Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
son yarinyar yake ba, na biyu kince daga kauye kawunan ta suka baku ita a gantale, na uku ke kika riqe yarinyar sai yanda kikaso zata tafiyar da Bilal, na hudu batada rawan kai da magana..toh me kikeso bayan nan" Hajiya tace "Allah ko..yanzu tayaya zan bullowa lamarin toh?" Larai tace "matso in miki dalla dalla"...... Ranar da Na'ima zata fara zuwa lecture tun asuba ta fara aikace aikacen gidan tana dokin zuwa school din, ita kadai tana aikin tana murmushi, bayan tayi wanka ta dauko gogaggun kayanta da hijabi dogo data ajiye wanda zata fara zuwa aji dasu, data shirya din ma a gaggauce taci abincin anan kitchen sannan ta nufi falon su Alhajin dan tayi musu sallama, bata samu Alhajin ba sai hajiya dake zaune tana kallo, tsugunnawa tayi nan qasan carpet ta gaishe da hajiyan, amsawa tayi tana bin ta da kallo wanda yasa Na'iman duk ta taqura, sai tace "makarantar zakije ne?" Na'ima tace "Eh" tace "Toh Allah ya bada sa'a Na'ima, Allah yasa kufara a sa'a" dan daskarewa Na'ima tayi Jin yau Hajiyan nayi mata addua akan abunda ya shafi rayuwanta sai kuma ta amsa tareda miqewa ta nufi fita daga falon Hajiya na bin bayanta da kallo... Rataye da class bag dinta taje hall din da zasuyi morning lecture din, bayan ta samu guri dan baya haka malamin ya shigo, nan ya fara bada darasin Na'ima ta maida dukkan hankalinta tana sauraro kuma tana joting key words a qaramin takardanta, sai sa suka kwashe 2 hours kafin malamin ya fita, Na'ima ta dan yi miqa tana hamma na gajiya, yan class dinne suka fara fita da daddaya Na'ima ta dan kwantar da kanta akan desk ta rufe idanunta kamar me bacci, ji tayi a jikinta kamar ana kallonta sai ta bude idanun nata, Ido hudu tayi da wata budurwa yar baqa haka dake opposite dinta tana kallonta at the same time chocolate ne a hannunta takai baki tana gutsura bata daina kallon Na'iman ba, dan gyara zama tayi ta miqe zauna tana kallonta, ganin Na'iman na kallonta kyam yasa ta dan daburce tafara murmushi sai kuma ta miqowa Na'ima chocolate din hannun nata alamun ta karba, murmushi ne yazowa Na'iman bata shirya ba ganin wai miqo mata chocolate take kamar wata yarinya qarama.... Bintu Musa ce ✍️ 📚 https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z ✨ KUNCIN ZUCI ✨ Na Bintu Musa Chapter 28 Sake miqo mata chocolate din budurwar tayi sai Na'ima ta jijjiga kai har lokacin murmushin be bar fuskanta ba tana mamakin wannan baiwar Allah, kawai daga ganinta sai miqo mata chocolate, sai tace "A'a nagode" budurwar ta sake cewa "Allah kisha, yanada dadi sosai" daga hannu kadan Na'ima tayi alamun "A'a" , kafin yarinyar ta amsa mata wata kawarta ta shigo cikin Hall din, dago hannu wacce ta shigo din tayi tace "Nafee" sai wadda aka kira da Nafee din ta miqe ta fara tattare kayayyakin ta data baza akan desk dinta su wayanta, ear pod, car key, chocolate har da cheesy, kuma duk wajen ciro chocolate dinne ta fito dasu duka, bayan ta gama saka kayan cikin wata qamar side bag dinta me kyau sai ta juyo ta kalli Na'ima tana murmushi tace "sai anjima" Na'ima ta gyada kai tana bin ta da kallo ganin sai faman gyara wani ficicin gyale dake kafadanta takeyi, fita daga hall din Nafee'n tayi tare da kawarta da kiratan, Na'ima bata dade ba itama ta tashi ta maida littafinta jaka ta fice dan dama shi kadaine lecture'n da za suyi ranan saboda farkon semester ne lokacin, abubuwa da dama basu miqe ba, sai da tayi tafiya me nisa sosai cikin makarantar kafin ta samu bus stop , nan bakin main gate aka sauqeta ta sake neman abun hawa, har qofar gida aka sauqeta ta sallami me mashin din ta shige gida, tunda ta nufi entrance din gidan take Jiyo kamar muryan Hajiya na tashi daga cikin falo, ji tayi kamar karta shiga gidan saboda yanda hankalinta ya tashi a take amma ta daure ta qarasa, bude kofan da zatayi tayi Ido hudu da Bilal daya doso kofan da nufin fita, fuskansa a hade cikin bacin rai yace "Get out of my way you B*tch" kafin Na'ima tayi azaman matsawa kawai ya qaraso ya hankadata da karfi saida ta bugu da jikin gini ta fadi nan qasa, dafa kanta tayi tadanyi qara, shi kuwa dama kansa tsaye wajen ya nufa ko kallonta bai sakeyi ba, Hajiya da ke ihun kiran sunansa ce ta biyo bayansa, sai ta tsugunna tana kamo hannun Na'iman tace "sannu Na'ima, tashi...tashi kinji" miqewa Na'iman tayi da taimakon Hajiya idonta yana kawo hawaye dan har lokacin mamaki ne da firgicin abunda ya farun shimfide a fuskanta, ita kuma me ta masa?.. Hajiya tace "yi hakuri zai dawo ya sameni ne" Na'ima ta jijjaga kai batace komai ba dan har wani sarawa kan nata taji yanayi,     Hajiyan ta sake cewa "sannu, kin dawo?" nan ma Na'ima ta gyada kai, sai ta sake cewa "kije ga abinci can a kitchen na ajiye miki" wani sabon mamaki ne ya kama Na'iman dan tunda take Hajiya bata taba yin abinci ta ajiye mata na musamman ba saidai inta je school din tadawo ta girka, haka ta wuce dakinta tabar Hajiyan nan tsaye tana leqa compound din cikin tararradi... Da Na'ima taje daukan abincin a kitchen sai taga anyi girkin har da wanda yakamata tayi anjima dan shafa batanan sai yamma zata dawo, da mamaki ta zauna nan kitchen din taci..da dare tana dakinta shafa ta shigo ta isar mata da saqon kiranta da hajiyan keyi, samun Hajiyan tayi zaune falo sai ta juyo tace "Na'ima sannu, ga magani nan nasan kanki ze yi ciwo na buguwan da kikayi dazu" to fah, abubuwan da Hajiyan ke yi sun ma fara daina bawa Na'ima mamaki sai kawai ta karba tayi godiya ta koma dakinta tana ta kallon maganin cikin al'ajabi... Washegari sai qarfe goma ta tafi makaranta shima sai da Hajiyan ta rakata da addu'o'i dataje yi mata sallama, as usual yau ma a seat din bayan ta zauna, kafin malamin ya shigo Nafisa ta shigo hall din, qarasowa tayi gurin Na'ima ta zauna a gefenta tana murmushi tace "Good morning" cikin sanyin murya Na'ima ta amsa da "Morning yakike" Nafisa tace "Lafiya Alhamdulillah..Sunana Nafisa kefa?" ta amsa da "Na'ima" nafee ta gyada kai tace "nice name, ke 'yar garinnan ce?" Na'ima ta gyada kai tana mamakin extroverted attitude din yarinyar, Sunanan zaune malamin da ze musu darasin ya shigo, kusan Rabin lecture din Nafisa tayi shi ne cikin danna waya, lokaci lokaci zata dago kanta koda malamin yana kallonta duk Na'ima na ganinta, da aka gama sai nafisan tace mata ta tashi su fita, da farko qi tayi sai da Nafisan ta sake requesting sannan suka fita taren, anan cikin faculty sukayi sallah, bayan sun idar Na'ima ta miqe tana salaqa jakanta bisa kafada tace zata tafi, Nafisa tace "muje muci abinci mana sai mutafi tare" Na'ima ta jijjiga kai tace "A'a zan tafi yanzu Nafisa, sai anjima" sallama sukayi ta wuce gida.. Ranan wata asabar Na'ima taje gyaran falon su Hajiyan tasamu bata nan, tana cikin goge gogen hajiya ta fito ta zauna tare da cemata sannu, can kuma sai tace "Na'ima in kin gama kizo mana, inason magana dake" Na'ima ta amsa da toh, sai da ta gama komai bayan taje ta ajiye kayan aikin nata sannan ta dawo, nan qasan carpet ta zauna cikin sanyin murya tace "nagama Hajiya" gyara zama hajiyan tayi tace "ya makarantan toh, dafatan kina maida hankali" ta gyada kai tareda amsawa da "in Sha Allah" cikin kwantar da murya Hajiyan ta sake cewa "ki maida hankali sosai kiyi karatu Na'ima dan muma munason kiyi karatun nan, kinga gatan da zakiyiwa kanki a yanzu shine karatun, da kuma aure Na'ima, ba abunda nake miki fata irin kema kiyi auren nan ki kama dakin ki asirinki a rufe" Na'ima ta gyada kai, ta cigaba "Na'ima a riqon da na miki nasan babu cuta cikinsa, sannan ke amanace a hannuna, duk abunda zansowa yar cikina shi zan so miki" sunkuyar da kai Na'ima tayi tanajin wari iri a zuciyarta , Hajiya tace " Allah ya baki baiwar nutsuwa,hankali da kuma haquri Na'ima, kicigaba da tafiya a haka watarana zakici moriyan halayenkin nan masu kyau, inason halinki sosai wanda har hakan yasa nakeson hada zuriya dake wallahi, ga dan'uwanki Bilal nan Na'ima, inason ki amince mu hadaku aure ko Allah zai sa ya nutsu sanadinki" zuciyar Na'ima saida ta buga da karfi a wannan lokacin, ta kasa ma dagowa ta kalli hajiyan, suka zaunan shiru babu wanda yace wani abu sai qarar Ac dake aiki kawai akeji a falon, Hajiya ta sake kwantar da murya tace "Bilal dan'uwanki ne na jini Na'ima, kaf duniya bakida kamarmu a yanzu, kuma riqon da muka miki Allah ya gani shi kadai zai bamu ladan, ko auren Bilal kikayi baki biyamu ba" Na'ima ta gyada kai har lokacin ta kasa magana saboda wani gumi daya fara yanko mata a goshi, Hajiya tace "ba lallai sai na baki lokacin yin tunani ba, magana ce da take buqatar Eh ko A'a" a wannan lokacin Na'ima tasani bawai amincewanta Hajiyan ke nema ba, A'a...umarni ne kai tsaye Hajiyan ke bata ta auri Bilal din, kuma tasani rashin amincewanta daidai yake da katse duk wani walwala na rayuwanta daya kunno kai a yanzu, rashin amincewanta daidai yake da katse makarantar ta, daidai yake da har komawanta qauye, toh inta koma qauyen menene makomarta a yanzu, talla ko auren lawan da har yau bata sake Jin labarinsa ba?,Jin shiru yasa Hajiya ta sake cewa "Ina sauraronki Na'ima" dago kai tayi cikin sanyin murya tace "Toh" ai atake fuskan Hajiya ya yalwanta da murmushi tace "kin amince Na'ima?" ta gyada kai idonta na kallon carpet, Hajiya tace " Masha Allah, Allah ya miki albarka Na'ima, kema Allah ya baki masu miki biyayya, tashi kije abunki" Miqewa tayi tanajin wani jiri na dibanta a haka har ta kai ga dakinta, zama tayi a gado tanajin zuciyarta na danqewa guri daya, hawaye ne suka fara taruwa a idonta sai ta kai hannu tana shafa kanta inda Bilal din ya bugata da ginin rancan hawayen na zubowa kan kumatun ta, har dare zuciyarta be rintsa ba dan data yi sallan isha ma nan kan darduman ta kwanta... Cikin wannan halin Na'ima takai kusan qarfe daya saura idonta biyu tana saqa da warwara, horn din motar Bilal tajiyo sai da zuciyarta ya tsinke dan a tunaninta da bata ganinsa kwana biyu agidan baya garin ne, tananan kwancen tajiyo tashin muryan Hajiya da Alhaji a falo, sai dai yau kuma masifa take jiyowa Alhajin nayi a falon Hajiya na tausarsa, qara juyawa Na'ima tayi ta ja hijab dinta ta rufe har qafarta tareda addu'an bacci yazo mata koda kadan ne.... A washegarin Sunday ma haka ta wuni cikin wannan kuncin na tararradin maganar da hajiyan ta  mata, har zuwa ranar Monday bata warware ba, da taje school ma kasancewan tayi latti sai ya zamto cikin sauri tayi excusing kanta ta shiga hall din har bata lura da nafisa data dan dago mata hannu akan ta zo gurinta ba, da aka gama darasin ma cikin sauri ta tattare kayanta ta fice daga hall din... Hajiya ce kwance kan gadon dake dakin Alhaji while shi yana bandaki, bayan ya fito ya kwanta nan kan gadon yaga still bata kashe side lamp dinta ba idanunta bude tayi matallafi da hannunta alamun tayi nisa cikin tunani, juyowa Alhaji yayi yace "menene ya hanaki bacci ladi, kinada damuwa ne?" Shiru tayi har se da ya sake maimaita mata tambayan sannan ta dan miqe zaune tana gyara zamanta jikin fuskan gadon, cikin kwantar da murya tace "Alhaji wata magana nakeson muyi" yace "inajinki" tace "ina neman alfarman ka hada auran Na'ima da Bilal" shiru Alhaji yayi sai kuma ya miqe zaune shima yace "kema tunanin da yazo kanki kenan" ganin kamar zancen nata zai samu guri a garesa yasa ta juyowa gaba daya tana fuskantarsa tace "me ka gani Alhaji" ya sauqe numfashi sannan yace "wallahi na dade Ina saqa abunnan a zuciyana, amma kinsan dan yau, ba'a garaje a lamarinsa, na yaba da hankalin yarinyar sosai amma kuma kinga shi Bilal watacan yagani yanaso kuma itama Na'iman bamusan zuciyarta ba kar mu mata dole" Hajiya tayi saurin cewa "duk wannan ba matsala bane Alhaji, kuma Na'iman da bakinta ta fadamin tanason Bilal din" Alhaji yadan ware Ido yace "dakanta kuma?" tace "zan maka qarya ne Alhaji, ai gaka ga itan sai ka kirata gobe ka tambayeta" yace "A'a bawai ban yarda bane, yarinyar nan 'yarki ce ai, kinfi kowa saninta, zan dai kirata in tambayeta dan fita hakkinta ne" farin ciki ne ya lullube Hajiya ganin haqarta na neman cimma ruwa tace "Allah ya kaimu goben"...... Washegari da safe bayan Alhaji yagama breakfast yana zaune tareda Hajiyan ya kira Na'ima, shima sai da ya fara yabon halayenta sannan ya dora da maganar da sukayin da Hajiya har da cewa cikin ikon Allah da wannan kyawawan halayen nata zata iya chanja Bilal , tunda Na'ima taji hanyar da zancensa ya dauko tasha ruwan jikinta, sai da yakai qarshe yace "inason Jin abunda yake ranki Na'ima karki ji nauyi na, Uba nake a gurinki, wannan batu ne na rayuwar ki, ke zakiyi rayuwan auren dan haka kina da 'yancin fadin Eh ko A'a" sai a lokacin Na'ima ta dago kanta ta kalli Hajiya dake kallonta kyam cikin Ido itama tana tijaran amsarta, duqar da kanta ta sake yi sai ta gyada kai alamun "Eh" tanajin qunci da dabaibayeta, tayaya zasu ce zasu aura mata dansu wanda tana gani suma yana neman gagararsu, Albarka Alhajin shima ya rinqa saka mata yace ta tashi ta tafi, cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi fita daga falon suka dan bita da kallo, saida ta fita Hajiya na murmushi tace "Ma Sha Allah kaga abunda nake fada maka ko" Alhaji ya gyada kai shima yana murmushin, tace "yanzu dai kasamu lokaci kaje qauyen nan ko ka kira su ka sanar musu, yarinya ta amince me zamu jira kuma, Bilal dai munsan ta yanda zamu bullo masa shi" Alhaji yace "gaskiya ayyuka sun min yawa kwana biyun nan zan kira Ayuban yazo muyi magana" tace "duk daya ai, gaskiya banason abunnan ya dauki lokaci  Alhaji, ka biya masa sadakin ayi auren inyaso ko daga bayama ayi lefen" Alhaji yadan hada rai yace "meye kike cewa haka ne ladi, 'yar tawa za'ayiwa aure babu lefe" tace "toh ai naga ze dauki lokaci ne" yace "A'a ko zai dauki lokacin dai sai anyi mata lefe, ki yi lissafi sai in tura kudin, in kuma hakan ze cinye miki lokaci ga Sufi nan babu abunda bai iya ba" tayi saurin cewa "za'ayin ma Alhaji wane Sufi kuma, kamanta nima Na'ima 'yata ce, in Sha Allah komai za'ayi" da haka Alhajin ya miqe ta rakashi nan bakin falon sukayi sallama ya wuce gurin aiki driver na jiransa a waje, wayanta ta dauka tayi kira, ana dauka tace "kawata abun dai yanata tafiya as planned, nagode da wannan shawara taki" ta dayan bangaren larai tace "nafada miki ba wani wahala zakisha ba ai, yanzu na gama magana da dan haure ma, yace indai akayi auren nan to Bilal din ze zauna anan Kano, kawai dai ba lallai yaso yarinyar bane saboda har yanzu abun tsinannniyar can din be sake shi ba" Hajiya tace "ita wannan ya dama, tunda ze dawo gabana Ina kallonsa ai an gama komai kuma, batun son yarinya kuma ai dama baso nake ya so ta ba tun farko" larai tayi dariya sai Hajiyan ta sake cewa "har yanzu yananan be koma ba kamar an masa dauri aqafa" Larai tace "bazai kuma koman ba"..... Da taje makaranta ranan tana shiga class dinda zasuyi lecture din Nafisa ta dago mata hannu tareda kiran sunanta tana murmushi, qarasawa tayi ta zauna kusa da ita suka gaisa fuskan Na'iman babu yabo babu fallasa, Har aka gama darasin batasan me akeyi ba tayi nisa a tunani, da suka tashi ma sallama tayi da Nafisan tayi wucewar ta ranta babu dadi, tafiya kawai take har tazo bus stop din ta wuce batareda ta shiga ba kawai ta miqe da nufin da fita a qafa ko zata samu sararin yin tunani dan inta je gidan ji takeyi komai yana suffocating dinta, tayi nisa da tafiyan ne wata babbar Jeep ta faka a gefenta se tayi saurin juyawa tana goge idonta daya kawo hawaye, rolling glass din motar akayi Nafisa tadan leqo kanta tace "Na'ima shigo in rage miki hanya" sai Na'ima tadanyi murmushin dole tareda girgiza kai tace "A'a bakomai, ai na kusa isa titin ma" Nafisa tace "Ki shigo Dan Allah, meye haka kuma kinata tafiya cikin ranannan" matsawa tayi jikin motan tareda bude front seat , sai Nafisa takai hannu tana kwashe su biscuits, iphad, laptop da sauran gadgets dinta dake kan seat din tana dan dariya tace "sorry i made a mess" saida ta wullasu duka backseat sannan Na'iman ta shiga suka tafi, qin sauketa nafisa tayi a main gate din tace ta fada mata unguwarsu takaita, bayan Na'ima ta fada mata sai ta dan ware Ido tace " Muna neighboring area daku ashe" Na'ima ta gyada kai kawai batace komai, har qofar gida Nafisan takaita sukayi sallama sannan ta juya kan motanta ta fice daga layin... Da safe taje gaisheda iyayen nata ta samu Bilal zaune kujera kanshi a sunkuye Alhaji na tsaye akanshi fuskanshi ta nuna alamun bacin rai ga Hajiya nan zaune dai itama fuskanta babu alamun raha, da farko kasa qarasawa tayi saboda yanda zuciyanta ya tsinke saida Alhajin ya mata iso cikin fara'a sannan, aikuwa tana gama gaishesu ta miqe ta fice daga falon cikin sauri ta koma dakinta, tananan zaune aka banko kofar ta Bilal ya shigo, firgita tayi ganin ya kulle kofan ta nufi toilet da gudu yayi azaman fusgo gashinta dake daure cikin dankwali yayi baya da ita ta fada kan gado, kuka Na'ima ta fashe dashi ta matsa qarshen gadon tana kallonsa, cikin huci yace "ki fadamin dalilin da yasa kika fadawa iyayena zaki aureni, am i your mate?" Tayi saurin girgiza kai cikin kuka tace "wallahi ban fada ba yaya" Mari yakai mata a fuska, ta dafe gurin tana dan qara, ya sake cewa "what's that your name ma?" tayi shiru kanta a qasa ya sake mata diri "Answer me" jikin ta har rawa yake tace "Na'ima" yace "Good, your doom has began Na'ima" da haka ya juya ya fice daga dakin, kuka Na'ima ta fara har jikinta na jijjaga ta sulale anan kan gadon ta kwanta bata daina kukan ba, ranar ko makaranta bata je ba haka ta wuni cikin hawaye, duk kuma Hajiya na lura da hakan amma tayi biris..... Shirye shiryen Auren Na'ima da Bilal su Hajiya suka fara babu sanya, a lokacin da Alhaji Abdullahi ya kira ya sanar dasu kawu Ayuba murna sukayi not minding ya Na'iman take, sudai kawai tunaninsu Na'ima zata auri dan Alhaji liqafa ta cigaba, zuwa wannan lokacin Na'ima har rama tayi dan makarantar ma ta daina gane komai yanzu saboda tsantsan damuwa data shiga ciki akan auren, tun daga lokacin da Bilal din ya shigo mata daki kwanaki bata sake ganinsa ba, nan kuwa yayi magana da iyayensa akan zaije settling wasu sauran ayyukansa dake Lagos sai ya dawo kanon gaba daya, hakan be wani damu Hajiya ba sanin shirin da tayi masa akan hakan dan tasani Lagos ta kusa fin qarfin dan nata kuma, fagen lefen dai toh sai dai ace Alhamdulillah amma dai kam Hajiya tayi son ranta da kudi, ta siyo abunda taga dama sanin masu kallon kayan ma mutanen qauye ne kuma sai akayi sa'a Hajiya babba tana Abuja gidan danta alokacin da za'ayi bikin ma.. Sai ana gobe daurin Auren sannan Alhaji ya tura motoci guda biyu zuwa Adamawa adebo 'yan uwan nasa da matansu suzo bikin, ranar da zasu zo Na'ima kasa zama guri daya tayi bini bini zata dauko tsintsiya kamar me sharan varenda ta zauna nan bakin entrance din gidan ko zataji shigowansu, inta tuna zata ga goggo da Anty Amarya sai taji damuwan nata na sauqa kadan, dan tayi making mind dinta sai ta fadawa goggo batason auren nan da za'a mata, tasani in sauran kawunnan nata bazasu tsaya mata ba to goggo zata tsaya mata, gajiya tayi da jiran ta koma cikin gidan wanda babu kowa cikinsa banda tsirarun kawayen Hajiyan guda uku zuwa hudu, babu wata alama da zata nuna wa mutum wai biki akeyi na dan gatan gidan... Sai yamma suka iso duk a gajiye, Na'ima najin shigowan mota ta fita da sauri harda dan gudunta, ganinsu tayi sun fito dukansu suna bin gidan da kallo harda iyalin Nasiru suma, kawu Ayuba da Nasirun na fito da kaya daga boot, saurin qarasawa tayi gurin anty Amarya tanajin kuka na zuwa mata, rungumeta Anty Amaryan tayi tana murmushi, Umma dake gefe baki washe tace "Oh ni jummai, wai Na'ima ce ta koma haka" salame dake gyara goyon danta a baya tace "toh umma ke bakiga gidan bane, ai Na'ima ta huta itadai" sake anty amaryan Na'ima tayi ta koma gurin umma Amma bata rungumota ba amma ta riqo hannunta tana murmushi, Hajiya ce ta fito cikin isa Umma tayi sauri karbe hannun ta daga gurin Na'ima ta nufeta tana tace "Hajiya sannu da fitowa" Hajiya tace "yauwa sannunku da zuwa" sai ta kwala kira wa maigadi tace yazo su miqa kayan can BQ inda shafa take zama, sannu tayiwa su kawu Ayuban suka amsa cikin fara'a kamar ba ita tayiwa Ayuban rashin mutunci ba da dadewa, Na'ima sai rarraba Ido take tana jiran ko zata ga goggo acikinsu amma dai shiru sai tace da Anty Amarya "Ina goggo fa, bakuzo da ita bane?" Tsit gurin ya dauka kowa ya fara rarraba idanu, ita Hajiya sai lokacin ma ta tuna ashe zuwan Ayuba ya fada mata goggon ta rasu da dadewa, ganin kowa yayi shiru yasa Na'iman kwantar da murya ta sake tambayan antyn, sai Umma tayi saurin cewa "tana gida ai bata Jin dadin jikinta ne shiyasa ba'a zo da itan ba" sanyi jikin Na'iman yayi sosai a haka ta tayasu suka kai kayan can masauqinsu, da dare bayan sun gama dafa abinci da shafa ta tafi kai musu, tasamu duk sun kwamutsu nan falon suna hira, mazan kuma Alhaji yasa ankaisu nan wani gidansa dake cikin gari, Umma ce tace "Na'ima yaushe zamu shiga cikin gidan ne, duk mun matse anan din, gashi Hajiyan tace zatazo kuma shiru" batace komai ba ta ajiye musu abincin nan tsakiyar falon, salame tace "ni sai na lura ma kamar ba mutane fa, sai kace ba biki za'ayi a gidan ba" Umma tace "ko sai gobe zasuzo inaga, angon ne ma mukeson gani dan bamu taba ganinsa ba" nan kuma jikin Na'ima yayi sanyi, Anty Amarya ta fito daga bandaki ta zauna gefen Na'ima tace "ya kamar ba'a miki gyara ba Na'ima, Hajiyan bata kaiki gurin gyaran jiki bane" nan ma batace komai ba dan tasan inta bude baki to kuka ne zezo shiyasa... Zuwan da Hajiya batayi ba kenan gashi Na'ima nason Jan salame suje dakinta amma tana tsoron Hajiya tayi mata fadan haka, sai tayi deciding ta kwanta nan tare dasu amma umma tace gurin ya musu matsi ta tafi,. Washegari ranar daurin Auren Hajiya ta kirata da safe ta miqa mata wani lace tace in tayi wanka ta saka, haka ta karba tayi godiya ta fice, Ranan ba qaramin dauriya Na'ima tayi ba gurin danne abun da takeji a zuciyarta, Lokacin da Anty Amarya ta fada mata an daura auren ji tayi iskan qirjinta ya mata kadan, kawai ta shige bandaki ta sulale jikin qofan tana kuka mara sauti, dasu kawu Ayuba da Alhajin suka kirata yi mata nasiha bata ma fahimtar su, dan abunda takeji ya wuce tunani, su Umma jummai dai anan Bq suka qare bikin dan Hajiya bata bar ko dayansu ya kwana cikin main building ba sai dai suje gaisheta sukoma, wannan abu ba qaramin daurewa daurewa Anty Amarya kai yayi ba amma sanin tanayin magana mijinta ze ce ba haka ba

Chapter 16 of 19