Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
botiran rigar sa.......... Seda ta cire su tas sannan ta cire na hannun rigar ta zare masa rigar, shidai bece komai ba babu kuma alamun se kulata koya dakatar da ita, nauyi ita kuma takeji jitake tamkar k'asa ta tsage ta shige, singlet d'in jikinsa ta zaro daga kasan wandonsa ta zare masa, se wani kallo yake binta dashi yana lumshe ido alamar gajiya......kallon shi tayi gargasan girjinsa daya wani kwanta luff har zuwa tsagun marar sa yayi k'asa ga packs d'innan guda shida sunsha zane,batada dabaranyi dan bazata iyaba "Kayi hakuri" Da d'an mamaki ya kalleta "Menene?" Shine tambaya daya mata "Bazan iya cirewa ba" lumshe idanshi yayi ya juya "Kibar d'akin kawai" tsaye tayi taga kaman yayi fushi "Kayi Hak'uri yaa mahii, wlhy ba raini bane ban iya bane" hannu ya d'aga mata alamar ya isa sannan ya mata alamar barin d'akin da hannun shi, Jiki a sanyaye ta juya kome ya sameshi oho, dukya sauya tana isowa d'akinsu sophie ta rik'eta "Ke yau kinga idon yaa Maheer, wlhy halin yakeji ni seda ma ya tsoratani da yanda yake magana kodai waccen kojajjiyar ce ta hautsino mana shi" Tabare fuska tayi tamkar zatayi kuka "Wataqil kam, dan cewa yayi na had'a masa ruwan wanka na rage masa kayan jikinsa to kuma sophie tsakani da Allah ni kunya nakeji, fisabilillah wai sena kama na cirewa babba kaya" Dariya tayi "To Amarsu ya kukayi da angon?" K'wallan datake tarewa ya subo mata "Ni nacire sauran wandone bazan iya cirewa ba, nikam nace yayi hakuri shine yayi fushi ya koroni har yana juyamun baya😭😭😭😭" Dariya tabaiwa sophie ta somayi har tana rik'e ciki "Wlhy kinada wawta Nancy, ina mijinki ne? Kin fasan wacece kishiyarki wlhy ki rage wawta da kunyan kin nan, ni wlhy aka auramun Mahal nizanna riqa yi masa wanka ma ba cire kayaba, mujin kine fa, tukunna ma tsaya ina tare kuka kwana jiya mesa bakiqi kwana da shiba?" Kallonta tayi "Sekinyi auren ki gane wlhy da kunya matsananciya sophie, tayaya zan kalli yaa Maheer na cire masa....kai dama bashi bane wani na aura, yayana fa" Dariya tayi "To ki ringa daurewa kina masa abinda yakeso, yaa maheer seku shekara dari tare baki san halinsaba bayasan gadda shi sam, kuma shi ai yaga ke matar sace bakomai bane wannan ai" shiru bata kulata ta qara cewa "Ki tashi kije gunsa ki bashi hak'uri" Ba musu ta mike tana kokarin k'ulle sumar kanta kamar yanda takeyi idan ya dameta seta masa kullin bakar leda..... A bakin gado ta sameshi ya zauna dafe da kanshi dagashi se towel d'ure a qugu, zama tayi kusa dashi tace "Yaa maheer kozan tayaka da shafa oil d'inne ?" D'ago kansa yayi ya kalleta tasha mamakin ganin idanshi yayi jajir, da sauri ta rik'o hannun sa "Subhanallah yaa Maheer meke damunka" bece mata komai ba se kallonta yakeyi ana haka wayanshi ya soma ringing banza yayi har kiran ya yanke,cen kuma kiran ya k'ara shigowa wannan karon janyota yayi yana lumshe jajayen rinannun idanuwan sa...ya d'auka tare furta "Assalamu Alaikum" A d'ayan b'angaren kuma Umma ce "Alaikassalam Mahii" "Na'am Umma ina jinki" "Cewa na maka ka sauyawa yarinya suna daga Hafsat zuwa wani sunan daban karka kasance namiji me haddasa fitina a gidansa, matarka takirani a waya tanata kuka, sanin kankane ba macen dazataji dad'i ace anmata kishiya bata saniba kuma da k'awarta, har kullum ina maka gargad'i akan yin adalci a tsakanin matayenka, Abbanka yanada dalilinsa na cewa kar a gaya mata yanzu, gudun fitina yakeyi kuma yasan halin mata su tashi hankulansu agarin daba nasuba basuda kowa" "Umma kiyi hak'uri ai nace zan sauya sunan inshaa Allah" "Sannan takirani yanzu ma akan wai kabar gidan zuwa gidan su Sophie, meye dalilinka nayin hakan? Baka gudun tayi zargin wani abu kota gano wane abun" Ranshi ya matuk'ar b'aci dandai Umma ce "Umma bazan iya kwana gida d'aya da sirikata ba wlhy, kana bazan iya zama awani wurin ni kad'ai ba, ki k'yalesu kurun suna kuma da kikace a sauya mata seki zab'a danni harga Allah bansan wani suna dazan baiwa babyn ba" Nisawa Umman tayi tasani sosai Maheer yanason sunan daya zab'a d'in nan takuma sani bazeji dad'in haban ba amma matar safa? Suna zaman lafiya idan ta gano sunan kishiyara aka sakawa babyn ta yaya zataji? Ai suma seta d'aukesu mutanen banza ... "Autan maza kayi Hakuri, ka baiwa yarinyar nan suna Aisha kaga itace mahaifiyar Abban ku semu sakala mata sunan daya dace ana kiranta dash shida kanshi zeji dad'in hakan, inshaa Allahu" "Babu damuwa Umma zanna rik'a kiranta Mamaa Allah yasanya albarka" "Ameen autan maza, Allah yamaka albarka, kayi hakuri nasan halinka da zuciya dakuma yawan ciwon kai idan ranka ya b'aci dan Allah kayi hakuri, kakuma nemi hanya me sauk'i ta gayawa matarka aurenka da Hafsatun idan kun dawo, naji ance nanda kwana 30 zasu kammala jarabawa suyi hutu seka tarkatasu ku dawo gida anan semu sanarwa matar taka" Nisawa yayi "babu komai Ummana yanda duk kikeso haka zanyi,albarkanki kurun nake nema" Albarkan ta sanya masa ta masa godiya sosai sannan sukayi sallama, kanshi dake sara masa ya danne da duka hannayenshi guda biyu jikinsa harya soma rawa tsabar macin rai, baze iya yiwa ummansa musu ba, kisane kurun zata sakashi yace bazeyi ba, amma Islam ta gama rainashi wlhy, shi zatawa iskanci da wulak'anci takai k'ararsa gun iyayensa abinda yafi tsana, bazata masa magana bama setaje ta gayashi da iyayenshi lallai ma Salaha....... Duk se Nancy taji wani iri batajin me umma ke cewa amma ta fahimci akan sunan baby ne...... Rintse idanta tayi ta kai hannunta sama waits nashi ta zagaye "Meyake damunka Zauji?" "Ba komai ki kawomun coffee" zuwa tai ta had'o ta kawo masa,da kanta ta bashi coffee din me zafi yasha sosai, sannan ya nemi gadon ya kwanta luff dashi, kasa barinsa tayi shi kadai taje ta rage kayan nauyin jikinta zuwa nashan iska, tadawo d'akin da wayarta a hannu, kai tsaye gadon ta d'are ta soma daddan na masa bayanshi da kafad'un shi yana jinta amma ko motsawa beyi ba, sabida harga Allah yanajin dad'in tausar seda taji ya soma minshari sannan ta rufe shi da duvet, tana shirin kwanciya ta huta wayanta yayi k'ara, lambar London ce amma batada lambar, a sukwane ta d'ag kiran "Bak'ar ashana k'ona gari, kina ganin kamar kinci galabane da kika sanya aka sanyawa 'yata sunanki? To na nuna isata na kira sirikata for ur information yanzu sunan yarinyata Aisha, banza karuwa mebin mazan mutane er tasha, uwarki ta k'are a karuwanci kema acen zaki k'are wlhy keda mijina har abada er dandi er dadiro yar kwararo haihuwar kan titi kawai" Ba kad'anba kalaman islam suna k'ona ran Hafsat tace "Yanzu islam ni kike jifa da muggan kalamai irin wannan mena miki? In isheni akan mijinki, wai idan har inason auren na mijinki ne ke kin isa ki hanani auren nashine? Wlhy so dubu yafi ganin k'ima na dake, ke kin manta inda aka fito ne dazaki rik'a kirana karuwa, kijimun iskancin banza wai bayarbe keceda inyamuri kafiri, bari kiji islam wlhy kika k'ara kirana kina zagina sena nuna miki baki sanni bq tukunna, halacci ne kurun nakeyi ina qyaleki bawai don ina tsoron kiba,k'wacen miji kuma zakiga yanda akeyinshi wlhy banza shasha.... " Uwarkice banza, nace matsiyaciyar uwarkice banza, mugayen buzaye masu bak'ar aniya, wlhy sena sanya an lahanta miki rayuwa akan maheer mayya kawai, ko a lahira idan ana aure bazaki tab'a aurar maheer ba bare kuma a duniya ana zaune, shegiya er tasha" tsaki nancy taja ta katse kiran.......kai tsaye Anty Fareeda ta kira, tana d'agawa ta saka mata kuka "Anty Fareedah ni dan Allah kicewa Abba a miyar dani school a kano, wlhy na tsani zaman garin nan islam ta sakoni agaba Anty Reedah bata bari inashan iska, yanzu ta kirawoni har ummana seda ta zaga tana cemun karuwa waye waye" Nisawa Fareedah tayi Aiki kuwa yagano islam tabbas, amma ke Hafsat ki dena damuwa, umma tamun magana ma akan sunan baby nina qara bayarda goyon bayan a sauya, yarinyar sekin tashi tsaye makissaciya ce,ki dena kuka ina kan aiki yanzu anjima zan kiraki" sallama sukayi ta zauna tanata kukanta seda ta gaji bacci ya kwasheta a wurin... Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 42 Batai aune ba taji hannunsa a saman nata, yace Ehm Princess? Bakya buk'ata ne? Bakyaso ki kasance tare da mijinki? Idan hankalinki be kwanta ba karkiji shayin komai ki fad'a namiki alk'awarin zan barki harse sanda kika buk'ata, abu d'aya nakeso ki saka a ranki ina cikin tsananin buk'atar ki a yanzu" Har lokacin batace komai ba, bata kuma kalleshi ba se murmushi datakeyi matsowa yae daf da ita "Princess hafsy sarautar ya motsane ko azumun magana ne kikeyi?, Nace inaso in kasance tare da matana ko rowa za'a mun" wannan kalmar daya fad'a kansa tsaye daf da kunnenta ne ya sanya ta shige a k'irjinsa tana b'oye fuskarta aciki, ya kula sosai takejin kunyar sa yana son mace me kunya, tana daga cikin matayen dayake daraja darajarsu akoda yaushe, yasha fad'awa Kabeer baze auri mace wacce batada kunya ba se gashi yanzu Allah ya bashi....rungume abarsa yayi gaba'aya ya sanya hannu d'aya yana patting bayan ta a hankali "Princess kunya na kikeji? Ehm? Bani amsa mana kunya na kikeji?" K'ara cura kanta tayi a k'irjinsa, d'agota yayi ya zare mata hijabinta, lumshe idansa yayi yana godewa mak'agin wannan halittar, se k'ara shige masa takeyi in d name of kunya😂😂😂... Nan kuwa bata saniba kashe wa gogan jiki take k'arayi, numfashinsa se hauhawa yake sakamakon dadd'an k'amshin turaren ta me sanyi da sanyaya zuciya, a b'angarenta kuwa itama hakance kwanciyar hankali tare da nutsuwa me tarin yawa take samu a wannan k'amshin na jikin Maheer ko kad'an bata so ta rabu da jikinsa, sunyi shiru dukkansu na kusan mintuna uku kowanne da abinda yake sak'awa a ranshi, shine yai jarumtar furta "Ki d'agani mana muje kan gado" Kotak'i kotaso zamanta ajikinsa yayi matuk'ar tasiri agareta, bata shirya fitar kalmomin ba seji tayi sun fito a bakinta, a ranta take sak'a hakan batada labarin kalaman zuci sun fito "Inajin dad'in k'amshin dake fita ajikinka yaa Maheer, dan Allah ka barni" murmushi yayi "Tozan barki ajikina harse sanda kikace kin gaji, amma dukda haka muje kan gado nand'in gajiya zakiyi" seda ya bata amsa ta ankare da abinda tace, kasa motsi tai seda da kanshi ya mik'e ya d'agata chak zuwa kan gadon, zare jallabiyar jikinsa yae kana yawa kansa masauki a akan gadon tallafota yayi jikin ta rufe idanta tai yaja dogon hancinta ya sauke idanshi akan black lips d'inta asalin na buzaye shisa koda wane lokaci koda bata shafa lipstick ba yake kyau sosai yayi brown seyayiwa farar fatarta kyau matuk'a, Murmushin dayake kan fuskarsane ya fad'ad'a ganin yanda take rufe ido yanzu, ashe dama rainin na k'aryane dacen har mamakinta yake yanda take cire ma ta daddage ta k'ura masa na mujiya ido cikin ido "Ki kalleni mana Princess" murmushi tayi "Idan na kuskura na sanya idona anaka bana iya janye nawa, wani magnet ne inaga dakai a ido, idan ina kallonka bana iya janye idona sedai ko idan ka soma janyewa....idanma ba kallon ka nake ba idan idona yana a bud'e se magnet na idanka ya janyo nawa zuwa kanka nika barni a haka" Wasu lokutan setayi kaman bata surutu wani zubin kuma se kaga tana zuba tamkar ba ita ba "Naji nine me magnet d'in,amma kefa meye naki? Nifa dazaran kina wuri to bana shakka ko waye a wurin sena biki dana mujiya nake jin sauqi, nutsuwa ta gaba d'aya tattarewa take ta nemawa kanta mazauni a gunki, ke kuma wannene magnet naki?" Murmushi tayi kantace wani abin wayanshi ya soma ringing....janyota yai ya kara a kunne bayan ya d'aga kiran yana me k'ara matseta ajikinsa "Maheer wlhy ina cikin tashin hankali, Anzo har hotel an sumar dani an sace mun Ummul da tsohon ciki, Alhj Baba bashida imani Maheer, ko kasheta ze iyayi ayanda yakejin haushina, bansan me zanyiba, idan ma da hukuma nace zan had'ashi banida hujjan cewa shine kuma kaga asirinmu nida shi duk ze tonu tunda banida wata madafa, sefa ta wurin rabbu sabida nina me laifi ne" Zabura Maheer cikin tashin hankali "Subhanallah Ameenu, kagani ko kaga abunda nakewa gudu ko, yanzu da tun farko ka turo ta nan da babu abinda ze sameta, Niger ai ba garin b'uya bane ba, beside kanata zarya sati biyu kazo ka koma dole na gaya maka su sanya maka ido, yanzu kaga amaimakon kaika cutu 'yar mutane ce aciki bakasan halin datake ciki ba" Kuka ya saka masa "Wlhy na yarda maraici bala'i ne da inada iyaye na a raye meze sanya wannan azzalumin ya d'aurani akan gurb'atacciyar hanya irin wannan? Yanzu gashi banida mafita, ka taimakamun da mafita Maheer banida wani danasan ze fad'amun Gaskiya sekai Maheer, wlhy ummul tausayi take bai matuk'a, ga Nana Ummimi ma ita ba wani girma ba gashi tasha ciki, gaba uwarta a tare da ita, bansan ko itama yazo kanta ba" "Ka kwantar da hankalinka Ameenu, babu abinda ze sameta itama jinjirin kurun yake so ta haifa masa, yanzu shawara biyu zan baka idan ma babu kud'i a hannunka nizanyi komai na visa ka had'o wannan Najar da Jinjirar suzo mun nan London dough dai ba jimawa zan dawo amma gwara basa k'asar, kai kuma ka lafe akan maganar Ummul, karma ka nuna masa kadamu da d'aukewan daya mata, hikima kurin zata iya dawo maka da matarka amma rigima sam bazatayi ba, ina kacemun kadena kuje masa yanzu ka kanje gunsa har kuna gudanar da kasuwancin ku shima yadena maka maganar laifin daka masa, to kaima lafe masa ci gaba da binsa kamar ba'ayiba harmu gano bakin zaren" Nisawa yayi "To Maheer inshaa Allah zanyi yanda kace, amma Naja da Ummimi har ma na kaisu wurin wani abokina dake Ghana yanada kud'i sosai kuma akwai security sosai a gidansa, munyi magana akan ba inda zasuje Matsalar su d'aya Ummimi dake yawan tambayar mamanta, ta dinga kuka akan Ammy Ammy" Nisawa Maheer yai "Ka rik'a yawaita adu'a kana sadaka ana maka, inshaa Allah komai ze daidaita, ka kuma sanarwa iyayenta" A raunane yace "Na sanar dasu, yanzu haka Babarta tana kwance a asibiti hawan jini ya kwashe ta, se ciwo take akan 'yar wlhy duk na damu" ban baki yashiga yi seda ya kwantar da hankalinsa had'e da shawarwari sunfi 40mns a waya, Nancy dukta rud'e kan sui sallama "Yaa maheer meya samu Ummul na ne, jiyan ma seda na kirawo wayanta amma bejeba meya sameta ne?" Tausayinta yaji ya janyo hannunta yace "Hafsat ki saurareni kiji mezan gaya miki, dama na sanar akan matsalar da Ummul da Ameenu ke ciki to shine shekaranjiya se aka.........ya kwashe komai ya gaya mata, aikam kuka ta sanya masa wiwi wai ita 'yar uwata.....janyota yai jikknsa ya dinga rarrashi da ban baki, a haka hartayi bacci a jikinsa se sauke numfashi takeyi da k'yar alamun baccin ma ba a dad'in rai take yinsa ba sosai ya shiga damuwa. ******** Washe gari kuwa koda ya tashi harta bar d'akin, da tsananin ciwon kai ta farka akan damuwa, tanata mafarkin 'yar uwarta, last call nasu ma video call ne har aka bata mamanta taga k'aton cikin ummul se dariya take mata tana cewa tayi k'aton hanci ta zama k'atuwa....tana buk'atar kad'aicewa sabida ta samu yin nazari, be takurata ba ya shirya ya wuce abunshi gun islam, sallamar farko da fad'a suka fara wai jiya ya tafi da wuri kuma ko waya me yake nufi da ita, ya mata ciki ta haihu ze wulak'antata aiko laplfiyan baby ya kira yaji, Hakuri ya bata had'e da yi mata 'yan wasanni kan ya shawo kanta suci gaba da hirarrakinsu na soyayya tsakanin miji da mata se Allah kankace kwabo sun gama daidaitawa kamar ba'ayiba.... Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 43 Ranar maheer bashi yabar gidan Islam ba se washe gari, se zuba love akeyi ta bashi hak'uri kuma yaji dad'in hakan, yana son mutum yayi kuskure ya kuma bada hak'uri, yanda aka nanuk'ewa juna tamkar ba jego akeyi ba, shinshina da shafe shafe yashashi a wurin islam seda ta tabbatar ta gamsar dashi da wasanni tukunna ta tsiri kukan ya kwana mata, Bayason rigimar islam sukai sharad'i akan daga ranar baze k'ara kwana mata ba se Inna ta wuce, haka tace ta yarda sabida ta shrya shagaltar dashi kullum idan yazo.....wannan ma yana daga cikin shirin Anty Nasara na ganin bayan auren islam wanda ita a zatonta sone....... ********* Tun wuraren k'arfe tara na dare Hafsat tawa su Sophie sallama ta wuce d'akin yaa Maheer, dayike sunada Exams setaje da takardunta tana dubawa, tun tana saka ran ze dawo har bacci ya d'auketa be dawo ba, ba ita ta farka ba se asuba, tasha mamakin inda yaje ya kwana be gaya mata ba, gata acikin damuwar abinda ya samu ummul har Baba iro sunyi waya akan Jikin Baba azumi ba kanta, gashi kuma yazo ya tafi ya barta ba sallama ba waya har yanzu baya kiranta a waya, tarasa dalilinsa nayin hakan......tamkar wacce k'wai ya fashewa a ciki haka tamik'e zuwa d'akinsu acen tayi wanka ta shirya ta wuce school tanada exams by 10:am......tana cikin school bus wayanta yai k'ara "Yaa Maheer" shine sunan data gani rad'au ya aiko mata message, a hankali ta bud'e message d'in "Good morning princess, hope kin tashi lapiya, jiyan na kwana wurin su islam ne, dafatan bakida matsalan komai?" Wani abu dabatasan ko meye shiba ya taso mata ya tokare mata k'ahon zuci, wani d'aci taji a yawun bakinta kanta ya sara mata, kashe wayanta gaba d'aya tayi aka huta, ta jingina da sit na kujerar datake kai, a hargitse tayi Exams din ta fito, amaimakon taje gidama library taje tanata karatu har yamma kuma bata bud'e wayanta ba, se bayan isha ta koma gida da azababben ciwon kan data rasa dalilin sa a rayuwa......sophie ta had'u da ita a parlor tana shan ruwa a cup "Ke Hafsat yau ina kika shiga anata nemanki, ko wayanki baya tafiya" a wahalce ta d'ago ta kalleta "Ina library karatu nayi ko gobe inada exams morning" jinjina kai tayi "To ai dakin gaya, yaa Maheer se masifa yake mana akan ina kikaje har yamma mukace school mudai mukasan kin tafi" guntun tsaki taja a hankali kan tace "Shima dai yasan ba b'ata zanyi ba a garin nan" ta wuce d'aki abunta, dama sunyi gulmansu da shauty akan be kyautaba jiya ya kwana cen gidan sun gano fushi tayi...... Yauma haka islam ta mantar da Maheer komai arayuwa, kissa da kisisna da iyayi, daga k'arshe ta bashi maganin bacci, bashi ya farka ba se washe gari karfe goma na safe, yasha mamakin wannan baccin, da girman sa baya iya tuna sanda ya rasa sallah asuba da sunan wai bacci ya sure shi, Amma kuskuren datayi sega tablet a gabanshi bata daukeba ta manta, ya shak'a sosai da ita har meeting yakeda ta hanashi ya halarta yanzu.....da fad'a suka rabu yau kam. ************* Yauma Nancy dukda daren suna ne amma bata koma gidan ba se bayan isha, bayan an sanar mata yaa maheer yace taje gidan islam su dafa abinci ze gayyato mak'insa by 12:noon sabida suma suga yanda suke nasu shagalin biki, yaji haushi dabata jeba duk bayan mintuna seya yiwa Sophie waya tace batazoba har dare, dama ta k'are da school seta wuce abinta gida, interval nata da exams kusan 2 weeks ne amma haka ta mak'ale a library da waya a rufe..........se wuraren sha d'ayan dare suka dawo dukkansu lokacin tana parlor zaune maid d'insu ta kawo mata snacks da drink tana sha....se yamutsa fuska takeyi kamar an mata dole, yau a cike take fam da Maheer tamkar zata fashe haka takeji, kai tsaye wurinta yanufo, tana sanye da gajeren boxer irin na maza, da guntuwar farar vest ta baje sumar kanta har tana sakkowa tana rufe mata fuska lokaci zuwa lokaci takan kai yatsunta ta sak'aje wacce ta zubo a bayan kunnenta, Tsaye yayi a kanta ya murtuk'e fuskar nan itama kuwa ko kallonshi batayi ba ta had'e wannan fuskar tata abinda kake fin shekara baka ganiba a fuskar ta fushi ba.......ko Gayar dashi batayi ba shima bece mata komai ba, sophie sarakan iyayi ne tazo wurinta "Ke Hafsat kwana biyun nan lafiyan ki kuwa, ki kama waya kin gark'ame ba inda banje nemanki ba a school dana kammala exams, kuma kinsan dai koma menene baki kyauta ba ko yaa Maheer zeyi bak'i gobe suna kink'i kizo mu masa girkin dayace alhali ya sanar mana dukkanmu" D'agowa tai ta kalli sophie, ita kanta ta tsorata da yanayin Hafsat idan nan tamkar ba nata ba, hadda bak'in ciki ya soma komawa brown akan jan dayayi, alamu ma sun nuna kuka tayi da sauri sophie ta sunkuya "Dama bakida lapiya bamu sani ba? Mesa baki fad'a ba" ga jikinta da zafi sabida wahalan data baiwa kanta ga rashin cin abinci amma haka ta daddage "Ni lafiyana k'alau yawan duba takadda ne kurun ya sanya idona yai haka" kallon tuhuma sophie ta bita dashi "To amma duk duba takaddan ne ya sanya jikinki ya soma zafi, gudun magani ko? Umma zan kirawo a waya yanzu kuwa" rik'e hanunta tayi tana yunk'urin mik'ewa "Karmuyi haka dake, wlhy lafiyana k'alau yanzu se umma tamun fushi kinsan halinta, kaina ke ciwo kuma ki tambayi catrina nasha magani ciwon kai" jinjina kanta tayi alamar gamsuwa "Yakamata kije ki kwanta ki huta, yafi wannan zaman anan kinji swt hrt" gyad'a mata kanta tayi da murmushin yak'e a fuskarta wanda akace yafi kuka ciwo a tare suka bar wurin, shi kuwa yana nan tsaye tamkar wani statue, kai tsaye d'akinsu na usul ta wuce tai kwanciyarta, kallon ta sha'awa tayi "Ke Hafsat ina yaa Maheer yana gidan me zakizo nan ki kwanta kuma, kefa Hafsat wlhy zan gayaki da anty Fareeda, ji yanda ya damu dake d'azu yakira yakai so goma komafi wlhy akan kinzo gida amma shine yanzu zaki k'yaleshi" Lumshi idan ta tae kanta yana ci gaba da sara mata, amma kanzil bata ceba, Catrine ce tashigo akan wai yaa Maheer yace Hafsat taje d'akinsa yanzu, bata kulataba kuma tafi 25 mns bata tashiba, harya cire rai da zuwanta ta mik'e tana ganin jiri taje d'akin nasa....... Mik'ewa tsaye yai cikeda masifa "Hafsat ni kika raina ko? Ni zaki rainawa wayau? Tun yaushe na aika akiramun ke? Tukunna ma ubanme ya hanaki zuwa kiyi aikin dana sakaku?" Wannan fad'an dayake hadda zugar islam akan wai tana bak'in cikine an fasa sanya sunanta yasanya tak'i zuwa har tana cewa wai tunda takira ta zageta karta shigo mata gida kuji sharri!!!! Da k'yar ta iya d'aga idanta ta kalleshi "Kayi Hakuri" shine abinda ta furta kanta zauna ragwaf akan gadon kasa zaman tayi taje luu ta kwanta kanta yana meci gaba da tsananin sarawa tamkar ze tsage gida biyu, ita da kanta tasan hadda yunwa bawai ciwo ba amma yanda takeji bazata iya cin komai ba.....binta yai da kallo yana nazarinta, jikinsa ne yai sanyi yabita zuwa gadon ya tallafo kanta sosai ya tsorata da zafin dayaji ajikinta, yakula dazaran ranta yana a b'ace se zazzab'in nan ya tashi mata seya kaita asibiti tukunna zeji meke sanya ta yin hakan, kar azo memory ya k'ara guduwa ya shiga uku "Hafsat bakida lafiya sosai ne haka wai?" Cikin rashin sanin me tace da k'unan rai tace "Da inada miji aida yasan banida lafiya, dayike ni gauruwa ce aidole inyi hak'uri na zama wacce ta rako mata duniya, ko albarkan kiran waya bana samu, kaje kaji da kanka gun Mowar gidan mana tunda yake albarka sanin zaka kwana a guntama ban samu ba sedai na nemeka na raba dare ina jiranka baka zoba, kai kuma wuni d'aya kacal daka nemeni dannaje nawa mowar gidan baka samu ba har ka rufe idanka kanacin mutun cina, babu ruwanka dani ko yanzu kana iya tashi ka koma gunta ai" Ya k'ara tabbatar wa kanshi fushin dai na kishine kuma yasan be

Chapter 18 of 20