Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
har ciwon rashinsa tae tsaitsaye, ji take tamkar ta janyo wata dayan daya rage ya zama gobe kowa ya huta!!! ************* Maheer wannan satin beje sokoto ba kasancewar islam ta sanar masa zasuje jega da mamanta biki, yana matuqar kewarta wannan ya sanya yace bari yaje gidan Ishmal danya ragewa kanshi zaman kad'aici da kewar Islam duk yaje sokoto tare suke wuni yau kam ta sauya zani tunda gashi bata kusa dashi har wani zazzabin rashinta yakeyi *********** A parlor Eshmal se hira sukeyi suna shewa, yace yana kallonshi "Gauro ko kaima ka nemo cook ne motsi nakeji da tashin qamshi agidan" murmushi yae yace "Wane cook wata ce er hannu na samu tazomun daga sokoto, girki takemun ba tun wednesday tazomun yarinyar tayine a rayuwa ai" girgiza kanshi yae "Kai har gobe bazaka dena neme nemen matan banza ba wai, nagode Allah daya yini badon mata ba Ina dalili wasu zunubai" tsaki yaja "Kaina zanci an hanani aure a gida, duk wacce nakawo sesun kushe na dena zancen auren Rayuwar bariki ta ishen" tsaki yaja "Ka dena duba gidanku kaji tsoron Allah" kan wani yae magana islam ta shigo d'auke da plates biyu ta zubo taliyar data dafa da kifi se tashin qamshi takeyi, tana sanye da riga iya gwiwa mazaunanta se magana suke, kai tsaye dining ta wuce ta dire su sannan ta kalli inda Eshmal yake !!!!!!!!! Mummunan dokawa qirjinta yae ganin Maheer ta kusa zamewa ta fad'i ta dafa kujerar dining d'in, idanta ta murza taga lallai shine shi d'inma ita yake kallo miqewa yae yace da friend dinshi .. "Bari naje Eshmal akwai inda zani" lokaci daya ya zaro wayarshi yana dannan Number ta, wayarta dake kusa da inda ya tashi ta shiga ruri ya juya ya kalli wayar "my Heart" yaga an rubuta, kan yae wani yunquri Eshmal yace da ita "Kizo ga garan daxe aure mana ke nan, dan baqin ciki yana miki waya" da sauri yae waje har anan hada kafa.....koda Eshmal yazo masa rakiya har yayi reverse yana shirin barin gidan hannu kawai ya daga masa ya figi mota zuciyar sa na masa tauna da tuquqi😭😭😭😭 Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 09 Shirinsa yae tsaf cikin shiga ta alfarma tamkar babu abinda ke damunsa kansa ya qurawa ido a mudubi yana kallon yanayin ramar dayae, ya rasa dalilin dayisa ya kasa jurewa idansa ganin islam!! Mesa zeje gunta? Mezata gaya masa? Me zeje shima yace mata? Ina dalilin wannan soyayyar dayike mata? Yana jin zafinta tamkar ya kashe ta amma soyayyar dayike mata ta wuce tunaninsa besan yana santa ba seda yae wa ennan kwanakin beji muryarta ba!!! Sanye yake da wani irin lallausan farin yadi me asalin kyau rigar guntuwace iya cinyarsa da wandon ta dinki big man amma me kame jiki hannun rigar dogone ya daure da clips yasha hula a kanshi qirar mu had'u a banki kalarta baqa wuluq, agogon hannunsa baqine takalmin kansa baqine kallon saman mirror d'in yae d'auki black shade d'insa ya manna a idon sa ya juya bayan ya zari key na benz d'insa baqa...... ************* *Sokoto* Cikin awanni hud'u ya isa a sokoton, kai tsaye gidansa ya nufa yaci abinci yae sallan azahar sannan ya miqawa kamala key yace "Gidan da kake miyarda islam kaje ka d'akko ta ka kawomun ita anan, bana samun wayanta dan haka ka aika amaka kiranta daga ciki" durqusawa yae ya karb'i key d'in ya juya bayan daya dire masa yan kakkun fruit's agabansa...... Yauma se kuka Islam kewa Nancy ita kuma se faman rarrashi takeyi "Dama shisa nace miki ki kame kanki daga bin mazajen nan na banza....... Baze amfaneki da komai ba se tarwatsa miki future kuma kije lahirarki skelin zunubin ki ya rinjayi na ayyukan alkhairin ki islam, tunkan aje ko ina kin had'u da musibar rashin me aurenki, batun yauba ya dace islam kisan cewa kanki kikewa mugunta yau ina Ashraf? Halinki nabin maza ya kore miki shi, ina Aminu bawa? Shima yabi ruwa yae tafiyarsa, mazaje nawane sukai ta kansu wane namijinne ze auri karuwa islam, nasha fad'a miki abinda kike international karuwan cine me lisence bazan boye miki ba hadda laifin innah dan Baba nagani ba gayamun akaiba bayaso, har cewa yake na miki magana akan halayenki na banza yanzu wa gari ya waya? Wannan ma basanshi kike ba ai kud'insa ne ya rud'eki dabadan kud'iba nasan bazaki zauna zaman kuka haka ba" wani yawu me d'aci ta had'iya sannan ta kalle ta kallon nutsuwa tace mata "Bawai banason Maheer bane wlhy ina sonsa sedai bawai akan inason sa nake kukan nan ba abu biyu ne suke sakani kuka,na farko koda zamu rabu da Maheer bata wannan hanyar naso mu rabu ba yanayin daya ganni a riqaqqiyar karuwa me zuwa kwanan gida, na biyu kuma na kwad'aitu da dukiyarsa tunda ya furta kalmar so agareni nake hangoni acikin gidansa na alfarma ina wulaqanta naira, Nancy shejarata ashirin da uku acikkn talauci se zuwan Maheer na somawar warewa, ina samun kudi har kyautar miliyan ammun a kwana d'aya amma ni zanbaiwa wani labarin kud'in karuwan ci basa tab'a albarka!! Rasa kike me kikai dasu, amma kudin Maheer ko naira dubu biyar yaban senaga albarka ta" d'an guntun tsaki taja tace "Kinga matsalarki ko Islam, babu Allah a ranki ko kad'an yanzu bakiji tsoron Allah ba dukkanin bayananki selfish interest nakine kawai kike fad'a haba mana islam dan Allah kiji tsoron Allah!! So nake inji kona istigfari akan abubuwan dakika aikata" kallon ta islam tae "Indai ze aureni zan tuba wlhy" haushi ya qara kama Nancy tace " Auu danshi xaki dena badan Allah ba? Ki tuba wa Allah kiyi komai dominsa ze cika miki burinki haba mana islam" nisawa tae "To Nancy namiki alqawarin inshaa Allah na dena, na tuba sabida Allah kuma koda Maheer be dawo gareni ba zan dena zinace zinace har abada daga waccen danai" murmushi Nancy tae "Nagode sosai Islam Allah ya baki ikon yin taibatun nasuha kinji qawata" murmushi tae ta rungume ta "But i still missd him ya zanyi nancy" kan wanu yae magana sejin muryan yaro sukai a tsakar gida " Innan salaha wai inji wani mutum yace sunansa Kamala salaha tazo suje inji Maheer" miqewa innan tae daga hura gawayin datake "Tana ciki jeka zan gaya mata" kan innan ta shigo har islam ta miqe ta soma neman mayafi koda inna tazo sunkai waje, suna ganin kamala suka fad'a mota.... ************** Sunyi zaman fiyeda 30 mns be shigo ba, islam dukta gama rudewa se zufa take duk AC dake parlor nan, se dukan uku uku qirjinta keyi tana zare ido tana jin qarar bude qofa ta miqe tsaye!! Kallon wurin take harya tura kofar ya shigo qirjin ta se dukan uku uku yake, a hankali ya tako ya qaraso daf da ita har suna jiyo bugun zuciyar juna, Kuka takeyi ta kasa tsayarda hawayenta!! Shi kuma idanshi yayi jajir tamkar gaushin wuta!! Dukta qarisa rikicewa wannan daf da ita daya matso, wannan ne karonsa na farko daya matseta har haka!! Kana kallonta zaka hango yanda jikinta ke qyarma dukta rikice kallon shigarta yae yau kad'ai yaga islam da hijabi, idonshi ya sauke akan qafafuwan ta,qafan islam kawai ta cancanci yabawa bare fuskarta da surar jikinta!! Miyarda dubansa yae zuwa gareta yace murya na rawa "Islam Why? What on earth kika nema kima rasa? That u stood so low!!! Mesa aduk sana'o in dake duniya se zina Islam!! Kinsan ko handa na tsani zina dame yinta? Kin tab'a sanin aibun zina? Zinar taki ma bawai da saurayinkiba with any man!! Meaning bakya gudin komai? Azabar Allah, daga qabari har xuwa tashin qiyama har yakaiga murqusaki cikin wutar sa islam? Ashe bakya tsoron cututtukan zamanin nan, ashe bakya tsoron mutunci da martabar iya yenki idan kinsan duk bakya tsoron wa ennan mesa arayuwa zaki shiga rayuwata? Ni dukkanin abubuwan dana lissafa ina tsoron su yaua zakimun haka?" Jin yayi shiru ya bata damar d'aga idanta ta kallesa dan tunda ya fara magana ta dire idanta a qasa!! Zubewa tae saman gwui wanta duka biyu "Maheer dan san manzan Allah ka bani second chance!! Wlhh zan sauya, zan sauya to a good and better person please karka fita arayuwa, kayi wannan jihadin ka fitar dani acikin wannan musibar ka tallafi addinin islama Maheer ka aureni, wlhy na tuba tsakanina da Allah bazan qara ba" ta qarashe maganar tana kuka sosai me sauti!!! Qura mata manyan idanuwanshi yae ya kasa koda motsi shin menene mafita? Ya amsawa Islam tayinta yayiwa addininsa hidima kokuma aa ya barta besan me iya auren karuwa ba?"...... *Mom Nu'aiym* *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* *Assalamu Alaikum, masoya kuma makaranta wannan littafin ina mai baku hakuri akan muhawarar danaketaji tana tashi duk inda na leqa akan wannan littafin, wasu lokutan idan zaka ilmantar ko wa'azantar kakan aniye wani selfish interest naka kayi komai dan Allah ka bari dan Allah, sabida haka kuyi hakuri dan Allah inshaa Allah i promise u guy's happy ending....Nagode* 10 Kujera ya samu ya zauna yace yana me mata nuni da hannu akan kujerar dake fuskantar tasa "Ki zauna anan" miqewa tayi ta zauna tana meci gaba da sharar qwallah....gyaran muryarshi yae sanan yace "Kinada kati a wayarki?" Kallonshi tae ta gyad'a masa kai alamar akwai yace "Yauwa saisaita nustuwarki kar kuma kiji tsoro!! Dukkanin wani tsohon saurayi da kike dashi ko kuma wani mutumin banza dakika san kun tab'a yin mu'a mala dashi ki kirasa a waya ki gaya masa kalmomin nan dazan fad'a miki.....a yanzu kuma" da sauri ta d'ago ta kallesa ya kawar dakanshi daga dubanta yace "Hand's free zaki saka kice da duk wanda kika kira bayan kun gaisa " Na gaji da wannan sab'awa Allah danakeyi yanzu mijin aure nake nema dan Allah ko zaka taimaka ka aureni?" Kallonshi ta qarayi a karo na barkatai kan tace "Bazan iyaba wlhy Maheer" "Idan bazaki iyaba ki tashi ki barmun gidana" Jikinta ne ya soma rawa, itada dai Nancy ta kasa gane inda ya dosa amma dai kanzil batace ba tun zuwansu "Kayi hakuri zan soma kiran" Wani Alhj Suraj ta kira wanda shine ya fara lalata mata duniyar ta kuma akan ze aureta yazo gidan su matashin me kudi daya gama da ita ya watsar,ya dauka suka gaisa a mutunce ta rattafomai yanda Maheer yace tae, dariya ya bushe da ita yace "Haba isy...tayaya zan aureki? Bayan na sanar dake tun farko bazan iyaba, islam dazan aureki aida na aureki tun farko tunda nasan nine silar b'ata rayuwarki, wlhy a gaskia bazan iya auren matar datake yawon tazubar ba, sabida haka kiyi hakuri kije ki nemi miji daidai dake" wani baqin cikine ya tinkarota tace cikin takaici "Amma suraj idan nime yawon tazubar ce ai kaine silar halakkkar da mutuncina ko, kakuma gujeni a lokacin dabanida wani gata se Allah yanzu yaya kakeso nayi da rayuwata?" Tsaki yaja "Kinga islam nifa wlhy sena wulaqantaki idan kikace zaki zomun da raini, haka kurun shekaru uku bama tare se yanzu dan cikar iskanci kice na aureki? Wama yasani ko kinada qanjamau" zafi zuciyarta keyi bazata iya saurara ba ta katse kiran da saurinta ta dafe qirjinta,tausayi ta bashi yace "Ki kira wani mana" Ba musu ta kira wank boy friend d'inta dake Arqillah Sameer yana d'aga kiran yace "Me bani kyauta!! Ta samu ne inzo muje mu hole?" Runtse idanta tae ta bud'e su kantace "Sameer Dan Allah zaka iya aurena?" Wata dariya ya bushe da ita cike da shaqiyanci kan yace " ke kina tunanin aduniya akwai wanda ze aureki ne, ai daga zaran kikaji yarinya tafito yawon ta zubar tokuwa seta zubar d'in dan bame aurenta!! islam ko d'an iska baya son er iska se'a bariki" katse kiran tae ta kalli Maheer murya na rawa furta "Kayi hakuri Maheer bazan iyaba" shima kallonta yae "Sekin kirasu, su goma sha biyar tukunna zan barki, akwai abinda nakeso ki sani dan kiwa kanki hisabi da kanki islam" batare data qara cewa komai ba tai kiran wani!!!! Shima ya yab'a mata magana haka taita kiransu suna cin zarafinta har su goma sha biyar, zuwa wannan lokacin ta gama kaiwa qolin qoli wurin b'acin rai bata tab'a kasancewa cikin namada ba se'a wannan lokacin!! Ita dake taqama da kyau da isa acewarta seta gama cin duniyarta d tsinke sannan tae aure a lokacin da takeso sanda kuma tae ra'ayi!!! Yanzu tunkan aje ko ina taga ta kanta, kasa d'aga idanta tae ta kalli Maheer ita kuwa Nanuwabta qulu sosai da wannan tozarcin daya siyawa qawarta.....miqewa yae tsaye ya kalleta "Islam dukda wannan abin daya faru acikin wa ennan susu goma shabiyar d'in bazamu karaya ba, zasu basu sati d'aya wataqil inshaa Allah wani ya sauya tunani yazo miki da zancen auren dan haka karki tashi hankalin ki kinji" Nanuwace ta miqe itama ta matso inda yake "Amma Maheer inaga idan ma bazaka hakura ba,be dace ka siya mata wannan tozarcin ba ko?" Ta qarashe maganar a hasale dason jin meze ce.... "Da bakyason a tozartar da ita aida kin koyar da ita saka niqafi yanda kikeyi, kinga ke sekinayin karuwan cinki asiri a rufe duk qwaqwar mutum be isa ya gane kiba" wani qululun baqin cikine ya tasowa Nanuwa ya tokare mata qahon zuci, wani qululun baqin ciki yaja zarya tsakanin harshenta zuwa maqogwaronta wani yawu me kauri da d'acin gaske yazo mata ta masa had'iyar bazata acikin bushashen maqoshinta....Da qyar ta tattaro kalaman ta "Niba karuwa bace balantana ka jefeni da mugwayen kalamai Maheer, bana daga cikin matan da duniyar su ke shawagi dasu acikin jirgin shed'an a wannan tafiyar, bana cikin matayen dasuke amfani da *WATA FUSKA* domin cinma wata muguwar manufa!! *WATA FUSKAR daka gani lullub'e a saman tawa bata Munafurtan mahalicci na bace!! Ban saka *WATA FUSKAR* ba seda na shirya kariyar mutuncin ta da nawa da kuma Fuskar dake a qarqashinta!! Ka sani wlhy *WATA FUSKAR* tafi gaban mari bare ka kalli tawa ka jefeta da muggayen kalamai irin wannan.... A taqamarka kaime hankaline baku ne kuke horewa matan kunne ba, kuke sabar musu da kud'i kuke rudar su da manyan motoci? Kuke miyar dasu qananun karuwai!! Yanzu banda kake d'aya daga cikin shaid'anun masu zuwar wa mata da *WATA FUSKA* menene ya sanya baka tsaya yin magana da ita a gidan ubanta ba ka kawo ta nan? Me qofar gidan ubanta yae maka?? Wlhy bazan gafarta maka ba idan har ka qara jifana da muggan kalamai irin wannan nasan darajar hijabina,nasan darajar mutuncina dana iyayena niba sakarai bace dazaka gasa mun magana nama shiru kuma zargin dakamun na zina Allah ya isa!! Lahira se an tsayar dani dakai kayi shedan hakan" dukkanin kalaman datake be kalle taba seda taja masa Allah ya isa! Da saurinsa ya d'ago ya kalleta yace "Bakida hankalina zaki jawa mutum Allah ya isa? Ni yaushe nace dake mazinaciya, ai bature yace show me ur friend and i will tell u who you are, so qawar ki danake ga bacci kad'ai ke rabaku ita nagani tana abinda na alaqantaki dani laifi ne wannan? Bance na tabbatar ba zargi nake" Wani takaicine ya qara lullub'eta tace "Agidan friend d'in naka daka ganota shiba friend d'inka bane? Idan haka ne dukkaninku mazinata ne kenan kaida abokin naka? Ya kamata ka sani cewar shiru shiru bawaifa tsoro bane gudun magana ne, idan kana takamar kai wanine nima haka nake taqamar ni watace! Idan kanajin cewa kaime arziqine nima haka nake taqamar cewar nidin nan me rufin asirin Allah ce, yanda baka neman komai a wurin kowa nima hakan take ina godiyawa Allah da ni'imonsa akaina" juyawa tae a fusace ga islam "Ke kuma mara zuciya ki tashi mu tafi idan bazaki jeba nai gaba abina,danni bazan zauna ana nunamun anfini sani ba" kallonta islam tae tana sharar qwallah "Kiyi hakuri muji tabakin sa mana Nancy" acikin niqafin ta hararota ta zare madubin idanta manyan idanuwata suka qara bayyana tace "Anan daikam banga wurin zamaba kinga tafiyana nikam" ta juya har tana had'a qafa shima ya bita da kallon mamaki lallai yarinyar nan ta wuce saninsa haka take da masifa tome yae zafi? ....... *************** Shirye shiryen auren Ameen akeyi da ummul babu qaqaquta se b'arin kud'i akeyi tamkar basusan zafin suba, Ameen ya zagewa Ummul bakin aljihunsa se wawura take tana murna batada labarin bashi takeci wanda zata fanshe shi.......Baba Azumi zaune ana lissafin kudaden da za'a kashe wurin yin datacciyar walima ta gani ta fad'a gefenta ummul ce da kuma Hafsat sedai sam hankalin hafsa baya jikinta yana cen wurin tunanin Maheer bata tab'a son wani namiji kamar yanda takeson Maheer ba kazalika bata tab'a jin tsanar mutum kwatankwacin yanda taji ta tsani maheer ba zargin dayike akanta ya mugun baqanta ranta sosai ba kad'an ba!! Mari taji an dire mata a kunce daya gigitar da ita sannan Baba Azumi tace "Er baqin ciki anata magana kinyi kamar bakijiba to wlhy ta Allah ba taki ba, kina duniyar nan Ummul zatai aure ta barki kegaki nan jiya iyau, kullum zaune a gida ko tsoho be tab'a cewa yana sanki ba bare kuma yaro" sadda kanta tae qasa batace komai ba "Akacewa kiwa ogarku waya inda kike zuwa koyon girki, abinci na mutum dari uku ranar walima da kaji asama da komai daya dace nawa zata mana?" Hakuri ta hau bayarwa ta kirata sukai magana sannan tae waje ganin wayarta na ringing kuma *Mahal* ne ya dameta akan yanasonta ita kuwa tasan na d'ibar takaicine yakeso yae da ita gashi bata shirya auren wanda bayya santa ba. *********** Maheer tunda yabar sokoto be qara neman Islam ba seda sati ya zago sannan tana kwance a d'akin innan ta, tayi wani rama tana tunanin duniya ba inda take zuwa tun faruwar abin, sega wayarsa yana kiranta a waya, jiki na bari ta daga yace da ita yana waje........ "islam wadawa suka qara kiranki dasunan zasu aureki tun daga ranar?" Kallon shi tae bataso ko gaisawa basui ba ya bijiro mata da wannan maganar gashi bataza iya masa qaryaba tace a raunane "Babu ko d'aya daya qara kirana har abokinka ma Eashmal" gyaran zamansa yae "To Islam karki zata cewar cin zarafinki ne na saka akayi,wlhy bako d'aya so kawai nake kiwa kanki hisabi da kanki tun a duniya, kuma kimun adalci, yanda wa ennan suka gujeki suda ma suka saba dake shin ni zan iya kuwa? Kije kiyi tunani idan kinga ya dace ya cancanta ki zamto matana seki gayamun" shiru batace komai ba gyaran murya yae "Nizan tafi islam ina miki fatan alkhairi" murmushi ta sakar masa "Dan Allah ina roqon wata alfarma agareka ban saniba kozan samu" kallonta yae shima "Inehmm wace irin alfarma kenan?" "Sonakeyi ka saurari labarina, tarihin rayuwata da yanda na zinci kaina a yanayin daka ganni, bzan qara takuraka ba idan har kaji labarina, nima so nakeyi kawa kanka hisabi a kaina tun a duniya bayan jin labarina kaji" jinjina kansa yae yace "Ranar talata zan dawo zanzo muje gidana ki bani labarkn dakikace zaki bani" godiya tai masa ta juya zuwa cikin gidan.... Mom Nu'aiym Please wattpadi'ans press d star buttom and vote for this page!!! If ur really enjoying it then do vote plss😍😍 *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 13 Ko kadan bataso Maheer ya ga fuskarta ba, sannan menene alakar sa da wad'an nan mutanen guda biyu? Ina zata soma kai wannan tunanin daya taso mata rayuwar kaf a kewaye take da wasu abubuwa masu firgitarwa! Meke shirin faruwa da wannan rikitaccen circle data gani yanzu? Tana jiyo surutun su amma bazata iya fad'ar me sukace ba dan bataji duka ba, me suka zoyi to tagansu bayanta zuwa cikin gidan atare!!!! ************ Tana shiga d'akin ta tarar dasu Mamanta suna cin abinci harda naman kaji an karramasu ta bangaren girki se duk taji kunya take cewa lemon baqinta ta siyo dazasuzo yanzu....tana nan khadeeja tazo kiranta akan ga angon da abokanan sa sunzo maganar kudin bikin dazasu bayar, tazo suje taso ta tirje mamanta tace lallai taje dole ta sauya kaya tare da d'ora niqafi saman firkarta kanta fice daga dakin zuwa inda en matan ke jiran ta ai zancen kudade!!! Tunda ta shigo idan Maheer ke kanta so barkatai suke had'a ido, girjin dukkansu se tsananta dukawa yake hafsat kuwa duk yayin data tunano yanayin data shiga sanda ya furta mata muggan kalamai setaji tamkar ma taje ta shaqesa a wuce wurin kowama ya huta wani haushin sa da takaicin sa suke mata dirar mikiya arayuwa yanda takejin Maheer aranta bata zata akwai ranar dazata zo a rayuwarta da har zataji tsanar sa irin hakan ba, yanda ya kalli tsabar idan ta ya aibata ta da kalmar karuwanci abin yana mata ciwo matuqa!! Beji kunyar kallon mafificiyar Fuskar dake asaman tata ba ya kalleta kanshi tsaye yake kira mata wannan mugun abun datake ganin data aikata gwara mata mutuwar quruciya!! Miyar da dubanta tae zuwa ga Mahal wannan karon bazata iya jure kallon Maheer ba, shi kuwa dayasan itace se nacewa kallon ta yake wannan ya sanya ta tsargu ta miyarda kanta a qasa a haka a haka dai sukaita surutun su da en matan dake wurin akan programs da zasuyi amma hafsat batace kanzil ba....... Ummul ta kula sam Ameenu bashida niyyan barin su sui wani fitaccen bikin dazeje tarasa dalilinsa nasab zuwa programe ko d'aya ne...amma dai acikin mutane seka gagara cewa komai illah kallon su kawai kamar yanda Nancy tae haka itama tae!! Maheer ne yace "Yanzu dai Nine zan dauki nauyin dinner da komai daya shafeta seku tsayar da matsaya d'aya akan kudad'en da ake bayarwa na al'adarku nawa kuke ganin ze isheku" kallon Mahal Ummul keyi tasani tana qaunar sa soosai kurun dai tarasa gane inda zuciyarta keta wurgi da ita! Wanj zubin idan ta tuna mahal har kuka takeyi yau kam tafi ko yaushe rikicewa ganinsa tare da Ameen, amma bata nuna ba sam ga alama shidin qani ne cox bataji bakinsa tunda aka zauna.....khadeeja ce tace "To Ku fad'i dai nawa zaku bayar semu ji idan zeyi mana karmu fad'i abinda ze baku wuya" murmushi su Ameen sukai har Mahal ma dake wurin, shi tausayi ummul ke bashi kuma yanzu, sabida yana jin qananun maganganu gameda Ameen d'in akan rashin sanin sana'ar sa gashi bashida mata yanata girma, yayi mamakin ma dasuke abota da Maheer sabida ya masa zarra har a shekaru sedai kuma Business men ne dukansu ba lallai bane ace se shekaru yazo d'aya zasuyi abota...Muryar Maheer ne ya qatse masa masa tinaninsa "Waccen me Fuskar a niqafi ta bamu acc details ku saka kudin acikin acc nata, idan tace ya wadatar shikenan na kula ita zataji tausayin mu ita kad'aine bata magana" Dariya suka sanya dukkansu banda Nancy dataji bala'in takaicin sa kamar ta shaqesa seda Ummul tace "Nanuwa ki bayar mana" *"NANUWA"* ya qara nanata sunan a ranshi ita kuwa bataso akaji bakinta ba sam, da qyar tace "Ka shirya in fad'a maka?" Tana bude bakinta yasoma tunanin yasan muryan amma seya kawarda wannan tunanin,Bayaso ya yaudari kansa.........Kallon ta yae kafin ya miyarda dubansa zuwaga Ummul "Ya kuke da wannan qawar kice?" Murmushi tae tace "Qanwa tace sedai ba sosai na girmeta ba, kanmu d'aya dai Babanmu d'aya" murmushi yae "Barin Baki Number wayana, ki turamun Text message na acc details naki, yanzu idan muka tafi zan miki transfer idan akwai damuwa seki kirani ko kuwa?" Batace komai ba dai se Godiya da en matan suka hauyi yayinda wasu duk sukaji haushin Maheer abinda yae...ya kula wata acikin su tafi kowa jin haushin hakan yace da

Chapter 5 of 20