Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita "En mata kefa ya sunanki" wani sanyi taji a ranta "Sunana zulaiha"jinjina kansa yae " zoto ga wannan ki riqe muku, idan zaku tafi kwa hau abin hawa" tana wani rangwad'a taje ta karb'e rafar d'ari biyar biyar da aka basun tana godiya godiyar sukai banda Nancy dakejin takaicin maheer ko a ina seya nuna cewar shid'in wanine ta tsani wannan show up d'in nasa......haka suka shige gida har yamma yana jiran acc details amma babu alamar sa seya tsinci kansa da damuwar daya rasa dalilinsa... ************ Nancy Amma dai kinsan baki kyauta ba ko, har yanzu tura acc details ya gagara idan bazaki yiba niki bani number dinsa dake wayarki na tura naga alamar ke er baqin ciki ce wlhy, yanzu ina xega bank after 5 kuma kin sani sarai ina buqatar kudin nan ko me decor half kurin na bata" murmushi tae "Kiyi hakuri wlhy shap na manta, yanzu zan tura" juyawa tae batare datayi magana ita kuwa ta lalubo Number tada rubutawa suna "Show up" ta tura masa acc details nata na GTbnk tana mamakin dagewar sa akan lallai se acc number nata yake so..... *********** Maheer kwance asaman kujerar dake parlor sa yana kallon wani korean series me suna Rebels film din yana masa dadi...jin qarar shigowar saqo a wayansa ya sanya ya tsayar da kallon ya duba wayarsa, kai tsaye transfer na 2.m yayi ya ci gaba da kallon dayake cikin nishad'i...... Ta jima sosai tana nanata karatun zirurrukan dake gaban 2 d'in bayanda alert d'in ya shigo mata kanta miqe da saurinta zuwa part d'in su Ummul.... Zama tai kusa da ita "Ummul kalli wannan alert daya shigo da sunan wannan abokin na Yaa Ameenu.... Wak kaman fa 200k nake gani 2.M ne?" Da sauri Ummul ta karb'i wayar ta duba ta miyar da dubanta zuwaga Hafsat "hafsat 2.m wlhy yanada kai kuwa?" "Oho dai nima dai nace ko kusjure yae ne" gyaran zamanta tae "Nasaka subamu 500k gaskia shine ma budget dina amma wlhy ban sakaran ko 1. Ba,kinga kirashi a waya kiji ko kuskure yae, ni Ameen dama yamun gargadi akan kiran ko daya daga cikin abokanansa,beside ni ban tab'a ganin abokansa bama se Maheer da wani Salah" gyaran zamanta tae ta soma dialing number sa "En mata yaya dai" ya fad'a daga bangarensa "Barka da yamma" murmushi yae kamae tana gabansa yace "Barka dai en mata ya kike ya komai, ina fatan kun samu saqona" "Ea saqonka yazo mana, amma munga kamar kayi kuskurene kudin yayi yawa" gyaran kwanciyarsa yae yace "Ina Amaryar tamu?" "Gata a kusa dani" ta basa amsa a taqaice "Ok ki sanar mata nace 1.m shine kudin dana bata na shagalin bukukuwa 1.m kuma tawa gudummawarce kyauta na bata kinji" Godiya tayi masa sosai sannan sukai sallama ta gayawa ummul yanda sukai ummul uwar er san kudi se murna ake tace "Ki dauki 100k ki turamun 1.5 m dama Baba ze nemo kudin abincin da season 7 zasu mana ki bashi 400k din data rage ni zanyi sauran abubuwa ke kuma kya karbi din kunanki ko?" Godiya ta mata tace "Amma kinsan fa acc din nawa,bazan iya cire kudi da yawa haka ba, amma goben zan baje bank nayi withrawing nasu duka" murna suke susu biyu a abinsu,ummul ta gayawa Ameen shima ya kirasa ya masa godiya yace ai yiwa kaine..... *Menene alaqar dake tsakanin Maheer Ameen?* Maheer yarone me tsananin qwazon neman na kansa, mahaifinsa kuma baya hanashi shiga sabgogin neman kudin sa da kasuwan cinsa, ko sanda yake zaune a turai sam be zauna a banza ba, acen ne ya had'u da Ameen a wani zuwa da yae china sarar wasu kayan decoration da bama samu a Niger shi kuwa Ameen yakanji yaran na qasar shangan dake china shiya taimaka yake saka baki inda rashin iya turanci ya shiga tsakainin Maheer da abokanan kasuwan cinsa wannan ne ya sanya alaqa me kyau tashige tsananin su, har yau Maheer besan gidansu Ameen ba amma shi yakanje har gidansu a runaninsa ma auren farko ne zeyi, jin yana sokoto ne ya sanya Ameen ya janyo Maheer ajiki ya san sa da matuqar san kyauta !! Dama ya gaji da kashewa Su Ummul kudaden sa beko saniba ko zata haifa masa yara da yawa, sabida biyar yakeso ya siyar a miliyan dari biyar biyar yasan zeja kaya..wannan kenan. *********** Washe gari Nancy tai shirinta tsaf na zuwa banka domin withdrawing kud'in dake bank d'in daya turo dama tana san qarin lace na sakawa ranar dinner tana ganin rashin dacewar shiga cikin en anko gashi ta samu 100k na 50 zata siya ta cancare abinta acikin qawayenta, ga kayan jikin mamanta ganinsa ya bata takaici ta kula har qaninta tanada wata er dubu 40 dayike tanashan kyauta awurin Aminu tace bara itama ta siyanmata kona 25k ne da atamfofi qanana guda biyu takai a d'inka mata kan wednesday ta siyawa qanin ta maza qananun kaya bazata iya ganin mamanta kamar jaka ba...bayan ta cira se kuma period ya mata dirar bazata wannan ya sanya ta sauya akalar zuwanta kasuwa ta juya gida takai kudin Ummul idan ta kimtsa seta fita zuwa kasuwar. *********** Bayan kammala shirinta tsaf tabaiwa ummul kud'd'enta seta juya zuwa kasuwa sabida tau takeso ta kaiwa suhailu tela din kunan kozata dace, dazata samu sarari ne data dinka da kanta amma ba halin yin hakan.....kai tsaye gate ta nufa domin ta nemi adaidaitan daze kaita kasuwa..... A qofar gidan taci karo da Maheer zaune a saman motar sa ko yau din batada zab'in daya wuce ta gaidashi dole ta matsa daf dashi ta qaqaro murmushin dole wanda baya ma ganin fuskar tata sabida niqafin data adana fuskarta aciki "Sannu yaa Maheer ina wuni" "Lapia qalau Hafsat ya gida ya shirin biki?" Murmushi ta sakar masa a karo na barkatai "Alhamdulillah" "Dama saqo na kawo miki, atamfofin yayin bikine zaki rabawa qawayenku Ameen ne yace na kawowa Ummul inata kiranki baki daukaba, qwaya d'arine na en mata ne, se kuma ni tawa gudummawar takice gaba d'aya" shiru tae ya bude but bayan ya diro ya zaro wata qatuwar jaka, ya dire ya kira wasu yara susu uku suka kinkima zuwa ciki,ya zaro wata madaidaiciyar jaka me kyau yace "Ungo wannan nakine tawa kyautar aje a dinka aci bikin sister" kasa karba tae ya b'ata rai " Da Ameen ne yamiki kyauta zakiqi karb'a ne? Gaskia banason hakan idan baso kike raina ya baci ba ki karba kawai, kuma banaso nama kyauta wani ya sani dagani sekai se Allah" hannu tasaka ta karba ta dinga godiya seda ya tsayar da ita ta juya se part dinta acen ta bude dakinta ta saka ta rufe ta nufi wurin ummul tamata bayanin atamfofin ta zari nata dana Islam da wata qawar su farida sannan ta koma d'akin dan ganin meke cikin jakar. Mom Nu'aiym. *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *πŸ—ΏWATA FUSKAπŸ—Ώ* πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰ *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 12 Yafi mintuna talatin yana nazarin maganganun islam se cen ya dawo ya zauna ya muskuta da kyau yae gyaran zamansa yace "Amma islam kina cikakkiyar sallah biyar awuni kuwa" dukda bataji dad'in maganar ba amma seta tsinci kanta da bashi amsa kamar haka "Ina yi mana Maheer, meze hana nayi saah na taso agidanmu an koyar dani tsare sallah akowane hali" jinjina kanshi yae alamar gamsuwa "Amma kuma bakyayi akan lokaci islam" shiru ta d'anyi kan tace "Ea to anan bazanyi qaryaba wani zubin se magrib nake yin azahar da la'asar dinma gaba daya senai maja" kalonta ya qarayi "Amma aka gayan miko cewa haka ake sallah? Idan fa kabari lokacin sallah ya wuceka da gangan kashiga uku islma, mesa zaki miyar da rayuwarki kamar ta marasa ilmi? Kina ganin ko wannan rashin kiyaye sllah akan lokaci baze jefaki ajikin ibtila'in rayuwa ba? Ya dace ace kisan cewa ba'awa sllah hakan ai, wanda ma yake hada salloli yaushe zega time din yin adu'a tukunna ma yaushe rabonki dayin azkhar? Kokuma ki zauna kiyi karatun alqur'ani me girma tayaya zakiga haske islam?" Shiru tae tana tunani ita wlhy tun quraninta na islmaiyya bazatace ma ga inda yake ba, ko na app da ake turowa a waya bata taba ajiyewa ba kuma ita abinda yasa bata ajiyewa shine sabida yanayin abubuwan dake kan wayarta, soda yawa idan taje wurin gardawan bariki setayi kallon fina finan batsa takejin sha'awa, sannan wani zubin idan taje wurinau sesu shagala da zancen sallah ta kula dan zaman nan datae agida sosai take sallah sam bata wuceta to kenan duk musababbin shigarta wannan halin hadda mugun abun nan datakeyi....seda ya qara cewa "kinaji kinyi shiru islam nace yaushe rabonki dayin karatun alqur'ani ko Azkhar? Hawayen dake kan fuskarta ne ya sauka tace.. " bazan iya tuna tuna tun yaushe ba Maheer" nisawa yae yace " Manta wa da Allah tamkar qulla qawancene da sheda islam, baze taba barinki ki mori tsufanki ba, zega yanda duk zeyi ki lalata quruciyar da hannunki ta yanda tsufanki baze miki kyau ba, kazalika koda kin mutu kafin tsufan ki shige wutar Allah, banji dad'in yanda rayuwarki ta kasance hakan ba, dukda kome kika aikata a rayuwa tare da Suraj za'a raba a baki naki kason shima yaja nashi, ga kuma haqqin ki na cutarwar daya miki gashi shine mutumin farko da kika nemi ya aureki sanda nace kiyi hakan, ki kasance acikin istigfari ako da yaushe kije gida yanzu sena qara neman ki kuma" sakkowa tai tabi gwiwowinta tana kuka tace "Ka taimakeni Maheer ka rufa asirina, ka aureni wlhy idan baka banida amfani" murmushi ya sakar mata yace "Kije gida karki damu My Islam zanzo gidan idan na dawo kinji" godiya ta masa ta miqe yace "Zoki karba ki riqe a hannunki banaso wata buqatar ta taso dazaki nemi wani abu awurin wani" sadda kanta a qasa tae ta kasa koda motsin kirki bare ta karbi kudin seda ya mike ya saqala mata a hannu sannan ta juya Kamala ya dauki hanyar gidansu da ita!!!! ************ Yau auren Ummul saura sati d'aya wannan ne dalilin dayisa gidan nasu ya qara kaurewa da hayaniya da ihun mutanen qauyensu da en uwa dakuma abokanan arziqi!! Ummul na zaune tana d'aye selotop dake tafin qafarta bayan ta gama cire lallin gargajiyar data saka, farar qafarnan ta d'akko jan lalli se sheqi takeyi! Ata gefenta qawar Ummul ce Khadeeja ke mata zuba "Yanzu ke Nancy meya alaqanta ki da lallin gargajiya za'ai biki a gidanku? Bakya jin kunyama kizo muje gun zarah uwar zane mana ranar laraba ta zane mana hannayen mu da qafafuwa dubu uku ce kun rabu lapia" Kallon sosai ta mata tana murmushi "Zanjene ai kurun dai dama dole wannan nake farawa dashi, shisa ma nakeyi da wuri danna cire a tare" murmushi tama tai ta sunkuya sosai tace "Wai nikam Hafsat Anya ke ba balarabiya bace? Wlhy danice ke da duniya seta gama ganin wannan surar tawa, sumar kanki kawai seta b'ata wa mutum lokaci wurin kallon ta nifa aduk cikin jikinki banga inda Allah ya kuskure miki ba dama kuma shiba me kuskure bane yasan daidai...ummul ita muke zuzuta kyawun ta amma wlhy Nancy bawai buzuwa ba babu wanda baze yarda cewar keba balarabiya bace idan ya ganki" sakin lallausan murmushi tae . "Khadeejahh abeg jeki kiyi sallah abinki" ta qarashe maganar tana dariya......itama khadeejan juyawa tae tana fad'ar "Anyi baqi daga Niger naga wata mata me kamarki ga alaama maman kice" murmushi tae ta zata wasa ne yasa bata kulata ba seda ta gama tae alwahala ta nufi d'akin Baba Azumi..... Acen ta tarar mamanta da qannin ta sunzo mata...Baba iro ne ya aika suzo dan ya bata haushi sabida taga yayi kudi data gujesa, acewar sa dan bashida kudine taqi zaman aure dashi yayanshi dayakeda abin hannunsa ai basui haka ba ta zauna..... Murna a wurinta ba'a magana sam, mamanta ma taji dadin ganin ta se yare sukeyi na Buzayen Niger Baba Azumi se harare harare takeyi tana yatsina fuska!!..... ********** Duk saurin datake ya hanata d'aukar niqafin ta ayau dinnan, dama wasu lokutan takan fita acikin unguwarsu hakan......murna sosai takeyi tanaso taje ta siyawa mamanta Lemu tasani akwai lemuka agidan taga ko abinci ba'a baiwa har qannin taba, bazata jira yaran su mutu ba da yunwa murnan ganinsu ya hanata shiga b'acin ran an hanasu abinci.....a qofar gidansu tae karo da Mahal da Maheer a tare suna hira sun haye saman motarsu ta baya sunata tafa hannu suna murna qirjinta ne yae mugun dokawa ganin yanda dukkaninsu suka zuba mata ido tamkar wacce qwai ya fashewa a ciki haka ta dinga wurgo qafarta tana kusanto gate din gidan dauke da ledar lemo a hannunta...kanta qaraso Ameen yayi parking zuqeqiyar motarsa ya fito ga mamakin ta wata qara suka saka shida Maheer ya diro daga motarsa yana ihun "MAZAJE!!!!!" Suka tungume juna bayan sun tafa yace "Ango kasha mai" dariya Amin yae "Tunkan akai Amaryar kake cewa nasha mai ya akai ka gane gidan harka rigani qarasowa" kallon Mahal yae yace "Wannan yaron ne qani nane dan wurin qanwar mahaifina ne anan suke zama shine muna tare dayaji kana kwatantamun yace ya gane wurin" murmushi yae shima "Ohk sannunka shima semuje dashi ai, wannan al'adar ta sakkwatawa dame tae kama ace se an maka taron en mata sun fadi adadin kudaden dasuke so ka basu" dariya Maheer yae yace "Tunda al'adar suce aisemu hakura, namata waya tace suna masaukin baqi na waje muje kawai" wucewar Nancy ne ya dakatar dasu duka ukun suka bita da kallo, dukse ta tsargu aciki Mahal ne kurun yasan fuskarta amma Maheer da Amin basu santa ba bata fata su santa ma se idanta da suke gani..... Maheer da qirjinsa ya ninka dukawa ganij cikin idon daya taba sani yace da Amin "Aboki ko wannan ce amaryar?" Dukan bayansa yae "Ko alama tawa matar taci uwar wannan a kyau da komai, baka ganin wannan da yanayin qauyawa" dariya sukai dukkansu ya sake cewa "Qanwar matana ce fa, nasha ganinta da wannan kayan na jikinta so am sure itace ma" kallon sa Maheer yae "Kayan kawai fuskar fa?" Be kulasaba sukai ciki ita kuwa se d'aga qafa takeyi zuwa cikin gidan kamar zata kifa. Mom Nu'aiym. *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *πŸ—ΏWATA FUSKAπŸ—Ώ* πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰πŸ¦‰ *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 11 Kallon Mahal take cikeda mamakin sauyawar halayensa, yanda yake roqarta akan ta daure ta auresa, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri Mahal wlhy bawai sanka ne bana yiba ko kuma na rainaka, ko d'aya wlhy ka sani bazan iyaba, na sani auren huce haushi kake shirin yi dani bawai soba, hakan kuma na sani cewar bakada labarin azabar da zansha a hannun su Ummul idan sukaji wannan maganar, ina roqon alfarma agareka daka janye wannan qudurin naka" nisawa yae yace "Amma menene zesa ki damu da abinda zasu mikin keda bawai dad'ewa zakiyi a gidan ba, auren danakeso nanda sati biyu ayi, dan Allah ki dubi maraici na" Nisawa tae "Banida wani gata a duniyar nan sesu mahal, bazan lamunci watsar da dangina akan ka ba, ka sani ni marainiya ce sabida su Baba iro sune iya yena, mahaifina ya rasu bayan nini kadai suka haifa a duniya!! Ya rasu ya barni inada qananun shekaru mahaifiyata er jamhoriyar Niger ce haka bayan rasuwar mahaifina ta auri mahaifin su ummul babu kalar qiyayyar daban ganiba nida ita qarshe ya saketa kuma taso tafiya dani ya hanata, a yanzu haka tana aurenta acen Niger da yaranta uku, ina shiga a Nigeria idan nae rashin su Baba iro? Bayan sune gatana gaskia ka sani wlhy bazan iyaba dan Allah kai hakuri" murmushi ya sakar mata yace "Bazan takuraki ba Nancy amma dai zan baki lokaci zuwa wani satin kiyi nazari akai" shiru ne ya rataa wurin kanta nisa tace "Banaso ka wahalar da kanka wurin neman aurena Mahal, sabida ni bazan tab'a iya aurenka ba har abada" Tana gama fadar hakan tae ciki abinta shi kuwa ya dafe kansa dukda haka bata tsiraba seda sukaci mutuncin ta sosai! ************ Sosai Maheer ya tattare nutsuwar sa yana kallon islam!! Duk ta masa fari tamkar batada jini, tayi baqi da komai.....gyaran zamanta tae kantace "Da farko dai ni sunana Salahatul islam Idris me walda, mahaifina da mahaifiyata haifaffun en sokoto ne acikin qaramar hukumar silame dake cikin jihar ta sokoto, wannan kyawun halittata ta bahaushe ce kawai dani sabida iyayena duka hausawa ne, haka na ganni ina kamada mahaifiyata sosai komai nawa natane, mun taso a unguwarmu dake tudun wada mahaifina walda yakeyi itace ta kawoshi zaman sokoto ma, wannan dalilin ne ya sanya ake ce masa idi me walda, ya taso da matuqar son yaga yaranshi suna karatu sedai bashida qarfi ina da yayyu guda hudu duka maza, biyu uwarmu d'aya ubanmu d'aya biyu kuma yaran kishiyar Mahaifiyatane amma ubanmu d'aya, dukkansu suna fara karatu har matakin jami'a amma da qyar biyu suka qarasa kuma suna nan har yanzu cikin gidan ba aikin ayi tun daga bautar qasa, biyun kuma sune muke uwa d'aya uba d'aya wanda khamis yanzu yake aji hudu shi kuwa Asheer yana gun bautar qasa dalilin dayisa se yanzu suka kai nan shine sabida kosun fara rashin transport kawai seya tsayar dasu, so biyu khamis yana fara zuwa coe rashin transport yana daqushe karatun harya watsar wannan ma dasuka kammala da taimakona ne!!! Nice na taso me nutsuwa acikinsu amma se Allah ya mayar dani haka tunda na soma karatun gaba da secondry school....so da dama nikan tashi agidan mu babu abinda zamuci wani zubin haka zamu wuni ina kallon yaran kishiyar Babarmu suna cin abinci amma bazasu bamu ba... Haka sabida ita en uwanta sunada rufin asiri mukuma bamuda kowa se Allah, bayan dana samu admission a jami'ar usman d'an fodii na soma zuwa school sena soma had'uwa da ibtila'in rayuwa... Wani zubin inaji ina gani lecture zata wuceni sabida rashin transport.. Idan zanje makaranta na dinga kame kame kenan na rashin suturar zuwa makaranta wannan abin yana damuna bame qawance dani sabida hatta turaren sakawa banida shi wani lokacin ma sekaga vaselin dazan shafa ya gagaremu senaje a hakan ta fata duk furfuri!! Haka idan nawa mahaifina zancen siyen handout baya kulawa seyace babu har wani zubin nakanji tamkar indena zuwa makarantar!! Haka dai naketa daurewa har muka qarashe zangon karatunmu na farko,nida Nanuwa ajinmu d'aya kuma mumu kad'aine yaran bayin Allah, abinda na kula dashi shine Ita nanuwa bata sakin fuskarta nima muna qawancene kawai amma befi naga face dibta so biyar ba, wani zubin tare da ita muke soleta har gida qasa, idan mun fita bama rabuwa se munkai dandima se kowa ya dauki hanyar gidansu da qafa, ganin inashan wahala ya sanya mahaiyta tace in dawo hostel da zama na daure haka nan na dawo tare da neman Nancy akan ta dawo amma se Baban ta yaqi yarda, sedai takanzo duk sanda takeda test ta kwana karatu......zamana a hostel ya sanya na had'u da qawaye iri iri kala kala, dana gari dakuma b'ata gari ganin banida gata ya sanya wata qawata danai a hostel me suna jameela ta dinga nunamun hanyar yin zina amatsayin sana'a amma fir senaqi yarda haka ya sanya ta soma rarrashina harna soma kaucewa hanya, wani zubin takanzo da maza muje hira a mota kuma takan bani kyautar sututu da kud'ad'e jamcy na yawan nunamun cewar ina cikin musiba na talauci gashi handout ma ya soma gagarana siya, Namcy ta soma ankaewa da yanayin dana soma shiga na wani sauyi ta matsamun na bata labari ta hau wa'azi da ban baki, harta mun magiya, a haka dai ta saisai toni tayi sa'an rabani da jamcy!!! Bayan nan kuma se Allah ya had'ani da wani saurayi me suna suraj haka na daddage ina qaunar suraj, suraj ya yaudareni har gidan mu yaje ya gayar da iyayena ya kuma tura neman aurena, komai suraj yana mun nafita a qangin talauci har ina samu in taimaki iyayena da qawata Nancy dake shan wahala matuqa agun Qanin mahaifinta dake riqon ta da matar sa, Suraj ya sabarmun da kud'i seya kashemun dubu hamsin a rana qarshen wata yana bani dubu dari yace nai laluran school suraj dan kasuwane kuma d'an siyasa ne riqaqqe!! Katsam rana d'aya suraj ya bijiro mun daneman hadin kaina akan mui zina, na nuna masa muda zamuyi aure menene abin rushing yayi yayi nace harammun bazan ba musamman shida yakeda matansa biyu yaje ya rage zafin sa anan, daganan ya nunamun gini yakeyi kuma yanada kwadayina, dayaga bazan yiba seya dawo rarrashin akan nai hakuri koda wasanni yana tattab'ani munayi tunda ba komai bane, haka na saki jikina dashi ganin kamar a hostel mafi akasarin mata suna yi, inajin suna hira mukanyi wasanni ta hanyar tabawa juna sassan jikinmu...wannan shine babban kuskuren dana tafka!!!! Na saba sosai da wasannin da suraj kemun ganin na fara sabawa ya sanya suran ya qara tadamun maganar zina, nace bazanyiba bece komai ba ya tafi tun daga ranar suraj seda yae watanni uku baya waiwayata ko wayana baya d'auka na shiga damuwa sosai, abubuwa ukune suke neman zautar dani na farko dai Ina matuqar son suraj a rashinsa har rama nai da kuma ciwo, na biyu kuma shine tsantsar talaucin dayamun dirar mikiya nasoma sabawa da kudi a wannan lokacin ina aji biyu kuma tun a zango na biyu na hadu da sura farkonsa kusan shekara munyi rayuwa me ma'ana sosai na shaqu dashi....haka kuma abu na uku shine tsantsar sha'awa na saba da wannan wasannin banzar, sena kasa sukuni inji ina son kasancewa da suraj harna soma jin koma waye zan iya wasannin dashi, adu'a naketayi haja dai har Allah ya karkato da suraj awurina, koda yadawo ko wasanin baya mun yace dani harammune nai hakuri koda wancem yaji wa'azi ya tuba, haka muka qara watanni biyu bama komai daya danganci wannan ko riqen ahnnu bayayi kuma duk abinda yakemun ya linka!! Ranar mukaje shopping akan kayana ya qare yace muje na rakashi yaudai na gayar da mamansa haka mukaje gidan ba komai a raina......"😭😭😭😭😭 shiru tayi tana sharar qwallah kantace cikin raunin murya "Maheer bayan mun shiga gidan har parlor muka zauna wata yarinya dagani er aikin gidance ta wadatani da abubuwan sha shi kuwa ya shiga ciki, nasha lemo da cake da aka ajiyemun dama na kwaso qishiruwa kuma naga alamar ba kowa tunkan suzo naji kunya....haka ta kasance Maheer daganan se farkawa nai na ganni cikin jini da wahala ko yatsana bana iya d'agawa, alamu duk suka nunamun fyad'e suraj yamun tun daga yanayin zogin danaji jiki na yanayi aciki, ina nan kwance ina tunanin meya faru se ganin suraj nai ya shigo dagashi se boxers yana murmushi ina hawaye nace " suraj mekamun mesa zaka cutar dani?" Dariya yae yace "Soyayyace ta sanya haka Islam kiyi hakuri" kukana ya qaru jinya tabbatarmun na qarasa rufe jikina da bargon dake wurin nace "Wlhy senayi qararka a kotu azzalumi kawai" kallon cikin idona yae yana wani shu'umin murmushi yace "Waye ubanki islam? Me waldar? Me zaku iyayi dani? Aganin bansan darajar kudi na dakuke taci bane islam? Inada hankalina wlhy nasan me nakeyi ki sani ba'a cin kud'ina haka kawai kuma kije kotun qoli shari'a zan iya kune zaku wahala tunda kune talakawa, ina zamana kika zo har gidana kuma waye shedarki? Banza jaka" kukana na tsananta haka na barwa Allah ban gayawa kowaba se kawai na hakura, tsawon watanni biyu suraj ya dena kulani kuma tun daga lokacin da abin ya faru har akai watannin biyu na nemi al'adata na rasa!!! Shiru tai na some seconds tana sharar qwallah kan taci gaba... Koda na ankara na gayawa jamcy setace muje asibiti gwajin farko aka tabbatar inada ciki, da taimakon Allah fad'uwar gaban jin inada ciki shine yayi sanadiyar soma bleading

Chapter 6 of 20