rabon yin aure wataƙila ma har da yara tsakaninta da Mukhtar? Ba tun yanzu ba yake bala'in burgeta. Auranta na farko dattijo ta aura, wanda ya auri wata matar kafin ita ta haifa masa ƴaƴa uku duk mata sai Allah yayi mata rasuwa. Ko da ya aureta ya aura ne da sa ran za ta riƙe masa marayun ƴaƴansa, da farko kuma rigiɗi-rigiɗi kamar zaman zaiyi daɗi a tsakaninsu. Daga bisani ta tasa su gaba da makirci da bita da ƙulli rikici ya ɓalle tsakaninta da manyan yaran biyu. Duk sa ido irin na mijin kuma ya rasa gane mare gaskiya a tsakaninsu._
_Daga ƙarshe dai dole a zaman ƴaƴan ya koma gaban yayar mijinta Hajiya Zainab, wacce ko ƙanƙani babu shiri tsakaninta da Fatima. Aure da rabo kuma wata goma sha ɗaya ta sunkuto ƴarta mace, aka saka mata sunan marigayiya uwar mijinta, Sa'adiyya, sai suke kiranta da Ummee. Wata shekarar na zagayowa ta sake haifo ƴa mace. Wannan haihuwa biyu da tayi a jere shi ya kawo sauƙin ƙiyayyar da Yar mijin ke mata, har sukan zauna inuwa ɗaya ba tare da ta caccaɓa mata baƙaƙen maganganu ba._
_A gefe guda kuma duk da waɗannan ƴaƴa biyun da ta haifa shaiɗaniyar zuciyarta bata daina bugawa duk sa'adda za tayi tozali da Mukhtar mijin Fareeda ba. A wani lokacin har baiken kanta take gani, tana ga kamar tayi sauri wajen zaɓin mijin aure. Tunda ita ta fara aure da shekara ɗaya da rabi kafin Fareeda tayi. Wata ƙil da bata yi gaugawa ba, ita Mukhtar zai gani ya ce yana so ba Fareeda ba, tun da duk inda ɗaya za taje tare take da ɗayan._
_Kwatsam kuma sai ga rasuwar mijinta bayan ta haifa masa ƴaƴa huɗu. Idan ta ce bata ji rasuwar mijinta uban ƴaƴanta ba ta yi ƙarya. Amma bayan kwaranyewar komai ta ci gaba da rayuwarta cikin walwala tare da ƙannenta biyu waɗanda ta ɗauko daga gida don su tayata zama. Da ƴaƴanta huɗu, tunda kafin rasuwar mijin ya bar wasiyar ta riƙe mishi ƴaƴanshi a gidanshi, idan za tayi aure ta ba Yayarsa Hajiya Zainab yaran ta haɗa da na hannunta ta riƙe har zuwa aurensu._
_Bayan shekara guda da rasuwar mijinta sai wannan shaiɗaniyar zuciyar ta sake yunƙurowa ka'in da na'in take ƙawata mata Mukhtar. Duk sa'adda taje gidan Fareeda ta gan shi ta dinga kwainane kenan da sunƙe-sunƙe na neman samun shiga, shi kuwa a lokacin ko kallo bata ishe shi ba._
_Ashe ba tare da sanin su biyun ba ƙaddarar aure zai iya shiga tsakaninsu a lokacin da basu taɓa tsammani ba. Lallai Allah da girma yake..._
"Tunanin me kike yi?"
Ya tambayeta da kulawa bayan ya gama cin abincin, ƙaramin kofin da ya tsiyayi zoɓo ne a hannunsa yana kurɓa a hankali yana lumshe idanu.
"Ikon Allah kawai nake tunani Aban Twince. Ummm nace ba? Ka faɗa ma Aunty Fareeda za ka aure ni?"
"Ke tsaya, wai Fareedar ce kike ce mata Aunty?"
Ya tambayeta yana dariya.
"Uhmmm ba dole in ce mata Aunty ba? Ko da na ɗan girme mata da ƙananun watanni kuma Aminiyata ce ai gaba take da ni a gidan miji, ka ga girma dole in bata a matsayinta na uwargidan farin cikin zuciyata.
Ni dai don Allah Aban twince"
Tayi ƙasa da idanunta ta haɗe hannayenta biyu alamun roƙo.
"Duk da na san ƙawata akwaita da bala'in taurin kai, duk abinda ta so kuma zuciyarta ta kitsa mata ko ba daidai bane shi take aikatawa. Na san za ka ga tashin hankali da masifarta idan ka faɗa mata maganar aurennan, don Allah kar ka biye mata.
Ka bi ta a sannu, idan tayi haƙuri ni ba da tashin hankali zan shiga gidanta ba. Alkhairi da albarka nake so mu haɗu mu gina bisa jagorancinka Haske nah! Kayi haƙuri da haukarta pls"
Lallai bahaushe yayi gaskiya, duk girma da shekarun namiji ƙaramin yaro yake zama a gaban mace. Duk tsauri da taurin Mukhtar sai ga shi salon da Fatima tayi amfani da shi ta bala'in tafiya da shi.
Bai bar gidan ba sai misalin ƙarfe tara da rabi na dare, ko sallar isha'i bai halarta ba. Ya tafi ne bayan sun gama tsara za suyi aure nan da sati uku! in dai sun samu yadda suke so babu daɗi ba ƙari.
******
Ido a buɗe Hajiya Aisha take kallon babban ɗan nata da mamaki, bayan gama sauraren duk irin maganganun da ya taho mata dasu a wannan dare. Daƙyar ta iya buɗe baki ta ce
"Aure nan da sati huɗu Malam? (Haka take kiranshi saboda kasancewarsa ɗan fari.) To wace yarinya za ka aura a cikin wannan taƙaitaccen lokacin?"
"Fatima, Fatima zan aura Hajiya. Don Allah ki saka albarka kar ki ce min a'a."
Ya ƙarasa maganar a marairaice, da damuwa sosai a fuskarsa.
"Wata Fatima kenan?"
Ta tambayeshi ba tare da damuwa da yanayin fuskarsa ba. Ita zancen auren ne ke ta bata mamaki, to wani rikici ke tsakaninshi da Fareedar da ita basu faɗa mata ba?
"Za ki santa ma yarinyar, Fatima ƙawar Fareeda. Wacce mijinta ya rasu kwanakin baya can..."
"Fatima dai Yaya? amma kam ta tabbata gagarumar munafuka kuma maciya amana ta ƙarshen zamani."
Ƙanwarsa Zubaida da tayi luf akan kujera kamar tana barci ta faɗi haka bayan ta wuntsulo daga kan kujerar ta faɗo ƙasa saboda yadda maganar ta jijjigata.
Idanu ya zazzaro mata yana galla mata harara
"Wa ya kasa da ke a wannan maganar ƴar sa'ido? Ɓace min daga nan kafin in tattaka ki."
"Yarinyar da auranta za ka taka ta Malam?"
Hajiyarsu ta tambayeshi tana jinjina kai alamun ƙarin mamaki. Sai kuma ta mayar da kallonta wajen Zubaida da ta daskare a zaune tana kallon Mukhtar.
"Shiga cikin ɗaki ki jira ni."
Tsam ta miƙe tsaye bayan ta ɗauki wayarta da ke ajiye a hannun kujera. Kamar baza ta sake cewa komai ba, sai da ta kusa shiga ɗaki ta jiyo ta kalli Mukhtar, da ɗaurarriyar fuska ta ce
"Yaya, gaskiya baka yi ba. Amma fa ka sani, duk wanda yaci amana ko ba jima ko ba daɗe tabbas amana sai ta ci shi. Fatan alkhairi."
Da saurin gaske ta shige cikin ɗaki ta banko ƙofar ganin ya miƙe a zafafe yana muzurai.
"Hajiya kina ganin Zubaida..."
"Zauna."
Uwar ta bashi umarni fuskarta a ɗaure.
A sanyaye ya koma inda ya tashi ya zauna, ya saukar da kanshi ƙasa, zuciyarsa cike da addu'ar Allah yasa dai kar Hajiyarsa ta hana shi auran Fatima, don gaskiya ba ya jin zai iya bin umarninta a wannan karon.
"Me Fareeda tayi maka?"
"Ba komai."
Ya amsa kai tsaye.
Girgiza kai tayi, kafin ta sake cewa
"To me yasa za ka auro mata ƙawarta ko in ce aminiya a matsayin kishiyarta?"
"Hajiyaaaa.... wannan auren fa ba haramun bane. Banzar magana ce kawai ta Malam bahaushe da yake wani cewa ana barin halas ko don kunya. A matsayina na namiji mijin mata huɗu na ga Fatima tayi min, ina niyyar auranta. Kuma na faɗa ma Fareeda bata tayar da hankalinta ba, har tayi min fatan alkhairi. To don Allah Hajiya menene kuma na wani damuwa ko ƙananun maganganu?"
"Babu! Fatan alkhairi Malam. Hmmm! Allah ya jiƙan Alhaji (Mahaifinsu Mukhtar da ya rasu shekaru shida baya tun Fareeda na amarya) Idan ka bar nan sai kaje gurin ƙanin mahaifinka yayi maka jagora."
Ta faɗa har lokacin babu walwala a fuskarta.
Ya buɗe baki zaiyi magana ta ɗaga mishi hannu alamar dakatarwa.
"Maganar da ka zo don muyi mun gama ta, kana iya tafiya. Dare yayi, kwanciya zanyi. Allah ya bamu alkhairi."
"Ameen."
Ya amsa jikinsa a sanyaye, yana ta kallonta amma ta hana shi sake magana. A dole ba don yana so ba ya miƙe ya kama hanyar fita daga falon.
"Malam"
Ta kira sunanshi.
Ya juyo da sauri zai dawo ta sake dakatar da shi.
"Ka tsarkake zuciyarka, kayi komai don Allah. Idan ba haka ba tabbas ƙarshen ko wace gaugawa da-na sani ce da cizon yatsa, don daga shaiɗan take. Ka gaida Fareeda, sati mai zuwa ina nemanta."
*A dai dinga yi ana siyan data a guri na😘😘😘❤️👇🏽*
*_Aminci + Ƙarko Data Services_*
*_Kina/kana buƙatar Datar MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE mai matuƙar aminci da ƙarko? Wanda za ki daɗe kina sauke abubuwa da kallace-kallace ba tare da yayi saurin ƙarewa ba?_*
Ga farashin datarmu a sauƙaƙe👌🏽 ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai a tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online a kira ni ta 09077591726.
*MTN data price👇🏽*
500 MB 👉🏽 N150
1GB 👉🏽 N280
2GB 👉🏽 N550
3GB 👉🏽 N800
4GB 👉🏽 N1100
5GB 👉🏽 N1350
6GB 👉🏽 N1600
*AIRTEL data price👇🏽*
300MB 👉🏽 120
500MB 👉🏽 150
1GB 👉🏽 N300
2GB 👉🏽 N600
5GB 👉🏽 N1350
10GB 👉🏽 N2500
20GB 👉🏽 N5000
*GLO data price👇🏽*
1GB 👉🏽 N500
2.9GB 👉🏽 N1000
4.1GB 👉🏽 N1500
5.8GB 👉🏽 N1950
*9MOBILE data price👇🏽*
500MB 👉🏽 N500
1.5GB 👉🏽 N1000
2GB 👉🏽 N1250
3GB 👉🏽 N1600
4.5GB 👉🏽 N2000
Hallau muna tura katin waya, katin startimes, go.tv, e.t.c👌🏽
*_Namu ba irin nasu bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_*
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*11*_
Sosai kanshi ya ɗauki zafi, ɓacin ran Hajiyarsa ba abu bane da zai murje fuskarsa ya shanye kamar babu komai.
Daga yadda ta amsa mishi ya san ta dai amince ne kawai, don ba ta da yadda za tayi. To amma shi ya zaiyi ne? zancen gaskiya bai fara neman auren Fatima don ya fasa ba.
Shi sai yau da suka yi ido biyu maganganu suka shiga tsakaninsu ya ji tabbas aurenta wajibi ne a gare shi. Aurenta shi ne zai zamo babbar maslaha tsakaninshi da Fareeda.
Kawai dai zai kwantar da kanshi ya cigaba da lallaɓa Hajiya yana bata haƙuri, ita ba mace bace mai tsananin riƙo, ya san cikin ƙanƙanin lokaci za ta haƙura ta yafe mishi.
Ganin dare ya fara yi sai bai yi yunƙurin zuwa gurin ƙanin mahaifinsa ba, kai tsaye ya nufi gida. Gajiya ke nuƙurƙusarsa yana mazewa, da yake ya sa maganar auren a ranshi yana so ayi komai da zafi-zafi, yadda ya shawo doguwar tafiyarnan ai da babu abinda zai fitar da shi a yau dai sai zuwa masallaci, ko kuma larura wacce ba'a fatan samuwarta.
Ganin wutan falon a kashe shi ya alamta mishi Fareeda ta kwanta, ya taɓe baki, ko kaɗan bai ji ba daɗi ba yadda yake ji a baya idan yana gari ya fita ya dawo ya tarar ta kwanta bata jira shi ba.
Kai tsaye ɗakinsa ya nufa, yayi tunanin zai tarar da ita ciki sai yaga saɓanin haka.
"Ma sha Allah"
Ya furta a fili cikin jin daɗi.
Ya gaji ƙwarai, hutu yake buƙata. Kuma a yadda yasan halin Fareeda kamar yunwar cikinsa shirun da tayi masa ɗazu yasan akwai rikici da bala'in tashin hankalin da zai biyo baya, duk masifa irin tasa sam ba ta tsoronsa a wasu lokuta, kuma bakinta bai cika mutuwa akan ko ma menene ba, sai dai kawai tayi shiru ba don ta rasa abin cewa ba.
Ya shirya mata, bai jin tsoron komai, duk wani rikici da za ta girgizo dai-dai yake da ita. Ita tasan a faɗa da masifa ya dame ta ya shanye.
A darennan ne dai yake buƙatar hutu, gara da ta bashi iska sa haɗu da safe, in yaso suyi duk wacce za suyi, ko ta ware ko ta warwaraye, ya shirya ma ko wanne a cikin abu biyun.
A shekarunsa na tashen ƙuruciya bazai sake yarda ya ɗauki wani zafin taurin kai da rashin jin maganar Fareeda ba. Ya kai maƙura, iya haƙuri da kawar da kai yayi, yanzu lokacinsa ne na ɗaukar matakin da yaga ya dace.
A gurguje yayi wanka, ya canza kayansa zuwa na barci, ya bi lafiyar gado. Yana kwanciya kiran Fatima na shigowa cikin wayarsa, da mamaki a fuskarsa yake kallon kiran.
Ya rasa dalilin da yasa shi jin babu daɗi a ransa, me kuma take nema bayan ɗazunnan suka rabu?
Ƙasa-ƙasa ya ja tsaki, ya danna maɓallin rage ƙara ya juya ma wayar baya. Addu'ar kwanciya barci yayi ya shafe jikinsa gaba ɗaya, yana runtse idanu babu ɓata lokaci nannauyan barci yayi awon gaba da shi.
Tun da ya shigo da mota cikin gidan tana jin shi, a wannan lokacin tana zaune ne kan darduma tana jan casbaha, bayan ta idar da shafa'i da wuturi.
Buɗe ƙofar falon da yayi yayi daidai da wani irin bugawa da ƙirjinta yayi, da sauri tasa hannun hagu ta dafe saitin zuciyarta tana jan Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.
Sai wani bahagon tambaya ya shigo cikin zuciyarta.
"Yanzu fa Mukhtar ɗinta daga gurin Fatima yake ko?"
"Uhmmm!"
Ta faɗa a fili, zuciyarta na sake tuna mata tsakaninta da Fatima. Aminiyarta ta ƙud da ƙud!
Fatiman da a baya babu jituwa ko na kwabo tsakaninsu da Mukhtar, wai ita ce yanzu har suka ƙulla za suyi aure...
Numfashi ta fara ja tana saukewa sama-sama cikin sauri saboda wani irin bala'in zafin kishi da takaicin cin amanar da suka yi mata.
Ta lumshe manyan idanunta da daga yammacin nan zuwa dare suka kumbura sosai, ga wani irin nauyi da suke mata saboda yawan kukan da tayi.
Ita ba jahila bace, ta sani babu haramci a cikin aurensu. Amma tsakani da Allah sun ci amanarta, ta yarda da su biyun sosai da sosai, aure tsakaninsu biyun abu ne da ko a mugun mafarki bata taɓa hasashen zai iya faruwa ba.
Wasu zafafan hawayen suka sake silalowa daga idanunta. Zuciyarta cike da saƙe-saƙen tunanika da tambayoyi mabanbanta.
"To wai shin, ta yaya aka haihu a ragaya? ko dai daman tuntuni akwai kyakkyawar mu'amala a tsakaninsu ita ce suke ninke ta a baibai saboda sun maishe ta sakarya?
Inaaa... Za ta iya rantswa Babu ! Duk da Fatima gwana ce gurin ɓoye-ɓoye, da iya yima ƙarya kwaskwarima don ta zama gaskiya.
Shi Mukhtar ba mutum bane mai fuska biyu, ya sha ce mata shi fa ya tsani Fatiman nan, ruwan munafukai gare ta. Kuma yadda yake maganar a kallo ɗaya za'ayi masa asan daga zuciyarsa ne, iya zallar gaskiyar abinda ke ransa yake faɗa.
Ko rantsuwa tayi babu kaffara a baya babu wata dangantakar arziki a tsakaninsu, a cikin kwanakin nan ne dai suka ƙulla dangantakar da har ta miƙa za suyi aure.
Saboda rashin jin maganarta ne Mukhtar zai auro ƙawarta don ya girgiza duniyar nutsuwa da kwanciyar hankalinta? Tayi wani murmushi mai ciwo, tabbas ya ci galaba a kanta.
Wani ƙaƙƙarfar kuka da ya ƙwace mata yasa da sauri ta cukwuikwuiye hijabinta ta cusa a bakinta, don kar sautin kukan ya fita har ya jiyota daga ɗakinsa.
"Ƴar'uwa, yanzu ba lokacin da za ki zauna kina ɓata lokacinki akan kuka bane. Ki tashi tsaye da ibada, ki ninka ki ƙara ninkawa a cikin nafilfilin da kike yi. Allah da ya halicce ki ya halicce su biyun shi za ki fuskanta ki kaiwa kukanki, idan akwai zalunci a ciki da gaugawa zai saka miki, domin shi Allah SWT mai saurin karɓar addu'ar wanda aka zalunta ne."
Maganganun da ƴar'uwarta Baby tayi mata ɗazu gab da za su bar gidan suka dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta kamar a lokacin take faɗa mata.
"Fareeda shalelen ƙanwata, ki kwantar mana da hankalinki don girman Allah. Kishiya ko? Anyi ma dubu bata kashe su ba ke ma baza ta kashe ki ba.
Idan matsananciyar damuwa ta turnuƙo ki ki tuna mu ƴan'uwanki da muke tsananin ƙaunarki, idan kika bari wani mummunan ciwo ya kama ki mu muke da asara ba Mukhtar ba.
Ki yawaita istigfari domin Allah ya yafe miki kura-kuranki, wataƙil laifin da kika aikata ne yasa Allah ya jarrabeki da wannan lamari ko za ki hankalta ki dawo cikin hayyacinki. Ki tuba ma Allah, domin shi ɗin mai karɓar tuban bayinsa ne ako wane lokaci.
Ki dinga faɗin Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel. Ki ta maimaita Lahaula walaa ƙuwwata illa billah. Kiyi kuka a gaban Ubangijinki Fareeda, ki kira shi da tsarkakan sunayensa waɗanda idan an kira shi da su yake amsawa. Ki roƙe shi da kyawawan sunayensa waɗanda idan an roƙe shi da su yake bayarwa. Ki yawaita maimaita Ya Allah ka jiɓanci lamurana, ka zama gata na, ka shirye ni shiriya madaidaiciya, ka kawo daidaito tsakanina da mijina. Ya hayyu ya ƙayyumu ka kawar da shaiɗan ko shaiɗaniyar da take tsakaninmu."
Shawarwarin Aunty Murja gareta kafin su bar gidan.
Shi kuwa Mustapha murmushin ƙwarara gwuiwa yayi mata, ya riƙo hannunta na dama ya riƙe a cikin nasa.
"Fareeda, mu maza muna so idan za muyi aure matayenmu na gida su dinga hauka da nuna mana tsananin kishinsu, hakan yana sa muyi ta jin daɗi muna ƙara manna musu hauka. Duk zafin da za kiji a zuciyarki kar ki kuskura ki nuna ma Mukhtar kin ji ko?"
Daƙyar ta iya ɗaga mishi kai.
"Na san fa ƙanwata Fareeda za ta iya, don ita ɗin mai aji ce. Duk tsananin son abu da take yi idan ya bata haushi tana aje shi gefe ɗaya ta cigaba da harkokinta lafiya kamar wannan abu bai dameta ba. Ko ta canza daga wannan halin?"
A dole ta saki murmushin yaƙe ga hawaye kaca-kaca da fuskarta. Ta girgiza kai alamar bata canza ba.
"Yauwa Luvly Sister. To yanzu amfanin wannan halin ya zo, ki yi mishi biyayya, amma ki kawar da kai a lamarinsa kin ji ko? Akwai addu'o'in da zan tura miki ta whatsapp, ki dage ki tayi, mu ma za mu taya ki. Idan kika fuskanci Ubangiji tabbas zai fuskance ki Fareeda."
Tunanin kyawawan maganganu da shawarwarin da ƴan'uwanta suka ba ta ɗazu kafin ficewarsu daga gidan yasa ɗif ta ɗauke kukanta.
A nutse ta miƙe tsaye, hijabin jikinta ta cire ta ajiye a gefen gado. Banɗaki ta koma ta sake ɗauro alwala.
A wannan dare, kusan kwana Fareeda tayi tana sallah, idan ta gaji, sai ta zauna tayi ta istigfari, hailala, tasbihi, salatin Annabi, sai ta cigaba addu'o'i cikin kuka take roƙon Allah ya daidaita mata al'amuranta.
Ƙarfe uku da minti biyar wani nannauyan barci yayi awon gaba da ita nan kan darduma. Barcin da ya zo mata da wani irin nutsuwa, kwanciyar hankalin da bata taɓa tsammanin samunsa a cikin ƙanƙanin lokaci haka ba. Lallai da gaske ne duk wanda ya dogara ga Allah ya isar masa.
Ƙarfe huɗu da minti arba'in daidai ta farka da salati a bakinta, idanunta na sauka kan agogo tayi saurin miƙewa zuwa banɗaki ta sabunta alwalarta.
Malamin islamiyarsu ya taɓa faɗa musu lokacin ketowar alfijir lokaci ne na karɓar addu'ar bayi.
Da nutsuwa ta cigaba da nafilfili tana addu'o'i a cikin sujada har aka kira sallar farko. Ta miƙe tayi raka'atanul fijr, aka kira sallar asubah ta gabatar da ita. Tana cikin yin azkhar ɗin safe wani nannauyan barci ya dinga fisgarta, daƙyar ta iya ƙarasawa tayi addu'a tabi lafiyar gado. Tana jin zuciyarta sakayau, kaso tamanin cikin ɗari na tashin hankalinta Allah ya yaye mata.
******
Tana idar da sallar asubahi ko addu'a bata tsaya yi ba ta tafi ɗakin da ƙannenta suke kwana.
Ta tarar da su kan dadduma ne, suna Azkhar, tsananin zaƙuwar da tayi suyi maganar da ke tafe da ita ta kasa jira su gama, umarnin katse Azkhar ɗin tayi musu, ta ce magana za suyi.
Hankali tashe suka yi addu'a a gurguje, suka tattara nutsuwa da hankalinsu kaf zuwa gareta.
Cikin hikima da yi ma zance kwaskwarima ta faɗa musu maganar za tayi aure, kuma Mukhtar za ta aura. Ƙure su da kallo tayi tana jira taga yanayin da za su nuna da irin maganganun da za su furta.
Sai taga gaba ɗaya su biyun shiru suka yi suna kallonta da matsananciyar al'ajabi da mamaki a fuskokinsu, kamar sun ga wata sabuwar halitta, bakunansu a buɗe.
Haushin yadda suka tsaya kallonta bayan tsawon daƙiƙun da ta ɓata tana faɗa musu maganar aurenta kawai sai ta ja wani dogon tsaki, ta daka musu tsawa cikin fushi ta ce
"Wani irin iskanci ne za ku tasa ni gaba da kallo kamar baku sanni ba?"
A tare ƙannen nata suka yi firgigit kamar masu barcin da aka sheƙa ma ruwan sanyi, sai kuma wannan ta kalli wancan wancan ta kalli wannan, aka rasa wacce za ta fara cewa komai.
Cikin hargagi da masifa ta cigaba da cewa
"Wallahi tallahi idan baku ce wani abu ba sai na ci mutuncinku da asubahinnan..."
"Kiyi haƙuri Aunty."
Suka haɗa baki gurin faɗin haka da damuwa a fuskokinsu.
Jiddah ce ta ɗan motsa tana jin yadda mazaunanta suka yi wani irin tauri kamar wacce ta shafe awoyi a zaune, ta kalli Fatima da take ta huci na ɓacin ran da suka guma mata, da sanyi a muryarta ta ce
"Aunty Fatee, Ni fa wallahi na yi shiru ne ina warware maganganunki, kamar ban fahimci me kike magana akai ba.
Wai kina nufin Yaya Mukhtar mijin Aunty Fareeda aminiyarki shi za ki aura nan da ƙanƙanin lokaci?"
Kafin ta amsa sai da ta ƙara haɗe gabas da yamma ta murtuke fuska don kar su kawo mata wargi, kar ma dai Jiddah ta ji labari. Gara Salma tana nuna jin tsoronta a wasu lokutan.
"Eh! ƙwarai! Mukhtar zan aura, shi ne yazo gidannan jiya da daddare..."
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Me ya shiga cikin hankalinki Aunty? Wannan wane irin mummunar saɓo ne kike ƙoƙarin aikatawa?"
Jiddah ta jefa mata tambayoyin fuskarta na ƙara bayyana matsanancin mamaki da firgici.
Kallon ƙasa da sama ta watsa mata, ta san halin Jiddah sarai, idan bata yi mata na mahaukata ba baza ta ƙyaleta salin-alin ta aikata hidimar gabanta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba.
"Ubanki ne ya shiga cikin hankalina, Jiddah na ce Babanki ne ya shiga cikin hankalina. Ina ruwanki da rayuwata? Da kike cewa zan aikata saɓo uwar me muka haɗa da Fareedar da ya wuce ƙawance da zaman unguwa ɗaya? Ina haramci a cikin aurena da mijinta? Wallahi akan maganar nan na shirya ja da ko uban wanene, duk wanda yasan bazaiyi fatan alkhairi ba ya rufe min ɗoɗɗoyan bakinshi, idan ba haka ba kuwa za mu hau sama mu faɗo da ko wane ɗan iska. A duniyar nan kakaf ban cire miki hula ba babu wanda ko wacce ta isa haramta min abinda yake halas a gurina..."
"Kiyi haƙuri Aunty, Allah ya sanya alkhairi."
Salma ta faɗi haka cikin sanyin murya, zuciyarta cike da tsoro da mamakin Yayar tasu.
Ita kuwa Jiddah tun da ta hangame baki ta ɗora hannu akai bata sauke ba har Fatima taja musu wani dogon tsaki ta fice daga ɗakin cikin fushi kamar za ta tashi sama.
"Amma dai wallahi ke banza ce Salma. Ina wani alkhairi a lamarin cin amana da har za ki ce mata Allah ya sanya alkhairi..."
"To me kike so in ce Jiddah? kina ganin yadda ta ɗauki zafinnan tsaf za ta iya rufe mu da duka. Kin ji dai ta ce ta shirya ja da uban kowa a duniyar nan. Ba gara da na faɗa mata hakan ta fice ba tare da tashin hankalin ya fi haka ba? Taje can da yawarta, kila rabon fige kazar wahala ke kiranta ga auren mijin Aunty Fareeda."
"Ai Wallahi ƙarya take yi, maganganunta a cika baki da zancen banza na ɗauke su. Inna zan kira yanzunnan in faɗa mata halin da ake ciki, baza mu zuba idanu ta janyo mana zagi da tsinuwa a cikin gari ba."
Jiddah tayi maganganun cikin ɓacin rai tare da janyo wayarta, ta buɗe wayar kenan buf Fatima ta dawo cikin ɗakin kamar an jefo ta.
Kai tsaye gurin Jiddah ta nufa a gaggauce ta fisge wayar hannunta, ta soke a haɓar zani sannan ta riƙe ƙugu tana kallonsu cikin wani irin fushi da basu taɓa ganin tayi irinshi ba.
"Ashe daman ku ɗin ƴan iskan yara ne matsiyata ban sani ba nake zaune da ku ina taimaka muku?"
Taja wani ƙaƙƙarfan ƙwafa, ta cigaba da cewa
"To duk maganganun da kuka yi ina laɓe a bakin ƙofa ina saurarenku.
Har da ke Salma da nake miki kallon mutumiyar kirki ashe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 26