ne banda haka wannan tun yaushe ta fita a yayi? Gyaran muryanshi yae dan kanshi ya saisaita nutsuwar sa yabi bayan Dr. Shema ganin harya qure cikin office d'in.....da sallamar sa shima ya shiga yayinda Hafsat ta mara masa baya tana me duqar da kanta wannan sabon malamin nasu yana santa gwiwowinta yin sanyi matuqa, wannan idan nasa suna neman razanar da ita gashi da kallo sekace maye, seya qura mata wannan gwala gwalan idan nasa baya ko qiftawa!! Ita kuwa duk sanda ta kalli cikin qwayar idansa se jikinta ya mata sanyi qalau, sallama tae Dr. Shema ya kalleta sosai yace
"Hafsag mesa kikaje class late abinda baki sababa" sauke idanta tae qasa dake cikin farin gilashin daya gagara b'oye kyawun idanuwan nata tace cikin sanyi
"Sir jiyanne na jima ina karatu har na raba dare, to kuma shine ko sallan asuba ban samu nayi ba da wuri se after 7 na farka a gurguje nazo nan sekuma nae rashin sa'a nayi late kayi hakuri" murmushi yae ya mayarda dubansa zuwa ga maheer da yae tsaye tamkar wani statue yana jin haushin Hafsat ji yanda take wani magana sekace wata sarauniya tana fitar da sautin d'aya d'aya....
"Malam Maheer dan Allah ka bata wani question's d'in tayi yanzu, nasan hafsat da san karatu bazatayi late haka kurin ba"
"Ok" itace kalmar daya furta kurun ya zauna ya zaro question's masu zafi har qwaya goma ya danna mata, cikeda nutsuwa ta zauna ta zane takar dar da soshin ta masu gamsawar ta miqe ta bashi tana meyin godiya wa dukkansu, bayan fitarta ya qurawa takardar ido yana nazarin amsoshin daba'a gabansa ta zauna tsit tayisu ba dabaze yadda cewar dakai aka amsasu ba acikin mintuna goma sha biyar......ya yaba karatun yarinyar sedai shisam baya san mace me yanga koda yake ruwan mijinta tunda ko ba'a fad'aba daganinta kaga matar aure.....
***********
A yangace Islam ta shigo lecture hall d'in tana tafiya ba abinda kake jiyowa se qarar takalminta qwas qwas qwas taku da d'ai d'ai da2 cikeda yanga daji da ajinta plus kyau na sura dama na fuska da Allah ya wadata ta dashi, cingom takeci amma ilahirin kumatunta lob'awa yakeyi, Maheer tamkar wani dutse haka ya tsaya yana kallonta koda yake d'aukacin mutanen dake hall d'in kallonta suke mata da maza kuwa, kasa korarta yae wanda ya baiwa kowa mamaki, kasancewar wannan ne karonsa na uku yi musu lecture amm sun lura 10mns yake idan time nashi yae kan yashigo kuma idan ya shigo baya bari kowa ya shigo amma yau yaya haka? Shi kuma a b'angarensa da qyar ya saisaita nutsuwarsa be tab'a ganin yarinyar a class d'in ba kuma course biyu yake musu to wacece ita?" Ci gaba yae da lecture d'insa yanda yafara tun farko a haka a haka harya kammala amma a rikice yake duk yayinda ya d'aga idanshi dan kallon d'aliban se idanuwansa su gagara kallon kowa se wannan baiwar Allah daya gani kusa dame niqafi a zaune (yanda yake kiran Nanuwa a zuci kenan) ......zuwa yanzu d'aliban sun karanci halayensa na san yin kiran register ma'ana seya kira sunan kowa bayan ya kammala lecture daya bayan daya idan aka kiraka seka fita hakan yae ko yau, ya kammala kiran kowa suka fice se mutum biyar daba sunansu a attendance na ranar.....mutum hud'u suka bishi suna roqon ya basu su rubuta amma fir yaqi saurarar su sedai tun a wurin ya kula me yanga (kamar yanda ya rad'awa Islam suna a zuci) bata bi bayan saba bayan ya tanbatar bata rubutaba sabida anfi 50 mns da fara lecture d'in kafin ta shigo ya kuma tabbatar attendace ya jima da baro wurin da take, yarasa dalilinsa na damuwa da halin ko inkula data nuna wa attendace d'in dashi ma baki d'aya.... Yafi 40mns zaune yana yaqi da zuciyar sa wurin ganin ya yakice tunanin salihatul islam a ranshi amma abun yaci tura ya fuskanci yana cikin damuwa akan baiwar Allah to kodai aljana ce? Banda haka yaya zata zo masa class late ya gagara d'aukar mataki a kanta? Yana tsakiyar tunanin hakan ya jyo knocking a qofar office d'in gyaran zaman agogon hannunsa yae ya kalli time sannan yace
"Yes come in" a hankali ta tura qofar ta shigo qamshin turarenta ya daki hancinsa ya lumshe idan sa sannan a ankali ya bud'esu ya dire a kanta bayan tayi masa tsayuwar d'aya ga wata a gaban teburinsa cikin wat murya dayake da tabbacin idan ya ci gaba da saurarenta zata tarwatsa masa tunaninsa tace
"Sir dama akan attendace ne nazi signing ban samu nayi ba" gyaran zaman sa yae yace yana me qoqarin had'e rai ya tsare gida
"Mesa baki yiba"
"Hanging nae a hanya nazo late yamun nisa" kallonta yae language datake usung kad'ai ya isa ya sanar maka cewar qwanqwasashiya ce yace
"Sekije kiyita hanging mana meye nawa aciki" hannunta ta sak'ala akan jakarta dake maqale a kafad'arta tace
"Na sakko ne ya sanya ka ganni anan sir Maheer, kai hakuri ka bani na zana abin dabefi mintuna biyu ba dan Allah ka bani" ya gano kanshi na shirin tarwatse masa idan ya daddage da sauraren muryarta wannan ya sanya ya janyo takardar ya bata....kallonsa tae
"Sir banida pen a taimakamun plss" ya gagara kallon cikon qwayar idanta shu'umin kallo take wurga masa baze iya jura ba kansa a qasa ya bata kawai, zanawa tae ta juya takardar ta fuskance sa ta d'aura biron akai tace cikin yanga
"Sir aikina ya kammala saura naka" be gane me take nufi ba sam seda tace cikin shagwab'a har tana maqe kafad'a
"Allah ni sir sekamun marking,naqi wayon" murmushi ya sub'uce masa dabe shirya wa ba ya daga biro yae alamar mark ajikin sunan ta, murmushi ta sake masa tace
"Nagode sir, Allah ya bar mana kai, dama kuma ina taso in gaya maka sunanka danaji abakin students yamun dad'i, inshaa Allah idan ban auri me suna maheer ba zan haifi d'a me suna Maheer" yaji dad'in kalamanta mutum ne me yawan san a yabawa wani abu nasa yace
"Nagode A jikin sunanki Naga kinsanya Salahatul Eslam, ni kaina sunanki yamun dad'i sosai, idan ban auri me sunan kiba zan haifi 'ya in rad'a mata wannan sunan kinji" tana dariya ta juya masa manya manyan mazaunanta tae gaba,kasa hakuri yae yafito office d'in yana kallonta tare da ya gansu dame niqafi ko yanzu to menene alaqarsu? Wannan er gayun da wannan kidahumar er qauyen? Tab'e baki yae ya juya office d'in yana me ayyana kyawun jiki dana surar da Allah yae wa Islam.....
Bayan la'asar ha fito qasan da yae parking domin ya wuce gida, acen daga nesa su Nancy da Islam suka hango tahowarshi suna kallo ya hude wannan farar qatuwar range din ya shige, Nanuwa tace
"Koda yike gulma ba kyau amma ina matuqar mamakin Sir Maheer, manyan motocin nan dayike hawa Anya malamin jami'a ze iya kuwa?" Dariya Islam tae tace
"Kinsan meya taka?, d'an iskan da iskanci zemun seda namai shu'umanci ya kame tsufansa ya adane" dariya tae
"Allahu ya shiryeki qawata, ni yau dinnan ma bacci nakeji wlhy, hostel zan koma kefa? ".......
Haka ya kwana tunanin Islam yayinda Nancy ta kwana tana tunanin Sir Maheer ta kasa gane alaqar dake tsakanin zuciyar ta da Maheer.....mesa zata damu dashi har haka, gobe sukeda psycholinguistic kuma tasan shiyake musu ta qagara goben tae bata da burin daya wuce ta ganta agaban Maheer tana kallon sa yanda yake rero lecture aka! Yake karanto abubuwa sekace shine yae kansa ohhhhh...........
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
08
Seda ya fita daga gidan yae parking motarsa ya d'aura kansa saman stiring motar ya soma miyarda numfarfashi a hankali, hannunshi yakai ya lalubi kuncinsa yaji shinwai da gaskene abinda yakeji qwallah yakeyi? Yaushe rabon da yae kuka a rayuwar sa? Ya manta whly akan wata yau gashi yana kuka wannan wace irin jaraba ce? Yafi mintun 30 a wurin batare daya san time ya tafi har hakan ba!!!!!!
************
Eshmal dan Allah ka kaini tasha, nahau mota akwai uzurin daya tasomun yanzun nan aka kira ni daga gida, kafita rakiyar friend dinka, namaka alqawarin zan dawo da kaina idan komai ya lafe" da zargi ya kalli fuskarta ta d'auke kanta gefe d'aya tana nazarin yanayin sa
"Ka taimaka Eshmal ka kaini kaji, wlhy akwai damuwa fa!!" Mamakin jin da yae muryanta na rawa ya kama shi,yace
"Subhanallah kaddai mutuwa aka muku" daganan ta samo qaryan dazata mai
"E mama nane batada lapia shine zanje gunta ance sosai ne"
"Ayya toki shirya muje ko, Allah ya bata lapia amma to abincin fa, ki danci ko kadanne mana"
"Banida appetite ka kaini tashar kurun"...... Haka suka fito cikin qasa da mintuna 30 a bakin hanya ha hango motar Maheer da plate an rubuta Sidi dala range 12 wacce ta baro compound dinsa yanzu, gangarewa yae ya parka ya fito yamai knocking d'agowa yae bayan daya zuge glass din yama manta aduniyar me yake, kuma ya manta yana kuka ma, mamaki ya kama Eshmal uace
" Subhanallah friend, menene ya samu haka da sauri sauri kuka fa" se a sannan ya tuna ya share qwallan sa yace
"Kasanni da raki ai, bawai kuka nake ba muddin dai ina numfashi wani abu namun ciwo senayi qwallah, ina baro gidanka cikina ya murda shine na paka anan se juyamun yake" kallon sa yae cikin tausayi yace..
"Ayyah toka kawo na qarisa maka da motar acikin gidana sena direka gida kanka samu sauqi driver ma yaje ya miyar maka motar gida" kasa yi masa musu tabbas ze iya fad'uwa ya mace idan yace zeyi tuqin nan.....haka ya fito ya miqa masa key ya nufi motar sa, mamakin ganin Islam yae ta sadda kanta a qasa batasan meke faruwa ba batama san da zuwan saba, kwantacciyar sumar kanta data sakko har wuyanta ya kalla ya tabbatar ita dince dan haka nata zubin yake ya bud'e gidan baya ya shige bata koda d'agoba tana cen tana kuka tana sauke numfarfashi a hankali kukan me sauti takeyi me ban tausayi, leqowa Eshmal yae yace da ita
"Sweetest barin je na sauke motar friend d'ina acikin gida nazo, cikinsa yana masa ciwo baze iya tuqi ba dan bani minti daya nai parking nazo muje" gyad'a masa kanta kurun tae, bata gano ma Maheer yake nufi ba shi kuwa ya dawo tsakiya ata bayan motar ya qura mata ido ko qiftawa bayayi har Eshaml ya dawo ya miqa masa key karba'a kurun yae ya tura aljihun gaba rigar sa
"Yaya cikin? Yana raguwa yanzu?" Gyad'a masa kansa yae ba tare dayayi magana ba, shi kuwa bayan ya saisaita motar kan titin seya d'aura hannunsa daidai ta bayan wuyan Islam yace
"Karki damu sweety, inshaa Allah maahmaah zataji sauqi kinji, ki dena kukan nan karkizo kiyi mana ciwon kai a banza" bata d'ago ba, shi kuwa maheer yabi hannun Eshmal da kallo yanaji tamkar ya dauki adda ya datse matsa wutsiyar hannun dake gangancin tab'a masa islam d'insa....katse masa tunani ya yana meci gaba da murza bayanta a hankali yace
"Maheer ka ganta nan se kuka take tunda ka fito aka mata waya mamanta batada lapiya sosai" Da sauri ta d'ago jinya ambaci Maheer amma seta gagara waigowa ta kalle sa shi kuwa yace da kyar
"Allah ya bata lapiya, zata samu sauqine inshaa Allah" batai magana ba dai Eshmal ya qara riqo hannunta, yace
"Ki bani acc details naki zan tura miki 200k nasan aikin dakikamun ba dare ba rana yafi qarfin hakan, wannan ba ladan aikinki bane kije asiya maman me sweet magani, ladan aikinki da yamma zan tura miki" kasa d'aukar maganganun kunnuwan Maheer sukai yace cikin qarajin daya baiwa su duka biyu tsoro
"Kaiiiiii" parkawa Eshmal yae yace "Maheer lafiya kake kuwa kodai muje asibiti naga alamar ciwon cikin nan naka baze barka ka huta ba" cikkn baqin ciki yace
"Dan Allah ka kaini gida, direni gida tukunna kankaje inda zaka kaji" beyi musuba ya karkata akalar motarsa zuwa lameed'o crescent domin diresa gida, yana tsayawa yafita a motar Islam ta bisa da kallo, had'a layi yake kukanta taci gaba dayi harya kaita tashar ya biya mata drop na qaramar mota ya bata 20k tasha ruwa a hanya yakuma yimata alert na 200k kai tsaye, yauga kud'in amma basuda amfani agareta, har suka isa sokoto kuka takeyi......
Tana isa gidan su innar ta dake wanke wanke ta miqe da plate a hannu tace
"Ernan bikin nan har an gama, bacewa kikai se litinin ba?, naga duk kin kumbura a fuska wani abin ne ya faru?" Lumshe idanuwanta tae tace
"Ba komai innah zazzab'i nakeyi yasa na gudo gida kai tsaye ba'a gama bikin ba yau asabar ake wuni, gibe bud'an kai" jinjina kai innan tayi tabi bayanta har d'akin, bayan sun zauna a bakin gado tace
"D'azu lamimi tazo nemanki, wai yaronta baida lapiya babu kud'in dazata kaishi asibiti nace bakya gari amma na bata dubu d'aya" murmushi tae na yaqe tace,tana kwanciya
"Akwai kud'i a jakana ki aika mata dubu biyar yau bana jin dadi innah, karki bari su faruk su tasheni idan na shiga d'akina" batace komai ta miqe tana murna yau tasan zasuci kaji tunda Islam taje biki......
***********
Part d'insa ya wuce yaje yayi kuka harda majina, yanawa islam wani irin so dabesan dame ze fassara saba, wannan abu da idansa ya gane masa yau besanya yaji ko gyazau ba game da yanayin dayake ji akan qaunar islam, b'acin ransa d'aya ta karya masa alqawari ta siyar masa da jikinta me tsada arha banza, awurin fasiqan bariki tausayinta yakeji yanda ta lalace, batun yauba ya kula Islam tana yawon banza amma babu abinda yafi dakar mar zuciya kamar wannan mugun abin dayaji yakuma gani, be shigar kallewa islam jiki yanzu ba, be shirya ganinta a yanayin daya ganta ba yau, dama yayi niyyan auren ta koda kuwa karuwan ci take aganinsa yayi jahadi!! Menene ke shirin faruwa da soyayyar sa? Yayi kukan harya gaji bame rarrashin sadole yae shiru!!! Yakoma kukan zuci...
**************
An kammala gyaran gidansu Ummul, ya dawo acikin jerin gidajen da ake lissafawa na masu kudi acikin unguwar ta lowcost, su ummul sun tare hatta Nancy ta samu an ware mata d'aki d'aya dayasha ado da kayan more life, wannan karon kam har qaramun plasma ne manne a d'akin na Nancy da wardrop gado dai set dan Niger me kyau!! Duk wannan daular duniyar nancy batajin dad'in zaman gidan nasu ko kad'an cikeda tashin hankali take na rashin Maheer, yaudai tayi shirinta tsaf na soma zuwa Catering school na billy galadanchi wanda takeyi a unguwar su na arqilla, acikin gidanta take koyarwar ta gaji da zaman ko oho datake agidan nasu, ada takanyi girki yanzu kuwa en aiki sukeyi an zauna daula, tanajin labarin wannan me koyarda girki ta ruga tae registration domin tana qaunar fannin girki gashi ko alihi bata iyaba banda abincin gargajiya daba laifi Baba Azumi ta koyar dasu!!.....a daidaita ta hau har zuwa gidan domin yaune zasu fara tarigada tayi registration da kud'ad'en da Maheer ya bata kanya bar garin.....tana sauka adaidaita wayanta ya soma bulayin neman dauki...dakatar da komai tae ta d'auki kiran na qawar ta islam
"Hafsat nashiga uku na" shine abinda ta furta tana kuka, hankalin hafsat ya tashi tace tae hakuri zata zo gidansu idan ta kammala da school aikam ana idarwa ta wuce gidansu nanuwa.....babu abinda ta b'oye mata komai seda ta sanar mata dake faruwa from A to Z abinda ya faru, nanuwa kanta ta girgiza tace
"To yanzu dai Islam kiyi hakuri na san zezo miki jibi saturday semu bashi hakuri" kallinta tae
"Tun ranar yau kwanaki kusan 5 be qara kirana ba, ni kuma gagara kiransa" shiru Nanuwa tae kan tace
"Zezo miki a lokacin dabakiyi tsammani ba ina gaya miki karki damu kinji?" Haka tae ta bata baki har yamma kanta wuce gida akan washe gari juma'a zata dawo...
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
*Assalamu Alaikum, ina me baku hakurin rashin cika alqawari hakan ya farune sabida matsalar wattpad sena kammala typing seya share gaba daya, sabida haka nakega zamu miyarda posting book din idan anyi yau gobe baza'ayi ba se kuma jibi*
07
**********
Zaman makarantar haka ya kasance cikeda wata iriyar shaquwa tsananin maheer damuka islam, kullum suna tare kokuma idan basa tare to kuwa suna nan maqale a waya amma Maheer betab'a furtawa Islam kalmar so ba....yayinda Nancy ke matuqar shan wahalar soyayyar datake wa Maheer wacce ta tabbatar koda babu Islam baze so er qauye irin taba, kullum setayi kukan rashin sa da soyayyar sa datake neman illatar da ita, yauma kamar kullum tana zaune yana zuba lecture yana musu sallama akan se sun dawo hutu tunda sun kammala exams dinsu yau, ji tae wani zazzafan zazzab'i ya mata dirar mikiya, koyaya zata iya jure rashin Maheer na watanni uku? Koyaya zataji bayan rabuwar da zasuyi? Ganinsa kawai yakan saukar mata da nutsuwa sosai azuciyarta mesa zuciyarta da gangar jiknta basu mata adalci ba akan soyayyar Maheer? Ina ita ina shi? Ko bayan talauci batada wani gata a duniyar nan se Allah.....haka aka watse kowa ya fashe hannunta Islam taja
"Muje office d'in sir maheer yace na sameshi office" badan bataso ba amma tasani sabon ciwon zuciya kawai zata samu sabida yanda Islam ke wani karairaya tana zuba shagwab'a kuma Sir Maheer d'in yana biyeta abin sam ba'a magana......
Kallon kallo suka tsayayi na en daqiqu yayinda kan daga bisani Maheer ya sauke ajiyan zuciya yace cikin zolaya
"En mata lapiya kinga fine boi kin bini da kallo se ince se an biyani kallo na da akeyi" shagwab'e fuska tae
"Allah ni Sir kaine kake kallo na, kuma kasan nafika kyau" murmushi yae yace
"Am dena yayin lukutayen mata ne silinda nake so kinji naga alamun so kike ki nanuqemun yanzu kuma meya kawo ki" murmushi tae ta zauna kusa da Nancy datae zaune tae quri da ido tana kallon su, kamo hannunta tae tace
"Dan Allah Nancy nida Sir wayafi kyau? Kuma ina agabanki yamun waya kafin mushiga exams cewa na sameshi office" murmushi tae aciki niqafin ta tace cikin muryan ta me sanyi
"Qawata kin fishi kyau shima yasani ai, kuma mu bamuce munayi dashiba sadakin mu tsadanr dashi baze iyaba" kallonta yae karo na farko kenan dayaji tayi magana da raha kuma me tsayi har haka yace
"Aini banasan lukutar mace, aje cen akai kasuwa" dariya suka saka dukkansu se yau yajiyo sautin dariyarta daya kusa kashesa akan yanda yaji yakeson yanayin dariyar ta cikin jan ciki murya can qasa qasa me taushi, kawar da wannan tunanin yae,cen kuma ya tsinkayi muryan ta tana fad'in
"Dama Lukutaye seme mota kaiko taya baka dashi, bana baiwa talaka qawata" dariyar suka qara sakawa dukansu ya zauna kana yace yana kallon islam
"Issy baby nifa daga nan se kano, shisa nace kizo mui sallama, inshaa Allah yau kano ta dabo zan kwana, tunda aka soma exams banje naga umma na ba zumud'i nake" Ga mamakin Nancy Qwallah tagani a idon Islam harya fara silalo mata ta tsinkayi muryanta tana furta
"Haba mana dan Allah, ka bari se gobe kaji" ta qarashe maganar murya na rawa har tana langwab'e kai, a rikice ya d'an kalle ta
"Bana san kukannan Islam ki dena naji sengobe shikenan?" Murmushi tai ta soma share hawayenta
"Zan bika muje gidan ka tare yau muyi hiran bankwana" murmushi yae yace
"Ina godiya Issy baby" miqewa tae tace
"Kanku fito Barinje in karbi saqo gun Asmy bala zan dawo" Islam tasan qarya take amma bata takura taba harta juya Maheer yace
"Nancy!!" A rayuwa setaji babu namijkn daya iya kiran sunanta kamar shi kai gabaki daya duniyar ma sunan yafi dacewa da bakinsa, juyowa tae ta kalleshi ido cikin ido ata madubin yake hango idanta masu d'aukar hankali tace
"Sir" miqewa yae ya janyo envelop a aljihunsa ya matso kusa da ita ya miqa mata
"Bana kyauta ace baza'a karb'a ba, karki mun gaddama ungo kawai kije ki siya sabon niqafi da hijabai, itama wannan lukutar zan bata na siyan mayafai" hannunsa ta kalla ta miyarda dubanta a kansa
"Amma Sir....."
"Shsssssssshhhhh" ya furta,tare da d'aura d'an yatsanta na nuni saman lips nashi
"Reserve it plss, ki karb'a kawai kinji" ya qarashe maganar da taushin murya, hannu biyu ta sanya ta karb'a har tana russunawa
"Allah ya saka da alkhairi ya qara bud'i" murmushi yae yace
."Banaji zaki samemu anan dan yanzu zamu bar nan so inaga kwa had'u town ko?" Murmushi ta masa dame san tanayi ba tunda ta lullub'e fuska tace
"Badamuwa ina maka fatan alkhairi, Islam mayi waya ko" haka ta fice zuciyarta tana mata quna ta sona zargin sun fara abinda islam ta iya da Maheer wataqil shima din ta gama dashi a wannan bangaren in shima fasiqi ne gwara tun wuri ta ciresa a ranta amma dukda haka zata tambayi Islam taji!....
Durqushe yake agaban Islam yana faman rarrashi, juyin duniya yayi amma taqi hakura ta dena kukan shiya yasan zeyi da rayuwarsa, cikin dakiya yace
"Yanzu abinda za'ayi kiyi hakuri duk bayan sati biyu namiki alqawarin zanzo har sokoto na ganki shikenan ya miki" kallon shi tae ta wani shagwab'e fuska
"Bazan iya yin sati bane ban ganka ba ai, ni gaskia yamun nisa" daganan taci gaba da rusa uban kukan ta wiwi tamkar wata jinjira, har cikin ransa bayason kukan yarinyar ya tsani jin kukan ta, ji yake tamkar ya rumgumeta amma sam baze iya ba sabi sanin haramcin aikata hakan dayayi, miyarda dubansa yae zuwaga hannunta yanaso ya riqo hannun nata ya rarrashe amma wani sashin na zuciyarsa ya masa hani dayin hakan, duk zamansa turai be taba yin irin wannan shashan cinba, yasandai yakanje gidansu qawayensa mata suma kuma sukan zo masa amma babu wannan aransa, yana dai ganin ziyarar ba komai bace idan kasan zaka riqe kanka da mutunci kaji tsoron Allah.
Note: muba al'adarmu bace kuma sam musulunci be aminta da keb'ewar mace da namiji idan har ba muharramarsa bace,so kar ayi tunanin zuwa gidan saurayi ko dakinsa a kallesa ba'a bakin komai ba.
"To kiyi hakuri sati d'aid'aya duk bayan sati d'aya zanzo ranar saturday da safe in koma sunday da azahar ya miki" tana qwalla tana murmushi ta gyad'awa Maheer kai,miqewa yae daga tsugunon da yae ya juya mata baya kanya soma magana
"Islam inaga lokaci yayi daya kamata kisan matsayin dakike dashi a zuciyata, ki sani tun farkon ganina dake naji kin kwantamun arai, ina qaunar ko qauna me tsanani zan iya yin koma miye akan in faranta miki rai, dan Allah Islam ki soni ki qaunaceni kamar yanda nake miki karki gujemun" miqewa tae wani farin ciki ya gama mamaye ranta tace cikeda shauqi
"Nagode sosai da soyayyar ka agareni Maheer bazan tab'a manta karamcin kaba ka sani nima ina qaunar ka sosai kuwa" dukda yake ya hango tsantsar tsoyayyarsa a wurin Islam beyi tsammanin zata amsa masa kai tsaye haka ba .....sosai ya fad'ad'a fara'arsa ya matso daf da ita yace
"Ina qaunarki islam sedai inada tsananin kishi, wannan hutun da zamuje na tsawon watanni uku inaga senayi rama dan Allah ki riqr amanar dazan baki na kanki, ki kularmun da kanki, ba alfahari ba amma dukkanin lalurar dakike da ita zan iya d'auke miki ita, base kin had'amun soyayyata data wani naba kinji Islam" murmushi tae
"Kar wannan ya dameka dear Maheer inshaa Allah baka tarar da kowa ba kaima ba wanda ze tarar dakai bare ya ture gwamnatinka koyace zeyi takara dakai, basemunje gayin quri'a ba ka cinye" zama yae yana murmushi.....
************
Acikin watanni biyu da akai hana hutu sosai Nancy tae jiki ta kuma freshh sedai damuwar fal a ranta akan Maheer, tayi iyakar yinta ta kasa ciresa aranta duk yayinda taso ta zamesa a ranta abin seya faskara gaba daya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 20