Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 01 Oxford, England. Zaune take kan sofa cikin madaidaicin apartment din nasu,gabanta laptop ce da textbooks guda biyu wanda ta ajiye kan karamin table dake cikin falon tana typing, agefenta kuma  cookies ne acikin plate da coffee a ajiye, jifa jifa take kai hannu tana dauka tanaci Dukkan hankalinta tamaida kan abunda take typing a laptop din wanda hakan yasa bata juya ta kalli wadda ta fito daga dakin dake cikin falon ba. A sannu nafisa ta qaraso gurinta ta zube akan kujerar, batareda ta juyo ba ko kuma ta bar abunda takeyi ba tace "Good morning" cikin sanyin muryarta wanda yasa nafisa juyowa tana duban abunda take typing tace "Morning, what are you working on?" Matashiyar tace "just some essay" Nafee tace "shine yayi keeping dinki almost all night?,nafarka around 1 naga lights are still on" Matashiyar ta sake amsawa da "Eh" Nafee ta tsaya kallonta kawai,can tace "NA'IMAAA" tsayawa tayi da rubutun da takeyi ta juyo tana kallon nafisan da manyan idanunta cikin sanyin muryarta tace "I have deadline for this" nafee tace "I know, but girl give yourself a break mana" bata jira amsan na'ima ba ta miqe ta wuce zuwa kitchen domin hado nata morning coffee din, na'ima batace komai ba ta maida hankalinta kan rubutun da takeyi while sipping her coffee, sanye takeh cikin kayan bacci peach color wanda ya haska farin fatarta ta rufe gashinta cikin hula,ta ajiye coffee din akan table din ta koma baya ta manna bayanta da kujerar tana cigaba da cin cookies dinta idonta nakan rubutun nata tana nazarin each line. Nafee ta fito daga cikin kitchen din hannunta riqe da mug itama ta zauna wajen da ta tashi dazun gefen na'ima ta ajiye coffee din saman table tace "kaii, i slept like a baby today" murmushi na'ima tayi tace " you always sleep like a baby ai" 'yar dariya nafee tayi tace "yau na daban neh" na'ima tayi murmushi batace komai ba nafee tace "zanje shopping anjima naga fast foods dinmu sunyi qasa sannan inason cin tuwo miyan ganye yau dinnan dan nagaji da noodles gaskiya" na'ima tace "dazu nima nayi tunanin nan but my plan is tomorrow don yau nakeson kammala essay dinnan" nafee tace "yaushe neh deadline?" ta amsa da "jibi" nafee tace "toh ai akwai gobe, in Allah ya kaimu sai ki qarasa, muje tare ajiman" na'ima ta juyo ta kalleta tace "nafee bansan me goben zatazo dashi ba,tunda I'm halfway through gwara in qarasa once and for all. Beside, saura kadan fa" nafee ta juya idonta dramatically tace "yeah,right" sannan ta dauki satchet na cookies din tana observing calories din jiki tace "wait....these much calories in one cookie?, have to keep my body in check,I have a reputation to protect" na'ima batasan lokacin da ta fara yar dariya ba tace "sannu miss world contestant" nafee ma tana dariya ta dauki throw pillow ta jefa mata suna dariyan tare. Saida suka lafa da dariyan nafee tace "nayi waya da Mami dazu, ta kiraki kuwa?" na'ima tace "Eh nayi waya da ita jiya da dare, meya faru?" Nafee tace "bawani abu bane,munyi magana akan bikin anty salma ne zan koma next month shine takeson mu taho tare,so i thought ta kiraki" Duk wani annurin dake fuskan na'ima a takeh ya bace tana kallon nafisa. itama nafisan kallonta take tana nazarinta da kuma jiran me zata ce,can ta juya tana jawo laptop dinta tace "a'a bata kirani ba maybe tayi tunanin ban tashi ba amma zan kirata, Allah ya kaimu lokacin zanje..why not?" Nafee dai kallonta take still,ta riqo hannunta daya tace "you don't have to go indai ranki bayaso, nima baifi nayi one week bama in dawo,ni na cewa Mami zan fara tuntubanki da zancen tafiyan tukunna don nasan inta fada miki straight zakice Toh, but kinsan Mami,ban zata ma zata jira nayi miki maganan ba i thought harta kiraki" ta qarasa maganan tana dan dariya, na'ima ta juyo tana murmushi tace "zanje nafee i missed Mami" nafee tace "aikuwa dai ta qagu bikin nan yazo dan kije taganki, always asking ko kinacin abinci ko kuma kinyi qiba ko rama" dan dariya na'ima tayi idonta nadan cikowa da hawaye tace "Mami dai" squeezing hannunta nafee tayi tana reassuring dinta tace "She Cares, and i do too,I'm here always" jijjiga kanta na'ima tayi tana hana hawayen idonta zubowa, nafee ta rungumota kadan tana dan buga bayanta batareda tace komai ba sukayi shiru na wani dan lokaci sannan ta sake ta tace "coffee na yayi sanyi" na'ima tace "nawa yayi qanqara nima" miqewa nafee tayi "bari kiga na dafa mana ko noodles ne" na'ima ta amsa "da kuwa kin taimakeni,yunwa nakeji" wucewa tayi zuwa kitchen din tana cewa "A'a ki dai tsaya nan yin assignment yunwa ta illataki baruwana" murmushi na'ima tayi tana maida hankalinta kan laptop dinta,fara typing dinta keda wuya tunanin maganarsu akan komawarta Abuja ya fado mata rai, shiru tayi ta fada tunani abubuwa dayawa suna dawo mata kanta, The last time she left Abuja in za'a tambayeta biggest wish dinta na rayuwa shine "karta sake komawa Nigeria" Amma yazatayi...shi gida,gida neh ko bata koma domin Mami ta fada ba,tasan dole watarana saita waiwayi rayuwar da ta baro acan Nigeria, dole ne watarana saita koma gida, she's here to find solace amma babu ranar da bata tuna abunda ya sa ta baro gida Nigeria..Ganin tunanin babu inda zai kaita yasa ta rufe laptop din ta wuce nata dakin dake gefen na nafisa don tayi wanka. Zuwa 11 na safe bayan sun kammala breakfast sun tsaftace gidan nafisa ta tusata a gaba ta chanja kaya suje shopping din tare,a cewarta tunda ta ajiye schoolwork din nata to bazata zauna ita kadai a gida ba..tana murmushi ta tambayi nafisan "ni ke ina naki school work din?" Dariya nafee tayi tana mata wani kallo tace "ni nawa bana hana bacci bane,ke nifah ko exam bazata hanani bacci da hutu ba,Ina dalili" na'ima tace "Eh nima shaida ce" tana tuna lokacin da suke Bayero University Kano nafee dai baza'a taba ganin ta maida hankali akan lectures bama balle sauran school activities, Kuma batacin grade mara kyau domin Allah ya bata ilimin daidai gwargwado,kawai ita haka Allah yayita irin mutanen nan ne marasa sawa aki damuwa bakowanne abu ne yake daga mata hankali har ta sashi arai ba balle lamarin makaranta, sai abun nata ya hadu da gata kuma kasancewarta ita kadai mace wajen iyayenta babu abunda ta rasa daga wajensu da kuma siblings nata maza. Haka na'ima ta shirya cikin maroon abaya tayi rolling gyalen ta saka flat shoe ta fito zasu tafi tana kallon kayan jikin nafeesa wadda sanye take da white silk jersey short dress ta hada da blue jean trouser tayi rolling white gyale hannunta riqe da car key, farkon zuwan na'ima England nafisa ta sha convincing dinta ta fara dressing kaman nata but she always stand by NO Abune wanda bata taso taga anayi ba a inda tayi rayuwa. Rayuwarta da ta nafisa kamar banbancin fari da baqi neh wanda tun daga nesa zaka iya hango banbancin su batareda ka matso kusa ba,Amma haka Allah ya hada jininsu suka zamo kawaye tun level 100 a BUK har ila yau da suke Msc tare a Oxford University England. Haka suka tafi wajen siyayyan a motan da Abban nafisan ya siya musu domin uzurin makaranta da kuma na yau da kullum. Sun siyo duk kayan buqatunsu harda personal essentials dinsu suka koma gida cikin walwala Bayan sun huta sunyi sallah nafee ta tafi kitchen zata jera kayan ta bar na'ima nan falo zaune kan sallaya saiga kiran Anty Amnah, qanwar baban nafisa ceh da take aure a London da yaranta biyu twins maza, daukan kiran tayi suka gaisa anty Amnah tace "na'ima munata jiran zuwanku tun jiya i thought zakuzo weekend, Boys suna ta murnan zakuzo har sun gaji,hope kuna lfy" na'ima tana murmushi tace " lafiya anty ,we are sorry, muna research akan wasu essays ne shiyasa bamu samu zuwa ba" anty Amnah tace "No bakomai na'ima dama saida nayi tunanin school activities ne suka riqeku this week, nakira nafee ma no answer hope she's okay" ta amsa cikin sanyinta "Eh lafiyanta kalau anty tana kitchen ne...In Sha Allah next week zamuzo abawa boys hakuri" tace "it's Okay kuhuta gajiya" sukayi sallama ta kashe wayan batakai ga ajiyewa ba kiran Mami yashigo ta daga da sallama tana gaisheta ta daya can bangaren Mami ta amsa da "lafiya kalau Habibti yakuke, ya karatu?" Na'ima tace "Lafiya Mami,yasu yah faruk?" "Lafiya na'ima,fatan babu matsala ko" tace "Alhamdulillah mami" Mami tace "nafisa tace zakuje siyayya yau" "Eh har mun dawo" "Ma Sha Allah, Habibti ki kwantar da hankalinki kiyi karatu kinji, sannan ki rinqa addu'a" Muryar na'ima na dan rawa ta amsa da "in Sha Allah Mami" Mami tace "it's alright Habibti, everything is going to be fine..in kinji bakyason zuwa bikin Salman ma kiyi zamanki in su amnah zasu dawo zan biyosu inzo na dubaki kinji" Na'ima tace "A'a Mami zanzo, zamu taho tare da nafisan" Mami tace "Toh na'ima,Allah ya bada sa'an karatu kinji" Hawaye na taruwa a idonta tace "Amin Mami nagode" Da haka sukayi sallama tagama goge idonta nafisa tafito daga kitchen hannunta riqe da chocolates guda biyu ta qaraso ta miqa mata daya itama tana bare daya ta zauna kan kujera tace "Anty Amnah ta kiraki?" Na'ima ta amsa da "Eh bamu jima da yin waya ba, takiraki baki dauka ba" Nafee tana gyara zamanta a kujera tace "Nakirata ai, wai tsaya... don't tell me anty amnah tana expecting mu rinqa driving for 2 hours to go to London every two weeks to spend weekend there" murmushi na'ima tayi ta miqe tana cire hijabin jikinta  tana girgiza kai draman nafee nabata dariya. ✨KUNCIN ZUCI✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 02 Lagos, Nigeria Mutane akalla sha biyar neh zaune cikin conference room din Oil & Gas company dake victoria island cikin garin Lagos, suna gudanar da meeting me muhimmanci tsakaninsu da turawan dake other side of the conference table. Cikin nutsuwa suke tattaunawa da Ahmad dakeyin nashi bayanin  cikin harshen turancinsa mai dadin sauraro, kasancewarsa mutumin da yayi rayuwan qasan turawa na tsawon lokaci,he sure has his way of interacting with them. Can dai yayi shiru kawai yana sauraronsu batare da yawan basu dogon amsa ba,Dan'uwanshi Adam dake gefenshi neh yayi saurin amshe conversation din knowing Ahmad bazai sake doguwar magana ba kuma tunda al'amarin yafara bashi haushi. Haka Adam suka gama sauran tattaunawan , suka miqe gaba dayansu akayi musabaha har dashi Ahmad din telling them zasuji nasu final answer dinsu zuwa jibi. Fitowa sukayi daga conference room din Ahmad yatafi wajen elevator zai koma nashi office din while Adam ya tsaya magana da wani employee dinsu. Shigarshi office din nashi keda wuya Adam ya biyo bayanshi, Ahmad ya qarasa kan executive chair dinshi ya zauna at the same time yana duba wasu folders da yasa secretaryn shi yakawo masa dazu, wucewa gurin fridge Adam yayi ya bude zai dauki ruwan sha , cikin husky voice dinsa  Ahmad yace "pass me one please" Adam ya dauko bottle water guda biyu ya qarasa ya ajiye masa saman table dinsa, Ahmad ya jawo ruwan yana muttering "thanks" Adam yace "so what do you think?" Batareda Ahmad ya kallesa ba yace "I'm Out" cike da mamaki Adam ya ajiye nashi ruwan shima kan table din yace "what?..Dude are you serious?" Ahmad ya dago kanshi yana kallon Adam with seriousness, cikin idonshi Adam yake kallo yace "you can't be serious" Ahmad ya juya yana duban foldern gabanshi yace "well..too bad I am" Adam yace "you can't cut out on this, ta ina aka samu matsala kuma?" Ahmad ya amsa da "The percentage...I don't like it" Adam ya koma gurin small lounge dake cikin office din a gefe yayi settling akan kujera ya juyo yana kallonshi yace "you know this deal is a fair one right?" Ahmad yace "we need to include some high risk, high return options" Adam yace "but we can't gamble with anything high risk" Ahmad yayi shrugging kafadarsa like he don't care yace " No good thing comes without a little risk" Adam yace " then what are you going to do now?" Baya Ahmad yayi akan kujeran yayi relaxing bayansa yana kallon Adam yace "I'll sort everything out" sanin waye Ahmad yasa Adam cewa "Okay..it's settled then" don yasan wasting din energy dinsa kawai zeyi wajen convincing din Ahmad saboda ya riga yayi making mind dinsa, yakuma cewa "I'll be flying back today, in few hours ma" Ahmad yace "Okay, take care" miqewa Adam yayi yana cewa "Dude, ka kwana biyu baka leqo ba fah"  shafa kanshi Ahmad yayi yace "akwai bikin yarinyar can wai ko, I'll be there next month in Sha Allah"  Adam ya qaraso ya miqa masa hannu sukayi shaking yace "see you then" Ahmad ya amsa da "thanks man,safe flight" Bayan tafiyar abokin nashi kuma dan'uwa, Ahmad ya maida hankalinsa kan desktop din dake gabansa kira yashigo wayanshi, Laila ya fito akan fuskan wayan ya juya yana kallo har ta tsinke bai dauka ba yakoma kan ayyukanshi. Daren ranar na'ima ta fito daga wanka tana zaune gaban madubi  tana shafe shafenta da ya zame mata daily night routine yanzu, Kuma nafisa ce ta koya mata this kind of routine, ita ta siyo mata all skin care sets da suka dace da kalan farin fatarta sannan ta rinqa koya mata a sannu sannu har ya zamto bata iyayin bacci yanzu batareda tayi shafe shafennan ba Ta dago hannunta tana ganin yanda yazama smooth and glowy, tasan kayan ba masu sauqin kudi bane domin fenty skin care sets nafisa ta siyo mata, And she's very grateful for all of it, when she says all of it tana hadawa da kyautatawan da nafee tayi mata a baya da kuma wanda take kan yi mata har yanzu. Nafee ba qawarta bace kawai, ta zame mata yar'uwa or even more so, dan bazata taba mantawa da ita ba a duk inda taje a rayuwan nan. Tana cikin tunanin nafisa ta shigo hannunta riqe da laptop a bude tana kallon movie, ta qarasa kan gado tareda kwanciya tasa laptop din agaba itama kayan bacci neh jikinta tace "BoBo, my crush is killing it in this new series" Na'ima ta juyo tana dan dariya tace "Au wai haryanzu dai Witcher din kike kallo?" Nafee tace "kinsan Allah..sabon nan yafi dadi ma, ki gama kizo ki gani" Na'ima ta juya ta cigaba da daure gashinta tace "A'a bazan gani ba"  Nafee tace "dalla can ya hadu kizo mugani, Ina zuwa ma" ta tashi ta fice daga dakin bayan minute sai gata tadawo dakin riqe da packs na cheese balls ta wulla na na'ima kan gado ta hau ta cigaba da kallonta tanacin cheese din Bayan na'ima ta gama itama ta hau gadon ta matso tareda daukan nata cheese din tana budewa tace "gaskiya ni kin taquramin da series dinnan" nafee tace "kiyi shiru ni mugani" Haka suka kai almost sha biyu suna kallon, na'ima da tace an taqurata sai ga ta itama ta zage tana kallon with full interest har nafee tayi bacci ta barta, saida ta gaji sannan ta tashi taje bandaki tayo uzurinta ta fito bayan tayi alwala tayi sallah sannan ta kwanta a gadon ta jawo duvet da nafee ta kwashe a jikinta ta lulluba, bata qara wasu mintuna masu tsawo ba itama baccin ya dauketa. ✨KUNCIN ZUCI ✨ Na Bintu Musa Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c WhatsApp group 👇 https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z Chapter 03 Schoolwork dinda Na'ima batayi ba washegari kenan suka shiririce wajen kallo,da suka gama na'ima ta tafi kitchen zata dafa musu tuwo miyan ganye Nafisa na tayata suna hiran samarin ita nafisan, da wa'inda ta baro a gida Nigeria da kuma wa'inda take kulawa sama sama anan oxford Na'ima na dariyan draman nafisa da umar, saurayinta da tun a BUK suke tare, yanzu haka yana aiki a central bank Nafisa tace "kinsan Allah, this time around idan nayi blocking dinshi bazan bude ba mun rabu kenan" Na'ima ta dan bude ido tace"toh fah,abun har yakai haka" Nafisa tace "I'm serious this time" Na'ima tace "toh yanzu dai bari mujira idan kikayi blocking dinshi dagasken sai mu cigaba da wannan maganar" Nafisa ta ajiye alayyahun hannunta data tara ta dauki roban gabanta dayake kan kitchen island din zata buga mata tana dariya Baya Na'ima tayi tana dariya itama tace "gaskiya ne ai,maganar blocking dinnan har nagaji da jinta kuma anjima zanjiku kuna waya kina kashe murya" Nafisa tace "zan baki mamaki kuwa, zaki gani" Na'ima ta dawo wajen girkin nata tace "aikuwa zansha mamaki randa hakan ya faru" Saboda har ta gaji da bawa nafisan hakuri karta rabu da guy din A haka suka gama girkin suna hira cikin walwala, bayan sunci sunyi sallahn la'asar kowacce ta tafi nata dakin yin wanka suka shirya suka fita yawon yamma, Walking through the street of the town zasuje Cafe , Nafisa ta tsaida su gefe tayi wa na'ima hoto tana murmushi, ta dauka musu tare sannan ta bawa na'ima wayan ta dauka mata ita kadai, sai da rana ta fadi suka koma gida hannunsu riqe da ledan snacks din da nafisa ta sa suka siya a wani supermarket kamar ba jiya suka yo siyayya ba. Bayan sun koma gida sukayi sallah suka zube nan falon, Na'ima ta dauko laptop dinta ta cigaba da essay dinta while nafisa kuma tanata danna wayanta,ta zabi hotunan da sukayi tare da wanda tayi wa na'ima ita kadai ta turawa Mami sannan ta zabi wanda take ita kadai banda na'ima tayi posting a Instagram handle dinta sannan ta tashi ta dauko nata laptop din don duba school work dinta itama Washegaria Monday zasu je school, Na'ima da wuri ta tashi zata hada musu breakfast dan tafi ganewa tayi musu if not nafisa toast da tea kawai zata musu Tana kitchen din tana kada kwai bayan ta gama chips nafisan ta shigo hannunta riqe da ipad sai lumshe Ido take alamun bacci bai isheta ba ta miqawa Na'ima ipad din, karba tayi taga fuskan mama akan wayan tana mata murmushi tace "Habibti ina kika baro wayanki inata kira" Na'ima ta amsa "yana daki ne, ina kwana Mami" tace "lafiya lau na'ima,kun tashi lafiya" kafin ta amsa Abubakar dan autan Mamin ya sako kanshi ta bayanta yana gaisheta, Na'ima ta amsa tana murmushi tace "Abu yau bakaje school bane" yace "jiya muka gama Waec anty" Nafisa ta matso tace "Kai dalla ka bawa Mami wayan su gaisa" Gwalo Abubakar ya mata , Na'ima tayi dariya sanin draman da suke kwasa a tsakaninsu tace "rabu da ita,saura Neco yanzu ko" yace "Eh" tace  "Allah ya baku sa'a"  ya amsa da Amin yana matsawa fuskan Mami ya shigo tace "daughter ba wani matsala ko?" Na'ima tace " A'a babu komai" "Ma Sha Allah,ku rinqa karatu fa kunji" ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" Mami tace "Allah ya taimaka yayi albarka" bayan ta amsa sukayi sallama ta miqawa nafisa itama sukayi sallaman. Na'ima ta gama hada musu breakfast sunaci anan kitchen din dayake akwai kujerun zama jikin kitchen island din nafisa tace "yau zamuje wajen taron movie premiere a London" Na'ima tace "Really?..wane movie ne" nafisa tace "British movie ne,Lauren ta siya mana tickets ashe tun last week" hankalin na'ima na kan plate din abincinta tace "then me zakujeyi awajen toh" nafisa tace "ita zataje for her content nima dai sort of that,kizo muje it'll be fun" Na'ima ta juya ta kalleta tana ware ido tace "waaa?..school zan tafi yanzu ma ina gama cin abincin nan" Nafisa tace "muma fa sai mun gama morning lecture tukunna, it'll be fun I'm telling you" Na'ima ta girgiza kanta tace "Bazan je ba" Tuesday.. Tsaye take a balcony na apartment din nasu dake 4th floor cikin 10-story building. Bayan tadawo daga school kadaici ya dameta a gidan ta fito nan don tasha iska, tana tsaye daga inda take tana hango wucewan mutane da dama a street din nasu, Most at times batason zaman shiru sosai in Nafisa batanan, takan nemi wani abu da zeyi keeping dinta busy to abstain herself from thinking. Wasu couple ta hango suna tafiya suna dariya, Na'ima ta bisu da kallo har suka wuce, ta dago hannunta tana kallon wani tabo dake tafin hannunta qurawa tabon ido tayi tanajin zuciyarta na karyewa abubuwa da dama suna dawo mata cikin kanta , digar hawayenta akan tafin hannunta ne yasa tayi saurin goge idonta tabar balconyn takoma cikin falo , dauko mopper tayi ta fara tattare gidan tana gogewa. Ranar har bandakin nafisa saida ta wanke , ta sake rearranging din wardrobe dinta dana nafisan ta dafa musu rice and stew, kuma duka ayyukan nan din tayi ne don kawai tasamu something to keep her mind off, something that will abstain her from thinking too much. Ranar juma'a suna zaune a falo da safe suna hira jefi jefi sun saka skin face mask, na'ima tana karatu a ipad dinta aka kira nafisa, tashi zaune nafisan tayi daga kwanciyar datayi kan kujeran a fili tace "yah faruk" Na'ima tabar abunda take ta juyo, amsa kiran nafisa tayi suka gaisa sai kuma ta miqe da sauri ta leqa balcony, ihun da tayi ne yasa Na'ima ajiye ipad din da sauri ta bita balconyn itama tana duban street din Yah faruk ta hango jikin mota a gefen street din

Chapter 1 of 19