da alaqan a aikace bada baki ba", hannu nafisa takai ta dan kwankwasa glass din Na'ima ta farga da ashe tana kallonsu, ta danyi saurin shiga gaban motan Ahmad ya rufe ya zagaya ya shiga suka wuce..
Shiru motan yayi Nafisa dake baya taqi cewa komai dan dama itace mai fara hira a motan to yau itama tayi shiru tana kallonsu, driving dinsa kawai Ahmad jefi jefi yana kallon Na'ima datayi shiru itama tana facing window, can yadan juya kansa back seat yace "bude muku abincin nan Nafisa", dauko ledan nafisa tayi ta dauki nata burger da ruwa sannan ta miqawa Na'iman tace "mungode yaya" baice komai ba, Na'ima ta ciro sai kuma ta miqo masa tace "zakaci?" juyowa yayi ya kalleta da dan murmushi a fuskansa yace "rowa zakimin" Na'ima tayi murmushi sannan ta girgiza kai tana qara miqo masa, kallon ta ya danyi sai kuma ya maida hankalinsa kan tuqinsa yace "naqoshi", bata ci sosai ba ta maida sauran burgern cikin box dinsa tafara karkade hannunta, zaro tissue Ahmad yayi daga ma'ajiyinsa ya miqa mata ta amsa tareda muttering "thanks", Nafisa dake baya tana kallonsu ta jijjaga kai tana murmushi ta miqo hannunta ta zari tissue din itama....
Saida suka ci rabin tafiyan sannan suka tsaya a wani gas station dake cikin wani town nan kan hanyan tafiyar tasu, fita Ahmad yayi zai qara mai a motan, Nafisa ta dan matso gurin Na'ima tace "sis bari naje restroom" Na'ima tacire seatbelt dinta ta juyo tace "bari na rakaki" girgiza kai Nafisan tayi tace "kijiki sai kace wata yarinya, yi zamanki yanzu zan dawo, mezan siyo miki cikin restaurant din" Na'ima ta jijjaga kai tace "naqoshi, Dan Allah karki dade" dan murmushi kawai Nafisa tayi ta fita daga motan, fadawa Ahmad dake tsaye yana filling motan inda zataje tayi, ya gyada kai yana cigaba da abunda yakeyi.
Bayan yagama ya shigo motan ya zauna batareda ya rufe kofan ba, rasa abun fada Na'ima tayi saitaga ya juyo gurinta a nutse yace "how have you been?" dago kai tayi ta kallesa tace "I'm fine" yasake cewa "ya karatun ku" tace "Alhamdulillah" sukayi shiru , ahankali tace "I'm sorry " yana kallonta yace "what for?" tadan sunkuyar da kanta tace "for what i said the other day" tajira jin amsansa sai kuma taji baice komai ba, dago kanta ta sakeyi suka hada ido tace "I didn't mean what i said" shima ahankali yace "I'm sorry too" bata kai ga tambayansa meyasa ba taji Nafisa ta bude kofan ta shigo, gyara zama Ahmad yayi ya rufo qofan shima ya tada motan suka tafi...
Isarsu gidan anty Amnah suka samu batanan taje asibiti, dayake sunsan pin din kofan yasa basu damu ba, Ahmad bai shiga gidan ba yace "ku gaisheta inta dawo" Nafisa tace bazaka shigo ka sha ruwa ba" ya girgiza kai yace "No" yana kallon cikin idon Na'ima yace musu "take care" Nafisa ta gyada tayi godiya, Na'ima tace "Mungode" itama, gyada kai yayi yakoma gun motarsa ya tayar yabarsu nan tsaye, Nafisa tabi baya motan da kallo tace "sai na karbo motan nan munje school da ita" Na'ima ta kalleta tace "kije dai bandani, daga ganin mota kin gigice nafisa" Nafisa na dariya tace "yarinya bakisan motan bane" jijjaga kai kawai Na'ima tayi suka wuce cikin gidan.
Sai yamma anty Amnah tadawo tareda twins data biya school dinsu ta daukosu, zuwa lokacin su Na'ima sunyi sallah sun huta har sun dafa musu abinci..
Suna zaune a falon ta shigo alamun gajiya bayyane jikinta tace "yan makaranta kun iso?" basu kai ga amsawa ba twins suka buga tsalle sukayi kansu, dariya Na'ima ta fara bayan sun danneta tace "oyoyo darlings" nan gurinsu Anty Amnah ta zauna tana kallon Na'ima tace "sai sun ballaki ai, Kai ku sauqa daga kanta" Na'ima tayi dariya batace komai ba
Gaisheta sukayi ya amsa tace da nafisa "How far..ya jikin naki?" Nafisa ta gyara zama tace "naji sauqi anty, gidannan kamar da magic cikinsa, sai naji na warware" dariya anty Amnah tayi sanin da hadin bakinta Nafisa tayi qaryan rashin lafiyan, tace "toh Allah ya qara sauqi" Na'ima tace "Anty akawo muku abinci ko sai kun huta" Anty Amnah ta dan girgiza kai tana murmushi tace "a'a daughter ki barshi zamuje muci, thank you"
Itadai tun ranan farkon ganinta da Na'ima take sonta, zamansu da ita kuma ta sake fahimtan dayawa daga cikin halayen yarinyar wanda a lokaci da dama takanyi ta tunanin ta Ina yarinyar ta gaza da har abubuwa suka faru da ita haka?, kallon Na'iman tarinqa yi wadda ke biyewa hiran twins batasan ma san tanayi ba, ganin zata dago kanta yasa anty Amnah tashi ta wuce dakinta zuciyanta cike da tunani...
Da daddare suna having dinner tareda uncle yasir shima, yace "kuyi zamanku anan ku qarasa karatun naku kunji" Anty Amnah tace "nima haka nace fa" Na'ima tayi shiru tana jiran Nafisa ta basu hakuri akan zasu koma sai taji akasin haka dan Nafisa cewa tayi "toh uncle in Sha Allah" dan dago kai tayi tana kallon Nafisan datake cin abincin ta hankali kwance, Uncle yace "yauwa ko ku fa, trains din yanzu suna gudu sosai dan within awa daya da rabi ma zakuga kun isa, ko ya kika ce Na'ima?" ya qarasa maganan yana kallon Na'ima, gyada kai tayi ahankali tace "toh uncle" yace "ma Sha Allah, ai kun fara dissertation dinku ba?" Nafisa tace "A'a uncle muna kan yin research akai ne" yace "Allah ya taimaka, hope kunada group mates" Nafisa tace "Eh uncle" anty Amnah ta sake tambayan Na'ima da "kema kin samu group mate dinne daughter?" sai sannan Na'ima ta dago kanta tace "Eh anty akwai kawata da zamuyi research din tare" Anty Amnah tace"ma Sha Allah, Allah ya baku sa'a" suka amsa da Amin...
Bayan sun koma dakinsu basu yi magana ba, Na'ima ta shige toilet ta bar nafisa na rage kayan jikinta, bayan ta fito tasamu har nafisan ta kwanta, changing tayi itama cikin kayan bacci ta zo ta zauna bakin gado tace "Nafee we need to talk" Nafisa tadan yaye blanket din daga kanta ta dago tana gyara zama tace "inajinki meya faru?" Na'ima na kallonta tace "are you hiding something from me nafisa?" Nafisa ta girgiza kai tace "haba dai..A'a kam, me kika gani" Na'ima tace "komai ma doesn't sit right with me nafisa, all of a sudden kince kin samu sauqi ko magani baki sha ba sannan uncle sunce muzauna bikiyi protesting ba kai tsaye kika yarda, kamar ba ke bace nafisan da nasani batason zirga zirgan tsakanin Oxford da London, what happened to you ?" Nafisa tadanyi murmushi tace "Kiji ki da wasu zance, dan na yarda mu zauna shine akwai abunda ke damuwa?" Na'ima bata komai ba ta qura mata Ido, dan matsowa Nafisan tayi kusa da ita ta riqo hannunta tace "habaa mana sis, kinsan ban taba boye miki abu ba fah" dan jijjaga kai Na'ima tayi tace "ai komai yanada mafari nafisa, nasani ko kin fara boyemin abubuwan da suka shafeki" Nafisa ta sake damqe hannun Na'iman tace "babu abunda nake boye miki, for better for worse kinsani you're my best person in this world" Na'ima ta gyada kai tace "nima haka, kawai banason changes din nan danake gani gurinki ne kwana biyun nan, you look strange" Nafisa tayi dariya tace "bawani changes Bobo" itama Na'iman dan dariya tayi tace "yanzu zamu zauna anan din kenan?" Nafisa tace "Eh..Amma in bakyaso sai mu koma" Na'ima tadan ware ido tace "A'a ni bance banaso ba, ai nan yafi ma" da haka suka fara hiransu da suka saba Nafisa ta ware suna surutu, dan dama shiru shirun nata bana Allah da Annabi bane...
Kiran Mami neh yashigo wayar Nafisan, tadan dakata da magana suna kallon fuskan wayan itada Na'ima, bayan ta daga sun gaisa daga dayan bangaren Mami tace "Baby nayi waya da maman twins tace min kunzo saboda baki da lafiya" Nafisa tace "Eh Mami banajin dadi ne" Mami tace "to kuma shine waninku bazai kira a fada mana ba, tun yaushe ne bakida lafiyan kuma me yake damunki?" ta amsa da "kwana biyu dasuka wuce ne fa Mami kuma na dan ji sauqi ma yanzu, dama ciwon kai ne sai kuma dan fever haka" Mami tace "toh Allah ya qara sauqi, tace min zaku dan zauna anan gidanta tunda ba wani lectures kukeyi a school din ba" Nafisa ta gyada kai tace "Eh..yasu Abba fa?" Tace "yananan lafiya bana kusa dashi, Ina Habibti fa bata muyi magana" miqawa Na'iman wayan tayi, bayan sun gaisa Mami tace "Habibti shine kuka qi kira ku fada mana babu lafiya" Na'ima tace "kiyi hakuri Mami wallahi na zata ta fada muku ne shiyasa ban kira ba" Mami tace "Antyn kuce ta kira ta fadamin, ya kuke toh, ba matsala ko" Na'ima tace "In Sha Allah Mami yasu Abba?" ta amsa da "lafiyansu kalau, kuyi zamanku nan gidan maman twins din tunda bakwa yawan shiga makarantan" tace "toh Mami in Sha Allah" da haka sukayi sallama tace su kirata fa in wani abun ya sake tasowa...
Basu je school ba washegari daya kasance Friday sai suka hutawan su suna taba karatun, dan anty Amnah ma ta fice gurin aiki ita da mijinta haka zalika twins Suma suna school....bacci Na'ima tayi mai dadi sannan ta tashi tayi brush da wanka ta shirya cikin qaramin riga da dogon straight skirt ta fice falon, Nafisa ta samu tana cin abinci taja kujera ta zauna tace "shine baki tadani ba, inata bacci har yamin yawa" nafisa ta zuba mata madara a cup ta miqa mata sannan tace "nima fa yanzu na tashi, masu gidan duk sun fice" gyada kai na'ima tayi takai cup din baki ta kurba tace "nafisa kaina yayi datti ki wankemin ko muje salon" Nafisa tace "wallahi kanki akwai wahalan wankewa, danayi miki last time fa kince salon zamuje next" Na'ima tace "toh ai yanzun ma cewa nayi ko kimin ko muje salon" Nafisa ta dan harareta sanin Na'iman tafison wankewan kawai fadan salon din take, dariya Na'ima ta farayi ta ajiye cup din tana kallon Nafisan tace "Dan Allah ki wankemin kinji sisi na" saikuma itama Nafisan tafara murmushi tace "toh zaki yarda ki rakani gidan yaya Ahmad ranan Sunday" tsaf Na'ima ta dinke fuska tace "ni narasa dalilinki na sai munje gidansa, kin fara maita ne bansani ba nafisa?"
Nafisa ta kwashe da dariya tace "bawani maita, ni nazata ma straight zaki amince ganin irin kallon da kukewa juna jiya" Na'ima ta harareta tace "banaso nafisa, ni yaushe na kalleshi?" Nafisa tadan ware Ido tace "lallai ma yarinyar nan kin rainawa kanki hankali ba ni ba, iyeee..sannu Na'ima" ta sake wani dariyan ta cigaba "ku gama kallon juna cikin soyayyar a gabana shine yanzu zaki wani kawo min wata maganan yanzu" Na'ima ta ajiye bread din hannunta ta miqe tace "barmin gashin nawa ya rube toh, soyayya kuma halan kin fara ganin komai a baibai ne cikin lamuranki yanzu" ta qarasa maganan tana wucewa daki fuskanta dauke da alamun murmushin da nafisan bata gani ba, Nafisa tayi wata dariyan tace "Muna tafe dai Na'ima"....
Bintu Musa ce ✍️📚
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
ArewaPen https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
WhatsApp group
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 19
Ranan Sunday babu yanda Nafisa batayi da Na'ima akan ta rakata suje gurin Lauren data shigo garin ba taqi, Na'ima tace "Nafisa da ban sanki bane sai in yarda dake" Nafisa tana murmushi tace "kinji narantse ba gidan yaya Ahmad zamuje ba, ai tunda bakya son zuwa kuma na hakura" Na'ima ta jijjaga kai tana qara jawo laptop din gabanta batace komai ba, Nafisa ta zauna kusa da ita tasake cewa "haba mana Na'ima" still bata kulata ba tasake cewa "NA'IMAA" still dai ko a jikinta, nafisa bata hakura ba ta sake cewa "Na'ima Yusuf Dabo" sai sannan ta dago kanta ta kalli Nafisan tace "ita Lauren din kullum ne take zuwa London wai" Nafisa tace "shikenan kartayi yawo tana matsayin influencer" Na'ima tace "toh ai yau batanan gobe bata can ne gashi tanason ku rinqa yawon tare" Nafisa tace "wallahi kam, tace wai muje Licester jibi ma, amma bazan samu zuwa ba munada group research ranan nida teammates dina" Na'ima ta girgiza kai tace "toh meyasa kike binta ne ma wani lokacin" tace "Ha'a shikenan bazanyi yawon ganin duniya ba Na'ima, bature fa yace all work without play make jack a dull boy, hausawa ma sunce taba kidi taba karatu" Na'ima ta cigaba da duba abunda take typing tace "toh nidai bandani, inkinga nafita to sai gobe Monday zuwa school" Nafisa tace "toh kizo muje daganan sai mu biya salon a wanke kai din" Na'ima najin haka ta amince dan dama ta gaji da kan tana babu wanki...bayan sun shirya suka ari motan anty Amnah dan tasu sun barota can oxford daman, dagasken kuma gurin Lauren din sukaje , sun sameta a wani restaurant babba, Lauren tayi musu ordern abinci already, itada nafisa suka hau baza magana, itadai Na'ima sai bin abincin take da kallo taqi ci dan har wannan lokacin bata saba da ire iren abincin qasar ba, tanadai cin wasu amma batacin nama a kowanne restaurant gudun abata haramtaccen nama...Lauren ce ta juyo ganin batacin abincin tace "what happen ne'ima" Na'ima tadanyi murmushi tace "I can't eat this" ta qarasa maganan tana daga hannu a waiter, sake order tayi na simple dish "fish and chips" ...
Salon din sukaje aka wanke musu kai harda Lauren din, tun kafin a fara wankewa Lauren din kai tafara video har qarshe, Rashin sabon ganin hakan a gurin Na'ima yasa ta dan kalli Lauren ta jijjaga kai tana dan murmushi da mamaki ganin komai nata yana media,Nafisa tunda ta samu wayanta bata kula da batun surutun Lauren ba ma....gashin Na'ima ba qaramin kyau yayi ba daya sha gyara aka daure mata shi in a dough, ita aka fara gama wa gyaran dan nafisa har da kitso za'a mata ita kuma Lauren za'a mata qari sosai..
Sai yamma suka koma gida bayan sun yi sallama da Lauren tace zata kawo musu ziyara nan gidan anty Amnahn
Isarsu gidan suka samu motan Ahmad fake a kofar gidan, Nafisa ta kalli Na'ima tace "iyee sai ga yaya Ahmad yadawo, shida yake wuyar ganuwa" Na'ima tace "ba kince dan'uwanku bane, ko dai banji da kyau bane lokacin da kikace cousin din ku ne" Nafisa ta fara dariya tace "wallahi in zan kwana Ina fadawa mutane iya yanko baqar maganar ki baza'a yarda ba" Na'ima ta danyi murmushi tace "ni me nace kuma" Nafisa ta nufi gidan tana dan dariya tace "babu..Amma kinsan dai inason alaqan ku ko sis, like seriously kuna burgeni, the match was perfect, ke fara shi fari ke dogon hanci shima haka, ga kyau Allah ya baki shima haka....soyayyarku me shirun nan tana burgeni Na'ima" itadai Na'ima tarasa me zatace a farko sai kuma a hankali tace "Nafisa bazan iya soyayya ba, besides Ahmad can't handle a messed up person like me" Nafisa ta dan dafa kafadanta tace "Haba Na'ima...kiyi living rayuwanki, ki ajiye duk wani batun abun da ya faru a baya ko wani auren da kika tabayi, idan anzo wannan ramin Ina tabbatar miki zaku tsallaka tare indai yana sonki, yaya Ahmad mutumin kirki ne kuma kinsan shine the right person da zai iya standing up to mahaukaci irin Bilal dasu Hajiya" Na'ima ta jijjaga kai hawaye na kawowa idonta tace "kinsan nakasa yarda har yanzu baisan inda nake ba nafisa, bansan me yake shiryamin ba kuma tunda yace duk inda naje sai yadawo dani gidansa" Nafisa tace "wannan ne kuma bai isa ba, shidin banza, Allah ya fisa wallahi, ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru" Na'ima tayi shiru tana kallon kofar gidan anty Amnah, Nafisa ta riqo hannunta tace "mu shiga sis, babu komai, shi bai isa ya hanaki son wanda kikeso ba wallahi" Na'ima ba biye da ita batace komai ba suka shiga gidan...
Zaune suka samu Ahmad shida anty Amnah a falon ga twins a kusadashi, suna hada Ido da Na'ima taga murmushi yayi mata sai ta samu kanta da maida masa murmushin itama, zama sukayi nan falon suma suka gaishe sa ya amsa idonsa akan Na'ima da itama kallonsa take jefi jefi, twins ne suka bar jikin Ahmad suka dawo jikinta, Jafar ya miqa mata popcorn din hannunsa akan taci, diban biyu tayi takai baki, anty Amnah tace "anyi wankin kan?" suka amsa da Eh, hawa jikin Na'ima jabeer yayi ya ja gyalen abayan nata atake gashinta ya bayyana yace "anty muga naki" ta dan ware Ido zata karbi gyalen Jafar dake jikinta ya ja ribbon din shima yace "anty naki yayi kyau", Anty Amnah tadan musu tsawa tana cewa "wallahi zan saba muku in baku daina wannan haukan ba, my friend maida mata gyalenta" saurin karban gyalen Na'ima tayi ta maida kanta, ribbon din kuma ta riqe a hannunta kunya duk ta rufeta ta juya ta kalli Ahmad da tunda abun ya faru yake kallonta, dauke ido tayi ta miqe zata tafi daki, yabi bayanta da kallo, nafisa ma miqewa tayi ta dunguri twins din daya bayan daya tace "marasa ji kawai" Anty Amnah tace "sai na mammakesu tukunna, wato kun rainata ko" hakuri suka bawa maman tasu suka koma jikin Ahmad da baice komai ba yananan zaune yana danna wayarsa....
Ranan Monday sun tashi zasuje school suna breakfast anty Amnah tace "jiya yayanku yace zai turo akaiku school din aiki sun dan riqesa bazai samu kaiku ba" Nafisa tace "Anty a yanayin aikinsa in mukace yakaimu makaranta ai mun taqurasa daman" Anty Amnah tace "nima hakan na fada masa" Na'ima batace komai ba tana sauraransu while tanacin abinci gabanta..
Drivern da Ahmad din ya aiko ne ya kaisu har cikin makarantan yace musu zai shiga cikin town din akwai uzurin da zeyi sannan yadawo daukansu, suka amsa da "babu damuwa" ...
Bayan Na'ima ta hadu da zara sukaje library duban wasu takardu ne take fada mata yanzu tana London da zama ba oxford ba saidai zata rinqa qoqarin zuwa suna research din nasu tare in Sha Allah, dayake itama zarahn tana yawan zama a London din tace mata karta damu zasu rinqa haduwa acan ma bawani abu..
Bayan sun koma ne ranar Thursday da safe sai ga kiran zarahn a wayan Na'ima akan tana cikin London din su hadun.
Na'ima ta shirya cikin black abayanta dayake sanyi yadan fara sauqa sai ta saka jacket din da laptop dinta cikin jakanta na goyon kafada, Nafisa na kwance a gadon tana duba wani littafi hannunta riqe da chocolate tace "Dan Allah na'ima karki manta da dunuts dinnan, zan kiraki ma" Na'ima ta gyada kai tana zuge jakan tace "zan siyo miki dai bazan manta ba" Nafisa ta sake cewa "Dan Allah ki siyo na gurin da mukaje ranannan yafi dadi wallahi" gyada kai Na'ima tayi ta miqa hannu ta wafce chocolate din hannun Nafisa tasaka a jaka tana murmushi tace "I'll take this" Nafisa tace "naji..nidai karki manta" sallama sukayi Na'ima ta fice, study room din Abban twins ta shiga tasamu anty Amnah zaune nan gabanta akan desk din kuma laptop ne da wasu manyan takardu tana dubawa , qarasawa ciki tayi a nutse tace "Anty zanje study group meeting" Anty Amnah ta dago tana cire glass din idonta tace "Okay, zarahn tana garin nan din ne" Na'ima tace "Eh itama tana zama gidan yayanta" gyada kai anty Amnah tayi tace "Toh..hope dai zaki fita da wayanki" Na'ima ta amsa da "Eh" taciro wayan daga jaka ta nuna wa antyn, Anty Amnah tace "yauwa daughter, ki kiramu fa if something came up, London is a big city, be careful, Allah ya bada sa'a" Na'ima ta gyada kai ta amsa da "Amin" sannan ta fice..
Uber dinda tayi booking ne yazo ya dauke ta har nan qofar gida inda take tsaye, A wani babban shahararren Cafe ta hadu da zarahn, hugging dinta zarahn tayi tana fara'a dan tanason Na'iman tun farkon haduwansu a school din, kawai Na'iman ce bata yawan kulata, a wani seat dake lungu suka zauna suna facing din juna, saida suka gama gaisawa zarah tamusu order na mocktail, da waitern ya kawo musu Na'ima ta tambayesa wifi password din su ya fada mata dan sunsan cafe din yana offering free wifi ne ma shiyasa sukayi deciding su hadu anan din, nan take suka bude laptops dinsu suka fara abunda yakawosu, suna discussion din sannan suna rubutu..
Hankalin Na'ima yayi nisa cikin abunda take typing zarahn ma haka, saida takai qarshen abunda take rubutawa din ta dago hannunta tana matse yatsunta da suka danyi tsami, bin Cafe din tafarayi da dan kallon ganin mutane sun dan cika wanda bata ma lura da hakan ba.
Idonta ne yafada cikin na Ahmad yana kallonta while yana sipping coffee, zaune yake da wasu maza su uku shi cikon na hudu yana facing din table dinsu Na'ima, tun shigowansu ya ganta amma hankalinta na kan laptop din gabanta bata lura ba, jefi jefi yake kallonsu while suna dan magana da abokan nasa, sai yanzu idon Na'ima yakai garesa...jitayi komai nata ya tsaya da irin kallon da yake mata, itama sai ta tsaya kallonshi, coffee din hannunsa ya ajiye still yana kallonta, zarah ta dan tabo ta sannan ta dauke idonta tace "Uhm" zarah tace "what happen?, you seem lost" Na'ima ta girgiza kai tace "No.. it's nothing" zarah tace "take a look at this, I don't understand this line" ta qarasa maganan tana juyo fuskan laptop din nata ma Na'ima, bayan Na'ima ta karanta suka fara magana akai, bata sake yarda ta kalli inda Ahmad yake ba,
Miqewa su Ahmad din sukayi bayan sun biya tab dinsu suka nufi hanyan fita Na'ima ta dan kallesa taga magana yake hade da murmushi shida daya daga cikin abokan nasa, fita sukayi tana kallonsu sannan ta maida hankalinta kan abunda takeyi
Saida suka sake spending wani 40 minutes din cikin Cafe din sannan suka fara tattara kayansu zasu tafi, sunje biyan kudin abunda sukaci ne akace musu ai an biya musu, zarah ta tambayeta waye ya biya, Na'ima tace mata yayanta ne..
Fitansu daga cikin Cafe din ta hangoshi tsaye jikin motansa hannunsa daya cikin jacket din jikinsa while dayan yana duba wayansa, dago kai yayi ya kalleta sai ya gyara tsayuwansa itadai duk ta tsaya tana kallonsa, zarah ta tambayeta ko shine yayan nata, ta gyada mata kai sannan suka qarasa gurinsa zarah nata fara'a ta gaishesa ya amsa shima babu yabo babu fallasa, sallama tayi da Na'iman ta tafi, Na'iman na daga mata hannu sannan ta juyo ta kallesa, murmushi kawai tayi a nutse tace "for how long kake tsaye?" Shima yana kallonta yace "ban dade ba" tace "kun kusa kai hour da fita fa" ya dago hannunsa ya duba wristwatch dinsa sannan yace "bansan lokacin ya tafi haka ba" dan girgiza kai kawai tayi batace komai ba tana murmushi, shima murmushin yayi bai ce komai ba, can kuma a hankali yace "I'm still making you uncomfortable ko" Na'ima tadan turo baki tace "nafa baka hakuri ranannan" yadanyi dariya yace "I like that you feel this way around me" juya kanta tayi tana murmushi, ya miqo mata safunan hannu daya ciro cikin aljhun jacket dinsa yace "here, put this akwai dan sanyi yau din" karba tayi tafara sakawa ta kalleshi tace "kaifa?" ya girgiza kai kawai baice komai ba, bayan tagama sakawa ne ya dan matso yana kallonta a hankali yace "you're beautiful Na'eemah", maganan nashi yayi taking nata by suprise ta kallesa tana murmushi, ya rinqa kallon idanunta shima yana murmushi yace "you have beautiful Eyes" ta kai tafin hannunta ta rufe fuskanta tana dan dariya, ji yake kamar ya kamo hannun nata amma sanin bazata so hakan ba yasa beyi ba, sai yace"Ina wayanki fa" ta bude fuskan nata takai hannu jakanta ta ciro wayan ta miqa masa ya karba, dama babu password akai daya bude, yayi danne dannensa saiga kira yashigo wayarsa sannan ya miqa mata wayan ta karba, a hankali yace "that is my number, kiyi saving kinji" Na'ima ta gyada kai tana kallon numbern,yana kallonta ya sake cewa "kin gama karatun yau din?" ta amsa da "Eh" sai yace "Okay let me take you home" sannan ya bude mata front seat din ya karbi jakan kafadan nata, saida ta shiga sannan ya miqa mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 19