Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
'yan school naku da za'a yi yau" Na'ima tace "nafisa tace zataje" yana kallonta yasake cewa "bakyason zuwa?" sai Na'ima taji tanason zuwan tare dashi, jijjaga kai tayi tace "A'a inaso" Ahmad ya fara tattare mata kayanta yana sawa a jaka suka miqe, sai da ya biya kudin abunda taci itada zarahn wanda Na'ima tana ta magiyan ya bari yace A'a, sannan suka fice daga Cafe din.. Isarsu London bridge din suka samu acike da mutane ta ko Ina, ahaka ya kamo hannunta suka kutsa cikin mutanen har suka kai gaba inda suke kallon komai a gabansu, Na'ima tsayawa tayi tana kallon racers din da duk suke cikin nasu boat din suna jiran abasu dama sufara, Ahmad ya sunkuyo yace mata "a bayan wane team kike?" Tadan kallesa tace "na makarantar mu mana, kaifa?" Ahmad yadan daga kafada yace "ya na iya, ina bayan na makarantar naku nima" ta danyi dariya tace "da Cambridge ka zaba?" yana murmushi yace "kedai ina bayan nakun kawai" ta cigaba da dariyan tadan jijjaga ta maida hankalinta gurin tseren.. Wasa yayi dadi saiga Na'ima har da ita acikin masu ihun son team dinsu suci, Ahmad sai kallonta yake yana dariya ganin ta dage itama tana daga hannu tareda cewa "go,go,go" wayarsa ya ciro yafara daukanta hoto batasani ba, ana cikin haka ta hango nafisa da team dinsu daga dayan bangaren bridge din sai yekuwa suke, dukansu sanye suke cikin blue din polo shirt da facing cap, turawan duk suna sake cikin gajerun wanduna baqaqe while nafisa ta saka dogo ita..Na'ima tadan tabo Ahmad tana dariya tace "yaya ga can nafisa" kallon gurin yayi yana dan girgiza kai ganin su nafisan sun dage da ihu harda waqa yace "Hajiya Nafisa".. Makarantar su Na'ima ne suka lashe kofin wasan, dazasu bar gurin bakinta yaqi rufuwa dan murna sai hiran take wa Ahmad shidai yanata binta da kallo ganin fara'anta abun sha'awa, tana yi masa kyau in tana dariya... Basu hadu da nafisa ba dan tabi 'yan qungiyarsu sun tafi, Ahmad dinne ya maida Na'ima gida ranan, rikice masa Na'ima tayi akan ala dole bazai shiga gidan ba, yana dan dariya kuma yana kallonta kamar yau ya fara ganinta, ta wani bata fuska bata sake cewa komai, ganin haka yasa Ahmad din yana murmushi yace "Okay,Okay, bazan shigan ba, are you happy?" ta gyada kai ta juya ta bude motannan sannan ta fita yana kallonta har sannan bai daina murmushi ba, hakanan ya hakura yaja motansa yatafi tananan tsaye, tabi bayan motan da kallo sannan ta juya ta shige gidan..... Bintu Musa ce ✍️📚 https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Chapter 21 Zaune suke a falon suna hira banda Laila da ta wani bata fuska tanajin ranta duk a dagule, wayanta ne riqe a hannunta tana sake trying line na Ahmad for the 50th times baya tafiya, ta sake buga tsuka tanajin kamar tayi ihu ko zataji dadi, Anty murja ce ta kalleta tace "ke kuma ke da wa? meye hakan muna zaune zaki rinqa mana tsuka" adan fusace Laila tace "babu ruwanki dani" Anty murja zatayi magana Mummy ta dakatar da ita dalilin daga mata hannun datayi, shiru murja tayi ta kama hararan Lailan... Mummy ta juya tana kallon Lailan tace "Wayan nasa bai shiga bane Auta" Laila tayi cilli da wayan anan kan kujera tace "Mummy da alamu blocking dina yayi, kuma wallahi zai san ni yayi blocking" Anty murja ta buga wani tsukan itama tace "banza wahalalliya, an fada miki namijin da baya yinki zai taba sauraronki ne, kin tsaya kina batawa kanki lokaci kamar wata mayya, may be yanacan ya samu wata ma bata ke yake ba" Nan Laila ta miqe ta fara masifa idonta rufe tana cewa "nifa ki fita harkata kar in karta miki rashin mutunci..kuma wallahi kinji na rantse ko za'a hada sama da qasa sai Ahmad ya aureni, ni kadai dinnan zaki gani" Mummy dake kallonta tace "to wayace daman bazai aureki ba Auta, ai hanyar da kikaqi tun farkon ita zamu bi yanzu, cikin sauqi ze shigo hannunki" Anty murja tace "barta mummy ta tsaya nan, anfada miki zamanin yanzu ko da namiji yana sonka basai ka hada da dan dabarbarun layoyin nan ba sannan a zauna lafiya, balle ke naki ma a fili kowa yasan Ahmad baida lokacin ki" Laila ta koma ta zauna tana hucin takaici tace "Dama lokaci nabasa ai mummy, a tunani na zai dubi kulawata a garesa amma gaskiya ni yanzu ko me za'ayi masa ma ayi, kuma wannan karon a hada da wannan sadaka yallan datazo gidansu Nafisa, kin tunata ai" Anty murja tace "wace kuma haka?" Laila ta amsa da "wata shegiya ce tana zama agidansu nafisa ta debo fari kamar wadda jini ya qare mata a jiki, ni tun ganina da ita na farko daman batamin ba" anty murja na sauraronta ta sake cewa "meya hadaku to?" Laila ta fara bata labarin abunda ya faru ranan da Ahmad yaje daukansu anty Amnah gidan Salma da kuma abunda ya faru a Airport ta qara da cewa "Ina tsaye Ahmad ya rinqa kakkama yarinyar nan a gabana Anty murja" murja da wangale baki ta kalli Mummy dake sauraron Lailan for the second time itama, dan tun ranan da abun yafaru Lailan ta fada mata Mummy ta sauqe numfashi cikin isa tace "duk me sauqi ne wannan Auta, ita wannan yarinyar qaramin issue ce, shi Ahmad din zamu bullowa da farko" Laila ta matsa kusa da mummyn ta kwanta a jikinta tace "wallahi kuma duk sai na rama shariya da wulaqancin da yayi min bayan aure, se ya gane kuransa" mummy da anty murja suka fara dariya Mummy na shafa kan lailan tace "tsaf ma kuwa Auta har fin hakan"..... Ranan talata sunje makaranta gurin supervisors dinsu, Ahmad ya kira Na'iman a lokacin da ta fito daga office din malamin, dauka tayi tafara gaisheshi, a nutse ya amsa mata sannan yace "where are you?" ta daga kai tana duban sunan arean da taken a rubuce saman ginin gurin, fado masa sunan wajen tayi sai yace mata "supervisor'n ya ganki?" ta amsa da "Eh" sai shima ya fada mata inda yake nan wani car park da ake kiran gurin da Westgate, Na'ima ta amsa da "Okay, bari na kira Nafisa ko ta gama abunda takeyi itama" Ya amsa da "Okay" sannan ya kashe wayan, kiran nafisa tayi daga can bangaren tace "kinganni yanzu ma fitowa nayi daga office din dan amsa kiran, ki dan bani mintunan kadan sai mu tafin" Na'ima tafada mata inda zata samotan inta gama sannan ta kashe wayan ta nufi car park din.. Tsaye Na'ima ta hangosa a jikin motansa yau kuma har da glass din sa a fuska, ta nufesa idonta na kansa ganin yanda baqin glass din ya qara masa wani masifaffen aji, bata kai da qarasawa gurinsa ba taga wani guy ya fito daga mota nan kusa da ita yace "Na'ima" tsayawa tayi da fara'a tace "yaya Umar" ya rufe cab din motan ya dan taho gurinta yana murmushi yace "idonki kenan a qasar nan, Ina nafisa?" Na'ima tace "kayi hakuri ai munzata ma ka bar England gaba daya" ya girgiza kai tareda cewa "inanan" gaishesa tayi ya amsa sai kuma ya fara tambayanta ya karatu, Na'ima ta daga kai ta hango Ahmad tsaye yana facing dinsu at the same time yana kallonsu, juyawa tayi tana bada amsa a guy din akan wata tambaya daya mata na ko sun kusa gamawa, tana cikin magana ta hango Ahmad din ya taho gurin nasu ta cigaba da kallonsa har ya qaraso nan ya tsaya kusa da ita yana facing guy din, dan daburcewa Umar din yayi sai ya miqa masa hannu da nufin suyi musabaha, Ahmad ya zare glass din fuskan nasa yana kallon cikin idon Umar sannan ya miqa nasa hannun suka gaisa yana amsawa babu yabo babu fallasa, rasa abunda zai sake fada Umar  yayi sai ya kalli Na'ima yace "toh Na'ima sai anjima, ki gaishe da Nafisa please" Na'ima ta gyada kai tana murmushi tace "zataji in Sha Allah, nagode" ya juya ya nufi gurin motansa Ahmad yabi bayansa da kallo, Na'ima ta dan dago kanta ta kallesa ganin irin kallon dayabi muhsin din dashi, cikin sanyin murya tace "meya faru" Ahmad bai dena kallon bayan Umar din ba ya wani hade fuska yace "sai wani kallon cikin idanunki yake yi while he was talking" Na'ima ta dan ware idanu tafara yar dariya tace "tun daga can din ka hango haka?" ya juyo yana kallonta "Eh mana, he kept staring at you" Na'ima tana murmushi tace "ni dai ban gani ba" sai ya sake cewa "but who is he? Your ex?" Na'ima tayi saurin jijjaga kai tace "A'a, abokin yaya faruk ne da ya hadamu dashi farkon zuwanmu school" Ahmad ya gyada kai yace "kallonshi yayi yawa, daya cigaba kawai cire idon zanyi in huta" Na'ima batasan lokacin da tafara dariya ba Ahmad na murmushin shima ya tsaya kallonta baya ko kifta ido, sai da ta tsaya da dariyan yayi qasa da murya yace "I'm serious Na'eemah, for a moment ji nayi kamar in hankadesa" dena dariyan tayi ta tsaya kallonsa cikin Ido tanajin zuciyarta na chanja bugu nan take, cikin kwantar da murya ya qara matsowa kusada ita ya sake cewa "I really want to be your first, kicemin baki taba saurayi ba please Babe" ai nan take Na'ima taji kaman an zuba mata ruwan qanqara aduk jikinta, duk wani annushuwa dake zuciyanta ya bace gaba daya, kauda fuskanta tayi batace komai ba Ahmad ya sake cewa "Babe" taqi kallonsa ma, zai matso kusada ita tadanyi baya tareda cewa "please stop" sai ya tsaya din bai kuma dena kallonta ba, ganin yanayinta yasa a hankali yace "muje mota toh", jerawa sukayi suna tafiyan bawanda yace komai cikinsu.. Sun isa gurin motan kenan Na'ima ta hango Nafisa sai tace masa "ga Nafisan can ma" shima ya juya gurin Nafisan wadda take tahowa fuskanta da fara'a, tana isowa tace "yaya kuyi hakuri na bata muku lokaci ko" Ahmad yace "A'a nafisa badamuwa" ta gaishesa ya amsa sannan ta sake cewa "wallahi riqeni supervisor din yayi and he kept talking in circle, sai je ka dawo yake tayi a maganan bana gane komai, wai nan gyara yakemin a papers din" sai sannan Na'ima tayi murmushi, Ahmad yadan kalleta yanajin ransa na sakewa ganin ta sake fuska... Yau ma nafisa baya ta shige tabar Na'ima da shiga gaban motan, cikin shiru sukayi tafiyan Ahmad na kallon gefen Na'ima jefi jefi ganin ta juya kanta tana kallon window, ya kunna qira'an Qur'ani a motan gashi basu wani tsaya ba kasancewan yau yanada isasshen mai a motan.. Ganin atmosphere din cikin motan ne yasa Ahmad nayin parking a kofar gidan Anty Amnah Nafisa tayi saurin fita, Na'ima da jikin ta yayi sanyi ganin yanda yanayinsa ya koma ne yasa ta juyo tana kallonsa, kuma sai ta rasa me zatace masa ma, shima kallonta yake ahankali yace "I'm going to California tomorrow, wani aiki yataso min" sai Na'ima ta sakejin jikinta ya qara wani sanyin takasa magana, ganin yanayinta yasa Ahmad yadan duqo cikin kwantar da murya yace "Babe..bawani dadewa zanyi ba, it's just a few weeks away" Na'ima ta gyada kai, ya sake cewa "zaki yarda mu rinqa yin video call din in na tafi?" ta dago idanunta ta kallesa, sai ya sake yin qasa da murya yace "Please" itama ta sake gyada kai, sai a sannan tace "Allah ya kaika lafiya" Ahmad yaji addu'an nata har cikin zuciyarsa, yana murmushi yace "Amin Na'eemah"...da haka suka rabu zuciyarsu na kewan juna tun ba'aje ko Ina ba..... Bayan tafiyan Ahmad  California sai ya kasance wayan nasu ba sosai suke yi ba saboda yanda ayyuka suka sha masa kai, dan tafiyar tasa tanada alaqa da expansion din oil and gas company din nasu wanda suke cuku cukun launching anan Los Angeles, Adam ma acan ya samesa suke aikin tare..dalilin banbancin dogon awannin dayake tsakanin qasashe biyun yasa basa samun yin waya akai akai, Dan kafin dare yayi yasamu nutsuwa ita kuma by then tsakar dare ne tayi bacci, sai dai yakan hana kansa bacci watarana in bai gaji sosai ba ya jira har safiyar garin London tayi sannan ya kirata wanda acan kuma shine tsakar darensu.. video call din ma baifi sau biyu sukayi ba shima lokacin ya dan samu sararawa ne within lokacin aikin.. Haka dai Na'ima suka maida hankali itada nafisa kan dissertation dinsu da sukeyi dan sunzo wani fage ne a karatun da ake kira da (Trinity term) ana nufin karshen karatun kenan wanda a wannan lokacin kawai dissertation din akeyi kuma shi yafi exams a fagen wahala, project ne babba kuma dogo da ake daukan lokaci gurin qaddamar dashi, research akan research akeyi kafin a kammalasa... Ahmad bai dawo ba saida ya kwashe tsawon kwanaki ashirin da biyar acan wanda jinsu yayi kamar yayi watanni baiga Na'ima ba, Ranan da zai dawo sunyi waya da ita amma bai fada mata zai dawo din ba, dan lokacin ma yana Airport sai Na'ima tayi tsammanin yana gurin da akwai hayaniya ne bata kawo airport a ranta ba, shi kadai yadawo London din, dan ya bar Adam acan shima daga can din zai wuce Nigeria saboda akwai pending ayyukan da Ahmad yabari acan Lagos zaije ya qarasa su.. Isarsa qasar ko gidansa bai wuce ba ya dira gidan anty Amnah Na'ima na zaune da Anty'n su kadai a falon dan Nafisa ta fice gurin Lauren a lokacin, ganin Ahmad kwatsam yasa Anty Amnah dan ware ido tace "son.. sauqan yaushe haka" Na'ima dake sanye cikin wani yellow boubou na kamfala tafara ware dankwalin zata yafa a kanta, idon Ahmad na kanta, zama yayi a kujera alamun gajiya duk a tattare dashi yafara gaisawa da anty Amnah tana tambayansa hanya, miqewa Na'ima tayi ta tafi kitchen ta debo masa snacks da drinks takawo, nan gabansa ta sunkuya ta ajiye a kan glass table din yana binta da kallo, komawa tayi ta zauna ta gaishesa ya amsa  tareda cewa "ya karatu" tace "Alhamdulillah".. casually suka gaisa wanda in ba fada maka akayi ba bazaka taba cewa there's something going on between them ba.. Magana sukadan farayi jefi jefi shi da anty Amnah sai Na'ima taga ya ciro wayarsa daga aljihu yafara dannawa, wayanta dake hannunta ne taji yayi vibration, ta dan dago tana kallo ganin message ya tura mata me dauke da saqon haka.. 'Gosh..i missed you' dago kanta tayi suka hada ido tayi saurin kauda kanta tana dan murmushi, bata sake kallon bangaren sa ba har saida taga ya miqe yana yiwa anty Amnah sallama akan zai wuce anty Amnah tace ya tsaya yaci abinci ana kanyi ne, yace "A'a anty zanje in huta tukunna" tace "Allah bazaka tsaya ba son, saura kadan fa" ya sake cewa "bakomai Anty, sai anjima" fita yayi Na'ima na nan zaune ta bi bayansa da kallo, sai kuma taji wani message din ya sake shigowa wayanta kamar haka.. 'Babe, bazaki fito in ganki me kyau ba?' Na'ima tayi murmushi ta tura masa emoji me kada kai da kuma gwalo, hakanan Ahmad dake tsaye jikin motan sa ya hakura ya tafi batareda ta fitan ba dan ita saitaji wani kunyan kallon idonsa takeyi ma kodan sun kwana biyu basu hadu bane oho Da nafisa tadawo Na'ima batayi gigin fada mata dawowan Ahmad din ba, Da dare suna kwance itada Nafisan a gado kiransa ya shigo wayanta, dan juyawa tayi taga Nafisa na kallo a iphad dinta nan kwance sannan ta daga kiran, daga can bangaren Ahmad yana zaune a babban falon gidansa ya miqe kafafunsa kan glass table dake gabansa yana kallon movie a Netflix, shiru sukayi bayan Na'ima ta daga kiran sai kuma taji yace "fushi nakeyi kuma baki ma san inayi ba Babe" Na'ima tayi wani murmushi me dan sauti tace "I'm sorry" Ahmad yayi sipping tea dinda ke riqe a hannunsa sannan yace "dagaske nayi fushi kuma bazan miki magana ba" sai ta dan yi dariya tace "yanzun me mukeyi" shima yana murmushin yace "I mean from now on" kawai murmushi tayi batace komai ba tanajin duk wani qofa dake zuciyanta yana budewa cikin annushuwa, daren ranan sunsha hira ba laifi wanda mafi yawan hiran shiru yafi yawa, in sukayi magana daya zuwa biyu zasuyi shiru kamar ba waya suke ba, Nafisa dake gefen Na'ima gar sannan, sau tari sai ta dauka ko sun gama wayan ne sai kuma taga an cigaba da magana, jijjaga kai kawai tayi tana murmushi ta gyara blanket dinta tayi baccinta.. Washegari suna cikin yin breakfast ne anty Amnah tace da Nafisa "jiya yayanku yadawo bakyanan" Nafisa ta juya tana kallon Na'ima with suprise sannan tace "Anty wai jiya jiyan nan?" anty Amnah tace "haka nace fa Nafisa" Nafisa na dan dariya tace "yi hakuri Anty, nadanyi mamaki ne, aikuwa anjima zamu je gidansa, dan inata masa alkawarin zamu kai masa ziyara kuma bamuje ba" Anty Amnah tace "yakamata kam, yana qoqari akanku, kuje ku gaishesa na musamman" Nafisa tace "in Sha Allah" ganin haka yasa Na'iman cewa "toh" itama.. A motan anty Amnah suka tafi, Na'ima na bin green forest din da kallo ganin ashe haka unguwarsa ke da nisa kuma yake zuwa gurinsu akai akai, Nafisa tace "Bobo baki fa fadamin meya hadaku ba daf da zeyi tafiyan nan" Na'ima ta juyo tana kallonta tace "bamuyi fada ba sis, me kika gani" Nafisa tace "shikenan, I thought wani abu ya faru ne a lokacin, sai kuma naji baki min maganan ba" Na'ima tayi shiru kaman bazatace komai ba, sai kuma can tace "Nafisa i think i should tell...." bata qarasa maganan ba kira ya shigo wayanta, ta dago wayan tana kallon sunan faruk dake kiran, dagawa tayi suka gaisa daga can bangaren faruk yace "Habibtin Mami kin manta da yayanki ko" tayi dariya tace "A'a yaya, kayi hakuri school work ne ya riqemu" Yace "shine babu kira Na'ima" tace "kayi hakuri" shiru yayi baice komai ba at first, sai kuma ya sauqe numfashi yace "it's Okay dear, Ina nafisa?" miqawa nafisa wayan tayi itama suka gaisa sannan tace "ka ganmu nan a hanyar zuwa gidan yaya Ahmad" faruk yace "wai har yanzu yana England daman?" Nafisa tayi dariya tace "kaima kayi mamaki ko yaya" sai ta juya ta kalli Na'ima da hankalinta nakan titi... Wani unguwa sukaje me shiru bakajin qaran komai sai kukan tsuntsaye dan tsakanin gida da gida ma wani forest ne, Nafisa ta faka a daidai mashigar wani baqin gate me raga raga kana iya hango farin babban ginin dake cikin compound din, dan miqo hannu nafisa tayi ta danna wani madanni dake jikin gini a gefen gate din, ba'a dauki lokaci ba gate din ya budu suka shiga, nan compound din tayi parking suka fito Na'ima na bin flower garden din gurin da kallo, ta gefe kuma motocinsa ne a jere kusan guda hudu, nafisa ta zagayo gefenta tana kallon motocin tace "yau sai na dauki makullin dayar can" ta qarasa tana nuna baqar Wrangler jeep din da yazo daukansu da ita rannan, murmushi Na'ima tayi dan ita hankalinta yafi kaiwa kan flowers dinda tagani..gaba Nafisa tayi Na'ima na biye da ita suka qarasa main entrance din gidan, basu kai ga tura grand door din ba suka ga ta budu da kanta, idonsu ne yafada cikin na Ahmad dake kallonsu with suprise, sanye yake cikin baqaqen kaya na 3quater da T-shirt, sai Na'ima taga farin fatarsa ya sake fitowa sosai...Dan yin baya yayi sannan yafara musu iso fuskansa da dan murmushi sai suka bishi cikin babban falon da komai na cikinsa ya zamo fari da baqi, idon Na'ima na duqe suka zauna kan kujeru, Ahmad dake kallonta shima ya zauna a kujeran da ke facing sannan ya kalli Nafisa yace "i thought bazaki gane gurin ba ai" Nafisa tayi murmushi tace "Haba dai yaya",gaisheshi Nafisa tayi ya amsa sai a sannan itama Na'ima ta kallesa tace "Ina kwana" kallonta ya dinga yi not minding Nafisa dake gurin, Sai kuma ya miqe ya tafi wani corridor dake nan downstairs din, Nafisa tace "Ehem Ehem" dan juyowa Na'ima tayi tana kallonta, ganin irin kallon da Nafisan ke mata yasa ta dauke kai tana murmushi Bai dade ba ya dawo hannunsa riqe da refreshment ya ajiye nan kan table sannan ya zauna, Nafisa tace "yaya amma ka chanja interior na gidan?" ya dan bi falon da kallo yace "Eh Nafisa" tace "yayi kyau sosai, can i take a tour?" Ya gyada kai tareda cewa "sure, go ahead" Nafisa ta miqe ta nufi stairs tafara hawa sai kuma ta juyo fuskanta da fara'a tace "yaya yau inason mutafi da jeep dinnan please" ya sake cewa "badamuwa, key din yana bedside drawer na" ta gyada kai sannan ta wuce sama, Juyowa yayi ya kalli Na'ima dake zaune har sannan batace komai ba, ya miqe yadawo nan gefenta a hankali yace "yau ma bazaki kulani ba" itama cikin sanyin murya tace "mun gaisa fa" ya rinqa kallon ta fuskansa da murmushi baice komai, tafara wasa da bakin gyalenta, jin beyi magana ba tace "me kakason ince to?" yace "tell me how you missed me Na'eemah" dago kai tayi tana kallonsa shima haka sai taji idanunsa sun mata nauyi nan da nan ta kauda kai tana dan gyaran murya tace "kadaina kallona irin haka" sai yayi dan dariya yace "fadamin ya nake kallon naki?" batace komai ba sunanan zaune Nafisa tadawo falon hannunta riqe da key tace "yaya wannan ne ba" ya daga kai yana kallon key din yace "Eh shine" zama tayi ta zuba musu juice din da yakawo musu dazun ta miqawa Na'ima sannan suka fara hira itada Ahmad din jefi jefi, kiransa akayi a waya ya miqe yana cewa "sorry i have to take this" sannan yayi hanyar fita waje, Cewa Na'ima tayi "Bobo muje sama in nuna miki wani abu" Na'ima ta girgiza kai tace "A'a nafee" Nafisa ta taso tafara Jan hannunta tace "Dan Allah kizo muje, kawai wani abu zaki gani sai mu dawo" haka taja Nafisa ta jata suka je side dinsa da nan saman, sai taga sun wuce falo da study room Nafisan zata jata wani daki, cewa tayi "Nafisa is not proper in shiga masa daki dai" Nafisa tace "meye wani proper, da'alla kizo mu shiga" shigansu dakin nafisa tajata gurin master bed, Na'ima na bin gadon da kallo ganin girmanshi, sai da suka tsaya daidai setin gadon nafisa ta kamo kafadunta ta juyar da ita suka kalli ginin dake facing gadon Hannu Na'ima takai bakinta tsabar mamaki tana kallon katon hoton ta da akayi framing anan jikin ginin, hoton ya kusa cinye gurin dan girma, dariya takeyi acikin hoton bazata manta ba ranar da sukaje gurin sport dinnan ne domin kayan ne ajikinta cikin hoton..sunanan tsaye Nafisa bakinta kamar ze yanke dan murmushi tace "Yaya Ahmad is Finished" sai kuma tayi dariya tace "Na'ima..I'm truly happy for, for all of you..this is clean" itadai Na'ima takasa cewa komai sai hawayen da ya kawo idonta tunani iri iri a ranta, janta nafisa ta sakeyi suka koma falon qasa nan suka samu Ahmad kishingide a sofa yana danna wayarsa, dagowa yayi yana kallonsu Nafisa tace "yaya zamu tafi" yace "so soon?" Na'ima sai kallonsa take tanajin zuciyarta wani iri, Nafisa ta sake cewa "Eh yaya, yauwa yanzu ya zamuyi da motan Anty Amnah, inason mu koma acikin taka" ya danyi murmushi yace "badamuwa nafisa, zan aika mata anjima" sai ya sake cewa "I've ordered food, ku tsaya akawo tukunna" Nafisa tace "A'a yaya a qoshe muke mukam" jakansu dake nan kan kujera nafisa ta dauka suka fara nufan hanyan fita, shima miqewa yayi yabi bayansu har nan parking space, bakin nafisa yaqi rufuwa dan itadai Allah yasa mata son motan, duk yanda yaso Na'ima ta kallesa taqi gashi kuma taqiyin magana, shigewa tayi motan nafisa ta tada suka fice yananan tsaye....Ranan da dare da ya kirata ma baigane kanta ba duk tayi wani irin sanyi, haka dai yayi ta magana tana amsawa sama sama, ita jin ranta takeyi duk a hargitse ma tarasa me zata fara tunani guda daya, what if yazo ya san ta taba aure , what if yasan tushenta, what if yasan su waye mutanen da ta rayu cikinsu.. dakyar bacci ya kwasheta daren ranan tsabar tunani.. Ranan wata laraba sun wayi gari da shirin

Chapter 10 of 19