"Don Allah ka yafe min mijina..."
A sannu ta silale zuwa ƙasa za ta durƙusa kan gwuiwoyinta yayi saurin riƙe kafaɗunta, ya ɗagota tsaye ya rungumeta a jikinsa.
Kamar daman hakan take jira, da saurin gaske ta sa hannayenta biyu suka zagaye bayansa ta ruƙunƙumeshi, tana cigaba da jan shessheƙar kukanta a hankali, da wani irin salo na karyar da zuciyar wadda aka yi ma laifi. Ta sani Mukhtar ɗin yana da faɗa, amma duk masifarsa ba shi da riƙo ko kaɗan, faɗarsa kamar mai hawa da saukar aljanu da yayi suka jirge shi kenan zai koma kamar ba shi ne ya gama zazzage tsiya ba.
Ko yanzu ta tabbatar yana wannan ciccijewar ne don bai samu ya sauke tsiyar da ke cunkushe a cikinsa ba, haƙuri da uzuri akan laifin da aka yi masa ba halinsa bane sam, ko ɗan yaya ne sai ya zazzageta. Da wannan rashin walwalar da ya tsira ita kam gara ya balbaleta da bala'i a wuce gurin.
Ƙananun kitson kanta da suka bayyana saboda hularta da ya faɗi ya shafa da hannunsa na dama, yayi ƙasa ƙasa sosai da muryarsa, faɗan dai da take jira yayi yau ba ya ra'ayi.
"Faree, ina tsananin sonki kin sani. Me yasa baza ki taushi zuciyarki ki bi abinda nake so mu zauna cikin farinciki ba?"
"Wallahi zan bi, na ma bi in Allah ya yarda. Don Allah kayi haƙuri, kayi min faɗa."
Ɗago kanta yayi daga ƙirjinsa yana kallon fuskarta, hawaye ne kaca-kaca, ƴar kwalliyar da akayi mishi duk ta gama ɓaci da hawaye. Ƙayataccen murmushi ya sakar mata, yasa babbar yatsarsa ya fara ɗauke mata hawayen, har lokacin murmushin da yake yi bai bar kan fuskarsa ba.
"Wannan faɗan da kike ta maimaitawa inyi miki yau dai ba na jin yin ta. Ko dole ne?"
Ƙara shagwaɓe fuskarta tayi ta girgiza mishi kai alamar a'a!
"Ki gane wani abu Baby, ba abin arziki bane kusan ko wane lokaci a gidannan inyi ta ɓaɓatu ina maimaita faɗa kan abu ɗaya. Maganar fita unguwa ba tare da izinina ba daga jiya na ɗaukar ma kaina alƙawarin in Allah ya yarda bazan sake miki hargagi na tashin hankali ba. Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba kin sha fita ba tare da izinina ba, na kuma faɗa miki ba na so, in dai faɗa da tashin hankalin miji na sa mata ta daina laifi da tuni kin daina.
Ya kike so inyi miki? wane mataki kike so in ɗauka a kanki? ko so kike in fara bi cikin ƴan'uwanki ina kai ƙararki?"
Ya girgiza kai sannan ya cigaba.
"Baza'ai haka da ni ba in sha Allah! Ni bani da ra'ayin in kai ƙarar matata gurin iyaye ko ƴan'uwanta. Soyayya ta sa na auro ki, wannan soyayyar ita za ta sa in cigaba da haƙurin zama da ke iya yadda zan iya. Amma fa ki sani, ni dai a matsayina na mijinki bazan daina hana ki zuwa unguwa marasa muhimmanci ba, tsarina ne wannan, ra'ayina ne.
Ke kuma ra'ayinki ne kibi dokar da na shimfiɗa miki, idan ba ki so ba kuma ki bi son zuciyarki. Ni kuma duk sadda haƙurina ya gaza zan ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ne da baki taɓa tsammanin zan iya ɗaukar irinsa ba.
Magana ta wuce, don Allah kar mu sake tayar da wannan zancen. Na haƙura, na yafe miki fitar da kika yi jiya, ina roƙon Allah ya yafe miki tsinuwar da mala'iku sukai ta miki jiya tun daga ficewarki a gidannan har zuwa dawowarki."
Jikinta ne yayi sanyi, sanyi kuma sosai. A iya zamantakewarsu basu taɓa zama yayi mata irin waɗannan maganganun masu bala'in kashe jiki da jefata cikin tunani ba.
A hankali ta mayar da kanta a ƙirjinsa ta kwantar, zuciyarta cike da addu'ar Allah ya bata ikon daina fita ba da izininsa ba, Allah ya bata ikon daina aikata duk wasu abubuwa da ta san ba ya so a halayyarta.
"Na gode Mijinah"
Ta faɗa mishi haka da muryarta mai bayyana sanyin da jikinta yayi.
Bata mishi alƙawarin za ta daina satar fita ba, domin ba wannan ne karo na farko da tayi mishi alƙawarin ta daina ba. Amma ta sha alwashin zai gani a ƙasa, za ta daina in sha Allahu, daga jiya in Allah ya yarda baza ta sake ba.
"Wayyoooo... Faree cika ni mana? Yunwa fa nake ji kin sani, na shigo ɗaki kuma kin biyo ni kin ƙwaƙumeni. Ko kema yunwar abinnan kike ji in fara ƙosar da ke kafin in ƙosar da cikina?"
Da saurin gaske ta sake shi tana ɗan dariya haɗe da sunkwui da kanta ƙasa alamun ya bata kunya, ta kasa cewa komai.
Dariyar shi ma yayi, yana son matarsa, ganinta cikin farin ciki ba ƙaramin jefa shi a farin ciki yake yi ba. Ƴar soyayya ce ita, ta san salo-salo na kwantar da hankalin ɗa namiji, a mu'amalarsu ta auratayya tana ba shi ƙololuwar farin ciki, shi yasa ko wane lokaci kishi da soyayyarta yake ƙara ninninkuwa a zuciyarsa. Shi fa bai ƙi ace a duniyarta bata san kowa ba sai shi kaɗai, shi kaɗai yake so ta fuskanta kuma ta sa a gabanta, idan ya ce mata baƙi fari ne ta kalle shi a fari tas tas! Idan kuma ya ce a'a ya zauna a a'a har abada.
"In kawo maka abincin nan ne?"
Ta tambaye shi bayan ta riƙe hannunsa na hagu a cikin na damanta.
"A'a! zan fita falo. Wai da so nake in ɗan watsa ruwa a gurguje ko zan fi jin daɗin cin abincin."
Da sauri ta shige banɗakinsa ta tara masa ruwan ɗumi daidai yanayin zafin da yake so.
Ko da ta koma cikin ɗakin har ya gama shirin shiga wanka.
"Allah yayi miki albarka."
"Ameen mijin Fareeda. Ko inzo in cuɗa maka baya?"
Ta ƙarasa tambayar haɗe da kashe masa ido ɗaya.
"Ina maraba da hakan ƴan matana"
Musayar murmushi suka yi a tsakaninsu, ya damƙi ƙugunta ya riƙe suka fara taku a hankali kamar wasu indiyawa zuwa cikin banɗaki, sai musayar kallon cikin idanun juna suke yi da lallausan murmushi kan fuskokinsu, masana sun ce kallon cikin idanu tsakanin miji da mata yana ƙara danƙon soyayya.
A ƙarshe dai sunyi wanka sun fito, bayan sun ɗauki lokaci mai tsayi suna murje juna da salon soyayya.
A gurguje suka gama shiryawa suka nufi falo, kai tsaye teburin cin abinci suka wuce, cike da girmamawa taja mishi kujera ɗaya daga cikin huɗu da suke gurin ya zauna.
Ita ta ciyar da shi cikin yanayin soyayya yana ci tana kora mishi da sassanyar zoɓo har ya bata tabbacin ya ƙoshi. Ko da ya nemi ya ciyar da ita ɗan kaɗan taci, tashin hankalin da ta shiga a yinin yau ya taka muhimmiyar rawa gurin cunkushe mata cikinta, ba ta jin yunwa sam, kuma ba ta jin cin komai.
Falonsu ya koma ya zauna kan kujera mazaunin mutum uku yana kallon labaran duniya ƙarfe tara. Ita kuma ta tattare kayan abincin ta kai kicin, a daren tayi wanke-wanken kwanonin da suka ɓata, sauran abincin kuma ta adana shi yadda bazai lalace ba.
Har ta kama hanyar fita daga kicin ɗin sai ta koma. Kofi ta ɗauka ta tsiyayi ruwan zafi ta jefa lipton a ciki.
Ta fasa ƙwai guda ɗaya a wani kofin daban ta karkaɗa shi sosai ya tsinke, sannan ta sake ruwan lipton ɗin a ciki ta jujjuya ya haɗe jikinsa. Runtse idanu tayi ta shanye.
Da sauri ta buɗe ɗaya daga cikin durowar kicin ɗin ta ɗauki cingam ƙwara ɗaya ta ɓare ta jefa a bakinta saboda tashin zuciya.
Ita ɗin ba gwanar shan magungunan mata bane, amma duk wani abu da za ta ji an ce natural ne tana ƙoƙarin gwadawa don ta ga ingancinsa. Ƙwai da lipton tun da ta gwada sau ɗaya ta ga yayi mata aiki sosai, da gaugawa yake saukar da ni'ima a jikinta, shi yasa tun da ta riƙe sirrin ba ta wasa da shi.
Can falo ta koma, a gefenshi ta zauna, ta zame ta ɗan kwantar da kanta a kafaɗunsa suka cigaba da kallo.
Basu tashi daga kallon ba sai sha ɗaya da kwata na dare, bayan labaran duniya arewa24 ya maida suka kalli shirin da ake haskawa a daidai wannan lokacin.
Da ganin take-takensa ta san a ɗakinsa za su kwana, don haka ta ba shi uzurin za taje tayi shirin barci a ɗakinta. Kwalbar zumanta mai kyau da yake ajiye a gaban madubi ta ɗauka ta tsiyayi cokali uku ta shi, ta dangwali kaɗan tayi matsi da shi. Yana saurin saukar da ni'ima, ko a bushe kike ƙayau mayau in dai ya karɓeki minti biyu yayi yawa za kiji saukar lema a ƙasa.
Wani irin biyayya da soyayya take sabunta masa a wannan dare, ta faranta masa fiye da yadda yake tsammani, ita ta riƙe linzamin dokin ta barshi yayi sukuwa yadda yake so, ko kaɗan bata nuna gajiyawa ba, sai shi ne ma ya dinga tausaya mata yana shi mata albarka.
*
A iya tsawon kwanaki huɗu da ya ɗauka na hutunsa zama na zallar farin ciki da soyayya ne a tsakaninsu. Har wani suna ya raɗawa kwanakin
"Ranakun sabunta amarci."
Tun ranar litinin ya kamata ya koma gurin aikinsa can kudancin kaduna, amma saboda armashi da daɗin da yake tattare da waɗannan kwanaki ya kira Ogansa yayi ƙaryar ba ya jin daɗi.
Kwanaki biyu aka ƙara masa, bahaushe ya ce daɗinsa da gobe saurin zuwa. Sai ga shi kuwa har ranar tafiyarsa ta zo. Soyayya ruwan zuma, kamar wasu sabbin aure haka Fareeda ta tasa shi gaba da ƴan koke-koke duk inda ya ɗaga kafa nan take mayarwa.
Sai da ya dakatar da duk wasu shirye-shirye da yake yi yayi rarrashi mai dalili, ya kwantar mata da hankali tare da alƙawarin ranar juma'a da wuri zai dawo in Allah ya yarda. Haka dai suka rabu ba tare da zukatansu sun so rabuwa a daidai wannan lokacin ba.
Da gaske ne fa soyayya ba ta tsufa sai dai masoyan su tsufa, ko ɗan kaɗan ne mu dinga ƙoƙarin sabunta soyayyarmu a zukatan mazajenmu.
*******
Tsawon sati uku da suka biyo baya zaman lafiya da ƙaunar juna ne a tsakaninsu. Yau litinin yayi sammakon komawa gurin aiki, tun da ya tafi ta kwanta tana sharɓar barci, wayarta na ajiye a daidai kanta, amma da yake ta rage ƙarar wayar shi yasa aka kira ta har sau biyu bata ji ba, sai a kira na uku ta jiyo ƙarar kamar a mafarki.
A kasalance ta buɗe idanu, miƙa tayi haɗe da salati, ta ɗauki wayar yana daf da tsinkewa. Ƙanwarta Masrura ce take kira
"Hello, Ummu Sultan barka da rana."
"Aunty Fareeda, kina gida ne?"
Ta tambayeta da murya mai baiyana damuwa da rashin walwala.
Ƙirjinta ne ya buga dam! da sauri ta miƙe zaune daga kwance, hankali tashe ta amsa da cewar tana gida, me yake faruwa?
"Tun ɗazu ga mu a asibitin Garkuwa da Aunty Binto, kiyi sauri ki zo, haihuwa ce ta zo mata da gardama, ni da Mustapha tun ɗazu ga mu a asibitin..."
Ƙit wayar ta katse...
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*5*_
Cikin wani irin matsanancin tashin hankali da fargaba ta dira ƙasa daga kan gadon, hannunta na hagu ɗore akai, hannun dama kuma riƙe da wayarta tana bin bayan kiran ƙanwarta, amma sam ya ƙi shiga, amsa ɗaya kwamfuta yake bata, wayar a kashe take.
Sai daga bisani ne tayi tunanin kiran yayansu Mustapha, ta kira shi kuma sau uku wayar tana ringing amma ba'a ɗauka ba.
Hankali tashe ta kira Aunty Murja. A ɗakinsu su Biyar ne, kuma iyayensu sun rasu tun kafin suyi aure, Aunty Binto ce kawai aka aurar da ita kafin rasuwar iyayensu.
Da yake mijin Aunty Binto mai halin dattako ne, shi ya tayata riƙon ƙannenta har zuwa aurar da su. Shi yasa Binta kamar uwa take a gurinsu, ta wahala da su, ba ƙaramin ƙauna da shaƙuwa ke a tsakaninsu ba, da wannan dalilin yasa idan abu ya samu ɗaya ji suke kamar ya samu dukkansu ne.
Hankalinsu bai kwanciya sai an samu maslahar wannan matsalar. Aunty Binto yaran da ta haifa a cikinta biyu ne kacal, wannan cikin shi ne na uku, ta same shi ne a lokacin da ta daɗe da fitar da tsammanin sake haihuwa.
Kuma cikin sai ya zo mata da matsaloli, da farko taita zubar da jini kamar bazai zauna ba, sai kuma Allah yasa cikin ya tsaya bai fita ba, saboda wannan zubar jinin da tai ta yi akai-akai yasa cikin ƙara watanninsa, yanzu cikin yana cikin wata na goma sha uku ne.
Dukkansu cikin zakwaɗin hauhuwar suke, hankalinsu a ƙumba, duk addu'arsu Allah ya sauketa lafiya. Ba'a kwana ɗaya biyu basu kira ta a waya sun ji lafiyarta ba. Ba ƙaramin shiri suke yiwa wannan haihuwa ba, saboda an daɗe ba'a yi ba.
Fatima wacce kakanninsu suke kira da Bintoto ita ce babbansu, sai Aunty Murjanatu, sai Yaya Mustapha, sai Fareeda, da autarsu Masrura.
Irin yadda ta ji muryar Aunty Murja a sanyaye tayi sallama bayan ɗaga wayar shi ne abinda ya ƙara ɗugunzuma hankalinta, a bayan sallamar kuma duk surutu irin na Aunty Murja shiru tayi, bata ce komai ba.
Sai Fareedar ce kiɗime ta ce
"Aunty Murja ya mai jikin? ta haihu kuwa...?"
"Har yanzu dai Fareeda, sai dai mu cigaba da tayata da addu'a, haihuwa ta ƙi zuwa sai uban wahala take sha. Likita ta ce nan da minti arba'in idan bata haihu da kanta ba sai dai ayi mata aiki a cire babyn..."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Tayi salatin jikinta na rawa, kasancewarta mai saurin kuka nan take idanunta suka cicciko da hawaye, babu abinda take tunawa a ranta sai yadda tun farkon samun cikin Aunty Binto ta yanke tsammani da rayuwar duniya, gani take kamar sanadiyyar ajalinta take ɗauke da shi.
"Ba komai, mun dogara ga Allah, za ta haihu lafiya in sha Allahu, kina hanyar zuwa ne asibitin ne?"
Murja ta tambayeta.
"Eh! gani nan zuwa yanzu. Allah ya sauketa lafiya."
Tayi addu'ar da wani irin sanyi a muryarta, lokaci guda hawayen da suke cikin idanunta suka gangaro zuwa kuncinta.
A ɗarare ta nemi gefen kujera ta ɗosana mazaunanta, kamar mai ciwon baya, saboda yadda jiki da hannayenta suke rawa daƙyar ta iya lalubo lambar mijinta ta kira.
Kiran biyu tayi mishi bai ɗaga ba, kafin ta kira na uku sai shi ya biyo bayan nata kiran.
"Paradise"
Ya kirata a tausashe, da ɗaya daga cikin kyawawan sunayen da yake kiranta da su.
Sai da ta ɗan ja shessheƙa sau biyu, sannan a kasalance cikin hawaye ta faɗa mishi abinda yake faruwa.
"Kukan ya isa haka don Allah, kiyi shiru, ki kwantar da hankalinki matata. Kin ji ko? Za ta haihu lafiya in sha Allah. Zan taya ki yi mata addu'a..."
"Hubbyna, don Allah, ka barni in je dubata a asibitin."
Ta ƙarasa maganar a marairaice.
Daga can ɓangarensa ɗif ya ɗauke wuta, kamar tana ganinsa lokaci ɗaya yayi kini-kini da fuska.
"Idan kin je me za kiyi mata a daidai wannan gaɓar da take ciki?"
Ya tambayeta da cusasshiyar murya.
"Duk su Aunty Murja fa suna can, har da Ya Mustapha, ni kaɗai ce ba na nan. Don Allah ka bar ni in je ko fargaba da tashin hankalin da nake ciki zai ragu..."
"Look Fareeda, a daidai wannan lokacin addu'arku ita tafi buƙata. Kuma ko daga ina za ki iya yi mata ya iske ta, su ma su Mustapha suna can ne kawai ba don za su iya sakawa ko hanawa ba. Don haka kiyi haƙuri, babu inda za ki je ayau, idan ta haihu lafiya na yarje miki gobe da misalin 11am ki shirya kije ki duba ta a gida ko asibiti. Faƙat!!!"
Ƙit ya katse wayar, ba tare da ya jira ko za ta sake cewa wani abu ba.
A kiɗime ta ɗaga idanunta ta kalli agogon falon, ƙarfe sha ɗaya da minti hamsin na safe.
Idan ta tuna ya hanata fita, kuma Aunty Binto da take matsayin uwa a gare su ita ce kwance a gadon asibiti, ƙafarta ɗaya a duniya ɗaya a lahira, amma mijinta ya hanata fita. Ƴan'uwanta duk suna can, ita kaɗai ce anan, tana zaune ba tare da sanin halinda ƴar'uwarta take ciki ba.
Kawai sai ta ɗora hannu biyu akai ta fashe da wani balaƴaƴƴen ƙaƙƙarfar kuka, a daidai lokacin kiran Ya Mustapha ya shigo wayarta, sai tayi cilli da wayar kan kujera ta cigaba da rusa ihu, hannu biyu akai, sai bubbuga ƙafafu a ƙasa take yi kamar ƙaramar yarinya.
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Me zan gani haka ni Fatee? Fareeda lafiya? Wa ya rasu?"
Fatima da shigarta gidan kenan ta tarar da ita cikin wannan mawuyacin halin ta jero mata tambayoyin fuskarta na bayyana matsanancin tashin hankali.
A irin yadda ta tarar da ita ta sa a ranta kawai rasuwa aka yi, rasuwar ma irin mai matuƙar muhimmancin nan.
Sai da ƙyar ta samu ta rarrashi Fareeda tayi shiru sannan ta sanar da ita abinda yake faruwa, kafin ta ce komai kicin ɗinta ta wuce ta buɗe frig ta ɗauko gorar ruwa mai matsakaicin sanyi da kofi, falon ta koma ta tsiyayi ruwan ta kafa mata kofin a baki.
Ba ta da zaɓin da ya wuce shan ruwan, sai sauke ajiyar zuciya take yi a jejjere irin na wacce ta daɗe tana kuka.
A gefenta Fatima ta zauna, cikin rashin damuwa ta fara cewa
"Ke kam Fareeda na ga ranar da za kiyi wayau. In banda rashin wayau irin naki ai da bari kikai sai kin isa asibitin sannan ki kira Mukhtar ki faɗa mishi abinda yake faruwa. Kinga a lokacin kin riga kin fice, ko ya ce ki dawo gida kin dai riga kin gano halin da ƴar'uwarki take ciki. Amma ni a ganina ko yanzu bai ɓaci ba, ba kin ce yau ya koma gurin aikinsa ba?"
A kasalance ta ɗaga kai, alamar eh!
"To ga shawara, amma fa idan kina so, kuma idan kin ga dama..."
"Wace shawara ce ƙawata?"
Ta tambayeta cikin zakwaɗi, da tunanin za ta sama mata mafita cikin sauƙi kamar yadda ta saba samar mata a baya.
"Ba kin ce yau Mukhtar ya koma gurin aiki ba?"
"Eh! Ɗazu da safe."
Ta sake amsawa a ƙagauce.
Fari da idanu Fatiman tayi, ta buɗe jakar hannunta ta ɗauki cingam guda ɗaya ta ɓare ta jefa a baki, ta yasar da ledar nan tsakar falon cikin rashin damuwa.
Hannunta da ta yar mata da ledar cingam a tsakar falonta da yake gyare tsaf ta bi da kallo, sannan ta kalli ledar cingam ɗin, ta cuna baki gaba, idan akwai abinda ke yawan shiga tsakaninta da ƙawartata ƙazanta ne, ba ta kiyaye inda ya kamata ta yasar da datti.
Ƙoƙarin danne ɓacin ran da yake yunƙurin taso mata take yi, ta haɗiye miyau sau biyu a jere.
"Kin fara magana kuma kin yi shiru."
Tayi maganar tana kallon yadda take tauna cingam ɗin cakal cakal babu aji ko misƙala zarrah, kamar ba ɗiya mace ba.
"Hajiyata ai kawai ki fice abinki, maganin dai tsinuwar mala'iku kina tafe kiyi ta istigfari. Aunty Binto ta fi ƙarfin komai a gurinku, ba ma kamar ke, ki tuna yadda duk cikinku ta fi shaƙuwa da ke da fifitaki? sau nawa tana ba ki abu ba tare da ta ba sauran ba? Dubiyar mare lafiya za ki je da sadar da zumunci, Allah ma bazai kama ki da laifi ba. Amma fa kar ki daɗe, kiyi sauri ki dawo ɗakinki."
Shiru tayi cikin tunani, a yanayin da take ciki Allah ya sani hankalinta ya fi karkata kan tafiya a bisa zaman. Ta san zance ne kawai na Fatima da ta ce maganin tsinuwar mala'iku istigfari, amma dai ko ba yau ba za ta roƙi mijinta ya yafe mata. Ta san in sha Allahu har za ta fita ta dawo ba tare da ya sani ba, tunda yau ya koma gurin aiki, babu yadda za ayi ya dawo balle har yasan ta fita, za ta je ta dawo lafiya ba tare da ya sani ba, idan ya dawo ko cikin hira ne za ta roƙi ya yafe mata ba tare da ta faɗa masa laifin da tayi ba...
Tana wannan tunanin Fatima ta katse ta da cewa
"Kin ga ni fa daman kasuwa zan tafi siyayya na ce bari in leƙo mu gaisa ko kina da saƙo? kin tuna kuɗinnan da Baban Jiddah ya bamu? ko za ki sayi wani abu a kasuwa? ni kam wata haɗaɗɗiyar doguwar riga na gani a jikin Nabila, irinta zan siyo."
"Taɓ! Ai ni babu abinda zan siya. Kina ganin hidimar kuɗi ya taho min, zagewa zanyi inyi ma Aunty Binto hidima ta bajinta, Allah dai ya sauketa lafiya."
"Ameen ya Allah"
Da haka suka yi sallama, Fatima ta fice daga gidan, ita kuma ta fara shirya tafiya duba ƴar'uwarta a gaggauce, ta rasa dalilin da yasa ƙirjinta ke yawan bugawa akai-akai, amma wannan fita ta riga ta yi niyya, babu abinda zai hana ta zuwa.
Tana kulle ƙofar falonta kiran Mukhtar ya shigo wayarta, ƙirjinta ne ya sake wani ƙaƙƙarfan bugun da yasa ta tsuguna a ƙasa tana jan inna lillahi, daƙyar ta iya daidaita kanta sannan ta ɗaga wayar, da cusasshiyar murya mai bayyana matsananciyar damuwa.
"Matata? ya Auntyn tamu da jiki? kin samu labarin ta haihu kuwa? na kira Mustapha in ji ya mai jikin amma bai daga ba."
"Da sauƙi dai, har yanzu basu kira ni ta haihu ko aikin za'a shiga da ita ba."
Ta jera mishi maganganun a hankali, ƙirjinta na cigaba da bugawa.
"Za ta haihu lafiya da yaddar Allah. Ki kwantar da hankalinki kin ji ko?"
Yayi maganar da kulawa.
"Tam! Allah yasa."
"Kiyi haƙuri Baby, na san kina jin babu daɗi na hana ki zuwa, idan kin duba ko kin je ba abinda za ki iya yi. Ki cigaba da yi mata addu'a daga gida kin ji?"
'Hmmm! Dole ka ce haka tunda ba ƴar'uwarka bace.'
Ta faɗi hakan a zuci, a fili kuma sai ta ce.
"Ba komai, na gode mijina. Allah ya huta gajiyar tafiya.'
"Ameen"
A zahirin gaskiya da wannan wayar da suka yi jikinta yayi sanyi da fitar, kamar ta haƙura ta zauna, amma shaiɗan ya cigaba da azalzala mata kan ta fita. Yana ƙara tunasar da ita muhimmancin yayarta a gare ta. Da saƙa mata wasu tunanika na banza da wofi.
'Ba fata take yi ba, yanzu idan Auntyn ta rasu fa? shi kenan duk ƴan'uwanta sun gana da ita itace basu haɗu ba? saboda wani umarni na namiji da ba shi da tabbas? mijin da za ta iya canza shi amma baza ta iya canza ƴar'uwarta ba'
Kawai sai ta miƙe tsaye, ta kalli jikinta, ɗinkin doguwar rigar atamfa ce, ta yafo babban gyale a kai. Sai ta buɗe ƙofar falon ta shiga cikin ɗakinta ta aje gyalen akan gado ta ɗauki hijabi ta saka. Da sassarfa ta fice daga gidan bayan ta kulle ko ina.
******
"Langes, hanga ta arewacin gabar kaga wata fatsa da take tahowa, idan ba gizo idanuna suke min ba sai naga kamar rangaji take tamkar reshen bishiya a cikin iskar damina."
Da jajayen idanunsa ya waiga zuwa inda abokin nasa yake magana, sai yayi arba da ita, duk da hijabi ne sanye a jikinta bai ɓoye asirin ƙirar jikinta ba, hijabin ya kwanta a jikinta, ƙirjinta ya taso sosai ta gaban hijabin, duk da tashin hankalin da take ciki ba bazar-bazar take tafiya ba, a nutse take tafiya, ga wanda bai santa ba zai iya cewa yanga take yi, amma a zahirin gaskiya haka yanayin tafiyarta yake.
"Kai, gaskiya ni fa na fola, miyau na ya tsinke. Ya kamata in mayar da kwaɗayina ta hanyar ɗanɗanawa..."
"Kai fa Villa ɗan iska ne, ba ka da mutunci, don Allah ka ƙyaleta ta tafi..."
Ko kafin abokin nasa ya rufe baki har ya fita daga cikin napep
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 26