hankalinsa ba shi a kanta, yana karanta saƙon da aka tura masa a waya ne yana sakin wani lallausan murmushi, har ta gama karaɗinta ta nutsu, ta dawo da hankalinta gare shi.
"Yauwa sai magana ta biyu, zan ƙara aure."
Wuta ne ya ɗauke mata na wucin gadi, wani hazo-hazo ya taho da saurin gaske zai gitta ta idanunta da sauri ta rufe ido.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Ta ja salatin cikin wani irin murya mai rauni da miƙa wuya ga Allah maɗaukakin sarki. A hankali ta saukar da kanta ƙasa, zuciyarta sai wani irin bugu da tsallen baɗaken tashin hankali take yi, daƙyar da jiɓin goshi tayi ƙumajin cewa
"Allah ya sanya alkhairi."
"Ameen thumma Ameen."
Ya amsa cikin rashin damuwa da halin da ya ga ta shiga lokaci ɗaya.
Tsam ya miƙe da wayarsa a hannu zai fice, daman ya ɗau wankarsa cikin wata ɗanyar shadda getzner fara kar, sai ɗaukar idanu take yi. Har ya riƙe ƙofar falon sai ya waiga yana kallonta ya ce
"Baki tambaye ni yarinyar da zan aura ba?"
A hankali ta ɗaga idanu ta kalleshi, daƙyar ta iya fito da harshenta ta ɗan lashi laɓɓanta da ta ji sunyi mata wani irin bushewa kamar ta yini bata shafa musu mai ba.
"Ya shafe ni ne dole in san yarinyar...?"
"Ƙwarai kuwa! Ai tabbas ya kamata ki san wacce zan kawo miki gidannan a matsayin abokiyar zama. Ko da yake miye ma na wani kwana-kwana? abinda ba haramci za muyi ba sunnar ma'aiki za mu ɗabbaƙa, ba wata ba ce zan aura face ƙawarki Fatima, ko in ce aminiyarki..."
"Fatima? Fatima dai Mukhtar? Ita ta amince za ta aure ka...?"
"Da gudu ma, ke a banzan tunaninki akwai wata haɗaɗɗiyar mace da za ta ga sankacecen miji kamar Mukhtar ɗin Fareeda ta ce ba ta so?"
"Babu fa! Allah yasa alkhairi."
Ta faɗa cikin wani irin matsanancin ƙarfin hali da juriya, daga zaunen da take tana ganin wani jiri da yake neman rufe mata idanu, tana gani Mukhtar ya sauke mata wani ƙatoton murmushi wanda a take ta fassara shi da murmushin ƙeta, ya fice daga falon sannan ya buga mata ƙofa, bugun da ya sauka har a cikin zuciyarta.
Lumshe idanu tayi a fili cikin wani irin mawuyacin hali take ta jan addu'ar
"Laa'ilaha illallul azeemul haleem. Laa'ilaha illallahu rabbul arshil azeem, laa'ilaha illallahu rabbus samawati, wa rabbul ardhi, wa rabbul arshil kareem."
Daga zaunen da take ta dungura ƙasa kamar wacce ta tafi sujuda, amma ba sujada ta tafi yi ba, sumewa tayi.
_Makaranta labarin RABON AYI ina miƙa saƙon godiya a duk inda kuke🙏🏽🙏🏽😘😘 ni Fareeda na gode da ƙauna, Allah ya bar zumunci. Da yawanku ina ganin coments ɗinku, amma ba na iya binku ɗaya bayan ɗaya inyi reply saboda hidindimun da suka sha kaina. Amma fa ina jin daɗin coments ɗin💃🏽💃🏽, bazan ɓoye muku ba maganganun da kuke yi kan labarin su ke ƙara min ƙwarin gwuiwar yin typing don kar in barku kuna jira. Na gode na gode🥰🥰😘😘😘😘 kar ku manta ina sayar da Datar MTN, wacce take so ta tura kuɗi ta acc ɗina da ke sama sannan a tuntuɓeni ta lambata da ke sama. 1gb 300, 2 600, 3 900, 4 1200, 5GB 1500._
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*9*_
Ba tare da ɓata lokaci ko wata damuwa a fuskarsa ba ya shige cikin motarsa. Zuciyarsa cike take taf da farin ciki.
Duk yadda Fareeda tayi jarumta wajen ɓoye tashin hankalin da ta shiga da jin sunan wacce zai aura shi kam ya gani, ai an ce labarin zuciya a tambayi fuska. Ƙarara ya ga tashin hankalin da zuciyarta take ciki zane ɓaro-ɓaro kan fuskarta.
"Kaɗan ma kika ji kuma kika gani Yarinya."
Ya faɗa haɗe da yin ƙwafa, babu tausayinta ko kaɗan a zuciyarsa.
Wannan wankan da ya ɗauka daman don Fatima yayi, tsawon sati biyun da suka kwashe suna zuba soyayya ta waya shi kam ɗari bisa ɗari ta yi masa, ya gamsu zai samu abinda yake so.
Irin alƙawurran ladabi, biyayya, gata, kogin so da ƙaunar da take ta ƙara kwaɗaita mishi idan suka yi aure shi kam ya amince ko bata kai haka a tsarin halitta ba zai iya auren ta.
Yo daman me ake biɗa a auren? ba kwanciyar hankali bane? A wannan matakin da yake kai na jin zafin irin ƙunci da baƙin cikin da Fareeda ta daɗe tana ƙunsa mishi ko tsohuwa ce zai iya aurenta matuƙar za ta bi tsarin da yake so, kuma su zauna lafiya ƙalau.
Yana gaf da ficewa daga cikin layinsu sukai clashin da motar Yaa Mustapha, da alamun gidansa suka nufa. Rage gudu Mustapha yayi da niyyar su gaisa, Mukhtar ya kawar da kansa ya ƙara ma motarsa wuta ya wuce a guje, ko fitila baiyi musu ba, kamar ma bai san motar waye ba.
Da mamaki Yaya Mustapha yake hangenshi ta mirrow har ya ɓace ma ganinsa.
"Wai wancan motar da ta wuce ba ta Mukhtar bane?"
Aunty Murja da take zaune gefen mai zaman banza ta tambaya, itama fuskarta na nuna mamaki.
"Shi ne. Ina ga bai ganmu bane."
Ya amsa yana ƙara gudu don isa gidan. Babban burinsa yayi tozali da ƙanwarsa, Shekaran jiya da ya kirata ta tabbatar mishi har ranar Mukhtar bai zo garin ba.
Yadda ya ganshi yanzu ɗinnan da yadda ya sharesu bayan sun haɗa idanu ya alamta mishi tabbas akwai matsala.
Bayan shigarsu cikin gidan sallama suke ta kwaɗawa a ƙofar falon, amma shiru suke ji. Duk su ukun kuma sun kira wayarta amma babu wanda ta ɗaga.
Cikin ɗan damuwa da ƙila wa ƙalan lafiya ko ba lafiya ba Aunty Murja da ƴar'uwarsu Rahama wacce ta kawo musu ziyara daga Rigacikun suka sa kai cikin falon don duba halin da ake ciki. Shi kuma Yaya Mustapha matsayinsa na namiji ya tsaya a bakin ƙofa hankalinsa a tashe yana jiran su gano halinda Fareeda ke ciki, domin tamanin bisa ɗari na tunaninsa ya tafi kan ba lafiya ba.
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ke Fareeda? lafiya? me yake faruwa?"
Ya ji muryar su biyun sun faɗa cikin da wani irin karaɗin tashin hankali.
Ko kafin ya banke ƙofar falon ya shiga a sittin zuwa inda suke sai jin muryar Aunty Murja yayi ta fashe da wani irin ƙaƙƙarfan kuka.
Ganin Fareeda kwance shamɓar a ƙasa bayan gyara ta daga sujudar da tayi ba rai babu alamunsa a jikinta yasa shi ya tafi taga-taga zai kife, Allah ya taimake shi hannunsa na hagu ya dafe bango. Cikin ɗaukewar hankali da tunani ya tafi a slow motion ya zauna daɓar a ƙasa ya zuba ma gangar jikinta idanu, na wasu daƙiƙu ƙwaƙwalsa ta tsaya cak daga sadarwar saƙonni.
Rahma, wacce su Fareeda ke kira Baby saboda tsananin gayu da yanga irin nata, ƴar'uwa ce ta kusa sosai a gurinsu. Karatun aikin jinya tayi, duk da tashin hankalin da take ciki na ganin aminiya kuma ƴar'uwarta cikin wannan hali tunaninta bai ɓace kamar nasu ba. A nutse ta dudduba Fareedar sai taga ba rasuwa tayi ba, suma tayi.
Da gaggawa ta nufi kicin, gorar ruwa mai matsakaicin sanyi ta ɗauko ta dawo. A nutse ta zauna ta fara tsiyaya ruwan kaɗan a hannunta tana shafa mata a fuska, ta shafa sau uku a na huɗun Fareeda ta ja wani nannauyar ajiyar zuciya ta sauke.
Da saurin gaske kuma a firgice ta buɗe idanunta, ido biyu da sukai da Baby yasa ta miƙewa zaune a zabure da wani irin ƙarfi a jikinta ta ruƙunƙumeta, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wani ƙaƙƙarfan kuka mai tafe da saƙon baƙin ciki da takaici tun daga can ƙarƙashin zuciyarta.
Kukan da ta fashe da shi shi ya zama kamar yarfin ruwan ƙanƙara ga Aunty Murja da Yaya Mustapha.
Da murna mai tsanani ganin ta farfaɗo suka matsa kusa da sauri, Aunty Murja ta ruƙunƙume su biyun itama tana nata kukan na farin ciki. Farkowar Fareeda ba mutuwa tayi ba ya kore mata duk wani damuwa da fargaba, a ganinta duk abinda zai biyo baya mai sauƙi ne.
Shi kuwa Yaya Mustapha gefe ya rakuɓe kamar ƙaramin yaro yana ta sassauke ajiyar zuciya a jejjere, zuciyarsa cike da farin ciki, babu abinda yake furtawa da murya ƙasa-ƙasa sai
"Alhamdulillahi alaani'imatihi tatimmussalihat."
Ganin kukan yana ƙara tsawo ya ƙi ƙarewa yasa Baby ta fara raɗa mata tausasan kalamai a kunnenta.
"Ya isa haka Besty, pls ya isa haka. Ummm?! Ba ga mu ba? ko ma wane al'amarin damuwa ne za mu fuskance shi tare, muna tare da ke, kin ji ko? duba kiga Aunty Murja riƙe da ke, kuka take saboda irin kukan da ta ga kina yi. Kin ga Yaya Musty zaune a gefenki shi ma cikin tashin hankali, kiyi haƙuri kin ji? kiyi ta maimaita Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ko wane bala'i ne in Allah ya yarda zai zo mana da sauƙi kin ji?"
A hankali take ta rage ƙarfin kukanta, har tayi shiru gaba ɗaya, sai sauke ajiyar zuciya irinna wacce ta daɗe tana kuka.
Har wannan lokacin kanta na kwance a kafaɗar Baby. Mustapha da Murja sun matsa kusa da ita suna riƙe da hannayenta a cikin nasu, a fuskokinsu tana kallon matsanancin damuwa da tashin hankali saboda damuwar da take ciki.
"Mukhtar... zai... ƙara aure..."
Tayi maganar a rarrabe.
Su ukun gaba ɗaya buɗe baki sukai cikin tsananin mamaki suna kallonta, ƙara aure a daidai wannan lokacin shi ne abu na ƙarshe da za suyi tunanin Mukhtar zaiyi, ba don komai ba sai don ganin matsananciyar soyayya da shaƙuwar da ke tsakanin masoyan biyu.
Tuna komai lokaci ne kuma muƙaddari daga Allah yasa Mustapha rufe baki a sanyaye. Ya haɗiye wani kakkauran miyau, ya rasa da wace kalami zai fara amfani wajen kwantarwa da ƙanwarsa hankali.
Ya buɗe baki zaiyi magana Fareeda ta katse shi ta hanyar cewa
"Ya tabbatar min da zai ƙara aure, kuma babu wacce zai aura sai ƙawata... Fatima ƙawata... Fatiman Mama Laure."
Ta ƙarasa maganar da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta.
"Kan ubancan kayyasa."
Baby ta lailayo wani ashar ta maka saboda yadda maganar ta bugi zuciyarta.
Duk su ukun babu wanda bai san Fareeda da Fatima ba, abin mamaki ne ƙwarai da jinjinawa a ce Mukhtar zai auri Fatima ƙawar Fareeda.
"Amma ita Fatiman ta amince?"
Aunty Murja tayi ƙarfin halin tambaya fuskarta na harhaɗewa da wani irin matsanancin ɓacin rai.
"Ƙwarai! Ya tabbatar min ta amince. Kuma daman sati biyu kenan ko na kirata a waya ba ta ɗauka, daga bisani ma sai ta kulle ni na daina samunta..."
Aunty Murja da Baby ne suka haɗa baki gurin cewa
"Kutmelesi..."
"Menene kuke yi haka kamar wasu ƙananun yara? Kun manta babu haramci ko kaɗan a cikin aurensu?"
Mustapha ya katse su da faɗin haka.
"Haba Yaya Mustapha, ai ana barin halas ko don kunya. Sai ka ce muna garin gaɓa-gaɓa(marasa hankali)?"
"Uhmmm! Baby kenan! ke dai kawai Allah ya iya mana. Amma muna cikin wani zamani ne wanda da yawanmu bamu ɗauki cin amana a bakin komai ba."
Lura da yayi maganganun matan babu abinda suke yi sai ƙara rura wutar kishi da baƙin ciki a zuciyar Fareeda duba da yadda take share hawaye akai-akai. Yasa Mustapha matsawa kusa da ita sosai ya fara rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali.
*****
"Wai yanzu ƙawata kina nufin wannan ɗan mitsitsin turaren shi ne zan shafa a goshi na muyi tozali da Aban twince? Ni wlh na raina..."
Da saurin gaske ƙawar ta rufe mata baki, sai zazzaro idanu take yi hankali tashe kamar wacce taji za'ayi saɓon Allah.
"Ki iya bakinki. Na rantse da girman Allah ki iya bakinki. Ba'a tantama ko raba ɗayan biyu a kayan Hajiya Zainab Harka gaskiya da gaskiya. Idan ba haka ba kuwa ina tabbatar miki za kiyi biyu babu, ke ba ga biyan buƙata ba, maƙudan kuɗaɗen da kika kashe basu dawo ba."
"Hmmm! Allah na tuba. Shi kenan Ramlah. Na gode. Zan gwada sai fatan Allah yasa mu dace."
"Yauwa ko ke fa Hajiyata. Ai duk abinda zan karɓo miki gurin matarnan ina tabbatar miki kiyi amfani da shi kawai da dukkan ƙwarin gwuiwarki. Magungunanta ƴan gaske ne, manyan malamai gareta waɗanda kafin ta fara siyar da ko wane magani nata sai sun kwana sittin suna sauke izu sittin."
"Taɓɗijan!"
Fatima ta ambata cikin mamaki da jinjina girman al'amarin.
"Da gaske fa, amma na tabbatar duk abinda zan faɗa miki a yanzu baza ki yarda ba. Sai kinga Mukhtar ya zama tamkar takalmin takawarki. Fareeda kuwa ko rantsuwa nayi ba kaffara kina shiga gidan zaiyi waje road da ita..."
"Hehehehe!"
Ta fashe da wata ƙaƙƙarfar dariya na jin daɗin maganganun ƙawarta.
Sai kuma ta gyara zama a gefen gadon, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa. Da dukkan gaskiyarta ta kalli ƙawar ta ce
"Kin san Allah? ni kuma ba na burin ya saki Fareeda. So nake cikin sanyi da wani irin taku na kissa in soya mata ɗanyar gyaɗa a hannu, ta wulaƙanta na ƙarshen ƙarshe, tana ji tana gani mijin da take tunƙaho da shi ya fi ƙarfinta, ya zamo sai hange daga nesa. Shi yasa Wallahi Tallahi Billahi ko nawa ne zan kashe don gyara kaina..."
A tare ƙawayen biyu suka fashe da wani ƙaƙƙarfan dariya haɗe da tafa hannayensu.
"Daman fa Hajiyarmu tana cewa burin kishiya abu uku ne. Ko ta fita ta bar miki gidan, ko ta mutu ta bar miki duniyar, ko tayi mummunar wulaƙantar da kare ma sai ya fita daraja a gurin mijin. Ki dage ƙwarai ƙawata ki tabbatar da ɗaya daga cikin maganganu ukun nan."
Ramlah ta faɗa da wani irin salon zuga da tunzurah zuciyar Fatima, ta kuwa samu nasara, nan take ta cigaba da shan munanan alwashi kan Fareeda.
Suna wannan halin Mukhtar ya kirata a waya ga shi a ƙofar gidanta.
*Kuyi maneji da wannan don Allah. Ba nan naso tsayawa ba, wayata ne ba caji. Na gode da ƙauna ƴan'uwa😘😘😘.*
*_Aminci + Ƙarko Data Services_*
*_Kina/kana buƙatar Datar MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE mai matuƙar aminci da ƙarko? Wanda za ki daɗe kina sauke abubuwa da kallace-kallace ba tare da yayi saurin ƙarewa ba?_*
Ga farashin datarmu a sauƙaƙe👌🏽 ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai a tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online a kira ni ta 09077591726.
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
Hallau muna tura katin waya, katin startimes, go.tv, e.t.c👌🏽
*_Namu ba irin nasu bane, shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*10*_
Lallausan murmushi ta saki jin cewar yana ƙofar gida. Mai gadin gidan ta kira, tayi mishi umarnin a buɗe ma babban baƙonta ƙofar gida ya shigo da motarsa.
Sai kuma ta kira ɗaya daga cikin ƙannenta biyu da suke zaune tare da ita da ƴaƴanta ta bata umarnin ta shigo da baƙonta cikin falon. Daman tun tuni ta sa sun ƙalƙale ko ina an baɗe shi da turaren wuta.
Tun ɗazu ta yi wanka, zaman jiran ƙarasowarsa take yi Ramlah ta kai mata saƙonta.
Tun da ya shigo cikin kaduna ya faɗa mata ya iso, ko da ya ce mata gida zai fara zuwa yayi wanka har da kukanta na kissa.
Cikin shagwaɓa ta roƙe shi to don Allah idan ya je gida kar ya daɗe, tun ɗazu ta gama shirya mishi kayan abinci ta yi kwalliya zaman jiranshi kawai take yi.
Ta sake ƙasa ƙasa da murya tana ɗan jan hanci, kamar har lokacin kuka take yi ta ce
"Aban Twince, ka ganni zaune hannuna a kunci, idanuna sun ƙure ƙofar shigowa da kallo, babu abinda suke so da buri sai suyi tozali da kyakkyawar fuskarka mai cike da annuri da haske, irinna mai riƙo da Addinin musulunci.
Hancina a buɗe yake, babu abinda yake muradi sai ya shaƙi daddaɗan ƙamshin da jikinka ke fitarwa Nawan"
Kunnuwana a burbuɗe suke, babu abinda suke kwaɗayi sai suji saukar sautin tattausan muryarka mai cike da amo da kwarjini na ingarman namiji.
Don Allah ka tausaya ma zuciyar da kullum take ta tsallen daka tana jiran isowar abokin soyayyarta.
Kar ka bari Aunty Fareeda ta tsare ka da surutunta har mu bushe ni da abincin da na shirya maka wajen zaman jiranka."
Daga haka ƙit ta katse wayar, tana jin shi yana ta sauke numfashi sama-sama tsabar yadda kalamanta suka rugurguza ɗan ragowar kuzarinshi.
Da yake ɗan halas ne, ko da ta kalli agogo yanzu sai ta ga mintuna arba'in da bakwai kenan da gama wancan wayar tasu. Lallai Mukhtar za'a je da shi.
Ashe ma bashi da wahalar sha'ani kamar yadda kullum Fareeda take cewa
"Ke ƙyale ni, Mukhtar murɗaɗɗen mutum ne. Lallaɓawa nake yi ina haƙuri don mu zauna lafiya."
Tunanin Fareeda a wannan gaɓar da tunanin irin maganganun da suke yi a lokuta mabanbanta yasa ta jan tsaki ƙasa-ƙasa.
"Ƙawata lafiya kuwa?"
Ramlah ta tambayeta.
"Ba komai ƙawata. Wani banzan tunani ne ya faɗo min arai. Ki jira ni anan pls in sallami Aban Twince, idan ya tafi sai in baki cikon kuɗin."
Ta miƙe da hanzari ta fara sabunta kwalliyarta, a fuska kaɗai za'a kalli Fatima asan tana cikin matsanancin farin ciki.
Cikin lokaci kaɗan ta rambaɗa wani ubansun kwalliya, kamar wacce za ta je gasar fitar da sarauniyar kyau ta jihar kaduna. Ta ɗauko wani ɗan ubansun leshi da aka yi mata ɗinkin doguwar riga, daga sama ya kamata tsam, daga gurin gwuiwarta zuwa ƙasa sai rigar ta baje. Ta ɗauko wani siririn gyale da zai shiga da leshin ta rataya a kafaɗa, ta yi kyau sosai.
Ƙawarta Ramlah sai zabga mata kirari take yi ita kuma kanta yana ƙara kumbura. Daga bisani ta fice daga ɗakin da salon tafiyar za tayi baza tayi ba, tana wani rangaji kamar reshen bishiya a iskar damina, hannunta riƙe da wannan turare wanda Ramlah ta karɓo mata.
A ƙofar shiga cikin falon ta tsaya ta buɗe turaren ta zuba fiye da rabi a jikinta, nan take gurin ya ɗume da wani irin ƙamshi mai tafe da ƙauri-ƙauri.
Ita kanta ƙamshin baiyi mata ba, amma kasancewar turaren magani ta san dole za'a ji haka, wataƙila a hancin wanda aka siya turaren dominsa tattausan ƙamshi mai matuƙar kwantar da hankali zai shaƙa.
Tunanin hakan ya sa ta sakin murmushi. Ta maƙale muryarta ƙasa sosai da wani irin salo na jan hankali tayi masa sallama, ta jira ya amsa sannan ta yaye labulen ta sa kanta ciki.
Suna haɗa idanu a tare su biyun suka sakarma juna wani lallausan murmushi, ta ƙarasa a hankali da wannan salon tafiyar nata har zuwa kusa da inda yake zaune, kan kujera mazaunin mutum uku.
A maimakon ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye falon, sai ta tsuguna a ƙasa, cikin ladabi da ƙanƙan da kai ta sauke idanunta ƙasa kamar baiwa a gaban ubangidanta.
"Haske nah, ina maka barka da zuwa akurkin muhallina a karon farko. Na ji daɗi matuƙa gaya, yau ɗin ta kasance rana mai matuƙar muhimmanci a cikin tarihin rayuwata. Barka da zuwa, ya hanya? ina fatan ka iso lafiya?"
Duk waɗannan maganganun da take yi tana yi ne da wani irin salo na jan hankali, ga miji mai matuƙar son girma da biyayya na ƙarshe irin Mukhtar.
"Mace mai ladabi duniya ce Alaji."
Mukhtar ya faɗa a zuciyarsa. Daƙyar ya iya mazewa don kar ya bada kanshi a karon farko ya amsa gaisuwarta.
Umarni yayi mata kan ta tashi ta hau kan kujera, buɗar bakinta sai cewa
"Miji fa tamkar Ubangida yake a gurin mace mai wayau. Taya zan iya hawa saman kan kujera in goga kafaɗa da kai alhalin kana saman kujerar? A ganina babu ladabi ko kaɗan a cikin haka. Ka barni haka Aban Twince, nan ɗin ma ya isa."
Sai ta ɗan muskuta ta gyara zama a kan kafet nan gabanshi, ta tsura mishi idanu tana kallon tsantsar kwarjini da zatin da Allah ya zuba a fuskar wannan bawan Allah.
Tunanin ko ruwa bata gabatar mishi ba yasa ta nemi afuwarsa a marairaice.
"Yi haƙuri Haske nah! kallon kyakkyawar fuskarka na neman shagaltar da ni in gabatar maka da ababen motsa bakin da na shafe tsawon yini guda ina shiryawa musamman domin kai Mijina. Ina sake neman afuwa a karo na biyu."
Lallausan murmushi kawai ya sakar mata, shi fa ya ma kasa magana. Babu abinda yake hasasowa a zuciyarsa sai irin kyakkyawan zamantakewar da za suyi shi da Fatima. Lallai wannan ita ce abokiyar burminsa.
Sai bin ta da kallo yake yi tana jera wasu ƙayatattun kulolin cin abinci a gabansa, bayan ta janyo wani ɗan madaidaicin teburin da ake ɗora abinci a tsakiyar falo idan ba'a sha'awar zuwa dining table.
Sai da ta kwaso kayan abincin tas, da wani jug ɗin gilashi mai cike taf da kakkauran zoɓo da yasha kayan ƙamshi.
"Haske nah! Ka yi min izinin in zuba maka abincin?"
Ta tambayeshi a ladabce.
A wannan karon ma ya kasa magana, sai kai ya iya ɗaga mata alamar yayi mata izini.
Martanin lallausan murmushi ta fara sakar masa, kafin ta fara buɗe kular miya tana satar kallonshi.
Daddaɗan ƙamshin miyan agushin da ya daki hancinshi yasa shi buɗe hanci sosai ya shaƙi ƙamshin, ya lumshe idanunsa. Kafin daga bisani ya buɗe idanu ya sauke kan kayan abincin, a daidai lokacin da ta ɗauko malmala ɗaya na sakwarar da ya daku luƙwui-luƙwui ta saka masa a faranti.
A wannan gaɓar kam ya kasa shiru, sai da ya ce
"Fatina? ya aka yi kika san abincin da na fi so a rayuwata?"
Ya tambayeta yana mamaki.
Far tayi masa da idanu, ta rausayar da kanta gefe guda. Muryarta ƙasa-ƙasa da rangwaɗa ta gilla mishi ƙarya da cewa
"Haske nah! Sakwara da miyar agushi nima shi ne abincin da na fi so a rayuwata. Kawai zuciyata ce ta raya min, idan da gaske so ya kai so tsakanina da kai tabbas zai kasance abinda nake matuƙar so kaima kana son sa. Abinda nake ƙi kaima za ka ƙi shi Aban Twince, kasancewar hakan shi ne cikar soyayya."
_A zahirin gaskiya a gurin Fareeda taji yana matuƙar son sakwara da miyar agushi. Idan ta je gidan a mabanbantan lokuta tana tarar da ita tana daka sakwara. Ita kuma Fatima abinda bai dameta ba kenan, idan ta fara ƙorafi ita ko wahalar daka ba ta ji kai tsaye take faɗa mata Mukhtar na tsananin son sakwara, ko laifi tayi masa idan tana so ya huce da sauri to tayi masa sakwara miyar agushi da busasshen kifi ko kuma da naman rago. Ta yi amfani da haka ne don ƙara saye zuciyarsa._
Shi kuwa tsananin farin ciki da jin daɗi ba kunya ya tare hannunsa a baki ya sumbata, sannan ya hura mata a cikin iska.
Lumshe idanunta tayi tana dariya ta ɗan rufe gefen fuska irin alamun ta ji kunyar nan, me ta tuna kuma oho! sai ta buɗe fuskar da sauri ta saka idanunta cikin nashi. A tare suka sakarwa juna murmushi.
Sosai ta zuba mishi miyar agushin da ta ji naman rago ya dahu luguf a gefen sakwarar.
Ko kafin ta miƙa mishi har miyan bakinshi ya gama tsinkewa. Don haka bai ɓata lokaci ba yayi bismillah ya fara ci a nutse, yana yaba ɗanɗanon girkin a fili da zuciyarsa.
Tagumi ta buga da hannu biyu ta gyara zama a ƙasa nan gabansa tana sake ƙare masa kallo.
_'Wato lallai Allah Al-musawwiru ne. Ashe akwai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 26