dukda yasan akwai kishi amma be dace tayi tunanin kishi akan Nancy ba sabida shi ba komai aranshi akanta se alkhairi kuma kwanaki da yawa tayi tana aikin lada, sadaukarwar data qara mata k'ima da daraja agunsa kwana biyu kuma se wani banzan kishi ya sanya ta b'arar da ladar ta na jinya....Babu wata walwala a tattare da islam amma ganin Nancy na kallonta ya sanya lokaci d'aya ta sake fuskarta tana fara'a taje ta rik'e hannunta sannu Nancy yaya jikin naki?
Murmushi Nancy tayi
"Lapia na qalau naji sauqi sedai inata ganin jiri, me kikeyi anan tare da Maheer" kallon Maheer ta juya tayi sannan tace
"Waya ce dake Maheer ne ya sanya aka saceki ne wai, kinga yayanki beji dad'in maganar ki ba, bakida lapiya kusan watanni uku kina kwance har loosing memory d'inki kikayi shisa kike ganin komai a haka ki kwantar da hankalinki zakiji bayanin komai idan kika k'ara samun sauqi, amma kan nan ki dinga yiwa Maheer adu'a shine sanadin samuwar sauqin ki da taimakon Allah" Batai magana ba, se shine ya kalli Islam
"Baby ungo key jeki mota nabar wayana d'akko mun" karb'a tayi da hannu biyu ta juya ya zauna a kujerar dake fuskantar inda take kwance
"Hafsat yaya jikin naki?" A maimakon tayi magana seta d'auke masa kanta gefe d'aya, be qara cewa da ita komai ba ya zauna kurin yana nazarin ta har Islam ta shigo da sallama a bakin ta, miqewa yae ya karb'i wayanshi sannan yace
"Baby barinje gun Dr. Zamuyi wata magana ne, da wuta na biyo tanan din idan na gama dashi idan kika gama zaman asibitin sekimun waya na turo miki driver yazo ya d'aukeki" kwanciya tayi asaman faffad'an qirjinsa
"Mesa yau kawai zakace bazaka dawo duba qanwar kaba" murmushi yayi
"Daddy yazone dole na ganshi yau bansan se yaushe zamu zauna ba, idan yana gari koke dakike matana bakida guarantee xaki ganni bare kuma k'awarki" Bataji dad'in maganar daya fad'a ba kanshi tsaye agaban Nancy amma setayi yak'e
"Idan dai zan kwana a saman qirjin kan nan toba damuwa, Allah ya tsare" Be qara kallon Hafsat ba ya fice abinsa.....
Ko kalma qwaya d'aya tak bata rage ba daga cikin abinda ya faru ta sanarwa Nancy, kuskuren ta d'aya shine Maheer be sakata aikata aikata hakan ba na biyu kuma bashida niyyan sanar mata cewan Antyn sa Nasara ce ta sanya amata wannan aikin, acikin labarin ta sanar mata zancen aurensu da maheer da dakatawar karatun ta itama....Nancy tayi kuka tamkar ba gobe, ta godewa Allah daya kub'utar da ita amma taji storon jin wai 'yan uwan Maheer suka kuskureta da islam suka mata abinda aka mata tunawa da abinda ta gani a jejin ne ya sanyata soma karanto adu'a tare da rufe idanta.
*Dan Allah kuyi hakuri, ina fama da students ne masu koyon girki shisa kwana biyu kuka jini shiru, kuma banida lapiya mura ce ta sakoni a gaba*
Mom Nu'aiym
[2/16, 11:35 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
[3/3, 5:54 PM] Billy Galadanchi🤪🤪: *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
25
A hankali ya gangara ya yae parking d'in motanshi, harga Allah baya cikin nutsuwar sa gameda Hafsat, yarasa dalilinsa najin haushin ta akan abinda ta masa abin ban mamaki kuma shine ya rasa meya sanyashi damuwa akan hakan? Ko gun Dr. D'in dayace zeje be biba, ranshine kurin yaji yana matuqar b'aci akan yanda be kula da Nancy ba yau...... Da k'yar ya iya saisaita kansa ya nufi guess house d'in daddyn sa cikin qunan rai,yayi matuqar mamakin jin cewar Mahaifiyar sa ta sanar masa dukkanin abinda Nasara ta aikatawa baiwar Allah yayi fushi me tsanani da har Maheer d'in dayazo d'aurin aure be gaya masa ba daya sani da tuni yarinyar tana waje ana kulawa da ita na mussaman....
"Yanzu sanar dani wane ci gaba aka samu ajikin yarinyar?" Kanshi aqasa yace anyi nasaran gyaran k'afar harma ta miqe kuma memory d'inta ya dawo normal idan ta k'arajin sauk'i ma aka sallameta zan miyar da ita sokoto" Jinjina kanshi yae ya miyar da dubanshi kan jaridar Daily trust dake hannun shi kamar bazeyi magana ba se kuma yace
"Akace baku sanar da iyayenta daga nan gidan aka aikata wa 'yarsu hakan ba,ko miye dalili?"
"Ea dama Abba rashin dacewar hakan kurin nagani, bazanso wannan maganar ta fita ba, tunda Allah ya kub'utar da yarinyar, kuma iyayenta ma ba wasu bane basu ma damu ba,ko mahaifinta tunda tazo nan garin basu zo dubata ba, kuma acikin watanni biyun datayi bekira waya so biyar ba yaji ya take ba, hasalima babu wanda yanemi ba'asin sanin inda aka ganta acikin su" kallonshi ya miyar akan Maheer yace
"Yace Mahee kai wanine kenan kake gani ko?" Da sauri ya kalli mahaifin nashi ya sani wannan kad'ai ya isa sanyashi ya dinga rigima,muryan shi na rawa yace
"Ba haka bane Abba rainane ya b'aci dasu mutane idan basu suka haifi yara ba sekaga ko mutuwa yaran zasuyi ko oho" Gyaran zaman shi yayi
"Su waye iyayen nata to?" Kallon Abban shi yayi
"A yanda naji dai wai mahaifinta ne ya rasu yabar dukiya me yawa, to ita kad'aice dashi shine se qanin mahaifinta ya auri maman nata ya kuma karb'i dukiyan azuwan ze riqewa yarinya shine fa zaman yaqi dad'i harya saki maman ta ta koma k'asarsu Niger to yarinyar se wahala takesha, yanzu gashi karatun nata ma data gama cin wuyar shi ya lalace sanadiyan haka nazata sunje sun mata defring ashe basuje ba....school d'inda take zuwa wani zubin da k'afa tun daga low cost har D'an fodio" wara ido yae ya jinjina nisan wurin kan yace
"Sanda naje sokoto nace zanje naga jami'ar d'an fodio nayi mamakin nisan ta, batada banbanci da jeji ai akwai nisa sosai, harna qosa naga isarmu bazakacemun mutum ze iya zuwa gun da k'afa ba tun daga gwiwa lowcost sabida nasan Gwiwa lowcost ai na sanar maka inada gida acen cen nake sauka idan naje sokoto, da nisa sosai fa"
"Allah abba ni shaidane takanje gida da qafa ko tazo da qafa ma, ai wasu mutanen basuda imani" kishingid'a yae kan kujerar dayake kai
"Kaima meya hana kaje kamata, ina kace d'alibar kace k'awar iyalanka kuma"
"Allah ko abba nazata iyayenta sunje" D'an guntun tsaki yaja
"Wanda be baka tranport kaje skul ba kaga alamun ze damune dan bakaje ba, kaida kace basa ma zuwa dubata kuma kace ko a waya basa kira, yaya zakayi wannan tunanin, yanzu abunyi mu had'e ta dasu sha'awa sedai iyayenta suna haqqin sanin me muke shirin yi, sabida haka ka shirya zamuje gobe sokoto" Be isa yayi musu ba dukda ba hakan yaso ba, had'e ta dasu sha'awa na nufin komawar ta london kenan gaba d'aya da zama da karatu toshi yaya ze rayu babu ita a rayuwarsa?....seda abban yace
"Ka tashi ka tafi mana",tukunna ya miqe,yana godiya yabar parlor d'in.
***************
*Bayan kwana biyu*
Har akayi discharging na hafsat maheer be k'ara komawa asibitin ba, abun duk ya dameta Islam da kanta tayi mamakin hakan duk sanda tace asibiti driver ke kaita tayi tambayar harta gaji amma be kulata ba, yau da akayi sallamar Reedah tana wurin kasancewar me gidanta ya sanar mata za'ayi sallamar, da suka gayawa maheer ma se cewa yayi akaita gidan umman shi, sunsha mamakin bece gidan islam ba, amma haka suka d'unguma har islam d'in.
Hannu bibbiyu umma ta tarbesu aka kai hafsat b'angaren da aka ware mata kusa dana su Shauty da sophie har ta k'ara jin sauk'i su kuma sukayi k'awanya a parlor suna zuba zance Umma se washewa islam baki tabke tana sakota a hira ita kuwa kunyarta sosai takeji ta kasa sakin jikinta, su sophie se yatsina suke an kai musu ita kusa dasu sufa basuga dalilin nanuk'e musu datayi ba yarinya se san abun duniya sun tsaneta wlhy.....
Maheer se bayan isha ya shigo gidan, bayan sun gaisa dasu Reedah ya buk'aci sanin inda take aka gaya masa tana can sama...kai tsaye saman ya haura ya k'wank'wasa d'akin a hankali, cen k'asan muryanta tace
"Bismillah, wanda seda ta fad'a so uku tukunna ya jiyota, ya turo k'ofar a hankali ya shiga, kallon sa tayi dan batayi tsammanin ganin saba ta sare akan ya tafi abunshi kenan
" Sannu da zuwa yaa maheer" shine abunda ta fad'a kanta a k'asa...Fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
"Yauwa ya jikin ki?"
"Da sauk'i Alhamdulillah" zama yayi akan gadon cen nesa da ita
"Ga sabuwar waya na siya miki dan taki ko labari, nayi k'ok'arin miki welcome back na layukanki duka biyu sedai d'ayan na Airtel dole sekinje da kanki wannan na mtn gashi nan banma gwadaba amma bari na gwada akan wayan yanzu" murmushi tayi
"Allah ya k'ara girma na gode sosai" Be kulata ba har messages suka fara dira akan wayar daga kunnawa kai idanshi yae akan wata number data turo message yafi so 20 se shigowa sukeyi ba adadi ya tsaya cak!! Akan lambar ya soma bud'awa
("Nayi kewar rashin ki nayi kukan nisan dakika mun nayi dana sanin rashin zame miki dan sandan ciki domin baiwa lapiyarki kariya, nayi sake dakika zamto acikin halin rashin tuna komai gaki kwance k'afa a karye Allah ya baki lapiya...Naki me k'aunarki Mahal")
Wannan shine saqo na farko dayayi tozali dashi a wayar
("Babu a duniya me iya sanya na nisanceki ki warke ki dawo gareni muyi auren mu na soyayya...Naki Mahal")
("Ina kukan rashin ki, ina keawarki abar sona, Allah ya tashi kafad'unki") haka messagea suka dinga shigowa sama da kasa na Mahal ya zauna harya manta da wanzuwarta agun seda ya gama karanta su tsaf!! NA K'ARSHEN ne yafi tsorata shi
("Labarin samuwar lafiyar ki ya riske ni daga gun Mahal!! Naji ance kin warke ina nan zuwa gareki soon tawan, bazan rayuba idan baki abar sona, ina fatan kiga saqon nina") wato dama Mahal shiya miyar wani sha ka tafi? Lallai ma wannan yaron yazo da salon raini, mik'ewa yayi yana kallonta, ta tabbatar ba haka idanshi yake sanda ya shigo ba to meye damuwar?
"Bana son wannan sim card d'in bazakiyi amfani dashi ba, zan siyo wani da safe, ki rik'e wayar a gunki" kai tsaye yacire layin a wayan ya ajiye mata wayar, cikin rauni tace
"Amma yaa Maheer naga layin ya hau lapiya, kuma komai nawa na school da bank da komai dashi nake using" wata muguwar harara ya wurga mata, cikin d'aga murya yace
"To nace bazaki yi amfani dashi ba ko kinada ja ne!" Nan da nan idanta ya kawo ruwa
"Kayi hakuri ba haka nake nufi ba, abari da safe akawo sabon" seyaji kuma duk beji dad'in hakan ba daya mata amma bece komai ba ya fice daga d'akin...
************
Bayan ya tafi kuma dukse ya kasa nutsuwar sa, ya gigice ya d'imauce ya rasa meke masa dad'i yafa kasa gane inda zuciyar sa ta dosa gameda Hafsat, abu k'alilan ya fusata sa akanta, abu kad'an indai ya shafeta yake susutar dashi wani zubin, yau kam be tab'ajin kwatan kwacin azabar radad'i da zafin zuciyaba kamar irin wanda yaji yau ganin saqon nin nan, yana mamakin wanann dama Mahal son ta yakeyi yake masa wayau? Lallai ma yaron nan....
Islam ma bata ganewa komai ba yau din dasuka je, sabida yasha mur baya ko magana,beko kwana a d'aki d'aya da ita ba.
Mom Nu'aiym ce
Inshaa Allah na dawo kenan daily update💃💃💃💃💃
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
28
Washe gari tayi mamakin ganin an tasheta tun asuban fari kuma ance tayi wanka, 6:30am suka fita susu biyu, mamakinta yanda Maheer da kanshi ke tuk'i agarin kuma babu inda ya b'ata yasan kan garin kamar cikin gidansu.... Wata Makaranta taga sun shiga me d'an karen kyau da tsari, kai tsaye wurin shugaban makarantar sukaje yamai bayanin komai da harshen turanci inda yace sesun mata interview...Ba jinawa aka kammala komai kuma kai tsaye ta lula level 1 a b'angare low a makarantar me sunan Brilliant university makarantar su d'aya dasu Sophie kenan su suna level 3 inda sophie ke bibiyar medicine ita kuma sha'awa ke karantar b'angaren zane zane........
***************
A waya yake sanarwa Abba k'udirinshi nason dawowa Uk din shima, seda yayi wani dogon nazari kanya amince masa da hakan, yana jiyewa yaron fadawa business irin nashi na rashin lokacin iyali kwata kwata amma yana masa fatan alkhairi.
Kwance yake akan kujerar dake parlor d'in yana kallon tv duka tunanin shi da hankalinshi yana gun islam, d'azu dasukayi waya yaji muryan ta cen k'asa alamun tanajin jiki b'oye masa kurun takeyi, baya ga hakan ma yanaso ya kasance tare da matarsa sabida yana missing nata.....Lumshe idanshi yayi ya k'ara budesu a hankali acen k'asan zuciyarsa kuwa yana wani tunanin ne na daban sam ya gagara dena tunanin daya zamto masa tamkar numfashin sa, idan Abin da yakeji gameda islam so ne to lallai ko yana sonta so bana wasa, amma inhar ya kasance abinda yakeji gameda Hafsat shine So to kuwa da banbanci tsakanin so dakuma k'auna sabida ita har cikin jijiyoyin jikinsa yakejinta, tana masa zagaye acikin jini da b'argon sa, takasance itace numfashinaa dayake shaqa yana mata *Son so* wanda babu irin shi, yana mata k'auna wacce mizani yayi kad'an ya aunata sabida duk girmansa ta masa nauyi, yana jin dad'in sauti da amon muryarta tamkar itace ta farko ta kuma k'arshe acikin halittun a irin jinsinta a duniya, tafiyarta tana burgeshi takan d'auke hankalinsa xuwa wata duniyar daban yakanji tamkar bow legs d'inta sunfi na kowa masu irin nata kyau, seyaga kamar kyau ma suka k'arawa tafiyar ta, idan yana kallon d'an siririn hancin ta seyake ji tamkar ya dinga jansa a hankali yana wasa dashi, idanta masu ruwan zaiba aciki yake k'ara narkar masa da duk wani kuzari ya rasa katab'us idan beyi tunanin taba, k'wayar b'akin idanta ke d'auke hankalinsa yayinda ya kalleshi ya hango kanshi aciki, seyaji inama zata bashi aronsu su zame masa madubi dan harga Allah yafi ganin kyawun kanshi acikin d'igon bak'in idan nata, Duk sanda kumatunta ya lob'a kuwa idan tana cin abinci ko dariya kota yamutsa fuska, jiyake yi tamkar yaje ya sanya dan manuninsa acikin ramin yana mata wasa dashi, sumar kanta ke k'ara hura wutar abubuwan dake damunsa akanta, yakanji inama ace ze samu damar shinshinar sumar kan nata, ya shak'i k'amshin kan nata yanayin kwanciyar sumar nata yana nuni sosai da tsantsar tsafta kota yanda yake zuba sheqi......yarasa makama ya rasa madafa, ya ayyanewa ranshi komai nata burgeshi yakeyi daidai da yatsun hannayenta dake zara zara da nails masu kyau farare masu d'igon ruwan zuma a k'asan su, lumshe idanshi ya k'arayi a karo na barkatai, wannan yarinyar tana shirin wargaza masa lissafi,tanaso ta rikita tunaninsa ta tarwatsa masa kansa......da wannan ya miqe domin barin gidan kwata kwata, sabida harga Allah yana so ya yakice ta a ranshi, tasan sirrin islam!! Tasan wacece islam koda yayi nasarar auren ta baze tab'a nasarar zaman lapiyar su, ita islam bazata ji dad'in rayuwarta kishiyarta tasan seda ta gama yawon duniya aka aureta kuma sanin na sosai ba rumours ba, ita kuwa Hafsat zata dinga goranta mata hakan koda wane lokaci kuma yasani a wurin yara ma se ansamu haka ga Islam na shrin soma zazzaga masa yara agida......
******************
Matashiyar dake tare da ummul ce tace da ita cikin fusata
"Baiwar Allah kinfa isheni da tambayoyi marasa kan gado!! Bake bace mace ta farko data fara zama anan gidan tare dani, kece ta biyar idan ma zaki kwantar da hankalinki ki kwantar dan bakida hanyar fita daga nan gidan, nida kaina na gudu yakai so bakwai amma da k'afana nake dawowa sabida wannan gidan dakika gani duk kyawun shi a jeji ne muke rayuwa, wanda bashida farko bashi k'arshe dubin duniya idan zakiyi bazaki gane komai ba ta inda ze sadaki da wani gari ko k'auye..... Idan kika kwantar da hankalinki kina haihuwa zasu maidaki inda kika fito, dama kwad'ayi ne ya kawoki kuma nasan kinci naki rabon da duk wacce bataci ba bata zuwa nan, sabida haka dan Allah da manzansa ki rufawa kanki asiri ki nutsu ki haife musu yaron cikinki ki huta da rigima" kallon rashin fahimta ta mata, ta rud'e sosai dajin wai yaron cikin ta zata haife musu!! Suwa?... Ta tambayi kanta, bak'in ciki tamkar ze kasheta da rud'u ta kuma durk'usa mata
"Ki taimakeni Naja'atu ki fayyacemun buri har wutsiya wlhy tallahi bansan komai ba game da zuwa nan gidan, hasalima wlhy tallahi ni matar Ameen ce, ba abinda naci nasa......
" Da haka yake yaudarar ku, nidai kuna bani mamaki wlhy, iyayen dayake kai muku kawai na bugi ne, dukkanin wani abu daze muku bana alkhairi bane ba, kukuma mata da iyayenku dazaran kunga me kud'i to ba wani dogon me bincike se aure, yanzu wa gari ya waya? Ki sabi tunda kikazo ta hanyar aure bakida odar barin nan gidan d'in sedai kiyita adu'a....yara kuma dazaran kin haife bakya ganin su kam ko labari sedai kamma kiyi arba'in suke k'ara danna miki wani cikin a huta gaba d'aya" ta karashe maganar tana d'age kafad'unta duka biyu....damuwa sosai ta nuna a fuskar ummul ta soma k'ok'arin kawo ruwan idanta k'asa...."Naja'atu mu kashe Ameen idan yazo semu gudu mana mu taimaki juna, na iya mota semubi duk sawun da tayoyin motar sa suka bi suka shigo" Dariya najan tayi
"Bari kiji Ummul kowama kike da suna, wlhy keda ganin Ameen seyazo sake yi miki ciki, abuncin gidan nan ma bansan da yanda yake shigowa ba nida na shekara biyar acikin gidan, sedai nikanga me gadine yake kawo abincin shima da bundigarsa yake yawo sannan duk wata idan za'a kawo kayan abunci me gadin dake kawowa daban, shi kamma bansan wayake bashi abinci ba,kina dai gani daidai da sylinder wannan guda bakwai ne agidan cike da gas, idan na fitar da wanda ta kare bansan yaushe ake daukewa sedai naga an miyar,gulma har bacci nake hana idona ina zuwa leqe amma bani ganin komai, gen din da ake kunna mana da solar bansan yaushe ake saka masa mai ba, hasalima bana ganinsa banjin kukan sa, ba'a tab'a hanani yiwa wata mace bayanin kan gidan ba, nidai kurun abinda na sani zaman iyayena nake a gidan nan" Shiru Ummul ta kasa magana tabbas ta d'akko ruwan dafa kanta, ta kashe kanta da kanta, ta tsoma kanta a uku da kanta....
************
Islam na kwance a d'akin Umma tun bayan da yayi tafiya agidan take kwana wurin Umma babu tsangwama ba kyara, sema wani tattali na musamman datake samu awurin ta koda wane lokaci.....yau Umma taje meeting bata gidan wannan ne ya baiwa Hajiya Nasara daman shigowa gidan tana wani yauk'i da uban k'aton kai da cikin dasuka mata yawa babu d'uwawu gatanan sekaje wani mayunwacin zaki......taunat cingam takeyi tana yatsina fuska sanda ta shigo d'akin...kallon wulak'anci da raini tawa Islam dake k'ok'arin gaisheta sannan tace
"Ke ina Umma?" Sadda kanta tayi k'asa
"Tajee meeting ne" ta bata amsa a tak'aice
"Kwanciyar me kike mana akan gado magajiya?" Kalmar ta daki k'irjin ta ba kad'an ba wannan ya sanya ta d'ago jajayen idanta daya riked'e mata zuwa ja ta kalli Nasara ido cikin ido amma batace komai ba....
"Dena kallona karuwa!!!" Ta furta mata cikin d'aga murya wanda yayi daidai da shigowa umma d'akin bata san da zuwan umman ba taci gaba
"Naji ance kinada ciki wato baki d'auki magana taba ko? Kina gani kamar wasane bazan iya kashe kiba akan wannan cikin? Kina tunanin bazan iya kassaraki ba bazan iya lahantaki ba kenan ko?" "Innalillahi wa inna ilahiraji'un" Itace kalmar da Umma ta furta a sarari
"Nasara dama haka kika juya? Dama zaman cikin daula haka kika dawo Nasara? Ganin kinada dukiya kike ganin tamkar ki sab'awa mahaliccinki ba komai bane ba? Lallai kin shayar dani zumar mad'aci, kin kunyatar dani kin tarwatsa tarbiyar damuka baki, yaushe kika koma haka Nasara? Matar d'an uwan naki tome ta miki? Meta kashe miki a rayuwa? Kuma koba itaba wannan kalaman basuyi tsauri ba kuwa? Anya Nasara? Anya bakya gudun sauyin rayuwa?" Shiru batayi nagana ba uwar taci gaba
"Fice mun agida, karki kuma dawowa sekinyi hankali, ko a waya karki k'ara kirana sekin yi hankali tukunna kinaji ba" Shiru tad'anyi nad'an k'ank'anin lokaci kanta ce
."ki Gafarceni Umma inshaa Allahu zan kiyaye" hararanta umman tayi
"Ki ficemun agida nace ko kuwa?" Sumsum ta fita ta k'udurta aranta seta ciwa islam zarafi acikin ruwan sanyi ........
*****************
Yau dai gaba d'aya Nancy ta tashine cikeda kasala kasancewar tayi mugwayen mafarkai game da ummul, a daddafe tayi shirin school taje ta gayawa su sophie zata wuce abinta tana sauri, Batabi school Bus nasu ba Maheer ne yace ze direta, ya kula sosai da rashin kuzarinta da walwala....kallon ta yayi yana murmushi
"Longon beb how far? Menene damuwarki kinyi wani shiru yau ko dimple din ma banga yana magana ba" tamkar yasani kuwa magana takeso tamasa amma ta rasa ina zata soma
"Yaa Mahii dan Allah number ummul zaka nemomun awurin Baba iro inaso nayi magana da ita" kallonta yayi adaidai sanda yake lankwasa sitiyarin motarsa don shiga kwana yace
"Kanki dawo skul inshaa Allah, zan masa waya sena bani in baki"
"Ni A a yanzu nakeso" na furta maganat tamkar zatayi kuka cikin shagwab'a, harga Allah Nancy ko a Nik'afi duk tadowar ta cikin rashin gata tanada shagwab'a, abune dai kawai wanda bakasan kanayi ba, gata da saurin kuka abu kadan kuka abu kadan kuka.....har wani zubin takan bashi takaicin kukan nan shi bayason kuka ya tsaneshi sosai.....kallon ta yayi fuskar nan tamau
"Bakida Number d'in Baba iro ke? Idan yanzu yanzu kikeso ki kirashi da kanki danni bazan nemo yanzu yanzu ba tunda ba fad'ar Allah bane ba" shiru tayi nad'an lokaci kan tacr
"Kayi hakuri" bece komai ba har suka isa, babu me magana yana direta ta sauka batako kalleshi ba..
************
Tunda taji bayanin haukan Baba iro taji hankalinta be kwanta da zancen ba, abinda ta tuna ta tab'a gani a motar sane ya fad'o mata aranta, cikin takaici tace da Baba iro
"Baba yanzu kunada yak'inin ummul tana k'asar waje? Niba gani k'asar wajen ba amma ana samun nunber na, gaskia da sake wai an baiwa me kaza k'afa ku bincika gidansu yarin mana" k'irjin Baba ne ya doka se'a sannan ya tuna da betab'a tambayar Ameen gidan suba, amma yaga k'anin Baban sa sananne ne shisa be damuba, duk da ya shiga damuwa
"To zan bincika gidan nasu Ameenu karki damu, yanda akayi na sanar miki" sallama sukayi ya dire kiran gwawar sa ba k'wari.
*Bayan watanni Biyu*
Tuni Maheer ya dawo Niger yayinda suke zaman ba laifi itada su fiyya, har mamakin yanayin kudad'en da ake basu takeyi, itama ta acc ake saka mata every month.....Basa shiri da shauty amma da sophie suke mugun shiri itane taketa wayar da ita amma shauty kulljm cikin zaginta wai kwadayine da ita.
Yau cikin ummul watanshi Bakwai, amma segashi tana ciwon mara da baya mara misaltuwa, tun tana iya daurewa harta kasa...Naja ce taketa kulawa da ita ashe Nak'udacr haka ta haifi yarinya susu kad'ai ke dumui niyar su, babu sanin kowa tunda ba kowa agidan, haka yarinya tazo Bakwaini, me tsananin kamanni da mahaifinta tayi kyau seda gatanan er mitsila tamkar lomar kishiya, haka Naja tayita tattalinta dama ita ke karbar haihuwa idan aka haihu amma bata taba karbar Bakwaini ba!!! Ko yaya zata rayu? Ko yaya Ameen zeji idan yaji tasha nono, a ka'idar yaran dasuke d'auka sam ba'a bari susha nonon uwarsu tasan kuma shida gidan se nan da watanni biyu idan yasan EDD na Islam
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 20