yasa taja bakinta tayi shiru..dan komai na bikin bata ganin yana tafiya akan seti..
Na'ima na kuka kamar zata shiqe su umma na bata hakuri aka sata a mota Sufi ya tuqasu aka kaita nan gidan da Alhajin ya siyawa Bilal din wanda babu wani nisan tashin hankali tsakaninsu....
Bintu Musa ce ✍️📚
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
Chapter 29
Basu wani dade ba suka isa gidan Bilal din da ya kasance bawani babba can ba amma me kyau sannan stair building ne, har dakin Na'ima dake sama suka kaita, balaifi Alhaji yayi qoqari sosai gurin saka musu kaya masu tsadan gasken da ko 'yar cikinsa iyakaci, su umma jummai sai santin gidan suke bakin su yaqi rufuwa, itadai Na'ima na zaune kan gadon idonta yayi jaaa, sunanan zaune Larai ta shigo dakin fuskan a dinke tace "yauwa ga mota can za'a maida kowa gida" su salame suka bude baki cikin mamaki dan sun taho da niyyan kwana ne gidan, umma zatayi magana anty Amarya tayi saurin miqewa tace "ku taso mu tafi" fashewa da wani kukan Na'ima tayi sai anty amaryan ta riqota tana bata hakuri da kuma nasiha, itadai Na'ima duk nasihohin nan da ake mata bata gane komai dan har lokacin bata iya hasko wane irin zama zatayi a gidan bama balle taji aranta ga abunda ya dace tayi, Matar kawu Nasiru ma sai qananun magana take tana cewa "toh angon da baya nan ne za'a bar yarinya ita kadai a babban gida haka" Larai tace "ba matasalarku bace wannan, ango kam duk inda yake ai yau zezo tunda an kawo masa amaryarsa" umma jummai sai ido ba baki ganin Hajiya larai na magana jiki duk gwalagwalai, haka Larai ta tusa kowa na gidan a gaba suka fice Na'ima na kuka, bayan tafiyansu sai ta kalmashe kafafunta a qirjinta anan zaune kan gadon ta cigaba da kukan babu me lallashi...
Har dare yaja Na'ima nanan zaune sai da taga kukan bazai kaita ko'ina ba sannan ta tashi fara cire kayan jikinta, kayanta ta gani plus na akwatin acikin wardrobe ta nemi dogon riga mara nauyi aciki ta saka sannan ta shiga bandaki tayo alwala, anan dakin ta sake neman sallaya tayi sallahn, cikin sujud ta rinqa addu'an sauqi cikin lamuranta tana kuka, nan kan sallayan tayi bacci....Washegari tunda ta idar da sallah bata koma bacci sai ta sauqa falon qasa Jin kamar qarar gate, leqawa tayi taga ashe da megadi ma agidan, sai taji hankalinta ta dan qara kwanciya jin ba ita kadai bace a gidan..har zuwa rana tana ta zuba Ido ko 'yan'uwan nata zasu dawo amma shiru, sai la'asar mota ta shigo gidan Na'ima tayi saurin leqawa taga Sufi ne ya fito daga motan ya qaraso yayi knocking, sai da ta koma ta sako hijab sannan ta bude masa suka gaisawa, zama yayi ta kawo masa ruwa sai ya miqo mata kwalin waya tareda kudi masu yawa yace "gashi inji Alhaji, yace zai kiraki" godiya Na'ima tayi ta karbi wayan tanajin kamar ta tambayesa dalilin rashin zuwan su umma, miqewa yayi ya mata sallama sai ta jefo masa tambayan ya amsa da "ai sun koma Adamawa tun da safe" daskarewa tayi nan tsaye tanajin hawaye na zuwa mata, sallama sufin ya mata ya tafi, Na'ima na nan tsaye cikin sanyi ta koma daki...
Ashe komawan su umma washegari da safe Hajiya ta kira motan da zai maidasu gida, aika shafa tayi akan ta fada musu su shirya da wuri drivers din na jiransu, da aka fada musu duk sunyi mamaki barin ma Anty Amarya da ranta yafi na kowa baci, cikin haushi suka fara hada kayan nasu sai ga su kawu Ayuba ma sunzo, da aka zo shiga motan ne anty Amarya tace dashi "yanzu Fisabilillah yarinyar nan ko sallama bamu je munyi da ita ba zamu koma, hakan ya dace kenan?" Ayuba yace "toh daman sintiri zakuyi tayi ne gidan yarinya" Umma tace "toh wai ina angon ma ni jummai" yace "yana hanyarsa ta dawowa daga Lagos, ashe wani uzuri ne ya taso masa babba shiyasa be zo ba" itadai Anty Amarya kawai sauraronsa take amma komai na bikin nan ya sire mata arai kuma tausayin Na'ima take sosai ganin akwai abunda ke damun yarinyar amma ta danne, saida suka shiga motan Hajiya ta fito ta miqawa Ayuba bunch din dubu ya karba baki har kunne yana godiya anty Amarya na hararansa ganin shi ko ajikinsa wulaqancin da aka musu.....
Week Later...
Na'ima ita kadai take rayuwa cikin kadaicin a gidan kuma abu daya ne ke debe mata kewa shine Jin motsin megadin gidan, inta tashi da safe haka zatayi wanka ta shiga kitchen ta dafa abinci dayake akwai komai na amfani cikinsa, tayi sallah tayi bacci dan ko baqo batayi, dama tun ranar da Sufi ya kawo mata waya bayan tafiyansa tayi waya da Alhajin suka gaisa ya tambayeta ko akwai abunda take buqata tace babu, hakuri ya bata akan Bilal din yana kan hanyar dawowa wanda ita Na'ima hakan fargaba yasaka mata da tashin hankali be sani ba, tun daga wannan lokacin kuma bata sakeyin waya da Alhajin ba kasancewan ya fita qasar waje wani aikinsa shima, ranar da ta cika kwana goma sai ta shirya zata tafi makaranta abunta, bayan ta shirya cikin doguwar riganta da hijab tayi sallama da megadin gidan da ya kasance bafulatani..
Batayi lattin zuwa ba dan tsirarakun mutane ta samu a ajin dayawa basu qaraso ba tukun ta samu waje ta zauna, can sai ga Nafisa ta shigo wadda ganin Na'iman yasata ware idanu ta nufeta, zama tayi nan kusa da ita kafin ma su gaisa tace "Na'ima lafiyanki kuwa, meya faru bakya zuwa? gashi banida number'n ki balle in kiraki" sai Na'ima tayi murmushi tace "wani uzuri ne ya tasomin Nafisa" Nafisa bata ja tambayan ba ganin Na'ima bata sake da ita ba har sannan sai tayi shiru, ranan har yamma suka kai kafin su gama school activities din nasu, da Na'ima tayi wa nafisan sallama sai ta nemi ta rage mata hanya, farko qi tayi sai da Nafisan ta nuna ranta ya baci sannan ta hau motan nata, sunyi nisa cikin tafiya Na'ima ta budi baki a hankali tace "Aure akaimin Nafisa" dan burki Nafisan ta taka kafin tace "what?..Aure kuma" Na'ima na kallonta ta gyada kai batace komai ba, ta sake cewa "yaushe? within last week zuwa yanzu kenan?" Na'ima tace "Eh", da farko shiru nafisan tayi sai ta dan yi murmushi tace "Ayya Allah ya sanya alkhairy kice da amarya nake tare yau din" murmushin dole Na'ima tayi batace komai ba suka cigaba da tafiyan cikin shiru, sake kwantantawa nafisan sabuwar unguwar su Na'iman tayi, bayan sun isa sai nafisa tace "Na'ima, to tell you the truth gaskiya banji dadi ba, I understand that baki sanni sosai ba or you don't want to be friends with me, amma ace har kiyi aure bazaki fadamin ba in miki ko addua ma" sai jikin Na'ima yayi sanyi tace "Dan Allah kiyi hakuri auren ne yazo cikin gaggawa shiyasa, na dade da daukanki matsayin kawata wallahi nafisa, ga wayata ma ki sakamin number'n ki" karban wayan Nafisa tayi tace "kuma dama tun can da goron sa ne akanki shiyasa akayi auren da wuri haka?" Na'ima ta danyi shiru sai tace "Cousin dina ne" Nafisa ta gyada kai sai Na'ima ta sake cewa "ki shigo mana ko ruwa kisha" Nafisa ta dan girgiza tace "A'a Amarya Nagode sai wani lokaci, may be ma Ango yananan ciki yana ta jiran dawowarki" ta qarasa maganan tana dan dariya, da farko dan stiff Na'ima tayi sai tayi murmushi ta mata sallama ta fice daga motan cikin sanyin jiki...
Kwance Bilal yake akan gado tareda stella dake kwance jikinsa, tunda Bilal ya dawo gari Lagos yake tunanin ta inda zai fadawa Stella maganar auren da akayi masa, gashi Alhaji ya bashi adadin wasu lokuta akan ya koma, shafa attachment din stella'n yafara yi a hankali yace "Baby i want us to talk" dago kai Stella tayi tana murmushi tace "What is it Baby?" Yana kallon idonta ya sake kwantar da murya yace "you know i love you right?" Ta gyada kai tanajin wani dadi a zuciyarta, yace "no matter what.. you'll always be my woman, no one else " dan gyara kwanciya tayi takai hannu tana shafa fuskansa suna kallon kallo cikin ido, sai da ya sauqe numfashi yace "iyaye na sunmin Aure Baby" dan stiff tayi daga kwancen sai kuma ta fara kokarin miqewa daga jikinsa ya kamota ta yi saurin fincike hannun tace "don't you dare touch me" miqewa sukayi dukansu suka tsaya nan tsakiyan dakin tace "wallahi baka isa ba" ya girgiza kai kafin yayi magana ta kai hannu tafara dukan qirjinsa tace "you've betrayed me Bilal, bamuyi haka dakai ba" ya rugume ta tareda cewa "ke kadai nakeso baby and you know that" hankali tashe Stella tace "you're not going anywhere Bilal" ta dago kai ta kallesa ta fara hawaye tace "in ka taba wata mace zan iya mutuwa" yayi saurin girgiza kai yace "what are you saying Baby? Me zanyi da yarinyar can da banason ganinta ko na minti daya" rungume Stella yayi yacigaba da fadin kalmomin lallashin da duk sukazo bakinsa, a wannan lokacin ji take komai zata iya yi akan Bilal din kuma har iyayensa bazata bari ba....
A rikice Stella taje gidan qanwarta yammacin ranan bayan sun gaisa chiamaka ta fara tambayanta meya faru ganinta ba'a nutse ba, Stella tace "shikenan chi, they've won against me, aure iyayen Bilal suka masa" chiamaka ta ware Ido tace "ta nan suka bullo kuma, lallai da mu suke zancen" Stella tace "I can't let Bilal touch her, zan iya mutuwa Chi" tace "meyasa zaki tada hankalinki akan wannan, kema fa kinsan abunda baze yiwu bane" dan jijjaga kai Stella tayi tace "sai kin ga yarinyar zaki shaida hakan Chi, i can't compete with her, duk da inada tabbacin Bilal ba sonta yake ba impact nasani yama tsaneta sosai, amma kinsan in akwai abu daya da bariki ya koya mana shine rashin yadda fully da namiji, wallahi bai isa yazauna da wata mace ba, wahalar da nayi akansa bazata fadi a banza ba" ...Stella bata bar gidan qanwar ta taba sai da suka gama qulle qullen yanda zasu bullowa lamarin kuma duk ba ta hanya me kyau ba...
Two months Later..
Zuwa wannan lokacin Na'ima har ta saba da rayuwan kadaici cikin gidan aurenta, sabo ne sosai ya shiga tsakaninta da nafisa zuwa sannan, yawansu a makaranta tare, cin abincin su tare karatunsu tare, kuma har zuwa wannan lokacin Na'ima bata samu courage din bayyana damuwanta ga Nafisan ba, ranar da nafisa ta fara zuwa gidanta wuni sukayi suna hira, sukayi girki sukaci anan kitchen din ma suna raha kamar ba Na'iman da take fargaban zamanta gidan ba,tana iya qoqarinta na zuwa gaishe dasu Hajiya in anyi kwanaki amma har zuwa lokacin basa wani dogon magana ita da Hajiya, Alhaji ne dai gamuwanta dashi baifi sau biyu ba saboda baya zaman gida sosai gashi bayan auren nasu yayi wata doguwar tafiya zuwa china wanda har sai da Hajiya ma ta bisa, a wannan haduwar nata dashi ya bata hakurin rashin zuwan Bilal, har ya nemi tabbatar da karyar da Bilal din ya masa akan suna waya da Na'iman har ya so ta bishi can Lagos din to sai tace A'a, shi Alhaji Jin wai Na'ima tace A'a din se ya dauka akan makarantar ta ne tace haka din shiyasa bai ja magana ba, amma a zahirin gaskiya ma Bilal be san Na'ima na zuwa wata makaranta ba ma, Na'ima ta amsawa Alhajin da cewa "Eh hakane" saboda batasan me zatace ba toh, dan har ranta batason dawowan Bilal Kano saboda tasan ba alkhairy ne zai hadata dashi ba...
Ranar wata asabar Nafisa tayi alkwarin zuwa gidan Na'iman akan zasuyi karatun exams dinsu dake gabatowa, zuwa 11 na safe sai gatanan da motarta, Na'ima na bude mata qofa suka fara fara'a, Nafisa ta dago ledan hannunta dake dauke da snacks da sweets tace "da guzuri na nazo, Mami bata bari insha zaqi a gida" Na'ima tayi murmushi tace "tanada gaskiya ai, kuma bakya ciwon ciki?" Nafisa ta zuba kayan nan kan kujeran falon ta zauna itama sannan tace "tab babu abunda yakemin, a boye nake sha in na seta lokacin da bata kusa ai" Na'ima ta danyi dariya tace "Laa to sai na fallasaki" Nafisa tace "aikuwa Mami na tambayanki sosai, yaushe zakije? kinsan na nuna mata hoton ki, da zan taho dinnan ma har Abu saida yace in gaishe da ke" Na'ima na fara'a tace "Ina amsawa, in Sha Allah zan je Nafisa" da haka suka hau hira a anan zaune falon basuyi karatun ba, sunayi sunashan chocolates din Nafisa na bata labarai suna dariya, sai da Na'ima taga lokaci na neman qurewa ta tafi kitchen dafa musu abinci, nan kitchen din nafisa ta biyota tafara tayata suna hira, bayan sun gama nafisa tajiyo wayanta na ringing acan falo ta fice daukowa, zuba abincin Na'ima tayi a plates guda biyu zata kai musu falon, shiganta Falon ta ganshi tsaye ga Nafisa nan zaune waya kare kunnenta binsa da kallo tareda wacce ke bayansa, wani irin bugawa zuciyan Na'ima yayi saida plates din suka fadi daga hannunta, da sauri Nafisa tayi gurinta ta tsugunna zata dauke plate din tace "lafiyanki Na'ima" idon Na'ima na kan Bilal dake kallon ta kamar yaga mutuwar sa, qarasawa kan kujera Stella tayi ta zube alamun ta gaji tana bin Na'iman da kallo, Bilal na kallon Na'iman ya nuna Nafisa yace "Who is this?" Kasa magana tayi jikinta na rawa Nafisan na kallonta, sai Bilal ya sake mata wani tsawan yace "I'm talking Na'ima" murya ta na rawa tayi saurin cewa "kawata ce yaya" yace "me tazo yimin a gida?" Miqewa tsaye Nafisa tayi hannunta riqe da plates din ta dan ware ido cikin mamaki sai Na'ima ta girgiza kai tace "kayi hakuri" kallon Nafisa yayi yace "Get Out" sai ta tsaya kallonsa cikin ido amma data juya ta kalli Na'ima taga tayi tsuru tsuru da ita sai batace komai ba ta ajiye plates din nan qasa kusada inda abincin ya zube sannan ta nufi kujera ta dauki jakanta tana bin Stella da wani irin kallo, cikin sanyin jiki Nafisa ta fita daga falon Na'ima na nan tsaye ta kasa bin bayanta...
Bintu Musa ce ✍️📚
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨KUNCI ZUCI✨
Na Bintu Musa
Chapter 30
Sai da Nafisa ta fita suka Jiyo tashin motanta sannan Stella ta kalli Bilal tace "Baby i need water" yace "Okay" ya sake kallon Na'ima yace "Get her water and clear this mess now, you stupid" ya qarasa maganan tareda nuna mata abincin dake zube nan qasan, gyada kai Na'ima tayi sannan juya ta koma kitchen din, sai sannan Bilal ya zauna nan kan kujeran kusada Stella yace "Sorry Baby, me kikeson ci?" tadan kwanto jikinsa tareda kashe murya tace "something light" Na'ima ce ta fito daga kitchen din hannunta riqe da bottle water da drinks dan dama Sufi ke siyo mata duk wani kayan buqatu na gidan tareda umarnin Alhaji, qarasowa tayi ta ajiye musu nan kan glass table din idonta a qasa bata kallesu ba, cikin isa Bilal yace "Cook something light now" ta amsa da "toh" still idonta na qasa, Stella na kwance jikin Bilal din sai kallonta take tana qarajin wani abu ya tsaya mata a zuciya ganin irin kyan Na'ima'n me fusgan hankali, saida Na'ima ta zuba musu juice din a kofi sannan ta juya ta koma kitchen din tana dan gyara wuyan riganta saboda taquran datayi under their Eyes, bayan ta gama kwashe abincin qasan tana aiki a kitchen din tana jiyo dariyan su, da ta gama ma nan dining area ta ajiye bata kallesu ba tazo ta wucesu zata tafi dakinta, Stella har da janyo fuskan Bilal zuwa gareta tana kissing, itadai Na'ima kanta na qasa ta wucesu..Fitowan da bata sakeyi downstairs ba kenan, bayan tayi sallahn ta ko wanka ma bata samu yi ba ta hau gado ta zauna, Jiyo muryansu tayi sun hawo saman sai taji an bude dakin da ke facing din nata, dan bariki sai Stella taqi rufe qofan, haka Na'ima ta fara jiyo badalarsu Stella har da ihun ta, cikin sauri ta nufi drawer na mirro'nta ta dauko auduga tasaka a kunne sannan ta qudun dune da bargo nan kan gado tana addu'an Allah yasa kar suyi dogon zama a garin su koma inda suka fito....
Dakyar Na'ima tayi bacci saboda yanda takejin zuciyarta a wannan daren, wayewar washegari shima kasa fita tayi, tana nan zaune aka fara buga mata qofa da karfi tayi sauran tashi ta bude, Ido hudu tayi da Bilal yana kallonta yace "do i have to say it before you make breakfast?" Tayi saurin girgiza kai tace "yanzu zanyi yaya, Ina kwana" bai amsata ba yajuya tareda banko kofar a fuskanta tana nan tsaye, sake budewa tayi ta fito tareda wuce kofar dakin nasu dake kulle ta sauqa qasa zuwa kitchen din, cikin sauri ta kammala musu breakfast din tana cikin jerawa a dining Stella ta sauqo sanye cikin t-shirt din Bilal din da bum short, fara bude flask din tayi ta bi chips da fried egg din da wani kallo sai ta yamutse fuska tace "where is the tea?" Na'ima tace "yana kitchen tukunna" sai ta juya zuciyarta na quna ta shige kitchen, saida ta zubawa Stella tea tananan zaune hakimce a dining chair, takai baki ta kurba sai tayi saurin burtsoshi daga bakinta wanda hakan yayi daidai da sauqowan Bilal, yayi saurin qarasowa yace "what happened Baby" Stella na kyabe fuska tace "Baby what kind of tea is this, jiya ma haka naji gishiri cikin abincin nan" karban shayin yayi ya kurba sai ya jefawa Na'ima cup din tayi baya duk da haka saida shayin ya zuba jikinta tajiyo zafinsa har cikin jikinta, bata farfado daga wannan ba taji Bilal ya sauqe mata wani mari mai dauke ji a kunne, dafe fuskanta Na'ima tayi ta sake yin baya idonta na kawo ruwa, jikinsa har wani tsuma yake tsabar masifa yace "Don ub*nki kashemu zakiyi, bakiji yayi daci bane" batayi magana ba kanta a qasa sai ya kai mata wani dukan a fuskan yana cewa "sai na rinqa repeating magana sannan zaki amsamin kenan" kuka me sauti Na'ima tafara yi tana bashi hakuri, Stella ta dauko chip daya takai baki tana kallonsu with amusement batayi magana ba, Na'ima na kuka ta koma kitchen ta dora musu wani shayin, da ta gama nan ta sake kawo musu suna zaune a dining din ta zuba musu sannan ta koma sama cikin sauri, kuka ta fashe dashi bayan ta shiga dakin tana tsaye, juyawa tayi ta kalli mirror sai taga gefen fuskanta yayi ja ga lebenta na dan fitar da jini, tana hawaye ta dauko tissue tafara gogewa bata daina kallon kanta a madubin ba,
Gashi tanada lecture zuwa 11 batasan ta yanda zata fara fita daga gidan ba, dan tsoron tambayansa take kuma...
Allah ne ya taimaki Na'ima ta Jiyo muryansu a parking space can taji tashin motan nasu megadi ya bude musu gate suka fice, da saurinta ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya sai ta hau neman face mask cikin kayanta tayi sa'a kuwa tasamu..
Bayan ta rufe gidan sai ta rasa yanda zatayi da key din kawai ta baiwa megadi tayi saurin tafiya bakin hanya dan neman abun hawa, isarta makarantar ta samu class mates din nasu suna fitowa daga hall din da za'ayi combined lecture din da nufin an samu change of venue, hango Nafisa tayi sai taga tayi saurin qarasowa wajenta tace "Na'ima lafiya kikayi latti, it's unlike you" ta amsa cikin sanyin murya da "Ban lura da lokacin bane" Nafisa ta gyada kai still tana kallonta ganinta yau kuma sanye da face mask, fara tafiya sukayi sai da sukayi nisa duk anyi gaba an barsu sai Na'ima ta kalli Nafisan cikin kwantar da murya tace "Nafisa Dan Allah kiyi hakuri da abunda ya faru jiya" da farko Nafisa batace komai ba sai kuma ta jefa mata tambaya tace "wacece wadda yazo tare da ita jiyan" juya kai Na'ima tayi idonta na kawo hawaye tace "bansan ta ba nima" cikin dan mamaki Nafisa ta kamo hannunta, qarqashin wata bishiya ta jasu suka tsaya sannan tace "Na'ima you can tell me everything, inaji ajikina akwai abunda yake damunki bazaki fada ba" kuka Na'ima tafara mara sauti sai kawai Nafisan ta dan rungumota tafara buga bayanta itama idonta taji yafara kawo hawayen, sai da Na'ima tayi kukan sosai sannan suka zauna kan wani rest bench a gurin Nafisa tace "Na'ima me yake faruwa dake Dan Allah" tana kallon gefe tace "He's assaulting me nafisa" tsabar mamaki har bude baki nafisan tayi sai Na'ima takai hannu tacire face mask dinta, cikin tashin hankali naifia ta kai hannu tana taba fuskan tace "he did this to you?" Na'ima ta gyada kai batace komai ba still idonta na hawaye, Nafisa tace "wane irin dabba ne wannan da zai kai hannu jikin mace, kuma kin fada a gidanku?" Na'ima ta girgiza kai, Nafisa ta sake cewa "baki fadawa maman ki ko babanki ba? Na'ima what is wrong with you, ace mijinki ya duke ki kuma sai kiyi shiru" tsayawa kallon Nafisan tayi cikin sanyin murya tace "iyayena sun dade da mutuwa Nafisa, a gidansu mijin nawa na tashi" zuwa lokacin kan nafisa ya kulle kuma sai ta damqo hannun Na'iman tana squeezing tace "tell me everything please" nan Na'ima ta sauqe idonta qasa tiryan tiryan tafara bawa nafisa labarin ta tun tana qauye har kawo yanzu da take zama gidan Bilal, hawaye Nafisa ta rinqa yi tana sharewa bata daina kallon Na'iman cike da tausayi ba, tace "you have to tell his father, this can't continue Na'ima, Kuma kinayin addu'a sosai?" sai Na'ima tayi shiru batace komai ba, Nafisa ta sake cewa "kina tashi cikin dare ki kai kukanki gurin Allah Na'ima?" Tunani Na'ima tafara dan gaskiya dan gaskiya ta fannin addini tanada rauni kasancewar both gidajen da ta taso duk ciki babu wanda aka bada himma ta fannin karatun addininta, sai ta girgiza kai Nafisa na kallonta tace "kina sake sosai Na'ima, Bilal yana alaqa da irin wadda nagani jiya kuma ace bakya yawan addua?" cikin sanyi Na'ima tace "ai bansan addu'o'in da ya kamata inyi ba" nan Nafisa ta fara karanto mata ganin bata ganewa sai ta dauko takarda daga jaka tafara rubuta mata su, shawarwari Nafisa ta hau bata suna nan zaune, lecture dinda basuyi ba ranan kenan, da nafisa ta tashi maidata gida nan ma tayi ta encouraging dinta akan ta samu Alhaji da maganan, itadai Na'ima sai gyada kai babu magana a haka har suka isa, tayi sa'a basu dawo ba kuwa nan ta hau dafa musu abinci cikin sauri, basu dawo gidan ba sai tsakar dare, Na'ima na kishingide kan sallaya tajiyo buruntun su, washegari ma sai da ta jira fitan su sannan ta fice school din, a bakin class ta hango nafisa na tsaye tana jiranta bata shiga ba, Na'ima na murmushi ta iddata sai nafisan tace "thank God, nazata wani abun ne ya faru" murmushi me fadi Na'ima tayi sai tace "shine kikaqi shiga class kuma" bata amsa ba mata ba sai tace "bazai barmu mu shiga ba yanzu, ya kusa gamawa", jansu tayi gurin cin abinci tayi musu order sunanan zaune, bayan sunci Na'ima tayi insisting biya Nafisa ta hanata tareda saurin miqa card nata, sai da suka tashi komawa gida na'ima tasan nafisan bata zo da motanta ba, tace su jira yayan ta da zai zo daukanta, basu wani dade ba wata wagon jeep ce ta faka a gabansu nan inda suke tsaye akayi rolling glass din gefen me zaman banza wani kyakkyawan yaron da bazai wuce shekara 13 years ba ya leqo kansa yana dariya, Nafisa ta hararesa tace "wallahi fitowa zakayi ma, dan ajiyata ce a gaban motan nan" wanda ke driving din yayi dariya yace "hala kwai kikayi a wajen" ta bata fuska tace "Yah faruk meyasa zakazo dashi Fisabilillah" bude motan yayi sannan ya fito be zagayo ba ya tsaya yana kallon Na'ima dake dan kauda kai dan ta cire face mask din a sannan, Nafisa tace "Yaya meet my friend
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 19