Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bayan tayi bacci... Washegari ma tayi mamakin amsa gaisuwan ta da yayi lokacin da kawo masa breakfast nan inda yake zaune a falo yana kallon Ball, da ta shirya zataje makaranta ma gyada mata kai yayi bayan tayi masa sallama yabita da kallo ganin yanda baqin abayan ya sake fito da haskenta, shi sai lokacin ya lura da yanda halittan idonta yake ma... Zaune Na'ima take tareda da Nafisa a wani rest bench hannunsu riqe da burger'n da Nafisa ta taho musu dashi suna ci, ganin Na'ima na kaiwa baki a hankali kamar ta fada tunani yasa Nafisan cewa "what is wrong with you Na'ima?, you seem lost tunda kikazo school dinnan yau" shiru Na'ima tayi sai kuma ta sauqe numfashi, ahankali tace "He's back Nafisa and bansan da me ya dawo ba" ajiye burger'n Nafisa tayi tana ware Ido tace "what?...yaushe yadawo, No wait..did he beat you?" Na'ima ta girgiza kai tace "A'a" Nafisa tace "Then.. me ya miki?" ta amsa da "He just keep staring at me" da sauri Nafisa ta juyo da kafadan Na'iman tana kallonta cikin ido tace "shi kadai ya dawo babu karuwar tasa?" Na'ima ta gyada kai, Nafisa ta cigaba "toh wallahi ki kula, Bilal HIV zai saka miki" saida zuciyar Na'ima ya buga na wasu 'yan daqiqu ta kasa magana, Nafisa tace "ya gama bin kan karuwan Lagos din shine  zai dawo kanki yanzu, we have to do something" hawaye ya ciko a idon Na'ima tace "Nafisa ya zanyi?" tace "duk yanda zakiyi karki yarda dashi, duk inda za'aje kuwa" tunani Na'ima ta fara yi ta yanda ma Bilal din ze ce zaizo gurinta bayan yace "in matan duniyar nan zasu qare he won't give a f*ck about her"...sunanan zaune Nafisa tayi ta bata qarfin gwiwa akan ko me Bilal din ze ma ta be kai cutan da zai qaqaba mata ba, har suka gama school activities dinsu na ranan hankalin Na'ima bai dawo jikinta ba, a hanyarsu ta komawa gida ma haka ta jinginar da kanta jikin window tana tunani Nafisa na sake bata qarfin gwiwa akan yanda zatayi facing dawowan Bilal din. Bayan Nafisan tayi parking anan qofar gidan sai ta juya ta kamo hannun Na'iman tace "Bobo let's talk" kallonta Na'ima tayi batace komai ba sai ta cigaba da magana cikin kwantar da murya tace "it's high time you leave this God forsaken marriage before you loose your sanity, Bilal zeyi ruining dinki ne Na'ima, zan iya rantsuwa ba ke bace a gabansa saboda inda ya damu da rayuwanki bazeyi shekarun nan batare da yasan yanda kike ba, and i sense that kallon nan da kikace yake miki kawai neman hanyarsa zeyi dake ya cuceki" hawaye Na'ima ta fara ta kasa magana, Nafisa tace "ki fadawa Alhaji bakyaso, nasan he'll listen" gyada kai Na'ima tayi tace "Toh" ganin bata iya magana yasa Nafisan yi mata sallama itama tana jin zuciyarta wani iri, da haka suka rabu rai babu dadi.. A wannan ranan ma bai wuni a gidan ba sai dare ya dawo, Haka suka cigaba da rayuwa na tsahon two weeks Bilal baida aikin yi sai kallonta inta fito zata giftashi, gashi dai ko wane dare da kalan macen da yake kebewa a club amma yarasa meyasa ya kasa dauke idonsa daga kan Na'ima, ranan wata talata ta gama hada masa breakfast tana jerawa anan dining ya sauqo qasan, nan gefenta ya tsaya tadanyi baya, sai yace "me kika dafe me qamshi haka" kasa magana tayi ganin ya matso daf da ita yana kallon idonta, matso da fuskansa yayi daf da nata har tana jiyo numfashinsa zuciyarta na bugawa cikin tsoro saboda maganganun Nafisa dake echoing a cikin kanta, kissing dinta ya so yi sai ta juya kanta kadan, again be daddara ba ya sake miqo fuskansa, batasan lokacin da ta dan dafa hannunta a qirjinsa ba alamun ya dakata, ji yayi ransa ya baci sai ya fara kiciniyar riqota duk da haka taqi juyo da kanta, Mari ya kai mata me qarfi sai da tayi baya, ya sake biyota ya hankadata ta bugu da dining table din abincin ya zube, cikin diri yace "Damn you Na'ima" ya qarasa maganan tareda shafa fuskansa cikin frustration, dafa kuncin ta tayi aranta tana fadin "there we go again" plate din gurin ya dauka ya sake bugawa a qasa yace "me kika dauki kanki da har zan kawo kaina wajenki kiyi rejecting dina, ke kin isa?" Na'ima na hawaye har sannan dafe da kumatun ta batace komai ba,ya juya cikin bacin rai ya koma dakinsa... Daren ranan bayan Na'ima ta samu bacci ya dauketa dakyar taji anja blanket dinda take kwancen, da sauri ta bude idonta jin mutum a gefenta, qoqarin miqewa tafara yi Bilal ya sa hannu ya danne ta sai ta fara kuka  bata daina kiciniyan kwace kanta ba, yaga rigan jikinta yayi bear skin dinta ya bayyana tayi saurin kai hannu ta kare jikin nata bata daina kuka ba tace "Dan Allah kayi hakuri" Bilal bai saurareta ba ya kai fuskansa wuyanta yana wani irin numfashi, sai da ya raba ta da duk kayan jikinta ta karfi kafin yaji kansa yayi wani irin bugawa wanda yasa cikin sauri ya dagata yana dafe kansa, ganin haka yasa ta miqewa ta lalubo bedsheet din zuwa jikinta kafin ta nufi hanyan fita ya finciko gashinta tayi qara me karfi, dawo da ita gadon yayi bata daina ihun ba wanda yake jinsa kamar ze tsaga masa kwakwalwa, nan ya hau dukan bakinta bata daina ihun ba, ranan Na'ima taga other side of Bilal da bata taba gani ba, monstrous side dinsa ya bayyana mata nan kan gadon yana dukanta kamar ba mace ba, ji yayi ya tsaneta kamar ya kasheta a wannan lokacin, sai da Na'ima ta galabaita sannan ya fice daga dakin cikin fushi, hannu takai hancinta tana tare jinin dayake fita har sannan hannunta damqe da bedsheet din tana kuka me tsuma zuciya...Har asuba idonta biyu ta kasa tashi daga kan gadon, zuwa sannan babu hawayen ma sai kukan zuci da takeyi, da asuban taji fitan motansa daga gidan, wunin ranan komai ji tayi baya mata dadi, kuka kam tashashi kamar ranta ze fita tana jin ta tsani har iyayen Bilal din... Bilal bai dawo gidan ba sai tsakiyan daren ranan, da aka wayi gari washegari Na'ima tayi masa breakfast ta ajiye nan dining be fito ba, ta nemi face mask tasaka bayan ta gama shirin zuwa makaranta, a falon ta samesa zaune, cikin sanyin murya ta fada masa zataje makaranta ya bita da wani mugun kallo da ya kada 'ya'yan hanjinta, calmly yace "Bazakije ba" kanta a qasa ta juya ta nufi upstairs tanajin wasu hawayen na zuwa mata...daga wannan lokacin zamansu yakoma bala'in dare kuma, wataran a buge zai dawo gidan ya biyota dakinta neman abunda yake so amma abu ya gagara, jin haushin rashin idda gaci yake sashi dukanta sosai, wani qunci zuciyar Na'ima ta shiga a wannan lokacin, zaman gidan ma yazamo a firgice takeyinsa, saida tayi sati harda dori bataje makaranta ba tun tana boyewa Nafisa har ta fito fili ta fada mata Bilal ne ya hanata zuwa school din, a ranar da ta fada matan sai ga Nafisa a gidan da yammaci, ganin yanayin Na'iman da ciwukan fuskanta yasa Nafisan fashewa da kuka ta rungumota suka fara kukan tare nan tsaye falon, sai da suka tsaya da kukan Nafisa tace "Na'ima mu tafi police station yanzu" da sauri Na'ima ta girgiza kai tareda cewa "A'a Nafisa" cikin bacin rai Nafisa tace "baki kalli yanda kika koma bane Na'ima, kinaso sai ya kasheki kenan" Na'ima na hawaye tace "zanje gun Alhajin, amma banda police station Nafisa"..ranar Nafisa ce ta tsaftace mata gidan har girki tayi sannan ta fita ta siyo maganin da zata shafa mata a ciwukan fuskanta da jikinta, tana hawaye tana shafa mata suka zauna shiru can tace "Na'ima you're slowly dying, this man is killing you slowly" Na'ima na hawaye batace komai ba Nafisa tace "kibini mu koma Abuja, let's run away Na'ima, mutafi gidanmu na can" Na'ima tace "They are my family Nafisa, i can't leave" cikin bacin rai Nafisa tace "F*ck that Na'ima, and they stand a side watching you like this" Na'ima ta sake cewa "zanje gurin Alhajin gobe, ai be san yana dukana ba" tsayawa kallonta Nafisan tayi sai ta miqe takai mayukan kan mirror..sai dare Nafisa ta bar gidan kuma tayi sa'a har sannan Bilal din be dawo ba... A daren ranar Bilal yadawo gidan tare da Stella data biyoshi Jin shiru bai koma ba, Na'ima na dakinta ta jiyo muryansu sun shiga dakin Bilal din..Ba qaramin nutsuwa Na'ima ta samu ba ranan jin Stella a gidan, bata tabajin dadi da hamdala ba irin zuwan da Stella tayi a ranan, bayan ta idar da salla cikin daren ranan har addua tayi akan zaman Stella yayi tsaho a gidan kodan ta samu sararawa kan uquban da Bilal ke gana mata.... Washegarin ranar bayan ta yi musu breakfast ta koma dakinta sai ta Jiyo tashin muryansu alamun suna sa'insa, bude kofan dakin Stella tayi ta fito Bilal ya riqo hannunta sai ta fincike ranta a bace tace "don't touch me" anan kofar dakinsa suka tsaya ta sake cewa "Have you touched her?" Bilal yace "meye hakan kike cewa ne Baby" ta daga masa hannu tace "just answer me Bilal, did you sleep with her?" ,Jinkirin da taji yayi gurin amsawan ne yasata juyawa ta nufi dakin na'ima tana fadin "where is this B*tch" ta banko kofar lokacin da Na'iman ke gaban madubi tana gyara gashinta, Stella batayi wata wata ba ta finciko gashin nata sannan ta dauketa da mari, Bilal ne ya biyo Stella dakin tareda riqota duk da haka taqi sake gashin Na'ima tana qunduma mata zagi, dakyar ya rabasu Stella na cewa "ka barni in koya mata hankali tasan ta shiga gonata" sai ta sake yin kan Na'ima, da sauri Na'ima ta nufi toilet Bilal ya sake riqo stella'n, beyi wata wata ba ya dauke ta da mari tayi baya tana ware idanu cikin mamaki, ransa a bace ya nunata da yatsa yace "No One, i mean No One..gets to beat Na'ima except Me" Stella na kallonsa cikin shock tace "Bilal ni ka mara akanta" yana kallonta cikin ido yace "Get out", fuu ta juya ta fice daga dakin, Na'ima na nan tsaye bakin toilet ya juya ya kalleta bai ce komai ba shima ya fice daga dakin..... Da daren ranan ta gama abinci Bilal ya sauqo daga upstairs yace mata "in kin gama ki kai mana abincin can dakina" gyada kai tayi ta amsa da "toh" bayan ta gama hada abincin akan tray sai ta hada da plates na tangaran as usual har da glass cups da take hadawa akai saboda bottle water'n da takeh kai masa..nufan dakin nasa tayi sai da ta gama hawa stairs din Stella ta fito daga dakin hannunta janye da akwatinta suka kusa cin karo, dan baya Na'ima tayi sai stellan ta matso daf da ita tana kallonta fuskarnan kamar hadari, hannu ta kai ta banke tray din daga hannun Na'iman kwanukan suka rinqa tumbling anan stairs har suka kai qasa, juyawa Na'ima tayi tana kallon yanda duk tangaran din suka tarwatse, duk sun fashe sunyi daddaya, kafin ta juyo ta kalli Stella'n sai taji ta hankadata da qarfi, tun daga matakalan farkon Na'ima ta fado har kan fasassun glasses dinnan a sume, jinine ya fara bin jikinta nan kwance... Bilal dama tun Jin qaran farko yayi saurin kashe shower dinda yake wanka a toilet, da saurin sa ya fito sanye da towel, daskarewa yayi a a bakin stairs din ganin abunda ke gabansa ga Stella nan tsaye itama tayi stiff tana kallon Na'iman dake kwance cikin jini... Bintu Musa ce ✍️📚 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19