Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
takalmi haka, har yalolon mayafin dazata yafa dukta siya d'ankunnayenta ma haka gashi uku saura. Shidai ficewa yae daga cikin motar ya nufi shagon bayan daya tambaya suka mai bayanin komai bece komai ba se godiya daya musu ya juya.....Da qarfinsa ya figi motar "Ki dena kukan nan haka, sekace wata jinjira tela seya sanyaki kuka, bari muje da akwai lace danake da a gida na siyane dama in sanya a lefe amma zan baki, nasan inda zasu miki d'inki cikin awanni biyu" "Nibase ka bani ba, ka barni kawai nafasa zuwa bikin, harfa head da takalmi da komai na siya kalar lace din shine zasumin baqin ciki" murmush yae sekace wata jinjira ji yanda take shagwab'a ya fada a ranshi, a fili kuma be kula taba yaje gidan nasa ya shiga ya d'akko, ya dawo ya tuqa motar suka dauki hanyar zabira mall ....Appareal sukaje ya kira babba acikin telolin yace dashi "Dinkin riga da skirt nakeso acikin awanni biyu zan samu?" Kallonsa telan yae "Yallab'ai sedai idan zakayi doubling kud'in" "Nawa kukeyine?" Ya buqaci sani "Dubu shida muke dinka set, kaga 12k zaka bayar amaka express kenan" zaro kud'i yae a aljihunsa ya miqa masa sunkai 15k yace maza ka aunata ga 15k nan, kuma yae kyau d'inkin nanda qarfe biyar da rabi zanzo na karba" murmushi telan yae ya hau godiya kana suka shiga daga ciki macen dake shagon ta aunata, ya karbo guntun lace din ya dawo mota suka tayar "Ki kaini kasuwan da kuke siyan Ashoeken zan siya miki da komai kinji" kallon sa tae "Ka bari wancen sena hadasu a haka kawai d'awainiyan seyae yawa" B'ata fuska yae ganin haka ta nuna mai, laylac purple ne touch up din dake jikin farin lace din haka suka siya komai suka biya MR.BIGS sukai take away, tawa Islam waya take sanar mata komai inda tace su hafu gun makeup sukam sun wuce abinsu..... Se after 6 d'inkin ya kammala, har lokacin suna nan atare, bayan angama taje gidan ta tarar na kowa, yace ta komatsa tazo haka tafito sanye da dinkin daya matuqar karbeta ya kaita wurin makeup daban yace tajira ya shirya yazo d'aukarta ........ ******** Shida kansa data fito be gama shaida ita bace ba, tayi asalin kyau na musamman makeup d'in babu wani hayaniya amma tayi kyau sosai, bud'e motar tae tashigo qamshin turaren daya siya mata d'azu ya daki hancin sa seda ya lumshe ido....beyi magana ba wayanshi ya soma ruri d'agawa yae "Baby" shine abinda ya furta a d'aya b'angaren "Kiyi hakuri gashima na d'akko qanwata zamuzo" shagwab'e fuska tayi "Honey kowa ya gama kallemun kwalliyana baka zoba ga angon ma naji yana tambayarka" "Kiyi hakuri Babyna, ina hanya yanzu zanzo naga kwalliyan zanma bada kudin wankan tunkan nagani na siya naira goma ina zuwa zam baki goman ki lakadan" dariya ta bushe dashi sosai yabata dariya ainun......Lokaci d'aya Nancy taji ba dad'i amma bata nuna ba sabida batasan dalilin jin hakan ba "Kinyi kyau Hafsat" kallonsa tae tana murmushi "Kaima kayi kyau yaa Maheer sosssai kuma banma ganekaba" Kallon ta ya qarayi,ita d'inma shi take kallo dukkansu suna murmushi ya d'age mata girarsa d'aya abinda ya sanya ta kwashe da dariya sosai har wushiryarta ta bayyana, shima qasa qasa yake dariyar yaja suka lula... Tun a qofar shiga wurin daze sadaka da hall d'in suka had'u dame d'aukar hoto nan take ya soma d'aukarsu hoto....tun suna kaucewa har suka tsaya ya musu haka suka doshi hall d'in bamewa wani magana amma murmushi ya kasa d'aukewa a fuskokinsu haka suka tunkari hall d'in aiko suna shiga kallo ya koma sama sabida d'aukacin mutanen dake wurin kallon su suke acikin dakakkiyar farar shadda maheer yake dinkin babbar riga yasha kyau ita kuwa farin lace ne me ratsin laylack purple tasha kyau, se haskawa suke tamkar wasu amarya da nagon me hoton da kanshi ya zata wasu ango da amaryar ne aiko ya soma danna musu pics hatta mutane da wayoyinsu se pics suke musu wasu basumasan dasu ba......islam qirjinta se dokawa yakeyi ganin shigowar su kasa hakuri tae tazo da sauri ta riqe hannun maheer murmushi ya sakar mata yace "Na matsu azo tamu dinner nanda jibi baby, duk naji tamkar ace nidakene, tajiyoshi sosai dukda waqar dake tashi ta saki murmushi "Allah ko?" Ta fada ya dage mata gira suka sanya dariya Hafsat kuwa harta sulale wurin Ummul dataga tana mata aamar tazo da hannunta...... Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 17 Yaune karon farko na had'uwar hannayensu wuri d'aya, zame hannunsa yae ya kalleta yace "Ba kyau kina had'e hannunki da nawa, tukunna dai" hannayenta ta had'e wuri d'aya "Am so sorry honey rud'ewa ne nayi dana ga kyawun dakayi" bece komai ta jagoran ceshi zama wurin da aka keb'e don abokanan ango da qawayen Amarya,kusa dashi ta zauna yayinda Nancy tazo itada khadeeja ita kuma ta zauna kujerar dake fuskantar tasa batare dama ta lura da shi ba, har kad'a kanta take sabida waqar na ratsa ta soosai😍😍😍 shi kuwa gogan ya shagala da kallonta har seda islam ta kula da hakan, deejah ce ta zungureta "Banza da zaran kinji kid'a se rawa, ikon Allah gaki saliha har saliha inda Allah ya rageki d'aya duk inda kikaji kid'a sekin raya" Dariya tayi ta dauki samosa dake gabansu acikin small chops da aka ajiye musu ta kai baki ta gutsura ta soma taunawa a hankali "Karkace kansa yae yana kallon yanda gefen kuncin ta na dama ke lob'awa idan tana chewing ramin is do deep gashi da tsawo shisa koba murmushi take ba sekaga kamar tana murmushin......islam kuwa kasa hakuri tae tace da Maheer " Honey mu koma sit na baya am not confortable anan" kallonta yae ya matso daf da kunnen ta ya rad'a mata "Kishine kawai kinga en mata se kallo na suke, karki damu duk kin fisu kyau kuma babu wacce nakeso seke, ko gani kikai idona ya sauka kan wata ni kece a idona,kuma kece a raina kinji?" Murmushi ya sub'uce mata ta saki murmushin tana wani mammaqale masa... Hafsat kuwa ta kaiwa moctail daya cafka ta soma tsotsa seda ta zuqi yafi rabi sannan ta dire ta miyarda kallonta ga khadeeja "Ina islam ke?" Dariya tae "Banza kinzo kina kwad'ayi ba gata a gaban ki ba" kallon gabantan tayi tana murmushi tace "Kai lallai ma wlhy islam ke er Air ce tunda kikaga yaa Maheer niko oho ko, zaki nutsune idan ma miki fushi" Dariya tai tana qoqarin yiwa Nancy magana aka qara muryan waqa dole tai shiru cox bazata iya ihu ba.... Waqar hausa ke tashi me taken Hasashena ya tabbata...sosai Nancy ke qaunar waqar wannan ya sanya ta kasa hakuri ta zari hannun khadeeja sukai cikin filin rawar a tare, wannan ne ya d'auke hankalin Maheer zuwaga islam bebi takan masu rawar ba sabida an cika.....suna hira aka sauya waqar zuwa waqar Arashi naso aikam se sowa suka jiyo, islam ce ta miqe Honey bari naga meke afkuwa acen wurin yasin dukda kake ganin nancy haka nan ne kawai Allah ya rageta yanda kasan me aljanai inda taji kida tokoda d'an yatsane seta taka rawa" murmushi yae "A sauka lapia to" juyawa kawai tayi taje ta shige cikin sahun gaba dayike duka a zaune ake masu rawar ne kawai a tsaye, to sekuma masu video dake gefe wasu har a wayoyin su......maheer ma juyawa yayi bil haqq Nancy da khadeeja se step dance skeyi duk inda aka sare ko aka karya a waqar ta arashi se sunyi murmushi ya sub'uce masa aranshi yace wannan ustazancin na Nancy yazo da wani salo irin na raini ma, kalli yanda take rawa har tana wani fari da ido wakar ma akanta yake, tsintar kansa yae dasoma yin video step dance da suke acikin wayar sa daga wurin dayake ya juyo gaba daya ya, dama sune a jerin gaba amma sit din dayake yana da nisa shisa islam ta koma gaban sosai ita kanta video take na rawar dasuke seda aka tsayar da waqar tukunna suka sarara wa kansu sukaje suka zauna,yanzu kam bata zauna da Maheer dan ita harga Allah ta manta dashi ma a wurin seshi da duk motsi yana kanta, aka qara kiran ango da amarya da abokanan ango da abaokanan amarya sui rawa haka suka jeru mata layi daya mazan ma haka, akwai wani gasa da ake na dance for the groom and dance for the bride qawayen amarya su mata na ango su masa aga wayafi iyawa,akan bada kyauta wa wanda yaci idan ango abokanan sa sukaci shi za'a baiwa in kuma qawayen amarya sukaci to....anyi anyi islam taqi ta shiga ita dai wai kunyar Maheer takeji ita kuwa Nancy ba ruwanta tunda ta soma rawar setaji ba kamar ranar kamu ba duk tadena jin kunyar beside acewarta ingaka fuskarta zuwa sunday anyi final....... Shida kanshi Maheer Bason yin rawar yake ba amma ya zeyi? Ameen shi ya saka a gaba akan lallai seyayi bashida zab'i mc ke zab'ar wa koea partner dazasuyi gasar anyi yakai mutane bakwai se a na 8 MC ya nuna maheer da kuma Nancy......tafi wurin ya d'auka har suna sowa akan zab'in na mc wasu daga ciki na ihun basu yarda ba a qarshe dai dukkaninsu kasa rawar sukai, shidai Maheer ya kasa rawar ne ganin yanda Islam tae kici kicin ita kuwa kunyar mutanen dake wurin dana Maheer ya hanata rawar, haka aka tashi a gasar maza suka cinye Bikin ba qaramun qayatarwa yayi ba zan iya cewa yafi sauran duka events da akayi.....Maheer da kanshi ya ebi su islam zuwa gida tare da khadeejah da Nancy, juyin duniya da shagawb'a Islam tayi amma Maheer ya kafe akan ita ze fara direwa gida tukunna sabida unguwarsuce cikin gari Nancy kuwa basuda nisa, badan tasoba ta hakura da haka ko sallama batawa Nancy ba ta shige ita kamma vata kulaba ta mance se dannan wayanta take....bayan fitar islam a motar ta dawo gaba ta zauna haka yaja suka tafi jugum jugum dama khadeeja gidansu take kwana wannan ya sanya suka d'auki hanyar gidan kai tsaye ya tsaya Flamingo ya siyan musu kaza da chips daganan suka lula hanyar gida, haka kawai daduka tsaya se khadeejah ta fita Nancy bata ko motsa ba deejah dai ciki ta wuce abinta,kallon ta ta miyar zuwaga Maheer "Yaa Maheer thank u so very much for everything i reallg Appreciate it, Allahu yabar zumunci ya qara bud'i ya kuma jiqan iyaye, Allah ya share maka hawayenka kamar yanda ka share nawa hawayen" Murmushi ya sakar mta dukda babu watacciyar haske yace "Ba komai ai yiwa kaine, yanzu se gobe kenan?" Murmushi itama tame kan tayi magana call yashigo wayarta tana dagawa islam tace "Frienf d'an bami deejah mana na tambayeta wani abin" bata kawo komai a ranta ba tace "Ki kira wayarta ta shiga cikin ni ina waje" qirjin islam ne ya doka tace "Waje kuma, after 11 fa keda wa?" Murmushi tae tamkar tana ganin ta "Nida yaa Maheer ne, na tsayane na masa godiyar d'awainiyar dayamun yau" tsaki Islam taja ta kashe wayarta kallon wayar Nancy tae da mamaki amma batace da Maheer komai ba, sallama ta masa ta fice a motar, taje tayita kiran islam bata dagawa tarasa dalilin wannan iskancin amma ba komai ruwanta. *********** Maherr dayaje gida ya kintsa wuraren sha biyu ta gota seya kira Islam so biyu bata d'aga ba, haka kawai yaji yanason yaji muryar Nancy kai tsaye ya juya akalar ntwrk dinsa zuwaga lambobin wayarta, ringin biyu ta d'auka "Yaa Maheer ka isa gida lapia?, kayi hakuri ban kirakaba na gajine wlhy" murmushi yae "Lapia lau ni gashi nakira ai, ya gajiya yaukin gaji ko?" Murmushi tayi me sauti "Na gaji wlhy duk jikina se tsami yakemun" "Ayya sannu kinji dear Allah ya baki lapia, dama nacene barin tab'oki,yanzu kin yi shirin kwanciya?" Gyaran kwanciyarta tae "Ea na kwanta amma na gagara bacci ko motsinsa banaji".... Hira suka hauyi sosai ita kuwa islam ganin call din Maherr ya sanya ta kira back amma shiru be dagaba se dogon call waiting haka ta juya tana kiran Nancy nanma call waiting, lokaci d'aya ta shaqa sosai wani azababben kishi ya bijiro mata na bazata ta gigice tana neman haukacewa Jin alamar kira nashiga wayar Nancy ya sanya Maheer yace " Hafsat wake miki waya cikin daren nan inajin qarar shigowar waya" tayi mamakin shi amma setace "Islam ce dayime nakirata bata daga ba shine take ta kirana ko zakamun uzuri injita" ya gano bincike take masa amma seya basar "Ba damuwa muyi waya da safe, promise that u'll call me early in d morning 2mrw" da murmushi tace "Allah ya kaimu goben zan kira" koda takira islam bata d'aga ba. A wannan daren islam ta gama shirin yaya zatayi da Nancy bazata bari wannan yarinyar tamata qwacen Maheer ba zata iya yin komai akansa!!!! ************** Washe gari asabar akayi wuni dakuma kai Amarya agidanta dake sama road en daukar amarya sun watse en mata sun dawo gidansu amarya amma babu Nancy babu labarin wayarta.....ankira layin har an gaji, kowa seyace rabon daya ganta tunkan isha!!! Wasa farin girki haka aka dinga neman Nancy har safe babu ko labarin inda take!!!. Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 19 Kai tsaye fareedah gidanta ta nufa tae wanka tae salla ta zauna ta qurawa wannan pic d'in ido ita sam ta kasa nutsuwa akan wannan maganar, yaya zaka dauki rayuwar d'an uwanka musulmi ba komai ba? Ko rayuwar arne babu wanda yace ka dauka ka kashe kace kaci bulus maganr nan da daddy keyi akan qyamatar talakan da Anty Nasara keyi har yaje wannan wurin!! Yasha yin fad'a akan korar mutanen datake yi idan sunzo masa, yakance mata yana tausayin ta kar wata rana wannan qiyayyar datakewa talaka ya janyo mata wata musibar, gashi yanzu ta fara gani tunkan aje ko ina, sabida tsabaragen iskanci da sonkai gashi nan ta soma safarar mutane....."Bazan iyaba!!!" Ta furta a sarari da d'an qarfi ladiyo me mata aiki tace "Na'am hajiya, Magana kike ne?" Murmushi ta sakar mata na yaqe tace....a gayawa d'an liti ya shirya zan fita, wayarta ta d'auka tawa Maheer waya yana d'agawa suka gaisa tace "Kana ina ne zamui magana dakai ne" "Shirin zuwa sokoto nakeyi ko ince nama kammala sokoton zani" "Idan na roqi aron awa daya zamui magana ban takuraka ba maganar tanada muhimmanci ne" murmushi ya sakar mata tamkar tana gabansa "Ba komai anty Reedah bari nazo" "Ka zauna kawai ni ganinan tahowa gidan naku" sallamah sukai ya zauna a parlor part dinshi yana nazarin dalilin reedah nasan ganin shi cikin gaggawa haka, yaga dai dazu dazun nan suka rabu, shikamma zewa sokoti shigar dare dan yanzu qarfe biyu ta kusa haka ya zauna wurin 30mns kanta iso........ Quryar dakinsa taja shi mahaifiyarsu nata murmushin ganin ana gudunta da zanje ta wuce dakinta abinta..... Zama sukai sannan ta kalleshi "Sorry lele na b'ata maka lokacin ka ko?" Kallonta yae bece komai ba ta zaro wayar ta, ta lalubo hoton dayake tare da Nancy sunsha kyau kamar ango da amarya an dauki hoton daidai lokacin da dukkansu suka daga qafarsu daya da zummar takawa suci gaba da tafiya kana ko wannensu dauke yake da murmushi a fuskarsa se glowing sukeyi........ A hankali ya karb'i wayar ya qurawa hoton ido hoton ya masa kyau ainun ya burgeshi hanun shi yakai ya miqa dan ya tsarsa d'aya ya tab'a saitin dimple nata d'aya daya lob'a besan yaushe hawaye ya zubo masa ba harga Allah wani tausayin ta yaji ya kamashi sabo fili, farkon b'atanta yakansa hotunanta da videon rwarta agaba ya dinga kalla amma yanayin azabar dayakeji a zuci game da ita ya sanya ya dena amfani da wannan wayar zuwa wata, akwai wani waya dasukai da dare shida ita sanda ya mata hidima a gun finner take mai godiya mistkenly ya danna record sanda suke wayar bemasan ya shiga ba se daga baya dayake duba wayanshi yaji shima yakan kunna ya dinga sauraro gwanin tausayi😭😭....... Kallon sa Anty Fareedah keyi cikeda mamaki ya shagala da kallon hoton amma ya gagara ce mata cikanki!!! Matsawa tayi kusa dashi ta riqe hannunsa d'aya ya d'ago ya kalleta tace "Wacece wannan Mahi?" Ta kirashi da sunan dasuke masa wani zubin ko ince yakusa ya zama sabon en gidan wato mahi...... "Anty qanwa tace, kuma kusan watanni biyu yanzu kenan da b'atan ta, ko bekai biyu saura kad'an....ta b'ata b'at anty wlhy, an nemeta an rasa sama da qasa" qura masa ido tae na wasu en daqiqu bilhaq kuka yakeyi kuwa lallai ta b'aci sabida tun suna yara maheer yakeda qarfin hali wani zubin komai girman dukan dazasu masa baya kuka harya girma kuwa baka ganin kukansa sabida dauriya har wani zubin sukan ce masa Biggest soldier.....hannu takai ta share masa qwallan sa akwai shaquwa me tarin yawa tsakanin sa da Fareedah tare suka tashi shekaru biyu ne a tsakanin su Twin brother take kiranshi shima yace mata twin sister har a waya haka sukai saving number's na juna..... "Twin kuka kuma, menene tsakanin ka da wannan yarinyar da kakewa b'atanta kuka, am pretty sure cewan she's not d first person daka samu labarin b'atan ta" "Anty Reedah wlhy mutunci yaufa muna tare gobe aka ce dani ta b'ata kuma shikenan fa anty ko labarinta babu, gwanda ace ta mutu ai ko" tausayin sa taji "Qawar kace?" Qwallan shi ya sanya yatsa ya d'auke "Qawar islam ce, kuma student d'inane, beside munada shaquwar wuni d'aya a tare, bama wannan ba kallon sister na nake mata tamkar ke da sauran en uwana ina qaunar yarinyar nan" shirune ya ratsa d'akin na wasu en daqiqu ya nutsu sosai yana kallon fuskar ta....muryan reedah ya tsinkaya tana magana "Twin akwai damuwa fa" kallonta yae "Mecece damuwar Twin sis?" Sadda kanta tae a qasa "Anty nasarace tasanya aka........."daga nan ta kwashe komai ta gaya masa tun yana gane zancen ta har ya zamana meji amma kurma sam baya ganewa, babu dalilin aikata hakan agun anty Nasara sabida selfish interest nata kawai seta b'atar da d'an adam qwaya d'aya jal!! Jejin Amanawa!!! Ya nanata hakan a zuci se kuma ya miqe kamar wanda aka tsikara ya kalli reedah " Anty fareedah wannan yana nufin kenan tuni Hafsat ta mutu aljanai ko namun jeji sun cinye ta ko?" Riqo hannun sa tae "Calm down twin pls, inshaa Allahu Allah baze bariba wanda suka kaita cen ai muta nene, suba sun dawo ba? Inshaa Allah yanda suka dawo haka zamu nemota ta dawo itama kaji" duk da AC dake bayarda ni'imtacciyar iska me dad'in qamshi hakan be hana shi had'a gumiba, ya kalleta a karo na barkatai yace a yamutse "Anty Reedah da tana raye aida an ganta tuni kusan watanni biyu fa cur?" Tausayi ya bata ta kula cewar akwai shaquwa sosai a tsakanin su kasa magana tae ya sake cewa "Barinje in gayawa umma wlhy Anty Nasara seta gane kuskurenta har daddy zan kira yaji wannan rashin imanin da ta yi" miqewa tae ta riqeshi "Karka soma zo muje gidanta kabi komai a hankali kaji" haka sukaje gidan a hanya se rarrashin sa takeyi har suka isa.... **************** "Amma anty binta hakan yayi kenan, da islam d'ince se ki mun asarar ta,kina nufin kenan dan abinda nakeso yana talaka bazaki tayani sonsa ba matsayina na d'an uwan ki" harara ta wurga masa "Dan ubanka ninace maka abinda akayi laifi nane? Na samar da reedah dataje ta d'akko ka y'ar akuri ce ta aikata waidan yarinyar taganta karta tona azaci mudin masu garkuwa da mutanene, cewa fa kurun a tsoratar da ita ta fasa auren ka ni meye laifi na sema dana dawo ake gayamun" kallon ta yae cikeda takaici da baqin ciki mara misaltuwa yace "Ba wannan ba yanzu ha d'amu da qawar taki ta nuna mana yaran da inda suka kaita nida kaina zan shiga neman ta da police" da dauri ta d'ago ta kalleshi "Da police kuma kanada hankali kuwa sekaje a riqa cewa wai yayarka me en ta'adda wlhy kayi kadan tunkan ba qanwar uwarka bace ba seka qyaleta ai" kallonta yae har idanshi ya kad'a yae jajir se zare mata su yakeyi ita kanta ta tsorata da yanayinsa ya dauke qafarsa d'aya ya d'aura kan d'aya yace "Anty Nasara ki sani wlhy baki kaimun cenba, na rantse da wanda rayuwata take hannun sa akan Hafsat zan iya yanke jinin dake yawo nawa acikin naki, zan yanke alaqa dake ta har abada, zan rabu dake rabuwa me girma zan nisanceki nisan ci me tsanani wlhy summa tallahi zan tsaneki tsana mafi muni a rayuwa!!! har a wurin Allah banida laifi idan nayi hakan sabida baki d'auki rayuwar d'an adam a bakin komai ba, zan kuma gayawa Daddy zan sanar masa cewar bakida imani yanzu kin sauya daga Fatima Bintar daya haifa kin zamo me kisan kai me gardawa,gwara miki tun wuri ki dawo hayyacinki zan rufa miki asiri na hana en sandan dogo bincike na binne sunanki kimun bayanin su dan naje nemanta da kaina" Mamakin kalaman sa ya sanya ta gaza furta koda kalma d'aya ta hango haqiqancewa a kalamansa iyakar gaskiyar sa kenan fa!! Reedah ce ta tare *look twin beje cenba abin sam ko kad'an beyi nisan daze cenba, ke kuma Anty dan Allah ki had'a mu dasu waike ko haqqi bakya tsoro" nisawa nasaran tae tace ba damuwa zan hadaku dasu yanzun nan amma dai kaikam ka bani mamaki ta yanda zaka fifita wata bare akaina har kana rantsewa akan datse zumuncin mu akanta lallai da mugun abinda ta maka" bece mata kanzil ba harta had'asa dasu. Mom Nu'aiym *Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)* *🗿WATA FUSKA🗿* 🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉 *Billy galadanchi* *Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham* 18 Maheer besan meke faruwa yana zaune a parlor gidansa babu abinda zuciyar sa ke masa se azalzalarsa akan yaje yaga Islam beson fushin ta ko b'acin ranta ko kadan, yayita kiran layinta a kashe gashi gaba d'aya ya damu, Maheer yana qaunar Islam sosai baso na wasa ba......breakfast kurun yake jira ya tafi ya qakara, whatsapp nashi ya shiga yaje gun status kai tsaye.....acen yaga wani friend dinsu ya saka rawan dasu Hafsat sukayi jiya beso hakan ba ze mata fad'a sosai akan rawa, tanada kamun kai koyaya takeson rawa tasan inda ya dace tayi rawar shine yafi,acikin maza bayaso yanzu gashi video din yana yawo hakan aibe kyautuba tsaki yaja a ranshi yace "Nikuma awa?" Wuce status d'in yayi sekuma ya miqe tsaye da sauri kamar wanda aka tsikara ya qara qurawa picture din ido, hoton sane shida ita anja arror akusa da ita wai ana cigiyarta tun jiya da dare daga kai amarya kowa ya mata shedar batada yawo an jajje gidajen en uwa ba'a same taba.......da jallabiyar jikinsa ya fita daga gidan jikinsa har rawa yakeyi b'ata fa, jiya ya ganta wurin kai Amarya to ina tashiga? Shida kanshi ya kula da rashin ganin dabe mata ba sanda ake qoqarin barin gidan amaryar akai en mata gida har layinta ya nema be shiga ba...... Kai tsaye gidansu islam yaje anan yakejin wai tana kwance babu lapia tun shekaranjia.....har ciki ya shiga suka gaisa yake gaya mata aikuwa ta nemi cutar dake damunta ta rasa, se kuka tare sukaje gidan su Nancy islam se kuka take masa amma hankalinsa baya gunta, koda suka je khadeeja ce me musu bayanin "A tare muka fito daga cikin gidan Amaryar fitsarine ya mayar dani da gudu inyi kafin mu dawo, na barta aharabar gidan...mune farkon fita gaba daya amma sena samu matsala danaje fitsarin nashiga toilet setai locking ga d'akin dana shiga babu kowa acikinsa haka nayita kici kicin na bude ga wayana

Chapter 8 of 20