Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nasu cikin gidan daya kasance babba wanda kana gani kasan masushi dasu ake murza nera a qasar suka hango Mami tsaye a entrance din building din ta fito Jin qaran mota, dasauri nafisa ta fice bayan sunyi parking tayi wajenta da gudu gudunta, Mami ta ware hannu tana dariya tace "oyoyo yarana" nafisa ta rungumeta tana murna cikin nutsuwa na'ima ta qaraso tana murmushi itama, Mami ta sake nafisa ta rungumota tana cewa "welcome habibti" kaso tamanin cikin damuwan da na'ima ta taho dashi taji ya washe jin embrace din Mami,cikin raha suka qarasa cikin main falon gidan suka bar Al'ameen yana debo musu kayan nasu megadi yana tayasa. Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 07 Sunga gata gurin Mami don tun kafin suyi wanka su huta ta fara sallamansu da home made juices datayi musu na musamman. Al'ameen ya shigo musu da kayan mami tasashi yakaimu dakunansu, Bayan sun huta kadan anan falon suka nufi stairs gurin dakunansu dake jere gefen na Mamin, na'ima ce dakinta daf da falon mami Tasamu dakin sai tashin qamshin turare yake, ko ina neat ta miqa hannu kan gadon ta dauko teddy bear dinda Abubakar ya taba kawo mata farkon zamanta gidan, ta rugume teddyn tana bin dakin da kallo kamar yau ta barshi,qarasawa tayi ta bude babban wardrobe dinta, nan ta ga kayanta jera cikin tsanaki sai qamshi suke ga sabbin kaya a gefe masu yawa an jera matasu wasu a hanger, tana nan tsaye gaban wardrobe din a sannu farin ciki yake samun waje cikin zuciyarta aranta tace "I missed this" lallai tayi missing pampering dinda mami take mata, and she made the right choice coming back Mami ce ta shigo hannunta riqe da sabbin towels wankakku tana cewa "Kinga dazu fa nace lantana ta jera muku su a bandakunan ku, ashe ta manta" na'ima ta qarasa da fara'a zata karbesu daga hannun Mamin, bata miqa mata duka ba ta dauki uku ta bata tace "sauran na nafisa ne" na'ima tace "bari nakai mata mami" tace "a'a kiyi wankan tukunna sai ku sauqa qasa ga abinci can, Na'ima ta amsa da "toh" Mami tayi murmushi tace "welcome home daughter" itama murmushin tayi kawai batace komai ba Mami ta juya ta fita daga dakin tajiyo shiganta dakin nafisa. Bayan tayi wankan ta shirya cikin simple black abaya mara nauyi tayi daurin dankwali da mayafin ta fice, tasamu nafisa a falon har ta fito itama suna magana da Al'ameen da Abubakar wanda yadawo daga school babu jimawa. Abubakar ya taso da fara'a yace "Anty nah oyoyo" na'ima na murmushi ta shafa kansa tace "kaima oyoyo". Cikin walwala suka zauna nan falon aka fara hiran yaushe gamo. Mami ta fito daga kitchen dinda ke babban falon  hannunta riqe da food flask tayi gurin dinning area tana jerashi jikin sauran 'yan'uwansa kan table  tace "abar surutun haka,kuzo kuci abinci tukunna" suka miqe dukansu suka qarasa dining din , bayan sunyi settling nafisa tace "Mami, Abba fa??" Mami tace "yana gurin aiki ai kinsani,bakuyi waya bane" nafisa ta janyo coolern dataga favorite dish dinta ta fara zubawa a plate tace "yacemin he'll be home when we arrive" Mami tace "bai baro gurin aikin ba tukunna" ta juya tana maida hankalinta kan Na'ima data fara cin abincin da ta zuba, tace "Habibti ki dudduba coolers din ko akwai favorite dinki" Nafisa tace "tuwon da ta zuba shine favorite dinta Mami" Abubakar juya yana kallon Na'ima yace "tuwo kuma anty" Na'ima ta gyada kai sannan tace "Ina yah faruk fa" Al'ameen yace "wannan ya fice aiki tun safe ai" Mami ta qara da "sai dare ma zai dawo halan, yace they have a lot of works" na'ima ta gyada kai tacigaba da cin abincinta. Daren ranan bayan Abba yadawo yaci abinci ya huta sukaje gaishesa cikin babban falonsa, bayan sun shiga da sallama nafisa ta qarasa kusa dashi ta zauna tana fara'a tace "Abba" shima cikin fara'a ya amsa da "yaran Abba, kun dawo lafiya" na'ima ta qaraso zata zauna nan qasa yace "tashi ki zauna a kujera daughter"  tana dan murmushi tace "nan yayi" ya sake insisting ta tashi din sannan ta tashin ta zauna a wani kujera dan nesa dasu,Mami ta shigo falon hannunta riqe da tray na tea flask da cups akai na'ima ta miqe ta karba ta qarasa  ta ajiye nan table din dake gaban Abban ta koma ta zauna, Mamin ta wuce dakin dake nan falon yin uzuri. Suka gaishe da Abban ya amsa yana tambayansu karatun nasu Nafisa na tsiyaya masa tea din a cup tace "Abba abokinka dinnan has been very helpful a lot, watanni biyu ma dasuka wuce shi yakaimu London gidan anty Amnah" Mami ta fito daga dakin ta qaraso ta zauna nan gefensa itama, Abban yace "haka yakamata ai, kuma yana bani report ai yace kuna qoqarin karatun balaifi" ya juya yana kallon Na'ima yace "haka ko na'ima"  na'ima tace "Eh Abba" Mami tace "nafisa zaka tambaya don na'ima bani da haufin tana karatu" murmushi na'ima tayi tace "nafisa tana karatu fa sosai Mami" Nafisa tayi saurin amsawa da " sosai sosai ma" Atare Abba da mami suka juya suna kallonta, Abba yayi murmushi yana kai cup din shayin bakinsa while mami da na'ima suna yar dariya sanin halinta. Sunanan falon suna hira Al'ameen yashigo falon da sallama yayi settling shima a kujera yadan dukarda kanshi tareda cewa "barka da dare Abba" Abba ya amsa then followed by Abubakar shima yaqaraso ya zauna kusada Al'ameen din. Har kusan karfe tara suka kai suna hira, na'ima ta sake anata hiran da ita jefi jefi take sa baki, nafisa na bawa iyayen nasu labari game da rayuwarsu a England din na'ima na tayata kadan kadan, by then sun sauqo qasa itada nafisa da Abubakar kan babban carpet din dake shimfide a falon hannunsu riqe da kofin shayin da nafisa ta zuba musu daga cikin na Abban. Faruk ne yayi sallama ya shigo cikin sanyi alamun gajiya a tattare dashi, yan'uwan na amsa masa tareda sannu, nafisa ta ajiye tea din ta miqe tana riqo hannunsa yana fara'a yace "yan gatan mami sun dawo kenan"  yajuya ya kalli Na'ima yace "habibtin mami, kun iso lafiya" tana murmushi ta amsa da "lafiya yaya" suka gaisheshi gaba daya ya amsa tareda zama nan qasan carpet shima yana me gaishe da iyayen nasa, suka amsa Mami na tambayanshi gajiyan aiki  Abba yace "arinqa sararawa jiki da brain din dai babana" faruk yace "Abba aikin ne these days suna buqatan lokaci sosai" Abba yace "Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin Mami ta tambayesa ko yaci abinci ya girgiza kai. Nan falon nafisa ta kawo masa abincin yanaci aka cigaba da hiran dashi cikin raha.   Cikin walwala da fahimtar juna iyayen ke gudanar da hiran tsakaninsu da yaran nasu, wanda hakan yasa yaran suke bude cikinsu openly suna fadan abunda ke mind dinsu wajen iyayen, idan fannin gyara ne take iyayen suke gyara musu cikin lumana,idan na raha ne suma ayi dariyan dasu. And for that moment Na'ima knew..This is home These people right here Are like missing piece of her heart And she won't trade them for anything. Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 08 Washegari.... Na'ima ce zaune kan sallaya bayan ta idar da sallahn asuba hannunta riqe da qaramin carbi tana azkhar, bayan ta gama ta dauki Quran din gabanta ta kaishi ta miqe ta kaishi ma'ajiyansa sannan ta nade sallayan, bata cire hijab dinta data dora kan dogon kayan baccin jikinta ba ta fice daga dakin ta shiga falon mami dake nan kusa da nata dakin, ta samu Mami zaune itama bisa sallaya tana azkhar Mamin tace "na'ima kin tashi" cikin sanyi tace "Eh" ta qaraso ta zauna tace "Ina kwana Mami" Mami ta amsa "lfy habibti,how was your night" tace "Alhamdulillah" suna nan zaune nafisa ta shigo itama sanye da hijab ta zauna tana gaishe da Mamin sannan ta juya suka gaisa da na'ima Mami tace "baby, meya samu idonki haka?" dan wutan falon tar yake a kunne hakan yasa ta ga idon nafisan wanda yadan kumbura, nafisa tafara hamma tace "bacci ne bai isheni ba Mami"  Mamin tace "aikuwa kije kiyi don ga idonki nan ya nuna" Nafisa ta miqe ta shige dakin Mamin Sanin Mami zata Dade zaune nan bata tashi ba yasa Na'ima miqewa ta shige dakin itama, ta qarasa kan gadon Mami da nafisa ke kai ta kwanta tana jawo bargon, nafisa ta juyo tace "kinsan Allah, har wani banging kaina yake" Na'ima tace "sannu sis,halan bakiyi bacci da wuri ba jiya" nafisa tace "fada mukayi da mutumin,in na tashi zakisha labari" na'ima tace "kuma dai, yi baccin to" nafisa ta juya tana gyara kwanciyanta, da haka suka koma wani baccin Sai wajen qarfe takwas Na'ima ta tashi ta fita daga dakin tabar nafisa dake bacci, sanin Mami na bangaren Abba yasa ta wuce nata dakin ta shiga wanka, bayan ta shirya ta sauqa babban falon dake downstairs, hango faruk tayi zaune dining yana breakfast shikadai hannunsa riqe da waya yana dannawa, ta qarasa wajensa da murmushinta, ya dago kansa daga abunda yakeyi yace "habibtin Mami harkin tashi" taja kujera daya tazauna tace "Eh yah faruk badai har fita zakayi ba" yace "yeah, I'm swamp up with work at office these days wlh" tace "Ayya, Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin sannan yace "kun sake zuwa kallon wani match din keda nafisan kuwa?" Kafin ta amsa taji nafisan dake bayansu tana tahowa tace "me nafisan tayi da sassafen nan yah faruk" ta qaraso taja kujera itama faruk yace "laifi kikayi babba" na'ima na murmushi tace "he was asking ko mun sake zuwa football match" nafisa ta kalli ya faruk tace "can you believe the tickets were sold out within 24 hours" faruk yace "may be baki siya da wuri bane, first hours akafi samun tickets daman"  Zatayi magana aka kirashi video call a WhatsApp dinsa, yadan dagawa nafisan hannu yace let me take this, ya dauka yana kallon fuskan wanda ke cikin wayan yace "Good morning yaya" ta daya bangaren Ahmad ya amsa cikin deep voice dinsa yace "morning faruk, ya mutan gidan?" Faruk yace "Alhamdulillah" Ahmad yace "Good...I've send you some papers via email, I need your review on them" faruk yace "sure, ba matsala yaya" nafisa tazo bayan faruk tasako kanta tace "Good morning yaya" Ahamd ya amsa "lafiya nafisa, yaushe kika dawo?" ta amsa da "jiya,yasu mamma?" Na'ima dai na sauraronsu tana binsu da kallo, saita samu kanta da sauraron na cikin wayan jin yanayin accent dinsa that was so thick and it sounds British but not that deep British. Bayan sun gama gaisawa Ahmad ya maida hankalinsa kan faruk yace "please do take a good look on them I need answers, karka dau lokaci" faruk yayi murmushi yace "in Sha Allah yaya, I'll drop by tomorrow to give you the feedback" Ahmad yace "see you then,thanks Man" sukayi sallama nafisa na kallon faruk tace "wai yadawo gari daman" faruk yace "ya rigaku dawowa ma" tace "ya Adam fa?" ya amsa "wannan yana gari da dadewa ma ai, what's with the questions?" Tadan daga kafada tace "I just want to know ne" . Na'ima ta miqe ta wuce kitchen tabarsu nan suna magana. Shiganta kitchen tasamu lantana tana aikin hada breakfast dinsu ta gaishe da Matar da kana ganinta kasan she's in her late 30's fuskanta cike da bille. Na'ima tace "mama sannu da aiki,Ina kwana" lantana ta amsa "lafiya habibitin Mami, jiya kun dawo bananan ko" Na'ima tace "Eh mama, ya hakuri Kuma Mami tace an muku rashi" lantana tace "wlh dai,can suleja naje, yar wata qanwata ce ta rasu,yarinya qarama da ita, jiya kwanana hudu acan" na'ima tace "Allah sarki, Allah yasa mai ceto ce" lantana tace "Amin habibitin mami, bakiga yarinyar ba kuwa fara sol kamar ke dinnan, abundai abun tausayi" na'ima tayi murmushi ta fara tayata aikin, suna aikin lantana na bata labarai gameda rasuwan wanda itadai na'ima ba fahimtan wasu take ba, nafisa ta shigo itama suka gaisa lantana na fada mata uzurin rasuwan, bayan nafisa ta gama nuna nata alhinin  tace "mama kince zaki soya mana gyada mai gishirin nan idan zamu dawo" ta qarasa maganan tana taya lantana bare maggin da zata saka a pepper soup dinda ke dahuwa nan gabansu, lantana tace "aikuwa yau zan soya muku" Nan suka kammala sauran aikin tareda lantana, Mami ta shigo kitchen din bayan sun gama tace "sannu lantana,sannunku kuma" suka amsa. Ta dauki breakfast dinsu ita da Abban ta tafi kaiwa can falonsa while su nafisa suka kai nasu dinning lantana na tayasu, basu jima da fara ci ba su Al'ameen da Abubakar sukayi joining. Bayan sun gama suka kai kayayyakin kitchen suka dauraye, don ladabtarwan mami ne akan bakomai mai aiki zatayi musu ba,abubuwa da dama dakansu sukeyi a gidan. bayan sun gama nafisa ta fice, na'ima ta dauko plate ta debi sauran cupcakes dinda mami tayi musu jiyan ta wuce upstairs, shiga dakin nafisa tayi ta sameta gaban madubi zaune, na'ima ta tafi ta zauna kan gadon nafisan dake gyare neatly ta ajiye snacks din hannun nata tace "oya..spill the beans, meya hadaki da umar din jiya?" Nafisa ta baro gaban madubin tadawo bakin gadon itama ta zauna tace "sis I don't know what is wrong with Umar, bansani ba ko jealousy ne ko kuma insecurity ne yake damunsa, kai duka ma" na'ima tace "Amma ai so ne yasa hakan sis" nafisa tace "Ina sonsa ai nima but this is too much and i hate it with all my heart, sometimes I wonder why i stayed with him for this long and why i can't let go" na'ima tace "I know that loop, kinsani...I know what it means to be trapped In a loop going around without escape" nafisa tace "But...." Sai kuma tayi shiru tana kallon Na'ima tarasa abunda zatace Na'ima tayi dan murmushi me ciwo tace "shiyasa bazan taba judging dinki ba akan wannan conflict relationship din da kuke having, the guy loves you and you do too, try and resolve things tunda kowa yasani ba iya rabuwa zakuyi ba" ta qarasa tana murmushi. Nafisa ta dau cake daya takai baki tace "tabdi, rabuwa kai, jiya ma nace masa I'm done yayi fushi kuma nakashe wayana" Na'ima ta jijjaga kai tana dan cin cake din itama tace "nidai banason ku rabu, Ina laifin mai kishinka nafisa?" Nafisa ta miqe ta koma bakin madubi tafara cleansing fuskan ta tace " I'm serious this time" Na'ima ta jijjaga kai tana dan dariya kawai, ta janyo laptop din nafisa dake kan bedside drawer ta kunna zata fara kallo. Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 09 A Week Later... Na'ima ce zaune cikin dakinta akan gado, hankalinta yana kan abunda take typing cikin laptop dinta, yau satinsu daya da dawowa gida and a lot has happened, sunje shopping, nafisa ta jasu outing cikin gari and all other fun things, jiya ma part dinsu ya farukn dake gefen main building din gidan suka wuni suna game din ps wanda har da Al'ameen da Abubakar din sukayi. Nafisa ce ta shigo dakin hannun ta riqe da leda ta miqa mata, karba na'ima tayi tana duban cikin ledan taga sweets da chocolates masu yawa, nafisa tace "karki fado sunana idan mami ta kamaki kinasha wlh" na'ima tayi dariya sanin Mami ta hanasu yawan shan kayan zaqin, farkon dawowansu ta barsu sunasha amma ganin suna iya shanye chocolate kusan ashirin a zama daya tace bataso, karsu sake siyo kayan zaqi masu yawa a gidan. Nafisa tace "ki shirya muje gurin fitting dinnan meerah nata kirana a waya" na'ima tayi mata questioning look tace "fitting kuma?" Nafisa ta amsa "na gown din da zamu saka wajen event din bikin salma mana" Na'ima tace "nifa bazanje event ba nafee" zama nafisan tayi kusada ita tace "meyasa? Mami ta hanaki ne" ta jijjaga kai tace "a'a kawai bazanje bane" shiru nafisa tayi batace komai ba har na'ima ta maida hankalin ta kan laptop din dake kan cinyanta ta cigaba da typing, can nafisan ta miqe ta fita na'ima ta bita da kallo jikinta na sanyi. Fitan nafisa ta shiga falon mami ta sameta nan zaune da faruk suna magana, turaren wutane gaban mamin tana mixing dinsu cikin kwalba, nafisa taqarasa kan kujeran gefen faruk ta zauna Mami tace "baby baku fara shirin fitan bane rana tanayi fa, kincemin zaku fita dazu" faruk yace "Ina zasuje?" Nafisa tace "dama fitting zamuje gurin meerah na gown din event din bikin, Mami kinji Na'ima nacewan bazataje gurin dinnern ba" Mami ta dago kanta daga abunda takeyi tace "ai daman ban aika kayan events da ita ba" kafin nafisa tayi magana faruk ya katse ta da "Ai tafiki hankali datace bazataje ba" nafisa tace "haba yah faruk it's just event fa" yace "yes but nafee kinsan kalan mijin da salma zata aura ai, you know who he is, yawanci guys masu ji da tashe acikin Abuja da wajenta zasu halarci event din, you can't be exposing na'ima to that sort of places" Mami dai na sauraron fadan da faruk yakewa nafisan batace komai ba, nafisa tace "but yah faruk i thought it's high time she starts living her life, doing the things she likes the way she wants to" Mami tace "Many things but not this nafisa, and you know things are not over yet" Nafisa na kallon Mami tayi shiru batace komai ba, Mami ta cigaba "quite sure zataje gidan bikin ta gaisa da wasu 'yan'uwan because it'll be rude of her not to,tunda komai dadewa zasu iya haduwa da ita a cikin gidan nan, but not going to parties...and that's final" nafisa tace "Yes Mami" ta miqe ta fice daga dakin suka bita da kallo. Haka suka shirya Na'ima zata raka nafisan gurin dinkin, cikin abaya na Na'ima black while na nafisan maroon color, bayan sunyi sallama da Mami ta basu saqon toiletries da zasu biya super market su siya mata, suka fice a motan nafisan. Bayan sun isa babban fashion store din wanda yakasance gurin dinki, designing da kuma saida dinkakkun kaya suka tadda meerahn tsaye a reception tana magana da receptionist din nata, ganinsu na'iman yasa ta tako garesu tana murmushi tace "look who we have in town" ta qaraso tayi hugging din nafisa suna fara'a sannan ta juya tayi hugging din Na'ima tasake cewa "I've been waiting for you guys like for'everr" na'ima na murmushi dan tasan meerah, ita tayi mata duk dinkunanta farkon zuwanta gidansu nafisa, Nafisa tace "sorry sis" meerah na fara'a ta amsa da "now you have to pay me double" sukayi dariya gaba daya ta jasu suka tafi fitting room din,bayan tayi serving dinsu ruwa na'ima na zaune kan resting sofa wasu staff mata guda biyu suka shigo tare da meerah suka hau gwada nafisa dake tsaye kan gajeran stool, nafisa tace "husna tazo kuwa?" Meerah tace "tazo almost a week now" Bayan angama sukayi salla a shagon dinki sannan suka wuce gurin aiken da mami ta musu, basu suka dawo ba sai yamma. Shigowarsu gidan bayan sunyi parking Na'ima ta lura da wata baquwar mota, wata sleek ride dake fake nan parking space din, suka fito Nafisa ma data lura da motan tace "Su yaya Ahamd sunzo kenan" suka wuce cikin gidan hannun nafisa riqe da ledan kayan da suka siyo. Shigarsu falon Na'ima ta hango Mami zaune da wasu maza biyu zaune kan kujera sunyi backing dinsu, dayan yana having conversation da Mami while dayan yana riqe da waya a hannunsa yana kallonsu mamin, qarasawa sukayi cikin falon nafisa na gaba, Mai maganan yadan dago ya kallesu yace "Nafisa" ta amsa da "Yah Adam sannunku da zuwa" yace "yauwa" Mami tace "baby kundawo" nafisa tace "eh Mami" Suka qarasa nafisa ta ajiye kayan gaban Mami sannan suka zauna kan kujera kan Na'ima na qasa, Nafisa ta sake cewa "Yaya sannunku da zuwa, Ina wuninku" Ahmad ya dago cikin husky voice dinsa yace "lafiya nafisa" shima Adam ya amsa, Cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tadaiji Adam ya amsa amma mai deep voice din da ake kira da Ahmad dinne bataji ya amsa ba, tadan dago kanta ta kalleshi, Caraf idonta cikin nasa yana nazarinta. Kauda idonta tayi da sauri ta maida kallonta kan tv dake falon tanajin bugun zuciyarta acikin kunnenta, Tunda take bata taba ganin idanun da suka mata kaifi takasa jure kallonsu kaman na bawan Allahn nan ba. Shima Ahmad dauke idonsa yayi yana cigaba da danna wayarsa, Mami tace "kadai ce bazaka dawo gida ba Ahmad, ka riqe Lagos dinnan har dawowa yana maka wahala" Ahmad ya juya ya kalli Mami a nutse yace "akwai wasu abubuwan danakeson nayi settling ne acan mami" Mami tace "ai zamanka dai anan din yafi,tunda can din bawai iyali ka ajiye ba" ta cigaba tareda juya wa tana kallon Adam "kaima Adam baka fada masa gaskiya ko" Adam yayi dariya yace "nima gajiya nayi da fada masa gaskiya, may be yanzu zeji taku Mami" Mami ta maida hankalinta kan Ahmad tace "Ai mamma tacemin kunyi maganan kuma har yanzu baka dawo ba" Ahmad yadan shafa kanshi yace "in Sha Allah za'ayi yanda kuka ce din Mami" Itadai na'ima duk ta taqure acikin falon kaman ace cass ta arce, Adam ya juyo yana kallonsu yace "nafeen Mami yaushe kika dawo?" Nafisa da tunda ta gaishesu ta maida hankalinta kan waya ta dago kanta tana murmushi tace "for a week now yaya" yace "Ma Sha Allah, kin kusa gamawa amma" ta gyada kai tace "Eh saura 4 to 5 months haka" yace "Allah ya bada sa'a" yana kallon Na'ima da tun dazu idonta ke kan Tv bata juyo ba yace "Mami baquwa kukayi ne" Mami ta amsa da "Eh 'yar dan'uwana ce dake can Nijar,tare suke karatun da nafisan ma" Adam yace "Allah sarki" Mami tace "zo ku miqamin kayan sama in na shigo zan waresu" na'ima ceh farkon miqewa kamar wanda falon ke mintsini, Ahmad yadan dago ya sake kallonta ta qarasa ta karbi kayan, nafisa tace "to yaya sai anjimanku" suka amsa da toh, tabi bayan na'ima da har ta isa stairs, suna shiga falon mamin nafisa tace "ke yanzu naga texts din mutumin bari kiga" Na'ima dataji duk kafafunta a sanyaye ta nemi kujera ta zauna anan falon tana tuna idanun wannan bawan Allah data baro a falo, nafisa ta qaraso kusa da ita tana nuna mata wayan tace "Kiji wai yanzu ma yana hanya zaizo" cikin sanyi na'ima tace "kibarshi yazo sis, you have to settle fadan nan naku once and for all" nafisa tace "Allah ko?" Na'ima ta gyada kai, shiru nafisan tayi kamar me nazarin wani abu sannan ta miqe ta tafi dakinta,diban kayan na'ima tayi ta dorasu kan table din dake nan falon sannan ta fice tana ture duk wani tunani daga ranta. Bintu Musa ce ✍🏻 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read My Book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen::https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 10 Daren ranan after maghrib suna zaune falon Mami itada nafisa, ipad ne a hannun Na'ima tana game don tunda suka dawo gidan bata bude wayanta dake ajiye cikin box dinta ba Hira sukeyi jefi jefi da Mami dake zaune itama tana kallon hiran da akeyi cikin tv a tashar BBC, Mami tace da nafisa "baby kina jira sai nace kije ku gaisa da iyalan uncles dinki ko?" Nafisa ta dago daga danna wayan datakeyi kwance a kujera tace "Mami I thought tunda za'ayi bikin nan basai naje bafa" Mami na kallonta tace "ke tunaninki bazai baki kije ku gaisa kafin ku hadu a gurin bikin ba ko, for a week now na zuba miki Ido ai" nafisa tayi shiru batace komai ba Mami ta cigaba "gobe ki shirya kuje tareda Na'ima ku gaishe su and that's final" Nafisa ta amsa da "Yes Mami" Mami ta maida hankalinta kan Na'ima data ajiye ipad din nata jin mamin na magana tace "Habibti, gobe kuje gidansu baba ku gaishesu" cikin sanyi na'ima ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" bayan sunyi sallahn ishansu nan

Chapter 3 of 19