ta siya dubu sha biyar ne ribarta a ciki.
"Amma Fareeda kin fahimci maganganun da na gama karanta miki a matsayin sharar fage kuwa?
Wallahi kin ji na rantse da girman Allah babban burin Fatima idan aka yi aurennan ki wulaƙanta a gidannan. Daga ƙarshe baƙin ciki da takaicin yadda za ki ga tana juya mijinki ya zama ajalinki.
Magunguna take amfani da su kala-kala, wanda suka dace da waɗanda basu dace ba, ba ta jin ƙyashin kashe ko dubu nawa aka faɗa mata kuɗin magani matuƙar aka tabbatar mata da ingancinsa..."
"Uhmmm! Taje tai tayi wallahi, Ramlah ƙyaleta taje tai tayi. Ni Allah ya sani tun farkon tarayyarmu ba Fatima kaɗai ba, da zuciya ɗaya nake zaune da kowa. Ko da suka ƙullah za suyi aure ni ba na mata fatan ta wulaƙanta, Aniyar kowa ta bi shi tsakaninmu."
Duk yadda Ramlah taso juyar da tunaninta don ta sayi maganinnan ko bashi ne bayan biki ta biya ƙin karɓa tayi. A ƙarshe dai haka suka rabu dutse a hannun riga, zuciyar Ramlah cike da takaicin buƙulun da Fareeda tayi mata, ta fice a gidan tana jan tsaki.
Bayan fitarta Fareeda ta daɗe zaune a gurin, hannayenta biyu tallabe da kunci, damuwar zuciyarta na ƙara ninikuwa.
Daga fara maganar aurennan zuwa yanzu matan da suka zo takanas ta kano har cikin gidanta da kuma waɗanda suka kira ta a waya da maganganu na ɗaga hankali baza ta iya ƙayyade yawansu ba.
Kaso biyu da rabi cikin uku na masu yi mata jaje da bata shawarwari ce mata suke yi
"Fareeda sai kin tashi tsaye, wallahi idan baki tashi tsaye ba kina ji kina gani gidan mijinki zai gagareki."
To don Allah ita ya suke so tayi da rayuwarta? A matsayinta na marainiya babu uwa ba uba ta tashi tsaye taje ina? Ita ba kuɗi take da shi ba, kuma ko tana da kuɗin tana roƙon kar Allah ya nuna mata ranar da za taje gurin wani ko wata don neman taimako akan Mijinta.
Tana neman taimako ne a gurin Allah kaɗai, kuma tana da tabbacin shi zai kareta daga duk wani sharri ko bita da ƙulli da zai sameta, ba ma akan al'amarin auren Mukhtar ba, aduk wasu lamura na rayuwarta a duniya.
Idan ta ce maganar da Ramlah ta faɗa mata kan Fatima bai tsaya a zuciyarta ba tayi ƙarya. Amma babu komai, ita dai tana ta cigaba da addu'a har a gama rugu-rugun bikinnan kar Allah yasa imaninta ya raunana kan ɗa namiji.
Ɗa namijin da bashi da tabbas, tun zamanin kakanninmu da iyayenmu har yau maza sun kasa mallakuwa. Ko a tarihi da labarun hikaya bata taɓa jin wata shahararriyar mace da ta samu nasarar mallake ɗa namiji ya mallaku mata har abada ba.
To me zai kaita ta kashe ƴan kuɗaɗenta sannan ta ɓata lokacinta a banza? Ba dai Mukhtar bane? Tana ta ƙara dagewa da Addu'a Allah ya cire mata damuwa da al'amarinsa a ranta.
Za tayi masa biyayya, za ta bi umarninsa kamar yadda addini ya umarta. Amma idan ya aje ta gefe Wallahi ita ma za ta aje shi ne, idan ya zaɓi Fatima ya ce ita Fareeda zai wulaƙanta za ta rabu da shi, rabuwa ta har abada.
Ta rasa uwa da uba a duniya tayi haƙuri ballantana wani ɗa namiji? Miji goma ba uba goma bane, za ta cigaba da zama ne kawai idan ya riƙe ta da darajarta. Allah bai wulaƙantata ba babu wani mahaluki da ya isa ya wulaƙanta ta.
Fatima kuwa in dai Mukhtar ne ga ta ga shi nan, Allah ya basu sa'a.
*****
"Mukhtar wai don Allah da gaske kake wannan maganar?"
Abokinsa Ibrahim ya tambayeshi, da fuskarsa mai ɗauke da matsananciyar mamaki.
"Au! wai kai baka yarda ba? Wallahi da gaske nake yi."
Ya rantse don ƙara tabbatar masa da gaskiyar maganar ƙarin aurensa, ya cigaba da cewa
"Yanzu haka ma na kai komai da ake buƙata, saura kwana takwas ɗaurin aure. Kaga tunda bazawara ce babu wani amfanin ɓata lokaci..."
"Amma gaskiya ka bani mamaki, anya kuwa wannan busasshiyar haka ta barka? Kai da kake da mace kamar Fareeda wani kuskure ko rashin rabo ne zai kai ka ga auro Fatima? Matar da a fuska kawai za ka gane duk bula ce, idan bata girma maka ba ba na jin kai za ka girme mata.
Ni a ture ma zancen Fatima Aminiyar Fareeda ce, tunda aurenku ba haramun bane duk mai hankali bazai tsaya ja'inja ba.
Amma don Allah me ya shiga cikin hankalinka? Kai da na sanka mutum mai bala'in tsantsenin bazawara? A cikin ƙungiyar abokanmu kowa ya sanka kan wannan aƙidar ta cewa baza ka iya mu'amala da wacce wani namijin ya rigaka mu'amala da ita ba, ko da kuwa sakin wawa ce.
Sai ga shi ba ma sakin wawa za ka kwaso ba wacce ta haife ƴaƴaye rututu, ina wani abin sha'awa ko burgewa a tattare da ita don Allah?
Ko ka manta falsafarka da kake cewa duk wanda zai ƙara aure ya tabbatar wacce zai auro ta fi matarsa ta gida da abu uku.
Tafi ta kyau
Tafi ta asali
Tafi ta ƙuruciya.
A cikin abu ukunnan wannene Fatima ta fi Fareeda?
Ka manta..."
"Ka ga don Allah saurara Ibrahim, tunano tsofaffin maganganun da nake yi a baya tun kafin in waye da rayuwar duniya ya isa haka."
Ya katse abokin fuskarsa na bayyana matsanancin ɓacin rai. Cikin zafin zuciya ya cigaba da cewa
"A ɓangaren zaɓin abokiyar rayuwa ni nake da ƴancin yin haka ba wani ba. Kuma duk waɗannan maganganun da kake yi a baya ne na furta su, a yanzu ina kan wani mataki ne na nemawa kaina mafita da hanyar ɓullewa cikin salama ba tare da baƙin ciki ya kashe ni tun lokacina baiyi ba.
Fatima dai ita ce zaɓina, ita nayi ra'ayin aure a matsayin mata ta biyu. Idan kuma akwai wanda yake da iko da rayuwata sai ya canza min ko kuma a hana ni ƙara aure gaba ɗaya."
Daga haka bai sake cewa komai ba ya shige ɗaya daga cikin ɗakuna uku da ke cikin ginin yana sake duba irin gyaran da ma'aikan sukai masa.
Lokaci bayan lokaci shi kaɗai yake jan tsaki. Ya rasa dalilin da yasa duk wanda ya ji labarin zai ƙara aure da kuma wacce zai aura sai ayi ta kushe lamarin, bakin mutane bai taɓa furta alkhairi kan lamarin.
Da yawan mutane nuna masa suke lallai ya tafka kuskure a gurin zaɓinsa. To ina ruwan jama'a da ra'ayinsa?
A wannan lamari shi ne mai ruwa da tsaki, kuma ga wacce yake ga tayi daidai da irin ra'ayinsa. Me yasa mutane baza suyi koyi da Hadithin nan da yake cewa a faɗi alkhairi ko ayi shiru ba?
Bai san Ibrahim ya fice daga gidan ba sai da ya fito daga cikin ɗakin. Ko da ya leƙa ƙofar gida bai tarar da motarsa a gurin ba.
Ko a jikinsa ya sake jan tsaki tare da komawa cikin gida bayan ya janyo ƙofar apartment ɗin da aka gama gyara ya kulle. Gyaran yayi kyau sosai da sosai, angama komai.
Sai dai duk tattalin arzikinsa ya kusa shigewa a wannan gyaran, maƙudan kuɗaɗe ya saki sosai aka gyara gurin don kawai ya faranta zuciyar Fatima.
Tunda ta bashi tabbacin kayan gado da kujeru masu bala'in tsada za ta siya ta zuba a ɓangarenta, shi yasa yayi gyaran da baza ta taɓa ji a ranta tayi asarar kashe kuɗinta ba.
Da sallama a bakinsa ya shiga ɗakin Fareeda.
A hankali ta ɗaga kanta daga kan wayar da take dannawa ta kalle shi tana amsa sallamarsa.
Cikin ɗakin ya shigo, ya nemi guri kan katifarta ya zauna, idanunshi a kanta. Cikin kwanaki goma sha huɗu da ɓullar maganar auren ta yi wani sanyi gaba ɗaya kamar ba ita ba, sam ba ta da karsashi.
Har wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar rama tayi a fuska, hancinta ya ƙara tsawo. Amma fa ko ya ƙi Allah ya san tana cikin nutsuwarta.
Babu abinda ta fasa masa na dangane da hidimar gidan, sai dai gaba ɗaya ta janye jikinta daga gare shi. Kuma babu wani ɓacin rai a fuskarta balle ya ce haukar kishi ke damunta.
Jingine shi tayi a gefe ɗaya, magana idan ba dole ba bata cika son yana shiga tsakaninsu ba, ko ɗakinsa ta daina zuwa, shi kuma ko sau ɗaya bai taɓa yi mata ƙorafi kan haka ba.
Ya zuba mata idanu ne yaga iya gudun ruwanta. Aure ne dai, bazai fasa ba.
"Biki saura kwana takwas"
Ya karya shirun da ke tsakaninsu da faɗin haka.
"Allah yasa muna da rabon gani."
Tayi maganar cikin rashin damuwa.
Wayar hannunta ta ajiye a gefenta, ta kalle shi cikin idanu, sai da taja addu'ar ya hayyu ya ƙayyumu kafin tayi ƙarfin halin cewa
"Ina neman alfarmar don Allah ka barni in koma wancan apartment ɗin da aka gama gyarawa..."
"Amma dai wasa kike ko?"
Ya katse ta da tambayar, yana aika mata da wani irin kallo mai kama da na lallai ba ki da hankali.
"Wasa dai? Uhmmm! Me zaisa inyi maka wasa a daidai wannan gaɓar? Da gaske nake yi. Idan ka bani dama zan koma wancan apartment ɗin in bar ma amarya wannan, ya ishe ta, tunda ba ta da ƴaƴa.
Idan baka manta ba wancan part ɗin ɗakuna uku ne, nan ɗin kuma biyu ne. Kuma wancan shi ne a farkon gida, nan kuma a baya.
A matsayina ta uwargidanka kuma uwar ƴaƴanka can ɗin ne ya dace da ni ba Amarya ba..."
"Fareeda. In dai ba tashin hankali kike nema da ni a tsakar ranar nan ba ki bar wannan maganar. Nan ɗin dai shi ne naki, can na gyara da sunan Fatee ne, ita za ta shiga ciki. Idan kina so zan iya sakawa ayi miki fentin nan ɗin, shi ma ya koma kamar sabo.
Amma can na Amarya ne, ita kanta ta sani, har na faɗa mata yanayin ginin domin siyo labulayen da zai isa. Ki bar ma wannan maganar."
Bai sake bata damar cewa komai ba ya fice daga ɗakin.
Ta bi bayanshi da kallo, zuciyarta na wani irin tafarfasa, a hankali ta lumshe idanunta tana maimaita
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Lahaula walaa ƙuwwata illah billah"
Su tayi ta maimaitawa tana ji ɓacin ranta na raguwa da kaɗan kaɗan, sai ta zame ta jingina da jikin gado, ba'a ɗauki lokaci sosai ba nannauyan barci ya kwasheta.
*****
"Hmmm! Fatima kenan, sai muka na samu labari a bakin Ummee wai za kiyi aure."
Wani mugun kallo ta juya ta aika ma Ummee, wacce duk cikin yaran nata ita ce mai bala'in surutu kamar aku.
Daƙyar ta iya ƙaƙalo dariyar yaƙe ta mannawa fuskarta, ta kalli Yar mijin nata a ɗarare, da alamun rashin gaskiya ta fara kalaman kare kanta.
"Kiyi haƙuri Yaya, wallahi daman ina shirin zuwa in faɗa miki da kaina... kawai dai..."
"A'a! riƙe kawai dai ɗinki. Ina fatan baki manta wasiyyar marigayi ba?"
Ƙiƙƙifta idanu ta fara yi, da alamun ta manta wane wasiyya ne tsohon mijinta uban ƴaƴanta ya bar mata? A yanzu Mukhtar da soyayyarsa ce kawai a zahirinta da baɗini, ta daɗe da manta duk wasu abubuwa da suka shuɗe. Gaba da abinda za ta haifar kawai take hange.
"Uhmm! ƳarAdam butulu. To bari in tuna miki, a gabanki da mu ƴan'uwan mijinki kafin rasuwarsa ya ce idan za kiyi aure in karɓi ƴaƴansa."
Wani ƙatoton ajiyar zuciya ta sauke a fili, wani murmushin farin ciki ya bayyana a fuskarta. Dama ina za ta iya kayan ƴaƴa ita da take burin yin ƙara'i na sosai a fannin soyayya.
Ta buɗe baki za ta tambayi a haɗo kayan ƴaƴan ne Yar mijin ta faɗi maganar da yasa ta ɗauke wuta na wucin gadi.
"To kinga tunda aure za kiyi, baza mu taɓa barinki da dukiyar marayun ƴaƴanmu a hannunki ba. Duk abinda kika san na Yaya ne ya siya a gidannan ki tattaro su guri ɗaya, daman already Mujittaba ya gama haɗo duk wasu takardun kadarorin da Yaya ya mallaka.
Za'a raba gado in Allah ya yarda gobe da yamma, za'a fitar miki da tumunin takaba a baki abinki. Su kuma yara za'a cigaba da juya musu dukiyarsu har zuwa sadda za su mallaki hankalin kansu. Na barki lafiya."
Ko bayan ficewarta Fatima ta daɗe zaune a gurin kamar mutum mutumi, ita yanzu idan aka raba gado aka ƙwace kason ƴaƴanta a hannunta ya za tayi da batun kayan ɗaki na garari?
*****
Daf da kiran sallar magrib Mukhtar da Fareeda suka karɓi baƙuncin Hajiyarmu. Da ƴan rakiyarta Shaheed da Sayyid (Ƴan biyun Fareeda), da ƙanwar Mukhtar Zubaida wacce har lokacin bata koma gidan mijinta a lagos ba.
"Ko bakuyi murnar ganinmu bane mu koma?"
Hajiyarmu ta faɗa ganin yadda suka ƙame guri ɗaya fuskokinsu cike da mamakin wannan ziyara ta bazata.
A tare suka ƙarasa da sassarfa suna yi mata sannu da zuwa.
Zubaida da yake akwai shaƙuwa sosai a tsakaninta da Fareeda hannu ta bata suka kashe suna musayar murmushi.
Ƴan biyu da gudu suka ruƙunƙume mahaifiyarsu, kowa na ƙoƙarin bata labari da hausarsu da bai gama fita ba.
Daƙyar Mukhtar ya janye su ita kuma ta fara jelar kawo ma Hajiya ruwa da abinci, cikin mintuna ƙalilan ta haɗa ma Hajiya kayan tarbar baƙi a mutunce.
"Mummyn Twince, akwai wata matsala ce?"
Hajiyarmu ta tambayi Fareeda cikin kulawa, tana kallon yadda ta rame a fuska ba kamar zuwanta gurinta satin da ya wuce ba.
"Wallahi ba komai, me kika gani Hajiya?"
Mukhtar yayi saurin amsawa kamar shi ne Fareeda.
Wani mugun kallo ta watsa mishi, ba shiri ya sunkuyar da kai yana ba ta haƙuri.
"Daman zuwan takanas don kai nayi ta. An gama gyaran wancan ɓangaren ko? To tunda dai ɗakunanshi uku ne nan kuma biyu gobe in Allah ya kaimu Fareeda ki kira ƴan'uwanki su taya ki tattare kaya ki koma can.
Nan ki bar ma Amarya. Nan da kwanaki uku za'a dawo da su Alhassan, a cikin ɗakuna ukun sai a ware musu ɗaya a shirya musu kayayyakinsu. Ka riƙe ɗaki ɗaya, itama ta riƙe ɗaya.
Nan ɗakuna biyu, falo, bayi, kicin sun isa amarya ko ƴar gidan uban wanene. Ina fatan ka ji abinda na ce?"
"Na ji Hajiya. Haka za'ayi in Allah ya yarda."
Ya amsa daƙyar kamar mai ciwo a maƙogwaro.
"Madallah! Zubaida tashi mu tafi..."
"Ayya mana Hajiyarmu wayyo, tunda kika shigo fa ko ruwa baki sha ba, don Allah ki bari ku gama cin abinci sai ku tafi."
Fareeda ta katse ta da ƴar damuwar rashin zamansu Hajiyar a fuskarta.
Amma fa zuciyarta Rai fes sunan wata zani. Haƙiƙa da gaske ne duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa. Ita ta fara mishi zancen komawarta can ɓangaren, ya ce bazai yiwu ba, sai ga shi cikin sauƙi wacce za ta bashi umarni ba tare da ya musa ba ta zo ta yanke hukunci, kuma ba tare da ta kira Hajiyar ta faɗa mata ga yadda suka yi ba. Allah mai girma.
Mukhtar dai tunda ya duƙar da kanshi ƙasa har su Hajiyarmu suka fice ganin sabon gini bai iya ɗaga kanshi ba. Daga can kuwa sallama suka yi ma Fareeda direban Hajiya yaja suka bar gidan.
*_Aminci + Ƙarko Data Services_*
*_Kina/kana buƙatar Datar MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE mai matuƙar aminci da ƙarko? Wanda za ki daɗe kina sauke abubuwa da kallace-kallace ba tare da yayi saurin ƙarewa ba?_*
Ga farashin datarmu a sauƙaƙe👌🏽 ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai a tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online a kira ni ta 09077591726.
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
Hallau muna tura katin waya, katin startimes, go.tv, e.t.c👌🏽
*_Namu ba irin nasu bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*14*_
Ta daɗe tsaye a tsakar gidan bayan tafiyarsu. Tunanin Mukhtar zai iya zargin ita ta kira Hajiyarmu ta faɗa mata wannan maganar yasa duk jikinta yayi sanyi. Lokaci ɗaya ta nemi matsanancin farin cikin da ya lulluɓe zuciyarta ta rasa.
Da taga dai tsayuwar bazai mata ba sai ta fara takawa a hankali zuwa cikin falon, hankalinta a tashe, zuciyarta a ɗugunzume.
Ko da tayi sallama bai amsa mata ba, yana zaune a inda suka barshi, har lokacin kanshi a ƙasa.
Saɗaf saɗaf ta kama hanyar shigewa ɗakinta.
"Fareeda"
Ya kira ta da wani irin murya da bata taɓa jin ya kira ta da irinsa ba.
Lokaci ɗaya idanunta suka cicciko da hawaye, daƙyar ta iya juyowa tana kallonsa, wani dunƙulallen abu da ya tokare mata a maƙoshi yasa ta kasa amsa kiran da bakinta.
Bai damu da rashin amsawar da bata yi ba. Ya miƙe tsaye da wani irin fusata kamar bajimin zaki, ya naɗe hannuwansa a baya. Fuska a ɗaure tamau kamar bai taɓa sanin wata aba wai ita dariya ba.
"Saboda na ce baza ki koma can ɓangaren bane kika haɗa ni da mahaifiyata? Yaushe muka fara haka a tsakaninmu?"
Kafin ta ce komai hawayen idanunta ne suka samu damar gangarowa, saukar hawayen da yayi daidai da ɗan matsawar wannan malolon da ya tokare mata maƙoshi. Ta haɗiyi wani kakkauran miyau, da rawar murya ta fara magana
"Wallahi, Tallahi, na Rantse da girm..."
"Akan ƙarya za ki rantse min?"
Ya katse a zafafe yana matsowa kusa da ita kamar zai kikkifa mata mari.
Da saurin gaske taja da baya, zuciyarta cike da wani irin bala'in tsoronsa. Tunda suka yi aure duk bala'insa bai taɓa dukanta ba, ba ta fatan ya fara daga yau.
"Saurareni ki ji da kyau! Don kin samu goyon bayan Hajiyarmu ta amincewa komawarki wancan ɓangaren ba shi zai sa in fasa auren Fatima ba.
Zan auro Fatima a matsayin matar aure na. Aminyarki ta ƙud da ƙud, wacce duk wani sirrinki na fili da ɓoyo a tafin hannunta yake.
Bari in faɗa miki abinda tun fara neman auren nan nawa ban faɗa miki ba.
Zan auro Fatima ne don kawai inga faɗuwarki Fareeda. Kin daɗe kina guma min takaici, kin daɗe kina ƙunsa min baƙin ciki, kin ɗauki lokaci mai tsawo kina gasa min ɗanyar gyaɗa a hannu ta hanyar ƙona min zuciya kina tsallake umarnina a matakai mabanbanta.
A yanzu lokacina ne. Lokacin da a sannu a hankali zan ɗauki fansar duk irin abubuwan da kika daɗe kina yi min. Kina ji kina gani wacce take zuga ki ta mayar da ke sakarya tana ƙara izaki wajen ƙetare umarnin mijinki.
Za ta shigo gidanki a matsayin matar mijinki. Za ta yi masa biyayya akan abinda ke kika kasa dannar zuciyarki wajen yi ma mijinki biyayya.
Za tayi amfani da sirrukanki da ta sani wajen rugurguza tubalin da kika daɗe kina ginawa..."
"Mukhtar !!! Ta katse shi ta hanyar ƙwalla kiran sunanshi. Mugayen baƙaƙen maganganunsa nema suke su saka zuciyarta mummunar bugawa.
Tunda ya fara maganganun wasu zafafan hawaye suke tsere a fuskarta. Idanunta sun kaɗa sunyi jajur, lokaci ɗaya fuskarta ta damalmale ta canja kamanni.
Ta ja shessheƙar kuka mai ƙarfi, ta sanya hannu biyu ta fara goge hawayen fuskarta da sauri, amma sam sun ƙi daina zubowa.
Ita da kanta ta bada tazara tsakaninta da shi, a yanzu da kanta ta fara haɗe tazarar da yake tsakaninta da shi, tana kallonsa da manyan idanunta da suke ta wani irin rawa rawa saboda kuka, sai wani irin numfarfashi take ja mai tafe da shessheƙar kuka sauri-sauri. Laɓɓan bakinta sai rawa suke yi, gwanin ban tausayi.
"Fatima ko Mukhtar? Ina sake maimaita maka ga ta ga ka nan! Ni Fareeda Allah ya sani, kuma yana ganin zuciyata, duk ku biyun da zuciya ɗaya nake zaune da ku.
Kuma ko da kuke shirin yin aure dai dai da sakan ɗaya ban taɓa yi muku wani fata saɓanin ta alkhairi ba.
Amma na lura duk ku biyun nema kuke ku hallakani. To ina so ku sani, wannan saƙo ne zan faɗa maka ka isar ma ita gimbiyar taka.
Ni Fareeda in Allah ya yarda ba dai mutum ba sai dai Allah. Alhaji Abdullahi Bawa kafin rasuwarsa hannayen mu ƴaƴansa gaba ɗaya ya dafa ya ce ƴaƴana, in Allah ya yarda a duniya baza ku taɓa taɓewa ba.
Hajiya Hajara Usman tana gargarar mutuwa da alƙur'ani a hannuna ina karanta mata suratul Yaseen, ta shafo kumatuna da tattausan murmushi a fuskarta ta ce Fareeda, idan anyi duniya don Manzon Allah SAW maƙiya sai dai su bi bayanki. Maƙiya su bi bayan Fareeda, Ya Allah ga Fareeda, ina roƙon maƙiya su bi bayanta.
Ta ƙara da cewa Ubangiji duk wanda zai so ganin bayan Fareeda da ƴan'uwanta Allah kasa sai dai su suga bayanshi. Ina damƙe da Alƙur'ani a hannun dama, hannuna na hagu na cikin nata na dama. Daga wannan maganar numfashi biyar ta ƙara ja mala'ikan mutuwa ya zare ranta.
Da waɗannan kyawawan addu'o'in na iyaye da hadithi ingantacce ya tabbatar da cewa yardarsu tana tare da yardar Allah kake tunanin za ku iya cin galaba a kaina?"
Sai ta saki wani tattausam murmushi da ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarta. Tana kallon yadda ya tsaya wani sagalau da baki yana kallonta, da wani irin yanayi mai kama da na mamakin ƙarfin halinta. Bata damu ba ta cigaba da cewa
"Mukhtar tunda ba don Allah kake shirin auren Fatima ba, ba baki zanyi maka ba. Amma idan baka tsarkake niyyarka ba ko rantsuwa nayi babu kaffara tafiyar taku babu nisan da za tayi, idan kuma za tayi nisan za tayi ne duk ku biyun kuna cikin fige kazar wahalar da Rabbi zai yanka muku.
Amma har yanzu kana da sauran dama, lokaci bai ƙure maka ba. Ka koma ka gyara Tubalin ginin ƙarin aurenka, idan ka cigaba da tafiya kan wannan TUBALIN tokar lallai... Hmmm! Allah ya kiyaye."
Da sassarfa ta shige ɗaki ta barshi tsaye a gurin.
Wani dogon tsaki yaja, duk waɗannan dogayen maganganun nata sam ko kaɗan basu girgiza zuciyarsa ba. Sai ma wani dogon tsaki yaja zuciyarsa cike da takaicin wannan girman kai da jiji dakai da bala'in bakin na Fareeda.
Ita a rayuwarta babu wani magana da zai saka jikinta yayi sanyi? Duk bala'insa ba ta tsoronsa, wai idan yana magana bakinta ya mutu? A'a ba dai Fareeda ba.
Idan tayi mishi shiru ya san tayi shiru ne kawai ba don tsoro ko bata da abin cewa ba. Yayi ƙwafa mai ƙarfi yana cije gefen baki, ya girgiza kai yana fitar da wani zazzafan huci daga bakinsa.
"Hmmm! Na san maganinki Fareeda. Za kiyi laushi, dolenki za kiyi laushi. A sannu zan dafa ki ki dahu luguf, ba dai mace kike ba? Za ki gane duk zafin kanki dole kiyi laushi ƙarƙashin ɗa namiji."
A fusace ya banke ƙofar ɗakinsa ya faɗa ciki, banɗaki ya nufa kai tsaye ya fara watsa ruwa a gurguje. Dole yaje gurin Fatima a darennan, ya kamata ya sanar da ita an samu canjin tsari, tun kafin ta lodo kayyakin gadon ɗakuna uku cif gara ya faɗa mata ta sai na ɗakuna biyu ne.
Ba tare da tunanin a banɗaki yake ba a karo na barkatai ya sake jan tsaki. Tun kwanaki sun gama tsarawa ɗakuna ukun ɗaya nashi ne, ɗaya nata, ɗaya kuma na ƴaƴan da za su haifa.
Har kimanin kuɗaɗen gadajen da za ta siya ta sanar da shi, wani abu kuma da ya ƙara faranta mishi rai shi ne, gadon da za ta saka mishi a ɗakinshi ya fi nata da na ƴaƴansu masu zuwa tsada.
"Ina son ki Fateena"
Ya faɗa a fili cikin wani irin shauƙi na soyayya, har yana lumshe idanunsa.
*******
"Aban twince saurara don Allah! Ban... fahimce ka ba? Wai kana so ka ce min ginin da ka gama gyara min har aka auna
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 26