takardan yai ta gagara karb'a a gefen ta ya ajiye ya juya mata baya
"Ga takardar sakinki nan, ban sakeki dan bana sankiba, Allah ya sani akanki nasan meye so kuma har gobe ina sanki, sedai bazan zauna da macen dake iya yin kisa ba, 'yata kije da ita sekin yaye ta tukunna ,zan k'arb'o abata, dummanin abubuwan dake ciki Gidannan danke na siya ki tattare ki tafi dashi har motoci dake mallakinki, zan turo miliyan biyar a acc naki kimun renon 'yata, ki shirya da safe za'a maidaki sokoto" Wata uwar k'ara ta k'walla tahau magiya har waje ta bishi amma be saurare taba!!!
....\ko saki nawane akawa baiwar Allah, ko zaman ze k'ara dawowa oho.....muje zuwa
Pheey gobe da safe akwai wani inshaa Allah,inayinki tawan kina k'aunar littafinnan fiye da kowa dame rubutun gaba d'ayaπππ
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*πΏWATA FUSKAπΏ*
π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦π¦
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
50
Jikin islam har rawa yakeyi sanda ta dawo cikin gidan, takardan data barshi akan gado ta d'auka amma ta gagara bud'ewa, tunawan datai da umma me ya bata damar juyawa tana d'ingishi da k'afarta ko 'yarta bata tsaya karb'a ba ta juya a sittin, da kanta tai tuk'i zuwa asibitin da takardan a hannunta, bata tsammanin ganin kowa a ICH wannan ya bata daman zuwa office na fareedah dan kuwa anan ta barsu, koda taje kuwa tai sa'a suna nan, wurin umma taje ta durk'usa da k'afufuwan ta tana kuka
"Umma dan Allah ki tallafeni ki ceceni ki kuma agajeni, Maheer ya sakeni umma kinga takardan daya bani wai inaso zan yi kisa harso biyu, wlhy umma k'addarane ya fad'o damu nida Hafsat amma wlhy garin ceton tane ma nima na fad'o, ki cewa maheer ya taimakeni ya miyar dani d'akina wlhy shine farin cikina dan Allah kimun tallafi" Tunda Islam ta soma magana umman ke kallonta ta gagara koda motsi, ko ba komai ta tsorata da yanayin yaronta d'azu be tab'a mata kwatankwacin yanda yae ba d'azu hankalinta yakai k'ololuwar b'aci tama rasa me zatace, yanzu mezata cewa Abba idan yaji? Farida ce tai k'arfin halin karb'ar takardan ta bud'e ta soma karantawa da sauri wata wawiyar ajiyan zuciya ta sauke ta zauna dafe da kai kantace
"Saki d'aya ne Umma, dan Allah awa tufkar hanci, dan gaskia wannan ya zama hauka, daga faruwar abu bakada ilimi akanshi blindly kurin ka sako saki, an gayawa Maheer aure abun wasa ne wai? Ko kuma muya mayar shashashai? Ubanwaye ma yace dashi islam ta wurgo Hafsat d'in? Ita ta wurgo ta kuma suka fad'o a tare? Gaskia umma bakwa duba lamarin rayuwar maheer yanda ya dace abubuwa yakeyi gaba gad'i, ko zancen auren nan na hafsat haka yae iskancin nan yazo ya narke kuka amince masa batare dakoda jin ra'ayin yarinyar ba, wannan kurin ya isa ya haddasa fitina, tun wuri gwara a kirashi wlhy a nuna masa kuskurensa" Nisawa Umman tai kanta rik'o hannun islam
"Baze k'ara aikata wannan kuskuren ba inhar dai nice na haifesa, sannan ki koma gidan ki yanzu karnaji zancen kin tafi gidanku, karma ki gaya musu wannan mugun labarin, zanga maheer d'in ai" Godiya islam tayi sannan ta nemi komawa hanyar gida....
****------****
Maheer kai tsaye asibiti ya koma, Wurin da Hafsat take yaje ya tsaya wurin glass daze rik'a hangota, se k'wallan dake wanko masa ziyarar ba zata yake zubarwa, yayinda sakin dayawa islam ya masa tsaye a wuya, yana wa islam wani irin so dabaya tunanin amma tab'a halittar irin sa, tafiyar da yai yabar nata gida yasha wahalan rashin ta, har mamakin kansa yakeyi ya daurene kurun sabida yanuna mata iya karta, yanaji ajikinsa idan yaje gidan zuwa anjima ze dakatar da ita akan tafiyar da tai niyan yi....ya kasa barin hafsat ne tausayinta yakeji kamar me, baiwar Allah tun tasowar ta a wahala take har yanzu...yana tsaye a wurin ya kusa da sauyawar yanayin kwanciyarta alamun ta motsa, be b'ata lokaci me tsawo ba ya juya zuwa officr na Fareedah don sanar mata acen ya tarar dasu rai a b'ace, umman ma ta had'a fuska be damuba ya gayawa Fareedah a gaggauce suka fita zuwa ICH d'in..
Dr. Sam yarigasu isa wurin sabida shi dama yana aikin yamma ne, taimakon gaggawa ya bata ganin tayi regaining conciousnes nata, dama sun bada 24 hours ne idan bata farfad'o bama suna ganin se wani ikon Allah, idan kuma ta farfad'o Alhamdulillah....to 1 hour ya rage 24 hours din ya cika shisa ma yazo dubata, yaji dad'i sosai ganin ta farfad'o sedai batai masa magana ba, se binsa da kallo takeyi haka aka hana musu shiga su Maheer Fareeda ne kurun ta samu damar shigowa inda taketa murna dan suna shirin fidda rai da ita ne..
****----***
Alhj Baba ba k'aramun tashin hankali yake cikiba, ganin babban mutum ya matsa lamba akan anemo masa shi, Abban Maheer ya matsa matuk'a akan neman sa, wannan ne ya sanya ya gudu daga Nigeria gaba d'aya zuwa Ghana tafiyan dabesan ran dawowa ba sabida da asirinsa ya tonu gwara a tsinta gawar sa......Ga cutar dayawa d'an uwansa (Mahaifin Ameenu") sabida rikon amanar aminun ya bashi amma yaketa hallaka masa 'ya'ya yasan hakki kadai seyaci qaniyar sa.
Su ummul kuwa ita da Ameen kamar su cinye junansu, jin kansu sukeyi tamkar sababbin had'uwa duk motsi idanshi yana kanta, Neman iyayen Naja ya sanya a gaba kuma inshaa Allah ze gansu ne sedai bashi da kanshi ke neman nasuba ya sanya ne amasa bincike.
****-----***
Maheer yasha fad'a sosai a wurin Umma, kuma Hafsat da bakinta ta fad'i yanda komai ya kasance tsakaninta da islam, hasalima islam ta fad'one garin ceton ta daga fad'owa ita, yaji haushin kanshi na yanke hukunci cikin fushi kuma batare da buncike ba ya baiwa islam hak'uri inda yai shirin ganin ya had'e kan matan sa da yardar Allah kuma baze k'ara baiwa wani damar daze shiga tsakanin suba...
Hafsat dai ana asibiti har lokacin jiki se adu'a yak'i dad'i an kasa gano bakin zaren... Maheer duk a rikice yake, yasha mamakin islm ma dabata masa fushi ba, dan kuwa dayaji musababbin faruwar abun duk seyaji kunya da nauyinta ya matuk'ar kamashi...
Dafe kai Maheer yai, lamarin na Hafsat yana d'aure kanshi, se tayi kaman taji sauqi da rana se kuma dare nayi zazzab'i ya kuma lullub'eta, ga komai taci amai take kelamawa, bata masan ganin abinci, tayi wani mugun fari ta rame sosai sumar kanta kurin ke k'ara tsayi se uban goshi, islam ce keta kaikawo a wurinta tunda yake Ummul ba lafiya ne da itaba, ita kanta Baba Azumi da Naja ke kulawa da ita
"Yanzh Anty Fareeda meye mafita, kodai zan kwashe tane mu tafi london a dubamun ita yanda ya dace, naga anan komai nata sekuce normal amma ciwo yak'ici yak'i cinyewa yarinya dukta rame, nida akace mamanta zatazo ma dukse naji kunya wlhy, kartazo taga 'yarta kaman ana d'ebanta ana miya" D'an murmushi Fareedah tai dabekai zuciba ta kalleshi sosai
"Maheer Hafsat fa cikine da ita, alamomi da yawa sun nuna mana hakan, bana tunanin wanin ciwon ne daya wuce haka, yanzu haka d'azu da kaina nakai jinin ta lab, za'a mata syrum pregnancy test" kallonta yai da murmushin yake shima
"Kai Anty Reedah ni se kika bani dariya wlhy, ciki dai sekace almara, nifa tunda taji wannan ciwon rabona da ita, abu so d'aya kurin" kan tai magana an soma knocking na k'ofar office d'in izinin shigowa ta bayar aka shigo, Lawal ne me aiki a lab datace idan result ya kammala ya kawo mata...karba kurun tai ya juya tana dubawa ta soma dariya
"Lallai k'anina ka iya aika aika, yanzu yarinya ko amarci batasan dad'in saba zaka mata haka, cikin ma me wahala irin hakan nan, to kadai gani cikin satinsa shida da kwana hud'u" wara idanshi yae wato wannan sati ukun datai a asibiti duk azaban cikine, amma be tab'a kawowa kanshi hakan ba ciki da wuri haka...shi d'inma dariya yai
"Anty gaskia wasane" Dariyan taci gaba dayi
"Wlhy ba wasa bane ba, ni dariya ma kake bani wlhy, koda yake tsarin Allah ya zarce na kowa, Allah ya bata lafiya yanzu kam se a duba cikin, sabida tayita shan magungunan dabe dace da itaba" haka suka zanta sosai akan hakan,yamma aka kaita hoto ciki lafiyan sa qalau, gogar tamu dama ashe ta fahimci hakan sabida al'adanta daya dena zuwa tun bayan da suka sadu da Maheer batai magana bane sabida kunya, ranar taga tarairaya kuwa, umma ma da abin yabata kunya ai barin d'akin tai gaba d'aya..
********---********
*Bayan wata d'aya*
Tsakanin Islam da Maheer babu wata damuwa, hafsat kuwa tana gidan umma gashi kuma hutu ya kusa k'arewa, umma ta hanashi matarsa wai batada lafiya koda yake hakanne, ganin ummul ba k'aramun dad'i yawa Hafsat ba, har kukan dad'i tai mara iyaka.....dukda yake ummul tabi hasken *WATA FUSKAR* ne dake k'ark'ashin fuskar Ameen me tsananin duhu ada ta cuci kanta da kanta, hakan baze hanaka tausayin taba ainun, ga k'uruciya ga rashin mahaifa, dama Allah yasota da idan Rahama tanada yara har uku sedai fatan Allah ya raya mata su.....
*Bayan wasu en kwanaki*
Har lokacin babu alamar umma zata sakowa maheer matarsa, wannan ne dalilin dayisa sam ya kasa dukuni, zuwa yai gidan Anty Fareedah ya sanar mata shifa yanason matarsa ta tare agidanta kan su koma, hutu ya k'are tawa umman magana, tasha dariya kanta kora masa bayanin damuwarta akan hukuncin Abba akan Anty Nasara, nan suka yanke shawarar baiwa Abban hakuri, hakan kuwa akayi yace ya wuce su kuma suka d'unguma zuwa gidan ta, acen kana ganinta kasan taji dad'in ganin su sun jima sosai suna magana har shawarwari suka bata da kuma Nasiha taji dad'in hakan ta sakko daga mugun dokin data hau na cewan setaga bayan auren maheer da 'yayan talakawa, ta bashi hak'uri sosai inda tace da safe da kanta zatawa Umman maganar Hafsat har gidan zataje.....
*************
Umman tacene bazata baiwa Maheer Hafsat ba seya mata kayan lefe, shikuma shap ya manta da hakan aikam shida yayyinsa mata suka zage suka nunawa dala rashin mutunci mara k'arewa ciki kuwa hadda kyautar motoci k'waya biyu.......gidansu na sokoto suka kai kayan gaba d'aya inda Baba iro se washe bakinsa yake inda Baba azumi da ummul ma tazo da en tagwayenta, Ameen da Maheer ana cewa Ameen Ameer, Maheer kuma Babul kasancewan yafisa jiki, haka nan Ameen yaji sakawa yaran sunayen nan nasa dana abokinsa awani bangaren kuma aminin saππ.....
Koda akace za'a kaita gidanta ranar wata juma'a tasha kuka, k'arara ta nunawa Anty Fareedah tsananin tsoron datakewa maheer, rarrashi sosai tasha daga gunsu itada Anty Nasara kan daga bisani a kaita gidan ta, cikeda mugun tsoro take zaune agidan, sanda ya shigo ma sosai ya mata kamada yanda take ganin mazan littafi na zuwar ma matayensu, jikinta se karkawa yakeyi sanda ya zauna a kusa da ita, be b'ata lokacin saba wurin aika mata kyakyawar ajiyan zuciya lokaci d'aya kuma ya sauke kyakyawan ajiyan zuciya, batace masa komai ba harya kai hannunsa saman mararta, d'an cikinta ya soma danno kai yana murmushi yace
"Amarya inaso zan gaisa da babyna, yaya kenan" Bata gane me yake nufi ba, amma seta tsinci kalamansa da sanya fad'uwar gaba!!!!
"Kafasan ina ciwo ko, kasan banida lafiya ya maheer, yaya kakeso jik.......bata k'arisa fad'an maganar taba ya manne bakinsu wuri d'aya, tun tana tattureshi har yae nasaran kashe mata jikinta, aikuwa lafiya lau yabi da abarsa yau dukda yasha kuka kam sabida a tsorace take amma bata wani ji zafi bama. Seda komai ya lafa ya bita da kallo, mata ko wacce da baiwarta a rayuwa, idan yace islam rake ce sarkin ruwa da zak'i mexe cewa hafsat? Yama rasa wacce ce acikin matansa zece tafi wata abu d'aya ya sani dukkaninsu suna matuk'ar gamsar dashi, kuma alfahari dasu, acikin mazaje bakowane yakeyin tsantsar sa'ar da yae ba......" Sannu Beautiful yau dai ba zafi ko?" fuskarta da rufe da tafukan hannayenta duka biyu alamun jin kunya matuk'a.....
************
Rayuwar girmama juna akeyi tsakanin dukkanin ahalin na Maheer, tubdaga kan gidansu har kowa ma, Sophie da Mahal auren su ya kusa ga cikin hafsat ya tsufa, shauty ma tasamu wani saurayin daze aureta yaron aminin mahaifinsu cikin kwanciyar hankali suke zuba love wanda atare gaba d'aya za'a ha'da ai bikin, su dama daga wannan hutun sun kammala karatun su.
Lafiya lau Hafsat ta haifi yaronta namiji me kyau, da tsananin kamanni da maheer ko kadan be dakko taba... Murna awurin maheer ba'a magana sam...yaro yaci sunan Abba ana kiran shi da Abbi..
*Bayan shakaru biyu*
Babu shakka zaman lafiya yafi zama d'an sarki, yanzu kam islam da Hafsat amintarsu ta k'ara ta ninka ta dawo fiyr ma da da, bazaka tab'a cewa sud'in kishiyoyi bane, a london duk sun kusa kammala karatu islam dai ciki har yau shiru ga babu an girma haka Hafsat ma, maheer anyi k'iba sosai sejinsa yakeyi wasai sabida ya had'e kan matansa ababen sansa.
Alhj Baba dai Anyi neman duniya babu labarinsa, har yanzu Allah shikad'ai ya baiwa kansa sanin inda yake kai jariran dayake garkuwa dasu an hakura ma an shareshi tunda yake yanzu ummul dame gidanta suna zaune kalau.
Naja kam babu labarin iyayenta, da wannan Ameen ya aureta tazo ata biyu, dole ummul ta hakura tunda kuwa batama haihuwar yanzu, wannan shine aminta da *WATA FUSKAR* dukda yake k'addara tarigayi fata dama.
*Tammat bi hamdillah*
Ba haka muka soba, amma bamuda abinyi ramadan yazo dole mu datse abubuwa da yawa, ina godiya sosau ga d'inbin masoyan wannan tafiyar Allah bar k'auna.
*Domin jin k'arashin labarin Alhj Baba, nemi littafi me zuwa idan munada rai da lafiya bayan sallah me suna *SA'A......TAFI MANYAN KAYA* na Billy galadanchi k'awar Billyn Abdulπππ€π€ kuma takwararta, ku daure ku rik"a banbanta sunayen nan dan Allah kuna bamu wuya.
Mom Nu'aiym ke muku fatan Alkhairi.
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.
AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.
We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction, non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors
We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with thier permission.
AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.
Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin, soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 20