Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na bata riqo yana jakarta qaramun wayana dake hannuna ba kati haka naita jiran tsammani da qyar na bude qofar koda nazo ba kowa shisa ban nemetaba na hau adaidaita kawai na dawo, neman wayana dana bata riqo ne ya ankarar da mutanen cewar ba'a gantaba a wurin sam!!!! Ta qarashe maganar tana kuka hadr da toshe bakinta da hijabin ta " tundaga lokacin wayanta da nawa aketa kira basa tafiya ko nan da cen, Mamanta sumanta biyu muna zargin kidnerpers dinnan dasukai yawa ne a gari" Shiru Maheer yae yana nazarin kalamanta kanshi yayi zafi yarasa ma mezeje ga islam se qara d'aga masa hankali take tana faman kuka... ************** Nancy se zare iso takeyi tarasa gane inda take bayan ta farka, hankalinta ya matuqar tashi ganin kanta datae acikin qungurmin daji ita kad'i kuma a d'aure jikin icce, takasa gane shin mafarki takeyi ko Gaske ne......innalillahi wa innah ilaihirraji'un itace kalmar dataketa nanatawa a bakin ta, bilhaq dai ta gano tana cikin musiba bazata iya tuna komai ba se ganin wasu maza suna tambayarta ko nane gidan Amaryar Aminu tace e shikenan seta wayi gari ta ganta a wani d'akin tare da wata mace kantae wani yunqurin kuma tarasa ina take se yanzu, waiga wa tae gabas da yamma kudu da arewa bataga alamar ko kadangare a jejin ba, babu alamar gari a gaba bare a baya, wurin yayi tsit se ita kadai runtse idanta tae ta soma rero duk wata addu'a datazo bakinta haka ta wuni har yamma ga jakarta a kusa da ita an ajiye mata amma bataza iya kunce kantaba bare ta dauki jakar ko zataga wayarta!!! Wannan shine tashin hankali wanda ba'a saka masa rana.....wata irin razananniyar qara ta saka sabida ta gaji ga yunwa ga qishiruwa, ta qosa ta ganta a kunce, babban abinda yafi daga mata hankali shine rashin yin salloli idan zata irga da kyau tunjiya da aka d'akkota rabon datae salla yo batamasan inda kanta yakeba bare tace zatayi salla.... Adu'ar taci gaba dayi ganin ihun ba abinda ze fitar da ita bane......duhu ya sauka se wannan lokacin tasoma jin kukan tsuntsaye alamun sun dawo daga inda suka tafi qishiruwa takeji sosai tamkar zata mutu, yawun bakinta ya gama qafewa wani duhu ta gani tsaye agabanta abinda , a hankali ta d'aga kanta sama domin kallon meye anan ta sume bayan ganin abin.... ************* Maheer ya rasa dalilin damuwar sa akan Mancy, ko Ummul bata cikin nutsuwa kullum setayiwa Ameen kuka, ango ya kasa gane kanta, mahaifiyar Nancy tana nan an miyarda yaranta Niger amma tana nan, gashi an koma skul amma Nancy bata nan yanzu tsawon wata d'aya kenan da b'atan Nancy amma bako wanda yaga sanda wani abu ya sameta, Islam kam an gama ramewa an lalacewa akan rashin Nancy indai ka santa to kallo d'aya zaka mata ka gano cewar tana cikin rashin kwanciyar hankali da nutsuwa na rashin Aminiyarta school d'inma tana zuwane kawai sabida babu yanda zatayi, auren ta kuma saura sati uku gaba d'aya ji takeyi batason auren nan kwata kwata, indai Nancy bata nan gani take auren ma gwara babu, da farko ta dauka kidnappers ne har tana shirin kudaden data tara na yawon duniya take shirin siyan kayan daki ta bayar a hada a karbo ta amma segashi shisu basu kiraba...tafi qaunar yau ace gawar Nancy aka gani tasan mutuwace akan hakan..... Maheer kam acikin ranshi yakejin azabar daya kasa bayyana ta sabida babu wata alaqa ta jiji a tsakaninsa da nancy dazata sanya ya kasa mancewa da lamarin ta ya bita da addu'a kawai, wani zubin har abinci yake kasa ci,abu mafi bashi mamaki shine yanda yake mata kuka duk sanda ya tunata seyayi kuka kenan kuka ya zame masa d'abi'a kullum sabida da ita yake kwana yake kuma tashi baya manta ta wanda ya sanshi ma yasani walwalarsa ta ragu sosai... Yauma kamar kullum kwance yake acikin bahon wanka an zuba flowers masu tsananin qamshi acikin ruwan dayake wanka dasu, ya kasa koda mosti bare yae wanka hawaye yakeyi yana tunanin Hafsat metawa mutane? Dawa take fad'a?, police sunyj shiru da binciken inda ta shiga to yaya hakane?..".. Kallon Anty reeda anty nasara tae tace "Wai matar tasa tana nan ne? Kike zancen an bugo IV?" Kallon ta tae "To anty ina zataje tana nan mana?" Biki fa saura sati biyu ko d'inkuna bamui ba, Umma kuma tayi zancen kayan lefe" Zaro wayarta tae jikinta har rawa yakeyi, ta nunawa Reeda wani hoto "Wannan dake tare dashi wacce suke ajikin wannan hoton atare wacece ita to? Nasha itace amaryar ai?" D'an murmushi tae ."Ba wannan nasani ba bari kiga wacce ze aura damukaje gidansu kina dubai" nan take ta nuna mata hoton islam jikin ta kuwa har rawa ya somayi ita anty nasaran ta kalli fareeda cikeda tsoro tace "Nashiga uku sis, wlhy nayi hauka da shirme kuwa?" Qura mata ido tayi tana mamakin kalamanta kantace "Ban fahimcekiba sis?" "Kinsan na sanar dake banason auren nan,nakuma kira Maheer namasa magana akan ya janye yaqi, shine danaga wannan pic a social media nace to lallai itace, senawa er akuri sending lokacin zanje umra daganan na wuce dubai, tofa shine dana tura mata nace a sace yarinyar a tsoratar da ita sosai akan maheer, ni tunda tace ansace yarinyar ban qarawa hajiya maganar ba, jin anyi shiru ya sanya nayi tunanin yarinyar ta janye ne shisa banbi ta kaiba, amma bawai sace yarinyar dawowar danai shekaranjiya hajiya azumi ke gaya mun wai taga fuskarta ta farka musu bisa kuskure shisa ta sanya aka kaita jejin amanawa wannan mugun jejin aka manna mata igiya suka jibge mata kayanta anan, wai idan ta mutu ko oho basu suka kashe taba, to nima banji dadin hakan ba amma senace bani nayiba ko lahira banida laifi" Mamakinta ne ya sanya Reedah miqewa tace "Anty Binta yaushe kika canja? Wannan wane irin mugun tane fisabilillah? Koda islam dince yanzu keba ruwanki kenan? Idan da ace Meerah ce zakiji kwanciyar hankali tana wannan jejin? Karfa ki manta ko masu shiga ciki seda tsafe tsafe haba anty Nasara wlhy baki kyauta ba, qyamar dakikewa talaka hartakai kiga kamar idan ya mutu ruwansa shisa kiyashi duk d'ayane a gunki? Lallai ma Anty" shiru ta danyi kantace "Karkimun raini wayau Fareedah kinaji ba" zama tayi ta dauki wayarta tawa kanta sending pic din ta wtsapp sannan batama mata sallama ba ta fita.......... Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 20 Maheer da police ne suka zagaye kwalawan bayan sunyi nasaran kame su ta hanyar wayau, babban cikine yake jawabin abinda ya faru tirtan tiryan ya qara da cewar "Cewa akayi ma mu kashe ta tomu a qa'idar aikin mu bama kisa ko bindiga ma bama amfani da ita qarqari yanki mutum inda mukasan baze mutu ba, shine mukace bama kisa se matar tace mukaita wannan jejin muda kanmu munajin storo seda aka qara dubu dari uku sannan muka kaita bama wani da nisa mukaje da ita ba muka daureta wurin kawai dan mukanmu a tsorace muke, sannan wlhy muba en fashi bane area boys ne kawai mabiya en siyasar sokoton nan" nisawa maheer yae yace "Yanzu kune zaku mana jagoranci zuwa jejin, tunda naji ku kunada dama dama inshaa Allah bazan bari a tsare kuba kuma zan daukeku ayyuka a company d'ina me zaman kaina zan kuma baku jari wanda zaku ja a dayan bangaren ku qara nidai kawai so nake na ganta ne" kallonshi ogan yayi yace "Malam tsakani da Allah zaka sama mana aikin nan ka rabamu da zaman banza, wani zubin abinshan koko ne seya fagaremu ka ganni nan NCE ce dani amma ba aikin yi idan har haka ne zan gaya maka gaskia" dan sandan ne yace "Au kai dama dan qaniyarka qarya kakeyi ba hakan bane" "Bafa qarya nayiba yallab'ai kawai dai wani abu yabiyo bayan mun ajiyeta ne" Riqe hannunshi maheer yae "Wlhy summa tallahi zan cika dukkanin alqawarin dana d'auka kurun dai ka gaya mun gaskia kai harma da qari zan maka wlhy" "Yallab'ai bayan munkai yarinyar nan abu biyu ne ya dawomun a zuciya, na farko dai nayi tunanin idan ta mutu mune da haqqinta na biyu kuma da akwai wani mutum dake so akai masa en mata ya bamu kud'i bansa me suke masa ba amma dai nasan ba kashesu yake ba wani zubin ma mu yake baiwa yaran muje mu mayar dasu inda muka dakko su, wasu bayan wata tara wasu shekara wasu har shekaru biyu suke kan mu maidashi, tose nayi tunanin na kai masa ita amma kuma nayita kiran wayarsa a kashe, ban taba sanin inane gidan saba kullum a hanya muke had'uwa....dukda haka senaje na dauketa koda naje ta suma a wurin amma haka na d'akko ta na kaita wani gidan mu na daureta kullum ko bayan kwana biyu nikanje sedai shekaranjiya naje batada lapia sosai, kamar ulcer ne da ita kwana biyu babu aiki ba kudi banida abun siyan mata abinci banjeba, inaso in sake ta ta tafi amma ina tsoron sena saketa oga me en mata ya dawo" Cakumo rigar sa maheer yar "kanada hankali kuwa yaya zaka daure mutum ka kwana biyu bakaje ka bashi abinci ba, to waima tukunna ita kadaice kenan a gidan koda me kula da ita?" Riqewa maheer hannu yae yaji maqura yace "Kayi hakuri yanzu muje cetonta shine yafi" sakeshi yae tare da tunkudashi yace ku tashi mutafi wlhy idan wani abu ya sameta duk sekun gane wlhy" haka suka d'unguma dukkansu har anty Reedah dake biye dashi kamar jela har sokoto ta bishi sanida en iskan a sokoto suke...... Da kanshi ya bude gidan ya kasa hakuri ya warce key d'in a tare suka shiga dukkansu wasu nabin wasu haka ya miqawa ogan key ya bude d'akin ya shiga shima yabi bayansa wasu police suka tsaya da wasu yaran a waje.......d'akin duhu sosai, Maheer jikinsa har rawa yake garin laluben fitilar wayarsa haka Anty Fareedah ma,hasken fitilar d'akin ya soma mamaye d'akin wannan ya baiwa Ilahirin mutanen d'akin damar fuskantar gabansu, Seda maheer yae baya sannan ya sake wayar hannunsa Nancy ce kam amma kamar ba itaba tayi baqi abin baqin ciki da takaici ma a tsaye aka d'aure ta kashi da komai anan takeyi kuma doguwar rigar dake jikinta dukta nannade a jikinta d'akin se tashin wari yakeyi na kashinta da fitsarin da takeyi...Maheer beko kalli kashin ba yae kanta da taimakon ogan suka kunce ta amma seta biyosu lago tana shirin fad'uwa riqeta maheer yae ya janyeta daga wurin najasar amma bega alamun akwai numfashi a tattare da ita ba, Se tsakar gida ogan ya kama masa suka kaita Maheer tamkar nagoye yake kuka hatta fareedah kuka takeyi police uku ma acikinsu kuka suke, lokaci daya nadama me tsanani ta saukarwa oga, ya kalli Maheer yace da kun shigar da ita bayin nan an dauraye mata jikinta bazamu iya fita da ita a haka ba, jikinta duk kashi" harara maheer ya wurga masa ya kalli fareeda yace "Twin tayani duba pulse d'inta dan Allah" Dayake dama fareedah medical doctor ce wannan ne ya basu damar dubawa tabbas akwai sauran numfashi ajikinta sedai she's too weak....kallan shi tae tace "tana buqatar taimakon gaggawa amma dole seda wanka babu asibitin dazamu nufa da ita haka, gashi bazata iya yiwa kanta ba harga Allah ni bazan iya taimakontaba, tunda gidansu anan yake mukaita gida kawai" kallonta yae "Banason sunan gidanmu ya b'aci twin, bazan kaita gida a haka ba dole seda wani plan, kinga police suje station da azzaluman nan ke kuma muje gidana ki gani... Hakan kuwa akayi islam yawa waya yana nemanta a gidansa da gaggawa dolenta ta hau adaidai ta rigasu gidan suna zuwa yaja hannunta ciki " ki nutsu babu lokacin dazan miki bayanin wani abu a yanzu maza jeki ciki zan kawo miki Hafsat tana buqatar wanka k mata mu kaita asibiti tana buqatar taimakon gaggawa" kallonshi ta qarayi "Wace hafsan? Tsawa ya mata " Nace bamuda lokaci salaha!!!" Bata qara magana ba, wlhy dataga hafsat bata gane taba seda yace Nancyn kice a haka fa Salaha, wlhy an cutar damu" tsayawa tae yace "haba salaha ki mata wankan nan wlhy bamuda lokaci sannan kuma kinga bata numfashi da kyau" A haka islam na kuka tawa Hafsat sab'i yakai bakwai seda taga ta soma haske sannan ta barta haka anty Fareeda ta kira suka dawo da ita dakin suka saka mata kaya wanda yauma da ake neman kayan da qyar aka samu doguwar riga abinda kullum akwai kayan kyauta yau aka rasa se rigar maheer aka sanya mata, aka shafa mata mai da komai sannan fareedah tasa akai rushin nata zuwa asibitin uduth, a gaggawa suka karbe ta sannan suka samu nutsuwa kad'an mota Maheer ya kira islam yace "Islam ki nustu kiji abinda zan fad'a miki, kuma ki sani wannan sirrine bana buqatar koa gidanku ki fad'a, sannan kuma ki sani abinda zan fad'a miki ya shafeki ne dakema bazan sanar miki ba" kallonshi tae amma batace komai ba yaci gaba "Duk kanin abinda ya faru da Hafsat ta dalilin kine" da sauri ta kalleshi alamun bata gane ba....atake ya bayyane mata komai har qarshe yace. "Bani buqatar sunan yayata ya fito sabida haka zan adana wannan maganar se Nancy taji sauqi gaba d'aya, sena nemo wani plan dazan fada kina jina ko?" Nisawa tae har tana qwallah tace "Amma wlhy an cuci Hafsat wai kasan na kula da qafarta d'aya daga qasanta kamar a karye take😭😭 karaya tsohuwa kuma dan hargun yayi baqi, dukda batasan inda kanta yake ba wlhy na kula cewar tana yamutsa fuska duk sanda na taba wurin kuma, duka qafafun guda biyu sun kumbura suntum se qyalli sukeyi wataqik dukanta sukayi a qafar" kallonta yae shima qwallan dayake tarewa seda ya zubo sannan yace "Islam a tsaye suka d'aureta kusan watanni biyu dole qafafunta suyi hakan ai, wataqil inaga ba karaya bace ba dai wani abinne karki damu kinji?" Gyada masa kai tayi tanata kuka, yau kad'ai maheer ya kamo kafad'un islam yana ganin wannan ne kawai ze sanyaya masa zuciyar sa gani yakeyi tamkar haqqin Hafsat ze dinga bibiyar zuri'arsu ne har qarshen ta . ************** Seda doctor yaja numfashi sannan kalli Maheer yace cikeda tausayawa "kaine mijinta?" Kallonsa Maheer yae ya kalli islam da fareeda sannan yace "Ea nine mijinta" doctor yace "Babu damuwa in fad'i abinda zan fad'a agaban wa ennan?" Daga masa kai kurun yae alamar e baze iya magana ba jikinsa har rawa yake yi sosai akan hakan, doctor yaci gaba "Ranka ya dad'e nayi mamakin yanayin abubuwan dake damun matarka har haka kanada arziqinka amma baka d'auki wani matakin ba, da farko dai yunwa tayi mata illa me tsananin wahalar magan cewa har indorscopy se an mata domun gano menene matsalar cikinta idan ta farfado, na biyu kuma tanada tsohuwar karayar da zance tafi wata daya ba'a dorata ba harma ta soma rube k'afarta ta dama, wanda ko shakka banayi dole se an yanke qafar, abu na uku kuma bata cikin hayyacinta jininta yayi mugun hawa, pcv dinta kuma is very low, yanzu zaka saka mana hannu ne a takardar cire qafar tata sabida a gaske bamason aikin ya wuce sati sabida qafar tanata ci karta qara sama tunda a qasane kawai, qarayar wurin ankle d'inta ne" kasa magana maheer yae ganin komai yake tamkar a mafarki yanzu kam har fareeda kuka takeyi sun gagara cewa da likitan komai se kuka har maheer din, mijin fareeda ne ya kira dama yace zezo sokoto shima dayake babban likitane, ta fice ta daga wayar tana kuka take sanar masa...... Haka Maheer be baiwa doctor amsa ba kuka yaci qarfinsa yaje mota yafi 30 mns yanayi, daga baya yaje dakin da aka ajiye Hafsat anan ya tarar da islam na kukan ta riqe hannun Nancy, shi dinma ya gagara rarrashinta zama yae ya qurawa fuskar nansi ido,se yamutsa fuska nancy keyi harse dimple nata ya lob'a, shafa fuskarta yae yace "Ki yafemun Hafsat, duk ta dalilina kika shiga wannan halin" haka ya dinga surutai yana kuka islam ta kasa magana se kuka take qwalawa harna tashin hankali shima maheer haka...... Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* *Ina godiya masoyana Umm Nass wannan shafin kyauta ne agareki ki kacaccala yanda kike so amma plss kada ki Baiwa sana s matazu ko kalma daya lollxx* 22 Yauma kamar kullum Maheer kwance yake acikin bahon wankan sa ya runtse idansa yana nazarin rayuwar duniya...Dukda yake yasan Anty Nasara mahaifiyarsu ta biyo na qyamar talakawa amma sam umma ita bata hakan takan yarda da qaddara sedai kurun bata hulda da talakawa ne ita...komai girman danganta karku idan bakada shi babu ruwan umma dakai sedai idan kazo mata tana haba haba da nan nan dakai, amma ita taje maka batayi fara'arta da haba haba da mutane ya sanya kullum gidan nasu baya rabo da en uwa, sab'anin Maheer da twin dinsa suna qaunar mutane sosai ga fara'a ta mahaifin su dasuka gado ta sosan ma, Matsaloli guda biyu se mutan america su safiya da sha'awa sarakan rashin ji da jiji dakai waisu yaran masu kud'i sune sukafi kowa girman kai a gidan kaf!! Nisawa yae ya qara lumshe idansa yanajin dadin ruwan d'imin dayake cikinsa....rashin memory din Hafsat bashi bane damuwar sa a yanzu,damuwar sa biyu ce na farko dai qafarta yau zasu shiga aiki na biyu kuma rashin maganar ta muryarta kadai yanasi yajita koze samu nutsuwa me sanyi!! Yarasa menene yakeji game da wannan yarinyar abu d'aya ya sani yanajinta har cikin jini,jijiya da b'arqon sa...kai harma qasusuwan sa sunsan da zaman ta acikkn jinjinsa da jijiya sabida sukan amsa suma.....yana yiwa Hafsat Son so!!! Qaunace daga indallah be tab'aji yana sonta da aure ko soyayya ba amma ya kasa fuskantar inda zuciyar sa ta dosa akan hafsat!!!! Haka ya gama wankan sa ya fito ya shirya tsaf ya nufi asibitin..... A kan hanyar zuwa asibitin islam ta masa waya dayike tana sokoto Hafsat tare da Mahaifiyar ta take..... "Honey dama cewa zan maka ko za'a d'auke lokacin bikin nanne naga saura kwana bakwai ko IV ba'a kawo ba gidan ma harsun soma mgana" Sajen fuskarsa ya kaiwa laluba kanya qara kame staring yace "Afwan Babyna, wlhy rashin lapiyan hafsat ne ya sanya na shafa gaba d'aya da zancen iv d'in nan amm kuma kinsan abba daddy baze tab'a sauya date d'in aurena ba sabida commitment nasa yagama schedulling da komai akan hakan,so yanzu inaga zan miki transfer seki nemi wani buga iv a garin naku ya buga muku naku na mata, na daurin auren ma daddy ya aiko nine zan aiko dashi but na manta wlhy" Bataji dad'in kalaman saba koda yike itama tanada damuwa sosai akan ciwon hafsat amma tana ganin be cancanci ya shaagala da sha'anin auren ba akan shi ace saura sati d'aya,cikin kasala ta furta "Amma Honey hakan ai ba daidai bane, daga wurinku ake aiko da kati da alawa a al'adar sokoto fa" Haka kawai ya saka mata fad'a "Haba Islam!! Ke bakya ganin ina cikin tashin hankali ne inada patient? Agidan mu wayakeda lokacin zuwa sokoto yin wannan abin, kinga dire al'ada gefe zanwa Ameena transfer koma namai magana asiya komai akai muku ina idan friend dina yazo babu damuwa?" Sekuma ya qarashe maganar cikin sigar rarrashi, hakuri ta bashi sukai sallama akan gobe za'aje akai.... *************** Tunda yaje asibitin ya kasa sukuni cox ana kan aikin qafar basu fito ba, tunawa da yae agidan sa na kano daza'a kawo islam akwai wuraren da babu funiture ya manta ba'a saka ba, tsaki yaja ya kira islam "Honey ina wuni yaya anfito aikin ne?" Ga alama tunkan su fara magana harya qosa da maganar "Ammm cewa nayi kin iya tuqi kuwa?" Bataji dad'in yanda yae ba amma jiki a sanyaye tace "Ea na iya amma automatic kawai ban iya manual ba" jinjina kansa yae kamar tana ganinsa "Kije gidan cen tunda key yana hannun ki ki shiga bed room d'ina ki duba a drower mirror akwai key's na motocin gidan farar jeeb dinda ke gidan kawai ce auto seki dauketa, idan ackin qannenki maza wanda ya iya tuqi seki bashi benz black sabida hidin dimun gida ke kuna ga naki hidima, sannan kuma gobe zan aiko kamala dukkanin abu nawa dayakeda muhimmanci agidan nan ze kwashemun shi zuwa sabon gidanki na sokoto, ku koma wannan gidan keda en gidanku da kowa ma, amm sannan kuma akwai d'akuna biyu acikin gidanki na kano dava komai aciki yaya kikeso ayi dasu, a zuba wane color zan kira company tun ban manta ba, amma se kuma nangidan shima daki biyune da furniture sauran tile ne kawai me za'a saka zanwa wani company magana a sokoto yazo yae wannan gyaran" Godiya taita masa kantace "Dan Allah Maheer hidimar nan tayi yawa ka taimaka kabarshi a hakan zamu saka anan din, Allah ya saka da alkhairi yabar qauna na kanon ma inda aka gyara ya wadatar" Shiru kamar bazeyi magana cen se kuma yace.. "Amm dan Allah salaha karkice zakiyi bidi'o in nan wlhy samun lapiyar hafsa ce a gabana, ki taqaita zanzo iya dinne kinji babyna, idan zakiyi jmahagulgulanki kiyi amma karkice ban zoba" Numfashi ta fesar ."Dinner da walima kawai zanyi karka damu, se magaana ta gaba yaya zancen tariya sokoto ne ko kano" gyaran zamansa yae "Kano za'a kawoki Mana ai nanne garinmu, abu na biyu sokoto sabida nan nakeyin aiki dole mu koma sannan na sanar dake bazaki ci gaba da karatu bako? Zan miyar dake wani skull daban bansan wannan yawon" haka taita binsa da toh har sukai sllam, annan ta durqushe taita kukan wahalar data daukarwa kanta... Lapia lau aka wa hafsat aikin qafar anyi nasarar daurin sedai fa dawuya be karkace ba se wani hukuncin na Allah. *************** Yau Ameen da ummul suna zaune a parlor ya hade girar sama data qasa, tamkar be taba dariya ba ummul ta kallesa tace "Yaa Ameen banida lapia ciwon mara nake da yawan tashin zuciya gashi daga zaran na zauna kome nake se bacci" wani annashuwa da annuri ya bayyana a fuskar sa na lokaci d'aya ya kalleta "Auu haba, barin kira miki Familu Dr. Dinmu ko" kallon mamaki take masa yanda ya sauya to ciwon nata ne abun murna, haka Dr. Yazo ya duba ta ya tabbatar cikine da ita 2 months mamaki ya kama Ameen shida yake da saurin gane ciki, kodan tayi period se biyune ya sanya yake tunanin babu, ya kalli Dr. Din "Takan yi period fa yallabai yazace ciki har 2 months?" Murmushi Dr din yae "Zata dena ne wasu matan sukanyi hakan, so kawai ta dena aikace aikace cikinta baya so shisa take ciwon mara" ranar murna awurin Ameen ba'a magana aikam hafsat har abinda ba'aso seda aka mata!! Kanta ya d'aure ta soma tunanin anya nrman haihuwabaure da watanni biyu hankaline kuwa? Amma dai dukda haka zataga qarshen abin. Mom Nua'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* *Assalamu Alaikum...masoya kuma makaranta wannan novel din ina me baku hakurin abinda zan fada, dan Allah kuyi hakuri daga page 20 na jiya nadena baiwa kowa daga farko, inasha wahala wurin turawa gaskia, dan Allah dukmeso ta nema a group kotaje wattpad nagode sosai da qauna.* *Maman Ramly wannan shafin nakine kyaita, ina godiya sosai da comment*

Chapter 9 of 20