ta maka ma Fareeda da ƴaƴanta ba.
Daƙyar ta iya danne zuciyarta ta shige banɗaki tayi alwala. A gurguje tai salla ta sabunta kwalliyarta ta ƙame akan kujera tana jiran dawowarsa.
Yau ranarta ce, lokacin gaba ɗaya nata ne. Ko kaɗan ba ta son tayi abinda zai janyo ɓacin rai tsakaninta da Haskenta.
Ko da ya dawo daga masallaci bai shiga gurinta ba, sai tashin motarsa taji alamun zai fita daga gidan. Da gudu ta leƙa ta window sai bayan motarsa ta gani yana gaf da fita.
Turus tayi a tsaye, zuciyarta cike da tunanin ina kuma za shi a wannan lokacin da ya kamata ace tana zaune a cinyarsa suna ciyayyar abinci a tsakaninsu?
A sanyaye taja ƙafafunta ta koma kan kujera ta zauna, ta zuba tagumi da hannu bibiyu, zuciyarta danƙare da saƙe-saƙe mabanbanta.
Minti talatin da fitarsa ya dawo gidan. Ko da ya shiga har lokacin tana zaune inda take, ta amsa sallamar da yayi a sanyaye.
"Barka da zuwa"
"Yauwa!"
Ya amsa haɗe da miƙa mata ledar hannunsa. Ya ƙara da cewa
"Ga alƙawarinki na cika. Rabin kazar amarcin da kike bi na..."
"Haba Haskenah, wallahi da ma baka wahal da kanka gurin siyowa ba. Ai ka fi ƙarfin kaza a guri na."
Ta ƙarasa maganar haɗe da kaɗa ƙwayoyin idanunta cikin salo tayi wani farrrr da su.
Sai da yayi dariya sosai sannan ya ce
"Kar ki damu. Ki ci kawai, hakkinki ne a al'adance matsayinki na Amarya. Ina dai ƙara roƙon afuwa kan jinkirin da nayi gurin cika wannan al'ada."
Martanin dariyarsa ta mayar mishi sannan ta shige kicin ledar na riƙe a hannunta.
A faranti ɗaya ta juye naman kazar, ta sako cokula masu yatsu guda biyu ta fito tana rangwaɗa ta ƙarasa kusa da shi ta zauna a kujerar da ke gefensa.
"Bismillah Haskenah! Jin daɗin cin kazar amarci a ci shi tare da ango, daga nan ko me zai biyo baya zai taho ne a marmarce kuma cike da armashi. Ko ba haka ba Aban Twince nawa?"
"Wannan haka yake Amaryata"
Ya amsa yana dariya.
Tare suka ci naman kamar yadda ta buƙata, ta zubo musu abinci a faranti ɗaya suka ci tare. Duk da ɗarewa kan cinyarsa bai samu ba soisai ta ji daɗin yanayin da suka kasance ita da shi.
Saboda tsananin shauƙi har bai san ji sadda aka kira sallar isha'i ba, sai ji yayi ana raka'ar ƙarshe. Ko kafin yayi alwala ya fice har an idar da sallar. Anan cikin falonta yayi sallar yana jin babu daɗi na rashin jam'in da bai samu ba.
****
Bai manta yadda ya tarar da Fatima a darensu na farko ba. Amma saboda yana so ya share ma kanshi tantamar ko ba shi da lafiya ne shi yasa tana fara tayawa ya amshi gayyatarta da gaggawa.
Wani irin salo ne taje mishi da shi cikin ƙanƙanin lokaci ta birkita shi, sosai jikinsa yake karɓar saƙonnin da take aika mishi.
Wani abin ban mamaki a gare shi, wani abin tsoro da firgici, wani abin tunani a gare shi shi ne yadda ya iya ratsa gonar Fatima ba tare da fuskantar matsala makamanciyar wacce ya fuskanta tsakaninshi da Fareeda ba.
Bayan kammaluwar komai gefe ya matsa a wahalce yana sassauke ajiyar zuciya. Ita dai Fatima har yanzu matsalar jiya na nan a jikinta, bai saba jin irin haka a jikin Fareeda ba, gaskiya bazai iya ba. Gara tun da wuri ya sanar da ita idan ma wani magani take amfani da shi da yake sakata bushewa ta daina, shi ba ya jin daɗi, ko kusa ba ya jin wani armashi a karo biyun da suka yi. Har ta fara barci ya tashe ta.
"Haskenah? Ya aka yi? Akwai wata matsala ce?"
Ta tambayeshi tana mutsutsuke idanunta.
"Fatima, in faɗa miki gaskiya ko in ƙyale ki cikin duhu?"
"Faɗa min Haskenah, don Allah faɗa min. Allah yasa dai ba wani laifi nayi maka ba. Idan nayi laifi ne don girman Allah kayi haƙuri ka yafe min, da alkhairai nake nufinka a zamanmu ba na so muna yawan samun saɓanin fahimta..."
"Dakata Fatima. Ni ban ce kinyi min laifi ba."
Ya katse ta. Sai kuma yayi shiru ya haɗiye miyau sau ɗaya.
"Fatima. Ni fa gaskiya a yadda nake tarar da ke ɗinnan ba na jin daɗi."
Ba tare da wani alkunya ko karantawa ba ya faɗa mata yadda yake jin ta a bushe ƙamas.
"Don haka idan ma wani magani kike amfani da shi da ya mayar da ke haka ina baki shawarar ki daina. Don wallahi ni bazan iya jurewa ba, shi yasa kika ga ko a wancan kwanakin na amarci tun daga sau ɗaya ban ƙara yunƙurin cewa zan wani taɓa ki ba."
Yana gama maganar ya faɗa banɗaki, ba tare da ya saurari ko za ta mishi wani ƙarin bayani ba.
Hankalin Fatima a tashe ta saka kuka ƙasa-ƙasa, wani iri take jin jikinta gaba ɗaya, irin a muzancen nan. Anya a duniya akwai abinda ya fi wannan ban takaici da baƙin ciki? miji ya ƙeƙashe idanunsa ba tare da jin kunya ko karantawa ba ya faɗa ma matarsa ba ya jin daɗinta a ɓangaren auratayya?
A wannan dare ta ci kuka har ta gode Allah! Barcinta raba da rabi ne, zuciyarta cike da tunanin hanyar da za ta bi don magance wannan matsalar da gaggawa. Ashe shi yasa ko irin ɗokinnan na amare Mukhtar ba ya nuna mata? To menene amfani duk magungunan da ta siya ta hannun Ramlah da sauran masu magungunan mata? Duk sun tashi a banza kenan? Yaudararta suka yi ta ɓarnata dubban kuɗaɗenta a banza ko kuwa ita ce magungunan basuyi aiki a jikinta ba.
Shi dai Mukhtar juya mata baya yayi yashaa barcinsa hankali kwance, cikin nutsuwa. Domin ya gama sakankancewa a zuciyarsa tunda ya samu nasarar ratsawa ta gonar Fatima, tabbas babu wani abu da zai hana shi samun kyakkyawan mu'amala tsakaninshi da Fareeda.
Washe gari da wuri ya shirya ya fice, a gurguje ya leƙa Fareeda ya duba lafiyarta da yara sannan ya fice daga gidan. Gurin aikinsa ya nufa, hutun sati ɗaya aka bashi don cin amarci. Tun jiya Ogansu ya kira shi ya jaddada mishi lallai yau ya zo Ofis akwai wasu takardu da ake buƙatar ya duba ya saka musu hannu, da gaggawa ake buƙatarsu bazai yiwu a jira zuwanshi jibi da hutunsa zai ƙare ba.
Ko wanka bata yi ba ta ɗaga waya hankalinta a tashe ta kira wata makwafciyarta da suka yi zaman mutunci da amana mai suna Aunty Ladidi.
Aunty Ladidi irin matannan ne masu tsage gaskiya komai ɗacinta. Duk yadda take aminci da ke ko take ƙaruwa da ke ba ta jin kunya ko tsoron ta wanke ki tas idan taga kina neman kauce hanya.
Ko a batun aurenta da Mukhtar har gida Aunty Ladidi ta bi ta tayi mata wankin babban bargo, ƙal tayi mata sannan ta bar gidan. Ko a yanzu ta yanke shawarar neman Aunty Ladidin ne saboda ta san ita ɗin idon gari ne, tana da mutane sosai. Kuma tana sana'ar haɗa magungunan mata ingantattu waɗanda take haɗawa da hannunta, dangin kayayyakin ciye-ciyenmu da ganyayyaki masu amfani a jikinmu mata
*Yau ne fa da misalin ƙarfe goma sha biyu daidai na dare Zee Maman Mujaheed za ta rufe garaɓasar siyan maganin a sauƙaƙe. Kin siya kuwa? A baya tana sayar da maganin 4k ne. A yanzu ta sauƙaƙa shi zuwa 2k.* Ƴar'uwa me kike jira? Maganin nata ya samu shaidar aiki ingantacce kuma da gaugawa ake ganin biyan buƙata in sha Allah. Idan kina fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin ina mai baki shawara kiyi gaugawar siyan maganin Zee Maman Mujaheed👇🏽
Ciwon gabobi, ciwon mara, fitar farin ruwa, kaikayi gaba, rashin Sha'awa, rashin kuzari gare ki ko ga namiji, rashin ni'ima, rashin haihuwa, kurajen jiki ko na gaba, jin Zafi yayin saduwa. Maganinta cikin sauƙi kuma a gaggauce yake magance duk waɗannan matsalolin. Ki tura kudin maganin ta wannan account ɗin da ke ƙasa, sai ki tura mata shaidar biya da garin da kike ta lambar wayarta👉🏽0 816 285 9027 Ga kuma acc ɗinta👇🏽
3968303018
Zainab Shu aibu
Fcmb
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*23*_
*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
Cikin kuka mai bayyana tana cikin masifar tashin hankali take roƙon Aunty Ladidi a waya don girman Allah ta taimaka mata, tazo gidanta da gaggawa a safiyarnan, tana cikin wani gagarumin bala'i ne da idan ba Aunty Ladidin ba babu wacce za ta iya fitar da ita a cikin wannan halin.
"Allah ya raba mu da bala'i"
Aunty Ladidi ta faɗa cikin rashin damuwa da irin kukan da Fatima take yi.
Daƙyar Fatima ta iya tsagaita kukan ta amsa da
"Ameen"
Ladidi ta gyara zama ta cigaba da cewa
"Maman Ummee (Inkiyar da suke ma Fatima da sunan ƴarta ta farko) a halin yanzu gaskiya bazan iya sakin ayyukan da nake yi in taho gidanki ba. Ah toh iya zallar gaskiyar magana kenan, bazan yi ƙarya don ki so ni ba.
Amma idan kin ga matsalar za ta faɗu ta waya ki faɗa min, ina saurarenki. Idan kuma baza ta faɗu ba to ki jira ko zuwa nan da sati mai zuwa, kila in samu sararin leƙowa."
Katse kiran tayi ta saka katin dubu ɗaya ta banki cikin ragowar kuɗin da suka rage mata, sannan ta sake kiran lambar Aunty Ladidi. Ba tare da ɓata lokaci ba ta zayyane mata irin matsalolin da take ciki ita da Mukhtar, tana maganar tana kuka. Idan ta tuna yadda ƙeƙe da ƙeƙe cikin dare ya iya sanar da ita yadda take sai taji zafafan hawaye sun sake ɓalle mata, zuciyarta sai wani irin suya da ƙuna take mata kamar ana babbakata ta ciki.
"Ashsha! Eh lallai Maman Ummee dole kiyi kuka. Miji ya fito ɓaro-ɓaro ya faɗa miki irin wannan magana dole hankalinki ya tashi afujajan ki fara neman mafita.
Amma na ce ba? Kin sha magungunan sanyi kafin ayi biki kuwa? Kin san shi ne babban ciwon da ke janyo matsala makamantan naki da wasu waɗanda suka fi naki. Kamar su ƙaiƙayin gaba, rashin sha'awa, jin zafi lokacin mu'amalar auratayya, rashin kuzari, ke ciwon sanyi har hana haihuwa yake yi. Kin sha maganin sanyi?"
"A'a!"
Ta amsa muryarta na fita da ƙyar! Ta ƙara da cewa
"Amma magungunan mata babu kalar wanda ban sha ba..."
"Shirme kika yi kenan! Ta yaya ga sanyi danƙare a jikinki za ki tsaya ɓarnata kuɗaɗenki a magungunan mata? Baza su taɓa yi miki aiki ba, dama maganin sanyin kika yi ko baki sha maganin mata ba in dai kin dace da maganin sanyi mai kyau ni'imarki da Allah ya halicceki da ita za ta dawo taf! Maganin mata ana sha ne kawai don bahaushe ya ce ko kana da kyau ka ƙara da wanka..."
"Yanzu ya zanyi Aunty? Don Allah ki taimaka min."
Tayi maganar cikin marairaita da rawar murya.
"Eh to akwai yadda za kiyi mana. Amma fa in kina da kuɗi. Shi ciwon sanyi da kike gani balaƴaƴƴen ciwo ne da idan ba dace kika yi da magani ba sai dai kiyi ta wahala. Kuma an fi dacewa da maganinsa a ɓangaren magungunan gargajiya, na asibiti sai tsananin sa'a za ki rabu da ciwon gaba ɗaya. Amma na gargajiya idan Allah ya taimakeki kika yi dace da ingantaccen magani kamar na Zee Maman Mujaheed cikin ƙanƙanin lokaci za kiga biyan buƙata..."
"Wacece ita? Aunty Ladidi ina son maganin, a ina take? Nawa ne kuɗin maganin? Wallahi ko nawa ne zan siya in dai zan samu waraka daga wannan matsala."
"Don waraka fa za ki samu da yaddar Allah! Mata da ɗunbin yawa sunyi amfani da maganinta kuma sun ga biyan buƙata. Kuma wani abin armashin shi ne sam maganinta babu tsada, galan dubu huɗu ne. Nima ba ta hannuna za ki sayi maganin ba, akwai wata ƙawar ƙanwata da take sayar da ingantaccen haɗin gyaran nono da cikowarsa ita naga ana kawo ma maganin masu siye anan kaduna suna karɓa a gurinta. Ita Zee Maman Mujaheed ɗin a katsina take, amma duk sa'adda kika yi magana kina son maganinta a cikin yinin ko washe gari saƙonki zai iske ki har garin da kike zaune."
"Maganin cikowar nono?"
Fatima ta tambaya cikin zakwaɗi, zuciyarta cike da tunanin yadda a fili Mukhtar yake tattaro suɗaɗɗun silifas ɗinta yana yamutsawa babu shauƙi ko kaɗan a tare da shi.
"Shi ma maganin nonon ina so. Nawa take sayarwa?"
"Dubu biyu da ɗari biyar ne ɗan ƙaramin bokiti. Kuma wallahi ina mai baki tabbacin maganin nonon da za ki siya gurin Farida ba nono kaɗai zai gyara miki ba, har ni'ima yana ƙara ma mace saboda nagartaccen haɗi take yi ba irin na ƴan kuci ku bamu ba. Bayan ni'ima zai sa jikinki yayi kyau, ki murmure, fatarki tayi ta sheƙi saboda kunun da kike sha na maganin..."
Jikinta a sanyaye jin sunan mai maganin ta ce
"Sunan mai maganin Farida? A ina take ?"
"Kinkinau, ta gurin masallacin musabaƙa."
Kamar baza ta siya ba, jin sunan mai maganin ɗaya da na kishiyarta da ta tsaya mata a ƙahon zuci. Sai kuma wata zuciyar ta umarceta da ta siya, ai ba gurin kishiyar bace balle a ce tayi abin kunya. Kuma Fareeda nawa ne a duniyarnan?
"Ina son maganin Infection ɗin galan biyu. Shi ma maganin nono ina son roba biyu. Amma zan samu da wuri ko Aunty? Idan da so samu ne a kawo min tun yau in fara amfani da su."
"Kar ki damu. In dai kina da kuɗi a ƙasa za ki samu magunguna akan lokaci. Bari in kira Farida in ji yadda za kuyi."
Bayan minti goma sha biyar Aunty Ladidi ta tura mata lambobin waya guda biyu, da bayani kamar haka.
"Ga lambobin masu sayar da magungunan ki kira su, za su baki acc no ki tura musu kuɗi za su faɗa miki lokacin da saƙo zai iske ki 09077591726👈🏽Farida Maganin nono. 0816 285 9027👈🏽 Zee maganin infection."
Akan gwuiwa take, don haka babu ɓata lokaci ta kira lambobin. Sosai ta saki jiki ta faɗa ma matan biyu halin da take ciki, saboda Farida da Zainab mata ne da suka iya kasuwanci, sun iya tafi da jama'a cikin haba-haba da fara'a.
Shawarwari sosai suka bata na yadda ko bayan tayi amfani da magungunan za ta kiyaye kamuwa da makamantan matsalolin in dai ba wata muguwar ƙaddara ba da ba'a fata. Sannan suka faɗa mata yadda za tayi amfani da maganin, kuma sai washe gari za'a kai mata maganin. Ita za ta biya kuɗin delivery.
Acc no suka tura mata ta saka musu kuɗaɗen siyayyar da za tayi. Yinin wannan rana haka ta ƙarasa shi cikin ƙunci da damuwa. Ko abincin rana sai gaf da la'asar ta samu ta dafa jallof ɗin taliya.
Bata ji kashaidin da Mukhtar yayi mata jiya ba, haka ta sake zuba ɗan cukul a kula tana zubawa tana ƙunci, ita wannan tsarin na yin girki ɗaya sam baiyi mata ba. Don dai kawai ba ta da yadda za tayi ne.
Tun safe ko wanka bata samu sararin yi ba, a taƙaice ma babu aikin da tayi a ɓangarenta. Tana kwance tana tufka da warwara, wani lokacin kuma ta cigaba da saƙa da mugun zare kamar yadda ta saba.
Gyale ta ɗauka ta yafa kan kayan barcin jikinta ta fice da kular abincin a hannunta, fuskarnan a ɗaure tamau. Ta nufi ɓangaren Fareeda tana tafiyar laƙaiƙaita za tayi baza tayi ba.
Tun daga nesa ta hangi Fareeda zaune akan kujeran roba a ƙofarta, daga ɗan nesa kaɗan kuma almajirin da yake yi mata wanki ne, ga kaya nan a gabanshi ya duƙa yana wankewa.
Ko da ta isa ƙofar Fareeda maimakon a mutunce tayi mata sallama, ko baza su gaisa ba ta ajiye mata abincin, sai kawai ta ƙarasa gurin almajirin kai tsaye. Sunan yaron Yusuf, ta san shi yake yi ma Fareeda wanki tun da daɗewa, a wasu lokutanma har ita tana kwaso kayan wanki daga gidanta ta kawo ma Yusuf ɗin ya wanke mata anan gidan Fareeda.
A fili ta kalli Fareeda ta galla mata harara. Irin yadda Fareedar tayi kyau cikin sakakken doguwar rigar jikinta shi ne abinda ya ƙara ƙuntata zuciyarta. Har baiken kanta ta gani, me yasa bata tsaya tayi wanka ta sha uban kwalliya kafin ta fito kawo abincin ba?
Taja dogon tsaki kamar bakinta zai taɓi ƙasa. Ta kalli almajirin ta ce
"Yusuf sannu da aiki. Karɓi wannan abincin ka miƙa ma wancan matar."
Ta ƙarasa maganar tana nuna Fareeda a wulaƙance da yatsarta manuniya.
Tun isarta gurin, Fareeda tana kallonta. Tana kallon yadda take ta wani kallon komai a wulakance, tana kallon yadda ta galla mata harara, amma sai tayi kamar bata gani ba.
Tana jin yadda ta ja mata tsaki amma duk ta basar, kamar bata san da wanzuwar Fatima a gurin ba. Fuskarta yana kan wayarta da take dannawa a hankali, lokaci bayan lokaci ita kaɗai sai ta saki murmushi.
Karaf maganar da Fatima tayi ya faɗa cikin kunnenta, wani ƙayataccen murmushi ta sake yi. Ta ƙasan idanunta take kallon yadda almajirin ya duƙa har ƙasa ya gaishe da Fatiman, sannan ya karɓi kular abincin ya nufo gurinta da shi.
"Yusuf ka faɗa mata ta sake abincin yanzunnan ta baka kular ka miƙo min. Sannan sabbin kulolina na jiya da Haskenah ya kai mata abinci ta baka ka kawo min, tunda ba uwar mace ta siya min ba."
Fatima ta faɗa cikin tsiwa da masifa.
Duk da ranta ya ɓaci da jin zagin da tayi mata a fakaice, ko kaɗan bata nuna a fuskarta ba. Kanta yana ƙasa tana cigaba da shafa fuskar wayarta, duk da izuwa lokacin ta daina fahimtar rubutun da take karantawa a fuskar wayar.
Idan akwai wani abu da Fareeda tayi matuƙar ƙwarewa akai shi ne ɓoye ɓacin ranta. Bata iya riƙe baƙin ciki a zuciyarta ba, amma idan ba ita ta so ba duk yadda za ka so ka ɓata mata rai ko ta ji haushi baza ta taɓa nuna maka ba.
Har wannan lokacin murmushin fuskarta duk da ya koma na yaƙe ne bata bari ya ɓace ba.
Yusuf na isa gurinta ya duƙa har ƙasa ya ajiye kular a gabanta, kusa da ƙafafunta, a ladafce ya ce
"Aunty wai ga shi, ki sake ki bata kular da kulolin jiya."
Irin yadda Fareeda ta janye ƙafafunta a ƙyamace daga jikin kular abincin da almajirin ya ajiye shi ne abinda ya fara dukan zuciyar Fatima. Bata gama farfaɗewa daga wannan takaicin ba ta ji Fareeda ta kira Yusuf da har ya miƙe zai koma kan aikin da yake yi.
"Buɗe kular mu ga jagwalgwalon da ke ciki."
Fareeda ta umarci Yusuf.
Babu musu kuwa ya tsuguna da hannunsa duk kumfa ya kama murza murfin kular, daƙyar ya buɗe saboda santsin hannayensa.
Taliya ce dafa duka ta manja, da yake a gurguje aka dafa ta sai bata wani ji kayan haɗi ba, kuma sa'adda ta gama dafawar ba'a lokacin aka kawo ba sai ta wani irin sanƙarewa a cikin kular babu ko armashin kallo a idanu.
Fatima tana kallon yadda Fareeda ta kawar da kanta da sauri daga kan abincin, ta mele baki gefe ɗaya.
"Yusuf za ka iya ci? idan baza ta ciwu maka ba ɗauko robarka ka sake a ciki, idan ka koma makaranta sai ka ba waɗanda basu samu abinci ba. Wata ƙil su su iya cin wannan busasshiyar taliyar mai kama da ta ƴan fursuna. Idan ka sake ka miƙa mata kular..."
"Aunty sauran kulolin da ta ce ki bata fa?"
"Yusuf ka faɗa mata wanda ya kawo abincin jiya, idan ya dawo shi zai shiga kicin ɗina ya ɗauko ya kai mata."
Tana gama faɗin haka a ƙasaice ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta ɗan zamo gaba kaɗan a kan kujerar da take zaune ta ɗaga wayarta ta cigaba da dannawa.
Fatima tana tsaye ita kaɗai sai huci take kamar kububuwa. Lallai wannan shi ne baki idan ya san abinda zai faɗa bai san abinda za'a mayar mishi ba. Tana kallon yadda almajiri Yusuf ya ɗauko robarsa ya kara saman robar daidai kan sabon kularta da ko Mukhtar bai taɓa cin abinci a ciki ba.
Ya dinga buga kular kan robar saboda taliyar ta fara sanƙarewa, shi kuma so yake ya kifa abincin cikin robarsa ba tare da ya saka hannu a ciki ba, zai iya kai bayan magrib bai koma makaranta ba, baya so ta fara saki.
A ƙoshe yake, tun ɗaya da rabi na rana Fareeda ta shaƙo mishi faranti da indomie da dankalin turawa, an zuba busasshen kifi wadatacce a ciki, duk loma ɗaya biyu sai ya ci karo da kifi. Da ya gama ya kora da ruwan pure water guda biyu, kun san indomie tana da riƙe ciki har yanzu dam yake jin sa.
Daƙyar abincin ya saku kirif a cikin robarsa, bayan kular ta gama shan buguwa da wujijjiga. Bakin kular jage-jage da manja ya rufe da murfin ya ƙarasa ya miƙa ma Fatima.
"Ga shi, an gode Allah ya karɓa."
Ta kasa karɓan kular saboda ɓacin rai, ta kasa amsa addu'arsa don ba tayi niyyar sadaka ba.
Shi kuwa ya ajiye mata nan gabanta a ƙasa ya koma kan aikinsa.
Fatima da ta rasa abinda za tayi ma Fareeda ta huce sai kawai ta cire gyalen da ta rufa da shi taci ɗamara, idanunnan sunyi jajur don ɓacin rai.
Ta buɗe baki za ta fara zuba zallar madaran rashin mutunci na bala'i sai ga Mukhtar ya shigo cikin gidan. Da manyan ledoji biyu riƙe a hannayensa.
"Oyoyo Abee! Da fatan ka dawo lafiya?"
Fareeda ta faɗa tana kallonshi da yalwataccen murmushi a fuskarta.
Martanin murmushinta ya mayar mata. Ya amsa gaisuwarta da kulawa yana tambayarta ya jiki?
Idanunsa na faɗawa cikin na Fatima ya ce
"Ke kuma lafiya kuwa?"
Ganin rigar barcin jikinta shara-shara ga almajiri na tsugune yana wanki a gurin ya saka shi ƙanƙance idanunsa.
"Menene haka? Wani wawancin shiga ne wannan?"
Ya sake mayar da idanunsa kan Fareeda ya ce
"Me yake faruwa anan? Kamar akwai abinda ba daidai ba.."
"Komai lafiya kalau Oga. A huta gajiya. Ni daman zan shiga ciki ne."
Tana gama faɗin haka tsam ta miƙe tsaye, ta nufi ciki hannunta riƙe da wayarta.
Bayanta Mukhtar ya bi. Itama Fatima a fusace ta bi bayanshi zuwa falon Fareeda.
Suna shiga ciki ta zube ƙasa gaban Mukhtar ta saka kuka.
"Haskenah! Menene laifina don na aure ka? Na zaci Aunty Fareeda za tayi haƙuri ta rungumi ƙaddara mu zauna cikin aminci kamar yadda muke a baya..."
"Don Allah saurara! Me yake faruwa?"
Yayi maganar yana kallonta. Sai kuma ya mayar da idanunsa kan Fareeda da taja ta tsaya a tsakiyar falon, ta harɗe hannayenta a ƙirji tana kallon Fatima da wani irin yanayi mai wuyar fassarawa.
A hankali ta sassauta kukan da take yi, ta gyara zama idanunta cikin na Mukhtar, har lokacin hawaye basu daina tsiyaya a idanunta ba.
"Haskenah kai ka saka dokar abincin rana da dare wacce take da girki ita za ta zuba ma mare girki. Yau tun safe yini nayi a kwance ba ni da lafiya, ban samu sauƙin shiga kicin ba sai ɗazu. Kuma ba don kowa na ƙuƙuta nayi girkin ba sai don ita da yaranmu. Kawai ina kawo mata abincin ko buɗewa bata yi ba ta fara saƙa min baƙaƙen maganganu, har tana cewa wa zai iya cin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 26