dina har cikin ya b'are nasha wahala seda akamun wankin mara banji ba ban gani ba!!! Daga wannan lokacin kuma se jamcy ta fara tsora tani akan nazo mui karuwanci kota nunawa kowa takartar miscarriage din dan shegen dana samu ya fadi har akamun wankin mara, sabida bazata rufamun asiri haka kawai ba ita idan ta kaini gun manya zata samu kudi, nayi nayi jamcy ta rufan asiri taqi haka na yarda akan zanje so biyu tace itama ta yrda, mutumin farko dana fra had'uwa dashi shine ya bani kyautar miliyan daya, ya baiwa jamcy dubu dari uku, na biyu kamma daya tashi seya 1.5m wannan ya qara bud'e idona tunda nasan dad'in kud'i shi kenan sena manta batun yi so biyu haka na manta haramcin aikata abin,Nancy har kuka takemun akan ma tuba na dena amma Allah be sanya nayi nadama se zuwanka, babu memun fada agidanmu mahaifina be taba bincikar inda na samo kudi ba" .....jin tayi shiru na mintuna biyu ya bashi damar miqewa tsaye ya miyar da hannayensa guda biyu baya yana zagayen parlor d'in yarasa mezece laifin waye to? Iyayen ta ko suraj ko kuma ita kanta?
Mom Nu'aiym.
Zan shiga hidima kwana biyu wataqil kujini shiru sedai yanda ta yiyu.
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
15
Tare da Ameenu yauma sukaje gidan su Ummul, wayar gafsat Ameenu ya kira ta fito suka gaisa sannan yace da ita
"Nancy en mata, an dinga b'oye fuskar nan acikin niqafi, keda ummul halinku ne ko ita seda nasha daga ta dena nace fuska aiba al'aura bane,kin dinga qudundune fuska kenan a qyalle haba qanwata" Jin ankira hafsat da suna Nancy ya ankarar da Maheer akan Hafsat, tabbas ya gaskata zarginsa akanta itace qawar Islam, tun ranar daya ganta awurin karb'ar kud'in nan ya ga kamar yasan qwayar idanta,yanayin tafiyarta ma ya hadda ce ya soma zargin Nancy ce tun ranar gashi yanzu ma ya qara tabbatar da zargin sa...
"Yaa Ameen zan riqa rage sakawa inshaa Allah" murmushi yae
"Enhen kokefa lil sis, yafiye miki ai, kuma ranar dinner da kamu plus arabi'an night dazamuyi karna ganki da wannan hijabin idan ma bakida mayafai zan bada kudi aje asiya wannan alfarmar kawai kiyi kwalli kamar wayayyiyar mace nace buqata kiyi ranar shagulgulan bikin nan" Dariya tayi sosai seda gaba bakinta ya washe acikin niqafin har suna hango hasken fararen haqwarenta kanta ce
"Na siya wasu ai, inshaa Allah zanyi gayen an decently" dariya suka saka har Maheer.....
"Dama saqon d'inkunan tane na karb'o mata danaje abj tace ana mata dilke shine tace nakira layinki ki karb'a so ki bude bayan mota ki dauka" da murmushi ta amsa da "to" sannan ta juya bayan ta dauko tazo zata musu sallam Maheer ya kasa hakuri yace
"Wainikam Nancy bake bace qawar Islam?" Murmushi ta masa
"Au dama baka ganeni ba? Nice kuwa qawarku" fad'ad'a fara'ar sa yae ya kalli Ameen yace
"Dama wannan dakake ganinta ai d'alibata ce, ka barni da ita kurun akan niqafin nan, a class tafi kowa iya kawo points amma iya muryanta kawai muka sani, muryan ma kaga tamu dabance da en gida dan wlhy ban shaidata ba se yanzu danaji ka kirata da suna Nancy dan haka frnds nasu ke kiranta dukda yake tun ganin farko qwayar idon yazomun da alamar sani"
"Kai haba kace mun zatasha carry over idn bata dena zuwa muku da niqafi ba" dariya yae yace
"Auu qanwar taka kakewa fata, qawar islam d'inace fa sosai kullum suna tare" da mamaki ya kallesa
"Wannan mara jin?" ga mamakin Namcy lokaci d'aya maheer ya had'a rai
"Yanzu sabida Allah seka kalli tsabar idona kace zaka gayamun koriya akan islam? Nazata kowani kaji ze zagarmun ita zaka tare, fiancee na be dace ace kaida kanka zaka zageta ba" murmushi ya wadata fuskarsa dashi yace..
"Allah huci zuciyar Abokina wasa nake, yanzu mu tafi kenan?" Be qara bi ta Nancy ba ya zaga ya shige gaban mota suka wuce, itakam dama tace wannan Maheer din be shaidata da kyau ba, daya ganeta sam dabaze sake mata ba yanda suka rabu ba arziqi a gidan sa zuwansu tare da Islam......
*************
Durqushe agaban mahaifiyrasa yake ya qasqantar da kansa sosai yana sauraren abinda zatace bayan da yagama zayyana mata bayani gameda son auren islam kuma lokaci d'aya ya sanar masa rayuwar da islam tayi mara kyau da kuma tuban datayi sabida Allah, abubuwan dabe dace ta sani bane kurun be sanar mata ba.....d'akin nata ya d'auki tsawon mintuna goma bakajin qarar komai se bugawar zuciyoyin mutanen biyu secen ta nisa sannan tace
"Tabbas Maheer Zaka samu d'inbin lada idan kayi hakan musamman idan kayine da zuciya d'aya badan ka wulaqantar da ita ko tozarta da ita ba, kakumayine domin ceton al'ummar annabi ka rage yawan b'ara gurbi acikin al'umma, sedai fa ka sani akwai qalubale babba agaban ka, kaga da farko dai akance yara sukan tsotsi ire iren abubuwan nan awurin iyayen su mata kaga matsala ta farko shine yaranka, na biyu kuma irin wa d'an nan matan sun saba da kashe kud'ad'e kamar ba gobe kakuma sani dukiyarka ta kasuwan cice bata siya sa ba, karkayi tunanin ana cewa aduk africa mahaifinka ne na daya a dukiya kakuma yi tunanin shine na uku a duniya ka sani komai yawan dukiyarka zata iya qarewa yau ko gobe kuma kud'i ayi amfani dasu ta tsafta tacciyar hanya, sabida haka nasan dole tazama me yawan buqatar kudi wa dan nan matsalolin sune abin damuwar dazaka duba amma ni bandaja ga hukuncin Allah, 'ya'yayen mu da muka gansu a shirye shirin Allah ne ba namu bane, idan Allah ya qaddari aure ka kasance me yawaita yin adu'a shiriyar wa 'ya'yayen dazaka haifa tunda kaga ita mahaifanta bawai sunyi yawon tazubar bane qaddarace ta haye kan ersu badon sunso ba, amma sakaci da addu'a yakan janyo hakan sabida haka ka dage ka kuma kula da er mutane, dan Allah idan kasan cewar zaka kawo er mutane ne ka wulaqantar da ita karka aureta , mahafinka kuma ka rigada kasan bawai zama yakeyiba seyafi 3 month bezoba be kuma dad'e da juyawa ba sabida haka zan masa waya tare da adane abubuwan dabe dace yajiba na kuma san ze amince inshaa Allah" Dama beyi tsammanin suyi masa gaddamaba sabida kasancewar sa masu sauqin kai da fahimta da wannan yabar komai awurin mahaifiyarsa ya zabga godiya ya miqe...
***************
Bayan kwana biyu dayin maganar su ranar data fado ranar talata ana i gobe wankan amaryar matar Ameen mahaifiyarsa ta sanar masa amincewar mahaifinsa akan auren, tare da wakilta en uwansa akan zuwa neman auren tare da sanya qalilan lokaci acewarta washe garin yace aje.........
*******
Kamar daga sama kuwa Ummul taji wannan labarin bakin mahaifinta wanda Maheer ne da kansa yazo ya sameshi ya masa bayanin komai kuma a washe garin sukazo akai komai aka sanya ranar auren nanda watanni biyu kacal!!!!! Wannan kenan.
***************
Yauce ranar wankin matar Ameen kuma an cashe daidai gwargwado,kamar yanda sakkwatawa keyi da safe sukai salalli da magrib akai wankan na amarya se kuma washe gari akai bikin kamu
Ba kadan ba Ummul tae kyau kuma ta tilastawa Nancy yin makeup ma ko islam tazo musu bikin, haka suka tasa islam agaba da zolaya suka kuma manna mata sirinrin mayafi shisa duk a wurin bikin a takure take ga maza sunzo ciki kuwa harda Maheer!! Ga wacce ta wadata wurin da abinci madam season 7 batasan kowa ba se Nancy so ita takewa nacin waza a kaiwa duk yayinda data miqe setakejin tamkar duk ita kae kallo.....tunda Maheer yaga wannan halittar hankalinsa ya tashi tunda yake be tab'a ganim mace me kyawun daya gani a fuskar Nancy ba, kai bama nan ba be yarda da love @ first sight ba se yau din nan, shibama kyawun ba yanayin murmushin datake zubawa ne ke dulmiyar dashi gefe d'aya kurin na kuncinta ke lob'awa haka kuwa ba qaramin kyau yayiwa fuskar tata ba, ga wushirya madaidaiciya dake tsakanin kyawawan haqwaranta!!! Wnnan murmushin yake bi da kallo ba fuskata ba, jin Ana kiranta da Nancy ya sanya ya ankare dacewar bega waccen ba kenan wannan itace Nancy?!!!!! Ya tambayi kanshi
Mom Nu'aium
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
14
Dogayen riguna ne guda biyu da mayafansu ja se kuma me black and dark purple sunyi matuqar kyau, se wani riga data kasa gane na material ne kona shadda me laushi dinkin ready made ne me asalin kyau yasha aiki ata gaban rigar shima guda biyu ne red and black ne kuma Emerald green se takalmi dako shakka batayi sun mata yawa wata kyakyawar sarqa data gani tafi komai burgeta acikin kayan, tana mamakin Maheer shidai ba tab'a ganinta yae ba mesa yake mata kyaututtuka ta tabbatar babu wanda ze iya shaidata acikin su se Mahal ranar dasuka ganta ba niqafi, menene alaqar sa da zuciyarta? Mesa yake mata kyaututtuka?" Nisawa tayi kanta janyo wayarta ta rubuta masa saqon godiya da adu'a.....murmushi ya sake bayan ganin message d'in nata ya mata reply Kamar haka
"Ameen ya nikeda godiya Hafsat" murmushi kurun itama tayi batae rply ba a sarari ta furta
"Wannan man din ya fiya nacin tsiya, narasa menene alaqar dake tsakaninsa da ruhi na ya ta'azzaramun" daganan ta miqe taje kasuwar da tae niyar zuwa.....yau kawai Hafst taga dacewan siyawa kayayyakin da Maheer ya bata mayafai wa ennan Rigunan qwaya biyu ko wacce ta siyan mata abinda ze dace da ita sannan ta siya fashion jewelries ta siya abubuwan datake buqata ta wuce shagon masu d'inki takai tukunna ta koma gida.
***********
Yau gaba d'aya Islam acikin damuwa take tunda Maheer ya tafi baya d'aukan call nata kuma shibe kirata ba, tashiga tsananin damuwa duk tayi rama, da wannan ta yanke shawarar ziyartar gidansa ko Allab zesa ta dace, har cikin parlor gidan kamala ya kaita ya gabatar mata da ruwa kafin yaje ya gayawa me gidansa yayi baquwa!!!
Kai tsaye kujerar dake fuskantar tata ya nufa ya zauna yana murmushi yace
"Manyan baqine yau agidan namu?" Kasa yin koda murmushi tae se yan tsunta datake murzawa a hankali cikeda qaguwa sekace me jiran wani abu....murya a dishe alamar tasha kuka
"Ina wuni Sir" kallonta yae yana murmushi yace
"Zaki kirani sir mana kinga hutunku yazo qarshe zamu koma muita gumurzu a class" Nanma batai magana ba yaci gaba
"Issy Baby yaya akayi ne? Na ganki da tsakar ranar nan" qwallan datake qoqarin tarewa ne ya silalo mata ta furta cikin raunin murya
"Maheer ka sani acikin dukkanin zagayen rayuwar d'an Adam akwai qaddarori iri biyu dake dabaibaye da akalar rayuwarsa, duk yayinda d'an adam yaso kaucewa wata qaddarar datazo masa da qarfin tsiya se reshe ya juye da mujiya, dukkanin abubuwan dake acikin qaddarar rayuwar mutum baya iya shallake su, na tabbatar kana sane da ingantaccen hadisin dayake nuni da yarda da qaddara ta alkhairi data sharri, kana kwai hadisin dayazo mana acikin arba'una hadith sahihin hadisin manzon rahma da bukhari da muslim suka ruwaito me bayanin ya da halittar d'an adam take tun daga mafarin samuwar sa har makomar sa ka, koda mutum shaqiyine kome ariziqi da abinsa ake haifarsa, hadisin be gushe ba seda ya tabbatar mana da acikin al'umma akan samu wanda ze kasance yana aikata aiki irin na en aljanna, harse ya kasance tsakanin sa da aljannar be wuce kamu d'aya ba sekuma ya aikata aiki irin ma en uwata kuma yashiga wutar, haka zalika d'ayanmu acikin al'umma ze kasance yana aikata aiki irin na en wuta harse ya kasance takaninsa da wutar be wuce kamu d'aya ba seya aikata aiki irin na en aljanna kuma yashigeta....ka sani Maheer dukkanin mutanen dake duniyar nan babu wanda baya kuskure koya aikata laifi kawai dai na wani yafi na wani munine, kuma Allah da kanshi yana yafe wa bayinsa bare kuma mu mu yafi juna? Na sani Ba duka maza bane zasu iya daurewa auren mace irina bama nida, amma ka sani auren na irina ma jahadi ne nayi tsarkakken tuba mezai hana ka tallafi maraicina ka aure na wlhy Maheer badan kai na tuba ba sedon tsoron Allah da kuma tunanin mezance masa idan ya karb'i raina ina mazinaciya sedai kuma maheer ina maka son daban taba yiwa wata halitta a doron qasa ba har kaina kuwa....Maheer ina maka *SON SO!!* ka kalleni da kyau ka gani wlhy banida *WATA FUSKAR* a qarqashin wannan ka dubi maraicina ka tallafi jihadina Maheer... Ka sanya Fuska ta tayi fice!!!! Tawa mazan bariki zarrah, ka taimaki salahatul Eslam ta sake *WATA FUSKAR* wacce tafi gaban mari awurin qadan garun bariki...dan Allah maheer" ta qarashe maganar a durqushe tana gunshshen kuka....nisawa yae gabaki d'aya maganganun islam gaskia ne ta ankarar dashi abinda ya gagara ganewa wanda addininsa ya sanar masa!! Cikeda tausayi yace
"Yanzu Islam me kikeso na miki?" Kallonsa tae
"Aurena zakai Maheer kayiwa Allah ka miyar dani macen danace in zama tun a baya" jinjina kanshi yae yace
"Kije inshaa Allah zan aureki cikin qanqanin lokaci, amma sekinyi bara'a kije ki tsarkake kanki namiki alqawarin aure inshaa Allahu" wani farin ciki ya mamaye ruhin Islam ta saki wani murmushi me qayatarwa kan tace
"Nagode maka Allah, na gode Maheer,Allah ubangji ya saka maka da mafificin alkhairin sa ya biya maka dukkanin buqatunka ya kuma tallafi bayan ka Maheer" gida ya sanya aka mayar da ita ya kwanta tunani shi sam baya sab'a alqawari kuma inshaa Allah ze gwada wannan wataqila auren na islam itace qaddarar sa shikuma yana ganin wata jarabawace yake gani akanta...yana roqon Allah ya bashi ikon cinyewa.
Mom Nu'aiym
*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*
*🗿WATA FUSKA🗿*
🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉
*Billy galadanchi*
*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*
16
Sosai yasha mamakin yarinyar to ita kuwa menene da riqa ninke wannan fuskar ta d'aura *Wata Fuskar* akan kyakyawar fuska irin wannan? Dukda ya kula akwai makeup a kan fuskar amma ya tabbatar da cewar itace tawa makeup d'in kyau bawai makeup d'inne ya mata kyau ba, tana sanye da rantsattsen lace maroon color ta yafa mayafi fari dayake ratsin fari ne ajikin lace din, mayafinta asaman kafad'unta duka biyu ta zagoshi be sauka ba bare ya rufe mata jikinta wannan ya sanya duk a takure take, yakuma kula sosai da hakan murmushi ya sakarwa kanshi ya kula ya shagala sosai da kallon Nancy yana qoqarin kawarda dubanshi gareta ta juya masa baya nan take doguwar sumar kanta da aka linke kusan hudu aka mata daurin zara buhari ya bayyana, kafe idanshi yae akan sumar kanta ko shakka bayayi yanayin Nancy ya masa shi duk wannan qaton qugun nata be dameshi ba sam hankalinsa yatafine akan murmushin ta me qayatarwa daya tabbatar murmushin ne yake sada zuciyar sa da tata wuri d'aya suke tattakin had'ewa su tarwatse masa!!! Gyaran zaman sa ganin dayae ta tinkarosa gaba d'aya, runtse idan sa yae haka halittar tafiyarta take ya gano hakan sanda take nufar sa ko a hijan haka tafiyar ke nunawa qafafuwanta ba tsaye suke ba miqe sundan bole aqasansu irin bow legs din nan sedai ba sosai ba kamarma heeps din dasuke shirin mata yawane suka miyar da qafafuwan haka, miyarda kallonsa yae zuwa ga fuskarta Allah ya mata arziqin goshi kam qatoto ma kuwa bazece yawa fuskar kyauba muniba amma bako shakka be wani yi mata kyau ba sedai yarasa ata ina kyawun ke fitowa to? Lumshe idon sa yae ya furta a sarari "Daga cikin ruhin mamammalakiyar fuskar ne bako shakka" Zuhair ya miqa masa kyakyawan kallo yace
"Kaima kana kallon wacce yarinyar ne ko, ban taba ganin bow legs sunyi kyau ba se nata dukda ba sosai suka bole ba amma kam ana gani tangaram, sedai kalli fuskar tsarki ya tabbatarwa ubangijin daya qera wannan halittar" kan Maheer ya lalubo wata kalma harta qaraso da yaron masu rarraba abinci a bayanta dauke da tray tana murmushi ta nuna ma yaron table tace
" yaa Maheer ga abinci kui hakuri se yanzu yake isowa ina wuni" yau kawai Maheer yaji kalmomin bakinsa sun masa nauyi ya kasa furta koda qwaqwaran kalma dayace se murmushi yake zuba mata itama haka aka gama jere abincin tace
"Yaa Maheer idan kana buqatar wani abun call me plss, islam fa banan na ganku atare ba" kallon wurin datake yae bema san yaushe ta tashi a wurin ba, murmushin sa kawai yake narka mata,kanma yace wani abun islam ta dawo, harara ta wurga mata
"Danla ni muje ki tayani nuna wa masu rabon abincin nan baqin mu na musamman Allah a tsauwale nake da mayafin nan, tamkar zan runtuma ihu" Dariya tayi
"To ai kuma wlhy kinyi kyau qawata kamar bake ba, babu ma wanda ze yadda kece Nanuwan Baba iro" dariya suka kwashe dashi dukkansu kan su juya a tare yanayin tafiyar Nancy yake kallo ata baya yana murmushi........
Mintsilinta lslam tai tace "ke mazari a hijabi yau banga kina rawar ba" Murmushi tae
"A wannan taron zanyi rawa Islam? Kumama babu sutura ajikina fa dan wannan mayafin wlhh gwara na wurgar ma nake gani nikam"
"Amma kinsan beyiba kice bazakiwa ummul lik'i ba, koda na 2 mns kiyi, kina sani sarai mutanen nan kallon maqiya suke muku, plss ki nuna musu kin fisu murnar bikin kije kiyi rawa abinki, bafa komai bane ba yanzu an wuce wannan abubuwan dakike Nancy" murmushi ta sake yi a karo na barkatai
"Zanyi liqin mana rawar cedai bazan yiba" haka suka wuce suna wannan zancen,tayi likin amma batai rawar ba sam har aka tashi a wurin bikin......
***********
Yayar Maheer sam ta kasa aminta da aurensa da islam yayinda mahaifiyarsu tace sam baza'a takura masa ba, idan bazasu tayashi da addu'a ba tokuwa su bari kawai sabida ita bataga dalilin fasa yin auren ba dan kawai ana taqamar yarinya bataji, a bincikenta kaf bataji inda akace yarinyar ta tab'a barin gidansu zuwa wani wurin domin yin zaman kanta ba, in ko hakane meye nasu na dirza rashin mutunci har suce bazasu bari ya aureta ba, qaddarace ta rayuwa kuma wlhy kowa ze iya afka mata" Badan sunso ba suka hakura tare da sanyawa abun albarka....Anty Nasara itace babba kuma itace fitinanniya acikinsu sam ita bawai dan ance yarinyar tayi yawon tazubar ba kawai batason talakawa, yanda friends dinta ke bata girna ace auren Maheer dataci buri zasuyi da er matsiyata qyaure kofar gidansu yarinyar ance basuda shi se fatar buhu a irin wannan gidan zasukai baqin su ko en rakiyar daukan amarya da en kai lefe? Gaskia da sake wai an baiwa me kaza qafa.....bari yaje amma taga maheer din!
A parlor shi ta sameshi zaune ya d'aura k'afarsa d'aya kan d'aya ta kalleshi da kyau ta murtuqe fuska alamar ba wasa...shi d'inma tashi fuskar ya had'e sosai
"Maheer mesa zaka mana haka?" Kallonta ya qarayi
"Name fa?"
"Kamar yaya name? Ita muna danace kaje ku shirya meta maka dazaka d'akko mata er gidan matsiyata kuma tsohuwar karuwa kace mana ita zaka aura, banda kake mara tunani ma menene alaqarka da er talakawa?" Takaici sosai ya kama sa harya gaza furta mata komai ganin haka taci gaba
"Gaskia maheer da sake, ka janye wannan zancen auren idan auren kakeso kaje mana ga muna tun yaushe take dauke sa sanka aranta, yarinyar er masu dashi wannan ma ai ko kayan gida sesu gagara yi" yanzu kam mutumina ya sosu, ko ita da kanta daya d'ago ya kalleta seda taji wani iri cikin takaici yace
"Danke zaki zaunamun da matar zaki gayamun wacce ta dace dani? Haba anty Nasara yaya da iliminki da komai zaki gagara gane cewar da arziqi da talauci duk na Allah ne? Da Allah ya had'aki da miji me arziqi mahaifinki ma me arziqi se akace miki wayonkine ko dabararki ya baki? Kokuma aa sabida kawai Allah yafisanki da sune ya barki ajikin daula su kuma akasin haka, ki sani wlhy bazan taba auren muna ba sabida ba zab'ina bace zab'inki ce islam nace inaso kuma inshaa Allahu kodan tsarkakkiyar niyyar danake da ita akan islam Allah ze bani aurenta, magana ta qarshe kuma gaskia karki qara kiranta da sunan karuwa cox ni banga wannan sunan a tattare da ita ba, salihatul Islam shine asalin sunanta incase baki san sunan ba" Harara ta wurga masa
"Au tunkan yarinyar tashigo ma harka soma mun rashin kunya Maheer abinda baka tab'a yiba lallai wannan yarinyar ga alama da bokaye ta had'aka" Miqewa yae
"Anty nasara zanje kano ne yanzu nikam, akwai bikin friend dina yau ake dinner friday kuma kinga goma ta gota" be jira cewarta ba yabar gidan ita kuwa tashiga neman yanda za'ayi tayi maganin d'an banza.....
**************
D'aya daga cikin jallabiyoyin da Maheer ya baiwa Nancy ta saka me ja din, tayi masifar karb'ar ta ta sanya takalminta ja mayafin abayar ma jane, tayi asalin kyau dukda kwalli ne kurin a fuskar nan se powder da red lips stick...... Sha biyun na ranar akai walima sabida suna so suje makeup din dinner da wuri yasan ya suka saka walimar da safe da wannan rigar taci walimar ta, ganin rigar ba wata me matsewa bace ya sanya tafita zuwa karb'o d'inkinta na dinner da ita, A daidaita take nema gashi so take tayi taje ta dawo kar su tafi gun makeup su barta amma shiru babu alamar adaidai tan tamkar anyi ruwa an d'auke ma gaba d'aya........motar data sha gaban tane yasa tadanja baya tana yamutsa fuska har dimple nata seda ya lob'a loda glass yaje qasa setaga islam da Maheer
"Banza da kin zata saurayine kimai halin ko, to nice ina zaki?" Murmushi tayi daya sanya Maheer lumshe idanuwan sa ya saukesu a kanta a hankali...
"Bauchi road zanje shagon su Munir, kayan dazan saka dinner suna cen kuma 4 zamuje makeup kinsan wannan" Sauke ajiyar zuciya tae
" kinsan me dama gidanku Maheer ze saukeni mu tafi makeup d'in a tare, amma nifa wanka nakeso inyi, abinda ze faru bari na sauka na qarasa da qafa tunda ga gidan cen ke kuma sekuje yakaiki ki karb'o ku dawo, kannan kinga nayi wanka semuje makeup d'in atare" Bataso hakan ba amma tasan Islam da wanka tamkar er agwagwa bazata yarda wai ta bisun ba dole ta fito ita kuma ta zauna agaban motar, shidai banda islam datace dashi
"Honey bye" ya sake mata murmushi tare da d'aga mata hannunsa bece kanzil ba, seda suka lula kan titi yace
"Ina wuni?" Wata iriyar kunya ce ta lullub'e ta taji tamkar ta nutse da qyar tace dashi
"Kayi hakuri Yaa Maheer senaga kamar mun gaisa" be kula taba jin yayi shiru ya sanya ta d'ago ta kalleshi sosai ya qura mata ido sekace ba tuqi yakeyiba ita yake kallo....kallon nashi ya nayar kan titin batare dare dayace qala ba itama shiru tae ya mata qwarjini a takure take jinta matuqa
"Rigar nan tamiki kyau fiyeda tunaninki" ta tsinkayi muryar sa yana fad'a.... Murmushi tayi
"Nagode yaa Maheer, yaya nane ya siyamun ita dama yasan zatamun kyau" Be zaci tanada barkwanci haka ba amna beyi magana ba se murmushi dayakeyi......har suka isa shagon Babu wanda ya qarayin magana acikinsu,fita tae bayan ya tsaya data nuna mai wurin tace tana zuwa........koda taje telan ya fita yakuma rufe durowarsa dayake ajiye kayan daya karba, abokin aikknsa kuma ya tabbatar mata indai kayan data kawone ta karbi wani ranar alhamis to kuwa be qara d'inka ko d'aya ba aciki, seda taji kanta ya sara mata ga wayansa a kashe, koda taje motar kuka takeyi juyin duniya kuwa Maheer yayi ta gaya masa menene amma se kukan take tamkar wata yarinya qarama.....head ma ta siya kalar lace d'in
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 20