Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciwo haka ta sauka daga steps din a hankali da zummar barin hall d'in...tsohon lecturer dinne yace mata "Hafsat kisameni office yanzu" jiki a mace ta juyo tace "Ok sir" tsaki maheer yaja wanda tasani da ita yake, shi kuwa a ranshi yace wannan me mugun girman kan tsiya kyaji dashi"..... A gafarceni najina shiru, rashin lafiya nai amma na samu sauqi Alhamdulillah. Mom Nu'aiym ce. *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*                                       02 **********      "Wainikam Islam ina zakijene haka? Goman dare yarigada ya wuce fa? Kuma sanin kankine munada test gobe morning abinma daya sanya nazo hostel kenan sabida in sanmu nutsuwar karatu" tsaki taja ta kunna turaren wuta me dad'in qamshi ta tsuguna aciki bayan ta lullub'e jikinta da barko batare data kulata ba, ita kuwa da abin magana baya isarta se cewa takuma yi "Islam wainikam kinawa kanki adalci kenan kike gani? Kinawa iyayenki adalci kenan islam, bakya jin tsoron Allah kenan islam, bakya gudun mutuwar ki tazo miki kina cikkn wannan halin, bakya tsoron cututtukan zamanin nan, bakya gujewa fad'awa cikin wutar Allah, bakya tsoron 'yq'yayenki su tambayeki game da rayuwar daza'a   goranta musu kinyi islam? Dan Allah islam ki rufa mana asiri ki dawo hanyar daya dace" miqewa tae "Ki adana kalamanki Nancy!!! Wata qil zasu miki amfani anan gaba, idan kuma zaki dauken lalurorin dake kaina ne na komai sena fasa sana'ata na zauna kimun su, gaskia wlhy kin soma isana huldar nan fa bawai dole bace kuma ina qabarinki daban nawa daban? To meye na damuwa?" Qwallan ta ta share daya silalo mata bata qara cewa komai ba.....Allah ya gani tanason  Islam bata mata fatan fad'awa halaka amma yazatayi iyaye suna suke taka muhimmiyar rawa wani xubin wurin gurb'acewar tarbiyan yaran su.... Babu me kulawa da karatun Islam, babu wanda yake damuwa da suturunta babu wanda ya tab'a cewa islam ina kima samo abu kaza!!! Yaya tarbiya zata ingantu? Yaya yarinya bazatabi ko wacce iriyar hanya ta nemi kud'i ba??..... ********    Tunda ta soma cin hanyar motar ke biye da ita tana yin tata tafiyar tamkar hawainiya.... Ba ai mata magana ba kazalika ba'a dena binta ba, tundaga gate din na jami'a har zuwa gidan man ada!! Ganin ta yanki dogon titin Rima Tv dayake tsit ya sanya ma mallakin motar yaje yae parking a gaba da ita kad'an kana ya bud'e motar tashi qirar range rover 2018 black wuluk ya fita, ji yajingina jikin motar  ya hard'e hannayenshi  asaman qirjinsa yana nazarin tafiyar nutsuwar da yarinyar keyi, yanda tae tamkar ma bata gan shiba shine  abinda yafi bashi mamaki dabita sabida ya saba harka da en matan jami'a wannan slow dayaje badole seya tsayar dasuba su zasu tsaya har sumai tayin number wayar su kuwa, gabanta yasha yace "Kenake bi en makaranta Ina san zanyi magana dake kina mun yanga, dan Allah ki bani time d'inki" ya soma furto maganar tamkar  wanda akawa dole" rausayar da kanta tae kantace "Bana saurarar mazaje a bakin titi, bana magana da maza akan hanya, gidanmu babu nisa danan wajen amma idan ka matsu zaka iya ci gaba da bina zuwa qofar gidan mu" kallon mamaki ya bita dashi, tsakani da Allah kuwa tai tafiyarta ya jima yana kallonta kanya tashi motarsa yabita a baya..... Yaso ya basar amma ya kasa,yaso ya wuce abinshi  amma yarasa dalilin dayisa zuciyarsa take azalzalarsa akan yarinyar dako fuskarta be tab'a gani ba kasancewar da niqabi sanye a fuskarta ga madubin data sanya baqi wuluk ta rufe idanta dashi......har duka isa qofar gidan yana biye da ita, ita kuwa tae shigewarta ta barshi a waje yana mamakin hali irin nata!!!!! Ganin yafi 20 mns tsaye bata dawo ba ya sanyashi kiran wani yaro yace dashi.. "Kasan budurwar dake nan gidan yaro?" Kallon sa yaron yae "Susu biyu ne se qaramar su, Akwai Ummul akwai kuma Nanuwa wacce aciki?" Shafa tsajensa yae "En matan guda biyu inaga daya ce daga cikin su a jami'a take kaje kamun kiranta bansan sunan taba, amma dai ba jimawa tashiga gidan kace nace wacce take sanye da niqabi da mudubi acikin kalar kaya koraye" juyawa yaron yae yace "Na santa barin maka kiranta" Da sallamar sa ya shiga cikin  gidan ya had'u da baba azumi "Baba wani ne awaje yana jikin motarsa yace amai sallama da wacce tashigo yanzu da niqafi da madubi inaga kamar nanuwa yake nufi" zabura tae jin an ambaci kalmar mota ta riqe hannun yaron da ake kira da suna ilu ta leqa waje da hannu ta nuna mutumin tace "Wancen na jikin wancen bakar qatuwar motar?" Murmushi ya mata yace "Ea Baba azumi shine wancen" washe haqora tae "Jeka kace tace gatanan zuwa" yaro ya jiya ita kuwa taje ta janyo hannun Ummul "Er qwarai jeki ki ari kayan Nanuwa har niqafin da madubin ido ki saka, wani me qatuwar motane ya biyota ya aiko yaron ko sunanta be sani ba, kinga kuwa zamu samu damar qwace shi wataqil ko gaisawa basui ba yaga ta shigo ne ya aiko kiranta" murmushi ummul tae seda haqwaranta suka bayyana tace "An gama hajiyar ummul barinje" Duk abinnan dasukeyi a kunnen Nanuwa ita dariya ma suka bata ta sani, dirinta kawai dako a hijab seya bayyana ne ya gayyato mata wannan mutumin data kasa yadda da nutsuwarsa da kamalarsa duk basui mata ba! Ita kamma aita huta dasuka rabata da shi salun alun haja ta shige toilet yin wanka yayinda Ummul ta sace kayan tafito dasu....d'akin Baba Azumi taje ta sanya kayan sannan ta fita waje....kai tsaye gun motar da Baba Azumi ta kwatanta mata ta nufa taje ta kalleshi "Sannu da zuwa bawan Allah" haka kawai seyaji muryan kamar ba wancen data mai magana ba d'azu yanayin sautin cikin nutsuwa yasha banban sosai da wannan gyaran tsayuwarsa yae "Kece kuwa?" Kallonshi tae daga cikin madubi wanda ya qara d'aura kokwantan shi akanta domin waccen bata kallon sama ya kula da hakan daga yanayin tafiyarta da kuma sanda take mar magana sam bata kallesaba, maganarta cikeda sanyi take yinsa amma wannan sauyin na miye haka?" "" Wa kace kake nema ne bawan Allah? Ina wacce tashiga gidan ba dad'ewa? Kodai Nanuwa kake magana nama sallama da ita? Koda yake batada lapia yau duk a kwance ta wuni,da wuya idan zata iya fitowa,sedai ko zaka dawo wani lokacin" da sauri ya dakatar da ita "Ko d'aya ked'ince dai, indai wacce ta shiga gidan ce da wannan shigar kuma, muryan ne kawai nake kokwanto,koda yike dazu kincene akan hanya ne bazaki tsaya ba" gyara tsayuwarta tae "Tonikam yaya zan zubar da mutuncina na tsaya yin magana da wani akan titi, nan din dai yafi ko" murmushi ya sake mata shima "Hakane amma to yanzu fuskar fa, zan iya ganin mamallakiyar zuciyar data sacen tawa tunkan nae tozali da fuskar?" Murmushi tae acikkn niqafin ta soma zare gilashkn idanta kanta yane niqafin gaba d'aya ta bayyanar masa da kyakyawar fuskarta me d'auke da qayataccen murmushi, shakka babu ummul kyakyawa ce ta nunawa sa'a ma kuwa,sedai asaran hali da akae, da qyar ya saisaita nutsuwarsa yace "Sunana Al-Ameen amma anfi kirana da sun yaro da kud'i!!! Ina fata na miki danni kinmun kuma bawai da wasa nazoba aurarki nakeso nae idan kin shirya kuma na miki" wani murmushin ta qara saukar masa dashi "Kamun yaro da kud'i!! Kuma nima da gaske nake ko gobe ka shirya kazo a d'aura" dariya ya bushe da ita "Allah en mata" itama tana dariyar tace "Allah kuwan d'an samari" dariya suka qarayi sannan ya miqa mata wayarsa yana me rungume murfin motarsa dayake a bud'e tun zuwansa yana binta da wani kallon shaqiyanci, "A zuramun digit inason naci gaba da jin wannan zazzaqar murya a kowane lokaci" ba musu ta cafe ta zura mai ya karba yae saving tare da kiran layin nata,wayan yae ringin ya kalleta ."Na saka miki sunan wife to be a wayana,ga nawa nan ki bani husband to be ko kuwa?" Murmushi tae wanda tun zuwanta shine a fuskarta "An gama Yaro da kud'i..... Koda baka buqaci jin sunana ba zan fad'a maka, sunana ummul khulsum" hade hannayensa yae...."Afuwan Babyna zumudi ne ya hanani tambaya" taji dadin sunan daya kirata dashi matuqa ta washe masa baki.....ya zaro rafar dubu d'ai d'aya a motar sa har qwaya biyu ya miqa mata ba wani musu ta karb'a yace "Aje a sauya waya, bansanki da wannan qaramar wayan, kuma a mun kwalliya kafin wani satin idan nazo, savida zan shiga jeji zan kwana biyu ban zoba" kalmar jeji ta nanata a zuci kan tace "Me zakajeyi jeji sekace mafarauci?" Dariya yae "Mafaraucinne kuwa, aikin dazanjeyi jejin kenan farauta, amma bata dabbobi ba" a wasa ta dauki maganar sa wannan ya sanya tace "Allah ya baka sa'a husband to be" "Naji dad'in adu'arki babyna....kuma ko yanzu kasuwar ta watse d'an koli yaci riba ai" kallon sa tae da rashin fahimta,ya d'age masa girarsa d'aya "Ea mana babyna, nayi sa'a had'uwata dake ai sa'a ne musamman yin na'am dani dakikai haka da sauri wannan shine babbar nasarar danai a rayuwata" taji dad'in zuzutatan dayae ta masa godiyar jin haka, daga haka sukai sallama ta juya tana sauri taje ta gayawa Baba Azumi yau dai ga dubu dari biyu har cikin gidansu!!! Al-ameen kuwa yau farin cikinsa ya ninka na kullum yau yafi komai yin sa'a ya bada d'ari biyi ya tabbatar seta zama miliyan d'ari biyu!!!!! Mom Nu'aiym ce. *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 06. Kallon shi class rep d'in yae, "Sir kudinnan yayi yawa dan Allah ka rage" murmushi yae "Malam mahmud nina baka fa, agogon ma zan kawo maka qaraminsa wanda bazaka siyar ba😁" murmushi ya sakar masa "Allah ya qara girma da d'aukaka Sir, wannan ma ya wadatar, Allah ne kad'ai ze biya da gidan aljannah, dan wlhy ina cikin tsananin buqatar abin ka bani, na sani adu'a dana keyi ce,Allah ya karba...." Murmushi yae ya daki bayansa yace bayan sun soma tafiya zuwa class din yana riqe da hannun sa "A hostel kake zama?" Gyad'a masa kansa yae Alamar e yace "Kai d'an sokoto ne?" Ya sake wurgo masa wata tambayar "E Sir anan nake sedai gidanmu yanacen badon hanya, yayi nisa sosai da makaranta bazan iya daukar nauyin kaina zuwa da komawa ba, shisa kurin na dawo hostel din" jinjina kanshi yae "To karatu kawai kake baka wani aikin hannu?" "E malam banayin komai se karatun nan, shisa muketa shan wuya ga maraici kuma" murmushi yae "A gidana akwai laundry area da washing machine har guda biyu da kuma iron da komai na drying tufafi, sedai bame wankin nayishine dan kaina kariqa zuwa sanda free qarshen sati kamun wanki da guga kuma kana iya karbar na wasu ma kana zuwa cen kanayi tunda da engine ne,kaga a memakon zaman banza ka samu abinyi ko befi maka ba?" Zubewa yae a qasa yana zuba masa adu'a da godiya,sake riqo hannunsa yae suka miqe tsaye yaci gaba da riqe hannun nasa har zuwa a class, a tare suka shiga kowa se kallon Maheer yakeyi, seda suka tsaya yace "Idan an tashi lecture seka bani Number, ranar saturday senazo na kaika gidan" godiya ya juya ya haye saman, haka aka kammala lecture d'in suka juya zuwa gida issy se satar kallon sa yakeyi... Sun ajiye da class rep akan shine zezo gidan ranar sati dayike ya masa kwatancen gidan, shi kuwa ya kama hanyar gida.... ********* Nisawa Issy tae dajin wannan zancen na mahmud bayan da ya kammala bata labari "Lallai kam Mahmud kayi dace, Sir Maheer yanada matuqar kirki gaskia, ban taba ganin mutum irinsa, bari na baka 7k d'inka danama alqawari" girgiza kanshi "Sanadinki na samu kyautar dubu hamsin, sanadinki na samu aikin dana jima ina neman me kamar sama ban samu ba, ko 3 k d'inki zan baki abinki yanzu bare kuma na qara wasu" dariya tae "Naji bazaka karbi 7k ba amma nima bazan karbi 3k ba rabon kane Allah ya saka da alkhairi kaidai" murmushi yae ya qara yi mata godiya . ************* Tafiya suke zuwa mini mart a wahalce sabida sosai Nanuwa ta gaji ga uwar yunwa, mini mart zasuje Islam ta kalleta tace da ita "Nanuwa naga se shiga da fita kike cikin sababbin kaya da hijabai, naga kin dena sanya hijabin nan meje da qasa meye sirin?" Murmushi tae acikin niqafin ta tace "Ai wannan ma ya wadatar yadi uku da rabi ne,kuma kinga yanzu Ummul tabani kayanta da yawa inada suturu shine na musu hijabi ko wane kaya da kalar hijabin sa, nama manta ban nuna miki ba, Mijin da Ummul zata aura ya siyan min waya samsung" wara ido tae ta d'aka mata duka a baya tace "Ke shine bazaki nunamun da wuri ba, mu wuni a tare kina qunshe da waya a jaka miqon na gani" zaro wayar tae ta miqe mata adaidai sanda zasu tsallaka titin daze sadasu da mini mart d'in ta daka tsalle har tana rungumeta "Shegiya qawa, kin shigo gari, haba kokefa amma da kin tsaya kina wani noqe noqe, ni dazakibi ta tawa dakin shige cikin jerin matan dake d'ebewa kansu takaici ta hanyar neman na kai da jikinsu" b'ata fuska tae kan tace wani abu motar maheer ta paka a gabansu, Islam ta ganeshi amma sam Nanuwa bata gane shiba...... Sauke glass yae yace "Islam zonan" matsawa tae kusa dashi ta sunkuya yace "Ina zakuje?" "Sir mini mart zamuje cin abinci" "Idan bakuda wani lecture kuzo muje town mana, sekuci acen" mayarda dubanta tae zuwaga Nanuwa ita kuwa ta had'e ran nan "Kizo muje town muci abinci acen ina dama kince yau town zaki kwana" qara had'e rai tayi dukda bata ganinta tasan halinta koshima yagano batason zuwa ne amma bece komai ba "Muje mana" Islam ta qara fad'a sosai taji haushi ta bud'e gidan baya ta zaune tare da cewa "Barka da yamma sir" be kulata ba sam, haushin ta yakeji matuqa,ta faye girman kai banza da ita takewa mutane raini...... Ita kuwa ta gama quluwa da rainin wayon dayazo mata dashi... ********** Kai tsaye gidansa dake sama road ya wuce dasu, batare da tunanin komai ba, be kuma nemi izinin kowaccen suba, a harabar gidan yae parkinh inda Islam tabi tsala tsalan motocin dake gaban gidan da kallo, shakka babu wanda dasuke ciki iri ukuce, ga wasu guda 4 manya manya a gefen ta, da murmushi ya kalli Islam yace "Oya muje ciki kuci abincin" kallon Nanuwa islam tae tace "Nanuwa nasan ba zab'in ki bane yin hakan amma dan Allah karki ce bazaki shigaba, Sir baze cutar damu ba" hawaye ne ya kwaranyo mata, taga ganin lokaci yayi dazata dena qawance da islam, tunda har tasoma kawota gidan maza shida kanshi ya kula da kukan datake kasancewar niqafinta ya jike sharkaf,amma seya dauke kansa ya janye jikinsa daga cikin motar ya basu space sui magana Shi sam bega abin tada jijiyoyin wuya anan ba....kallonta islam ta qarayi "Karki mana haka anan Nancy, ki fito muje dan Allah" batace komai ba ta b'alle murfin motar ta fita itama islam suka d'unguma cikin gidan a tare a parlor ya ajiyesu ya zauna shima ya daura qafarsa d'aya kan d'aya , hotunan sane da mahaifinsa birjik a parlor a manya manyan frames an ajiyesua qasa wasu kuma bana ne sunyi kyau sosai, Nancy ta gano dalilin samuwar kudin Sir Maheer ganin pic na mahaifinsa yaron me kudin garin su gaba daya dolene ai....wani sukaga ya fito ya durqushe a gabansa "Yallab'ai barka da zuwa" murmushi yae ya miqa masa hannu "Kamala ya gida Yaume ka girka mana,ka ganni da baqi" "Ranka ya dad'e favorite d'inka ne dai gashashen kifi ne da farfesun kayan ciki da moi moi da jollof rice,se kuma na had'a maka zob'o kan kankana da kuma cucumber😁" jinjina kanshi yae yace "Akai komai dining kuma akawowa baqi lemuka ba lallai zob'o suke so kamar niba" da sauri ya miqe zuwa ciki shi kuwa wayanshi dake ruri ya d'ago yana ganin umma ya shagwab'e fuska "Umma nayi fushi" dariya tae a d'aya b'angaren "Haba shalelen umma yi hakuri kaji jiyan na kwana da ciwon ciki, senaita rankon bacci shine fa ban tashiba se azahar se ya zu na nutsu" rud'ewa yae "Me kikaci umma? Kinje asibiti? Sosai yake miki ko kadan? Ko nazo kanon ne yanzu umma?" Murmushi tae "Bakaji nace maka nayi rankon bacci ba ai sauqin kenan dana samu karka damu kaji na samu lapia" qara narkewa yae da shagwab'a "To amma Umma shine baki kirani ba da daren insan halin dakike ciki" "Kaga Maheer bafa komai bane ba, yanzu seka tsiri rigima ka girma kana shagwab'a" ci gaba yae da sakuwa da qyar ta rarrashesa sukai sallama, ko waccensu ta sake bakinta tana kallon ikon Allah sekace wani jinjiri,ya dinga wannan abin, kamala yazo ya zube agun "Yallab'ai dining kai yake jira" miqewa yae lokaci d'aya ya kallesu "Kuzo muje" a tare suka miqe, suka isa dining din Islam se zuba take tana yaba kyawun gidan "Idan kika tashi aure zan baiwa mijinki kyautar irin ginin na saka miki kayan gida irin wannan" dariya tae "Kacika zolaya sekace gidan kwali irin na wasan yara, kawai dai na yaba ne" itadai Nancy ta kasa sakewa se tsakurar jollof rice d'in takeyi a hankali ga wahala seta d'age niqafin ta take sanya loma abakin ta.....su kuwa se hirar su sukeyi cikin nishad'i har suka kammala Anan dining suka barta suka wuce warsu cikin parlor anan ta samu sakewa ta yane niqafinta tayi nak har kajin taci sosai tasha lemo da zob'o sannan ta wuce ta samesu" sun dad'e har kusan magrib se a sannan Nanuwa tae magana "Inaga Islam zan wuce na barki gaskia sabida magrib tayi kinsan Halin Baba" miqewa islam tae "Sir mun gode sosai da karamci fa, Allah ya saka da alkhairi ya qara bud'i" miqewa yae yace "Ku xauna ina zuwa" zama sukai ya juya cikin cikeda qasaita kai kace wani basaraken ne.....da wata madaidaiciyar leda ya fito ya miqawa Islam yace "Ga wannan kuyi hakuri ba yawa, ya d'aura envelop saman leda data runguma yace wannan ma kwa siya kati na gode sosai da kuka amsa gayyatata Allah ya sanya albarka a karatun, hafsat na gode sosai" murmushu ta masa ya kula da hakan suka d'auki kaya niqi niqi suka fice har sunkai qofa ya daga muryarsa "Islam zo mana" juyawabtae zuwa gunsa yace da ita "Idan kunje harabar motocin dake waje zakuga kukun gidan nan, ze kaiku gida, amm kuma ki bani digits naki mana" tana murmushi ta dire mai ta juya abinta,kai tsaye gidansu Nancy aka diresu suna yin magrib suka duba envelop sukaga dubu hamsin rafar dari biyar biyar...sunsha mamakin hakan suna bude ledar sukai karo da laces masu kyau daya red daya blue, se flat shoe guda biyu suma iri daya, sunsha mamakin gidan ba mace namiji ma ke girki to ina ya samo kayan mata? Basuda labarin d'abi'ar sace kyauta sabida haka baya rabo da kayan kowane jinsi harna yara, ko gidansu dake kano danginsa sunfi so a rayuwa su ganshi idan sunje gidan har kayan yara yake ajiyewa mace ko namiji...... Ameen ya d'agawa Su Ummul hankali akan za'azo neman aure baze bari iyayensa suzo suga wannan gidan ba, sedai sun koma samaroad yana fili ze sanya a gine shi ya basu kyauta, Baba iro ne yace dole sedai idan gyaran gidansu se musu amma baze bar gidan sa na low cost ba, haka kuwa akai suka koma gidan babar su baba iro kakar su Nanuwa kenan aka soma gyaran gidan. *Waye Al'Ameen* Al'ameen maraya ne bashida uwa bashida uba a duniyar nan, qanin mahaifinsa shine ya renesa shi kuma Allah be tab'a bashi haihuwa ba abin kuma daga gareshi ne, shisa yake jida Al-ameen kamar ransa, shine ya sakashi a gurb'atacciyar hanya, auren yaran mutane yake sakashiyi gari gari idan an aura se'a gudu da yarinyar jeji sunada gidajr acen amata ciki da zaran ta haihu a siyar da jinjinrin tanayin arba'in kuma a sake danna mata wani cikin haka sukeyi wannan itace sana'ar Amin, bama shiba har yara maza sukeda dasuke sato mata suzo a kaisu gidan jeji a qarqame a danne idan sunyi ciki sun haihu a siyar da yaran mutane!!!!!! Ana sakrwa matan kudi ne kuma har tsafi sukeyi sunada bokansu baya bari sui sallah ko ina se a wannan gidan na jeji shisa basa sallah dole se jeji!!! Mom Nu'aiym Inata wankin laifi ga shafi na biyu saura na uku😍😍😍 *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 05 Tsaki Ummul ta saka ganin me kiran wayarta ta mike zuwa waje batare data dauki wayar ba, tasani Mahal ne kuma yana waje dama ya mata saqon texy message nacewar zezo, a tsaye qiqam ta tsaya masa aka tace "Menene na damuna ina karatu ne wai Mahal? Nafa rigada na sanar maka nidakai sekuma wani ikon Allah" qura mata kyawawan idanuwan sa yae cikin kasala ya furta "Yanzu ummul duk girman soyayyar nan damuke wa juna haka kike shirin tarwa tsashi? Kina ganin cewar soyayyar damukewa juna ta cancanci ai fatali da ita lokaci d'aya?/ anya na cancanci haka a wurin ki kuwa ummul? Idan ke baki dauki tawa soyayyar da muhimmanci ba nina d'auki taki fiye da hakan bazan rayu ba idan baki" tsaki taja masa "Ban yarda akwai soyayyar da kud'i basa siyaba yallab'ai, naga kud'i na siyar da taka soyayyar ma waninka! Bana qaunar koda ganinka ne wlhy nadai rayu dakai ada sabida banida na sama yanzu kuwa na samu wanda yae maka zarra sabida haka kowa ya kame gabansa" kasa koda qiftawa yae sanda ya qura mata ido, duk yanda yaso karya yae qwallah seda ta silalo masa sosai yake son ummul, cikin takaici ya furta "Ki taimakeni ummul, zan baki dukkanin abinda kikeso a rayuwa, zan wadataki dajin dad'i me d'orewa shekaru uku ina tare dake bazan rayu ba idan bake ummul" "Wane jin dad'in zaka bani Mahal? Bayan tun ina gidan mu kyauta tsakanina dakai be tab'a wuce dubu hamsin ba, idan naje gidanka me zanci? Anan kuwa inada me bani har dubu d'ari biyar kyauta be girgiza ba, kaga Mahal nifa banso na yaudari mutum dan Allah kai ta kanka, ka mance dani a rayuwar ka kurun" tashi tsaye yae daga zaman dayake acikin mota ya fuskance ta sosai "Ina sonki sosai ummul ina matuqar qaunarki amma ki sani koda baki gujeniba bazan iya aurar mace irin kiba yanzu danasan halinki, ke makwad'aiciya ce kuma had'amammiya ke karyace mebin abincn qasa kinaci, ki sani a yanda rayuwarki take u can easly kill a being for money, irin kune masu zama en yankan kai sabida kud'i....nagode Allah daya nunamun halayenki munana tunkan naje ga auren jaka irin ki, kije keda Allah kuma yaudarana da kika jima kinayi Allahu ya sakamun Allah ya isa ban yafe ba" tsaki tae ta juya tae shigewarta cikin har tana wurgo zagi "Dama akwai uban daya sanya ka kyautar ne dan iskan kawai" bece komai ya shige motar sa ya mata key😭😭😭😭. ********** A class se ihu akeyi ana gaddama akan wani wani topic dasuke na chimp's da gorilla's, Maheer ne ke d'aukar course me suna psycholinguistic's......sosai ake fafatawa da class rep da kuma Nancy yana gadda akan lallai dabbobi ma suna magana irin ta mutane, ita kuwa ta kafe akan ba haka bane....sosai ta burge Maheer yau kawai a rayuwarsa ya dakatar dasu yace class rep d'in "Menene hujjar ka na cewa hakan? Since ya zama debat" murmushi yae yace "Sir dia was a chimpanze that was raised in human and thought only human language for 5 yrs her name was Nala and was able to pronounce few human word's that is papa,mama, cup, up and down.....so with this nake ganin ganin cewar suma suna magana and not only Nala akwai gorilla's dayawa da akai renon su acikin mutane and were all able to speak human language even though it was'nt fluint" class d'in ne ya d'auki tafi raf raf raf!!!!! Maheer ya jinjina kai dukda yasani cewar hujjar sa tayi qaranchi...mayarda dubansa yae zuwaga Hafsat yace "Ke kuma meye hujjar ki?" "Sir hujjoji da yawa kawo

Chapter 2 of 20