ne muna aika kayanmu ko ina kuma a gaggauce💃🏽💃🏽💃🏽 Muna maraba da masu sayen ɗaiɗai ko sari. Sai kun zo❤️❤️❤️*
*Kuyi haƙuri. Ku ƙara min uzuri don Allah. Wallahi wani irin rashin wuta ne muke fama da shi yanzu, sai a hankali. In sha Allah ko ɗan yaya ne zan dinga samu ina muku posting ko babu yawa. Na gode🥰🥰🥰🥰*
*Ƴar'uwa ciwon sanyi ne ya dame ki? Har bakya jin sha'awa ko ɗanɗano idan kun leƙa can babban birnin maji daɗi😘😘? Ki tuntuɓi Zee maman mujaheed +234 816 285 9027 domin siyen maganin sanyi mai kyau sosai akan farashi mai rahusa😍😍💃🏽💃🏽💃🏽 Baza kuyi da na sani ba in Allah ya yarda*
*RABON AYI*
*28*
*©Fareeda Abdallah*
*Dangane da batun mai bayar da maganin rashin haihuwa.* Mata da yawa sun biyo ni ta private da ƙorafin iyakar magungunan da take bayarwa kenan? Nayi ta bin su da cewar zan tambaya. To a jiya dai Allah ya nufa na tafi har can ƙauyenmu mun gana fuska da fuska da wannan mata, saboda ita ba ta da wayar da zan kira inyi magana da ita kai tsaye.
*Bayan maganin rashin haihuwa na maza da mata. Tana bayar da maganin sanyi, idan mace ta san tana fama da ciwon sanyi, akwai wasu ɗaurin sauwoyi da ta nuna min duk guda ɗaya 500, jiƙa shi ake yi da mazarƙwaila, citta, kanunfari, idan ya jiƙu sai a dinga sha da Oga da yara gaba ɗaya. Akwai wani garin magani da ta nuna min shi ma dai duk na sanyin ne, irin sanyin haihuwar nan musamman masu jego, ko wacce take fama da sanyi tun na haihuwa, garin maganin ɗaurinshi 500, za'a haɗa shi a cikin yaji ne a dinga cin abinci da shi. Tana bayar da maganin gyaran nono ga masu ciki da masu shayarwa, shi ma ɗaurinshi 500, idan mace ta dimanci shan maganin tun tana da ciki da yaddar Allah da ta haihu baza ta fuskanci matsalar ruwan nono ba. Mai shayarwa ma idan ta fara amfani da maganin za taga yadda nononta zai gyaru, yaronta yayi tubarkallah. Ko da yaron ya yanƙwane da yaddar Allah zaiyi kumari, hatta ƙurarrajin ko ela da yara ke yi idan mace tana shan garin maganin da yaddar Allah ɗanta bazai yi ba. Ina matan da suke fama da matsalar rashin jin sha'awa? Har suna ji a dole mazajensu ke kusantarsu, wasu ma har aurensu ke mutuwa saboda wannan matsalar, sai a dinga cewa ko suna da aljannu? Matar tana bayar da haɗin magunguna da yaddar Allah in dai mace tana da rabo za taga yadda za ta samu waraka cikin sauki. Matan da mazajensu ba su da kuzari, sanyi da basir ya musu illar da sai ayi watanni basu nemi iyalansu ba, su ma akwai maganin da take bayarwa a jiƙa ma miji, cikin lokaci za ki ga yadda lafiya za ta wadatu a jikin mijinki, hatta kuzarinsa sai kin ga ya ninnika na da.* Masu buƙatar ɗaya daga cikin maganin matsalolin da na bayyana a sama idan sun san da gaske suke yi su tuntuɓeni ta wannan lambar 07039080978, don Allah duk wacce tasan ba da gaske magani take so ba kar ta tuntuɓeni balle har mu ɓata ma juna lokaci🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽
Ƙara matse mata waje yayi, a hankali ya riƙo tsintsiyar hannunta yana ɗan matsawa
"Ina son ki Fareeda."
Ya faɗi kalaman cikin salo a rarrabe.
A yanzu ma dai kallonshi ta sake yi, sai kuma ta taɓe baki ta mayar da fuskarta ga t.v.
"Haushi na kike ji?"
Ya tambayeta, da muryarsa a sanyaye.
"A'a"
Ta amsa daƙyar bayan ta ɗauki tsawon daƙiƙu tana jan fasali.
Ya buɗe baki zai sake magana ta katse shi da cewar
"Haba Mukhtar, saboda Allah abincin ma baza ka barni in ci cikin kwanciyar hankali ba? Sai da safe ce ya kawo ka ko? to na amsa, Allah ya tashe mu lafiya. Don Allah ka kwashi kulolinnan ka koma gurin matarka, bazan ɓoye maka ba Allah ya sani na fi jin daɗin zama ni kaɗai ba tare da wani a kusa da ni ba."
Ta faɗi maganganun da dukkan gaskiyarta.
Ya daɗe yana kallonta, zuciyarsa a jagule. Ya kasa ce mata komai, wai yau shi Fareeda ke ce ma ta fi jin daɗin zama ita kaɗai ba tare da shi a gefenta ba. Ya murgina kai gefe ɗaya abin tausayi, ya sani, Ibrahim ya faɗa masa. Shi da kanshi ya ƙona sunkurun kashinsa, don haka fushin fari ba nashi bane. Dole zai cigaba da bin ta yana lallaɓata har zuwa sa'adda za ta sakko don kanta ba tare da ya tilasta mata ba.
"Fareeda, ni dai ina neman afuwa. Allah ya huci zuciyarki. Bari in tafi, Allah ya tashe mu lafiya."
"Ameen"
Ta amsa da sauri.
A kasalance ya miƙe ya nufi ƙofar fita.
"Ka kwashe waɗannan kulolin, ka mayar mata da kayanta."
Ta faɗa ganin zai bar mata abincin Fatima a gabanta.
A hankali ya juyo, gabanta ya tsuguna ya ɗauki kular abinci ya bar mata na kayan ciki. Ya kalli cikin idanunta, a marairaice ya ce
"Zan mayar da abincin, waɗannan biyun kayan ciki ne, farfesu da soyayye. Don darajar fiyayyen halitta SAW kar ki ce baza ki ci ba ko kuma ki ce in mayar. Don Allah"
"Shi kenan! Allah ya ƙara buɗi."
Ta faɗa saboda darajar waɗanda ya haɗa ta da su. Ya ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, sun fi ƙarfin a roƙe ta yin abu don su ta ce a'a.
"Bari in juyo ka mayar da kulolin."
Har za ta miƙe sai ya dafa kafaɗunta ya komar da ita ta zauna.
"Yi zamanki Baby. Bari in ɗauko wasu kulolin in juye a ciki."
Ko da ya shiga kicin ɗauko kulolin sai da ya haɗo mata da faranti da cokali, ko da za ta ɗiba ta ci ba sai tayi wahalar tashi ba. Duk da ya ga ruwa a gabanta sai da ya ɗauko wani ya ƙara ajiye mata.
"In ɗiba miki ko kaɗan?"
Ya tambayeta sa'adda yake juyewa a kulolinta.
Abinku da mai ƙaramin ciki, tun sa'adda ya buɗe kular ƙamshin farfesun ya daki hancinta miyaun bakinta ya tsinke. Amma saboda ta tankwaɓe shisshigin da yake mata sai ta ce
"A'a! Ba yanzu zan ci ba. Pls rufe kular, ƙamshin ya fara hawa min kai."
Da sauri ya rufe jikinsa na rawa. Bawan Allah sai sannu yake jera mata ganin yadda take yamutsa fuska. Bai tashi a gabanta ba sai da yaga ta daina ɓata rai, haka ya fice gwuiyawunsa a saɓule, kamar wanda yayi amai da gudawa.
Ko da ya koma can ɓangaren Fatima duk tsawon lokacin da ya ɗauka gurin Fareeda tana zaune gaban abincinsu tana jiranshi. Duk da ranta ya sosu da daɗewar da yayi, ko kaɗan bata nuna mishi ba.
"Sannu da zuwa Haskenah"
Ta faɗa da fara'a sosai a fuskarta.
"Ya Auntyn tawa take? Ina fatan ka tarar da ita lafiya kalau?"
Ta sake faɗa kafin ya amsa sannu da zuwan da take mishi.
Da murmushi a fuskarsa ya amsa mata. Sosai ya ji daɗin yadda ta tambayi lafiyar Fareeda, ya tuno yadda ita Fareeda ta gama kushe lamarin Fatima yanzunnan kafin ya baro wajenta. Hakan ya saka shi jin babu daɗi kaɗan a zuciyarsa, bai bari tunanin yayi nisa ba ya watsar da komai ya zauna cin abinci.
Bayan sun gama tana tattare kwanonin zuwa kicin shi kuma yana zaune kan kujera, wayarsa ce a hannunsa yake dannawa. Jefi-jefi yana ɗaga idanu ya kalli Fatima da take zirga-zirga a gabansa.
Ta zo za ta gitta ta gabanshi ya riƙo hannunta ɗaya haɗe da cewa
"Zo nan in gani Amaryata"
Ya janyo ta a hankali ya zaunar kan cinyarsa.
Yana kallon idanunta ya ɗaga hannunsa a hankali ya zura ta saman rigarta. Idanu ya ɗan bubbuɗe jin tudun da ya shafo, tun dazu da take wucewa yana ta kallonta gaba da baya ya zaci cikon da ya hana ta yi ne tayi. Shi yasa ya yanke shawarar dubawa don kar ma ya tambayeta ta faɗa mishi ba daidai ba.
"Iyyeeeee... Amaryar tawa ce haka? Yaushe aka samu wannan gwaggwaɓar cigaban ba ni da labari?"
Ya tambayeta yana ɗan mammatsa mazaunanta yana jin yadda tsoka ya fara rufa ma ƙasusuwan gurin asiri, da murmushi a fuskarsa.
Hajiya Fatima dai ta kasa magana, a yangace ta ɗan saki siririyar haɗe da kwantar da kanta a ƙirjinsa.
"Au! Abin ƴar haka ne? Baza ki faɗa min ba Fatina?"
Ya raɗa mata a kunne yana taya ta dariya.
"Haskenah ka ga ka bari, ba na so."
Ta faɗa a shagwaɓe tana ɗan dukan ƙirjinshi.
Aikin da bata ƙarasa a wannan dare ba kenan. Tun a nan falon wasan ya sauya salo, daga ƙarshe dai cak ya ɗauketa kamar wata baby zuwa cikin ɗakin barcinsu.
A wannan dare, Mukhtar ya shayar da Fatima zallar madarar farin cikin da ta daɗe tana burin kwankwaɗa a auren matashi sabon jini. Irin wannan salon soyayyar ta indiyawa ne yasa a mafiyawancin lokuta zamanin marigayi take cizon yatsar auren tsoho. Ta zaci a wancan ranar ne da ya tabbatar ta samu lafiya ne suka ci amarci, ayau ta tabbatar wancan ranar ba'a yi komai ba illah shafar mai. Yau ita ce ranar da suka ci uwar sabada ita da Haskenta. A daren ta ƙara tabbatar da Haskenta wani Haske ne mai muhimmanci a cikin rayuwanta, tun yanzu ya fara tsundumata cikin wasu daɗaɗan duniyoyi da ko kusa basu taɓa ziyarta ita da Babansu Ummee ba ina ga can gaba sun ƙara dunƙulewa ta hanyar zama abu ɗaya?
Haka ya sake ɗaukarta cak suka shige banɗaki, bayan wankan tsarki a tare suka yi na soso da sabulu. Yana cuɗa mata baya tana cuɗa mishi, kamar wasu ƙananun yara har da su wasan watsa ruwa da shafe-shafen kumfa bayan an ɗauraye jiki. Wannan wanka a lalace suka ƙarasa shi sannan suka fice daga banɗakin.
Da sauran awa ɗaya kafin a kira sallar asubah, don haka suka bi lafiyar gado. Tana kwance luf a ƙirjinshi tana sauke ajiyar zuciya sannu sannu.
"Barci za kiyi Fatina?"
Ya jefa mata tambayar bayan ya ji numfashinta ya fara canzawa.
"A'a! Kawai dai na ɗan gaji ne."
Ta amsa a kasale.
"Na san kin gaji. Sannu da ƙoƙari, ki daure muyi sallar asubah sai mu kwanta. Yanzu dai tashi muyi magana."
A hankali ta zare jikinta daga cikin nashi ta zauna a tsakiyar gadon. Shi ma zaman yayi, amma sai ya juya yana fuskantarta. Hannayenta biyu ya kama ya riƙe a cikin nashi, babu alamun ɓacin rai ko kaɗan a fuskarsa, sai ma wani ƙayataccen murmushi da yake sakar mata akai-akai.
"Fatina, tambayarki zanyi. Amma ina so ki ɗaukar min alƙawarin duk abinda na tambaye ki za ki faɗa min gaskiya tsakaninki da Allah da ya haliccemu."
Ƙure shi da kallo tayi, zuciyarta cike da tunanin me zai tambayeta.
"Tambayar mecece?"
"Ai baki ɗaukar min alƙawarin ba..."
"Na ɗauki alƙawari. In dai na sani zan faɗa maka gaskiya tsakani da Allah."
Ta katse shi da ƙagauta a muryarta.
Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara magana. Can sai ya daure ya ce
"Fatina, a gurin binciken abinda ke damuna har yake hana ni kusantar Fareeda an tabbatar min matsalar ba daga ita bane, daga ni ne..."
"Daga kai kuma? to taya ni baka fuskantar irin matsalar a gurina?"
Tayi mishi tambayar tana yatsuna fuska.
"Mai maganin da ya faɗa min haka ya ce, da yawan mata idan za suyi aure musamman zawarawa sukanyi amfani da magunguna daban daban domin su gyara jikinsu. Idan kuwa gidan da za su shiga akwai wata matar suna ninninka yin magunguna saboda su sha gaban uwaren gidansu. Shi ne mai maganin ya ce in tambayeki, wata ƙila a irin haka kika gamo ni da wannan matsalar ba tare da kin sani ba..."
"Wani tsinannen mai magani ne zai ƙulla min wannan sharrin?"
Ta katse shi a fusace. A zabure ta ƙwace hannunta daga cikin nashi ta dira ƙasa daga kan gadon tana zazzare idanu.
"Banyi komai ba. Ni kam babu abinda nayi na wani shirmen magani can. Mu gidanmu da muke ahlussunnah ta ina za'a bar mutum yayi wani magani? Babu abinda nayi, ba ruwana. Kar shegen da ya kuskura ya ƙulla min jakar tsaba balle kaji su bi ni da tsattsaga. Alum da bagaruwa kawai na san nayi ta tsarki da su shi yasa ka ji ni a matse, bushewar da ka ji nayi a farko kuma saboda ban haɗa da lalle wajen tsarki bane. Yanzu da na fara amfani da lalle shi yasa ka ji ni zam-zam yadda ake son ko wace mace mai ni'ima..."
Haka ta saki baki tana ta zuba shaaaaa, ta kamo wannan maganar ta saki wancan. Duk a ƙoƙarinta na wanke kanta daga maganganun da Mukhtar ya tunkaro ta da shi.
Shi dai yana ta kallonta, yana ƙara karantarta. Bai ga komai ba illah naɗe tabarman kunya da hauka da take ƙoƙarin yi. Ganin ta yi shiru tana zare idanu yasa shi ƙara kamo hannunta a karo na biyu, kusa da shi ya zaunar da ita.
"Fatima. Kinga ni magana ce nazo miki da ita na nutsuwa da fahimtar juna. Don Allah ki saurara min, ki kwantar da hankalinki, ki zurfafa tunani ki faɗa min, a cikin matan da kika sayi magani a hannunsu babu wacce ta ambata miki magana makamanciyar wannan matsalar tawa kan wani magani?"
A maimakon ta amsa, ko kuma ta nutsu ta zurfafa tunani yadda ya ce, kawai sai ta fashe da kuka. Ta ƙwace hannayenta ta fara yarfe su kamar wacce ta tsoma a ruwan zafi
"Na shiga uku! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Haskenah zargina kake yi? Daman na sani ba ka so na, ba ka ƙaunata, ka aure ni ne don kawai Fareeda ba ta jin maganarka, na sani. Amma ina so ka tuna abu ɗaya, soyayya da ƙauna ce tasa na aure ka. Ni ina son ka Mukhtar, na daɗe ina son ka, ko don soyayyar da nake maka ban cancanci irin wannan wulaƙancin da tozartawa ba."
Izuwa yanzu, zuciyarshi ta fara kaiwa ƙololuwa gurin ɓaci. Sanyayan halayen da ya aro ya yafa kan halayenshi na zafin rai tuni sun fara yin nasu wajen. Ya fara dawowa asalin Mukhtar ɗinshi mijin Fareeda.
Kamar ba shi ne yanzu ya gama ɗaga ta sama yana rirriƙewa cikin soyayya kamar jaririya ba. Wani gigitaccen tsawa da ya daka mata a take ta haɗiye kukan da take yi kamar ɗaukewar ruwan sama. Ya kalleta da jajayen idanunsa, alamun rashin gaskiya ne ƙarara a tattare da ita.
"Baza ki faɗa min gaskiya ba ko Fatima?"
"Gaskiya nake faɗa maka. Wallahi gaskiya ne nake faɗa, na rantse da Allah. ka yarda dani don girman Allah..."
Tsam ya miƙe tsaye ya fice daga ɗakin kafin ta kai ƙarshen maganganun da bai ɗauke su a komai ba illah tsagwaron ƙarya.
Ta zaci ya bar maganar kenan. Ta gyara zama haɗe da takurewa tana sauke ajiyar zuciya kawai sai ga shi ya dawo cikin ɗakin, a hannunsa takarda da biro ne.
"Hasssssskkkkkeeeh! Mmmmmmmme kakkkkkkkeeeee ƙoƙƙƙƙƙƙƙarinnnnnn yiiiiiii?"
Ta tambayeshi bakinta na rawa da wani balaƴaƴƴen in-ina a muryarta.
Gefen gadon ya zauna, ya buɗe takardar ya yago falle ɗaya, ya ɗora biron akai alamun zai fara rubutu. Ya kalleta a ɗage
"Fatima tunda kin ƙi faɗa min gaskiya na rantse da girman Allah babu abinda zai hana ni datse igiyoyin auren da ke tsakaninmu. Banga amfanin don kawai na auro ki wata ƙozai ƙozai da ke ki shiga ki fita ki hana ni kusantar matata abar ƙaunata ba. Gara ni da ke duk muyi biyu babu."
Ya sauke idanunshi ƙasa, cikin sauri ya fara rubuta
"Ni Mukhtar..."
"Na sani, wallahi tallahi na sani, zan faɗa maka gaskiyar, don ya rasulullahi kar ka sake ni Mukhtar"
Ta faɗi maganganun cikin ihun kuka na tashin hankali haɗe da fincike biron hannunsa...
*Ma su buƙatar yin sub don karanta labarin LOKACI, ba sai sun sauke app ɗin ba. Su shiga ta wannan link👇🏽ɗin suyi reg,*
https://hikaya.bakandamiya.com/
*Gurin rubuta password su saka a harhaɗe abcd da 123, misali 👉🏽 Aliya*123. Abinda baku gane ba sai ku tuntuɓeni a lambata da ke sama*
*_Hds jewelleries and more babban kamfani ne da muke bayar da kayayyakinmu akan farashi mai rahusa. Ƴar'uwa kina buƙatar ganin samfur ɗin kayayyakinmu don sayen nagari ki mayar da kuɗaɗenki gida? Ki shiga group ɗinmu ta wannan link ɗin👇🏽 Ko kuma ki tuntuɓemu a wannan lambar a kaiki group don ganin irin kayayyakinmu +234 814 496 5394*
https://chat.whatsapp.com/LpxLzmsKFFfBatQoY8q1jA
*👆🏽Domin ganin irin kayayyakin da muke sayarwa, danginsu laces, atamfofi, shadda, material, kayan kicin, dogayen riguna tsala-tsala ƴan dubai masu bala'in kyau da sauƙin kuɗi🥰🥰🥰 Ƴan kunnaye da sarƙoƙinsu masu bala'in kyau waɗanda idan kika saka za'a miki kallon zinari kika sanya🥰🥰😘😘 Kuma wani abin jin daɗi shi ne muna aika kayanmu ko ina kuma a gaggauce💃🏽💃🏽💃🏽 Muna maraba da masu sayen ɗaiɗai ko sari. Sai kun zo❤️❤️❤️*
*Kuyi haƙuri. Ku ƙara min uzuri don Allah. Wallahi wani irin rashin wuta ne muke fama da shi yanzu, sai a hankali. In sha Allah ko ɗan yaya ne zan dinga samu ina muku posting ko babu yawa. Na gode🥰🥰🥰🥰*
*Ƴar'uwa ciwon sanyi ne ya dame ki? Har bakya jin sha'awa ko ɗanɗano idan kun leƙa can babban birnin maji daɗi😘😘? Ki tuntuɓi Zee maman mujaheed +234 816 285 9027 domin siyen maganin sanyi mai kyau sosai akan farashi mai rahusa😍😍💃🏽💃🏽💃🏽 Baza kuyi da na sani ba in Allah ya yarda*
*RABON AYI*
*29*
*©Fareeda Abdallah*
*_Ƴar'uwa ki tuna, kafin saukar da ko wace irin cuta, sai da aka saukar da maganinta. Don kinyi magani da yawa baki dace ba ba shi zai sa ki yanke tsammani daga samun waraka ba. Ki gwada maganin da muke karɓa ma al'ummar Annabi SAW, wata ƙila warakarki a wannan maganin yake baki sani ba. Haihuwa kike nema? Baki taɓa yi bane ko kuwa jinkiri ne kike samu tsakanin haihuwar? Sanadiyyar planning ne kika samu jinkirin ko kuwa sanyi ne yake damunki ko haka kawai? Matsalar rashin haihuwar daga mijinki yake? Muna da ingantaccen magani garanti wanda aka gwada muka tabbatar da aikinsa, in Allah ya yarda ko me ya shafi mahaifar mace da mararta wanda ya hana ta haihuwa in dai tayi amfani da saiwoyin maganinmu za ta samu biyan buƙata da yaddar Allah. Matsalar mace ko namiji 2k ne.*
*Akwai ƙullin maganin da muke sayar da shi 500, in dai matsala ta shafi nonon mace da yaddar Allah za ki samu waraka. Mai ciki, mai shayarwa, mare shayarwa duk za su iya amfani da wannan magani. Ko da matsalar ciwon daji ne da ya shafi nono in sha Allah za ki sami waraka sanadiyyar amfani da wannan magani. Akwai garin maganin sanyi da za ki haɗa a cikin yaji, shi ma 500. Akwai ingantaccen maganin sanyi da za ki saya muku ke da Oga, 2k ne. In Allah ya yarda za ki sha mamakin yadda lafiya zai wadace ku ke da Oga, za ki ga yadda za ku dawo kamar sabbin amaren da suke mararin junansu😍.* *Akwai ingantaccen haɗin magani na gyaran nono wanda ni Fareeda Abdallah nake sayarwa, bokiti 1litter 2500, ƴar'uwa in dai za ki juri dama kunun garin maganin safe da dare, za kiga yadda ba cikowar nono kaɗai ba, hatta fatar jikinki sai ta canza, za kiyi kuɓul-kuɓul😍, sa'annan ni'ima bazai taɓa yanke miki ba in Allah ya yarda saboda irin haɗe-haɗen da ke cikin wannan magani. Ga duk mai buƙatar ɗaya daga cikin maganinnan da gaske ta tuntuɓeni ta whatsapp a 07039080978, idan kira ne a kira ni ta 09077591726. Duk jihar da kike a ƙasar nan za mu iya aika miki da maganin amma ke za ki biya kuɗin mota, har ƙasar nijar muna aikawa kan farashi ƙalilan. Don Allah ƴan'uwa🙏🏽🙏🏽🙏🏽idan ba da gaske kike yi ba kar mu ɓata ma juna lokaci.*
"Ina saurarenki."
Ya faɗa mata da fusata a muryarsa, fuskarshi a ɗaure tamau. Ganin ta ƙi magana, ta duƙar da kanta ƙasa tana ta rusa kuka.
Daƙyar ta iya sassauta kukan da take yi, idanunta na kallon ƙasa kamar wacce ke gaban surukinta. A hankali ta fara magana
"Tabbas na biya kuɗi don ayi aikin da za'a salamta Fareeda. Amma wallahi ni ban ce ayi aikin da za ka kasa kusantar Fareeda ba. Don girman Allah..."
"Idan kika sake haɗa ni da girman Allah sai na zubar miki da haƙora. Za ki tafi kai tsaye kiyi min bayani dalla-dalla na abinda ya faru ko sai na miki wani mugun shaƙa da zai sa ki fara jiyo ƙamshin mutuwa?"
Ya katse ta da faɗin haka cikin tsawa.
Ta sani Mukhtar ya daɗe da wuce saninta. Duk abinda ya ce zai aikata tabbas sai ya aikata shi. Jikinta na rawa ta buɗe baki za ta cigaba da magana ya sake katse ta a karo na biyu
"Sauka ƙasa ki zauna."
Ya faɗa cikin gadara da iko.
Ita da gadon kwanciyarta haka ta sauka ƙasa ta zauna kan dandaryar tiles tana fuskantarsa. Kamar baiwa a gaban ubangidanta.
Nishi yake ja a fusace yana kallonta. Zuciyarsa cike da wani irin takaici da baƙin cikin da ko kusa baki bazai iya baiyanawa ba.
"Wani tsinannen mai magani ne yayi miki wannan aikin?"
Da rawar jiki ta buɗe bakinta ta fara faɗa mishi tun farkon yadda al'amarin ya kasance.
_Maman Murad wata tsohuwar mai aikatau ce da Fatima tayi tun tana da cikin Ummee. Daga bisani zamansu baiyi tsawo ba bayan haihuwar Ummee, saboda su biyun da mun gamu ne da mun dace. Maman Murad ɗan banzan ƙwaɗayi da roƙo, ita kuma Fatima balaƴaƴƴen rowa da wayau. Ko da tafiyar ta ɓaɓe lokaci bayan lokaci Maman Murad tana kai ma Fatima ziyara. Haifaffiyar garin Gusau ce a jihar zamfara, amma tana zaune a hayin rigasa da ƴaƴanta da mijinta._
_Wata rana ta kawo ma Fatima ziyara sai ta cimma Ramlah a gidan, ta kawo ma Fatima wasu magunguna, a gabanta kuma suke ta maganar maganin ba tare da tunanin ita da take zaune gefe ɗaya kan kafet ba. Ko da Ramlah ta tafi, sai Maman Murad ta gyara zama ta ce ma Fatima_
"Hajiya Fatima, ni kuwa na ce da irin waɗannan magungunan da ake kawo miki na ƙila wa ƙala me zai hana in haɗa ki da Kawuna ki biya shi kuɗi ƙalilan yayi miki aikin salamta kishiya?"
"Ban gane ba. Miye kuma salamta kishiya?"
Fatima ta tambayeta da mamaki sosai a fuskarta.
Ko da Maman Murad tayi ma Fatima bayanin abinda kalmar take nufi, ta kuma kira ƙanin mamanta wanda yake aikin a waya ya ƙara yi ma Fatima cikakken bayanin yadda aikin yake, da irin nasarar da mace take samu a gidan miji idan aka yi ma abokiyar zamanta irin wannan aikin. Jikinta na rawa ta ɗauko dubu ashirin ta damƙa ma Maman Murad. Dubu goma aka ce mata kuɗin aikin, amma saboda son ayi mata zazzafan aiki yasa ta bada dubu ashirin.
Duk da zuciyarta na ƙila wa ƙalan idan aikin zai tabbata kamar yadda Maman Murad da kawunta suka faɗa, amma tana fatan ko ɗan yaya ne aikin ya ci. Babban burinta a duniya shi ne tasha gaban Fareeda ta ko wane ɓangare a zaman gidan Mukhtar.
Za ta so ganin yadda Fareeda za ta wulaƙanta a gurin Mukhtar. Shi yasa ba ta jin ƙyashin kashe ko nawa ne wajen siyan maganin da aka tabbatar mata da asiri aka haɗa shi.
Bayan kwana uku Maman Murad ta sake komawa gidan, ta tabbatar mata aikin salamta kishiya angama. Bayan aure ta zuba ido tasha kallon abinda zai faru. Saboda tsananin farin ciki kyautar dubu biyar ta ba Maman Murad.
Bayan bikinta ganin babu wani canji na rashin daɗi tsakanin Mukhtar da Fareeda sai tayi tsammanin duk magungunan da tayi asarar kuɗinta tayi. Bata san aikin ya ci ba sai da Allah ya matsi bakin Mukhtar ya faɗa mata shi fa baya iya kusantar Fareeda.
A lokacin tayi mamaki ƙwarai, domin ba irin aikin da aka ce za'a yi mata ba kenan. Amma da yake ita ɗin mai bala'in wayau ce da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 26