Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da komai ku ba kutare ba, banaso haka kunajina ?" suka amsa da "toh" Mami tace da faruk "kuma fa tsaf nake hadawa Al'ameen daddawan in qulle masa yatafi da ita Toronto baya wani zancen wari" faruk yace "Al'ameen kikace Mami ba mai bakin rezan nan ba" Nafisa da Na'ima suka fara dariya... Ana gobe zasu tafi Na'ima na tsaye gaban madubi a dakin nafisan tana tattare mata mayukan da zata koma dasu, wasu oil ta dauka ta juya gurin nafisa dake zaune kan gado hannunta da waya tace "zaki koma da wannan?" Nafisa ta dago kai ta kalle ta tace "a'a inada wannan acan" ta maida kanta kan wayan tacigaba da dannawa. Deban wasu mayukan na'ima tayi a hannunta ta nufi gurin akwatin nafisan datake mata arranging kayan tace "har zamu koma baki hadu da umar ba nafee, meya faru ne?" Nafisa ta ajiye wayan hannunta tana kallon Na'ima tace "we broke up since" Na'ima dake arranging kayan cikin akwati ta dago ta kalleta tace "you're taking a break dai, badai break up ba" nafisa ta gyada kafada tace "Dagaske im done with that guy kuma, i need my sanity, it's high time infara prioritizing peace of mind dina na'ima" Na'ima dai sai kallonta take sanin it's a big decision for her, aranta tana ayyano yanda nafisan keda kyau, gata, kudi amma sai Allah bai sa mata sa'a akan soyayya ba, namijin da bai kai ba yake juya zuciyar kawartata son ransa.. miqewa tayi ta zauna kusada nafisan cikin kwantar da murya tace "but are you okay with this decision?" Nafisa ta gyada kai tace "tunda mukayi fadan nan nayi blocking dinsa, he makes no efforts akan gyara relationship din, zanyi ta bata lokaci na ne akan someone that will not make effort to have me neh Naima?" Na'ima tadan riqe hannunta tace "it's okay...Ina bayan duk abunda kikeso ko kikayi deciding..in umar ba alkhairy bane a cikin rayuwanki a sannu Allah zai kawo wanda yafishi, the one that will make the most effort to love you earnestly" Nafisa tayi murmushi tana riqe da hannun Na'ima tace "thank you sis, you know I'm grateful to have you in my life right?" Na'ima tayi murmushi tace "me to nafee" ta miqe tana kama kunkumi tafara bin dakin da kallo tace "saura me kuma zan hada miki, banason sai mun koma ki fara mitan bakiga wasu abubuwanki ba" Nafisa tayi 'yar dariya ta koma ta kwanta tace "toh mummy na'ima,kin sakamin inner wears din" na'ima ta gyada kai ta sake komawa bakin madubi tana duban ko akwai abunda zata qara dauka... Washegari ya kasance flight din sha dayan safe garesu, dawuri suka tashi kasancewan na'ima anan dakin nafisan ta kwana yasa bayan sun idarda sallah suka wuce dakin Mami tare Zaune suka sameta kan sallaya dan yawanci in Abba yatafi masallaci ita dakinta take dawowa tayi nata sallan..bayan sun gaisa Mami tace "kun gama shirya kayan naku dai ko, dan banason mantuwa" Na'ima tace "Eh Mami in Sha Allah" nan suka zauna tare da mamin sukayi azhkar dinsu da karatun qur'ani, Mami na musu nasiha akan makarantan dazasu koma.....Karfe goma saura suka shiga falon Abba, sun sameshi zaune kan zujera hannunsa riqe da cup din tea yana hira ya samarin gidan, na'ima ce ta fara zama a qasa nan kan carpet sannan nafisa ta bi bayanta suka gaishe da Abban, yana murmushi ya amsa gaisuwan sannan yace "yaran Abba kun shirya ko" suka amsa a sanyaye, Abba ya sake cewa "Toh, Allah ya kaiku lafiya, Allah ya bada sa'an karatu" suka amsa da Amin, Abba ya cigaba.."banason wasa, kumaida hankali akan ibadunku da karatu, I'm very proud of how hard kuke maida hankali ga karatun amma ku qara himma, sannan a batun ibada kuma nasan indai akan tarbiyan da muka baku ne banida haufi akan kuna maida hankali, Amma tunda ba'a gabanmu kuke ba inason kuji tsoron Allah ku maida hankali akan sallolinku, Allah ya muku albarka.. we'll surely missed you" kasa amsawa nafisa tayi ta miqe ta qarasa gurin Abban tafara kuka tana riqe hannunsa, ajiye tea cup din yayi ya bude mata hannunsa ta fada jikinsa tana kuka, Abba yana dan buga bayanta yace "saura kadan ai daughter, besides zamuzo celebrating gamawanku ai" , idon na'ima itama ya kawo hawaye tananan zaune, Mami dake zaune kan kujera a gefe ta bude nata hannun tace "Zo Habibti" tashi na'ima tayi ta qarasa gurin Mami itama ta shige jikinta tana hawaye, barin jikin Abba nafisa tayi ta koma jikin Mami itama tana sake wani kuka, Al'ameen da Abubakar suka koma gurin Mamin suka tsaya jikinsu duk yayi sanyi, Faruk yace "kukan nan ya isa ku tashi mutafi kafin lokaci ya qure" suka dago daga jikin Mamin tana goge musu hawayen tace "saura kadan fa yarana, ku maida hankali kunji, sannan ko menene yafaru ku kiramu, it's just a call away" Haka su na'ima sukayi sallama da iyayen nasu cikin sanyin jiki, faruk ya tisa qeyarsu mota, maigadin gidan ya qaraso ya taya su Al'ameen saka kayansu a booth, tare suka tafi dasu Abubakar airport din, suka bar Mamin da Abba nan tsaye bakin entrance din gidan suna daga musu hannu Zaune suke a waiting lounge suna jiran lokacin tashin jirginsu yayi, Nafisa tace "Abu please siyo mana abun tabawa, banason zaman shiru" miqewa Abubakar yayi ta sake cewa "ice coffee please" ya tambayeta flavor din da takeso ta fada masa ya juya gurin na'ima itama ta fada masa kalan wanda takeso, miqewa Al'ameen yayi suka tafi tare. Sunanan zaune Na'ima ta hango shigowar su Ahmad gurin shida Adam kafadarsa rataye da jaka while Adam jaye da qaramin akwati, sai Laila dake biye dasu itama, kauda kai na'ima tayi daga kallonsu, Faruk ne ya fara miqewa ya isa wajensun yana miqa musu hannu sukayi musabaha sannan su na'iman suka miqe suma, nafeesa tace "ita kuma wannan me kama da mayun ko meye na biyosu airport oho" Na'ima na jinta bata ce komai suka qarasa wajenda su Ahmad din suke tsaye, gaishesu sukayi Ahmad ya amsa yana kallon Na'ima wadda itama yau tayi nata jarumtar ta kallesa, baifi na few seconds ba Na'ima ta dauke idonta jin yanayinta na canjawa ta juya tana kallon Laila dake kallonta itama, samun kanta tayi da qin saka mata gaisuwa ta kuma dauke kai... Adam yace "yan makaranta, za'a koma kenan" nafisa tace "wallahi kuwa yaya, kuma London din zakuje ne?" Adam ya nuna Ahmad daya maida hankalinsa kan waya yace "ga Mai tafiyan nan ai" Nafisa ta kalli Ahmad tace "Ashe flight dinmu daya yaya" Ahmad ya dago kansa daga danna wayan, cikin nutsuwa yace "It seems so..kuma flight din 11 dinne?" Nafisa ta gyada kai tace "Eh" sannan ta juya ta na kallon Laila, in a mocking way tace "hajiya Laila..kema London din kika nufa ne?" A daqile Laila tace "A'a" tana dan qara matsawa kusa da Ahmad, Na'ima na kallonsu... kallonta Ahmad yayi suka hada ido sai taga yadan matsa daga kusa da Laila still bai daina kallon idonta ba, Na'ima ta kauda kanta jin zuciyarta namata wani iri ta koma kallon mutanen dake wucewa. Su Abubakar ne suka qaraso wajen hannunsu riqe da ice coffee, Adam yace "wannan kuma fa, nasu waye?" kafin nafisa ta amsa Laila ta rigata miqa hannu ta karbi duka cup biyun dake hannun Abubakar tace "Abunda naketa craving this days..thanks" Nafisa ta dan harari Lailan ta karbi na hannun Al'ameen, Abubakar ne yace "Anty Laila ki riqe nawan amma vanilla flavor din na Anty Na'ima ne" Laila tace "Oh sorry" ta miqawa na'iman, Na'ima ta miqa hannu kafin ta karba Laila ta sake matashi a jikin ta, nan ice coffee din ya kware gaba daya a jikin brown abayan na'ima, baya Na'ima tayi tace "Bismillah" ta riqe daidai gurin da ya zuban gashi har gyalenta ya taba, faruk ya taka zai je gurinta sai ganin Ahmad yayi ya rigashi isa, kowa daskarewa yayi nan tsaye, Ahmad ya kamo dan bakin gyalen daidai inda shima ya tabun, cikin kwantar da murya yace "Are you okay?" gyada kai kawai na'ima tayi, Ahmad ya juyo ransa adan bace yace da Laila "Are you blind?" Laila ta wani juya kai tace "to ai bansani ba" Nafisa ta harareta sannan ta isa gurin na'ima ta ciro hanky daga jakanta dake sakale a kafadanta ta fara gogewa na'ima jikin riganta..Sai sannan su Abubakar suka nufi gurin na'ima suna mata sannu, faruk dai na tsaye shida Adam. Adam sai kallon abokin nasa yake da dan mamaki, Nafisa na goge wa na'iman jiki tace "muje restroom a dan wanke" ta kalli Ahmad tace "yaya bari muje restroom kawai" Gyada kai Ahmad yayi ya sake bakin gyalen na'ima suka wuce, Laila kaman ta fashe haka taji a wannan moment din, bata taba zaton Ahmad din zai nufi gurin na'ima ba, atake abubuwa dayawa suka darsu mata acikin rai..... Bintu Musa ce ✍️📚 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa ArewaPen https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c Chapter 15 Tsaye suke a restroom din gaban sink me madubi, nafisa ta kunna famfo ta tara hanky din sannan ta cigaba da goge jikin rigan na'ima, itadai na'ima ta riqe rigan tana kallon yanda nafisan ke goge mata ranta in yayi dubu to ya baci a wannan lokacin, dan itadai tasan miqa hannun datayi beci ace hannunta ne beyi reaching to Laila ba har coffee din ya kware mata a jiki, tarasa me ta tsarewa yarinyar da ta fara sakota a gaba haka, tana cikin wannan tunanin taji nafisa tayi tsuka me karfi tace "narasa ta Ina Laila ke tunani, ita duk wani abu dazatayi cikin rashin da'a yinsa take kamar ba mace ba, dan ko kaffara bazanyi ba da gangan ta juye miki a jiki, kuma wallahi kinji nayi rantsuwa..bashi taci" Na'ima tadanyi murmushi da iyakacin sa leban ta tace "ki barta nafisa, yaushe ma zata sake ganina?" Nafisa ta dago ta kalli Na'iman tace "Ai batada hankali ne shiyasa zan koya mata" na'ima jijjaga kai tace "a'a wallahi ki barta nafisa" Ahaka suka gama goge gurin da coffee din ya taba suka fito tare daga restroom din. Komawansu gurin 'yan'uwan nasu basu samu Laila ba a wajen sai mazan dake tsaye still, dan barinsu na'ima wajen takaici ya ishi Laila anan tsaye tamusu sallama inda ba wanda yakulata cikin su sai Adam da Al'ameen, haka ta juya cikin qunan rai ta bar gurin ta koma gida.. Isowarsu na'ima gurin faruk yadan matso garesu yace da na'ima "Are you sure you're okay na'ima?" Na'ima tayi murmushi ta gyada kanta tace "ya gogu ai yaya" faruk yace "but you're drenched ai, ko zaki koma a chanja kayan" na'ima ta sake jijjaga kai tace "a'a babu komai zai bushe a hankali" Ahmad dai dan kallonsu yake baice komai ba, Adam yace "sorry na'ima" ta gyada kai tana murmushi tace "laa bakomai dai yaya"...ice coffee dinda kowa bai sha ba kenan aka barshi anan waiting area kan kujera. Sunanan tsaye bada jimawa ba akayi calling jirginsu , sallama suka farayi da juna, Nafisa tayi hugging siblings din nata da daddaya, na'ima na tsaye tana kallonsu jikinta duk a sanyaye, kasa daurewa Abubakar yayi sai da ya matso gurinta yayi mata hug din, yace "anty na..we will miss you" tadan shafa bayansa tana dan dariyan qarfin hali. Ahaka sukayi sallama Ahmad yayi gaba su na'ima suna biye dashi a baya janye da box dinsu, shigarsu cikin jirgi sukaga shi yayi hanyan kofan da zai sada mutum da first class, qarasawa seat dinsu sukayi dake business class..bayan sun ajiye kayan nasu a sama Na'ima ta zauna jikin bakin window tafara maqala seatbelt dinta.. Basuyi nisa da tashi ba wata waitress tazo seat dinsu ta tsaya ta kalli Na'ima tace "are you Na'ima?" dan gyada kai na'ima tayi tana yiwa waitress din kallon tambaya while nafisa ta amsa da "Yes..she is" miqo wa na'ima jacket din hannunta tayi wanda qamshinsa duk saida ya cika musu hanci tace "here...someome from other side of the plane send me to give you this" kallon waitress din na'ima ta tsaya yi bata karbi jacket din ba, sanin Ahmad ne ya aiko wa na'iman jacket din jikinsa ganin jikinta a dan jiqe earlier yasa nafisa karban jacket din daga hannun waitress din, tayi murmushi tace "thank you miss" murmushi waitress din tayi ta juya tabar gurin su, Na'ima ta juya kanta tana kallon window batace komai, kawai ji tayi nafisa na lulluba mata jacket din a jikinta tayi saurin juyawa tana kallon nafisa dake murmushi kamar bakin ta ze yanke, hannunta tasa tafara ture jacket din daga jikinta itama tace "ni nace miki inaso ne, ke ki lullaba ajikin naki mana" dan dariya nafisa tayi tace "to ai bani na jiqe ba baby na'ima" Na'ima ta harareta tace "wace babyn?" Nafisa ta dan daga gira tace "ke mana... gashinan saboda riganki ya jiqe ana lallabaki harda jacket" Na'ima ta tsaya kallonta kawai takasa magana ma, dariya nafisa tayi itama tana kallon nata tace "Kinga wani instinct dana gani gurin yaya Ahmad yau, girl you have alot to gist me and i mean everything" Na'ima ta sake juya kanta tace "kin shiga uku da wannan mind din naki nafisa, ni babu komai tsakaninmu" nafisa ta cigaba da lullaba mata jacket din tace "naji..yanzu dai let's get you warm baby" na'ima ta sake buge hannunta tana dan murmushi tace "zan miki ba dadi nafisa" Nafisa tana dariya ta sake cewa "Baby" Haka Na'ima ta hakura nafisa ta lulluba mata jacket din a jikinta qamshin rigan na cika mata hanci, ahaka bacci ya dauke ta zuciyarta na saqa abubuwa daban daban... Sai shida saura jirginsu ya isa London, bayan anyi announcing fitan su, na'ima ta sauqe jacket din daga jikinta ta miqa kan cinyan nafisa tafara shirin miqewa, dan ware Ido nafisa tayi tafara dariya tace "lallai ma yarinyar nan, ni na lulluba dashi ne?" na'ima ta miqe tana gyara squeezing din riganta tace "ke kika karba daga hannun wadda ta kawo ai" kawai dariya nafisa tayi ta dan gyada kanta...fitarsu basu gamu da Ahmad ba suka fara tafiya Nafisa nata waige waigen inda zata hangoshi suka shiga cikin airport din, saida suka wuce arrivals nafisa ta ciro wayanta daga jaka ta fara kiransa, bayan ya dauka sun gama magana Nafisa tace da Na'ima "muje sis" A wajen airport din suka samesa tsaye da jaka a rataye cikin white t-shirt mai dan kauri, jacket dinsa dake rataye hannun nafisa ta miqa masa tace "gashi yaya mungode" karba yayi ya kalli Na'ima dake tsaye, bude bakinta tayi a hankali tace "thank you" Ahmad ya gyada kansa yace musu "The driver is on his way"  sannan yafara saka jacket din a jikinsa, nafisa tace "toh yaya" Dayake spring season yadanyi nisa sai ya zamto garin babu wani sanyi sosai....suna nan tsaye wata sleek ride tayi parking a gabansu wani bature yafito yana gaisheda da Ahmad, amsawa yayi, drivern ya gaisa dasu nafisa sannan yafara diban kayansu yana sakawa a booth Ahmad na tayashi..bayan sunyi settling acikin motan Ahmad na gaba ya fadawa drivern unguwar anty Amnah suka dauki hanya. Isarsu gidan anty Amnah bayan driver ya sauqo musu da kayan nasu suka wuce bakin entrance din nafisa ta danna door bell din, basu jima anan tsaye ba Anty Amnah ta bude, cikin fara'a tayi hugging dinsu tace "oyoyo 'yan makaranta sun dawo" ta jasu suka shige cikin gidan nata mai kyau dake screaming luxury, twins basa nan suntafi makaranta shikuma abbansu yana asibiti, kafin su zauna nafisa ta wuce gurin dining area ta dauko musu bottle water data gani a gurin ta dawo falon tana miqawa na'iman daya tace "anty tare muke da yaya fa" Anty Amnah ta dan ware ido kafin tayi magana taji an danna door bell din again, miqewa tayi ta je ta bude Ahmad yace "Momma kin rufeni a waje" Anty Amnah tayi dariya ta riqo hannunsa suka shigo cikin gidan tana cewa "Na isa son, kaida ganinka yayi tsada a London ma" zama shima yayi nan falon Anty Amnah tasake cewa "Kasan ban kawo araina tare kuke bane wallahi" Ahmad yadanyi murmushi kawai..miqewa anty Amnah tayi ta debo musu drinks harda snacks, da kuma abinci tace "zakuci yanzu ko sai kun huta?" Na'ima batace komai ba sai nafisa ce tace "A'a anty zamu huta tukunna, sai munyi changing ma" Anty Amnah tace "toh" nafisa ta juya gurin na'ima tace "muje sis" suka miqe suka nufi dakinsu dasuke sauqa in sunzo gidan suka bar anty Amnah takawo refreshments din nan gurin Ahmad. Bayan su na'ima sunyi wanka sun dan nutsu, komawa sukayi falon basu tadda Ahmad ba anty Amnah tace musu ya wuce, dining area suka nufa suka fara cin abinci, bayan sun gama ne suka dawo falon sannan suka fara hira da anty Amnah Haka su Na'ima sukayi zamansu nan gidan anty Amnah suna hutawa akan sai Sunday zasu koma oxford, Kuma sun fadawa anty Amnah hakan Ranan Saturday da safe nafisa tayi waya da kawarta Lauren akan tashigo london, haka nafisa ta shirya zasu hadu a wani Cafe tace da na'ima suje tace bazataje ba.. Wunin ranan na'ima da twins tayisa dan su anty Amnah da mijinta ma basanan sunje asibiti sunada shift, ta tafi kitchen da twins ta hau yi musu cake, dan nafisa ce ta koya mata yanda akeyin cake din farkon zuwansu oxford harta koya, twins sai hira suke mata tana biye musu, sunyi having fun sosai dan twins suna sonta sosai indai tazo gidan kuma sunanan to bini bini duk inda na'ima tasa qafa suna biye da ita kaman dama tuncan sun santa tun tashinsu. Daren ranan Na'ima na zaune dakinsu ta jingina bayanta da fuskan gadon tana kallo a laptop, gefenta plate ne dauke da sauran cake dinta tayi, kwance Jafar yake a dayan gefenta yayi bacci shima...Nafisa ce tashigo dakin na'ima ta dan dago ta kalleta, Nafisa tace "sannu uwar twins, sudai yafe mamansu sukeyi ma in kikazo" Na'ima tayi murmushi tace "kin dawo?" zama nafisa tayi a bakin gadon ta dauki cake daya dake plate nan kusa da Na'iman takai baki tace "Duk na gaji ma" Na'ima tace "Ina da Ina kukaje haka?" Nafisa ta amsa da "ashe housewarming party Lauren tazo attending garinnan da kuma yin content akan gurin partyn....sis akwai masu kudi a London, waiii.." Na'ima tayi murmushi tace "kijiki saikace bakisan kudi ba" Nafisa tadan ware Ido tace "banda irin wannan kudin Bobo" Na'ima ta dan jijjaga kai ta cigaba da kallonta, Nafisa ta cigaba"Guy dinda ya sayi mansion din ashe cousin din Lauren ne....kawai sai gani ga yaya Ahmad, na zagaya wajen pool din gidan naganshi zaune da wasu friend dinsa" Na'ima ta dan dago ta kalli nafisa tace "Allah sarki" Nafisa dake lura da expression din na'ima tace "kinsan ya tambayeni yakike" Maida idonta kan kallon Na'ima tayi cikin sanyin murya tace "Ayya, ya yake shima?" Nafisa tace "lafiyansa lau, narasa ina yake haduwa da friends irin wa'inda nagansu tare yau, they all scream money" Na'ima bata ce komai ba Nafisa tasake cewa "kinsan yaya Ahmad yasha creating apps da sukayi gaining global reach" sai sannan na'ima ta dago kanta tace "he's a programmer?" Nafisa tace "babba ma kuwa, bayan aikinsa na company da baba ya dora shi head ai yana programing manya manyan apps, zuwansa dayayi this time ma maqasudin zuwan ashe saida wata app din yazoyi gurin investors, ina tsaye kusadasu naji yana maganan da wani white friend dinsa" Na'ima ta gyada kai kawai batace komai ba, Nafisa dake son cusa mata maganan Ahmad din ta sake cewa "dan dai ba shaquwa nayi dashi bane, saboda sai nayi shekara abu bai hadoni dashi ba kuma shi bayason arinqa shige masa cikin al'amuransa kai tsaye, dana jaki watarana munje gidansa dake London dinnan" Na'ima tace "to ma tayaya zamu kwashi kafa muje gidansa nafisa..akan wane dalili?" miqewa nafisa tayi tafara rage kayan jikinta tace "Ha'a muda yayanmu..yanada kirki fa kawai ba komai zaki gansa yasa kansa aciki ba kamar yaya Adam" Na'ima jijjaga kai tace "ai bance baida kirki ba kawai bazan je bane" cikin son kawar da zancen yasa ta sake cewa "Bayan celebrities dinda Lauren din keyin content akansu, yanzu ta koma yi har a gurin housewarming party ne? Ko bada ita kukaje yin content gurin movie premiere ba kwanaki?" Nafisa tace "wannan babu inda bata tabawa indai akazo batun content, da celebrities din, Entrepreneurs, business tycoons duka ko ina ma" Na'ima ta gyada kai tacigaba da kallonta.. Washegari Sunday yakasance ranar komawarsu oxford, da wuri suka shirya komai nasu bayan sun idar da sallan safe, sannan suka tafi kitchen girka nasu breakfast din dan yau Sunday su anty Amnah yawanci suna yin dogon bacci na hutu, Bayan sun gama hada komai nan dining sannan suka zauna suka fara ci, Anty Amnah ce tafito cikin long pajamas, gaisheta sukayi ta amsa sannan taja kujera ta zauna tace "sannunku...kun gama shirya kayan naku dai ko" nafisa tace "tun tashinmu" Na'ima tace "twins basu tashi bane anty?" madadin anty Amnah ta amsa sai tace "meya samu muryanki daughter? Mura ne?" Na'ima tayi gyaran murya tace "nadan tashi da tari ne anty" anty Amnah tace "sannu dear, akwai magani a cikin first aid box, zaki gani a study room din abbansu, ko bari idan natashi zan dauko miki" Na'ima ta gyada kai tace "toh anty nagode" Nan sukayi breakfast din da anty Amnah suna hiransu, bayan sun gama suka koma daki sukayi wanka suna cikin Shirin anty Amnah tashigo dakin tace musu "ku fito yayanku yazo daukanku" sannan ta fita. Na'ima ta juya ta kalli nafee tace "wani yayan" nafisa na zipping riganta tadanyi murmushi tace "yaya Ahmad mana, I told him yesterday akan yau zamu koma da safe" Na'ima ta dan tsaya kallonta sai kuma ta juya ta cigaba da saka kananun kayayyakinta a qaramin jakanta batace komai ba. Fito da kayansu suka fara yi Abban twins yatayasu daukan wasu ya fita waje dasu, bin bayansa su na'ima sukayi dauke da wasu kayan anty Amnah ma haka. Bintu Musa ce ✍🏻 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c Chapter 16 Tsaye na'ima taga Ahmad bayan motansa suna saka kayan nasu shida Abban twins at the same time suna magana, qarasawa sukayi gurinsu Anty Amnah tace "son mun tado ka da sassafe ko, ai da ka turo driver ya kaisu bakomai" rufe booth din Ahmad yayi yana murmushi ya matso ya karbi ledan hannunta yace "Bakomai Anty..ina kwana" ta amsa masa su na'ima suka miqa nasu kayan back seat suma Nafisa ce ta fara gaishesa ya amsa sannan ya kalli Na'ima, gaishe sa tayi cikin sanyin murya sai kuma tari yadan zo mata tafarayi kadan kadan, dan qura mata Ido Ahmad yayi sai kuma ya kauda kansa ya yayi sallama dasu anty tareda bude mota, sallama suma sukayi dasu anty Amnah, tayi hugging dinsu tace "sai na ganku on weekends kuma" Abban twins yana murmushi yace "bayan sun koyi qin zuwa akai akai yanzu" nafisa tayi dariya tace "uncle hanyan ne akwai gajiya wani lokaci, amma upper week zamuzo" ya gyada kai yana murmushi yace "Allah ya nuna mana" Na'ima tace "anty in twins suka tashi ki gaishesu" gyada kai anty Amnah tayi tana murmushi tace "toh daughter, safe journey" Haka sukayi sallama, na'ima tayi saurin bude back seat ta shige, nafisa na dan dariya ta zagaya ta shiga front seat Ahmad ya tada motan suka wuce aka bar su anty Amnah tsaye suna daga musu hannu.. Shiru sukayi while Ahmad yana driving, Nafisa tayi breaking silence din tace "yaya baka taba zuwa gidan da muke zama a Oxford ba ko?" Ahmad ya gyada kai idonshi na kallon titi yace "nadade banshigo England ba nafisa.... bedsides, ai daga baya ma naji labarin tahowanki nan karatun" Nafisa ta gyada tace "hakane...kuma har yanzu kana living a gidanka dinnan dana sani?" Ya amsa da "Eh inanan nafisa, zakije ne?" Tana murmushi tace "Eh yaya zamu kai maka ziyara nida na'ima in Sha Allah..ai zaka dade kafin ka koma ba" yadan kai yatsa yana sosa girarsa kadan yace "I don't know, ina tunanin zuwa New York ne next week" Nafeesa na kallonsa ta gyada kai, ya cigaba "but ba damuwa, ku kirani time dinda kuka shirya zuwan i may be around" idon

Chapter 6 of 19