Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
maqale da waya a kunne yana dago musu hannu, ware idanu tayi ta rufe bakinta da hannu saboda mamaki, buga kafa nafisa tafara yi tana ihun murna batareda damuwan mutane na dago kai suna kallonsu ba, Yana dariya ya matsar da wayan daga kunnenshi Jin tana ihu, da gudu nafisan ta koma falo tayi hanyan fita kayan bacci neh jikinta me dogon hannu da dogon wando ta fice da sauri. Na'ima ta dawo falon ta tsaya tana murmushi don har ga Allah itama tayi murnan zuwansa don yah faruk mutuminsu ne kuma yayansu....An investment banker sannan first born a gidansu nafisa,shine wanda nafisa take bi, daga ita sai Al'ameen da yake makaranta a Toronto Canada sannan last born dinsu Abubakar. 'ya'ya hudu yan gata wajen Mami da Abba sai Na'ima da suka hada ta zama cikon ta biyar acikinsu. Tananan tsaye a falon taji beep din password suna kokarin shigowa, da sauri ta juya ta koma daki don dauko hijab itama kayan baccin ne jikinta dan tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci nan falon, tashinsu ne bayan sunyi brush sunyi breakfast nafisa ta tsiro musu da saka face mask kafin suyi wanka Bayan ta sako hijab din tacire face mask din ta dawo falon, suna zaune nafisa sai zuba take kamar gyada, na'ima ta qaraso ta zauna kanta a qasa ta fara gaisheshi tana murmushi Amsawa yayi shima yana murmushin sai kallonta yake ganin duk ta chanja from the broken girl he once knew, cikin tsokana yace "Habibtin Mami" miqewa tayi tana sunne kai cikin kunya ta wuce kitchen don kawo masa abun sha Nafisa tace "ya faruk I thought direct flight to Abuja ko Lagos zaka bi daga can Paris din fah" ya juyo yana kallonta yace "what's that on your face?" Sai lokacin nafisa ta tuna da abunda ke fuskanta ta fara dariya tana cirewa. Na'ima tadawo falon riqe da plate with snacks,drinks and bottle water ta jawo tabe zuwa gabansa ta dora akai ta koma ta zauna suka qara gaisawa yana tambayansu karatunsu Hira sukasha sosai nan falon cikin raha, a dan zaman da tayi can gidansu nafisan ta fahimci yah faruk mutum ne mai kirki da son 'yanuwan sa, ga kyauta da fara'a, shekara shida ya basu itada nafisan ayanzu da suke cikin shekarunsu na ashirin da hudu Ganin hiran taqi qarewa especially yanda nafisa take ta zuba yace "toh yanzu dai ku shirya zan koma London tare daku, anty Amnah tace intaho mata daku" nafisa tace "dama fa gobe muke shirin zuwa" yace "Nah..ku shirya mutafi yanzu dan nima goben nakeson wucewa gida" nafisa ta turo baki "haba yaya, kabari sai Sunday mana" yace "a'a ai nazo naga lafiyarku" ya juya yana kallon Na'ima yace "ko habibtin Mami" tayi yar dariya tana kauda idonta tace "kayi kokari yaya mungode sosai" yace "yauwa...ku tashi ku shirya karku dau lokaci please" suka miqe kowacce tayi nata dakin suka barshi nan falon ya miqe yafara kashe kayan wuta na gidan. Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 04 Basu wani dau lokaci ba suka Isa London,suka dau hanyar gidan anty Amnah dake arean Kensington. Anty Amnah likitace kuma tana auren babban likita mazaunin London da yaransu twins maza kimanin shekaru bakwai. Sunyi murnan ganinsu sosai, twins sai tsallen murna suke. Bayan sun huta anty Amnah tayi serving dinsu abinci sunaci ana hira Daren ranan suna bisa gado cikin dakinsu wanda suke sauka idan sunzo gidan, Na'ima na zaune ta miqe kafanta hannunta riqe da ipad dinta twins suna kwance jikinta suna game tare, Kiran Abba ne yashigo wayan ta dauka da sallama tana gaisheshi, amsawa Abba yayi ta dayan bangaren tareda tambayanta ya karatu,tace  "Alhamdulillah Abba" yace "hope babu wani matsala" tace "Eh" yace "Ma Sha Allah, ku dage da karatu Na'ima,banason wasa" tace "in Sha Allah,nagode Abba" yace "Ina nafisan" ta amsa da "gatanan" tana miqawa nafisa wayan, bayan sun gama gaisawa da Abban taji nafisan na tambayan ina Mami,  Suna cikin maganan dinki da Mamin ta miqo mata wayan bayan ta saka a handsfree, bayan sun gaisa Mami tace "Na'ima ga kayanku nan ansiyo wanda zaku saka a bikin, inason aika muku wajen me dinkin nafisan bansan wani kalan dinki kike so ba kuma" cikin sanyin murya Na'ima tace "kowanne kalla yayi" Mami tace "A'a badai kowanne kowanne kala ba,saka wayan a handsfree" Nafisa dake gefe tace "a handsfree yake fa Mami" Mami tace "yauwa kinaji nafisa, ta fada miki kalan wanda takeso din sai ki turawa meerahn, nidai zan aika kayan gobe sai ku gama tsakaninku" Nafisa tace "toh Mami zanyi magana da ita a WhatsApp" da haka sukayi sallama nafisa tace "Meerah never disappoint, zansa ta turomin latest one's sai mu zaba" Na'ima bata amsa mata ba  ta karbi wayan nata ta miqawa jabeer dake kusa da ita ya cigaba da game dinda sukeyi. Suna nan zaune anty Amnah ta shigo dakin tace "sun hanaku bacci ko" na'ima tace "a'a game ai mukeyi" nafisa tace "anty ya faruk bai dawo ba?" tace "A'a" don tunda yakawo su nafisa aka taba hira dashi ya sake ficewa akan akwai gurin da zaije. Anty Amnah tace "Boys, it's time for bed" jabeer yafara kukan shagwaba akan shifa a wajensu na'ima sai kwana tace "my friend get down from that bed" Na'ima tace "anty kibarsu mu kwana anan din" anty Amnah tace "a'a zasu takuraku, oya muje" Haka ta tusa kansu suka bar dakin tana musu saida safe. Washegari suna breakfast gaba dayansu, nafisa ta saka faruk a gaba da roqon sai yayi rescheduling flight dinsa anty Amnah ma na tayata , mijinta da yake gurin yace "what if he has something to do back home" Anty Amnah tace " babu ma...beside, it's weekend. work can wait till Monday, right son?" faruk ya danyi dariya yace "zan duba available flight for Monday then" nafisa tace "zaka samu in Sha Allah" mijin anty dasuke kira uncle yasir yace yayi murmushi yace "su nafisa qorafi ya fara karbuwa" dariya tace tace "zai samu uncle" Itadai na'ima tayi shiru tanacin abincin dake gabanta sannan tana sauraronsu, faruk ya amsawa nafisa da "I'm not sure yet" ya dauki wayanshi dake kan table din zai duba Nafisa ta juya ta kalli Na'ima tareda kai mata qaramin bugu a kafada tace "kinaji inata faman roqo ko ki tayani" Na'ima tayi murmurshi batace komai ba tacigaba da shafawa jafar nutella a jikin bread, faruk ya dago kansa yace "habibtin Mami ko in tafi" dariya tayi kadan tace "a'a yah faruk" Anty Amnah tace "itama batason ka tafin ai, kawai nafisa tafita baki ne" Faruk ya gama rescheduling flight din ya ajiye wayan yace "there... it's done, saiku shirya anjima mu tafi park" nafisa ta ajiye tea din hannunta tayi masa thumb up tace "you're the best" twins ma sai sannan suka fara ihun murna jin ance park Haka suka tattara aka tafi park anty Amnah ta hada musu lunches dinsu suka saka a booth dan ita da Abban twins sunce baza suje ba zasu huta a gida. Wunin ranan a park sukayi, acan sukayi sallolinsu suka ci abinci, faruk yasasu sun hau different wheels yana musu video sannan sunyi games kala kala shima har nafisa taci kyautan teddies ma twins, sunci banza sunci wofi dai sannan suka koma gida da yamma duk a gajiye. Washegari wayewar sunday yakamata su na'ima su koma oxford don school, amma tunda suka tashi nafisa take mitan itafa ta gaji, bayan sun idar da sallah ta cigaba da mitan, na'ima najinta batace komai ba ta miqe tana linke sallaya. Ganin na'ima bata kulata ba tace "sis ko mubari sai gobe?" Na'ima tana murmushi tace "Allah ya kaimu toh" dan tasan qarshenta hakan ce zata faru daman, nafisa tace "Kinga dama bawani lectures muke ba dama, it's not a big deal"  na'ima ta koma kan gadon ta kwanta tace "hakane anty Nafisa" A gurin breakfast nafisa ta fadawa su anty Amnah bazasu koma school ba acewarta basuda wani active school activity ranan Monday din" faruk ya juya yana kallon Na'ima yace "dagasken take?" ta gyada kai tace "Eh" baice komai ba anty Amnah tasake tambayanta "na'ima are you sure" ta sake amsawa da "Eh dagaske ne anty"  nafisa tana murmushi tace "bafa karya mukeba" faruk yace "ai nasanki ne nafisa" anty Amnah tace "toh shikenan sai ku huta sosai, nima zanje hospital akwai patient dina dazan duba she's under my care" faruk yace "Ina uncle fa" tace "yana bacci tukunna, ya kwana a hospital jiya" Yammacin ranan sai ga faruk da ticket na football match da za'ayi da dare cikin Chelsea stadium, one of the most known stadiums in London, tsalle nafisa ta rinqa yi kamar ba ita tayita mitan gajiya ba, itadai na'ima nata fara'a batasan komai gameda ball ba amma tanason zuwa taron itama don she's curious to see the match in person. Dawuri faruk ya kaisu stadium din dan 8:00 pm za'a fara match din, bayan yayi parking a gurin da yayi booking suka fito zasu taka zuwa cikin stadium din babu anty amnah, tace batason shiga hayaniya kanta yana ciwo kuma ta gaji, shigansu cikin stadium din yayi gaba suna binsa a baya yana neman seat numbernsu. Nafisa ta juyo ta kalli Na'ima tace "Nice huh?"  Na'ima tana murmushi tace "it's beautiful..so beautiful" after sun samu gurin zamansu basu jima ba aka fara match din faruk ya miqe yace "I'm coming" yafara kutsawa cikin mutane zai fita daga stadium din, bai jimaba yadawo hannayensa riqe da popcorn da drinks ya rumgumosu a qirjinsa, zama yayi yana miqa musu yacewa nafisa "what did i missed?" ta amsa da "not much" At first na'ima bata gane yanda wasan yake tafiya ba sai nafisa ke kwatanta mata kasancewar ita ta taso cikin maza a gidansu suna yawan kallon football match. Cheering din mutane da ihun nafisa dake gefenta ne yafara sa mata interest sosai akan wasan, aqarshe dai da ita aka miqe ana ihu a stadium din. Ba qaramin nishadi match dinnan ya sanya na'ima ba, bakinta har kunne dan fara'a, faruk ya sunkuyo kusa da ita yana daga murya yace "do you like it?" Tana jijjaga kai cikin yar dariya tace "sosai" Ranan taga football celebrities dinda ko a mafarki bata taba tsammanin ganinsu face to face ba, it's one of the nights that na'ima bazata manta ba. Bayan an tashi daga match din suna komawa gida ta tambayi faruk "Kuma yanzu shikenan an kori dayan team din" yana dariya ya amsa da "Eh" ganin she's new to it, nafisa ta juyo daga front seat tace "BoBo zan siya mana tickets muje next match tunda kinaso" Na'ima tace "ai da dadi ne,bansan haka ball din yake da dadi ba"  nafisa ta juya tana kallon faruk sukayi dariya sannan ta juyo tace "welcome to the team girl" Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 05 Washegari da safe suka kai yayan nasu airport da motan anty amnah, hatta na'ima saida taji kaman tayi kuka balle nafisa datara fara hawaye Faruk yace "come on girls, nan da 3 weeks or so zaku dawo fa kuma" Nafisa ta qarasa kusadashi tariqo hannunsa tana hawaye, yana murmushi ya zare hannunsa,ya dagawa na'ima hannu alamun Bye itama ta daga nata hannun cikin sanyin jiki, ya juya na nufi cikin waiting lounge. Na'ima tadan daga murya tace "Allah ya kaiku lafiya yaya" haka suka koma gurin motan su cikin sanyin jiki suka bar airport din. Bayan sun koma gidan anty Amnah suka shirya kayansu tareda mata sallama suka tafi train station dan komawa oxford saboda motan da faruk din yaje daukansu na anty Amnah ne. After that memorable weekend in London, rayuwa ta cigaba yayinda suka maida hankali kan karatunsu wanda saura few months su gama. The weeks that follows sunyi qoqari wajen hada wasu daga cikin thesis dinsu before the spring break, don dama auren Salman yazo within their break, hakan yasa lokacinsu yazamo swamp with schoolwork, dukda basa zuwa school din akai akai don sun shigo phase na research a fagen karatun nasu, wani lokacin raba dare suke zaune nan falo kowacce tana nata aikin bisa laptop Duk da ayyukansu na makarantan da suka sako gabansu hakan bai hanasu zaman hira da cinye cinyen banza da hofi ba, Dan nafisa ta koyawa na'ima cinye cinyen itama basa zama shiru haka nan, aikace aikacen gidan nasu kuwa daman tun farko basu raba a junansu ba, duk wacce ta samu time yi take wanda dama na'ima ce rinjayen aikin da dafa musu abinci most at times, Kuma hakan bai taba damunta ba infact she love doing all the work tabar nafisan ta huta because she'll ba glad to do more than that to nafisa. Ance kaso mai sonka, to hakan take wajen Na'ima, tanason kyautatawa nafisan most at times takan shiga dakin nafisan ta gyara ko Ina ta wanke toilet sannan ta debo kayanta na wardrobe ta goge mata su tas ta jera. Wani irin bond ne mai tsafta a tsakaninsu wanda in ba wai sani kayi ba bazaka taba cewa qawance ne mafarin haduwarsu ba. Gashi dai ko daga yanayinsu mutum zaiga banbancin dabi'a sosai yayinda na'ima ta zamo mara hayaniya,don in kaga tana dogon surutu to da nafisa ne, ga hakuri da shanye komai a ciki while nafisa mutum ce mai surutu da rashin hakuri a wasu lokutan, But friendship blend them together and became sisters from different mothers. As lokacin tafiyansu gida yana kusantowa sai Na'ima ta zamo so uneasy ta zamo wata sanyi sanyi har nafisan tafara ganewa amma batayi mata magana ba saboda wasu dalilai Ana gobe zasu tafi, na'ima na dakinta tayi wanka tana zaune gaban mirror tana shafe shafen ta na al'ada, bayan ta gama tacire hulan wankanta tana kallon kitson da sukaje saloon aka mata ta dauko wani hair oil tafara shafawa acikin lines na kitson tana tunani, bayan ta gama ta maida hulanta tasaka kayan baccinta ta hau gadon,ji tayi ta kasa baccin, ta jawo laptop dinta dake bedside drawer shima zata dan duba ko zai dauke mata hankali, shima tana dannawa ne absent minded, daga karshe kawai ta miqe ta tafi kitchen bude cupboard tayi ta debo chocolates da cheese balls ta fito ta nufi dakin nafisa Samunta tayi ta dora box dinta akan gado tana gaban wardrobe tana zaben kayanda zata koma gida dasu, Na'ima ta shigo ta zauna kan gado tana cewa "wai dama baki gama hada kayan naki ba?" Nafisa na tsaye ta kama qugu tana nazarin kayan wardrobe din tace "sai na hada sai kuma inji badasu nakeson tafiya ba" na'ima tace "Allah ya shiryeki nafee, hada kayan ma saikinyi ruwan ido bayan tulin kayanki da kika baro can gida" Nafisa ta juyo tace "Hey...it's not my fault, I want nice and big collections" Na'ima tayi murmushi tace "ruwan ido dai,bawani nice or big collections, kowanne so kike" Nafisa tace "wlh kuwa, duk wanda na dauko sai inga inason bari, kawai zan barsu Inaga" Na'ima tace "kinjiki, sai munje ki damemu da mita akan da kin dauki wasu,matsa in nema miki" ta amsa da toh tana dawowa wajen gadon ta dauki chocolate daya zata bare. Miqewa na'ima tayi ta tafi wajen kayan tana dubawa sukayi shiru na wasu mintuna sannan cikin kwantar da murya Nafisa tace "na'ima in bakyason komawa babu me saki dole..you know that" juyowa na'ima tayi tace "nafee we've talked about this over and over and i said yes, why don't you believe me?" Nafisa tace "the eyes don't lie na'ima I saw it in you, how you became silent these days, shin in tambayeki...why do you choose to deprive yourself happiness ne wai na'ima?" Ta miqe ta qaraso gaban na'iman tace "that pathetic,stupid person!! Should be the one hiding, not you" ta dafa kafadan na'ima tace "those vicious and wicked people should be the one's living unhappy now, not you Na'ima" Fashewa da kuka Na'ima tayi nafisa na riqe da ita suka zauna nan gadon, nafisa na hawaye. Tayi kukan tana goge idonta cikin sanyin murya tace "tsoro nake kada ayi forcing dina back to where i left, I don't don't know how to face what I've left nafisa" nafisa tace "Abba da mami bazasu taba barin hakan ya faru ba kinsani" Na'ima tace "Amma dole watarana hakan ya faru" Nafisa tace " bance bazakije wajensu ba tunda bakida kamarsu, but forcing you back dinne ba wanda zai saki hakan, kuma kisani Allah yana tare dake a komai" Na'ima batace komai ba tana share hawayenta idonta na kallon kasan dakin. Nafisa tacigaba "we will always be there, abubuwan da suka faru sun riga da sun faru,bance babu sauran gwagwarmaya agabanki ba amma what I want you to do is to Embrace life strongly as it comes,life is too short for you to be stuck up because of that stupid man, Embrace love when you find it,rayuwar nan bata jiran kowa  na'ima, it's high time you actually start living to the fullest" tana gama fadin haka ta miqe ta koma wajen kayanta tafara diban na tafiyan, Na'ima na nan zaune tayi shiru tana maimaita maganganun nafisa, encouraging words din suna shiga cikin kwakwalwanta. May be it's high time she start seeing all of this in a different direction, duk abubuwan da suka faru a baya zata ajiyesu for now idan lokacin komawanta yazo Allah zai mata jagora. Nan dakin nafisan ta kwana sukayi ta hiransu kafin suyi bacci nafisa na bata labarin yanda umar ya dameta da kira wai zaizo daukan su in sun sauqa, na'ima tace "blocking dai ya fasu" nafisa ta ture ta da hannu tace "kin shiga uku da rashin mantuwa" na'ima ta kama dariya Wayewar washegari suka tattare gidan sukayi storing abunda sukasan zai baci kafin su dawo sannan suka tafi airport dan jirgin safiya zasu bi Jirginsu ya tashi zuwa Nigeria zuciyar na'ima cike da wani irin yanayin da bazata iya fassarashi ba. Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02 ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 06 Tsaye yake a parking space dake compound din babban gidan. gida ne babba wanda kana gani kasan naira ta zaunu gurin mazauna cikinsa, Yananan tsaye jikin motansa da ya bude driver seat kuma bai shiga ba, wayarsa yake dannawa cikin nutsuwa yana nazarin saqon da aka turo masa. Mai gadin gidan ya qaraso ganinshi tsaye nan bai shiga motan ba yace "yallabai ko da abunda za ai maka?"  ya dago yana kallon maigaidin yace "a'a yakasai jeka abunka" yakasai yace "toh yallabai afito lafiya" ya juya yana komawa bakin aikinsa. Shiga driver's seat din yayi batareda ya kulle kofar motan ba ya miqo kafarsa daya waje yacigaba da abunda yakeyi. Yananan zaune for almost twenty minutes wata mota ta shigo compound din, bai dago kansa ba saida ta qaraso tayi parking dan nesa dashi sannan ya daga Ido yana nazarin motan, ganin wadda ta fito daga driver seat yasa nan take yayi danasanin tsayuwarsa a wajen bai fita ba, aranshi yana cewa me yasa tun dazun bai tafi ba inyaso sai yadawo inya nutsu ya duba saqon nashi. Laila ta juyo ta kalleshi, take ta fara murmushi tana gyara gyalenta data saqala a kafada, a daya side din ma qawartace ta fito suka taho tare Laila na gaba tana qarasowa cikin zumudi Duk wani mood din fitan yaji ya fita daga ranshi, ya fito daga motan ya rufeta yana maida wayansa aljihu. qarasowan su wajen Laila tace "yaya ashe kadawo?..Ina wuni" gently Ahmad ya amsa da "lafiya" batareda ya amsa tambayanta na farko ba, qawarta mai suna luba ta gaisheshi ya amsa shortly, Laila tace "nakira ba adadi baka dauka ba, i just want to know how you are" ta qarasa tana murmushi bakinta kamar gonar auduga" Ahmad yace "oh really?, may be bana kusa" Amasanshi ta qular da ita wanda har yanayin fuskanta yaso nunawa tayi saurin waskewa da wani murmushin tace "Kai yaya, I've been calling fa" bai bata amsa ba ya dago hannunsa yana duban wristwatch dinsa yace "I'm late Laila, and nayi mantuwa" ya juya tareda cewa "ki gaida su mommy" ya nufi babban part dinsa shida Adam wanda ke nan compound din gidan, yabarsu Laila nan tsaye a parking lot. Laila ta cika kamar zata fashe, qawarta ta tabo kafadanta tace "kawata waye wannan din?, kinga yanda yake mana magana kuwa,ko shine Ahmad din naki?"  Laila bata juyo ba balle ta bata amsa ta qurawa side din su Ahmad ido ta jijjaga kai tana kwafa tace "daman naji labarin yadawo nazo na ganewa idona" luba tace "uhm, guy dinnan is full of himself" Laila tace "zanyi maganinshi ne, nikuma!!...yakusa zuwa hannu wlh" luba tace "a yanda kike rawan kafa a gabansa dinne zakiyi maganinsa, girl you must be fooling yourself" Laila ta juyo tana murmushi kadan tace "kedai ki zuba ido ki gani" ta nufi gurin motanta tace "mutafi" luba tace "ha'aa bazamu qarasa ciki mugaisa da mutanen gidan bane?" Laila tace "nagama abunda yakawoni nidai, in zaki zo mutafi to" luba ta kyabe baki ta taho suka shiga motan. Haka Laila ta tada motanta ba kunya megadi yasake bude musu gate suka bar gidan batareda ta qarasa ta gaishe da iyayen Ahmad ba, wanda mahaifishi ya kasance yayan nata mahaifin Bayan Ahmad ya shiga part din nasu yawuce Adam dake zaune nan falo yana kallo ya nufi stairs zaije dakinsa dake sama zai chanja kayan jiikinsa don dagaske kuma fitan ya fice masa arai, bayan yayi changing into qananan kaya ya dawo nan falon ya wuce qaramin dining area ya hado tea dinda Mamma, mahaifiyarsa ta aiko musu dazu. Ya zauna a kujera Adam ya juyo ya kallesa yace "badai har kaje kadawo ba" Ahmad yace "nafasa fitan" Adam ya gyada kai yana maida hankali kan kallonsa, sukayi shiru while Ahmad ya ciro wayansa yana dannawa as yana sipping tea dinsa. Bayan wasu mintuna Ahmad ya ajiye cup din shayin yana kallon Adam yace "the investors has reached out, they want a meeting" Adam ya juyo yace "wait....about the app?" Ahmad yace "yes" Adam yace " but for real though, you really want to sell it?" Ahmad ya gyada kansa, Adam ya cigaba "Dude, you have almost 6.5 million users, this is huge you know" Ahmad yace "I know, but they are offering big money on this. Beside, this year nakeson launching sabon ai" Adam yace "it's settled then, a Ina sukayi setting meeting din?" Ya amsa da "London but bamuyi arranging date ba tukun" Adam yace "Okay, dama ka dade baka leqa branch nacan ba, this is your chance" Ahmad yayi murmushin gefen baki yace "mundade dai" Adam yace "Dude I'm not the head,you are" ya daga kafada yace "it's part of your job too" murmushi kawai Adam yayi yace  "anyway, I'm happy for you...for real" Ahmad yace "thanks man" ya miqa hannu ya dauko ipad dinsa dake kan table yana qara duba email dinda investors din suka tura masa. Wuraren qarfe sha biyun rana jirginsu Na'ima ya sauqa Abuja,suka fito duk a gajiye Bayan sun gama duk wasu formalities suka wuce bangaren arrivals, nafisa sai juye juye take tana neman wanda yazo daukansu, tayi tsuka tace "yaron nan bai iso ba kenan" Na'ima tace "waye yaron, Umar?" Nafisa ta juyo tace "wani Umar kuma, haka kurum yaga kamar nima ina zumudin ganinsa ne" Na'ima batasan lokacin da dariya tazo mata ba tace "nafee babu mai iya miki sai Allah" nafee ta juya tana neman qaninta da Mami tace zaizo daukansu tace "sis mazan ne kamar zuma suke saida wuta" na'ima jijjaga kai kawai tayi batace komai ba. Can gefe suka hango Al'ameen riqe da name sign da sunayensu rubuce ajiki, shima hangosun da yayi ya ajiye sign din ya nufosu yana fara'a su na'ima suka nufeshi suma, qarasowa yayi tareda yin side hug wa nafisa sannan ya juyo yana kallon Na'ima yace "anty na'ima ya zaman gajiya" tace "Alhamdulillah" Ya riqe wasu daga akwatin nasu suka qarasa wajen motansa nafisa tace "shine ko ka fada mana ka dawo sai gurin Mami mukejin labari" yana murmushi yace "surprise naso muku fa Mami ta batamin shiri" Suma murmushin sukayi suka shiga motan,bayan ya gama sa kayansu a booth din  ya shiga motan yaja suka bar airport din suka dau hanyan gida. Shigan motan

Chapter 2 of 19