Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mari. Da wani irin fusata da ɓacin rai matsananci ta buɗe idanunta da suka canza launi lokaci ɗaya, ta ɗaga ƙafa a fusace za ta ƙarasa gurin Fatimar sai taja ta tsaya cak, tunawa da tayi da wata magana ta Malam bahaushe da yake cewa. "Ka so naka, duniya ta ƙi shi. ka ƙi naka, sai duniya ta so shi." Fatima da take kallon yanayin Fareeda ta ƙasan idanunta ganin ta ja ta tsaya sai ta sake ɗaga hannunta na dama fuska cike da murmushin mugunta ta sake fallawa yaron mari, sannan ta saki hannayensa haɗe da ture shi ya faɗi ƙasa yana rusa kuka. "Don Uwarka waccan da take tsaye zan nuna maka kai ƙaramin mare kunya ne. Idan ita gantalalliya ce ta kasa baka tarbiya mai kyau ni zan koya maka." Da gama faɗin haka sai taja ta tsaya ta riƙe ƙugunta, jira take Fareeda ta zaburo ta naɗa mata nata marukan kamar yadda tayi ga ɗanta. Sai taga ko da Fareeda ta ƙarasa gurin ɗanta ta ɗaga jikinta na rawa ta rungumeshi a ƙirjinta. Ta ƙarasa kusa da Sayyid ta kama hannunsa suka nufi ɓangarenta, har lokacin jikinta bai daina rawa ba. Tana jin sa'adda Fatima taja mata wani dogon tsaki haɗe da cewa "Sakarya kawai." Daƙyar ta iya ƙarasawa cikin falonta. Nan kan kafet ta zauna ta rungume ƴaƴan a jikinta ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka, zuciyartaa in banda tuƙuƙi da suya babu abinda take yi. Fatima ba fin ƙarfinta tayi ba, amma ko kaɗan ba ta son zubar da mutuncinta ta hanyar biye mata su dinga kace-nace kamar wasu dabbobi. Balle irin yadda Fatima ta dinga marin yaron kowa zai san da gayya tayi, ta yi ne domin ta tanka mata. Ita kuwa in Allah ya yarda baza ta ƙara biye mata suyi cacar baki ba, ba ita ce sa'ar yin ta ba, Mukhtar ne, don haka zai dawo gidan shi zaiyi wannan shari'ar, ita kam baza ta iya ba. Tana lallaɓa lafiyarta asa ta cikin wani mummunan hali na tashin hankali da ko kusa ba ta fatan shigarsa. Acan ɓangaren Fatima kuwa tana shiga ɗakinta wayarta ta ɗauko, ta nemi gurin zama akan kujera ta lalubo lambar Mukhtar ta danna mishi kira. Yana ɗagawa daga can ɓangaren sai ta sakar mishi kukan kissa. A rikice ya fara tambayarta menene? me yake faruwa? Wa ya taɓa mishi ita? Sai da ƙyar ta iya sassautawa da kukan ta fara magana "Haskenah! A tunanina ko ban aure ka ba ƴaƴan Fareeda ƴaƴana ne?" "Haka ne! Me yake faruwa?" Ya tambayeta cikin zaƙuwa. "Wai kawai don na ji su Sayyid suna wasa a tsakar gida na fita ina tsokanarsu nan take Fareeda ta fito a fusace ta janye ƴaƴanta. Ta saka su sukai ta min rashin kunya suna zagina, kalaman tozarci ta dinga faɗa musu da turanci tana nuno ni su kuma suna kwaikwayonta haɗe da min daƙuwa. Na tausaya maka Haske, wallahi idan baka yi da gaske ba, Fareeda sai ta lalata maka tarbiyar waɗannan ƴaƴan da kake alfahari da su, ba don komai za tayi hakan ba sai don baƙin kishi irin nata, idan za ka ji shawarata, ka ɗauki mataki da gaggawa tun kafin lokaci ya ƙure maka." Ta sake fashewa da kuka sannan ta katse wayar, daga bisani ma sai ta kashe wayar gaba ɗaya yadda ko ya kira bazai same ta ba. Nan kan kujera ta miƙe ƙafafu tana ƙyalƙyala dariya ita kaɗai kamar sabuwar kamu. Daƙyar da suɗin goshi ta samu ƴaƴan suka yi barci. Daƙyar ta rarrashi kanta ta tsayar da kukanta, ta fara rarrashin su biyun da suka urunce da kuka kamar duk su biyun aka mara. Bayan tsawon lokaci suka yi shiru, lamo sukai kwance a jikinta suna sauke ajiyar zuciya. Jikinsu ya ɗauki zafi sosai, da ta kalli fuskar Shahid sai wasu zafafan ƙwalla su sake taruwa mata saboda yadda shatin yatsun Fatima suka fito ruɗu ruɗu. Kan kujera ta lallaɓa ta kwantar da su, ciki ta shige ta haɗa musu ruwan wanka. Ko da ta fito sai ta tarar duk sunyi barci. Kamar za ta tashe su, sai kuma taga yadda jikinsu yayi ɗumin nan ga ajiyar zuciyan da suke ta saukewa duk da suna barci gara ta bari idan sun tashi sai tayi musu wankan. Ɗaya bayan ɗaya ta ɗaukesu zuwa cikin ɗaki ta kwantar da su kan gado. Falon ta koma ta zauna, tagumi ta buga da hannu bibiyu, zuciyarta cike da tunanin inda ta taɓa kuskure ma Fatima a mu'amalar ƙawance da suka gudanar na tsawon shekaru. "Ashe ƙauna da yarda suna juyewa su zama matsananciyar ƙiyayya da jin haushi? Tun bayan da Mukhtar ya auro Fatima cikin gidannan babu abinda take kallo a cikin idanunta sai matsananciyar tsanarta da jin haushinta. Ga shi yanzu abin har ya fara gangarowa kan ƴaƴanta. Ko dai akwai wani mummunan abu da ta taɓa yi ma Fatiman a baya ne da take burin ɗaukar fansa a yanzu? Tayi imani da Allah, ta san aure tsakanin Fatima da Mukhtar ko kaɗan babu haramci a ciki. Kalmar ana barin halas ko don kunya bai taɓa samun matsuguni a zuciyarta ba balle har ta ƙullaci Fatimar. A tunaninta ko basuyi zaman daɗi ba, za suyi zama ne irinna kowa tasa ta fisshe shi. Amma na miye duk wannan tsana da ƙiyayyar da take nuna mata?" Tun daga bakin ƙofar falonta take jin yadda Mukhtar yake ƙwallah mata wani irin mahaukacin kira. A gigice ta miƙe tsaye tana zare idanu, ya buɗe ƙofar ya shigo fuskarsa na bayyana wani irin ɓacin rai da fusata da ta daɗe bata gani a tare da shi ba. "Mmmmme ya faru? Menene?" Ta tambaye shi cikin rawar murya. "Fareeda, me nayi miki da zafi da za ki dinga nuna min irin wannan matsananciyar tsanar? Kin nesanta kanki da ni, ƴaƴan nawa da nake gani ina jin daɗin samunsu daga gare ki su ma so kike ki nesanta su da ni ta hanyar lalata min tarbiyarsu?" Idanunta a warwaje, fuskarta cike da mamaki da tsoro, a ƙwaƙwalwarta take ta jujjuya maganganunsa don gano inda ya dosa amma sam bata gane ba. Da sassarfa ta taka ta haɗe tazarar da ke tsakaninsu, ta miƙa hannuwa za ta riƙo nasa da sauri ya janye hannayensa kamar wacce ta nufe shi da bakin wuta. Ta buɗe baki za tayi magana yayi saurin dakatar da ita da wani irin gigitaccen tsawa. Daman tun safe akwai fushi da ɓacin ran jin maganar ita ke amfani da magani don kar ya samu damar kusantarta. Don haka yanzu da ya samu damar da zai wanke ta wani irin tsiya na bala'i yake zazzaga mata kamar bai taɓa sanin wacece ita ko kuma daga ina ta fito ba. Daga ƙarshe ya ɓuge da maimaita mata abinda Fatima ta ce ita da yaran sunyi mata ya kuma kora mata kashaidin kar ta kuskura ya sake jin makamancin irin wannan shirme da dabbancin, idan ba haka ba zai ɗauki mummunan matakin da bata taɓa tsammani ba. Fareeda ta kasa kuka, sai wani irin ajiyar zuciya take saukewa cikin zafin rai. Tun tana tsaye tana saurarenshi, bata san sa'adda ta sulale zuwa ƙasa ba, mamaki da ɓacin rai haɗe da baƙin ciki ke neman sumar da ita. Bata san sa'adda ya fice ba, kawai buɗe idanu tayi taga baya falon. Minti uku ta ƙara durƙushe a gurin tana nishi kamar mai naƙuda. Sai kuma ta miƙe a zabure ta nufi cikin ɗakinta, har lokacin su Sayyid suna kwance suna barci. Tun a tsakar ɗakin ta fara cire kayan jikinta tana hurgi da su, har ta zama daga ita sai rigar mama da ɗan kamfai. Durowar kayanta ta buɗe ta fara janyo kayan cikin sauri tana ɗaɗɗagawa har ta ciro wasu sakakkun riga da wando ƙananu, wandon iya gwuiwa, rigar kuma da kaɗan ta ɗara cibiyarta. A gurguje ta saka kayan a jikinta, ta fice daga ɗakin gudu-gudu kanta babu ko ɗankwali, daman shekaran jiya ta tsefe kan, yalwataccen gashinta ya kwanta a saman kafaɗunta. Silifas ɗin da take sakawa a cikin ɗaki tana tafiya saboda sanyin tiles shi ta zura a kafafunta ta fice daga apartment ɗin gaba ɗaya. Kai tsaye ɓangaren Fatima ta nufa da sassarfa, idanunta sun kaɗe sunyi jajur. Wani babban sa'a da ta ci shi ne tana murɗa hannun ƙofar ya buɗe, aikuwa ta afka cikin falon a guje kuma a haukace. Mukhtar na kwance kan doguwar kujera, Fatima ta sa gwuiyawunta a ƙasa tana mishi tausa kawai Fareeda ta afko cikin falon babu ko sallama. Ko kafin suyi wani yunƙuri na magana ko na miƙewa tuni Fareeda ta isa ga Fatima ta damƙi wuyarta ta miƙar da ita tsaye, da wani irin ƙarfi kamar ba ita kaɗai ba ta wujijjiga Fatiman sannan ta haɗa ta da bango, ta shaƙe ta da hannu ɗaya hannu dayan kuma ta fara gaura mata mari, tana marinta tana cewa "Ni za ki gwadawa makirci?" Ko kafin Mukhtar ya samu nasarar ɓanɓare Hannayen Fareeda a wuyan Fatima ta yi mata maruka sun kai sha biyar. Fatima kamar wacce aka riƙe ma hannaye ta kasa wani kataɓus na ramawa ko kuma yunƙurin ƙwacewa, ihu kawai take ƙwallawa tana faɗin Haskenah ka ceceni, ta haukacee za ta kashe ni. A haukace Fareeda ta damƙi damtsen hannun Mukhtar na dama ta kai bakinta ta gantsara mishi wani matsiyacin cizo kamar za ta gutsure fatar gurin. Saboda azaba Mukhtar bai san sa'adda ya ƙwallah ihu ba. Ita dai Fatima tunda ta samu tsira ko ta kan Mukhtar bata bi ba da rarrafe ta shige ɗakinta ta rufe ƙofa. Daƙyar da gumin goshi ya samu nasarar ɓamɓare hannunsa a bakinta bayan yayi mata wani mugun damƙa a gashinta, yadda Fatima ta shige da rarrafe haka ya bi bayanta yana yi yana waigen ko Fareeda ta biyo bayansa... *Ina da mare lafiya, jiya a asibiti na kwana sai da yammannan na dawo gida. Sannan ina da biki wannan satin. New update sai kun ji ni lahadi ko litinin in sha Allah* *_Laifin daɗi aka ce ƙarewa😍😍😍 Promon maganin Sanyi na Zee maman Mujaheed ya ƙare. Yanzu maganin ya koma farashinsa na ainahi wato 4k! Ya ke ƴar'uwata mai karanta labarin RABON AYI, a gurin neman lafiya daga wannan fitannen ciwo na infection da yake damun mata da yawa, ko dubu ɗari kika kashe wajen siyan ingantaccen maganin sanyi bakiyi asara ba. Lafiya ta fi komai a duniyar nan ƴar'uwa👌🏽 sai da lafiyarnan za ki kankaro ma kanki mutunci da daraja a gurin Oga😘. Ki tuntuɓi Maman Mujaheed ta wannan lambar wayar domin sayen naki akan farashi mai rahusa 0816 285 9027_* *RABON AYI* *©️Fareeda Abdallah* *_26_* *Kina da fama da matsalar rashin haihuwa ko dogon jinkiri ba tare da wata ƙwaƙƙwaran dalili ba tsakanin wannan haihuwar da wancan haihuwar? Ko kuma kina da ƴar'uwa ko ƙawa da kika san tana fama da wannan matsalar?* Magani ne zan tallata muku. Amma wannan maganin ni Fareeda ba ni nake sayarwa ba. Ƙauyenmu muka je biki, ƙanwar mamana tayi mentioning maganin ga wata ƴar'uwata da ta daɗe bata sake samun ciki ba. Kamar wasa muka je gurin mai maganin muka karɓa, dubu biyu kuɗin magani. In taƙaice muku zance Wallahi tana gama shan salalar maganin na kwana sha biyu sai ciki. Ko da muka sake zuwa wani sha'ani take faɗa ma ƙanwar mamanmu magani an dace, sai mata da yawa a gurin suka tabbatar mana su ma maganin suka karɓa suka dace. Ashe har daga gari-gari zuwa ake ana saye maganin a gurin wannan mata mai magani. Kuma bayan maganin rashin haihuwa ko dogon jinkirin haihuwa daga mace har maganin matsalar rashin haihuwa na maza tana bayarwa. Shi ma dubu biyu ne kamar yadda na mata yake. Idan kuma matsala ya shafi mata da mijin sai ku amshi maganin duk biyu. 4k kenan. Amma ku sani ni ina kaduna ne, kawai dai ba na rasa mai zuwa daga can ƙauye da za'a kawo maganin zuwa gidana a kinkinau musabaƙa. Amma kai maganin inda mai siye take ko ina ne wacce ta siya ita za ta biya kuɗin mota ko mashin. Masu son magani da gaske ga acc no su saka kuɗin magani, 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai su turo min shaidar sun biya da bayanin inda suke ta private a lambar wayata 07039080978. Don Allah don Annabi duk wacce ta san ba da gaske take yi tana son magani ba kar ta tuntuɓeni, don Allah🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽🙏🏽 Kaso arba'in da biyar cikin ɗari na baƙin cikin da suka ƙunsa mata ya ragu sanadiyyar wannan matakin da ta ɗauka a kansu. Ko banza ta rama ma Shahid ninkin ba ninkin marin da Fatima tayi masa. Shi kuwa Mukhtar! Ƙaƙƙarfan ƙwafa ta sake tana jijjiga kai, alamun da ke nuna basu gamu ba tukun! Za dai su gamu. Ƙofar ɗakin da suka shige ta gallawa wata matsiyaciyar harara, sannan ta fice da sassarfa zuwa ɓangarenta. Ko da ta leƙa ƴaƴan har lokacin barci suke yi, har ta juya za ta shiga banɗaki sai kuma ta juyo da sauri ta sake kallonsu. Barci suke yi, amma suna ta ɗan rawar ɗari alamun suna jin sanyi. A gaggauce ta ƙarasa ta taɓa jikinsu sai taji zafin ya ninninka na ɗazu. Hankalinta ne ya ƙara tashi. Idanunta suka cicciko da hawaye. Bargo ta janyo ta rufa musu sannan ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwalar sallar la'asar. Jikinta a sanyaye ƙwarai, akai-akai take sharar ƙwallah har ta kusa idar da sallar. Tana sujuda a raka'ar ƙarshe tana fara addu'a hawaye ya ɓalle mata. Cikin kuka take faɗa ma Allah ga halin da take ciki ya dubeta ya kawo mata mafita da gaggawa. Bayan ta idar ta daɗe zaune kan sallaya, babu abinda take yi sai istigfari, tasbihi, hailala. Gaba ɗaya zuciyarta babu daɗi, lokaci bayan lokaci take ɗaga idanu ta kalli ƴaƴan da suke barci da zazzaɓi a jikinsu. **** "Hello! Hajiya kina ji na?" Ta tambaya bayan ta ji ntwk ɗin wayar kamar ya fara rawa. Ba sosai take jin muryar Hajiyar na fita ba. Tsinkewa kiran yayi, kafin ta sake kira sai ga kiran Hajiyarmu ya shigo cikin wayarta. Sabon gaisuwa ta sake yi ma Hajiyar a ladabce, da muryarta a sanyaye ƙwarai, har sai da Hajiyarmu ta ce "Ina jin ki Fareeda. Me ya samu muryarki? Kina mura ne? "A'a! Lafiyata ƙalau Hajiya." Sai kuma ta ɗanyi shiru, kafin ta cigaba da cewa "Hajiya ga su Sayyid kwance babu lafiya. Don Allah, idan babu damuwa ki aiko direba ya kwashe su zuwa gurinki." Sai muryarta ta fara rawa, alamun ko wane lokaci za ta iya fashewa da kuka. "Zafin jikinsu ƙara hauhawa yake yi tun da rana. Tsoro nake ji, don Allah ki aiko..." Ƙit wayar ya sake katsewa a karo na biyu. Ajiye wayar tayi a gefe ɗaya ta kifa kanta hannun kujera, hawaye wasu na korar wasu a idanunta. Yanzu gurin awa huɗu da rabi kenan suna kwance, tun suna barci da rawar sanyi da zafin zazzaɓi sama-sama, yanzu jikin nasu ya sake ɗumewa sosai da zazzaɓi. Sun farka, sai suka fara wani irin nishi sama-sama suna kuka suna surutan da sam ba ta gane me suke cewa. Ko da tayi yunƙurin ɗaga su zuwa jikinta sai suka zame suka ƙara kwanciya kan gado. Shahid da ya fi Sayyid zafin zuciya har wannan lokacin bai daina sauke ajiyar zuciya ba. Farar fuskarsa ta ƙara wani irin jaaaa, shatin yatsun Fatima sun sake fitowa ruɗu-ruɗu a ƴar ƙaramar fuskarsa. Da da ne da bata shiga cikin hankalinta kan fita ba da izinin mijinta ba a fujajan za ta kwashe su zuwa asibiti. Amma a yanzu baza ta iya ba, ko kusa baza ta iya sake maimaita makamancin kuskuren da ta dinga aikatawa a baya har ya janyo mata faɗawa cikin ƙaƙanikayi a yanzu ba. Wani irin fushi ne ta ɗauka da Mukhtar, ko da zazzaɓin yaran zai ninka haka ya sake ninkawa ba ta jin za ta iya ɗaga wayarta ta kira shi balle har ta sanar da shi halin da suke ciki. Kuma ba ta son kiran ƴan'uwanta ta ɗaga musu hankali. Tsoron kar yaran su mace mata ita kaɗai a cikin ɗaki yasa ta yanke shawarar kiran Hajiyar, ta sanar da ita halin da yaran suke ciki. Wai aka ce abin cikin ƙwai ya fi ƙwan daɗi, jika wahal da kaka. Fareeda da take ta saka idon ganin direba ya zo kwasan yaran sai ga Hajiyar da kanta, wani abu da Hajiya ta kwana biyu bata yi ba shi ne tuƙa mota da kanta zuwa unguwa. Amma yau saboda zaƙuwa da son ganin halin da ƴan biyun jikokinta ke ciki ta kasa jiran ƙarasowar direba, tun da ta kira shi ya ce mata yana hanya taga an shafe mintuna goma bai zo ba kawai sai ta tuƙo motar da kanta, ga dare ya fara shiga, lokacin ƙarfe bakwai da rabi na yamma. Ƙarfe takwas da minti ashirin sai ga sallamar Hajiya a ƙofar falon Fareeda, sai kuma ta ƙara da ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi ta yadda duk inda mai ɗakin take za ta ji. Ta fito daga kicin kenan ta haɗo musu tea ɗan kaɗan ko za su sha ta tsinkayi ƙwanƙwasa ƙofar. Da gaggawa ta ƙarasa ta buɗe, suna haɗa idanu da Hajiyar ta kasa riƙe kanta, sai kawai ta faɗa jikinta ta fashe da kuka mai ƙarfi. Da walakin goro a miya. Tun daga yadda Hajiyarmu ta ji muryarta a waya ta san ba damuwar ciwon ƴaƴan bane ya ɗaga hankalin Fareeda haka. Tana riƙe da ita a jikinta taja ta zuwa kan kujera suka zauna, tsawon lokaci tanz sharɓen hawaye kanta na kwance kan kafaɗar Hajiya. Kafin ta fara ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. "Ya isa haka. Ummm?" Daƙyar ta samu ta tsayar da kukan da take yi, ta zame ƙasa ta gaishe da Hajiya, idanunta sun kaɗa sunyi jajur, har wani ɗan kumbura suka yi. "Me yake faruwa? ina yaran?" Hajiyar ta tambayeta. "Suna cikin ɗaki." Ta amsa tambaya ta biyu kanta a ƙasa. Bata sake cewa komai ba ta miƙe ta nufi cikin ɗakin, Fareeda na biye da ita a bayanta. Ganin wani irin kwanciya da yaran suka yi yasa hankali tashe Hajiyar ta zauna gefen gadon haɗe da janyosu zuwa jikinta. "Subhanallahi, Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wani irin zazzaɓi ne haka ya rufe su lokaci ɗaya? Ko sun daɗe suna ciwon ne?" Ta jero tambayoyin a ruɗe tana kallon Fareeda. Sai kuma ta mayar da hankali kan yaran, ta taɓa jikin wannan ta taɓa na wancan, hankalinta a tashe. Karaf idanunta ya faɗa kan fuskar Shahid, idanu warwaje ta shafa gurin shatin yatsun a tsorace "Miye nake gani haka? Wannan ai kamar shatin yatsun hannu ne. Dukansa kika yi? Fareeda wannan ɗan ƙaramin yaron kika mara haka? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un... Fareeda kin haukace ne...?" "Hajiya ba fa ni na mare shi ba." Ta faɗa cikin rawar murya. "Amaryar Mukhtar ce ta mammareshi." Ta ƙara da faɗin haka don wanke kanta. Tsuru Hajiyar ta ƙura ma Fareeda idanu, kamar wacce ta warke makanta, bakinta a buɗe, don tsananin mamaki. "Ta mam-mare shi?" Ta figo maganar daƙyar daga maƙogwaronta. "Marin ma ba ɗaya ba? To me yayi mata?" "A kan idanuna tayi mishi mari biyu. Ni ma bazan ce ga takaimaimai abinda yayi mata ba. Fita suka yi suna buga ƙwallo ina kwance kan kujera na jiyo ihunsu." Wani irin matsanancin ɓacin rai ne ya mamaye mamakin da ke kwance male-male kan fuskar Hajiya. Ta yunƙura ta miƙe tsaye da Shahid rungume a jikinta. "Ɗauko Sayyid ki fito min da shi." Ta umarci Fareeda. Sannan ta fice daga cikin ɗakin. Ko da suka fita falo ita Fareeda ta zaci Hajiya za ta fita da yaran zuwa gurin motarta ne sai taga Hajiyar ta zauna kan kujera. Ta ɗauko wayarta a cikin jaka ta danna ma Mukhtar kira. A can tsakar gidan shi kuma Mukhtar ya dawo sallar isha'i kenan ya ci karo da motar Hajiya. Mamaki ne ya kama shi, da sassarfa ya nufi ɓangaren Fareeda, fuskarsa a ɗaure tamau. Zuciyarsa cike da tunanin irin zazzafan matakin da zai ɗauka kan Fareeda. Duk a tunaninshi ko Fareeda ta kai ƙararshi ne gurin Hajiyarsu, wato ita ne mai bakin kai ƙara bayan duk irin haukan da ta zuba musu ɗazu ko? Lallai zai nuna mata ita ƙaramar mara kunya ce. Fatima tana zaune a gefen gado, hannunta riƙe da ɗan ƙaramin madubi tana kallon kumatunta da suka tasa saboda marukan da ta sha a hannun Fareeda. Man zafi ne ajiye a gefenta, idan ta dangwalo man zafin sai ta shafa a kumatun, zuciyarta a ƙuntace da ɓacin rai. A zamanta gefen gadon ta tsine ma Fareeda ya fi baki ɗari. Kwatsam kira ya shigo wayar Mukhtar da ke ajiye a gaban madubi. Kamar baza ta ɗauka ba, sai kuma ta miƙe a hankali ta ƙarasa gurin tana kallon fuskar wayar. Gabanta ne ya ɗan faɗi ganin sunan wacce take kiranshi. Ta san mahaifiyarsa ce, don ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ta sha raka Fareeda gidansu Mukhtar ɗin. Ta san ƴaƴanta gaba ɗaya har Fareeda da Hajiyarmu suke kiranta. Kamar baza ta ɗaga ba, sai kuma wata zuciyar ta ingiza ta ta ɗaga kiran, ta lanƙwashe murya sosai cikin firirita ta fara gaishe da Hajiyar. "Keh! Wacece ke da har za ki ɗaga kiran da nayi ma mamallakin wayar?" Aka faɗa mata cikin tsawa daga can ɓangaren ba tare da an amsa gaisuwarta ba. "Kiyi haƙuri Hajiyarmu. Baya nan ne ya tafi masallaci. Amaryarsa ce, Fatima, ina yini?" A daidai wannan lokacin Mukhtar ya murɗa hannun ƙofar falon Fareeda ya shiga ciki, bakinsa ɗauke da sallama. Tsakanin Hajiya da Fareeda babu wacce ta amsa sallamarsa a fili. Hajiya ta kalle shi da wani irin fusataccen kallo ba tare da ta katse wayar ba ta ce "Wace ƴar iska ce ka ba damar ɗaga min waya idan na kira?" Tsuru yayi cikin dambarwa yana kallon Hajiyar, ya rasa ta cewa. Abinda ya sani kawai shi ne ya bar wayarsa a ɗakin Fatima, amma shi bai bata umarnin idan an kira shi ta ɗaga ba. A can ɓangaren Fatima cikin sauri da tsoro ta katse wayar. Tayi saurin ajiye wayar a inda ta ɗauka. Jikinta a saɓule ta koma gefen gado ta zauna. Ta buga tagumi da hannu bibiyu. Sai kuma ta miƙe zumbur ta nufi falonta, labule ta yaye ta leƙa tsakar gidan. Ganin baƙuwar mota a fake yasa ƙirjinta bugawa da ƙarfi. "Hajiyarmu na cikin gidannan ke nan? ko dai Fareeda ne ta kira ta?" Ta tambayi kanta. "Na shiga uku!!" Ta faɗa a fili, idanunta a warwaje ta ɗora hannu akai. Nan take ta fara safa da marwa a tsakiyar falon cikin ruɗu da tashin hankali. Cikin ƙanƙanin lokaci ta haɗa zufa tayi kashirɓin. Sai tufka da warwarar maganganun da za ta faɗa don kare kanta a gaban Hajiya take yi. Ruwa ba ya tsami banza, zuwan sarkuwar nasu bagatatan a wannan dare dole akwau dalili. Tana wannan zurga zurgar sai ga Mukhtar ya buɗe ƙofar falon ya shigo babu ko sallama. Fuskarnan a ɗaure tamau. Ya kalleta ya aika mata da wani mugun kallo. "Me yasa kika ɗaga min waya?" Ya tambayeta a fusace. Ƙwalƙwal tayi da idanunta, ta lanƙwasa kanta a hankali ta ce "Kayi haƙuri. Na ga Hajiyarmu ce..." "Hajiyarki ko tawa?" Ya daka mata tsawa da wannan tambayar. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta ƙasa, jikinta sai kyarma yake yi a tsorace. Yayi ƙwafa, ya juya ya nufi hanyar fita yana cewa "Ki biyo ni zuwa falon Fareeda. Hajiya tana son ganinki, saura kuma ki tsaya ɓata mata lokaci ki ga yadda za mu kwashe da ke a darennan" Ko da ya koma can falon ya sanar ma Hajiya ga Fatima nan zuwa kamar yadda ta buƙata juya mishi da fuskar Sayyid tayi yaga abinda ke kwance a kumatunsa. Don ɗazu da ya shigo hankalinsa na kan Hajiyar, duk a tsammaninsa ƴaƴan barci suke yi, Shahid a jikin Hajiya Sayyid a jikin Fareeda. Ckin fushi da fusatar da ya daɗe bai gani a fuskar Hajiyarmu ba ta ce "Ka ga fuskar Shahid ko? To ba shatin komai bane wannan sai shatin yatsun amaryarka. Idan ita shafaffiya da man taka ta shigo, ka tambaya min ita me wannan ɗan ƙanƙanin yaron yayi mata da

Chapter 19 of 26