21
Haka Anty Reedah da mijinta Dr. Muheeb suka shigo suka samesu, ya kasa ya tsare tamkar ya rungume ta yakeji ita kuwa islam ta kifa kanta jikin gadon tanata kukanta a hankali.......Hannun Maheer d'aya tsaqale acikin na patient d'in yanzu kam qwallan ma ya gagara yi se numfarfashi yake saukewa da sauri da sauri itakam Hafsat batasan ina kanta yake ba oxygn mane aka sanya mata, kallon muheeb yae ya saketa da sauri yaje wurin shi ya riqe masa hannu
"Ka taimaki baiwar Allah nan muheeb banaso acire mata qafa qaramar yarinya ce muheeb, dan Allah ka dubi maraicinta ko aure batayiba ace a gundule mata qafarta waze aureta?" Rungumeshi Muheeb yae
"Calm down Twin kaji, komai zezo da sauqi na nemi transfer ma zuwa asibitin frnd dina me zaman kanta ta qashi dake kano, ni kasan ba ainahin wurin qashi nake ba amma nasan sosai akan bangare, zan duba qafar kuma yanzu da condition dinnan idan muka dauketa komai ze iya faruwa se dole an ciwo kan numfashin ta, abu na gaba shine ka sanar wa iyayenta cewar ka kama mutanen dasuka saceta sedai ka boye sunan yayarka dana qawar ta kakuma ce zaka dauki mataki akansu karka fadi wani dalili se bakasan komai ba faqat" binshi yae da kallo shikuwa ya sakeshi yaje ya duba qafar.....tabbas karaya ce ta wurin Ankle dinta sedai wannan karayar bazata wuce sati uku ba, kuma a yanda yaga hoton babu wani nama dataci sosai sedai fa tabbas koda zasu gyara qafar har abada bazata tab'a dawowa normal ba seta dan karkace idan akayi sa'a karkacewar bazata nuna ba amma idan akai rashin sa'a sedai yazamana qafar ta karkace yanda ze nuna sosai kamar me dingishi ko kurkuwa ma dan idan daya tafi daya tsyi dole seda sanda.....dafe kanshi yae cikin bacin rai anty Nasara tayi aiki irin na jahilai kuma jakai, talakan data raina yafita har a wurin Allah indai ze fita jin tsoron Allah......waigowa yae ya bayyanawa Maheer abinda yake hange ya qara da cewar
"Abari amma Dr. Sunusi yazo muji nashi tunda a wannan gefen guru ne yafini sani, sabida haka ka shirya muje gidansu hafsat a gaya musu abinda ya dace su sani sannan aga yanda zamui mu koma kano da ita amma gaskia dole se anyi amfani da private jet na Abba wurin daukarta" Hakan kuwa akayi Baba azumi se gwatsina takeyi akan qaryane seda sukaje taga yanayin hafsat itama seda tae qwallah jin an daureta a tsaye kusan watanni biyu ga kuma yanda jan buzu ya dawo kala kala ajiki, Mahaifiyar hafsat kasa kuka tae se zare ido takeyi dukta rikice........
*****************
Maheer ga mahaifiyar hafsat a asibiti amma ya kasa ya tsare yaje ya riqe hannunta yanata mata addu'a yana tofa mata yana ganin kota farka a firgice zata tashi dukda likitan ya sanar masa abincin dasuka bata ta hanci ya taimaka mata zata farfad'o anytime soon.....amma cire ox da aka daura mata,ganin haka ya sanya ta koma qaramin dakin dake farkon shigowa cikin dakin....
Hannunta ta motsa kad'an dayake yana riqe da hannun seya kaiwa wurin kallo ya dawo da dubanshi zuwa gareta a hankali ta bud'e idanta qura masa idanta tae na wasu en daqiqu batare data qifta ba shi dinma kallon ta yake har yana washe baki ya matsa daf da ita ya tallafi kanta
"Sannu Hafsat ya jikinki kin farka, inane yake miki ciwo sannu kinji yanzu kin dawo gida komai ya wuce ki kwantar da hankalin ki" kallon sa tae alamun bata fahimtar komai ya kalleta sosai ya fara sunsuno wani abin, saketa yae yaje ya kira Babarta itama tazo tayi maganar harta gaji amma shiru hafsat ba amsa se kallon su takeyi tamkar wasu wawaye.......Ana haka ummul ta shigo itada Ameen, sukai kanta amma ga alama ba wanda ta gane se kallon mutane takeyi, fareedah ma da Muheeb dasuka gama kaiwa qarshen neman hanyar kaita kano suka shigo......da kanshi muheeb ya dubata yanda yaga kowa ya zagayeta har islam itama tazo amma batawa kowa magana ba se kallon su takeyi
"Lost of memory!" Ya furta a hankali bayan ya gama tab'a kanta dako ina amma bata ko damuba se binshi takeyi da ido, wannan yarinyar taga rayuwa ya furta a sarari, cikin gaggawa ya nemi hoton qwalwa batare daya musu bayani ba kiran wani dr. Kurun yae ya qara dubata sukazo aka tafi da ita hoton Kai....
Tunda aka gayawa maheer da sauran mutane cewar a kai ake hangen matsalar se suka rikice, abin ya daurewa kowa kai ga ummul dama tana cikin damuwa, Ameen kullum sesunyi fad'a yana cewa ya auretane danyaci riba da yaran dazata haifa amma wata biyu shiru babu ciki, tana mamakin sa ko shekaru biyu tayi batai ciki ba aibata cancanci hakan daga gareshi ba zaman su yaqi dad'i, har yana cewa dole tasan yanda zatai da samu ciki inba haka ba akwai damuwa cox bazeyi asaran kudinsa a banza ba...... Maheer ko yanzu mota ya koma yarasa meyasa yakeji kamar ana cewa za'a kashe shi duk sanda akace ga abinda ke damun hafsat, kwana biyu ma beje lecture ba, yanzu baya iya koda qwalla ne akan Hafsat tun ranar dasuka baro gidan nasara take kiransa baya d'auka sam!! Har dakanta taje ta gayawa ummansu abinda tae tare da yin qarairayi ta kare kanta umman tamata fada amma ta yarda bada hannunta akawa er mutane hakan ba....Abba ne kawai besan miyan da ake shaba sabida baya garin.
*************
Bincike ya nuna qwalwar hafsa babu inda ya tab'u amma fa tayi lossing memory dinta gaba d'aya wanda suke saka ran ya dawo bada jimawa ba, a wannan ranar suka wuce kano domin yiwa hafsat aikin na qafar.......
Mom Nu'aiym
*mu hadu a page na gaba anjima da yardar Allah.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
23
Bayan sun kammala wayar ne kuma tana tsakiya da kukanta mahaifiyarta ta shigo ta zauna gefen gadon ta kalleta
"Salaha lapiya dai? Kukan me kikeyi ne haka?" Share hawayentabtae tace tana murmushin yaqe
"Dad'i nakeji zakuji dad'in rayuwa ta dalilina akan auren da zanyi Inna, Maheer ne ya bamu gidansa daya tashi yace mu zauna anan garin, be furta yace kyauta bane amma dai yace mui mooving ciki Inna bakiga gidan ba ya had'u wlhy gidan masu kud'i ne fa" murna innar ta shigayi tana rarrashi akan abin farin cikine ta dena kuka kantace da ita
"Dama Nikuwa salaha cewa nai zancen kawo kayan lefe naji shiru har yanzu, en uwa sun soma tambaya kinsan mutane" Murmushi tayi
"Bam masa magana ba tukunna amma barin masa waya" Yana wurin Hafsat ya kasa ya tsare seda yaga farfad'owarta yana tsakiyan mata sannu yaji qarar wayansa.....Ganin islam ce ya sanya ya fita waje
"Baby" shine abindabya furta bayan d'aga wayar
"Ina wuni honey?" Yana murmushi yace
"Lapia lau my baby, hafsat fa ta farfad'o" se yanzu ta gane dalilin dinga fadan shi d'azu akan bega hafsan ta farfad'o bane, farin cikinsa yanzu kuma akan ta farfad'o ne
"Alhamdulillah Allah ya qara mata lapia" shine abinda ta furta tana murmushi
"To Babyna how far meye a qasa" sakon barkwancin da yae ne ya sanya ta saki jikinta takumaji sanyi a ranta, itadai tana matuqar qaunar maheer...
"Honey dama cewa nai zancen kayan lefe najiku shiru kasan a nan kafin biki ake kawo wa" Dafe kansa yae shap yama manta
"Dan Allah baby kuyi hakuri, kinsan Allah wlhy na manta ana lefe a aure ma, kumafa umma na kullum setayi maganar ranar da twin tamun magana ranar aka samu labarin hafsat duk wannan abun ne ya mantar dani yanzu kinsan meze faru,barin wa umma waya inyaso kinga sena kiraki back yanda mukai" Bataso jin hakan daga gareshi amma setace.
"Ba komai dear, sena jika" haka ta ajiye wayar ta kalli mamanta
"Ammm Inna wai akwai shirin dasukeyi amma ze kira mamanshi yaji inyaso seya kirani muji yaushe zasu kawo" murmushi uwar tayi
"To kuma zancen kud'in saka lalle da wankan amarya shifa yaya za'ayi? Ko kaya zasu kawo ne?" Nanma yaqe tayi tace
"Na manta dubu dari ne ya bayar suna nan acikin jakana" Gud'a uwar tayi ta karb'i kud'in tafita waje tana murnar an musu qoqari ta samu kudin yin kayan tuya na gara!!...
****************
"Ummana yaya maganar kayan lefen nan ne wai, kinga ni na shafa wlhy" Dariya tae har yana jiyo sautin muryanta tace
"Mahi auren nan sekace dole aka maka, waya tab'a manta kayan lefen matarsa? Kaga nifa enkai lefe nakan hanyar sokoto yanzu ma haka sun mun waya akan suna kan hanyar shiga layin su a unguwar....dama Fareedah bata sanar maka ba tare fa suka tafi, itada qawata da qanwar mahaifinku" Daria yae
"Nayita neman layinta beje ba kuwa, to Allah ya qara girma ummana nagode sosai"..
Kallon kayan aketayi ana mamakin had'uwarsa da uwar dukiyar da aka narka zani babu na qasa da dubu 25 komai yaji, tsayawa fad'ar dukiyar dake cikin kayan lefen ma bata baki ne, Islam tasha mamakinsa har taji kunyar hakurin data kasayi tayi kiranshi sabida kamma su gama wayar aka soma sallama ana shigo da kayan.
Agurguje plss
Auren Maheer da Islam dai Babu wasu bidi'o i da akai se dinner se kuwa gagarumar walimar data daddage ta shirya me qayatarwa, Maheer yai qoqarin zuwa gun Dinner wacce ta haska bilhaq anja dala an cuci naira kuma manya manyan en kasuwa sunzo anci ansha an wakita, islam kam tayi kyau na nunawa sa'a Maheer duk yanda ka kalleshi zaka tabbatar yana cikin kwanciyar hankali,nutsuwa da ni'imtaccen farin ciki mara misaltuwa shida kanshi shaidane akan tabbacin son dayakewa islam, dukkanin abubuwan dayaji yakuma gani akanta babu daya da yae tasiri akansa ya manta dasu tamkar yanda ka manta rayuwarka ta quruciya ko kuma tamkar wanda bema tuna komai ba na dangane da rayuwarsa ta jarin taka, yayi murna matuqa da aurensa, yanzu damuwarsa d'aya hafsat dabata magana har yanzu inda yake cikeda tsoron akan bayanin da aka masa kan cewar idan basui hankali ba maganar ma se an dawo fresh cox ko kashi takeji bata fadan zatayi da susuce ta lalace ta zama wata kala wata iri abin tausayi Yana ganin cewar duk abinda ya sameta ta dalilin sane domin akansa aka mata, shisa yake ganin haqqinta yana rataye ne a wuyansa, zuwansa sokoto ma be barota da kowa ba mahaifiyarta ta koma Niger sabida mujinta ya matsa en uwanta na sokoto anyi anyi Baba azumi taqi zuwa ita acewarta ummul ma batada lapia.... So Wata er aikin gidansuce larai kurun tare da ita hankalinsa duk kashi 30 yana gunta dukda murnar dayake ciki a qauyan su aka daura auren inda manya manyan en kasuwar duniya sukazo aka daura auren islam da Maheer amarya ta samu kyautar mota kusan 5 awurin daurin auren daga wurin abokanan mahaifin maheer se murna mahaifinta keyi haka washe garin d'aurin aka wuce da amarya agidanta dake kano.
*******************
Amarya duk inda hankalinta yake baya kwance kasancewar rashin adanar budurcinta zuwa gidan mijinta, a tsorace take da abinda zeje yazo fad'uwar gaba ya sanyata ramar wuni uku kacal shigowarsu gidanta na sunna ya qara gigitar da ita ainun!!! Haka en rakiyar amarya suka watse zuwa masaukin da aka ware musu aka barta ita kad'ai qwallin qwal!! Girjinta be dena bugawa dukda gyaran data samu daga Anty billy... Batasan yaya mijinta ze kalletaba ba akan wannan abin..tana nan zaune har Allah mad'aukakin sarki ya kawo Maheer da tawagarsa amma sesuka tarar ba qawayen amarya ko d'aya wannan ya basu dama baiwa amaryar kudin siyan baki 500k suka juya... A wannan daren sukai alwala da sallar nafila, sosai darajar islam ta qaru agun maheer ganin cewar tasani sosai akan addinintabya mata nasiha sannan ya bata wuri domin ta kintsa amma abinda ya bashi mamaki haryaje ya dawo bata sauya kayan ba tana takure a hijabin da tae sallah dashi, zama yae ya kamo hannun ta yaji wani asalin laushi me d'aukar hankali da sanya nutsuwa, murza hannun ya somayi a hankali hannun acikin tafinsa gumi yakeyi
"Babyna yaya, bazaki sauya kayan jikinki zuwa na bacci ba mu kwanta?" Kallanshi tae se ta kawar da kanta, jikinta rawa yakeyi ya kula da hakan sabida hannunta dayake riqeda se karkawa yakeyi,ya kula hankalinta baya jikinta kuma ga dukkan alamu bata cikin nutsuwarta ko kad'an,alamu ma sun nuna cewan a tsorace take....bayaso ya saka a ransa cewan wai dalilin yawon datai ne takejin tsoro wannan ya sanya ta tattaro nustsuwarsa shima ya janyota jikinsa, mamakin yanda jikinta ke rawa gabaki d'ayansa yakeyi, amma seya kawar
"Yau ina tsiwar ne eee matana? Ina tsokanar ina bakin duk sun tafi kema kinsan bawai sassauta miki zan ba, barin lalubo miki kayan baccin ki ko?" Runtse idanta tae, yaje ya bude jerin akwatunan daya gani ya nemo wata riga me tsantsi ya dawo.... Tanaji tana gani ya cire dukkanin kayan jikinta ya zura mata wannan, yauce ranar farko data somajin kunyar wani namiji arayuwa, sanda aka qwace mata budurcinta batasan ya akaiba, sanda ta fada bariki babu tsoro ko kunya a tattare da ita!!! Kashe fitilar dakin yae ya zare jallabiyar jikinsa ya dare gadon sannan ya janyota jikinsa hannunsa ya shinfid'ar ya d'aura mata kanta a saman hannun nasa suna fuskantar juna, hannunsa daya ya sanya ya zagaye bayanta a hankali ya shafi bayanta wanda wlhy babu qarya acikin ni'imtaccen dad'in dayaji da had'uwar jikinsu da shafar dayawa bayanta...runtse idanta tae jikinta se rawa yakeyi tana sauraren yanda yake sarrafa jikinta san ranshi, Maheer sam ya manta a wacce duniyar yake baya tunanin ya tab'a kasancewa akan ni'ima me kwantar da hankali sama da wannan, Murzarta yakeyi tako ina baji ba gani, Kasa hakuri yae sabida beso fara yin wani abu da ita ba yau, amma tunda ya had'a jikinsa da nata ya tabbatarwa kansa Islam d'insa ta daban ce, lalubo bakinta yae ya kai masa cafka, yau kawai duk jarumtar islam seta gagara aiwatar da komai tayi lago se yanda yae da ita, haka ya kaiwa dukiyar fulaninta cafka!! Ya dinga murzanshi a takaice dai seda ya yae mata jiga jiga ita kuwa ta kasa komai banda rawa da jikinta keyi babu abinda take iyawa, koda yazo domin gaabatar da aiwatar da shirin bayan gabatarwa seta sanya masa kuka sabida anan take ganin tagama wulaqanta, yauce ranar farko da islam ta tabbatar wa kanta ta wulaqanta rayuwarta na wofintar da Kanta awurin mazajen bariki, dama ace sanda akai mata fyad'e ta barwa Allah wataqil dabata tsinci kanta acikin wannan halin ba......
Kwanciya yae ya janyota ajikin sa
"My islam karki mun haka mana, ki barni in karbi haqqina idan kikamun rowa wurin wa kikeso inje? Ke kadai gareni islam na jima ina jiran ranar nan,ranar dazaki samto mallakina inyi yanda nakeso dake" Shiru ta masa ya kai harshensa a kuncinta ya lashe qwallan datakeyi sannan ya koma ruwa duk yanda taso ta kame kanta seda ya cimma burinsa da manufarsa akanta, a wannan lokacin daya samu nutsuwa jiyakeyi tamkar ya miyar da ita ciki, Ya kansance cikin farin ciki mara misaltuwa, haka ya dinga mata sambatu yana saka mata albarka me tarin yawa....nauyi da kunyar sa suka dirar mata ta kasa koda motsi haka suka kwana yanata daukinta yayi abu d'aya yakai so biyar, da asuba da kanshi ya mata wanka yana mata fi'ili akan bakinta da ya mutu ita kuma se mamakinsa takeyi bata tab'a koda mafarki tunanin zata samu tarairaya haka daga wurin gwarzon mazajen taba, shuya yane bed sheet ya turashi cikin ingin wanki ya sauya wani, kuma ya hanata aikin komai daga gidansu aka kawo break fasat da kanshi ma ya bata taci....
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
24
Se yamma ya qara yin waya gidan nasu aka kawo abinci, sukaci sannan suka nufi asibiti wurin Hafsat.... Bayan sun tsaya yamata umarni da taje ciki yana zuwa, kifa kanshi yayi saman Staring motar tasa ya runtse idansa, yana da damuwa sosai akan yanayin daya riski Islam, ya sani ya shiryawa hakan kuma ya tabbatar wa kanshi ya samu gamsuwa me tsanani a tattare da islam to amma ya rasa dalilin damuwar sa akan riskarta matsayin cikakkiyar budurwa, yana ganin hakan baya rasa nasaba ne da kasancewar sa me tsananin kamun kai da kame jikinsa ga matan banza, ya sani Fasiqi se fasiqa amma a wannan lokacin yana kyautata zaton banda wacce ta tuba! Yana kallon islam a matsayin mace mafi tsarki aduniya baya jeranta ta a matsayin fasiqan mata, kasancewarta kamilalliya a yanzu Allah ne ya masa zab'inta kuma shine yawa alqawarin bazata tab'a ganin wani wulaqanci daga wurin saba danwai be sameta a matsayin budurwa ba, yawa kanshi alqawarin har abada indai ta wannan b'angaren ne bazata tab'a ganin wata alama daga gun saba ta rashin jin dad'i koya wulaqanta tata ba har abada......cikin damuwa yace
"Allah ka sanya islam ta shiryu kenan har abada, dazan samu wannan dana riqe islam har abada,idan zan iya bada shaida a lahira dasena bayar da ita acikin mata mafi salihanci na duniya"...... Kashe motar yae ya fita waje ya nufi d'aki, acen ya tarar da islam zaune tayi tagumi ita kuwa Nancy ta qurawa tv dake d'akin ido tana kallon wani film...gashinan an sato wani yaro yanata tattalin qwacewa shima seya raja'a da kallon cen kuma se aka qwalawa yaron kwalba akai nan take ta qwalla qara me tsanani ta had'e da dafe kanta, atare sukai wurinta suka ririqeta se ihu takeyi, Islam kuwa itace tae qarfin halin fita waje neman Dr., a d'aya b'angaren kuwa likitan dayake wani dakin duba patient qaran dayaji ya gayyato sa zuwa d'akin, seda sukai karo da islam da sauri yanufi kan Nancy ta gagara nutsuwa ta kwantar da hankalinta se ihu take, cikin gaggawa ya sanya aka kawo masa allurar bacci ya danna mata kana ya nemi ba'asin yanda abin ya faru....Bayani Maheer ya masa, yae murmushi ya dafa kafad'ar sa
" karka damu inaga mun soma samun nasara zata samu memory d'inta, hopefully ma yadawo gaba d'aya" Nisawa Maheer yayi
"Allah yasa hakan, daka duba qafanta naga tayita jijjiga" Nanma murmushi yae
"Lapia lau qafan take karka damu kaji" bece komai ba ya miyarda dubansa zuwa gareta yana nazarin yanayinta,se yamutsa fuska takeyi dukda bata cikin hankalinta alamun akwai abinda ke damun ta.....
*Bayan sati hud'u*
Acikin wa en nan satitiitkan Hafsat ta samu sauqi sosai, kuma tana magana sedai abinda muke tsammani na dawowar memory d'inta abin ya faskara ci gaba d'aya ne ta soma yin magana, kullum Maheer da islam wurinta suke wuni zamu iya cewa rayuwar amarcin Islam ya k'arene awurin sintirin asibiti da jinyar Nancy, Baba azumi dai taqi zuwa haka Ummul laulayi takeyi me matuqar bata wahala yayinda take samun tsananin kulawa awurin Ameen....Batada kowa se islam da Maheer su kad'ai ta sani su kad'ai take gani, acikin satin nan d'aya jal gaba d'aya islam bata zuwa asibitin sabida zazzab'in datakeyi, damuwa sosai take ciki akan yanayin yanda Aunty Nasara ke mata wulaqanci da nunin wariyar launin fata, a shekaranjiya ta sanar mata karta yadda tayi ciki ta haife musu dan tsohuwar karuwa tayi kukan wannan maganar harta godewa Allah amma sam bata gayawa Maheer ba, wannan dalilin ne ya sanyata jin zazzafan zazzab'in daya kwantar da ita, tayi dana sani me tsanani na halin rayuwar data aikata a baya, ta kuma kasa sanarwa kowa dama ace Hafsat d'inta nada lapia dama ace 'yar uwace bata rasa tunanin taba data gaya mata ko zata samu sassaucin abin da takeji......
***************
Maheer yayi wata shaquwa me tsanani da hafsat da har bayason zuwa sokoto kullum idan zeje seyasha fama, ganin tana masa rigima ya sanya yau yace baze ma sanar mata ba ya shirya ta tafi abunshi ya barta da islam, se dare ita kuma ta barta da Inna wacce dama hayarta sukayo domin tana kwana tare Hafsat d'in.....kwana biyu hafsat bataga maheer ba ta soma yiwa islam rigima akan yaa maheer kamar yanda taji qannin sa na fad'a idan sunzo mata dubiya... Da q'yar islam ta shawo kanta ta dena rigimar hadda kukan ta kuwa, abun ya matuk'ar dami islam, ta kasa gane alaqar zuciyoyin biyu, shima a b'angarensa hakanne ko waya ya kira Hafsat ze fara tambaya' yauma kamar kullum tana tsakiya da tunanin nan wayarta ya shiga ruri ko bata duba ba tasani Maheer ne ko daga yanayin waqar dake tashi....karawa tayi a kunne bayan data d'aga kiran a hankali ta furta
"Assalamu Alaikum Honey" murmushi
"Amin wa Alaikissalam Baby na ya gida"? Murmushin tayi itama
" Alhamdulillah"
"Ina Hafsat da jikinta?" Kallon Hafsat d'in tayi a ranta tace "Ni bazece ya nake ba se hafsat? A sarari kuma seta furta
" Taji sauqi Alhamdulillah" washe baki yayi
"Ki bani ita muyi magana" bataso hakan ba dama kenan ba ita ya kira ba? Badan ita ya kira wayar ba kallon hafsat din tayi ta mik'a mata wayar tana murmushin k'arfin hali....Bata karb'a ba kuma bata kula taba wannan ya sanya tace
"Yaa Maheer ne zaku gaisa ki karb'a mana" kallon ta tayi ita ma
"Bazan yi magana dashiba bayan ya tafi wani wurin ya barni kuma yace muyi magana bazan yiba nidai" Haushine ya ishi islam na sosan ma ta kalli wayar kanta daqile kiran tasoma k'osawa da wannan iskancin itakam ma gani takeyi tamkar memory d'in Nancy ya dawo rainine kawai dacin zarafi koda ya k'ara kira bata d'aga ba tamai banza Hafsat kuwa ta sanya kuka sekace wata jinjira baqin cikine ya sanyata barij asibitin batamawa hafsat sallama bama, ta barta da inna cena gwamatse masu bazata iyaba salon wulaqanci kawai.
****************
Washe gari ma Islam bataje asibitin ba da Maheer ya kira tace masa batajin dad'i shikuwa ya rasa dalilin daya sanya zuciyar sa take azalzalar sa akan yaje gun Hafsat wataqil hakan baya rasa nasaba da cewar da aka masa Hafsat ta soma yin tafiya da kanta kuma Dr. Ya tabbatar masa ta soma samun memory d'inta dan an sanar masa tasoma tambayar en uwanta su Baba azumi dasuke en iska basu zauna jinyar taba Ummul ce kad'ai me yawan kiran waya gashi batada lapia sosai laulayi takeyi kamar me.....Jikinsa har mazari yakeyi akan yaje ya ganta.....kai tsaye asibitin ya wuce daga zuwan sa garin na kano, yaji dad'in ganin ta tana tafiya da qafarta kuma lapia lau ba laifi tayi daidaito da y'ar uwarta sedai tak'i sake masa fuska gaba d'aya ta b'ata ranta...zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta
"Lil sis menene kuma na fushi? Na kikkira kinqi ki karb'i wayan mu gaisa" kallon sa tayi
"Ba komai" ta furta a taqaice da murmushi d'auke a fuskarsa yace
"Kinsan Ni lecturer ne a makarantar ku udus dake sokoto, baze yiyu na dinga jeka ka kawoba kano zuwa sokoto akwai nisa sosai"
"Udus kuma?" Ta nanata a sarari se kuma ta lula a duniyar dunani...kamar kuma wacce aka tsikara seta warce hannun ta ajikinsa
"Innalillahi yaa Maheer dama kaine ka sanya aka satoni ko, dan Allh ka kaini gun su Baba azumi mena maka a rayuwa" Wasa wasa dai da k'yar da sid'in goshi Dr. Ya kwantar da ita da alluran bacci se hamdala sukeyi ta samu memory d'inta back...sedai Beji dad'in hakan data zata ba amma ba komai ze jira farkawar ta seya mata bayani.
************
*Bayan kwana d'aya*
Islam da Maheer atare suka shigo d'akin, ga maheer ranshi a b'ace yake da islam akan rashin zuwanta asibiti kwana biyu, sarai ya sani lapiyan ta qalau yakula kishi ne ke d'awainiya da ita
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 20