ƙazantaccen jagwalgwalon abinci na? Don ƙarin wulaƙanci a gaba na ko taɓa kular bata yi ba ta ce almajirinta ya sake a robarsa..."
"Me yasa haka Fareeda?"
Ya tambayeta fuskarsa na nuna ko kusa bai ji daɗin abinda Fatima ta faɗa mishi ba.
Ita kuwa Fareeda mamakin ƙarya da munafurcin Fatima ke neman kifar da ita a tsaye. Har wani jiri jiri ne taji yana ƙoƙarin kayar da ita. Daƙyar ta iya ɗaga yatsarta manuniya ta nuna masa agogo, ƙarfe huɗu da minti goma.
"Ni da yara baza mu iya jure har ƙarfe huɗu bamu ci abincin rana ba. Tun da naga ɗaya ta wuce na dafa mana indomie muka ci, ko na karɓi taliyar da ta kawo min ba ci zamu yi ba, shi yasa na ba almajiri. Ka faɗa mata, daga yau girkin rana idan ya wuce ƙarfe biyu ta dafa ita kaɗai kawai, bazan rasa ƴan dabarun da zanyi mu ci ni da ƴaƴana ba."
Bata ƙara tsayuwan minti ɗaya ba ta shige cikin ɗakinta, ta barsu a gurin suna kallon-kallo.
"Yanzu saboda Allah da Annabi ke ko kunyar fitowa a haka baki ji ba? Dube ki fa? Dubi jikinki? a madadin ki saka ƙaton hijabi da zai rufa ma ƙasusuwanki asiri sai ki fito haka ƙozai-ƙozai kamar bulala? Kuma wannan ɗamarar da kika ci ta menene? Dambe kike shirin yi da ita?"
Da sauri ta fara warware ɗamarar da tayi ba tare da ta ce komai ba. Sosai ranta ya ƙara ɓaci, so tayi reshe ya juye da mujiya Mukhtar ya goyi bayanta yayi ma Fareeda gagarumin cin mutunci. Sai ga shi buƙatarta bata biya ba.
"Tashi mu tafi."
Ya bata umarni.
Gyalen da ta warware ta rufa a kanta ta wuce gaba yana biye da ita a baya har zuwa ɓangarenta. Kamar tayi mishi maganar ledojin da ya shigo da su ya bari a falon Fareeda, sai kuma dai taja bakinta ta tsuke.
Nan falonta taja ta tsaya shi kuma ya wuce cikin ɗakinta, sai ga shi ya fito wuf kamar wanda wani abu ya biyo.
"Fatima? Wani irin iskanci ne haka za ki bar shimfiɗa kaca-kaca tun yadda na fita da safe na barshi?"
Ta fara kame-kame ya dakatar da ita ta hanyar daka mata wani gigitaccen tsawa da ya saka ta durƙushe ƙasa tana riƙe cikinta da taji lokaci ɗaya ya ƙulle a guri guda.
"Kin ga, ba na ciki da iskanci da rainin wayau! Kar ki kuskura ki ce za ki kawo min banzar uzurin baki da lafiya. Ƙazanta, shi ne babban abinda zai sa a fara jin kanmu da ke, ba na son ƙazanta ko kaɗan, ba na ƙaunar ƙazama, ko na minti biyar ba na jin zan iya jure zama kusa da wacce na san ba ta da tsafta. Minti ashirin na baki ki tabbatar kin gyara ko ina ƙalƙal. Kina ji na?"
Yayi mata tambayar cikin tsawa.
"Eh! eh! eh na ji. Kayi haƙuri. Zan kiyaye"
Ta amsa bakinta na rawa.
Ficewa yayi daga ɗakin gaba ɗaya ya koma can ɗakin baƙi. Ransa a ɓace, in banda ƙazanta irinna Fatima ko singiletin da ya cire ya aje a gefen gado ta kasa kawar da shi daga gurin balle tayi tunanin wankewa? Da alamun akwai wasu notocin kanta da basu gama ɗauruwa da kyau ba, shi kuwa zai ɗaure mata su gam don ta san shi ba irin sakarkarun mazannan bane da suke jure ƙazanta daga matayensu.
Ko da ta gyara ɗakunan zuwa falo ya leƙa bayan ya dawo sallar magrib babu wani walwala a fuskarsa.
Abincin Fareeda ya ɗauka da yara ya miƙa mata, ya kwaso mata waɗancan kulolin na jiya. Ya dawo ya zauna a falo yana ta daddana wayarsa. Ko abincin da ta jera mishi cewa yayi sai yayi sallar isha'i zai ci.
Haka ta rakuɓe gefe ɗaya, kallo ɗaya za'ayi mata a gane a ɗarare take. Allah Allah take gobe tayi a kawo mata magungunan da ta siya ta fara amfani da su, don ita a ganinta waɗannan matsaloli guda biyu su ne manyan dalilan da suka sa Mukhtar ya juya mata baya a lokacin da ya kamata ace yana tsananin tarairayarta.
Haka suka kwana zuciyoyinsu babu daɗi. Kamar yadda yayi sammakon ficewa gurin aikinsa jiya, yau ma haka ya fice bayan ya karta mata kashidin saura tayi lattin abinci, ko kuma ya dawo ya tarar bata gyara ɗaki ba.
Ƙarfe ɗayan rana aka kira ta a waya, kwatancen gidanta aka tambaya, tana faɗi babu ɓata lokaci cikin minti talatin ɗan saƙo yakai mata magungunanta ta bashi kuɗin mota.
Jiki na rawa ta shige can ƙuryar ɗaki ta kira Farida da Zainab Maman Mujaheed a waya suka yi mata cikakken bayani na yadda za tayi amfani da maganin biyu.
Saboda zaƙuwa tun a wannan lokacin ta fara amfani da su, sai fatan dacewa. Bata yi kuskuren yin lattin abinci kamar jiya ba, ƙarfe biyu saura kwata taje ƙofar Fareeda ta dangwara kuloli biyu a bakin ƙofar sannan ta ƙwanƙwasa ƙofar da ƙarfi sau biyu tai wucewarta, ba tare da damuwar Fareedan ta ji ko bata ji ba.
Inda Allah ya taimaki Fareeda a lokacin suna zaune a falo ita da yaranta. Ta jika musu Conflakes a kofi suna sha, taji wannan ƙwanƙwasa ƙofar.
Ko da taje ta buɗe sai kulolin ta gani. Tsaki taja ta kwashe su tayi ciki, kan dining ta ajiye, tana buɗe babbar kular taga farar taliya, a ƙaramar kuma miyar tarugu ce da aka soya ta ɗanye-ɗanye.
Rufe kular tayi ta koma gurin ƴaƴanta ta cigaba da kallon da take yi.
*****
Da ɗoki sosai a tattare da Mukhtar ya koma ɓangaren Fareeda. Ko a mugun saƙa irinna tunani bai taɓa kawowa a ransa matsala makamancin ta rannan za ta maimaitu tsakaninsa da Fareeda ba. Sai ga shi an kuma, washe gari ma haka aka sake maimaitawa.
Izuwa yanzu sosai lamarin ke bashi tsoro da kaɗa mishi ƴaƴan hanji. Duk tunaninsa ya ƙuƙe ne akan ta yaya za'ayi haka? A gurin Fatima lafiyarsa ƙalau a gurin Fareeda ba lafiya ba.
Me yake faruwa? A ina matsalar take? Ganin Fareeda ko a jikinta bata nuna lamarin ya dameta ba yasa shi kasa sanar da ita a gurin Fatima fa ba ya fuskantar irin wannan matsalar. Kawai sai ya bar zancen a cikinsa, zuciyarsa cike da tunanin wani irin al'amari ne wannan mai sarƙaƙiya?
*_Laifin daɗi aka ce ƙarewa😍😍😍 Promon maganin Sanyi na Zee maman Mujaheed ya ƙare. Yanzu maganin ya koma farashinsa na ainahi wato 4k! Ya ke ƴar'uwata mai karanta labarin RABON AYI, a gurin neman lafiya daga wannan fitannen ciwo na infection da yake damun mata da yawa, ko dubu ɗari kika kashe wajen siyan ingantaccen maganin sanyi bakiyi asara ba. Lafiya ta fi komai a duniyar nan ƴar'uwa👌🏽 sai da lafiyarnan za ki kankaro ma kanki mutunci da daraja a gurin Oga😘. Ki tuntuɓi Maman Mujaheed ta wannan lambar wayar domin sayen naki akan farashi mai rahusa 0816 285 9027_*
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*24*_
*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
Kafin a saukar da ko wace irin cuta, sai da aka fara saukar da maganinta. Sai dai idan bawa baiyi dace da magani ba sai ayi ta wahala, a faɗa cikin ƙunci da ƙaƙanikayi.
Cikin kwanaki biyu da Fatima ta fara amfani da magungunan da ta karɓa babu abinda za ta ce sai godiya ga Allah. Duk da basuyi arangama da Oga Mukhtar ba, ita kanta tana ji a jikinta e lallai fa an samu gagarumin sauyi.
Zo kuga baki har kunne, duk wani ƙunci da baƙin cikin da maganganun Mukhtar suka dasa ma zuciyarta ta kawar da su gefe ɗaya, jira kawai take su gamu yasha mamaki.
Kwanaki shida bayannan ranar girkinta ne. Mukhtar ya waiwayeta ba don tunanin jin daɗi ba sai don kawar da matsuwar da yake ciki, tunda ɓangaren Fareeda dai har lokacin sifili ne.
E lallai fa Mukhtar ya sha mamaki, har ma fiye da yadda Fatima ta so ya kasance. Mukhtar ya amsheta cikin haba-haba da rawar jiki, an kuma an sake kumawa an kuma ƙara kumawa. Ita kanta duk wannan zafi da raɗaɗin da take ji ko kaɗan bata ji ba.
Bayan kammaluwar komai bai juya mata baya ba, kamar yadda ta daɗe tana muradi, ruƙunƙumeta yayi a ƙirjinsa suna sauke ajiyar zuciya. A sannu a hankali kuma wani nannauyar barci yayi awon gaba da su, zuciyar Fatima cike taf da wani irin matsanancin jin daɗi da alfaharin da ko kaɗan bakinta bazai iya baiyanawa ba.
Ita kaɗai ji take kamar tana yawo a sararin samaniya saboda tsabar shauƙin soyayyar Haskenta.
A wannan rana, hatta sallar asubah ita da shi basu samu sararin gabatarwa ba sai ƙarfe bakwai da rabi na safe. Saboda tsabar soyayya ma a tare suka yi wanka, suka ɗauro alwala. Ta bi bayanshi yaja su sallar asubahi.
Yana kishingiɗe akan kujerarta mazaunin mutum uku wani nishaɗi na ratsa zuciyarsa ta kawo musu abin kari. Nan gefenshi ta zauna, ta ɗora kanta a kafaɗarsa suna karyawa cikin wani irin salo da soyayyar da ta ci burin ya faru tun a kwanaki ukun amarcinta, amma ko yanzu ma bai zo a makare ba.
"Fatina"
Mukhtar ya kira ta da sunan soyayyar da tun darenta na farko bai sake faɗa mata ba.
"Na'am Haskenah"
Ta amsa a hankali haɗe da sakar mishi fari da ido. Sai kuma ta ƙalle mishi ido ɗaya ta ƙara da cewa
"Ya aka yi? Ko kana buƙatar ƙari ne?"
Farantin dankalin turawar da ke ajiye a gabansu ya kalla, sai yaga ko rabi basu ci ba. Nan take zuciyarsa ta tunano mishi ƙarin da take magana akai, sai yayi murmushi kawai, ya mayar da fuskarsa kalar zai mata magana mai muhimmanci ya ce
"Wai ni ya aka yi haka ne? A gurin Fareeda fa ba na iya taɓuka komai. Anan ne kawai nake namiji lafiyayye. Ko kin san abinda ke janyo irin wannan matsalar?"
Wani irin tsallen baɗake zuciyarta tayi daga gabas zuwa yamma. Ta zazzaro idanu warwaje tana kallonshi tana jujjuya maganarsa a cikin zuciyarta, sai kuma tayi tsam ta ƙura ma guri ɗaya idanu, banda luguden daka babu abinda ƙirjinta ke yi.
"Kin yi shiru, ki ce wani abu mana. Ni kam na ma kasa tattauna maganar da Fareeda saboda ban san ta inda zan fara faɗa mata anan ina iya kusantarki ita ce ba na iya komai da ita ba."
"Uhmmmmm!"
Taja wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Lokaci ɗaya kuma tayi narai narai da idanunta ta tara ƙwallah. Hannayensa biyu ta riƙo a cikin nata, tayi ƙasa ƙasa da murya sosai da wani irin matsanancin damuwa a fuska da muryarta ta ce.
"Haskenah! Ka roƙi Fareeda, ka roƙe ta. Idan ka damu da rashinta ka roƙe ta, idan ta kama ko durƙusa mata a ƙasa ne ka durƙusa, ka tabbatar mata da cewa aurena da kai ba shi zaisa ka juya mata baya ba. Idan za ka iya ma kayi mata ƙaryar kai fa tunda ka auro ni baka taɓa kusantata ba. Idan ta so, za ta baka maganin ciwonka, daman ita ta ƙirƙiri cutar da gangar ka ga kuwa makarin ciwon na hannunta..."
"Ban... gane..ba. Me kike nufi?"
Ya tambayeta bakinsa na rawa.
Hannayensa ta sake ta zuba tagumi da hannu bibiyu.
"Ta ya zan faɗa maka sirrin da daga ni sai ita sai Allah muka sani? Ko ni da ta san juyin juya hali irinna ƙaddara zai kaimu ga matakin da zan zamo matarka baza ta taɓa faɗa min wannan maganar ba."
Cak ya ɗaga ta daga kan kujera ya ɗaura kan cinyarsa. Ya kamo fuskarta ya riƙe cikin tafin hannayensa. Ya ƙureta da kallon soyayya mai ratsa masoya na tsawon wasu daƙiƙu, sai da ya tabbatar ta nuna luguf, jikinta ya mutu murus, sannan ya fara magana a tausashe, da wata irin siga ta matasan da suka ƙware a soyayya.
"Fatina. Kin san ina bala'in son ki ko?"
Saboda yadda jikinta ya mutu ta kasa buɗe baki ta amsa mishi, sai kai ta iya ɗagawa.
"Ashe a duniya akwai wani sirri da za ki iya ɓoye min? Na zaci ni ɗin abokin sirrintakanki ne? Akwai wani abu ɓoyayye da yake tsakaninmu ne?"
Nan ma dai kai ta iya kaɗa mishi alamun babu.
"To faɗa min! Kin ji ƴar matata? Rabin raina, masoyiyata, abar ƙaunata. Kogin zuma ta..."
Kwantar da kanta tayi a hankali ta fara cewa
"Fareeda, ta taɓa rantse min da girman Allah duk ranar da mijinta yayi gangancin yi mata kishiya za tayi amfani da maganin da bazai ƙara samun damar da zai kusanceta ba.
Kai baka yi mamakin irin kwanaki casa'in casa'in ɗin da tai ta ƙara mana ba? Ta ƙara ne saboda ta san ko ka je can ɗin babu wani abu da za ka samu daga gare ta..."
"Fatima, kar ki faɗa min ƙarya fa"
Ya katse ta muryarsa na bayyana shiga cikin gagarumin tashin hankali. Sai kuma ya sake ɗago fuskarta yana kallon cikin idanunta a rikice.
"Na san ke aminiyarta ce, baza ki ƙirƙiri ƙarya ki faɗa min don kawai kiyi mata sharri ba. Faɗa min gaskiya don Allah, ki ce min wasa kike min. Ta ina Fareeda za ta sami irin wannan maganin?"
"Hmmm! Kana tantama ko? Kai baka yi mamakin yadda duk matsanancin kishi irinna Fareeda ko kaɗan bata tashi hankalinta jin za muyi aure ba? Ka tambayi masana magunguna ka ji, tabbas akwai maganin da mace za ta matsa a al'aurarta daga zaran namiji ya nemi kusantarta zai kwanta ligif."
Tsam ta tashi daga jikinsa ta shige cikin ɗakinta, ta barshi zaune cikin zazzafan tunani.
Hannayensa biyu yasa ya tallabe gemunsa. Ya ƙanƙance idanu ya ƙura ma guri ɗaya idanu tsawon lokacin da shi kanshi bazai ce ga iyakarsa ba.
Tunani yake yi, zuciyarsa cike da ƙila wa ƙala. Ya kasa samun matsaya guda ɗaya. Idan wani sashen na zuciyarsa ya fara kore maganar Fatima, da saurin gaske eani sashen yake ƙara tabbatar masa da gaskiyar zancen, idan ya tuna yadda Fareeda take ta ko in kula da al'amarinsa tun ɓullar zancen zai aure ta har zuwa sa'adda aka yi auren.
Bayan kuma shi kanshi shaida ne kan irin matsanancin kishin da take da shi. Da walakin goro a miya, lallai biri yayi kama da mutum.
Akwai alamun gaskiya dumu-dumu a cikin wannan maganar. Idan ya ƙara tuna ko a yanzu, shi kaɗai yake nuna damuwarsa idan lamarin ya sake maimaituwa. Ko sau ɗaya bazai iya tuna wani lokaci da yaga damuwa a fuskar Fareeda kan lamarin ba.
Karyawan da basu ƙarasa yi ba kenan. Ita tun da ta shige cikin ɗaki bata fito ba, shi kuma da yake ya gama shirin tafiya gurin aiki daga nan bai koma cikin ɗaki ba. Wayarsa da makullin mota ya ɗauka ya fice zuwa ɓangaren Fareeda.
A hanya sai saƙe-saƙe yake yi, ransa ya ɓaci sosai da jin wannan magana da ya gama haƙƙaƙe ma zuciyarsa gaskiya ne. Amma sai yake ta tunanin yai mata magana ko kar yayi mata magana? A ƙarshe dai sai ya yanke shawarar ya zura mata ido yaga iya gudun ruwanta, zai ga cikin su biyun wa zai fi shan wahala da jigatuwa? Shi da yake da wata matar ko kuwa ita da tayi ma kanta sagegeduwa?
Da wannan shawarar yayi ƙoƙarin faɗaɗa fuskarsa da murmushin yaƙe sannan ya buɗe ƙofar ya shiga bayan yayi sallma an amsa mishi daga ciki.
Tana zaune a tsakiyar ƴaƴanta tana biya musu ƙulhuwallahu ahad! Amsawa suke da hausarsu da bata fita tana sake maimaita musu.
Sun yi kwalliyarsu tsaf, gwanin ban sha'awa da burgewa. A guje yaran suka tashi suna mishi oyoyo, bayan ya zauna kan kujera suna jikinsa ta gaishe shi.
Idanunshi na kanta ya amsa, wani irin kallo yake bin ta da shi tun bayan shigowarsa. Kallon da ya jefa ta cikin tsarguwa, har sai da ta ce
"Abee, irin wannan kallo Allah yasa dai ba laifi nayi ba..."
"Uhmmm! Laifi dai Fareeda? Wani labari ne na jiyo da ya ɗaga min hankali."
Ya amsa yana sake ƙure ta da kallo.
"Tooo...! Allah ya kyauta."
Ta amsa fuskarta ɗauke da yanayin jimami.
"Fareeda, wai da gaske saboda kishi mace za ta iya yin abinda zai hana komai ya shiga tsakaninta da mijinta?"
Ya tambayeta.
"Kishi fa ka ce Oga?"
Sai ta ɗanyi murmushi.
"Kishi halitta ce da Ubangiji yayi a cikin zukatanmu. Ko wace mace tana da kishi, sai dai na wata ya fi na wata. Baka taɓa jin labarin matan da saboda matsanancin kishin da suke da shi suna halaka mazajensu sannan su halaka kansu ba? Amma da yake komai na duniya yana da linzami, linzamin baƙin kishi mace ta tsananta addu'a, sai kaga komai ya zo mata da sauƙi. Allah dai ya ƙara sassauta mana."
"Hmmm! Ameen"
Ya amsa a hankali, a zuciyarsa yake ta auna maganganunta, bai hangi komai a ciki ba face ƙara samun gamsuwa da maganar Fatima.
Bai sake wata maganar ba yayi mata sallama ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da mamakin wannan al'amari.
Ita kuwa ko bayan fitarsa bata ɓata lokacinta gurin yin wani tunani ba. Amsa ta bashi da zuciyarta ɗaya ba tare da tunanin da wata a ƙasa ba. Hidimarta ta cigaba da yi ita da ƴan ƴaƴayenta da ko kaɗan ba su da rigima ko ɗaga hankali irinna wasu ƴanbiyun.
*****
Da ƙarfi ta ƙwanƙwasa ƙofar, ta haɗa da buɗe murya ta rafka sallama, fuskarta cike taf da murmushi.
"Alaikissalam! Ina zuwa."
Ta jiyo muryar Fareeda ta amsa daga can ciki.
Sai da ta kintaci ana daf da buɗe ƙofar sai ta buɗe murya ta fara waƙar
"Hooohotihoooo, hotihoooo, hotihoooooo, hotihoooo. Baaaaa ki da amfaniiiiii, sai dai zaman ƴaƴaaaa, ko in ce zaman hoooootihooooo hotihoo."
Da mamaki Fareeda ta ɗaga idanu tana kallon Fatima da har lokacin da ta buɗe ƙofar bata daina rera wannan waƙa da ƙarara yayi kama da habaici ba.
"Lafiya dai ?"
Ta jefa mata tambayar da ɗaurarriyar fuska.
"Hotiho, au Fareeda uwargida. Me kika ce?"
Fatima tayi maganar tana wani irin dariya mai bayyana isgili da tsantsar wulaƙantarwa.
Wani kakkausan kallo Fareeda ta watsa mata, ta mayar da ƙofarta za ta rufe da saurin gaske Fatima tasa hannu ta tare.
"Saurin me kike yi Hajjaju? Abincinki na kawo miki, ki ci, ki sha, kiyi ƙaton kashi. Ko kina da wani amfanin da ya wuce wannan a gidannan Hotiho?"
Wani kakkauran miyau ta haɗiye, ta lumshe idanunta tana addu'a a zuciyarta haɗe da ƙoƙarin danne ɓacin ranta, ba ta son biye ma Fatimar, ita a tsarinta ko da miji bata cika son ta dinga yawan cece kuce ba balle kishiya. Tun rannan da suka yi a gaban mai wanki da ganin irin yadda Fatima ta nemi juya zancen bayan dawowar Mukhtar yasa ta shan alwashin in sha Allah ta bar ƙara biye ma Fatima suyi cacar baki. A karo na biyu ta sake turo ƙofar za ta rufe.
"Ke Hotiho, ki saurara min. Wallahi Tallahi idan kika kulle ƙofar nan komawa zanyi da abincina..."
"Kin daɗe baki koma da shi ba. Useless"
Baam ta mayar da ƙofarta ta rufe haɗe da jan dogon tsaki.
Tana jin muryar Fatima tana zazzaga tsiya a bakin ƙofar haɗe da kiranta da munanan sunaye, har tana cewa taje dai ta bincika cikin su biyun wacece mare amfani a gidan? Akwai ma ƙatotuwar hotiho irinta? Wacce sam ba ta iya amfanawa miji komai sai dai ta cinye mishi abinci...
Waɗannan jimlolin na ƙarshen maganganunta, su suka tsaya ma Fareeda a zuciya. Tayi tsai a tsakiyar falon tana tunani.
Sai kuma maganar da Mukhtar yayi mata da safe ya faɗo mata arai. Ƙirjinta ne ya buga daram!! Wani jiri da ya fara ɗibanta yasa da saurin gaske ta dafa kujera, a hankali ta laluba ta zauna.
"Kar dai ace Mukhtar ya faɗa ma Fatima ba ya iya komai da ni?"
Tunanin hakan kawai yasa hawaye gangarowa daga idanunta.
"Amma kuwa wallahi da ya gama da ni, kuma in dai yayi hakan bazan taɓa yafe masa ba. Zai dawo gidan ai, zan ji ta inda maganganunta suka samo asali, babu rami me ya kawo maganar rami?"
Daƙyar ta iya rage damuwar maganar a cikin ranta ta kwanta lamo akan kujera, ba ta son saka ma kanta damuwa. Ƙaramin ciki ne da ita, ba tun yanzu ba tasan ba ƙaramin illah damuwa ke haifarwa ga mace mai ciki ba.
Tana wannan kwanciyar sai ga su Sayyid sun fito daga ɗakinsu, hannun Shahid riƙe da sabon ƙwallo, ɗaya daga cikin tarkacen kayan wasan da Hajiya ta haɗo su da shi.
Har sun fara buga mata anan cikin falo sai ta buɗe musu ƙofa ta ce su buga anan harabarta. Ɗan sakaya ƙofar tayi ta koma kan kujera ta kwanta, a hankali ta fara addu'ar kau da damuwa da gaggawa a zuciyarta, a hankali ta dinga jin sauƙi sauƙi har wani daddaɗan barci ya fara kawo mata farmaki...
*_Ya ke ƴar'uwata mai karanta labarin RABON AYI, a gurin neman lafiya daga wannan fitannen ciwo na infection da yake damun mata da yawa, ko dubu ɗari kika kashe wajen siyan ingantaccen maganin sanyi bakiyi asara ba. Lafiya ta fi komai a duniyar nan ƴar'uwa👌🏽 sai da lafiyarnan za ki kankaro ma kanki mutunci da daraja a gurin Oga😘. Ki tuntuɓi Maman Mujaheed ta wannan lambar wayar domin sayen naki ingantaccen maganin sanyin akan farashi mai rahusa 0816 285 9027_*
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*25*_
*Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘*
_Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
10GB👉🏽 N2500
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
*_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
https://hikaya.bakandamiya.com/lokaci-babi-na-daya/ Ƴan'uwa ku danna wannan link ɗin, kai tsaye zai kai ku page ɗin Bakandamiya hikaya domin karanta sabon labarin da ni Fareeda Abdallah nake rubutawa, sunan labarin LOKACI, daga babi na ɗaya za ku cigaba da danna *Next* zai kai ku har babi na huɗu.. Da fatan za'a nuna min ƙauna ta hanyar yin dafifi wajen karantawa, comment, yin rating ɗin labarin. Na gode😘😘😘
Kamar a mafarki, Fareeda ta ji muryar Sayyid da Shahid sun yanka wani rikitaccen kuka mai cike da ƙara da taratsi. A firgici tayi wani irin juyi ta dirgo ƙasa daga kan kujera, da sassarfa ta fice don gane ma idanunta abinda yake faruwa.
Ƙanƙance idanunta tayi da wani irin bala'in ɓacin rai tana kallon Fatima da ta riƙe hannayen Shahid da hannunta ɗaya, ɗayan hannun kuma babu tausayi babu jinƙai ko tunanin ƙaramin yaro ne a gaban Fareeda ta sake ɗaga hannu ta tsinka ma yaron mari.
Da Shahid da aka tsinkawa mari, da Sayyid yake tsaye gefe ɗaya ya ƙanƙame hannayensa a ƙirji yana makyarkyata cikin tsoro da firgici, a tare suka sake ƙwalla ihun kuka.
Ita kuwa Fareeda kawar da kanta tayi da sauri ta lumshe idanu, nan take suka cicciko da hawaye. Wani irin zafi ya lulluɓeta lokaci ɗaya, har wani ƙaiƙayi take ji a kumatunta kamar ita aka tsinkawa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 26