Na'ima" da sauri Abu ya fito daga gaban motan yana murmushi yace "itace Anty Na'iman dama, ina wuni" murmushi Na'ima tayi ta amsa sannan ta kalli faruk tareda gaishesa, ya amsa bai bar kallonta ba, Abu na murmushi ya danyi qasa da murya yace da Nafisa "she's beautiful" a bayyane Nafisa tace "kai dalla tanada Aure" sai sannan faruk yayi saurin kauda idonsa yace dasu "ku shiga muje mana"... Har gida suka kai Na'ima dazata fita tayi musu godiya Abu yace "yaushe zakizo gidanmu anty?" tana murmushi tace "zanzo wani sati in sha Allah" da haka sukayi sallama nafisa tace "I'll call you" shidai faruk bai sake cewa komai ba idonsa na kan wayarsa yana pressing...
Karfe dayan dare na ranan tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah taji shiru har Lokacin Bilal basu dawo ba gashi ta bar qofan falon nasu a bude, tsoro ne taji ya dan fara shiganta sai ta miqe ta fice daga dakin taje ta kulle kofan sannan ta koma daki, bata fi 30 minutes da fara bacci ba taji an fara buga kofan falon da qarfin bala'i, ta miqe da sauri har jikinta na rawa ta isa falon ta tsaya, kasa budewa tayi dan bugun ya mata karfi sosai, Jin muryan Bilal tayi da qarfi yace "Open this damn door Na'ima" sai tayi saurin qarasawa jikin kofan, bata qarasa bude kofan ba ya banko ta tareda hankata tayi baya ta fadi da karfi, fuskan nan tasa tayi jajir sai warin taba da alcohol yake, miqewa Na'ima ta farayi ganin yanayinsa aikuwa beyi wata wata ba ya qaraso ya kwasheta da kafa, tiim ta fadi qasa tareda yin qara, yana huci yace "ko a gidan ubana da kika zauna kin taba ganin sun kullemin kofa?" Ta girgiza kai tana kuka dakyar kafin ta sake wani magana ya sake kai mata wani harin da qafa, dukanta ya hau yi iya kafinsa yana cewa "who are you, da zaki kullemin kofa" tana kuka ta cigaba da jijjaga kanta, sai da ya gaji dan kansa sannan ya sake mata wani tsawan "answer me" tana daga kwancen kan tiles tana kuka tace "kayi hakuri" ya buga tsuka me karfi ya tsallaketa ya wuce sama, kifa fuskanta tayi kan tiles din tana kuka mara sauti tareda dafa cikinta, saida takai almost 1 hour a wajen sannan ta miqe dakyar ta gyara gashinta daya sauko fuskanta, dafe da cikinta ta nufi saman zuwa dakin ta tana hawaye, baccin da batayi ba kenan har asuba idonta biyu, data hada breakfast ma shi kadai ta samu zaune kan dining chair din, tayi serving dinsa hannunta nadan rawa shikuwa gogan idonsa na kan wayarsa, tsuka ya buga me karfi tareda Kai hannu ya tunkude plates din suka kife nan qasa, da sauri Na'ima ta masa gefe tana damqe idanunta dan ta dauka duka ze kai mata ma sai taga ya nufi sama da sauri ransa a bace, tsugunnawa tayi ta fara kwashe kayan idonta na cikowa da hawaye, saida ta gyara gurin sannan tafi dakinta, tana tsaye gaban mirror tana shafa rob a ciwon dake gefen idonta tajiyo fitar motansa, da sauri da shirya itama amma madadin ta tafi makaranta sai ta wuce gidansu aranta tana addu'an samun Alhaji....
Dont forget, your reaction gives me courage to do more❤️
Bintu Musa ce ✍️📚
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
Chapter 31
Isarta gidan nasu bayan ta sallami mai mashin suka gaisa da megadi sannan ta shiga cikin gidan tana gyara face mask din fuskanta, shiganta falon yayi daidai da fitowan Hajiya daga corridor'n kitchen hannunta riqe da tray alamun zata kai breakfast din Alhaji, tsugunnawa Na'ima tayi har qasa ta gaishe da hajiyan ta amsa tana mata wani kallo sai tace "zauna anan bari inzo" gyada kai Na'ima tayi tareda amsawa da toh sannan ta zauna anan main falon Hajiya ta wuce sama, bata wani dade ba ta dawo, nan falon ta zauna tana kallon Na'iman tace "ya da sassafe haka?" Na'ima ta danyi jim batace komai ba kanta a qasa sai Hajiyan tace "zama zamuyi tayi cikin shiru kenan" ta girgiza kai idonta na kawowan hawaye ta sauqe face mask din, kallonta Hajiya ta tsaya fuskan ta babu alamun wani emotion guda daya, cikin rawan murya Na'ima tace "dukana yayi jiya Hajiya" kadan ya rage Hajiya batayi tsaki ba ta danne zuciyarta tace "shine dan Miji ya dake ki sai ki taho gida da sassafen Allah ke mai iyaye kenan, kin fa san waye Bilal kuma kinsan muma a sannu muke bi dashi a gidan nan, in kikace bazaki saka hakuri cikin lamuranki ba to bazaki taba ganin daidai ba Na'ima, kowa da kika gani hakuri yake a gidan mijin nan, asannu ake bin miji sai kiga komai yawuce kamar ba ayi ba" Hawaye Na'ima ta rinqa yi tanajin zuciyarta na mata zafi, a hankali ta amsa da "toh Hajiya" miqewa Hajiyan tayi tace "Alhajin na bacci yanzu kije tukunna, dududu ma auren naku wata nawa ne ma har kin fara kawo qara Na'ima, hakane hakurin naki da muka sanki dashi kenan?" Na'ima ta girgiza kai bata daina hawaye ba, sai Hajiyan ta sake cewa "ki koma gida yanzu, in ya tashi zan san yanda zan masa maganan, kuma shima Bilal din zan ja kunnenshi" Na'ima ta gyada kai tareda miqewa itama tace "zanje daukan kayana a daki" sai Hajiyan ta gyada kai tareda cewa "toh, ki gaida gida, arinqa hakuri shine ribar zaman duniyan gaba daya" nan kuma Na'ima batace komai ba ta nufi dakinta da take zama a gidan a da hajiyan na bin bayanta da wani kallo har sannan bata dai yi tsukan ba amma ita kwata kwata ma ji take ta tsani Na'iman, saboda ada tayi zaton auren zai zaunar da dan nata a garin sai kuma taga ba haka ba shikenan ta fara shiga dana sanin auren wanda har hakan kusan saka sabani yayi tsakaninta da Larai, ga abunda ta gano kwanaki a dakin Alhaji cikin takardun dukiyarsa...
Na'ima na shiga dakin ta fara kuka mara sauti ta zauna kan gado, tasani Alhajin na nan bai fita ba kuma taci alwashin sai ta hadu dashi yau dan babu wani abu da zata dauka a dakin kawai zaman jiran fitowan Alhajin zatayi, aikuwa bata wani dade ba taji alamun sauqowarsa yana waya ya fita daga falon, cikin sauri ta fito daga dakin ta bishi, iddashi tayi a parking space yana waya har sannan bai gama ba sai ta tsaya tana jiran ya gama, bai dauki mintuna ba ya gama ya juyo yace "Ahh Na'ima yanzu kikazo ne, ya gidan naki" gaishesa tayi ya amsa sannan ta ja face mask din fuskanta ciwukan fuskanta duk suka bayyana, kafin yayi magana sai ga Hajiya ta fito, juyawa Na'ima tayi ta kalleta sai da zuciyarta ya tsaya na wasu daqiqu ganin Bilal abayanta shima yana tahowa, hankali adan tashe Alhaji yace "meya samu fuskarki haka Na'ima?" kasa magana tayi sai Hajiya tayi saurin cewa "wai faduwa fa tayi a bandaki jiya shine tazo ta nuna mana" Alhaji ya sake kallon Na'ima yace "subahanallah garin yaya haka ta faru" sai Na'ima tayi qasa da kanta wasu hawayen na cikowa a idanunta, Alhaji ya juya ya kalli Bilal yace "kana kula sosai Dan Allah son" sai ya sake kallon Na'iman yace "sannu Na'ima Allah ya kare na gaba" Hajiya tace "ita ce ai yakamata tana kulan, banda rashin nutsuwa kawai sai ki fadi a bandaki da girmanki" shidai Bilal sai kallon Na'ima yake yanajin ranshi na qunaa, Alhaji yace "duk ba wannan ba yanzu dai son ka wuce da ita asibiti a wanke ciwon nan babu dadin gani" ciki ciki Bilal ya amsa da "toh" sai ya kalli Na'ima yace "ki samoni a mota" ya qarasa magana tareda sallama a iyayen nasa, cikin tararradin Na'ima ta musu sallama Alhaji na sake mata sannu har da Hajiyan ma dan ganin idon Alhajin, sannan ta bi bayan Bilal din zuciyarta na bugawa, saida ta shiga motan ya tada suka fice daga gidan Alhaji ya kalli Hajiya yace "sai naga kamar batada lafiya ma, ko an samu qaruwa ne?" da sauri Hajiya ta kallesa sai tayi masking fuskan nata da murmushi tace "ze yiwu, ai kasan yanzu wata kunya ta qaro, nikuma na fada mata ba sirikarta bace ni" Alhaji na murmushi yace "Allah yasa muji alheri" azuciyarta tace "ba Amin ba" a bayyane tace "Amin" tana murmushi.....
A hanyarsu ta komawa Bilal baice da Na'iman qala ba Kuma har sannan ji yake kamar ya shaqeta ko zai huta ma shikam, kiran wayansa akayi ya dauka tareda sakawa a handsfree, Stella dake dayan bangaren tace "Baby har zanyi fushi bazaka kulani ba" yace "in kina biye Nasir zamu samu matsala sosai kinsani" cikin shagwaba tace "dagaske ne ya ganka da macen a club din fa, raina ne ya baci na koma lagos" ya dan gyada kafada yace "I'm not in the mood right now, I'll talk to you later" da haka ya kashe wayan be jira cewarta ba ya juya ya kalli Na'ima dake kallon window still be ce komai ba, gidan nasu ya nufa kamar yanda Na'iman tayi predicting, bayan yayi parking suka fito sai taji kamar ta ruga da gudu ta fita daga gidan, bece komai ba ya nufi entrance din gidan ta bishi a baya cikin sanyin jiki, bayan sun shiga har ya fara takawa stairs sai ya juyo ya fara takowa gareta, da sauri ta juya zata gudu waje ya funcikota ya hada kanta da hannun kujera, ihu tayi yana kallonta cikin bacin rai yace "Na'ima har kinyi gut din da zaki kai qarana gurin iyayena" tayi saurin girgiza kai hawaye na fitowa a idonta, ya sake cewa "do you think ko matan duniyar nan zasu qare I'll give a f*ck about you?" Nan ma ta girgiza kai bata bar hawayen ba, ganin kallon da yake mata yasa ta bude baki zata bashi hakuri ya dauketa da mari...ranan jikin Na'ima ya fada mata a hannun Bilal saboda duka ya mata sosai har se da ya gaji dan kansa ya barta nan kwance gefen dining table jikinta babu qarfi, wucewa sama yayi yana cewa "it's you or me in this house Na'ima, get that in your dumb skull" sai sannan ta bude bakinta tafara kukan cikin sauti tanajin ta tsani komai a duniyar, a wannan lokacin ji tayi tanason mutuwa dan ta huta da komai ma, tananan zaune ya fito ya sake wuceta ya fice daga gidan gaba daya, sai da taji kiran salla ta tashi tana jan jikinta ta wuce dakinta bata daina kukan ba wanda a sannan sautinsa baya fita ma... Dakyar ta wayi gari washegarin ranar saboda komai nata jinsa take ba daidai ba, a hakan ta hada masa breakfast, data kawo masa nan inda yake zaune a falon yace "fitan da kikeda freedom din yi ne yasa har kikeda tsaurin idon kai qarata gurin iyaye na, zanyi maganinki" batace komai tacigaba da zuba masa tea din tayi serving dinsa sannan ta miqe ta wuce sama cikin sanyin jiki yana kallonta, bata tashi yarda da maganansa ba sai da tazo fita zataje makaranta taga ya kulleta ta waje, dawowa tayi bakin window nan ma bataga alamun megadi ba, sai ta sulale nan gurin tafara wani kukan..
Fitan Bilal daga gidan ashe bayan ya kulleta sai ya sallami megadin yace zasuyi tafiya, daganan waya yayi da iyayen nasa akan maganar tafiyarsa da zeyi na company dinsu zuwa qasar china, har Alhaji yace ya tafi da Na'ima amma tuna tana makaranta sai bai ja da maganar Bilal din da yace ai yayi magana da Na'iman akan zata rinqa binsa can lokaci zuwa lokaci ba, Hajiya dai daman tun dawowan Bilal din da ya fada musu batun tafiyan bata nuna tana so ba har sannan, amma haka ta hakura sukayi sallama sanin dolenta zataje ganinsa bada jimawa ba..A ranan yayi sallama da iyayensa ya wuce Lagos da nufin ya dauki Stella su wuce china'n...
Wuni biyu Na'ima tayi cikin gidan tana jiran dawowarsa gashi maigadi daya tashi tafiya se ya kashe wutan gidan ta waje babu halin ta fita ta kunna, a rana ta ukune wayanta daya kusa mutuwa kiran nafisa ya shigo wayanta ta dauka da sauri idon ta na kawo hawaye, Nafisa dake dayan bangaren tace "Na'ima shiru kwana biyu ko a school ban ganki ba, gani kofar gidanki kuma gate din a kulle" Na'ima batakai da magana ba wayan ya mutu ta nufi window da sauri, daga nan tsaye ta hango motan nafisan sai ta juya cikin gudu ta sauka qasa ta dauko kwanon silver tadawo nan bakin windon tana bugawa da aqarfi ko nafisan zata Jiyo ta, bugawa take tana kiran sunan nafisa sai gani tayi motan ya fara tafiya ze bar layin ta fashe da kuka me qarfi kanta na jikin windon...sai da Na'ima tayi sati cikin gidan bataga hanyar da zata fita ba, babu ranar da bata kuka da roqon Allah ya kawo mata dauki, a rana na takwas ne tana kwance nan falon tajiyo kamar qarar gate an bude, da sauri da nufi window sai ta ga megadin ne ya shigo, same abunda tayi na ranar da nafisa tazo shi tayi yau ma, megadin ya taho building din da saurinsa tace "ka budeni Dan Allah" nan ya ciro key ya bude ta tareda cewa "hasbunallah Hajiya kayi hakuri wallahi bansan kana nan ba, megida cemin yayi kunyi tafiya inje gida, kaga dawowar nan danayi ma rashin abunda zanyi ne acan garin yasani na dawo" Na'ima ta gyada kai tareda wucesa ta fita compound din ta tsaya dan gidan ma wani iri takejinsa, hakuri ya dinga bata har saida tace babu komai yaje abunsa sannan ya hakura, sai dare ta koma cikin gidan bayan ya kunna mata wutan gidan, da ta bude wayanta message har kusan guda sha biyar daga nafisa, nan take ta kirata, tana dauka ta fara tambayan meya faru, sai Na'ima tasamu kanta da cewa tayi tafiya qauye ne, nafisa tace "tafiya kuma babu sallama, naje can gidan ku ranan basanan suma" Na'ima tace "kiyi hakuri dan Allah gobe zan shigo school muyi revision" da haka sukayi sallama..
washegari da safe kuwa ta shirya ta tafi makaranta duk da batada abunda zatayi sai karatun saboda anyi placing time table dinsu, saida Sufi ya kirata dan sanar da ita ya tura mata kudin watan da ake bata sannan taji labarin tafiyan Bilal, shima a dalilin gaisheda Bilal din dayace tayi in sunyi waya, a wannan lokacin Na'ima ji tayi kamar an yaye mata damuwanta, babu abunda take fata irin yayi dogon zama acan kar ya dawo...
Haka Na'ima ta sake runguman rayuwa da karatun ta sosai, tun tana tararradin dawowan Bilal har ta sake ranta jin shiru bai dawo din ba, lokacin da suka fara exams da tayi waya da iyayen nata sai Alhaji yace ko zata koma can gida, ganin tana ta kame kame sai yace to tayi zamanta nan gidan mijin nata amma ta kula sosai..Sunyi exams dinsu sun gama lafiya a wannan hutun ne ta fara zuwa gidansu Nafisa, ranar da taje tun shiganta falon gidan tagane mutanen nan sun mata sani sosai a gurin Nafisa, Mami na falon Abba lokacin sai su Al'ameen tasamu a babban falon gidan suna PS, da gudu nafisa ta sauko daga stairs ta rungumeta su Al'ameen na dariya wai finally aminiya tazo, Jan hannun Na'iman tayi ta kaita har falon Abba su gaisa, Na'ima na ganin Mami ta fara murmushi zata zauna nan qasa sai gani tayi Mami ta miqe ta rungumota tace "lale lale Na'ima munata jiran zuwanki shiru" Abba dake zaune yace "yau zamu huta gurin Nafisa tunda Na'ima tazo" duk sai suka kama dariya harda su Al'ameen da Abu dasuka shigo suma, cikin jin kunya Na'ima ta gaishesu suka amsa cikin fara'a, nan falon suka zauna tun Na'ima najin nauyi har ta fara sakewa dan hira taga iyayen nayi da 'ya'yan nasu gashi an cika mata gabanta da kayan marmari, tashi Nafisa tayi ta riqo hannun Na'iman tace da iyayen nata "Mami zamuje dakina" suka amsa da "toh" Abu harda cewa zai bisu Nafisa ta hararesa while Na'ima na murmushi..wuni tayi a gidansu nafisa cikin walwala ranan suna hira, da ta tashi tafiya ma nafisan ce ta maidata gida tare da rakiyar Abu, sai da suka tsaya wani mall suka sayi kayan ciye ciye sannan suka kaita har gidanta ta musu sallama tanajin wani iri aranta...daga wannan ranar wani zumunci ya sake dorewa tsakaninta da Nafisa da kuma 'yan'uwan ta...
Three years Later..
Na'ima tayi salloli tayi addu'o'i kuma Allah ya karbi addu'an ta ya zaunar da Bilal a qasar da yaje, while Hajiya tayi addu'o'i tayi kuka akan Bilal yadawo amma abun yaci tura, Alhaji yayi fadan, yayi fushin amma Bilal bai waiwayo gida ba, a wannan shekarun abubuwa dayawa sun faru, Na'ima taje Adamawa har sau uku kuma ko wanne da kayan tsarabarta lodi guda take zuwa amma ko "ya hanya" babu wanda yake kira daga cikinsu yaji daga gareta inta dawo Kano, zuwanta da tayi na farko tasha kuka Jin labarin mutuwar goggo, su Ayuba sunanan a yanda Allah ya yisu, still those selfish and ingrates people da Na'ima ta sansu dai sudunne har wannan lokacin dan afili suke nuna son abun hannunta, a lokacin da taje din duk wani kudin cefane na gidan a gurin Na'ima ake karbansa, sai da ta koma ciyar da gidan na wannan satin har kudin motan dawowa yaso gagararta..
Zuwa wannan lokacin abunda ke cin Hajiya akan Na'ima har ya fara bayyana, dan Na'ima tararradin zuwa gidan take saboda maganganun da Hajiya ke jefo mata na auren ta da Bilal ne silan qin dawowarsa qasar ma, dan da babu auren at least ze waiwayo gida, da akwai ranar da Hajiyan tace "in dan Bilal ya dakeki ne kika kadamin shi toh gwara tun wuri kisan yanda zakiyi ki dawomin da dana, dan na lura ke ba damuwarki bane zama qaramar bazawara" wannan magana ta tsayawa Na'ima a rai sosai...
Zuwa wannan lokacin har dan qiba Na'ima tayi na kwanciyar hankalin da tasamu a gidanta, batada damuwa sai na makaranta, dan ko da wasa bata taba jin babu dadi na rashin dawowan Bilal ba, har mantawa take da auren ma wani lokaci, bata waya da Alhajin akai akai saboda shi nauyinta yakoma ji akan rashin dawowan Bilal din, zuwa sannan wani license me qarfi Na'ima ta samu na zuwa gidansu Nafisa freely abunta, ko Nafisan bata nan tana iya zuwa su taba hira da Mami da sauran mutanen gidan amma bata samun faruk saboda zaman Abuja yake yi, mostly sai weekend na biyu zuwa uku yake dawowa nan kano...makarantansu suke yi itada Nafisa hankali kwance inda a yanzu suna final dinsu ta fannin computer science dasuke karanta, duk wanda yasan Na'ima shekaru uku zuwa hudu da suka wuce ya sake kallonta yanzu sai ya ga chanji sosai, da karfi da yaji Nafisa ta rabata da saka hijaban nan zula zula, sai dai bata cikason saka gyale ba sai ta dauko saka abaya sosai, kala kala Nafisa ke tusata su je siyowa, wannan yanayin na Na'iman ba qaramin baqin ciki yake sakawa Hajiya ba ganin hankalinta kwance bayan danta yanacan wata qasa dawowa ta gagara..
Ina Labarin Bilal?....wata sabuwar rayuwa ya bude a Shanghai dake cikin qasar China, gida company din nasu suka bashi acan duk a tunaninsu Stella iyalinsa ce, dan rayuwansa yake da Stella tamkar matarsa, saida Hajiya ta kusayin dambe da Stella a wani zuwa da tayi ganinsa, da kuka tabar gidansa tana fadin "yaje ta yafesa a Stella" wannan maganar ba qaramin tsayawa Bilal arai tayi ba, tun daganan hankalinsa ya fara karkata kan komawa gida kuma, ta fannin aurensa da Na'ima kuma bawai mantawa yayi ba, asali ma rashin nemansa da tayi tsaya masa a zuciya hakan yayi dan yana yawan tunawa da ita, amma taurin kai irin nashi ya hanashi daga waya ya kirata, har zuwa sannan bazaice ga abunda yakeji akanta ba, iya saninshi Na'ima batakai matsayin aurensa ba, bata daga cikin kalan matan da yakeso, yana riqe da aurenta a wuyansa ne saboda bin umarnin iyayen sa..A lokacin da ya tashi komawa gida sunyi rikici sosai da Stella har hakan yasa shi tafiya ba tareda yabi ta kanta ba, inda hankalin Stella ya tashi matuqa acewarta Bilal yafara juya mata baya, ba shiri itama ta koma Lagos....
A ranar da Bilal ya isa Kano gidansu ya fara zuwa, ga mamakinsa sai iyayen nasa suka karbe shi da hannu bibbiyu, rungumesa Hajiya tayi tana kuka tana fadin bazai koma China ba, saida ya zo kwanciya da dare Alhaji yace ya tafi gidansa gurin matarsa, qememe Hajiya tace sai danta ya kwana gurinta tukunna, haka Alhajin ya hakura dan shima har ransa yayi missing dan gudaliyan nasu.....
Wayewar washegari Na'ima nada wani test me zafi a school, cikin saurinta ta gama kintsa gidan sannan ta shirya cikin wani maroon abayanta ta tafi makaranta, waya tayi da Nafisan ta biyo nan bakin hanya ta dauke ta suka wuce tare, basu fito ba sai karfe goma, shima suna fitowa Na'ima tace da Nafisan zataje gida ta yi bacci kanta na ciwo na karatun da tayi jiyan, tare suka sake barin makarantan Nafisa takaita har qofar gida sukayi sallama ta ja motanta ta bar layin, sai lokacin Na'ima ta samu nutsuwan gaisawa da megadin ta shige ciki, baquwar motan data gani a parking space sai da yasa zuciyarta harbawa tuna Bilal, dan stuff tayi a tsaye nan compound din bata shiga gidan ba tana kallon motan, can ta ja kafafunta cikin sanyi ta nufi entrance din gidan, a hankali ta tura kofan falon dake bude ta shiga, qarasawarta cikin falon yayi daidai da fitowan sa daga kitchen hannunsa riqe da cup yana sipping tea, tsayawa kallon kallo sukayi jikin Na'ima na dan rawa, it's been three years.... Amma Na'ima bata daina jin tsoron wannan bawan Allah'n ba, bata daina kyarma aduk sanda ta gansa ba..
Muryanta na dan rawa tace "sannu da dawowa" yana kallonta shima cikin nutsuwa yace "Yauwa, ina kika ajiye sugar, i've been looking for it since" Mamaki ne ya lullube Na'ima najin yana mata magana cikin nutsuwa yau din, sai tayi saurin nufan kitchen din zata dauko masa kanta a qasa tana gyara zaman gyalen abayan jikinta, bin ta da kallo Bilal yayi har ta shige......
Bintu Musa ce ✍️📚
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
Chapter 32
Bayan Na'ima ta shiga kitchen din sai da tadan tsaya ta sauke numfashi sannan ta nufi cupboard dinda take ajiye sugar'n, daukowa tayi sai ta fara tunanin yanda zata qara komawa wajen Bilal dake tsaye can falon, cikin sanyin jiki ta bar kitchen din ta nufeshi yananan har sannan a tsaye yana kallonta, kanta a qasa ta miqa masa, karba yayi ahankali yace "thanks" sai ta nufi stairs da dan saurinta ya bi bayanta da kallo..... bata sake fitowa daga dakin ba har sai bayan azahar taji ya kwala mata kira a falo, cikin sauri ta yafa gyale ta fita, samunsa tayi nan bakin stairs yana tsaye ranshi a dan bace yace "Aren't you making me lunch?" Na'ima tayi saurin girgiza kai tace "kayi hakuri yanzu zanyi", sauqa tayi ta wuceshi tana dan saurin nufan kitchen din, cikin sauri take aikin tana duban bakin kitchen din aikuwa sai gashi ya shigo ya tsaya nan bakin kofan kitchen din hannuwansa harde a qirjinsa yace "daga ina kike dazu" tsayar da aikin tayi cikin sanyin murya tace "makaranta naje" sai lokacin Bilal ya tuna da tana makaranta ashe, sai ya juya zai bar kitchen din ya sake cewa "in kin gama ki kaimin can dakina" ta amsa da "toh" sannan ta cigaba da aikin..a tray ta hada abincin ta nufi dakinsa tanajin zuciyarta na dan bugawa, shiganta ta gansa nan tsaye bakin wardrobe sanye da only boxer, cikin sauri ta juya kanta da kadan abincin ya zube saboda yanda zuciyarta ta buga ganinshi hakan, Bilal dake duban kayansa ko a jikinsa ya nuna mata bedside drawer yace "ajiye acan" cikin sauri ta kai ta ajiye kanta a qasa ta nufi fita daga dakin yana kallonta, bata sake jin motsinsa ba sai bayan magrib taji fitan motanshi wanda bai dawo gidan ba sai tsakiyar dare
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 19