wulaƙance na fitar da ke?"
Ai a saba'in Fatima ta fice daga falon. Zuciyarta cike da mamakin wannan irin murɗaɗɗen hali na Mukhtar!
Shi kaɗai ya tsaya a tsakiyar falon yana ta safa da marwa. Zuciyarsa sai wani irin tuƙuƙi take yi na ɓacin ran maganganun da Fareeda tayi mishi waɗanda ƙarara suke nuna mishi bata damu da shi da lamuransa ba.
Lallai zai nuna mata bata isa ba, son da yake mata ba shi zai ba ta lasisin da za ta fara wasarere da al'amarinshi ba.
Kuma zai tabbatar mata har yanzu yana nan a zazzafan Mukhtar ɗinnan da ta sani, auren Fatima da ya ƙaro bai sa yayi laushi ba.
A fusace yaje ƙofar ɗakinta ya murɗa hannun ƙofar domin suyi duk wacce za suyi sai ya tarar da kofar a rufe.
Dogon tsaki yaja, ya shafa aljihunsa yaji makullin motarsa na ciki don haka ya fice daga falon. Motarsa ya hau ya fice daga gidan ba tare da ya koma ɓangaren Fatima da take tsaye jikin window tana kallon harabar gidan ta ɓangaren Fareeda ba, a zuciyarta take lissafin mintunan da ya ɗauka bayan fitarta, tare da shan alwashin ko ana ha maza ha mata sai ta rama wannan abu a ranar girkin Fareeda.
Ko da ya fita daga gida kai tsaye unguwar dosa ya nufa gidan mahaifiyarsa. Bai tarar da ita a falo ba, sai ya zauna kan kujera yasa hannaye biyu ya tallabe ƙeyarsa, ya ƙura ma guri ɗaya ido cikin zuzzurfan tunani.
"Lafiya? Tunanin me kake yi haka ina ta sallama baka ji ba?"
Hajiya ta tambaye shi da kulawa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. A hankali ya ɗan zame zuwa ƙasa ya fara gaisheta a ladabce.
"Ya Fareeda da mazajena? Allah yasa dai lafiya suke?"
Ta tambayeshi bayan ta amsa gaisuwarsa.
"Lafiyarsu ƙalau Hajiya..."
"To tunanin me kake yi?"
"Babu komai"
Ya amsa a kasalance.
Ƙure shi tayi da kallo tana ganin yadda ya ɗab faɗa a idanunta. Shi kam ko irin kumarinnan na angwanci baiyi ba.
Tsakanin ɗa da uwa sai Allah. Karo na farko da taji tausayinsa ya ɗan ratsa ta tun bayan da ya fara rugu-rugun neman aurensa.
Nasiha mai ratsa jiki ta fara yi masa a tausashe, cikin hikima irinta manya da balagar iya magana. A fakaice tana ƙara nunar mishi da muhimmancin adalci a cikin iyali. Da kuma hanyoyin da zai bi wajen gujewa zama munafuki a tsakanin matan nashi guda biyu.
Sosai ya samu nutsuwa, shi da yaje gidan zuciyarsa danƙare da ƙunci sai ga shi ya samu nutsuwa da walwala.
A masallacin ƙofar gidan yayi sallar magriba da isha'i, sannan yayi mata sallama ya kama hanyar komawa gida.
A Taraba suya ya tsaya ya sayi kaza, guda ɗaya daban sai kuma ya sayi rabi itama aka naɗe ta daban. Exotic ya siya babba da ƙarami ya shige cikin motarsa ya bar gurin.
Ko da ya isa gida, kai tsaye ɓangaren Fatima ya nufa. Da ledojin biyu riƙe a hannayensa. Sallama yayi ya shige cikin falon, fuskarsa yalwace da fara'a.
Tana zaune akan kujera tayi kwalliya daidai gwargwado. Jikinta sanye da kayan barci, wayarta ce riƙe a hannunta tana dannawa.
Ganin fuskarsa a sake yasa ta cewa
"Oyoyo Hasken zuciyar Fatimah"
"Amarya ƴar shagali, amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Hutawa ake yi ne?"
Yayi maganar da salon tsokana yana ƴar dariya. Ya nemi guri a gefen ƙafafunta ya zauna.
Da sauri ta janye ƙafafun ta saukar zuwa ƙasa, da murmushi a fuskarta ta ce
"Amare dai suna can inda suke! Mu kam maneji muke yi..."
"Maneji? Me yasa kika ce haka?"
Ya tambayeta da mamaki.
"Maneji mana Haskenah! Wace irin amarya ce har yanzu Ango bai biya bashin kazar ta na amarci da yayi alƙawarin biya ba?"
Ta faɗi maganar a wasan dare tana ƙara buɗe hancinta sosai tana sake shaƙar ƙamshin gasasshiyar kazar da take ji tun bayan shigowarsa.
Dariya ya ƙyalƙyale da ita, a zuciyarsa yake yaba girman rainin wayau irin nata. Wato duk kwanaki ukun da yayi a ɗakinta bata san tayi ƙorafin kaza ba sai yanzu da ta ji ƙanshin ya taho da kaza.
Har da yayi niyyar mutsuke fuska ya hanata kazar yaga in tana da yadda za tayi da shi. Sai kuma ya tuna girman hakki da ɗazunnan Hajiya ta gama tunasar da shi, ledar da aka ƙunshe rabin kaza da ƙaramin lemun exotic ɗin ya miƙa mata.
"To ki kwantar da hankalinki. In dai kaza ce tasa kike ganinki a amaryar maneji ga ta na kawo miki, kici ki more, ke kaɗai ba tare da Ango ya miki giɓi ba."
"Hmmm! To na gode."
Ta faɗa da fuska ba yabo ba fallasa. Ledar da ya bata ta karɓa ta kalla dakyau, sai kuma ta kalli ɗayar ledar da take ajiye a gefensa taga ai naɗin ya fi girma.
Ba tare da wani tunanin ya kamata taje kicin ta ɗauko faranti ba ko kuma ta bari ya fita kawai sai ta warware naɗin kazar tun a nan gabansa.
Kallo ɗaya tayi ma naman ta gane rabin kaza ce. A raunane ta ɗaga idanu ta kalle shi
" Haskenah? Kana nufin a matsayina na amarya ban ci arzikin da za ka sayo min gudar kaza ba sai rabi?"
"Ikon Allah"
Ya faɗa da mamaki, bai bata damar cewa komau ba ya cigaba da cewa.
"Haba Fatima, ki dinga jin tsoron Allah mana. Fisabilillahi tunda dai kazar nan ba addini bace ya kamata ki karɓi abinda ya samu. Kuma in ba neman tayar da zaune tsaye ba duk kwanaki ukun da nayi anan baki tuna da wata kaza ba sai yanzu da kika ji ƙamshin na shigo da kaza?"
Shiru tayi mishi, ta duƙar da kanta zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Duk yadda kazar nan take ta tururi da nasha-nashan mai ga uban kayan haɗin da aka zuba wajen gasuwarta ji tayi sam bata burgeta ba.
Saboda Allah da Annabi ita da Fareeda wacece ta cancanci gudar kaza? Da ganin waccan babban ledar kaza guda ce ko kuma ɗaya da rabi, sai ita ne saboda ya raina ajinta zai kawo mata rabi?
Ganin yadda take ta cika tana batsewa yasa shi ɗaukar ɗaya ledar ya miƙe tsaye tsam! So take ta ɓata mishi rai a darennan shi kuwa gaskiya bai shirya ma hakan ba.
Nasihar Hajiya yayi tasiri ƙwarai a zuciyarsa. Tunda ya tara mata biyu to dole sai ya ninninka haƙurin da yake da shi.
"Allah ya huci zuciyarki Fatima. Kiyi haƙuri, ki daure ki ci rabin kazar. Gani nayi ke kaɗai ce anan shi yasa na siyo miki rabin kaza.
Ita kuma Fareeda ga ta, ga yara, ga kuma ni da zan kwana a gurinta. Kuma ma dai gurin sayen kazar nan wallahi ko kusa ban tuna da kina bi na bashin kazar amarci ba, amma ki ci rabin, ki yi haƙuri ki sake biyo ni bashin rabin. In Allah ya yarda in girki ya zagayo kanki zan biya wannan bashin.
Sai da safe."
"Hmm! Ba komai, Allah ya tashe mu lafiya."
Ta amsa a cuccushe.
Har ya nufi ƙofar fita daga falon sai kuma ya koma ciki. Nasihar mahaifiyarsa ya tuna, ɗazu ta jaddada mishi lallai haƙƙi ne da ya rataya a wuyanshi in dai yana da yadda zaiyi yayi ƙoƙarin saka ko wace mace a cikin su biyu cikin farin ciki.
Ledar hannunsa ya ajiye kan hannun kujera ya karasa kusa da ita ya durƙusa a gabanta.
Hannayensa biyu ya ɗora kan gwuiyawunta yana kallon fuskarta, ɗan girgiza kai yayi, sai ya sakar mata lallausan murmushi.
Ya tausasa murya sosai kamar saurayi a gaban budurwar da yake mutuwar so ya ce
"Haba Fatina, Haba Fatin Haskenta. Haba Amaryata ƴar shagali na. So kike in tafi can in kasa barci saboda barinki da nayi cikin ƙunci? Don Allah ki ɗan yi min murmushi mana ko na tafi da hoton kyakkyawar fuskarki a zuciyata."
Tun kafin ya rufe baki ta sakar mishi faffaɗan murmushi kamar bakinta zai yage.
Ledar naman hannunta ya karɓa ya ajiye a gefe, ya miƙar da ita tsaye, a slow motion da salo irinna indiyawa ya janyota jikinsa ya rungume. Wani abu da tun ranar farko da ta shigo gidan bai sake bari ya shiga tsakaninsu ba
Luf tayi a ƙirjinsa tana jin wani irin sanyin daɗi da nutsuwa yana kwarara a zuciyarta. Tana son Mukhtar, Allah ya sani tana son shi. Duk irin ɓacin ran da ya cusa mata a cikin kwanakinnan ƴan waɗannan kalaman da rungumar nan duk sun share wani fushi da take yi da shi. Lallai da gaskiyar bahaushe da ya ce
"So hana ganin laifi."
Tsawon wasu daƙiƙu yana rungume da ita sannan ya sake yi mata sallama. Ya sumbaceta a laɓɓa ta mayar mishi da martani cikin rawar jiki.
Ya ɗauki ledarsa ya fice suka rabu tana farin ciki, bayan ta raka shi har bakin ƙofar falonta.
Yana fita ta kulle ƙofar, kamar ƴar tsuntsuwa ta fara daka tsalle a tsakiyar falon tana ɗebo shoki tana watsawa, zuciyarta cike da farin cikin irin rabuwar da suka yi ita da Haskenta Mukhtar a wannan dare.
Ko da yaje ɓangaren Fareeda, wani abin mamaki sai ya tarar da ƙwayayen lantarkin falon duk a kashe, sai wani mai duhu guda ɗaya da ta bari a kunne.
Kan teburin cin abinci ya hanga idanunsa. Sai yaga sabbin kuloli masu bala'in kyau da tsada ajiye akan teburin. Da saurin gaske ya ƙarasa gurin, ledar hannunsa ya ajiye a gefe ya buɗe babban kular abincin.
Farar shinkafa ce da aka dafa ta tayi wara wara da koren wake da karas, yana buɗe kular miyar ƙamshin soyayyar miyar stew ya daki hancinshi. A gefe guda kuma ga yankakken kabeji nan da albasa a cikin wani ɗan madaidaicin kwanon tangaras mai murfi.
Muƙut ya haɗiye miyau. Duk yunwar da yake ji bai tsaya cin abinci ba ya nufi ɗakinsa, a tunaninsa zai tarar da ita a ciki ta yi ƙayataccen kwalliyar barci tana jiran dawowarsa, sai yaga wayam.
Ga dai gadonshi nan lafe da sabon zanin gadon da bai taɓa ganinshi ba. Amma ya duba ko ina ba ta a cikin ɗakinshi.
Da sassarfa ya fita zuwa ɗakinta, wani abu da ya bashi mamaki kuma ya kashe mishi jiki shi ne ƙofar ɗakin Fareeda kulle yake gam da makulli.
A hankali ya fara ƙwanƙwasawa, amma har ya kwashe mintuna uku yana ƙwanƙwasawa ko motsinta bai ji ba balle ya saka ran za ta buɗe mishi.
Hakanan ba don ransa ya so ba yaja sanyayar ƙafafunsa ya koma wurin teburin cin abincin, zuciyarsa cike da tunanin ko me yasa Fareeda ta kulle ɗakinta? Shi har ga Allah ya ma manta a yadda suka rabu da ita ɗazu...
Promo! Promo!! Promo!!! A baya tana sayar da maganin 4k ne. A yanzu ta sauƙaƙa shi zuwa 2k. Za ta rufe wannan garaɓasar ne a cikin sati ɗaya kacal! Ƴar'uwa me kike jira? Maganin nata ya samu shaidar aiki ingantacce kuma da gaugawa ake ganin biyan buƙata in sha Allah. Idan kina fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin ina mai baki shawara kiyi gaugawar siyan maganin Zee Maman Mujaheed👇🏽
Ciwon gabobi, ciwon mara, fitar farin ruwa, kaikayi gaba, rashin Sha'awa, rashin kuzari gare ki ko ga namiji, rashin ni'ima, rashin haihuwa, kurajen jiki ko na gaba, jin Zafi yayin saduwa. Maganinta cikin sauƙi kuma a gaggauce yake magance duk waɗannan matsalolin. Ki tura kudin maganin ta wannan account ɗin da ke ƙasa, sai ki tura mata shaidar biya da garin da kike ta lambar wayarta👉🏽0 816 285 9027 Ga kuma acc ɗinta👇🏽
3968303018
Zainab Shu aibu
Fcmb
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*21*_
Duk da matsananciyar yunwar da yake ji, ɗan kaɗan ya tsakuri abincin ya kora da ruwa. Duk ƙamshin da naman yake baɗawa ko buɗe ledar baiyi ba balle ya ɗanɗana.
Abu ɗaya da ya iya yi shi ne saka ledar naman a cikin firij, saboda kar ya canza ɗanɗano zuwa safe tunda akwai kayan haɗi a ciki.
Yana gama cin abinci ya shige cikin ɗakinsa. Hanci ya buɗe sosai ya shaki wani ƙamshi mai bala'in daɗi na turaren wuta, wanda a ɗazu sa'adda ya shiga duba Fareeda hankalinshi yayi gaba, sam bai ji ƙamshin ba.
"Hmmm! Fareeda ba dai son ƙamshi ba."
Ya faɗa a fili sa'adda ya buɗe banɗakin nasa ya ji ƙamshin turaren wutan ya daki hancinshi.
Yana gama biyan buƙatarsa bai ɓata lokaci wajen yin shirin barci ba, ya gama komai ya canza ƙwan lantarki zuwa mai duhu ya bi lafiyar gado.
Jikinsa a saɓule, wayarsa ya janyo ya danna mata kira, nan take kamfani suka faɗa mishi wayar a kashe take. A dole ya haƙura ya kwanta ba don ransa ya so hakan ba.
Allah ya sani yau ya saka ran jin ɗumin jikinta, yayi kewarta, irin sosai ɗinnan. Sai a lokacin ma yake tunawa ashe rabonshi da ita tun dawowar da yayi ya zo mata da zancen zai auri Fatima.
Tun lokacin ta raba musu makwanci. Shi kuma duk ƙulafucinta da yake yi bai taɓa nuna mata ya damu da raba makwancin ba.
A sannu ya runtse idanunsa, yana jin yadda wani matsanancin kewa da sha'awarta ke ƙara lulluɓe shi. Zuciyarsa cike da fatan nannauyan barci yazo yayi awon gaba da shi.
Bayan tsawon lokaci yana juye-juye daƙyar ya samu barci ya ɗauke shi a wahalce.
****
Motsin da ya ji a kicin yasa shi ƙarasawa da sassarfa. Ita ya gani, tana tsaye gaban cabinet tana fasa ƙwai a cikin roba.
A firgice ta juya jin anyi ma ƙugunta wani wawan damƙa. Ganinshi yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kwaɓe fuska, tayi narai-narai da idanunta ta ɗan tura baki gaba
"Ashe kai ne, ka tsorata ni..."
Cikin salo ya juyo da ita suna fuskantar juna. A sannu a hankali yana riƙe da ita ya dinga matsawa da fuskarsa zuwa tata, ita kuma ta dinga ja da kanta baya har sai da ta kusa kwantar da kanta kan Cabinet ɗin
"Abee ka bari mana don Allah, za ka sa inyi ɓari fa."
Tayi maganar tana zazzaro idanu ƙirjinta na bugawa. Bata san me yasa ba sam ba ta son ya sumbace ta.
Hannayensa ya ɗaga daga ƙugunta zuwa bayanta ya tallabota dakyau, a hankali ya janyota ya matso da ita tsakiyar kicin ɗin, har lokacin yana riƙe da ita.
Murmushi ya sakar mata. Ita kuma ta ƙara daidaita yanayin fuskarta zuwa ba yabo ba fallasa.
"Jiya, na zaci zan tarar kin shirya min kyakkyawan tarba? Me yasa kika ƙi zuwa ɗaki na? Kuma nai ta ƙwanƙwasa ƙofarki kina ji na kika ƙi buɗewa"
Idanunta ta wulƙita kamar tana harara, kamar kuma tana kallon gefe da gefe.
"Abincinka, da duk wani abu da na san za ka buƙata na ajiye maka. Ɗakinka duk da ko wane lokaci a gyare yake sai da na sake ƙalƙale shi. Me kuma kake buƙata bayan waɗannan Habeebee?"
"Ke"
Ya amsa kai tsaye.
"Ke nake buƙata Fareeda! Allah ya sani ina kewarki..."
Katse shi tayi ta hanyar sakin wata irin dariya a sakalce.
"Dariya kike yi...?"
"Eh to ai dole inyi dariya Habeebee! Ni da tun kafin amarya ta zo aka tattarani aka aje gefe ɗaya? Ai kaje ka ji da Amaryarka kawai, babu komai, zan baku lokaci sosai har fiye da yadda kuke buƙat..."
A bazata ya haɗe bakinsu guri ɗaya. Ya fara aika mata da wani irin zazzafan sumbata, duk yadda ta so ƙwacewa ta kasa, sai kawai ta mishi kakim shi kaɗai yake kiɗansa yake rawarsa.
Hakan bai dame shi ba. Daga bisani ma ɗaga ta yayi cak suka nufi ɗakinsa. Duk yadda take ƙoƙarin zillewa bai sauke ta ba sai da ya kaita har kan gadonsa.
Ko kafin tayi yunƙurin sauka ƙasa har ya mata rumfa ta yadda baza ta iya sauka ƙasa ba sai ya bata dama. Daman har lokacin kayan barci ne a jikinta, don haka bai sha wahala wajen zame mata da cillar da su ba.
Da wani irin zafi-zafi da rawar jiki kamar wanda ake ingiza shi yake aikata komai. Sosai jikinsa ke karɓar duk wani abu da yake yi.
Duk da a ɓangarenta babu wani armashi ko tallafi a hakan dai ba ƙaramin samun yadda yake so yayi ba.
Sai da ya gama taɓo duk wani guri da zai motsa shi yana gyarata da nufin ayi mai gaba ɗaya ba zato ba tsammani gaba ɗaya kuzarinshi ya tafi. Ya wani kwanta lakaf kamar ba shi ne yai tsaye ƙiƙam yana zakwaɗin samun biyan buƙatarsa ba.
Hannunsa yakai gurin, a tsorace ya janye hannu ya kai idanunsa jin kamar ya taɓo lagwani don sanyin da yayi.
Ya ɗago idanu a tsorace ya kalli Fareeda da take kwance da ɗaurarriyar fuska, ya sake mayar da idanu jikinshi yasa hannu ya ɗan taɓo bakinshi na rawa ya ce ma Fareeda
"Lllllla...fiya.. kuwa...? Kin ga... yadda...na zama?"
A lalace ta ɗaga idanu ta kalli inda yake nuna mata. Ganin yadda yayi lakaf kamar wanda ya gama aikata komai yana buƙatar hutawa sai ta kawar da kanta gefe ɗaya.
A bazata wani irin faɗuwar gaba ya sameta.
'Mukhtar lafiyayye kuma jarumin namiji ne da ko bai gani ba bai taɓa ba haka kawai yake miƙewa saboda tsananin lafiya da jarumtarsa. Amma yanzu ace ya kwanta ligif tun ba'ayi komai ba? Lallai an gogu da Amarsu ta Ango mai zaƙin miya."
Da sanyin jiki sosai ta zame ƙafafunta ta mirgina gefe ɗaya, ajiyar zuciya take saukewa a hankali kuma akai-akai.
Tunanin kwanciyar me za ta cigaba da yi tunda ba halin yin abinda yasa shi ɗaukota sai ta yunƙura za ta tashi.
Da sauri Mukhtar ya riƙota ya sake komar da ita kan gadon.
A hankali ya fara yamutsata jikinsa na rawa, ƙoƙari yake ya taɓa duk inda ya san zai tayar da kanshi da gaggawa.
A yanzu ɗin wani irin salon soyayya yake gabatar mata wanda ba shi kaɗai ba, ita kanta duk ɗaurewarta da kawar da kai sai da ya samu nasarar kunnata. Da armashi sosai ta juyo tana mayar mishi da martanin wasanninshi, sai a lokacin ita kanta tasan ta yi kewar mijinta.
Wani abin mamaki da ban tsoro ga su biyun kamar ɗazu dai haka ne ya sake faruwa. Duk yadda Goga Mukhtar ya miƙe tsaye ƙiƙam kwanciya ya sake yi lakaf sa'adda ya zo zai ratsa gonar da ta daɗe da zama halaliyarsa.
Ruƙunƙumeta yayi da ƙarfi a ƙirjinsa yai shiru, zuciyarsa na bugawa fafafat! Hankalinsa a bala'in tashe.
'Me yake faruwa ne haka?'
Tana kwance a jikinsa wani irin tashin zuciya ya fara zuwar mata bagagatan, amai take jin yi, duk da cikinta babu komai da ta ci a safiyar nan sosai amai ke taso mata.
Jin miyaun bakinta ya tsinke sosai alamun ko wane lokaci aman na iya ƙwace mata yasa ta fara ƙoƙarin ƙwace jikinta.
Mukhtar bai lura da halin da take ciki ba. Hankalinsa yayi nisa gurin tunanin inda matsalar take, sai ya ji ta fara ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon da yayi mata.
Jajayen idanunsa ya ɗago ya zuba mata sai yaga yunƙurin da take yi da yadda take kai hannu tana tare bakinta.
"Lafiya...?"
"Amai"
Ta amsa daƙyar sannan ta sauka a guje zuwa banɗaki.
Wani irin ƙaƙƙarfan amai ne take yi kamar za ta amayar da ƴan cikinta. Jin yunƙurin ya ƙi ƙarewa dole ya taso zuwa bayin yana jera mata sannu.
Hankalinsa ne ya ƙara tashi ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ta galabaita. Ta gama aman kumallo yanzu kuma yunƙurin aman take yi babu abinda ke fitowa. Kuma ta kasa daina yunƙurin.
Sosai ya riƙe ta a jikinsa ganin tana ƙoƙarin zubewa ƙasa saboda rashin ƙarfin jiki. Hankalinsa a ɗugunzume. Sannu kuwa ya jera mata ya fi baki ɗari.
Bayan tsawon lokaci suna cikin banɗakin daƙyar yunƙurin da take yi ya ragu. Ruwa ya tara mai zafin gaske cikin kulawa da tarairaya ya salleta soso da sabulu.
Cikin rashin ƙarfin jiki ita kuma ta lallaɓa tayi na tsarki, duk da ruwan zafi take amfani da shi tana yi jikinta na kyarma-kyarma.
Babban tawul ya rufa mata yana riƙe da ita a gefen kafaɗarsa ya kaita gefen gado ya zaunar da ita, sannan shi ma ya faɗa wanka.
Ko kafin ya fito daga wanka ta kwanta, bayan ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta har saman kai. Wani irin rawan sanyi take yi sosai yadda ko daga waje ne ana kallon yadda take jijjiga a cikin bargo.
Ko mai be shafa ba ya zura kaya a gaggauce yana yi yana kallonta. A daidai lokacin kuma daga can falo ya ji muryar su Sayyid suna ƙwala kiran Ammee, da raunin murya mai nuni da alamun ko wane lokaci za su iya fashewa da kuka.
Da sauri ya fita falo gurinsu. Ganinshi yasa suka taho da ɗan gudu gudu suka rungume shi suna gaishe shi cikin harshen nasara.
"Ammee ba ta da lafiya. Me kuke so?"
Ya tambaye su da kulawa bayan ya amsa gausuwarsu.
"Abee, yunwa muna ji."
Suka amsa da gwaranci a muryoyinsu.
Ganin kayan barci ne a jikinsu ya bashi tabbacin yanzu suka tashi. Sai yaja hannayensu zuwa banɗaki ya goge musu baki, yayi musu alwala. Ya shimfiɗa musu sallaya ya durƙusa a gabansu ya ce
"Kuyi sallah, idan kun idar yanzu zan kawo muku kayan break fast. Kun ji?"
Kawunansu suka ɗaga.
Sai ya wuce kicin da sauri, wani ƙwan ya sake fasawa ya soya musu, saboda wancan da Fareeda ta fasa a buɗe suka bar shi.
Ya haɗa musu tea a ƴan kofunansu ya ɗauki biredi da ƙwan da ya soya ya kai musu.
Gurin kayanta ya nufa, bayan ya ɗauki Inner wears sai ya ɗaukar mata doguwar rigar atamfa mai faɗi, ya ɗauki babban hijabi mai kauri ya koma gurinta a ɗakinsa.
Yanzu ta rage jijjigar da take yi, barci take, amma irin wahalallen barcin nan mai tafe da zazzafan zazzaɓi. Ko da ya taɓa jikinta zafi sosai.
A hankali ya ɗaga ta ya saka mata kaya, ya sa mata hijabin ya sake kwantar da ita ya lulluɓa mata bargo.
******
"Barr. Ka taimaka min, don girman Allah ka taimaka min. Wallahi tallahi ina cikin wani matsanancin hali ne da idan ban samu kuɗaɗen ayau ɗinnan ba rayuwata za ta ƙara shiga cikin garari..."
"Hajiya Fatima wai saurin me kike yi ne? Idan kinyi haƙuri, wata huɗu ya rage su sake biyan kuɗin hayar nan. Da yau da nan da wata huɗu ai kaman gobe ne in dai muna raye..."
Jin da tayi yana neman yi mata yawo da hankali alhali yana da ikon taimaka mata kawai sai ta sakar mishi kuka. Shi kaɗai ne hope ɗinta na ƙarshe da take tunanin za ta iya samun rancen kuɗi a gurinshi kafin ƙarshen shekara a biya kuɗin hayar shagon da take da kaso a ciki.
Dubu ɗari biyu da hamsin ake biya duk shekara, to ita a rabon gadon da aka yi duk sa'adda aka biya kuɗin tana da dubu saba'in da biyar a ciki.
Wani abun armashi shi ne, masu biyan kuɗin hayar shagon idan sun tashi biya suna bada na shekara biyu ne. A lissafi tana da dubu ɗari da hamsin kenan.
Yanzu saura wata huɗu kenan a biya kuɗin. Jiya da daddare ta yanke shawarar kiran lauyan da yake tsaye akan kadarorin ƴaƴan mijinta ta roƙe shi ya taimaka ya bata kasonta tun kafin lokacin biyan kuɗin yayi.
Shi ne yake ta mata yawo da hankali, sai yayi kamar zai taimaka mata sai ya zille, ga ɗari biyar ɗin da ta ci bashi a wayarta kuɗin na tafiya a iska babu biyan buƙata.
Jin kukanta ya ɗan karya mishi zuciya, da sauri ya dakatar da ita ta hanyar cewa
"Tsaya, tsaya, saurara Hajiya Fatima. Ai abin duk bai kai na kuka ba. Kin dai san yanzu lokaci ya canza gwamnati ta hana aikin da babu riba ko?"
"Eh!
Ta amsa da rawar murya.
"Zan taimaka miki, amma bisa sharaɗi ɗaya idan kin amince. Kuɗinki na shekara biyu dubu ɗari da hamsin ne, idan kin amince zan cire dubu talatin, yanzu in baki ɗari da ashirin ni kuma idan sun biya in riƙe ɗari da hamsin ɗin. Kin amince?"
Shiru tayi cikin tunani, ya za ta yi? Ba ta da wani hanyar samun kuɗi da ya wuce wannan. A baya al'mubazzaranci
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 26