na'ima kaman ya zazzago dan hararan nafisa, ita ta rasa meyasa nafisan ke son suje gidan Ahmad din all of a sudden, hada Ido tayi dashi yana kallonta ta mirror din gaban motan, tayi saurin kauda kai ta koma daf da window tana kallon titi, tana jinsu suka cigaba da hira sama sama har bacci ya dauketa....
Shigarsu cikin town din Ahmad yayi parking gaban wani babban store yace "I'm coming" sannan ya fita ya shige ciki, bai wani dau lokaci ba ya fito da wata qaramar leda a hannu ya shiga motan suka tafi, basu kai ga isa arean su nafisan ba ya sake tsayawa a gaban wani restaurant nan ma yashiga bai dade ba yafito hannunsa riqe da takeouts, miqa package din yayi gurin nafisa ta karba ta ajiye kan cinyanta, ya zagaya ya shiga motan..
Bayan sun isa haka Ahmad ya tayasu diban kayansu suka shiga elevator dazai kaisu floor dinsu..
Shigansu apartment din Ahmad ya dan bi middle space din nasu da kallo sannan ya wuce gurin mini dining area din nasu ya ajiye su takeouts din da car key dinsa, Na'ima ta fara daukan kayan dake nan falon tana kaiwa dakinta batareda ta kalli inda yake ba, ruwa nafisa ta dauko daga kitchen takawo masa ya karba, yace "Ina duster?" Ta koma ta dauko saita fara goge masa kujeran dining din, bayan ta gama yace "thank you" sannan ya zauna ya ciro wayansa yafara dannawa, fara bude takeout din nafisa tayi yace mata "kunada kayan shayi nafisa" ta gyada kai tace "Eh akwai yaya, in hada maka ne" ya miqe yace "No, zo kibani" shigewa kitchen sukayi Ahmad zai dora shayin
Itadai Na'ima tunda tagama shigo da kayansu daki bata sake fita ba, ta cire dankwalinta da ribbon din da ta daure timilin gashinta sannan ta nemi waje nan bakin gado ta zauna tana jin wani iri sanin presence din wanda ke cikin apartment din nasu...
tananan zaune tana jiyo hiransa da nafisan jefi jefi can kuma saiga nafisa ta shigo ta juya ta rufe kofan sannan ta qaraso gurin na'ima cikin qasa da murya tace "meye hakan kuma na'ima mutum yakawo mu tun daga London amma kin wani shigo daki kin barsa a falo" Na'ima tana kallonta tace "ba gashi kuna hiran ba nafee, mezance masa in na fitan" Nafisa tace "A'a Na'ima, yayanmu ne fa, saikace wani baqo, at least show your care mana, shida ba wani dadewa zeyi ba yanzu zakiji yace zai tafi ma" Na'ima ta gyada kai tace "to ganinan fitowan" Nafisa ta miqe tace "yauwa ko kefa" ta fice..shiru Na'ima tayi sai can kuma ta dauki ribbon din nata tasake daure gashinta ta dau veil din tamayar jikinta kafin ta fice falon, zaune ta gansa shi kadai a falon yana danna wayansa, ya dago kai suka hada ido tayi saurin sauqe nata idon, rasa abunda zatace masa tayi sai kawai ta nufi kitchen a tunanin ta nafisa na can, Ahmad yadan bi bayanta da kallo yadanyi qaramin murmushi baice komai ba
Bata samu nafisan a kitchen ba sai taga takeout din nasu anan kan kitchen island, qarasowa tayi ta fara budewa da daddaya takai hannu ta dauki chip daya tafara ci, Ahmad yashigo kitchen din ta dan kallesa ta dauke kai, shima wucewa yayi gurin gas ya duba tea din, sauqewa yayi ya dauki cup ya dauraye a pampo sannan ya juye shayin ya juya gurin na'ima dake nan tsaye, miqo mata shayin yayi yace "Here..drink this" dan kallon shayin na'ima tayi ta kuma kallonsa taga idonsa akanta, miqa hannu tayi ta amshi shayin takai baki, ya juya ya fita sai gashi yadawo da ledan abunda ya siya a store dazu, dan tari Na'ima tafara kadan, ahankali yace "sorry" ta gyada kanta kawai, bude ledan yayi ya ciro wasu magunguna na mura da tari ya balli daya ya dan kalleta yace "dauko ruwa" ta ajiye tea din ta dauko bottle water a fridge sannan ya miqo mata maganin yace "Here..sha wannan" itadai na'ima batace komai ba ta miqa hannunta, bude tafin hannunta tayi da nufin ya saka mata maganin sai taga shiru bai bata ba, dan dagowa tayi ta kalleshi sai taga kallon tafin hannun yake baya ko kifta ido, kafin ta dauke hannun taga ya sa dayan hannunsa yana riqo tafin hannun yace "what's this?" Jin kamar an jona mata electric wire yasa Na'ima saurin kwace hannunta ranta adan bace tace "don't touch me" ajiye maganin yayi yana kallonta cikin sanyin murya yace "meya wannan a hannunki? tabon menene?" tayi shiru batace komai ba yasake kwantar da murya yace "Na'eemah" dagowa tayi ranta yana dan baci akan tamabayar da yayi mata wanda a ganinta ba abunda ya shafesa bane, tace "karka sake tabani" shidai yana kallonta ya gyada kai alaman "toh" sai kuma yasake cewa "what's that on your hand Na'eemah?" Na'ima ta hade rai tace "ciwo naji..but wait, why are you even here? all of this" tayi maganan tana nuna su takeouts da shayin sannan ta dago ta kallesa tace "all this caring..nasan zakace don mu qannenka ne shiyasa but all of these are making me uncomfortable, you're making me uncomfortable har nafisan ma" Tsayawa kallonta kawai Ahmad yayi ta kasa jure kallonsa ta kauda kanta ta cigaba da cewa "we are fine on ourselves for more than half a year now please stop making us uncomfortable"
Ahmad bai daina kallontan ba, can kuma ya gyada kai baice komai ba ya juya ya fara takawa ya fice daga kitchen din yabarta nan tsaye tana jin wani iri kuma..
Tananan tsaye taji fitansa daga apartment din, a wannan moment dinne kuma taji duk wani qunci ya daure mata zuciya, dana sani ya fara shiganta sai kuma ta dago tafin hannunta tana kallon katon tabon dake cikinsa, kawai hawaye ya fara fita daga idonta tana sharewa...
Takasa motsawa daga inda take tsaye a kitchen din, tanata kallon shayin da magungunan tunani iri iri suna mata yawo a cikin zuciya, Nafisa ce ta shigo kitchen din tace "sis naji kamar an fita, yayan ne ya tafi?" Na'ima ta dago ta kalleta tace "bansani ba nima nafisa" Nafisa takai hannu tafara duba magungunan tace "Allah sarki maganin mura ashe ya siyo miki, toh ina ya tafi kuma babu sallama" nan ma Na'ima bata amsa ba, nafisa ta juya ta fice daga kitchen din sai gata tadawo da waya a hannunta tayi dialing line din Ahmad tasaka a handsfree..daga wayan yayi tacan bangaren tareda sallama, nafisa tace "yaya nafito banganka ba nace ko wucewa kayi babu sallama" cikin nutsuwa yace "Eh nafisa, sorry something came up ne" Nafisa tace "bakomai yaya mungode Allah ya saka da alkhairy, sai munzo din muma" yace "Okay bakomai" tareda kashe wayan.
Nafisa ta kalli Na'ima tana nazarinta batace komai ba, cikin sanyin murya Na'ima tace "shine kikace in fito kuma na fiton ke kika shige daki nafisa" Nafee tadanyi dariya tana kai chips bakinta tace "Abu fa naje nema a dakin kuma bansamu ba" jijjiga kai kawai Na'ima tayi ta juya ta fice da kitchen din nafisa na bin bayanta da kallo, murmushi tayi sai kuma ta juya ta kalli kofin shayin data samu a gaba na'iman lokacin shigowanta...
Bayan Na'ima ta koma daki tayi changing into qananan kaya mara nauyi, fitowa tayi ta hau share gidan nafisa ma ta fito suka hau tsaftace gidan tare suna hira, sai da sukaga ko Ina yayi tsaf yana kyalli sannan suka tafi yin wanka kuma, Bayan na'ima tayi wanka ta saka wani kayan ta dauki kayan nafisa dake dakinta ta fita kai mata.
Yammacin ranan suna zaune anan falo itada nafisa, cheese ball ne a hannun Na'ima tanaci amma absent-mindedly, ta qurawa carpet ido bama ta Jin gulman da nafisa dake gefenta take mata akan lamuransu na IG, tunani Na'ima ta fada sosai .... tayi abu kuma ya dameta, duk wani iri takeji wunin ranar akan maganganun da tafadawa Ahmad
Wani fannin na zuciyar na encouraging dinta akan abunda tayi yayi daidai amma wani fannin kuma akasin hakan takeji, bini bini zata dago hannun nata ta kalli tabon, Amma inta tuna cewa dalilin namiji wannan tabon ya zanu a tafin hannunta sai taji cewa gwara da ta kyari Ahmad din, ta dade da yiwa kanta alqawarin itada maza kuma haikata haikata sai kallo daga nesa, shiyasa har yau duk mazan da suke binta anan oxford bata taba sauraran ko daya ba kuma batajin zata sauraran, Amma meye Ahmad yake yiwa zuciyarta aduk lokacin da suka hadu ne? Ta sake tambayan kanta a karo na ba adadi kuma babu amsa..
Jin shirun nata yayi yawa yasa Nafisa dago kai ta kalleta tace "NA'IMAA" juyowa na'ima tayi adan birkice tadan ware ido tace "Uh" nafisa tace "tun dazu inata miki magana, me yake damunki ne" Na'ima ta jijjaga kai tace "babu komai fa" nafisa ta sake cewa "gashinan kinata tunani tun dazu, me ya faru dazu tsakaninki da yaya Ahmad?" Na'ima tace "ni babu komai" nazarinta nafisan ta tsayayi sai kuma ta juyo gaba daya tana facing dinta tana murmushi tace "akwai abunda ya hadaku ne da muka koma gida sis...Ina jin kamshin wani abu tsakaninku" Na'ima ta cusa cheese ball din hannunta a bakin nafisan tana dan dariya tace "wai kamshi..mezanyi dake ne nafee? Yaushe ma na hadu dashi" Ta qarasa tana jijjaga kai, nafisa ta fara tauna cheese din tana dariya itama tace "in tayi tsami zanji ne, da bakinki zakimin bayani yarinya" na'ima ta jijjaga kai tana murmushi sai ga kiran Mami yashigo wayanta....
Washegari ya kasance Monday akwai zuwa school Amma Na'ima bata tashi ba sai wajen qarfe 10 kasancewar batada lecture ranan kawai submitting wani essay dinta zata je yi, brush tayi harda wanka kafin ta fita zuwa kitchen dan tayi breakfast, nafisa tasamu a kitchen din ta dafa musu noodles tana zaune jikin kitchen island din suna video call da faruk, leqawa na'ima tayi tana murmushi tace "yaya Ina kwana" faruk yana murmushin shima yace "habibtin Mami nakiraki ashe kina bacci" ta gyada kai cikin sanyin muryarta tace "yau baka fita aiki ba ne yaya" yana kallonta yace "Eh banje ba....a train kuka dawo ne jiyan? naji muryanki wani iri kamar sanyi ya kamaki" kafin ta amsa Nafisa tace "yaya Ahmad ne fa yakawo mu" faruk yadanyi stiff sai kuma yace "Ma Sha Allah, cemasa kukayi yazo ya kaiku kenan?" cikin sanyin murya Na'ima tace "Nafisa ce ta fada masa yaya" faruk yadan kalli nafisa data dan harari Na'ima,yana dan hade giran sa yace "ce miki akayi baida aikin yi ne" Nafisa tace "nifa shi ya tambayeni yaushe zamu koma, kuma laifi ne dan ya kawomun yaya" faruk ya dan sake fuskansa yace "yayi kyau hakan, ya taimakeku ma" da haka suka gama wayan, bayan sunyi breakfast din suka fice zuwa school din.
sai da suka biya park dinda suka bada ajiyan motan su dazasu koma gida, suka daukota sannan suka wuce makaranta..
Bintu Musa ce✍🏻📚
ArewaPen @Bintu Musa
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
ArewaPen
https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 17
Hankali suka maida sosai akan karatunsu, basa wani samun lokacin kansu kuma yawanci a gida sukeyin researches din nasu kasancewar sunzo wannan gandun, gidan anty Amnah ma saida sukayi wata guda tukunna sukaje shima waya ta kira ta rinqa mita sannan sukaje, zuwa yanzu na'ima ta dan cire tunanin Ahmad daga ranta ganin babu inda tunanin zai kaita, tanajin time to time yana gaisawa da nafisa tun tana expecting zai tambayi ya take har ta hakura ganin yayi keeping boundaries dinsan yasa itama tadan ajiye batunsa a gefe dan harga Allah batason abunda zuciyanta keji a duk lokacin da idanunta sukayi tozali dashi, nafisa bata sake zancen suje gidansa ba wanda daman Na'ima batada niyan zuwa ko nafisa ta nemi hakan
Zaune suke a a falo da daddare na'ima na typing abu cikin laptop dinta, nafisa dake kwance gefenta tace "kin fara dissertation din ki kuwa?" Na'ima ta bar abunda take ta juyo tace "kin tuna course mate dita dinnan wanda nace miki sunanta Zara?" Nafisa ta gyada kai tace "yar Lebanon dinnan, na'ima ta cigaba "ita..jiya ta tambayeni ko zan amince mu hada study group da ita akan dissertation din" Nafisa tace "dama bakida writing buddy kedin" Na'ima ta gyada kai tace "I thought zan iya ne, kuma naga yamin wahala sosai yanzu" Nafisa tadan jijjaga kai tace "kinada matsala Na'ima, ai dole sai kin samu group mates daman a irin situation haka, yanzu me kikacewa zaran" na'ima ta amsa da "na amince ai tun jiyan tace zamu rinqa ware lokacin shiga school din" nafisa tace "hakan yafi ai, namu fa study group din munkai takwas" Na'ima ta juya ta cigaba da typing tace "naku da maza ai naganku ranan" dariya nafisa tayi tace "ke kuma sune abun gudunki, sis many men don't bite" Na'ima batace komai ba ta cigaba da aikin gabanta..
Ranan wata talata bayan sun gama baccinsu da hidimominsu nafisa ta jasu suka tafi shopping abubuwansu da sukayi qasa, sai da sukayi sallahn la'asar sannan suka shirya suka tafi, kaya suka siyo dayawa na abinci dana qananun buqatunsu, bayan sun gama jera kayayyakin a kitchen suka fito na'ima ta zauna nan kujera ta fara ware kayan toiletries din nasu da na skin cares din, Nafisa ta ciro wayanta tafara dannawa, shiganta cikin IG taga saqo a DM dinta dauke da sunan da ko cikin magagin bacci zata gane waye, dan gyara zama tayi daga zaunen ta dan dago ta kalli Na'ima da hankalinta ke kan duba kayayyakin gabanta bata dago ba, miqewa Nafisa tayi ta shige dakinta ta rufo qofan
Sake kallon message din tayi me dauke da rubutu kamar haka
Bilal Dabo: Saqo na ke son ki isar wa kawarki, tunda alamu sun nuna batasan ma'anan space dinda na bata ba and she's taking it too far, Tell her "it is not Over until i said so" ta dawo da kafarta , karta bari inzo daukanta dan lamarin bazai mana dadi ba, AUREn mu kuma na maidashi....
Saboda wasu dalilai ne kawai yasa nafisa bata maida masa da amsan zagi ba, dan ko jahili yasan auren da ya mutu kusan wata goma baya, bazai maidu ba sama taka, sanin cewa ko weed dince ta motsa masa yasa nafisa qin maida masa martani,
Atake kuma Nafisa taji duk wani
k
uzari na jikinta ya bace, bata san ma me zata fara tunani ba, a wannan lokacin kuma babu abunda take tunani irin kwanciyar hankalina Na'ima, she can't know of this and there's no way she's telling Mami saboda tsaf zata iya aiko Faruk yayi wasu cike cike a school ya koma mata da Na'ima saboda nutsuwan Na'ima yafi komai wajenta, ji tayi jikinta yayi sanyi tafara safa da marwa a dakin abubuwa dayawa suna dawo mata, in ta tuna ranar da Na'ima tazo gurinta da dare zuciyanta qara karyewa yake, ji tayi hawaye na kawowa idonta..
Tana nan tsaye a dakin ta kasa zama Naima ta shigo hannunta riqe da laundry basket zata debi kayan Nafisan dazata wanke mata, juyowa Nafisa tayi suka hada ido a take Nafisa taji zuciyanta ya kuma karye wa, ta daure tace "har kin gama ware kayan" Na'ima dake dan lura da yanayinta ta jijjaga kai tace "Eh ga naki ma" gyada kai Nafisa tayi ta juya a sanyaye ta zauna bakin gado tana dan kallon Na'iman, wuceta Na'ima tayi ta qarasa gurin madubi ta debo wasu mayuka daga cikin basket din tafara jerawa sannan ta wuce toilet takai sauran, dawowa tayi gaban wardrobe din nafisan ta bude zata debi kaya, ajiye basket din tayi tafara duba kayan, saikuma tajuyo a nutse tace da nafisan "akwai wasu kaya dana ware anan Ina kika kaisu kuma"
Nafisa tace "kamar yana qasa ai" duqawa tayi ta fara bincikawa nan qasan tana mita "haba nafee nafa waresu ne zan wanke kika hadesu guri daya da masu kyau" qunquni takeyi nafisa na kallonta tana dan murmushi mai ciwo, aranta tana ayyana how kind and innocent Na'ima is, Allah kuma ya jarabceta da wasu irin mutane zagaye da ita sukayi amfani da shirunta da kuma haqurinta wajen cutar da ita.
Inaaa...ai bazata taba bari Bilal ya samu haduwa da Na'ima a qasar nan ba, dan guntun nutsuwan da suka samu Na'ima tadawo cikinsa duk zai wargaza komai, ya kuma hanata karatunta da yazama saura kadan ta gama,
Miqewa Na'ima tayi bayan ta gama zuba kayan a basket ta kalli nafisa, sai ta samu kanta da tsayawa tana nazarinta tace "nafee meya faru ne?" Saurin jijjaga kai nafisa tayi tace "babu komai, me kika gani?" Na'ima ta matso kusada ita ta ajiye basket ta zauna tace "naganki kinyi sanyi ne all of a sudden, Dan Allah me ya sameki?" dariyan qarfin hali nafisan tayi tace "gani uwar surutu kullum, kawai kaina ke ciwo" Na'ima tace "Ayya sannu", daukan basket din tayi ta fice Nafisa na kallonta, tashi tayi ta rufe kofan sannan ta qara daukan wayan tafara dialing numbern anty Amnahn..
Bayan ta dauka suka gaisa nafisa ta fara mata bayanin saqon da tagani a wayanta, dayake anty Amnah tasan almost everything gameda Na'iman yasa ta fahimta, itama tace kada Nafisan ta kira Mamin dan sai hankalinta yafi na Na'ima tashi,
Na'ima ce ta dawo dakin dauke da maganin ciwon kai da ruwa ta balla ta miqawa nafisan, karba tayi amma bata sha ba sai tace "sis tunda bama shiga school din yanzu, why not mu koma gidan anty Amnah toh" dan hararanta Na'ima tayi tace "keda kike mitan gajiyan zuwa shine kuma all of a sudden zakice muje" Nafisa tace "ji nake kaman banida lafiya ne sis, kafin yayi nisa gwara muje ta dubani" Na'ima ta dan bata fuska tace "to ki bari mana kigani, may be ma stress din fitan nan da mukayi ne" ganin kamar ba yarda zatayi ba yasa Nafisan gyada kai tace "toh shikenan" ta juya ta kwanta Na'ima ta miqe ta dauki qaramin blanket din gadon ta lullaba mata tace "sannu" sannan ta fice daga dakin.
Ranan anan dakin kusada Nafisan ita Na'iman ta kwana, Nafee sai tunanin uzurin da zata bullo dashi take, wanda zai sa Na'ima ta yarda su koma gidan anty Amnah in yaso sai su rinqa zuwa school din daga can din jefi jefi tunda ba wani activities suke gudanar wa a school din ba yanzu.
Washegari ma Nafisa qin fita tayi suyi breakfast sai Na'iman ce ta biyota dashi nan dakin tana mata sannu, kadan nafisa taci abincin tayi wani laushin qarya duk acikin batada lafiyan, ita kuwa baiwar Allah Na'ima sai hankalinta yafara tashi kuma tace "sis ko zamu je asibiti to" Nafisa tadan koma ta kwanta tace "a'a kam, ai nadan fara Jin dama dama" shiru Na'ima tayi batace komai ba....
Yammacin ranan Na'ima na zaune anan falon aka danna musu door bell, dan tsayawa tayi da duba wani takarda dake hannunta tana son qara tabbatar da kofan su ne ake dannawan kuwa, qara ringing din akayi kafin ta miqe sai ga Nafisa ta fito daga dakinta cikin sauri ta nufi qofan kamar zata fadi, binta da kallon Na'ima tayi tana dan mamakin firgicin nata itama ta miqe, ganin Nafisan tayi nan bakin kofan bata bude ba tana leqa peephole din jikin kofan, tace "nafisa waye ne?" Juyowa Nafisa tayi kamar mara gaskiya tace "order nayi mana na pizza sai na zata mai delivery dinne ya qaraso" Na'ima na kallonta ta gyada kai tace "toh bude mana muga waye" budewa nafisan tayi sukaga ashe Lauren ce , hugging din juna sukayi itada Nafisa cikin fara'a suka wuce ciki Na'ima tabi bayansu, Zama tayi nan gurinsu a falo bayan sun kawo mata abun sha..
Nan Lauren tafara zuba musu surutu, itadai nafisa tanason ta zage suyi hiran dayake kawar surutun ta ce amma babu hali saboda tayi qaryan rashin lafiya, ga Na'ima kuma zaune gurinsu itama, sai kawai ta rinqa amsawa sama sama har se da Lauren din ta tambayeta ko lafiyan ta, Na'ima ce ta amsa da "she's sick"...
Sai dare lauren ta tafi, bayan tafiyanta nafisa ta koma daki ta kwanta, abinci Na'ima ta dafa musu bayan ta gama ta debi na nafisan ta bita dakinta dashi, duqe ta sameta ajikin gado, dasauri Na'ima ta ajiye abincin ta qarasa gurinta ta dagota tana tambayanta "meya faru" nafisa ta amsa da "amai nayi sis", sannu ta fara mata saita dagata ta zaunar da ita akan gadon cikin damuwa tace "sis bari in fara hada mana kayan mu mukoma gurin anty Amnah din gobe, this is getting worse, sannu" gyada kai Nafisa tayi tanajin dadi aranta, dama abunda takeso kenan.
Kayan Nafisan tafara hadawa cikin babban akwati sannan ta wuce dakinta dan hada nata kayan itama, bayan ta gama tace da Nafisa "yanzu yaya zamuyi sis, ko bus zamu hau, dan kinga ni hannu na bai fada sosai ba a driving din, kuma kema babu lafiya" Nafisa tace "nakira yaya Ahmad yanzu yace yana gari, zaizo ya kaimu goben" Na'ima tadan bata rai tace "baga bus ko train ba nafisa" Nafisa tace "sis gwara dai shidin yakaimu" shiru Na'ima tayi tanajin wani iri, tarasa ma ita fushi zuciyanta keyi dashi ko kuma son ganinsa takeyi oho..... dan har yanzu bata manta da maganganun data kyaba masa ba ranan, ta kuma quduri niyyan zata bashi hakuri akan hakan.
Ranan ma sake kwana Na'ima tayi a dakin nafisan washegari bayan sunyi sallah da sassafen ta fara tattare gidan, kayan abincin da suka siyo jiyan ta ware wanda tasan zasu baci ta maidasu leda zasu tafi dasu can gidan anty Amnahn, bayan ta gama tayi wanka ta gyara gashinta into dough ta shirya cikin wani sky blue din abaya tayi rolling gyalen, lip balm ta shafa dasu mascara sai kuma ta tsaya kallon kanta a madubin, aranta tana dariyan meyasa take saka effort gurin kwalliya kuma, tananan tsaye tajiyo door bell dinsu yayi qara...
Bintu Musa ce ✍️📚
ArewaPen @Bintu Musa
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
ArewaPen https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 18
Goge lip balm din Na'ima tayi tana kallon kanta a madubin, ta koma gurin wardrobe dinta ta cire kayan jikintan sannan ta nemo dogon jalbab maroon tasaka, dan zama tayi bakin gado bata fita daga dakin ba tajiyo fitan Nafisa zata bude kofan
Saida taji shigowan Ahmad sun gaisa da nafisan ya tambayeta ya jikin sannan ta bude kofan ta fito a nutse, bata kallesa ba tace "Ina kwana" taji ya amsa ya kuma cewa "hope kun shirya" Nafisa tace "Eh yaya bari mu dauko kayan", bin bayan Nafisan itama Na'ima tayi suka fara dauko na Nafisan tace "ki bari sis in fitar, jikin ki babu karfi" ta qarasa ta dauko akwatin suka fice, ahaka suka fitar da kayan Ahmad na tayasu, sai kallon Na'ima yake zuciyarsa na muradin su hada ido ganin taqi kallonsa kwata kwata..
Fitansu waje Nafisa ta ware ido ta tana kallon motan dayazo da ita wata sport wrangler jeep baqa, wuce su Ahmad din tayi ta qarasa gaban motan tace "yaya this car is fire" dan murmushi Ahmad din yayi suka qarasa gurin motan shida Na'ima da itama sai kallon motan take, yace da Nafisa "bakida lafiya da kinyi driving dinmu ai" juyowa Nafisa tayi ta kalli Na'ima da suka hada ido tace "hakane yaya, amma naji sauqi sosai ai yau din" ta qarasa maganan ta yin mita aranta tayi qarya kuma abun ya dameta yanzu ga ci ga rashi, zagayawa bayan motan Ahmad yayi ya fara saka musu kayan nasu yana cewa "sai kinji sauqi sosai tukunna" nafisa ta dan turo baki ta bude back seat zata shiga Na'ima tayi saurin riqe hannunta tayi qan qan da murya tace "nafee ki shiga gaban mana" Nafisa tana danne dariyanta tace "zan kwanta ne ai, jikina yana ciwo" da haka ta bude ta shiga ta bar Na'ima nan tsaye bata shiga motan ba, Ahmad ya qaraso wajenta bayan ya gama saka kayan, a hankali yace mata "ko zakiyi driving din?" Na'ima ta kauda kai cikin sanyin murya tace "ban iya ba" shidai kawai kallonta yake ganin kamar kyau ma ta qara yi cikin kwanaki dayawan da bai ganta ba, ganin bazata juyo da kanta ba yasa ya bude mata front seat din ya tsaya yana jiran ta shiga, Nafisa na kallonsu ta cikin motan sai murmushi take lamarin nasu na sata nishadi, aranta tana ayyanawa wato "mutune biyu ne marasa yawan magana suka hadu guri daya sai ake gudanar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 19