qware din" Na'ima ta bude driver seat ta shige itama, haka tayi driving din nafisa na qara nuna mata yanda zatayi,Kuma balaifi ta iya din.
Isarsu gidan Baba bayan maigadin ya bude musu gate din babban mansion din na'ima tayi parking, ta fito tana dan bin gidan da kallo ganin yafi nasu mami girma, shigansu babban falon gidan suka samu babu kowa sai Mai aiki dake faman goge goge suka gaisa nafisa ta tambayeta ko su mamma na nan, ta amsa da Eh tana sashinta.
A falonta suka samu mamman, na'ima ta dan tsurawa kamilan Matar Ido ganin kamarta daya da Ahmad, bayan sun gaisheta ta amsa da "lafiya nafisa, yakuka baro Mamin ?" Nafisa ta amsa da "lafiya,tace agaisheki" Mamma ta amsa tana kallon Na'ima tace "yarinyar wajen Mamin naku ce wannan ko" nafisa tace "Eh mamma itace, sunanta na'ima" mamma tace "ma Sha Allah sannu na'ima,ya zaman qasar tamu, ba kamar nijar ba ko?" Na'ima ta dan sunkuyar da kanta tana jin yanayin ta wani iri aduk lokacin da aka dangantata da nijar,gurin da bata ma taba sanin inda yake ba balle taje, murmushi tayi tace "Alhamdulillah" bayan Mami tasa an kawo musu drinks da snacks suka dan taba hira gameda karatunsu sannan suka miqe nafisa tace "mamma zamu je gurin anty" mamma tace "toh nafisa" nafisa ta sake cewa "Husna tananan kuwa?" Mamma tace "bansani ba ku duba dakinta , dan dazu tacemin zataje gidansu course mate dinta" Nafisa ta amsa da to sannan tayi gaba na'ima ta bita suka fice daga falon mamma. Bayan sun fito da part din anty wacce suka gaisa da ita sama sama dan mace ce wadda nukurci ya cinye mata zuciya bata cika fara'a ba, batasan na'ima ba kuma bata damu da tambaya ba har suka fice, dakin husna suka shiga suka sameta kwance kan babban gadonta,tana ganinsu ta miqe tadanyi ihun murna ta riqo hannun nafisa
Nafisa ta fusge hannunta tace "dalla sakeni bayan kinsan nadawo amma ko kizo"
Husna tace "Bobo Dan Allah kiyi hakuri school ce ta riqeni amma kina raina wallahi" Na'ima ta kalli husna jin kalman "Bobo" a bakinta,dama nafisa ta fada mata sunan dasuke kiran juna ne itada Salma
Nafisa ta kyabe baki tace "bawaninan" dariya husna tayi ta juya tana kallon Na'ima tace "sannunki da zuwa" na'ima tace "yauwa sannu" ta qarasa zata zauna kan resting sofa data gani a dakin husna ta riqo ta tace "mu qarasa gadon yafi dadin zama" na'ima ta girgiza kai zata zauna husna ta riqe hannunta ta jata kan gadon da nafisa ta hakimce aka ta miqe kafafu harda cire gyale. Bayan sun gaisa husna ta kawo musu yogurt me sanyi ba cups haka ta miqawa kowannensu a hannu ta hau gadon itama riqeda daya, tana kallon Na'ima ganin itadai bata Santa ba ta juya tadan taba nafisa tana mata sign da Ido alamun "wacece wannan" a fili nafisa tace "Na'ima ce fa wadda nabaki labarin muna tare a Oxford" husna tace "ohhh cousin dinki dinnan?" Na'ima ta hada Ido da nafisa, waskewa nafisan tayi tace "Eh ita" Husa tace "Ma Sha Allah, she's so beautiful" ta juya ya kalli Na'ima ta sake cewa "sis, you're beautiful" Na'ima ta sauke idonta tana murmushin kunya batace komai ba, nafee ta dan daki kafadan husna tace "dalla kina sata kunya" husna tayi dariya tace "Aiiii...sorry"
Bintu Musa ce ✍🏻
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
ArewaPen::https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 11
Suna cikin hira husna ta tambayi nafisa "Sis meya faru jiya nakiraki zan miki gulma naji wayanki a kashe?" Nafisa tace "na kashe ne dan nasan Umar zai kirani" husna ta jijjaga kai tace "Kai..keda guy dinnan dai bansan yanda zanyi defining kalan taku matsalar ba wallahi" Na'ima batasan lokacin da tafara yar dariya ba suka juya suna kallonta husna na dariya tace "Allah kuwa, yanda kikasan numfashinsu ne ajikin na juna, su basu rabu ba,Kuma matsalar taqi qarewa, Na'ima ta girgiza kai tace "karma ace sai sun rabun,dan banason su rabu but it's high time su fahimci a Ina matsalarsu take" Nafisa tace bazaku gane bane" Husna tace "toh fahimtar damu yanda zamu gane din, guy dinnan kunason juna amma kullum matsalar yau daban ta gobe daban, Bobo get a break please" Nafisa bata amsa ba ta cigaba da shan yogurt dinta, Salma ce ta shigo dakin Na'ima tadan kalleta ganin bazata wuce mate dinsu ba,ta qaraso bakin gadon ta tsaya tace "sannunku" suka amsa nafisa nacewa "amarsu kinsha qamshi" Salma tayi yar dariya sannan tacewa husna "dazu yaya Adam ya shigo yana neman ki bakyanan" husna tace "Eh munyi waya dashi ai" Salma ta juya tana kallon Na'ima tace "wannan da,daga Ina?" tsuka mai karfi husna tayi tace "kefa matsalata dake kenan, meye hakan kuma" nafisa ma ta juyo tana hararan Salma
Salma tace "Ha'a daga tambaya" cikin fusata husna tace "dalla to haka ake tambayan? Ji rainin wayo wai 'daga ina' " ta qarasa tana quoting maganar Salman
Nafisa tace "banida lokacinki Salma". Na'ima tayi tsuru tsuru ganin fada zai kaure akanta, tadan kamo skirt din jikin nafisa alamun su bari.
Sanin masifa da rashin hakurin husna da nafisan yasa Salma juyawa ta fice tana cewa "kwaji dashi" Husna ta dan daga murya tace "zamu hade ne, yar rainin hankali" tamaida hankalinta wajen nafisa tace "wallahi duk Laila ce take koya musu salon magana mai dauke da rainin nan,balle yanzu da tunda watan bikin yakama suke sintirin yawo tare, idiots" Nafisa tayi tsuka tace "can gidansun zamuje daga nan, Mami harda min gargadin batason fada" husna ta kyabe baki tace "Lailan ce sai kana mata zafi zafi" nafisa tace "ita tasa Salma ta fitar da wannan ankon mai kama dana 'yan iska ko?" Husna tace"Eh mana, ba don mamma tace sai nayi ba su sun isa su sa nayi wannan kayan ne" nafisa ta sake tsuka jin ranta yana neman baci tace "wace gulman kika kirani zakimin din jiya?" Husna tace "ke jiya Farha tasake hotunan wanda ta auran a insta" nafee tace "haba? Kice anata rugumtsumi babu ni kadai" husna tace "kedai bari..5k comments a jiyan fa".
Cikin zumudi suka fara maganganunsu da ya shafi Instagram wanda na'ima ba ganewa takeyi ba dan duk ta qosa su tafi kuma, jitayi duk ta taquru.
Bayan sunyi sallama dasu mamma akan zasu tafi ta basu humra da turaren kabbasa sukayi godiya suka je wajen anty itama,sama sama ta amsa musu, husna ta rakasu suka fice, sun fito compound din gida suka hango Ahmad sunkuye cikin boot din motarsa yana neman abu , husna tace "tab ga yaya can" nafisa tace "bari muje mugaisa" riqo hannun nafisa husna tayi tace "mamma takai qarata jiya, kuzo mu wuce tun bai ganmu ba" nafisa tace "to inya juyo fa,Kinga na'ima zo muje" ta qarasa tana riqo hannun Na'ima itama, Na'ima jitayi kamar tacewa nafisan "bazai juyo bama" amma ganin husna yasa bata fada ba, haka dai ranta babu dadi suka qarasa wajensa da har a lokacin yana duqe
Nafisa ce tafara magana tace "sannu yaya" ya dago ya rufe boot sannan ya juyo, idonsa bai sauqa kan komai ba sai Na'ima, suka sake hada Ido na'ima tayi saurin kauda kanta ganin yauma kallon ta yakeyi, jitayi kafafunta na neman gagara daukanta gashi saita ganta qarama a kasansa don Allah ya masa tsayi da qaqqarfan jiki,dauke idonsa yayi daga kallonta ya maida hankalinsa wajen qannen nasa yana amsawa cikin muryarsa dake hana na'ima nutsuwa yace "yauwa sannu nafisa,ya gida" nafisa ta amsa, cikin low voice na'ima tace "Ina wuni" tana kallon everywhere but not his face, dan motsa lips dinsa yayi wanda inba lura kayi ba bazaka kace murmushi yayi ba, yana nazarin yadda take escaping kallon fuskansa,ya amsa mata da "lafiya" Husa tace "'yar'uwarsu nafisa ce yaya, sunanta na'ima" ya sake kallon na'iman yana nanata sunan a zuciyarsa, a Fili yace "I know" Na'ima tadan juya ta kallesa ganin ya maida kallonsa wajen qannensa, within sakanni Sha biyar ta gama kallon fuskansa a sace sannan tayi saurin kauda kanta kar ya juyo, nafisa ta tambayi Ahmad "yaya Adam yana nan kuwa yaya?" Ya dan gyada kansa yace "yana falo" hanyar bangarensu Ahmad din suka nufa, yadan bi bayan na'ima da kallon gefen Ido kafin ya shiga motarsa ya tayar.
Sun tadda Adam yana Shirin fitan shima yana maqala link jikin hannun rigarsa, suka gaisa yace musu fita zasuyi shida Ahmad shima, tare suka fito ya musu sallama ya wuce gurin motan da Ahmad yake ciki suka fice, Suma tasu motar suka shiga suka bar gidan husna na nan tsaye ta daga musu hannu.
Isarsu gidan Daddy basu samu kowa a falo ba, basuyi azarbabin bin mummy part dinta ba nafisa tasa sukayi zamansu nan falon, basu jima da zama ba mummy ta sauqo cikin shiga ta alfarma cike da qasaita ta qaraso ta zauna tace "sannunku" suka gaisheta kan Na'ima na qasa dan tunda mummy ta shigo taji kwata kwata Aura din matar bai mata ba sam, suna gama gaisawa mummy ta dan kwala kira wata mai aiki ta shigo mummy ta umarceta ta kawo musu refreshments, sunanan zaune shiru babu me magana mummy ta kalli Na'ima sannan tace da nafisa"Ina kika samo wannan fa? Kawarkice?" Nafisa ta amsa da "A'a yar uwar muce" mummy ta qarewa Na'ima kallo tace "to sannu"
Laila ce ta fito daga wani qofa alamun kitchen ne a gurin, ta qaraso cikin falon ta zauna gefen mummy tana kallonsu sama sama tace "sannu fa" nafisa tadan juyo itama sama sama tace "sannu" Na'ima ta dago ta kalli Laila zata gaisheta atake ta rasa me zata fada ganin attachment da nails din da suke jikin Lailan yayi triggering wasu memories acikin brain dinta, tayi saurin sauqe idonta , Laila da kyawun na'ima took her by surprise ta kalli nafisa tace "wannan fa,daga Ina?" Nafisa najinta kuma bata kulata ba tacigaba da kallon tv kamar bada ita Lailan ke magana ba,mummy ce ta amsawa Lailan tace "nima yanzu nake tambayanta,wai 'yar'uwarsu ce,Inaga sai dai ta fannin Mamin tasu daga nijar"
Laila tasake tambayan nafisan tace "daga gidan baba kuke ne?, Salma tananan?" Sai lokacin nafisa ta juyo ta amsa coldly da "Eh" Laila tace "yaya Ahmad fa?" Nafisa tace "bansani ba nima" tasake juyawa tana kallon tv, na'ima dai kamar ta arce daga falon haka takeji, the atmosphere become toxic to her, daga mummyn har Lailan tuna mata suke da wasu mutane a rayuwan ta da batason tunasu kwata kwata yanzu. Jin Laila na tambayan Ahmad yasa mummy tace "ba kince zaki kirasa ba" cikin rashin da'a Lailan ta amsawa mummy da "toh nakirasa bai dauka ba yazanyi mummy, ni zuwa kawai zanyi dakaina in kaimasa cakes din,tunda bai dauki kiran ba" ta miqe tana turo baki ta sake suka ga wuce stairs su nafisa na bin ta da kallo, mummy tace "ke kika sani ai" ta sake kwala kiran me aiki tace mata "ki dan debo musu snacks dinda Lailan tayi" ta amsa da toh ta koma kitchen din tadawo dauke da different shape of small pieces of cakes ta ajiye gabansu, basu ko taba plate din ba nafisa ta fara miqewa tareda cewa mummy zamu wuce gida" na'ima ta miqe tana mata sallama mummy tace "toh aigaida gida" suka fice, isarsu wajen motansu nafisa tace "shegiya" juyowa na'ima tayi zagin yayi tooking dinta by surprise tace "haba nafee" adan fusace nafisa tace "ke bakiga yanda shegiyar ke mana magana bane, wallah badan Mami ta gargadeni akan fada da Laila ba da watarana sai na zubar mata da haqora tas" na'ima tadan ware Ido tace "toh ba gashi har mun gaisa mun fito ba, komai dan haquri ne ai, keda ba wani haduwa kukeyi bama" nafisa tayi tsuka suka shiga motan suka bar gidan tana mitan sai sun koyawa Laila hankali itada husna, itadai na'ima Allah Allah take su qarasa gida ta huta da wannan tunanin da suka zo ranta tun safiyar yau har zuwa barinsu gidansu Laila.
Bintu Musa ce ✍️ 📚
ArewaPen @Bintu Musa
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
ArewaPen::https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 12
Isarsu gida suka samu anty Amnah tazo,sunzo saboda bikin itada twins, ihun murna twins suka fara ganinsu na'iman, da gudunsu suka tafi na'ima na ware musu hannunta suka maqalqaleta, nafisa tace "yarannan kun gama yayi na wato" Mami da anty Amnah dake falon sukayi dariya anty Amnah tace "boys babu amana"
Zama sukayi nan falon bayan sun gaisa anty Amnah take tsokalan na'ima wai tayi qiba,na'ima tayi dariya tanajin duk wani tunani data kwaso gidansu Laila yana washewa,
Har dare anty Amnah na nan saida sukayi sallah sukayi dinner sannan ta kira driver ya maida ita gidanta dake nan abujan wanda suke sauqa in sunzo qasar.
Daren ranan bayan na'ima ta gama shirin bacci cikin riga da wando dogo ta saka hula akanta ta fice zuwa falon Mami sanin cewa mazan gidan basa gurinta by now, bata samu Mami a falon ba ta qarasa cikin dakin ta ganta a duqe gaban bedside drawer tana bincikawa, qarasowa cikin dakin na'ima tayi tace "barka da dare Mami"
Mami tadan dago tace "Habibti,bakiyi bacci ba?" Na'ima ta amsa da "Eh" ta zauna bakin gadon Mamin tasake cewa "Abu kike nema ne mami" Mami tace "waifa nayi ajiya ne na manta specifically inda nayi ajiyan" ta qara da "lantana ta qara soya muku gyadan ku yananan a kitchen" na'ima ta gyada kai tace "har munci ma"
Tananan zaune Mamin ta miqe ta wuce toilet nafisa ta shigo tace "nan kikayo?" Na'ima ta gyada kai,nafisan ta zauna kan gadon itama ta zubawa na'ima chocolates masu dan yawa akan cinyanta, na'ima ta ware Ido zatayi magana kenan Mami ta fito daga toilet idonta ya sauqa kan chocolates din, nafisa datayi expecting mami na falon Abba ta ware idanu tace "laaa Mami ashe kinanan, nazata kina kitchen fa"
Mami ta harareta tace "shiyasa kika shigo da abunda na hanaku sha din kenan" na'ima ta juya kanta dariya na taho mata, nafisa ta fara dariya tace "wallahi mami tun safe bamu sha ba sai yanzu" Mami ta wuce gurin wardrobe zata dauki abu tace "yamuku kyau, ku cigaba" Atare suka bata hakuri bata kulasu ba ta fita daga dakin. Nafisa ta juya ta daka duka a na'ima, sosa gurin na'ima tayi tana dariya tace "Auchh..to ai zan miki magana naga ta fito daga toilet din"
Hiransu suka zauna nan dakin Mamin sunayi, nafisa na pressing wayanta, cannta yi wani tsuka mai karfi tana kallon wayanta tace "ni nataba kallon yarinya mara zuciya da aji irin yarinyar nan kuwa" na'ima na kallonta tace "me kuma ya faru?" Nafisa ta tashi zaune ta miqo mata wayan a fuska tace "Laila mana,kiga post dinda tayi a IG, ke yanzu wannan yamiki kama da hannun yaya Ahmad dan Allah" shiru na'ima tayi tana kallon wayan wanda hoton hannun mace da namiji ne sarqe cikin na juna dan ba sanin hannun Ahmad din tayi ba tace "nafisa nikuma Ina nasan yanda hannunsa yake?" Nafisa tace "nidai ko kaffara bazanyi ba wannan ba hannunsa bane,yaushe ma ya dauki kiranta balle har ya kai da riqe hannunta" na'ima tace "to ke me ruwanki in ma hanunsa ne,ba budurwarsa bace, meye na rantsuwan" nafisa ta dan harareta tace "waa? Yaya Ahmad din, lallai bakisan wannan ba, anfada miki yanada lokacinta ne...ke har matan ma in general, harkan kudade kawai yasani wannan kowama yasan haka" Na'ima tadan kyabe baki tanajin wani iri aranta batace komai ba nafisa tacigaba da maganan tace "har da wani love caption, Eh lallai Laila" ta qarasa tana dan dariya ta sake miqa wayan fuskan na'ima tace "kiga caption din har da hashtagging din sunan yayan fa" Na'ima ta kauda idonta daga kallon wayan jin ranta na dan baci babu dalili tace "amfanin me kallon zemun,kinada problem wallahi nafisa" Ta juya ta jawo blanket din kan gadon Mamin tayi kwanciyarta, ganin abunda tayin like she's not interested in the talk yasa nafisa daukan pillow ta kwada mata,fashewa da dariya na'ima tayi tace "Allah kedin ce ai nafee,hiran is not productive,I don't see why kike tada jijiyan wuya" nafisa ta sauqa daga gadon tace "bazaki gane bane" ta qarasa tana fita daga dakin Na'ima ta bita da kallo tana tunani aranta kan meyasa ma zataji wani abu a ranta game da hiran to, after all batada hadi da kowanne cikin biyun, bata dade da fara bacci ba nafisan ta dawo ta kwanta, nan dakin Mamin suka kwana ranan.
Lokacin bikin yanata matsowa and na'ima is not even interested in it, itadai ta dawo taga su Mami ne daman bawai bikin wata Salma can da bata santa ba.
Da bikin ya zama saura kwanaki kadan meerah ta aiko musu da kayan nasu, kaya sunyi kyau har Abba saida aka nunawa
nafisa ta kaisu salon akayi musu qunshi akayiwa nafisa kitso while na'ima tace bataso aka gyara mata gashin kawai.
Cikin week din bikin nafisa tace suje can gidan bikin Na'ima ta jijjaga kai tareda cewa "A'a bazanje ba nafee sai ranan auren" Kuma Mami ta yarda da hakan lokacin da nafisa ta kai qaran na'iman.
Haka na'ima na gani Mami suke zuwa gidan bikin tace ita sai ranar auren zata je..Ana gobe auren duk 'yan gidan sun tafi can gurin event aka bar Na'ima ita kadai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19