da lantana, girki sukayi bayan sun gama na'ima ta wuce dakin Mami ta debo kayan ta na laundry sannan ta shiga dakin nafisa ta debo nata ta wanke su tas a washing machine
Har dakin Abubakar ta shiga dake nan falon downstairs ta gyara masa ko ina, she kept herself busy sunata hira da lantana.
Sai dare faruk yadawo dasu Mamin, sun shigo lokacin tana salla a dakinta bayan ta idar ne ta tafi wurinsu nan falon Mami, shiganta dakin Mami tace "habibti ya zaman shiru" ta shigo ta zauna gefen mamin tace "sannu da dawowa Mami"
Mami ta amsa da yauwa, nafisa dake gefe akan kujera itada faruk bayan ta chanja kaya, tace "Husna tace in bakije ba gobe dakanta zatazo daukanki" faruk yayi murmushi yace "meyayi zafi, kamar abun dole" ya kalli Na'ima yace "habibtin Mami kiyi zamanki ma in goben bakyason zuwan" na'ima tayi murmushi tace "toh yaya" ta qarasa maganan tana dan ware Ido ma nafisan alamun "to dai kinji" Nafisa tace "wallahi baki isa ba sai kinje, in ban ciccibeki nakaiki ba" Mami da faruk sukayi yar dariya Mami tace "to fah" ta juya tana kallon Na'ima tace "Habibti kinci abinci dai ko" na'ima na dariyan nafisan ta gyada kai tace "Eh Mami, akwai naku a dining ko a kawo muku nan" Mami tace "barshi mu huta tukunna"
Faruk sai kallon Na'ima yake ganin she was openly herself these days, harda tsokala wanda a farkon zuwanta gidan she can go days batayi murmushi ba.
Ranan ba'ayi hira falon Abba ba, kowa ya tafi makwancinsa da wuri a huta gajiya.
Washegari da sassafen Mami ta tafi gidan bikin ta barsu suna bacci, na'ima bata tashi ba sai almost nine shima yunwa ce ta tada ita ta sauqa yin breakfast cikin purple color din kayan bacci Mai laushi kamar cutton a jikinta, hulanta yayi baya kwantaccen gashin goshinta duk a waje, kitchen ta shiga, tana tsaye bakin fridge nafisa ta shigo itama da kayan baccin tana miqa alamun tashinta kenan, zuba madara na'ima tayi a cup ta miqa mata, nafisa ta karba tana kaiwa baki tace "yaushe zamu shirya mutafi,husna called me" Na'ima tayi hanyar fita daga kichen din hannunta riqe da kofin madaran tana cewa "nafee mu dan bari anjima mana,it's so early" nafisa ta bita suka fita tace "kinsan fa zamuje wurin makeup dinnan" zama sukayi a nan dining zasuci abincin.
Basuyi nisa da fara cin abincin ba faruk yashigo, on a normal circumstances na'ima ba wani damuwa tayi ba dan babu hijab a jikinta sanin cewa tana zama da normal kaya ko a gabansa dan kamar yaya na jini ta dauki faruk kuma shima bai damu ba, Amma ganin wanda ke biye dashine yasa ta daskare a wurin takasa kai cokalin abincin bakin ta aranta tana cewa "yau kuma me wannan mutumin yazoyi da safe haka" because tunda ta fara rayuwa a gidan bata taba ganinsa ba sai kwanannan.
Qarasowa dining din Ahmad yayi yana dan kauda idonshi daga kallonta ganin yanayin kayan jikinta.
Sanye Ahmad yake cikin white polo shirt da blue jean shima in a casual way, ganinsu yasa nafisa cewa "Yaya,good morning" Ahmad ya zauna yace "nafisa,kin tashi lafiya" nafisa ta amsa tareda gaisheda faruk sannan ta miqe ta fara serving dinsu abincin, Na'ima ta ajiye cokalin tadan fara gyara hulanta da jelan gashin yaqi komawa duka tace "Ina kwananku" faruk dake kallonta ganin how cute she looks, yace "lafiya na'ima,I thought kun tafi gidan bikin fa" na'ima tadan jijjaga kai tace "sai anjima" Ahmad ya kasa jurewa saida ya dago ya kalleta, na'ima taqi kallon gefensa, murmushinsa na yau saida yadan bayyana ganin still dai she can't look at him kuma baisan meyasa ba yake bidan ta kalleshin .
Hira sukeyi sama sama suna cin abincin, nafisa tace "yaya anan ka kwana ne?" Ya dan jijjaga kai hankalinsa na kan abincin dayake ci kadan kadan,yace "A'a can gidana na kwana" faruk yace "gidan baba is crowded i don't know how yaya Adam is cooping" Ahmad ya dan gyada kafada yace "wannan jama'a basa damun baccinsa ai" nafisa da faruk suka danyi dariya
Na'ima dake jinta so uncomfortable under his Eyes yasa tun dazun idonta ke kan plate din gabanta bata dago ba aranta tana ayyana meyasa wannan bawan Allahn ke sa mata rashin nutsuwa ne, samun kanta tayi da dan dagowa tana kallon hannunsa hoton rannan da nafisa ta nuna mata yana fado mata arai.
Koda su na'iman suka gama bata tashi ba har seda Ahmad ya tashi suka nufi falon Abba sannan ta miqe tafara taya nafisa tattare wajen.
Bayan sunyi wanka suke shirya cikin simple attire, nafisa ta saka musu kayansu cikin bag suka wuce gurin makeup din.
Sunyi kyau sosai bayan angama make up din barinma na'ima kamar ka sace ta, ankon daya kasance na leshin ba qaramin haskata yayi ba.
Isarsu gidan bikin bayan sun gaisa da mutanen da suka idda a main falon gidan suka wuce part din mamma dan nafisa tasan acan zasu Sami Mami, aikuwa ta na zaune tareda wasu yan'uwansu manyan mata, bayan sun gaisa dasu, nafisa ta jasu dakin Salma
'yan mata suka samu a dakin kowacce na yauqin ta isa, husna da salma basa dakin,Laila da qawayenta sun hakimce kan gadon salman, nafisa tace "sannunku..Laila Ina husna?" Laila ta amsa dakyar "bansani ba" Zama sukayin kan tsabtacaccen carpet din dake shimfide a dakin, na'ima daman bata kulasu ba tayi zamanta ko kallonsu batayi ba.
Laila ta kallate sannan tace da nafisa "yar zaman gidan naku bata tafi ba kenan" Nafisa ta juyo tana dan hararanta Lailan tace "bangane ba, what do you mean?" Laila ta kyabe baki tace "wannan ta kusa da ke din" Nafisa tace "first of all sunanta Na'ima and secondly, I'm in good spirits yau dinnan Laila karki batamin rai dan banida lokacinki" kafin Lailan ta amsa luba tace "Ha'a taga bare a cikinku ai dole tayi magana" Nafisa tace "sannu lubabatu, sannu 'yar'uwarmu ta jini, kinga idan ina magana ta hankali ki daina tsomamun baki, ke asuwa?" sanin masifan nafisa yasa luba juyawa tana tsuka me qarfi, cike da tsiwa Laila tace "An fada din bare, dan wannan farin nata ba ta inda kuka hada jini da ita" Nafisa ta miqe Na'ima tayi saurin riqo gyalenta, ranta ya sosu da wannan maganar da suka fada har hakan saida ya nuna akan fuskanta tace da nafisa "Mu fita nafee" ganin yanda bacin ranta ya fito fili yasa nafisa batayi musu ba ta jira miqewan na'ima sukayi hanyar fita daga dakin,'yan matan dakin da suka tsaya kallon drama suka bisu da kallo, Laila tayi tsuka tace "gwara ku fitan dan nima banida lokacinku" wata qawarsu tace "to ke Laila me farar yarinyar ta miki?" Laila ta kalleta a fusace tace "babu ruwanki"
Haka na'ima tayi wunin gidan bikin ranta duk babu dadi dan nafisa ta zage itada husna sai bidirinsu sukeyi, na'ima ta qi binsu haraban gidan da ake taro ta na zaune a main falon gidan riqe da yarinyar anty Fatima immediate sistern Ahmad, sai wasa yarinyar take da dankunnen na'iman.
Bayan ankai amarya dasu gidanta dake cikin wata shahararriyar unguwa nan Abujan, suna zaune cikin Mini falon amaryan na'ima tace "nafisa ki tashi mu tafi" husna tace "A'a ku bari ango suzo mana" Na'ima tadan bata rai sai kuma a hankali tace "har sai mun jirasu?" kafin husna tayi magana Nafisa tace da husna "kinsan jaraban na'ima kuwa, muje naji anty Amnah tace zasu tafi yanzu dan har ta kira za'a zo daukansu" Miqewa na'ima tayi Jin haka dan duk a taqure take a gidan gashi ta gaji, gurin su anty Amnah nafisa ta kaita, anty amnah tace "gaskiyarki na'ima bari mutafi tare, barsu su gama rawan kansu" nafisa tayi dariya tace da na'ima "to sai na dawo"
Sunanan zaune aka kira anty Amnah, bayan tagama magana dana dayan bangaren ta kashe tace "tashi muje na'ima mai daukanmu yazo" ta qarasa tana fadawa wata mace dake gefenta, miqewa sukayi anty Amnah ta sake cewa bari muyi sallama da amarya suka wuce upstairs, Hanyan waje na'ima tayi akan zata jirasu can gurin motan, fitanta ta hango wata black mota a haraban gidan ga light dinta a kunne, qarasawa tayi tadan tsaya ba daf da motan ba, nacikin motan ya bude ya fito yana kallonta, dan riqe numfashinta tayi kadan ganin Ahmad.
Bintu Musa ce ✍️📚
ArewaPen @Bintu Musa
ArewaPen
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 13
Rufe cab din motan Ahmad yayi bayan ya fito, ya jingina jikin motan hannuwansa cikin aljihun kayan jiikinsa yana kallonta, kauda kai na'ima tayi daga kallonsa Jin zuciyar ta tafara bugawa kamar yanda takeyi aduk lokacin da suka hadu, dan sunkuyar da kansa yayi yana dan murmushi sannan ya dago ya cigaba da kallonta baya ko kifta ido, sunanan tsaye babu me magana ya dan gyara tsayuwa zai fara takawa gurinta Laila ta fito daga gidan, Ahmad ya dauke kai daga kallon Na'ima ya kalli lailan, tuni ya dinke fuskanshi kamar bashi yake murmushi yanzu ba, tunkarosa Laila tayi, tadanyi wani irin kallo a na'ima sannan ta qarasa wajensa tana murmushi kamar bakin ta zai yanke tace "yaya..Ashe kazo, Ina wuni" babu yabo babu fallasa yace "Lafiya" Laila tace "ko inzo mu koma gidan tare" Ahmad yadan kalleta yace "tare mukazo ne?" Laila batasan lokacin da ta juya ta kalli Na'ima data juya kanta ba, ta sake juyawa tana kallon Ahmad tanajin kunyan tsinka ta dayayi a gaban na'iman, ta sake cewa "kaiii yaya" coldly Ahmad yace "su anty Amnah nazo dauka" kafin ta amsa sai ga anty Amnah ta fito daga gidan itada wasu wata guda biyu, qarasowa sukayi gurin motan daya daga cikin matan tace "Laila kema dake zamu koma kenan" Anty Amnah ta riga Laila amsawa da "a'a haba dai, ai salma bazata ji dadi ba, bayan ga 'yan uwanta can suma suna jiran ango da abokansa" matar tace "Gaskiya dai, ki jira abokan angon suzo su maidaku tukun" Shidai Ahmad tuni ya bude motan ya shiga, Laila ta matsa zasu bude kofan motan, anty Amnah ta juya ta kalli Na'ima dake Shirin shiga back seat tace "zo na'ima ki shiga gaba, mu saimu shiga bayan" Na'ima ba don ranta yaso ba ta bude gaban motan tashiga, Laila sai hararanta na'ima jin kamar ta maketa.
Shigan na'ima cikin motan qamshin turaren Ahmad mai sanyi wanda ya rikide dana motan ya bugeta, Jin proximity dinsu yayi kusa yasa ta Jin kamar ta fice daga motan amma haka ta dake idanunta na kallon gabanta, Ahmad yatada motan suka wuce aka bar Laila nan tsaye kaman ta fashe....
Na'ima tayi shiru kamar bata cikin motan, su anty Amnah sai hiransu suke, sunyi nisa anty Amnah tace "Habibtin mami yaushe hutun naku zai qare" cikin nutsuwa da sanyinta daya zame mata jiki na'ima ta amsa da "next week in Sha Allah anty" Anty Amnah tace "mu zuwa Monday zamu koma gaskiya" daya daga cikin matan tace "itama a England din take ne?"
Anty Amnah ta amsa da "Eh suna makaranta acan tareda nafisa, yarinyar Mami ce itama" matan suka amsa da "ma Sha Allah...Allah ya taimaka" ciki ciki na'ima ta amsa da Amin, Ahmad yadan juyo ya kalleta.
Isarsu gidan Mamin sun fito dukansu Anty Amnah ke tambayan na'ima "Anan zaki kwana ne kema" Na'ima ta dan jijjaga kai tace "yaya faruk zaizo mu wuce, zan dauki jakan mu a dakin husna ne" Anty tace "toh"
Wuce su tayi tabarsu nan suna magana da Ahmad din daya fito shima ya tsaya.
Shigarta falon ta tadda mamma ta fito daga kitchen din dake nan downstairs hannunta riqe da wasu ledoji, na'ima ta qarasa zata tayata riqe wasu, mamma tace "No, kibarshi daughter i can manage" duk da haka saida ta karba suka fara tafiya zasu wuce upstairs su anty Amnah suka shigo, mamma tace "kun dawo" a gajiye su anty Amnah suka zube akan kujera nan falon tace "mun dawo mamma, Ahmad ne yakawomu, kinganshi can waje wai bazai shigo ba da mutane gidan" murmushi mamma tayi tace "nima sai asuba yake shigomin tunda aka fara hidiman bikin nan" ta qarasa magana ta na maida hankali kan Na'ima dake tsaye tana jiran su gama magana tace "muje daughter", Sai da na'ima ta taya mamma ajiye ledojin inda yakamata sannan ta wuce dakin husna dauko jakarsu, wasu 'yammata tasamu a dakin kwance kan gadon kowacce na danna waya, dagowa sukayi suna kallonta
Na'ima ta wuce gurin wardrobe din husna ta dauko kayan nasu ko kallon gefen 'yammatan batayi ba, daya daga cikinsu tace "kema a garin nan kike ne?" Na'ima tace "Eh" suka sake tambayanta "ke yar'uwar su nafisa ce?" wannan karon gyada kai kawai na'ima tayi ta fice daga dakin aranta tana mitan "kamar ita kadai ce aka gani baquwar fuska a taron bikin, sai tambaya ake mata kaman wadda taje gidan jarida"
Tana sauqa stairs kiran faruk ya shigo wayanta ta dauka, daga dayan bangaren yace "Na'ima kinanan gidan Baban ne?" tace "Eh yaya" yace "to ki fito compound ki jirani ganinan na kusa qarasowa" ta amsa da "toh" sannan ta qarasa sauka tayi sallama da su anty Amnah dake nan falon basu tashi ba..
Fitanta wajen taganshi tsaye jikin motan hannunsa daya cikin aljihu dayan kuma yana danna wayanshi, Jin takun mutum yasashi dagowa ya kalleta
Na'ima tadanyi stiff a tsaye ganin Ahmad aranta tana tunanin "daman bai tafi ba"
Gyara tsayuwa yayi yana kallonta yace "Let me drop you" Na'ima bata bashi amsa ba ta tsaya kallonsa, sai da taga ya bude front seat sannan tace "daman yaya faruk yace...uh..uh..munyi waya.." Zuba mata idanu Ahmad yayi batasan lokacin da tafara tako wa gurinsa ba, miqa hannu yayi ya karbi jakan ta sake masa, ya zagaya ya saka a booth sannan ya dawo wajenta ya jira ta shiga motan ya rufe mata kofan sannan ya shiga driver seat.
Sun fito daga street din gidan Baban na'ima ta hango motan faruk zai shiga street din shikuma, juyawa tayi ta kalli Ahmad da hankalinsa na ga tuqinsa, dan juyowa yayi, tayi saurin kauda kanta..Saida sukayi nisa na'ima taji yace "Did i got something on my face?" Na'ima tadan juyo batareda ta kalli fuskansa tace "Na'am?" parking motan yayi a gefen street, na'ima batason lokacin da tadan ware idanu ta juya ta kalleshin ba, hada idanu sukayi yadan duqo kanshi kusada ita yana kallonta, na'ima jitayi isakan motan ya mata kadan kamar ta bude motan ta fice.. Ahmad yayi qasa da murya yace "meyasa bakyason kallona?" Na'ima ta kauda kanta tana kallon titi bata amsa ba, ji take muryanshi na karya duk wasu gabobi na jikinta, ya sake yin qasa da murya yace "Look at me Na'eemah" tadan juyo bata kalleshin ba cikin sanyin murya tace "meyasa zan kalleka" still yana kallonta shima cikin sanyin murya yace "because i want to see your eyes" batasan lokacin da ta juya kanta tana kallon window ba tana dan murmushi, shima murmushin yayi yace "Na'eemah kin maida ni sirikinki ko" ta jijjaga kanta tana cigaba da murmushin, shidai Ahmad duk ya lalace wajen kallonta, baisan meyasa yarinyar nan takeda effect me karfi akansa ba, ganin ba kallonsan zatayi ba yasa ya tada motan yace "shikenan, I'll have to try harder"
Babu wanda ya sake cewa komai a cikin su,Ahmad yana driving din jefi jefi zai juya ya kalli Na'ima da har yanzu kallon window take, amma zuciyoyinsu are aware of each other, wani irin yanayi suke shiga dukansu biyun aduk lokacin da sukayi gamo da juna and it seems like zuciyarsu kowannensu is reaching out to one another.
Bayan Ahmad yayi parking a kofar gidan Daddyn, na'ima ta bude qofan zata fita taji muryasa cikin sanyi yace "Gidan anty Amnah kuke zama a England din?" Na'ima ta dan juyo tace "a Oxford muke" ya sake cewa "when are you going back?" Na'ima tadan dago ta kalleshi kadan tace "sai next week thursday" bata jira Jin abunda zaice ba ta bude kofan ta fice, fita Ahmad yayi ya zagaya booth yaciro mata jakan sannan ya qaraso gabanta ya miqa mata, karba na'ima tayi cikin sanyinta tace "thanks for the lift" ya dan gyada kai yace "Take of yourself Okay" Na'ima ta gyada kai alaman toh sannan ta juya ta shige gate din gidan yana binta da kallo
Shigan ta falon ta samu Mami da samarin gidan suna hira, Mami tace "Sannu habibti, kun dawo?" Na'ima ta qarasa ta zauna kujeran kusada Mami tace "Eh Mami" Mami tace "Faruk dinne ya dawo daku?, don daga nan ya fita zaije daukoku " Na'ima tace "A'a..yaya Ahmad ne" Mami tace "ya kyauta kuwa, shine bai shigo" Na'ima batace komai ba, Abubakar yace "Ina anty nafisan" Na'ima tace "Su zasu jira abokan ango" dan dariya sukayi Al'ameen yace "ai abokan angon ma sun shigo uku a hannun su anty nafisa" Mami tadan kada kai tana dan dariyan itama tace "ai baby sai godiyan Allah" Abubakar yace "anty nafisa ba sauqi, sai sunjira sunyi cash out tukunna, suyi draining abokan angon tas" suka sake kwashewa da dariya shida Al'ameen, na'ima na kallonsu tana murmushi ta jijjaga kai tace "wannan maganan kamar a kunnenta" Abubakar yadan ware idanu yace "haba anty" Al'ameen bai fasa dariyan ba, Mami tace "rabu dasu, kije ki dan watsa ruwa ki huta tukunna" amsawa na'ima tayi da "toh" sannan ta miqe tana daukan jakarsu ta nufi upstairs
Shiganta dakin ta jefa jakan akan gado tacire veil dinta sannan ta danyi qaramin tsalle ta kife akan gadon tana sauke numfashin gajiya, tunanin moment dinta da Ahmad tafara, his eyes..his voice... Ta tambayi kanta, why is she luring herself into another trap? as if her past didn't teach her enough to stay way from any man, gamuwanta dashi baifi 'yan satittika ba, amma why is her heart reaching out to him aduk lokacin da suka gamu...yakamata ta farka daga wannan mafarkin da ta fara, ya kamata ta gina katanga tsakaninta da Ahmad don this is not the right time for it.
Tananan kwance taji anfara knocking door din dakin nata, miqewa tayi ta bude, Ido hudu sukayi da Faruk dake kallonta yace "Na'ima naje daukoki anty Amnah tace kin fita kina jirana kuma banganki ba" Na'ima ta dan kauda idonta daga kallonsa tace "Eh nafito...uhm..shine yaya ya dawo dani" yana kallonta yace "wani yayan?" tace "yaya Ahmad" kallonta yayi baice komai ba, Jin shiru yasa Na'ima dagowa ta kalleshi, ya kauda idonsa yace "Okay, saida safe" ta amsa da "toh" ta mayar da qofan ga rufe
Wanka tayi ta saka doguwan riga na cutton mara nauyi ta fice downstairs don neman abunda zataci, su Mamin still tasamu a falon suna hira Mami tace "Habibti ga abinci can na ajiye muku a kitchen" Na'ima ta amsa da "toh" ta wuce kitchen ta debo abinci tadawo tazauna nan aka cigaba da hiran da ita, sunanan zaune faruk ya sake shigowa shima ya samu wuri ya zauna, tambayansa na'ima tayi ko zata kawo masa abincin yace "Eh" ta miqe ta je ta debo masa shima, Abba ne yashigo falon yace "yau kunyiwa falona yaji kenan" sukayi dariya gabadaya, yasamu guri ya zauna aka cigaba da hiran dashi.
Sai qarfe tara nafisa suka shigo gidan itada husna, duk mutan falon suka dago kai suna kallonsu, qarasowa sukayi a gajiye nafisa ta zube kusada Mami, Al'ameen yace "sannu uwar bikin gaba daya" sukayi dariya, Abba yace "'yar'uwarku tadawo tundazu shine bazaku biyota ku dawo baki daya ba, me kuka tsayayi can gidan salman daren nan?" Nafisa ta marairaice tace "Abba itafa na'ima cewa tayi bazata jira rakiyan abokan angon ba" Abba yace "menene shidin?" Abubakar yace "charges dinsu suka tsaya karba Abba" Al'ameen ya buge masa kafada suna dan dariya, nafisa ta juya tana hararansu, na'ima dai jijjaga kai tayi tana murmushi, Husa tace "Abba daman ana jiran abokan ango suzo sai su maida kawayen amaryan gida" Abba ya sake cewa "to from henceforth, banason ku sake yin dare haka a ko'ina" suka amsa da "Toh Abba" Husna ta miqe tace "Mami akwai abinci" Mami tace "kije gashican a kitchen din" Nan suka zauna cin abincin nafisan da husna sukayi ta fayyacen yanda suka wanki abokan angon millions, Na'ima na mamakin yanda wasu basa jin nauyin cire kudi a familyn su nafisan.
A daren na'ima tazo kwanciya su nafisan suka shigo dakinta, hayewa kan gadonta sukayi nafisa nacewa "Bobo wani abu ya sake hadoki da Laila ne" Naima ta miqe zaune ta jingina jikin fuskan gadon tace "nafee me ya taba hadoni da ita nikuma" Husna tace "ke madai nafisa kinsan wannan
yarinya mara setin ko ba'a mata abu ba haka take" na'ima tace "wani abu ya faru ne?" Nafisa tace "babu komai"
Bintu Musa ce ✍️📚
ArewaPen
https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
✨ KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 14
Dan gajeran hutun su na'ima yaqare suka fara shirye shiryen komawa makaranta, duk wani abu da zasu buqata 'yan qananu qananu na amfanin yau da kullum Mami ta hada musu, bawani shopping sukayi ba don acan din babu abunda suka rasa.
Dawowar da na'ima taji bataso sai akasin hakan ya faru, batayi tsammanin zuwanta gidan zai saka mata nutsuwa mai tarin yawa ba wanda har zataji batason komawa England , sai dai tasani komawanta school din yazama dole shiyasa ta ke ture iren iren tunanin daga ranta.
Zaune suke a main falon gidan da yamma, na'ima dake cikin boubou mara nauyi tana zaune gefen Mami nan zaune kan carpet tana tayata ware wasu kaya a leda da mamin ta aiki driver ya siyo safiyar ranan, Mami ta ciro wani expensive air freshener ta miqawa na'ima tace "Habibti sa muku wannan cikin kayanku zai muku amfani" karba na'ima tayi tace "toh" ta ajiyeshi gefenta a kan carpet, nafisa ta dan dago daga kwancen datake kan kujera tace "Mami duk munadasu fa" Mami ta kalleta tace "wai da nace ku qara akan nakun" Nafisa ta miqe zaune tace "Mami kayan zasu mana yawa fa" Mami ta juya gun na'ima tace "Habibti barshi toh" Na'ima tace "A'a Mami munaso, mungode" Mami tace "to kekadai zaki rinqa amfani dashi kar naji kin bata, tunda ita ba'a mata gwaninta" Nafisa ta fara dariya tace "kiyi hakuri Mami" Mami tace "ke kika sani, yauwa nasa lantana ta siyo muku kuka da busasshen kubewa sannan ta hado da daddawa mai dadi dan nacan basa sarrafashi me kyau" bude baki nafisa tayi saura kadan na'ima ta kwashe da dariya ta dan kauda kanta tayi tana murmushi, Nafisa tace "Mami daddawa fa..wallahi warinsa duk cikin jirgin nan sai kowa yaji" Mami tadan tsaya kallon nafisa, dan turo baki nafisa tayi alamun shagwaba ta koma ta kwanta akan kujera tana gyara skin face mask dinda ta saka, Mami ta juya ta kalli Na'ima tace "bakwayin tuwo ne Na'ima?" Na'ima tayi saurin jijjaga kai alaman a'a, tayi murmushi tana dan kallon gefen nafisan tace "munayi Mami"
Faruk ne yashigo cikin qananun kaya bai dade da dawowa daga gurin aiki ba, ya zauna nan falon shima, bayan sun gaisa nafisa tace "yaya kaji wai daddawa Mami zata bamu mu sa cikin kaya mutafi dashi" faruk ya danyi dariya yace "daddawa kuma?" Na'ima tayi murmushi, Mami tace " ni tambayata anan shine, basa dafa tuwo ne ko me?" Faruk yace "Mami inkinga fridge din yaran nan danaje last time, inaga sai kin kai hannu a kowannensu, fast food kawai suke dirkawa cikinsu" Mami tadan bude baki tajuya ta kalli Na'ima tace "harda ke Habibti? naga kuma tuwon yana cikin favorite dinki" Na'ima tayi saurin gyada kanta tace "Allah mami muna dafawa time to time, amma miyan ganye" Mami ta kada kai tace "yamuku kyau, nasan kuma baby ce shugaba, da Abban ku yasiya muku mota kurinka uzurirrika dasu bakwa zuwa shopping na kayan abincin ne ko me?" Nafisa tace "wallahi muna zuwa shopping din Mami" Mami ta harareta tace "na kayan kwalliya da fata ba, my friend shut up" faruk dake zaune ya kada kai shima yana murmushi, Mami ta sake kallon Na'ima tace "na'ima kurinka yin abinci me kyau kunaci banason zama da yunwa, ko baby bataje siyo kayan ba ke kirinqa zuwa kina siyowa inyaso in kin dafa ma karki bata" Nafisa tafara dariya tace "Na'ima sarkin karatun kike bawa saqon nan Mami" Mami tace "nidai na fada muku, meye kuma na rayuwa da fast food da lafiyanku
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 19