Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zasu kai project papers dinsu gurin supervisors dinsu, da wuri suka shirya ko breakfast ma basuyi ba dan zuwan wuri sukeson suyi, bayan sunyi sallama da Anty Amnah suka fice , fitowan su kofar gidan zasu nufi gurin motan Ahmad dake nan fake sukaga wata Uber tayi parking dan nesa dasu, Tsayawa kallon Laila data fito daga bayan motan sukayi dukansu, drivern ya fito yafara ciro mata akwatin ta daga bayan motan..Nafisa da ke gefen Na'ima tace "A'uzubillahi minash shaidanir'rajim..ji wani mummunan gani da farar safiyar nan" duk yanda Na'ima takai da Jin ranta babu dadi saida ta kusa fashewa da dariya Sunanan tsaye babu wanda yayi gigin tayata kama akwatin data ja da kyar, dan tsayawa Laila tayi tana kallon motan Ahmad dake fake a kofar gidan sannan ta qaraso gurin su nafisan. Nafisa tace "ke kuma sauqan yaushe da safiyar nan" Laila tana mata kallon banza tace "ban sani ba" Nafisa tace "hattara dai Laila, babu wanda nake shakka kaf London, da dutse zan miki gugan baki wallahi" Laila tayi wani tsuka me qarfi tana hararan Na'ima da taqi kallonta, wucewa tayi har tana dan bangaje kafadan Na'iman tayi cikin gidan Anty Amnah'n janye da akwati suna binta da kallo, sai kuma Nafisa ta daga hannu sama afili tace "Allah ka yafemun zanyin abunda uwata ta haneni da yi".. A hanyarsu na tafiyan ne Na'ima ta juya ta kalli nafisa tace "sis ko zamu koma namu apartment din tunda kin samu sauqi" Nafisa ta dan harareta tace "wa? Akan Laila tazo kenan, wallahi bazamu bar gidan ba saidai ita ta bari, tsoronta ma mukeji kenan" Na'ima ta girgiza kai tace "banason tashin hankali nafee" Nafisa tace "babu abunda zai faru dai sis, kema kinsan Anty Amnah ai, bazata dauki nonsense ba" shiru Na'ima tayi batace komai ba Nafisa tasake cewa "ki kwantar da hankalinki dan Allah, ba wani abu"... Na'ima ce zaune akan wani rest bench cikin school premises din itada zarah hannunsu riqe da ice coffee, hira sukeyi Kiran Ahmad ya shigo wayanta, bayan sun gaisa a nutse yace "Babe where are you" Na'ima tace "Ina school" ya sake cewa "I'm on my way now" sanin daga London ya kamo hanya yasata cewa "Allah ya kawoka lafiya" ya amsa da Amin sannan ta sake cewa "zanje apartment dinmu dauko mana wasu kayan" daga can bangaren Ahmad ya amsa da "Okay zanje can din daukanki" sannan sukayi sallama ya kashe wayan, tashi tayi tayi sallama da zarahn akan zata tafi, saida ta tari cab anan bustling street na bakin makarantan sannan ta shiga suka wuce, a hanya ta kira nafisa bata dauki kiranba kawai ta maida wayan jaka... Isarta apartment din nasu ta fito daga elevator anan corridor din nasu taga wani kamar delivery man a tsaye a bakin kofan dake gefen nasu apartment din, wuce sa tayi bata ga fuskansaba dan sanye yake da facing cap har da face mask, saida ta tsaya daidai kofar su ta saka door pin din ta bude zata shiga taji an hankadota da karfin gaske ta fada cikin gidan nasu, kifewa tayi anan falon zuciyarta yayi wani bugawa da qarfi har tanajin bugawan a kunnuwanta sanin mutum daya ne zai iya mata haka a kaf duniya, ta juyo daga kwance tana kallon sa, rufo kofan yayi yacire face mask din yana kallonta da wani irin kallo dayake kada 'ya'yan hajinta tun fi azal, fari ne guy din kamar Na'ima Amma babu ta inda suke kama sannan yanada dan kakkauran jiki, qarasowa yayi falon cikin muryansa me kaifi yace "yaushe na fara wasa dake Na'ima" baya tafarayi tana dan jijjaga kai, isowarsa gurinta beyi wata wata yakai mata hari da kafansa akan cikinta, Na'ima tayi wani qara tana kama cikin nata, sai da yayi mata harbin sau uku cikin tsawa yana cewa "Tell me...yaushe na fara wasa dake" Na'ima ta fara rarrafawa tana dosan gurin kujera tana hawaye ya kamo gashinta ta bata ya dagota, hannu takai tana kama gashin nata da ya riqe tafara wani irin kuka, dagota yayi ya bugata nan jikin kujeran ta sakeyin ihu, yana huci yace "har zan bada saqo gurin banzar kawarki sannan kiqi complying, who are you Na'ima" kuka take bata ce komai ba har sannan, ta miqe zauna tana kallon cikin idonsa, yana kallonta shima ya sake cewa "I warned you haduwan mu bazatayi kyau, dan haka ki tashi ki wuce daki ki debo kayanki mu tafi gida, and i mean NOW before i wound you" Na'ima dake kallonsa tanajin zuciyarta yana bushewa for the first, a hankali tace "bazanje ba" tsayawa kallonta Bilal yayi with shock written all over his face.. Na'ima na kallonsa idonta na zuban hawaye tasake cewa "bazanje ko ina ba Bilal" ta qarasa maganan itama tana mamakin irin qarfin gwiwan data samu a karo na farko na tsawon rayuwanta tareda Bilal, tunda ta mallaki hankalin kanta a rayuwa take tsoron Bilal da duk abunda ya shafesa.. Miqewa tayi still yana kallonta tace "wallahi ko zaka Kash.." bata qarasa ba ya dauke ta da mari bata farfado ba ya sake kai mata wani, baya tayi zata gudu ya kamota ya bugata da bango tana ihu, yana huci yace "maimaita abunda kikace" ta fara jijjaga kai zata kwace kanta kawai ya hau kai mata mari tana tarewa da hannunta, burinta daya a wannan lokacin shine takai ga zuwa kitchen ko zata samu wuqa, dakyar ta kwace ta nufi hanyar kitchen ya kamota ya sake bugata da kofan dakinta, Jin kofa a bayanta yasa ta bugawa ta fada dakin yana biye da ita, hannu takai ta daki mirror da karfi ya tarwatse a nan dakin ta dauki babban yanka guda daya ta juyo tana nuna Bilal din dashi, jikinta na rawa tace "ko ka fita ko muyi mutuwar kasko" yana kallonta Bai motsa ba ta sake matsowa tana taka fasassun mirro'n daya zube nan qasan dakin, cikin ihu tace "ka fita Bilal, ko in kasheka nima in kashe kaina" Bilal ya shiga shock a wannan lokacin ganin yanda Na'iman daya sani ta rikide ta koma wata daban, sai yayi qasa da murya yace "Na'ima you've tasted freedom, is this really you?" Ta fara dosowa gurinsa yadanyi baya ganin da gasken zata iya caka masa, tace "Wallahi ko ka fita daga gidan nan ko in kasheka" baya yafari suka fito daga dakin yace "Na'ima listen to m.." cikin ihu tace "I'm done, I'm done Bilal" sai kuka yazo mata kuma, tasake cewa "ka barni nayi rayuwata, kabarni hakanan" Ya daga hannun sa alamun surrender yace "Alright zan fita, ki ajiye abun hannun naki tukunna" ta girgiza kai gashinta duk yayi daddaya tana zare masa idanu ta cigaba da doso sa da mirro'n hannunta yana jini, da baya da baya Bilal ya fita daga kofan, tana ganin ya fitan ta jawo kofan ta rufe da qarfi ta jingina bayanta nan jikin kofan tana fashewa da kuka me karfi, yardar da abun hannun nata tayi ta tsugunna nan bakin kofan tacigaba kuka tana dafe hannunta a setin zuciyanta... Qarar wayarta ta Jiyo anan kan sofa ta miqe dakyar ta isa gurin, sunan Ahmad tagani rubuce a fuskan wayan, sai lokacin ta tuna ashe yace zaizo daukanta, daukan wayan tayi bata daga kiran ba sai ta nufi gurin balcony tadan leqa kanta.. Numfashinta ne taji ta tsaya a wannan lokacin ganin Ahmad a tsaye jikin motansa waya a kare kunnensa,  daga gefensa a nan street din kuma Bilal ne tsaye shima hannunsa cikin aljihu da alamun yana jiran abun hawa, dukansu kusa suke tsaye da juna batareda daya yasan daya ba.. Na'ima ta dago wayan hannunta tana kallo ganin Ahmad ya sake mata wani Kiran, kallon su ta rinqa yi tananan tsaye in idonta ya kalli Ahmad sai ta kalli Bilal shima dake nan gefe........ Shin wai wacece Na'ima? Menene asalin alaqarta da Bilal? Shin ya kuke ganin wannan lamarin zai qare a tsakanin wa'innan mutane? Kudai ku biyoni dan Jin labarin Na'ima da abubuwan da rayuwarta ya qunsa ...... Zaku iya samun complete book dinnan a ArewaPen ko Wattpad.. Ko ku tuntubi wannan numbern (08134692758) Bintu Musa ce ✍️📚 https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Chapter 22 Tushe Gandun Labari.. Asalin Na'ima Yusuf Dabo...... Na'ima jika ce a cikin Ahalin Malam Hamisu Dabo dake cikin garin Mayo-Belwa, Adamawa state, Malam Hamisu ya taso cikin nema sosai na sana'ar gwari kuma da ita Allah ya rufa masa asiri yake daukan nauyin 'yan'uwa da kuma iyalinsa, Matar sa daya mai suna Habiba wadda ta kasance bahaushiya yar garin kano suna rayuwa cikin rufin asiri, haihuwar Habiba biyar suna komawa babu rai wanda hakan ba qaramin tashin hankali yake sa musu ba, Habiba tasha tsangwana gurin dangin hamisu wanda har 'yan uwanta sun shaida hakan, rigima akayi sosai tsakanin danginta da na hamisu saboda har maita sun jingina mata akan hakan, 'yan uwanta sun shigo cikin lamarin gurin  neman magani har daga qarshe suka rugumi dangana da hakuri, kuma Allah ya dubesu da rahama ya bawa Habiba wani cikin wanda ya kasance na shida kenan, cikin ikon Allah ta haifo danta namiji ranar suna yaro yaci Abdullahi, Hamisu sun raini dansu na tsahon shekara kafin Habiba ta koma ga Allah, sanadin ciwon jeji da yayi mata mummunan kamu, mutuwanta ya jijjaga Malam Hamisu da 'yan'uwanta sosai amma haka suka rungumi kaddara sukayi hakuri, ranar da 'yan'uwan habiba suka tashi komawa bayan zaman makokin ita Habiban, sun nemi abasu Abdullahi su koma garinsu dashi amma Malam Hamisu Sam yace "A'a" abar masa dansa zai kula dashi, danginsa da ba wani son Habiban suke ba tun can asali, basu nuna damuwarsu akan hakan ba, dakyar Malam ya yarda wata qanwar habiba dake zama anan garin kano ta karbi Abdullahi dan itama a lokacin tana kan renon danta qarami wanda zeyi sa'an Abdullahi shima.. An dauki shekaru kafin Malam Hamisu ya sake wani aure, Kuma wani ragon azanci sai be bibiyi bayan dansa ba 'ance dan Adam ajizi' , daga baya ya auri wata ana kiranta lantana me kai musu tallan nono gurin sana'arsa, sunyi zaman lafiya da lantana kuma a wannan karon sun samu haihuwa har yara hudu, babban cikin sunansa Ayuba, Nasiru, Yusuf sannan lubabatu data kasance kurma, acikin yaran Malam Hamisu babu wanda bai kama sana'ar gwarin ba, amma sai yazamo Yusuf ya hada tasa sana'ar da boko... Yusuf ya taso daban cikin 'yan'uwansa tayanda daga kan halayyarsa har zuwa hazaqarsa daban take, ga nutsuwa da rashin hayaniya, babu yanda Malam Hamisu beyi dashi akan ya kama sana'ar sa kawai ya ajiye boko amma abun yaci tura, su Ayuba da Nasiru kam dama 'ina zakuje? Kudi.. daga Ina kuke? Kudi.....' sai zafin neman kudi, kuma sunqi taruwa kamar wa'inda akayiwa baki, ta bangaren Yusuf kuma Allah ya rufa masa asiri daidai gwargwado, a iya karatun secondary din da yayi ya samu aka daukesa aiki anan makarantar primary na gwamnati dake cikin garinsu, Ana tafe bayan wasu shekaru kowa yakai ga gacin aure acikinsu,Lubabatu  ce tafara aure aka miqata wani qauye dake nan kusada garin nasu, Ayuba da Nasiru kusan tare ma sukayi auren, zuwa wannan lokacin sunyi neman kudin har fita ci rani zuwa manyan gari sunyi amma kudi sunqi zuwa kaman abun masifa... A lokacin da Yusuf ya tashi aure shikuma yadanyi kwari a fannin aikinsa da kuma sana'arsa dayake tabawa, wata yar maqotansu yagani yanaso sunanta Binta wadda afarko dai kyawunta ne abunda yafara rinjayarsa gareta, asannu asannu suka kuma daidaita ganin halayenta abunso, gashi mahaifiyarsa tana sonta, Binta ta taso gaban kakarta ne tareda qanwarta Halima, iyayensu sun rasu sai zama ya dawo dasu itada qanwar tata gurin kakarsu ta wajen Uba kuma se ya kasance ba wani dangin azo agani garesu ba, Allah ne gatansu sai kakarsu da ta tsaya musu akan komai nasu..Aure akayi na so da qauna tsakanin Yusuf da Binta yarinya mai hakuri da kawaici, sai ta hadu da Yusuf shima mara hayaniya da kuma nutsuwa, anan cikin unguwa Yusuf ya fulaste gidansa daya siya me dauke da daki biyu aka kai masa Bintarsa..Zama sukayi na so da tattalin juna, Yusuf na matuqar son Matarsa, Binta bata rufa shekara ba ciki ya bayyana jikinta, murna wajen Yusuf ba'a cewa komai, haka suka rinqa tattalin cikin tare gwanin sha'awa har Allah ya kawo ranan haihuwar Binta suka samu diyarsu mace inda taci suna NA'IMA, yarinya son kowa gurin kyau da haiba, gashi Allah ya zubawa Yusuf son 'yarsa kamar ya maidata ciki, bini bini yake yawo da abarsa akan keke, abu kuma indai Na'ima tace tanaso a gidan nan to sai an mata shi, dayawan lokuta hakan baya yiwa Binta dadi sanin me rayuwa ta qunsa yau mune gobe ba muba, Yusuf yakance "tunda muna rayen, kuma Allah ya bamu iko sai muyi mata" Binta takan jijjaga kai kawai sanin kome zata ce masa bazai fahimta ba saboda son 'yarsa ya rufe masa ido, 'yan'uwa da dangi kowa ya shaida Yusuf yana son 'yarsa Na'ima dan baya iya boye hakan agaban kowa.. Na'ima na datawa mahaifinta ya sakata nan makarantar da yake koyarwa, aka sakata a primary, tare suke tafiya da mahaifin nata kuma tare suke dawowa gida a kekensa, kuma har zuwa lokacin Allah bai qara basu wata haihuwan ba, hakan kuma bai taba damun Yusuf ba sanin cewa komai na Allah ne, Binta ce ma mai saka damuwan hakan a ranta wani sa'in.. Babu dalilin hawa balle na sauqa kawu Ayuba ya fara mitan wai Yusuf ya saka 'yarsa a makarantar boko nan Nasiru ma ya karba dan dama ko menene Ayuba zeyi to bakinsa hade da shi Nasirun , haduwa sukayi su biyu suka yiwa Yusuf caaa, saida Malam Hamisu ya shiga maganar tukunna suka kama kansu, itadai mahaifiyarsu irin matan nan ne masu sanyin bala'i, sai abunda 'ya'ya suka aiwatar kawai tana gani babu tsawatarwa sosai.... Kwanci tashi Na'ima nada shekara 8 a duniya Allah yabawa Binta wani cikin, Sunyi murna har ba'a magana, Yusuf kamar ya maida Binta ciki saboda murna, a wannan lokacin ne kuma Allah yayiwa Malam Hamisu da kakar bintan rasuwa, bi da bi kowanne ya koma ga Allah banbancin kwanaki uku, abun ya taru ya hade musu guri daya tun ba ma binta ba, ga ciki ga mutuwa, qanwarta da itama zuwa lokacin tayi nata auren a garin yola ce tazo suka hadu sukasha kukansu,  su Yusuf sunji mutuwar mahaifin nasu sosai suma, ahaka dai akayi zaman makoki kowa ya sake runguman kaddara, yazamto Malam Hamisu  da kaka sunzamo tarihi saidai abisu da addua.. Ina labarin Abdullahi?...'yan'uwan mahaifiyarsa basuyi riqo da amana ba, basu dubi zaman so da amincin da Malam Hamisu yayi da Habiba ba lokacin da take raye, tunaninsu a koda yaushe shine wannan sabanin da aka samu tsakanin 'yar'uwarsu da dangin mijinta, wanda har hakan yasa qanwar maman Abdullahi bata zamo uwata tagari me sashi akan hanyar da zai nemi 'yan'uwansa ba, kasancewar mijin hajiya babba (ayanda suke kiranta kenan) ya na da rufin asiri sai Abdullahi yasamu kula da ilimi daidai gwargwado a gidan, ya taso cikin nema a fannin kasuwancin da mijin hajiya babba yakeyi, asannu asannu hajiya babba take sa Abdullahi bin mijinta kasuwa yana ayyuka har shima Allah ya hore masa yayi nasa shagon, a wannan lokacin ne kuma ya waiwayi gidan, babu yanda hajiya ta iya haka ya dan tattaro guntun chanjinsa yazo duba mahaifinsa, su Ayuba sai a sannan suka sanshi, Yusuf bai hadu dashi ba dan baya gari ma lokacin da Abdullahin yazo, ganin jikinsa da alamun maiqo ne yasa Ayuba da Nasiru suka rinqa yin nan nan dashi kamar su maidashi ciki, Abdullahi bai wani dade ba ya koma kano gurin aikinsa... Bai sake waiwayansu ba saida Malam yayi kwana arba'in da mutuwa ya dira garin, rana tsaka ya zo musu da wata mota mai dumi ya faka ta nan qofar gidan Malam, lokacin duk su Ayuba suna gurin aiki, goggo Mahaifiyarsu Yusuf dince ta sauqe shi sannan ta tura ayi mata kiransu su Ayuba dake nan kasuwar da ba nisa tsakaninsu, Yusuf dai qin barin aikinsa yayi, dan duk wata martaba ta Abdullahi kuma ya daina gani tunda har mahaifinsu zai mutu ace har ayi taro a watse babu alamunsa, sudai Ayuba da Nasiru cikin mazari suka kada kafarsu suka tafi, hankalinsu bai sake tashi ba saida suka ga motan da Abdullahi yazo da ita nan kofar gidan, Yanda kasan fir'auna da bayinsa haka suka rinqa tsugunnawa yayan nasu kamar su goya shi, babu wani batun baizo mutuwar ubansu ba, wannan bayanin ya kau kuma tunda yazo musu da chanji..ganin irin yanayin 'yan'uwan nasa ne yasa Abdullahi yi musu rabon kudi suna godiya kamar bakinsu zai yage, sai yammaci Yusuf ya baro gurin aikinsa, gidan mahaifiyarsa ya nufa dan gaisheta kafin ya wuce gida gurin iyalinsa, yayi mamakin ganin motan Abdullahi har sannan bai tafi ba, shima Abdullahin ganin Yusuf din sai yaji ya kama kansa, gashi dai ko da wasa Yusuf bai kaishi a shekaru ba amma yaqi sake masa kamar yanda su Ayuba sukayi, kuma cikin wani ikon Allah sai nan da nan Abdullahi yaji yanason Yusuf din, babu yabo babu fallasa Yusuf ya gaisa da yayan nasa sannan yace zai shiga cikin gidan ya gaisheda goggo, gyada kai Abdullahi yayi ya bayansa da kallo, Ayuba dake nan tsaye kusada Abdullahin ne yace "kasan ai da'aka je kiran namun baya nan shiyasa baka ganmu tare ba" Abdullahi bai ce komai yana kallon bayan Yusuf din..Da yammacin ranann Abdullahi ya juya bai kwana garin ba... Lokacin da Haihuwar Binta yazo sai abun yazo mata da matsala sosai, yau ciwo gobe lafiya, Hankalin Yusuf duk ya tashi sai mahaifiyarsa ce me dan saka hannu a lamuran nasa dan 'yan'uwansa dai kowa ta kansa yake, kar ma azo zancen Ayuba, dan shi idan bazaka qareshi da kudi ba to kai da banza ma duk daya, ta yanda hatta mutan gari sun san halinsa , kudinka mutuncinka a gurinsa dan kome kace yayi maka indai zaka bashi kudi to tsaf zeyi.. Ahaka dai binta tayi ta fama da jinya 'yan kudaden Yusuf duk suka tafi wajen neman magani, a satin da haihuwan ta fara tasowa gadan gadan wani irin sanyi Binta tayi har hakan yana baiwa Yusuf din tsoro, Na'ima dake Shirin shiga shekara na 9 a duniya ma saida ta fahimci wani abun na damun mahaifiyarta duk itama sai tazama shiru, makarantar ma bata son zuwa dan Yusuf daman tunda rashin lafiyan Binta ya tsananta ya maida zuwa aikin nasa sama sama.. Ranar da naquda ya tashi daman da asuba Yusuf ya nufi wajen mahaifiyarsa suka taho gidan nashi tare tashiga dakin wajen Binta daketa salati da juyi, Yusuf nanan tsaye bakin gadon mahaifiyarsa tace ya dauko kaya su kaita asibiti wanda shi sai a lokacin ma hakan yazo masa kai tsabar birkicewa, riqo hannunsa Binta tayi tace ya matso kusa tanason suyi magana, anan ne kuma tashin hankalinsu yafara linkuwa, dan Binta wasiya tafara bashi akan Na'ima, ta nemi ya kula da ita sannan ta fara neman yafiya, damqe hannunta Yusuf yayi ya fara kuka kamar qaramin yaro yana gyada kai tareda da tabbatar mata zata samu lafiya, Na'ima da tashinta kenan daga bacci, ta shigo dakin mahaifiyar tata itama, kuka ta farayi goggo ta dauketa suka fice, Kafin tadawo dakin Binta tace ga garinku nan, ta koma ga Allah da cikin da bata haifeshi ba kenan.... Hasbunallah...ranar Yusuf kowa ya shaida gigicewarsa, magana yake yana kauce layi, duk wanda yaga yanayinsa sai ya tausaya masa ainun, saboda wani irin tashin hankali ya shiga na rashin abokiyar rayuwan tashi da ba'a iya misaltawa, Na'ima babu baki sai kuka, in ta juya nan da can taga tarin mutane a gidan nasu kuma babu ummanta sai kuka, kuka kam sunyi shi ita mahaifinta har akayi sadakar bakwai basu dawo daidai ba, da qanwar maman Na'ima dake yola tace zata dauke ta Yusuf atake daman yace babu wannan zancen, zai riqe 'yarsa abar masa abunsa,ga kuma mahaifiyarsa tana raye zata tayasa kula da Na'iman, haka ta haqura bayan zaman makoki takoma gidan mijinta babu Na'ima.. Haka rayuwansu ta cigaba me cike da gibi babba, in sun tashi da safe daman tsaf ze wanke 'yarsa ya shiryata, tare zasuje siyo abun karyawan su dawo, sai ya tabbatar ta qoshi sannan ya zuba mata na tafiya wanda zataci a lokacin break, dorata yake bisa Keke su tafi makaranta, a lokacin break daman tun fil azal ma gurinshi take cin abinci, da zaran an tashi kuma ba gida yake maida ita ba, can gurin goggo yake kaita sannan ya wuce gurin sana'arsa a kasuwa,daga gurin goggon ne kuma zata sake shiryawa ta tafi islamiya, sai ya dawo kuma ya sake daukanta su wuce gida wanda babu yanda ita goggon batayi dashi akan ya bar mata Na'iman ba amma abun yaci tura, shidai be fito fili yace A'a ba, amma bini bini in 'yarsa na gidan to ko ya dawo anan zai kai har dare, har se goggon tace ya tafi, da fari yana tafiya gida ya kwana shi kadai amma daga baya sai yayi shinfidi nan bakin kofar goggon yace nan zai kwana, da ta tambayesa dalili yace "goggo gidan yana sakamin kunci arai kullum na shigesa" ganin haka yasa tafara barinsa ya tafi da Na'iman in yaso in sun taso daga makaranta sai ya kawota, dan lamarin Yusuf babu alamun qara aure nan kusa kuma.... Ina labarin Ayuba da dan'uwansa  Nasiru? dan lubabatu tayi nata auren da da dadewa daman har da yaranta manya anan qauyen dake kusa da garin, shi dama Ayuba mata biyu garesa ta farko Jummai sunanta yara na kiranta umma, sannan ta biyu mai suna Abida ana kiranta anty Amarya, shikuma nasira Matarsa Mai suna Laraba yara na kiranta da umma laraba har 'ya'yanta ma haka suke kiranta, Ta fannin gidan Ayuba dai Allah ya hadasa da guda daya shima, dan jarabar Umma har shi Ayuban tsotsewa take balle anty Amarya, irin fitinannun matan nan ne wanda su a rayuwa kar a zauna lafiya ga son abun duniya, cikin 'ya'yanta mata babu wanda bata dorawa tallan abinci kuma ko nawa za'a kawo mata ko da akwai qari akan kudin baruwanta itadai lafiya lafiya, A lokacin da Binta ta rasu bayan an kwana biyu tisa Ayuba tayi a gaba sai ya dauko mata Na'ima, yarinya ga kyau ba qaramin kudi zata kawo mata ba, to sai aka samu akasin shi Yusuf ba irin mutanen nan bane masu saka saka da lamura, yayun nasa ma tun sa'in da ya fahimci irin rayuwar da suka daukowa kansu , ya rage shiga sabgoginsu, haka duk suka zubawa Yusuf idanu yana kula da 'yarsa tare da tallafin goggo.... Ranan Na'ima suna kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta ita da mahaifinta, ya tsaya nan wani kanti ya siya mata biscuits da sweets tanata murna, saida ya bare mata ya bata tafara ci sannan ya hau keken suka qarasa gidan goggo, sun sameta zaune nan kan taburma a tsakar dakinta hannunta riqe da tasbaha tana zikr, bayan Yusuf ya gaishe ta, Na'ima ta miqo mata ledan biscuit din tana murmushi tace "goggo gashi kici kema" ta qarasa maganan cikin muryanta me sanyi hadeda yarinta, murmushi goggon tayi itama tace "kici abunki Na'ima, Allah yayi albarka" Na'ima ta gyada kai ta zauna nan kan taburman, miqa hannu goggo tayi qasan gadon karfenta ta ciro musu kwanon abincinsu da take ajiyewa kullum kafin su dawo, miqawa Yusuf tayi yananan zaune, Na'ima ta miqe ta debo musu ruwan wanke hannu, tare suka ci abincin anan dakin goggon suna hira jefi jefi har suka gama, sai da Yusuf ya miqe zai wuce kasuwa goggo tace "zan aika yarinyar nan taje gidan kawunanta su gaisa anjima tunda babu islamiya" Yusuf yace "toh goggo can din zanje daukanta kenan" goggo ta girgiza kai tace "ai ba wani dadewa zatayi ba" ya gyada kai sannan sukayi sallama ya shafa kan Na'ima dake yi masa murmushin sannan ya fice Bayan fitarsa ne goggo tace da Na'iman "maza yi sallah sai kiyi wanka ga kayanki nan na fitar miki, kije gidan kawunki ki gaishesu" gyada kai Na'ima tayi tace "gurin anty Amarya?" Goggo tace "A'a har umma ma duk zaki gaisar in kinje" ta amsa da "toh" sannan tafara yin abunda aka sata.. Bayan Na'ima ta shirya goggo tace ta dauki biscuits din nata taje, dayake gidan kawu Ayuban

Chapter 11 of 19