suka tashi suna mishi Oyoyo. Har ƙasa ya durƙusa ya rungume su yana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren da suke fitarwa a jikinsu.
"Abee ina kwanna"
Suka haɗa baki gurin gaishe shi da muryarsu na yarinta.
Cikin jin daɗi ya amsa musu sannan ya ja su zuwa kan teburin.
"Iyyeee! Madam irin wannan kayan daɗi haka babu ko tayi?"
Ya faɗi haka idanunsa cikin na Fareeda, fuskarsa taf da murmushi. A zuciyarsa yake yaba irin kyawun da tayi cikin doguwar rigar atamfar da ke jikinta.
Sai da tayi faree da idanu da murmushi a fuskarta ta amsa mishi
"Haba Oga! Kai da ke da Amarya ai kayan daɗi sai dai a gani a gurinku. Mu kam abinda ya samu ne kawai muke ɗan lasawa don mu kauda tsamin baki."
Idanunsa idon alkaki sam ba ya wuce tayi, a yanzu ma hannu ya miƙa ya ɗauki guda ɗaya yakai baki ya gutsura. Lumshe idanu yayi yana jin wani irin garɗi da daɗi da ya ratsa bakinshi gaba ɗaya,
"Ummmn! Gaskiya duk wacce tayi alkakinnan ta cancanci a bata tukwuici. Ba ƙarya ta iya."
"Kai dai santi kawai kake yi Oga, bari in saka maka waigi..."
"Da gaske nake fa."
Yana gama cin na hannunsa ya sake ɗaukar wani. Sannan ya fara faɗa mata abinda ya kawo shi.
"Kayan abinci ne na siyo, ina so a ɗiba ma Fatima ta ajiye a gurinta, sauran sai ki ajiye anan! Tunda yanzu ga yara na san cin abincin zai ƙaru sosai akan na da."
"Haka ne! Allah ya ƙara buɗi da arziki mai albarka."
"Idan kin gama muje ki gani mana."
Bata gama ba, amma saboda ba ta son ya cika daɗe mata a gurinta sai ta miƙe tsaye.
Su Shahid ma suka miƙe da sauri ganin iyayen za su fita su barsu su kaɗai.
"Abee"
Sayyid ya faɗa yana ɓata fuska alamun zai saka kuka.
Da sauri ya dawo ya ɗauke shi, ya riƙe hannun Shahid suka nufi ƙofar fita daga falon.
Suna fita suka tsaya jirab fitowar Fareeda, tana fitowa suka jera, tafiya suke cikin nutsuwa zuwa gurin motarsa.
Sayyid da aka ɗauka sai surutu yake yi yana ba uban labari, iyayen fuskokinsu cike taf da murmushi, a kallonsu kawai za'a gane kyakkyawan iyali ne da suke cike da farin ciki.
Fatima tana tsaye kan kujera tana gyara ƙarfen labulenta na gurin window, ɗan lanƙwashewa yayi kamar zai karye. Shi ne ta taka kujera ta hau tana ƙoƙarin gyarawa, kamar ance ta kalli harabar gidan, kwatsam idanunta suka yi kyakkyawan gani.
Saboda tsananin firgici da baƙin cikin da lokaci ɗaya ya turnuƙe zuciyarta ƙiris ya rage ta faɗo ƙasa, Allah ya taimaketa tayi saurin faɗawa kan kujera.
A maimakon kuma ta nema ma kanta salama ta hanyar wucewa daga gurin ta daina kallon abinda ke ƙona mata zuciya, sai taja ta tsaya. Ta buɗe labulen sosai tana kallonsu, zuciyarta sai tafarfasa take yi da kishi da baƙin cikin Fareeda.
Ta kalli yadda tayi kyau cikin doguwar rigar jikinta, fuskarta babu kwalliya sosai amma ko maƙiyinta bazai ce bata yi kyau ba.
A daidai lokacin Shahid ya ɗauki wani abu da bata san ko menene ba a cikin boot ɗin motar Mukhtar ya ruga da gudu, a yangace Fareeda ta bishi da ɗan gudu-gudu da niyyar ta kamo shi, a fili take kallon yadda mazaunanta sai saɓar saɓar suke a cikin riga.
Ƙanƙance idanu tayi sosai ranta yana ƙara ɓaci, a hankali ta miƙa hannu ta shafo nata shafaffun mazaunan, sai taja tsaki.
Ganin yadda Mukhtar yayi wani dagalo yana bin Fareeda da kallo yadda suke ta zagaye motar ita da ɗan, shi yaƙi tsayawa, ita kuma ta ƙi daina bin shi. Sayyid da Mukhtar sai dariya suke musu.
Ita kuma Fareeda sai tura baki take yi a shagwaɓe tana bin yaron tana maganar da sam ba ta jin me take cewa.
"Sakarya kawai wawuya."
Ta faɗa cikin jin haushi. A zuciyarta ji take kamar ta janyo Fareedan ta zauna a ruwan cikinta tai ta ɗibga saboda baƙin cikinta da takaicinta.
Caraf taga Mukhtar ya cafke yaron, ya amshi abin hannunsa ya miƙa ma Fareeda, ta karɓa tana ƙara tura baki haɗe da ɓata fuska.
Tana ganin yadda Mukhtar da ƴaƴan suka haɗa hannuwa alamun bata haƙuri suke yi.
Ita kuma ta ɗan kama kumatun ƴaƴan biyu ta ja, ta aika ma Mukhtar hararan wasa sannan ta saki murmushi. Hannun ƴaƴan ta kama suka ja da baya.
Mukhtar ya fara fito da kayayyakin abinci daga cikin boot ɗin. Tana tsaye tana ganin yadda Fareeda take nuna mishi yana ajiyewa guri daban daban har ya gama fitar da kayan boot ɗin gaba ɗaya.
Ya buɗe kujerun baya ya fito da gas da kwalin ƙaramin flask ɗin. Kusa da Fareeda ya matsa da su ya ce
"Kiyi haƙuri Madam! Na san yanzu haƙƙoƙin duk ku biyun ya rataya a wuyana ne. Amma ni a ganina babu laifi don ka sai ma wacce ba ta da abu wani abin da bai taka kara ya karya ba.
Kamar yadda kema wata rana zan siyo miki abinda kike buƙata ba tare da na sai mata ba. A ganina wannan shi ne adalci. Babu laifi ko?"
Murmushi tayi, kuma ko kaɗan bata ji ba daɗi a ranta ba. A ganinta yadda ya faɗa ɗin shi ne adalci na gaskiya, tabbas itama wani lokacin za ta buƙaci abinda zai sai mata ba tare da ya haɗa da Fatima ba.
"Babu komai Oga. Allah ya ƙara arziki."
Martanin murmushinta ya mayar mata sannan ya ajiye Gas da flask ɗin a gurin kayan abincin da ba shi da yawa.
Izuwa wannan lokacin ɓacin rai da baƙin cikin Fatima ya kai ƙololuwa, ta kasa daure ma zuciyarta. A fusace ta ɗauki tsintsiya da abin kwashe shara ta buɗe ƙofar falonta ta fita waje, cikin hikima ta fara ƴan kakkaɓe kakkaɓen dattin gurin, alamun dai shara za tayi.
Mukhtar na juyawa zai fara kwasar kayan abinci mai yawa zuwa ɓangaren Fareeda sai ya hangi Fatima tana shara.
"Fatima, Fatima, Ke Fatima"
Ba tare da wani yanayin ƙauna ko girmamawa ba ya buɗe murya ya dinga ƙwala mata kira.
Bata amsa ba, sai ɗagowa da tayi a fusace ta zuba mishi ido.
Hannu yasa ya yafito ta, ya ƙara da cewa
"Zo nan"
Tsintsiya da abin kwashe sharar ta ajiye gefe ɗaya, ta fara tafiya a ɗan tattale ta nufi gurinsu tana wani nannarke idanu.
Kallo ɗaya Fareeda tayi mata ta kawar da idanunta daga kanta.
Yanzu ta canza kayan jikinta, daga na turawa zuwa leshin akwatinta da ta ɗinka tayi fitar biki. A cikin kayan turawa babu cikon da Mukhtar ya hana ta sakawa sosai ramarta ke fitowa, shi yasa ta yi ma kanta ƙiyamullaili ta canja kayan, ko babu komai kaurin leshi zai hana ramar armashi a idanun mai kallonta.
Akan kayan abincin da suke rabe ta fara sauke idanunta, cikin ladabi ta ɗan duƙa ƙasa ta ce
"Haskenah barka da dawowa. Ga ni."
Bai amsa ba sai nuna mata kayan abincin da bai da yawa yayi ya ce
"Ki ɗauki abinda za ki iya cikin kayayyakinnan kije da su ɓangarenki. Idan na shigar da waɗannan zan shigo miki da ragowar."
Kafin ta amsa sai da ta sauke idanunta akan wancan kayan mai yawa da yake ajiye gefen Fareeda, ta haɗiye wani maƙwallato na ɓacin rai.
Ta ƙaƙalo murmushi ta sakar ma Mukhtar, ta durƙusa har ƙasa ta ce
"Na gode Haskenah. Allah ya saka da alkhairi. Allah ya ƙara buɗi, Allah ya jiƙan Babanmu ya ƙara ma Hajiyarmu Lafiya, Allah ya..."
"Ameen! Ameen!! Ameen!!!"
Ya katse ta da sauri. Umarnin miƙewa tsaye yayi mata.
Har ya sunkuci buhun shinkafa a kayan da zai kai ɓangaren Fareeda kamar wanda aka matsa bakinshi sai ya kalli Fatima ya ce
"Daga yau kar ki sake durƙusa min gwuiyawunki a ƙasa. Malamai da yawa sun haramta haka, kuma ko ba haramun bane ni ba na so!!"
A tare mata biyun suka bi shi da kallo. Fatima kallo ne take mishi na rauni da kunya haɗe da takaicin gwasaleta da ya tsiri yi yau a gaban Fareeda. Ɗazu yayi mata, yanzu ma ya ƙara wani, idanunta ne suka cicciko da hawaye.
Ita kuwa Fareeda kallo ne take mishi na yadda a wasu lokutan ba ya iya tauna magana, sakinsu yake kamar ya ci kashi. Fisabillahi ina daɗin irin wannan? Tunanin ba abinda ya shafeta bane yasa ta watsar da abin a ranta ta kawar da kanta gefe ɗaya.
Itama Fatima ba yadda ta iya haka ta mutsuke idanunta, ta ɗauki ƙananun ledojin da suke cikin cefanenta taja ma Fareeda dogon tsaki ta wuce tana karkaɗa ƴan ƙananun mazaunanta. Ko ta manta babu ciko ne oho mata!!
Ita Fareeda abin ma dariya ya bata, ta bi Fatiman da kallo tana jinjina ƙarfin halinta. Ita ta rasa gane wannan al'amari, ita ce ya kamata tayi mahakacin kishi da Fatiman da bata duba sanayya ba ta aure mata miji ko kuwa ita Fatiman ce ya kamata tayi mahaukacin kishi da ita?
Ko da ta ƙara kallon bayan Fatiman taga ƴan ɗuwaiwakan da take kaɗawa ta kasa hana kanta darawa.
"Ke kuma da wa kike dariya?"
Mukhtar da ya isa gurin hannunshi riƙe da alƙaki yana taunawa ya tambayeta.
"Kai dai Oga kana da son jin magana. To Ni da matar mijina ne"
A tare ita da shi suka sake kallon Fatima da take gaf da isa ɓangarenta, har lokacin kuma bata canza yanayin tafiyarta ba.
Da ɗan ƙarfi Fareeda ta ƙyalƙyale da dariya, shi kuma yaja tsaki ƙasa-ƙasa.
Bai sake cewa komai ba ya cigaba da jidar kayan abinci har ya gama kaima Fareeda nata. A lokacin taja ƴaƴanta bayan tayi mishi sannu da aiki suka shige ɓangarenta.
Tsaf ya kwashe na Fatima ita ma ya loda mata a store ɗinta. Bai ganta a falo ba, bai nemeta ba ya fice zuwa ɓangaren Fareeda.
Tashar da ake karatun yara ya tarar ta kunna ma su Sayyid, ita kuma tana kicin tana wanke-wanke.
Ɗakinsa ya wuce kai tsaye, suturunsa masu ɗan yawa ya ɗiba ya fice da su zuwa ɓangaren Fatima. Sai a lokacin ya tarar da ita cikin falon, tana zaune kan kujera tayi tagumi, idanunta sun kaɗa sunyi jaaa.
"Haɗa min ruwan wanka."
Ya bata umarni ba tare da ya bi takan yanayin damuwar da yake gani kwance male-male kan idanunta ba.
Cikin ɗakinta ya shige, ya zuba kayan akan gado. Ita kuma ta wuce bayi ta haɗa mishi ruwan wankan, tana fitowa kafin ta ce ta haɗa ya kalle ta da yanayin rashin jin daɗi ya ce
"Ke gadon ma ko arzikin sif baki samu ba, yanzu a ina zan zuba kayan sakawa na?"
"Kayi haƙuri. Bari in kwashe kayan babban akwatin can sai ka zuba kayanka a ciki."
Kallo ɗaya yayi mata ya shige banɗaki.
Ita kuma ta janyo akwatunan da yayi mata na aure ta kwashe kayan cikin babban akwatin ta loda a ƙananan da babban ghana must go ɗin da ta zubo tsofaffin kayan sakawarta.
Tana kwashe kayan zuciyarta cike da tunanin inda za ta samu kuɗi da gaggawa ta sayi sif ta biya a gyara mata katakon shimfiɗar gadon da ya ɓalle da hannayen kujerun da suka ɓalle.
Ya fito banɗakin ya tarar da ita har ta gama shirya mishi kayanshi a cikin akwatin. Gaban madubi ya wuce yana goge gashin kansa zuwa wuyansa da tawul. Da murmushi a fuskarsa yana kallonta ta cikin madubi ya ce
"Na ci alkali mai daɗi a gurin Fareeda. Ni fa mayen alkaki ne, gara ki hana ni nama da kiyi min rowar alkaki. Ina nawa?"
"Alkaki?"
Ta tambaye shi da mamaki a fuskarta.
"Eh! Ba ke kika bata ba?"
"Ni wallahi ban bata wani alkaki ba. Kila dai a wani guri ta samo."
Ta amsa da dukkan gaskiyarta.
A ɗofane ya ɗora mazaunansa gefen gadon, bai manta karyewar da yaji ɓangaren da ya zauna da ƙarfi yayi jiya da daddare ba. Ya juyo da fuskarsa yana kallonta ya ce
"Alkaki fa nake nufi irin na kayan gara da amare suke zuwa gidan miji da shi. Ba ke kika bata ba?"
"Eh!"
Ta amsa a raunane, sai kuma ta saukar da ƙwayoyin idanunta ƙasa tana murza yatsun hannunta na dama cikin na hagu. Domin kawo ƙarshen duk wasu tambayoyinsa ma sai ta ce
"Kayi haƙuri. Ba ni da kuɗi ban samu yin komai na ciye-ciye ba. Rabon gadon su Ummee aka yi kuma ƴan'uwan babansu duk sun riƙe komai. Shi yasa komai ya zo min a hagugunce..."
"Au! Wai daman da kuɗin gadon ƴaƴanki kika so ki ƙayata min gida?"
Bakinsa a buɗe yayi mata tambayar.
Kamar wacce aka ɗinke mata baki. Kai kawai ta iya ɗaga masa alamar haka ne.
Shi ma dai ba shi da zaɓin da ya wuce yayi shiru. Amma a zahirin gaskiya Fatima ta sane masa, lamarinta a birkice yazo mishi, irin yadda ko a mummunan hasashe bai taɓa tunanin lamarin zai zo musu ita da shi a haka ba.
****
A bala'in maneji ko in ce a daddafe Mukhtar ya gama kwanaki ukunsa a ɓangaren Fatima. Lamarin dai ga shi nan... Ƙarerayin da tayi mishi ya rusa armashin komai.
Har Fareeda ta lura da babu wani rawar kai ko girigiɗishin amarci daga duka ɓangarorin biyu. Ita dai nata idanu, su ta kawo ta zuba musu ta cigaba da harkokinta da ƴaƴanta hankali kwance.
A yammacin da zai koma ɓangaren Fareeda jikinsa har rawa yake yi. Sosai murnarsa ta gaza ɓoyuwa, har Fatima ta lura da haka, wannan yasa jikinta ya ƙara sanyi, zuciyarta ya ƙara cika da tumbatsa da tsanar Fareeda.
A karo na biyu ya sake haɗa su a falonta Fareeda matsayinta na uwargida. Nasihar a zauna lafiya yayi musu, sannan ya faɗa musu shi ba ya sha'awar matanshi su raba girki.
"Girkin karin safe ne kawai na yarje ma kowa tayi a ɓangarenta. Amma girkin rana da dare duk mai girki idan tayi ta ɗiba ma wacce bata da girki a wadace yadda zai ishe ta.
Da za ku haɗa kanku ma ta hanyar yin girki tare da cin abinci tare ba ƙaramin farin ciki da jin daɗi zanyi ba. Kuma zan samu nagartaccen kwanciyar hankali da nutsuwa a zuciyata."
'Ashe kuwa baza ka taɓa samu ba Mukhtar'
Fareeda ta faɗi haka a zuciyarta. A fili kuwa fuskarta cike taf da murmushi.
"Fatima kin gama kwanakinki uku da addini ya baki. Yau da yamma zan koma ɗakin..."
"Oga minti biyu don Allah! Zan iya magana?"
Fareeda ta katse shi, daa muryarta a sanyaye kuma cikin ladabi.
"Ina jin ki"
Ya amsa yana tsatsareta da idanu.
Itama Fatima kai ta ɗaga ta kalleta, a sace ta gallah mata harara.
Karaf a idanun Fareeda. Murmushi ta saki cikin rashin damuwa. Idanunta ta mayar cikin na Mukhtar, da dakiya a muryarta ta ce
"Oganah, rannan kai da amarya Fatima kun nemi alfarmar in ƙara muku kwanaki. To nima dai daga baya nayi tunanin inyi ƙoƙarin kasancewa cikin uwaren gida masu adalcin da ta ambata kai kuma ka maimaita min.
Don haka na ƙara muku wata uku, sati goma sha biyu, kwanaki casa'in. Waɗanda addini ya basu kwanaki uku na ninninka muku uku sau talatin ai na ɗan kyautata ko...?"
"Kan'uba!!! Fareeda Wallahi baki isa ba!!!"
Mukhtar ya katse ta cikin fushi haɗe da miƙewa tsaye a fusace...
*Kuyi min uzuri masu karatu. Satinnan muna da biki. Daga gobe da safe za mu fara hidindimu, ina mai baku haƙurin cewa bazan samu lokacin zama yin typing ba. Ko kun ganni online na hau in duba saƙonni ne kawai ko kuma zancen masu sayen data. Sabon posting zai zo komai dare ranar lahadi in sha Allahu. Kuyi hakuri. Ina tunasar da ku ku kira ni a wannan lambar don siyen data 09077591726. Ku kira Maman Mujahid ku sayi maganin sanyi, maganinta babu da na sani in Allah ya yarda, duk wacce ta siya baza ta ciji yatsa ba👇🏽*
*Zee Maman Mujaheed mai sayar da ingantaccen maganin sanyi za ta sauƙaƙa kuɗin sayen maganin don faranta zukatan kwastomominta👇🏽*
Promo! Promo!! Promo!!! A baya tana sayar da maganin 4k ne. A yanzu ta sauƙaƙa shi zuwa 2k. Za ta rufe wannan garaɓasar ne a cikin sati ɗaya kacal! Ƴar'uwa me kike jira? Maganin nata ya samu shaidar aiki ingantacce kuma da gaugawa ake ganin biyan buƙata in sha Allah. Idan kina fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin ina mai baki shawara kiyi gaugawar siyan maganin Zee Maman Mujaheed👇🏽
Ciwon gabobi, ciwon mara, fitar farin ruwa, kaikayi gaba, rashin Sha'awa, rashin kuzari gare ki ko ga namiji, rashin ni'ima, rashin haihuwa, kurajen jiki ko na gaba, jin Zafi yayin saduwa. Maganinta cikin sauƙi kuma a gaggauce yake magance duk waɗannan matsalolin. Ki tura kudin maganin ta wannan account ɗin da ke ƙasa, sai ki tura mata shaidar biya da garin da kike ta lambar wayarta👉🏽0 816 285 9027 Ga kuma acc ɗinta👇🏽
3968303018
Zainab Shu aibu
Fcmb
*RABON AYI*
*©Fareeda Abdallah*
_*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_
_*20*_
Cikin nutsuwa taja da baya ta ƙara shigewa cikin kujeran da take zaune. Da wani irin salo ta ɗaga ƙafa ɗaya ta ɗora kan ɗaya, ta ɗaga hannu guda ta tallabe kumatunta. Ta ƙure shi da kallo tana wani irin narai narai da fuska kamar za ta saki kuka.
Tunani take yi
'Saboda Allah a maganganunta ina abin ashar da fusatarwa? Shi fa Mukhtar haka yake! Idan tsiyarshi ta motsa da abin faɗa da ba na faɗa ba duk faɗa yake yi, kamar mai aljanu ne, idan ba jirgewa suka yi ba sam ba'a samun sauƙi. Ita kam gaskiya ba ta jin za ta iya biye mishi ya ɓata mata rai a wannan lokaci da take jin zuciyarta sakayau babu wata damuwa.'
Muktar dai har lokacin yana tsaye yana huci kamar wani bijimin sa.
Yana so yayi magana, amma ya san idan ya buɗe baki domin yin magana mai daɗi baza ta taɓa fitowa daga bakinshi ba, don haka ya zaɓi yin shiru yana ƙoƙarin rage ƙarfin fusatar da yayi.
Fareeda da bata san dawan garin ba a hankali ta sake kallonshi, ta mayar da idanunta kan Fatima da take zaune tsamoo kamar kazar da aka tsamo a cikin ruwan zafi. Ta ƙura ma kan kafet idanu, ko tunanin me take yi oho!
Idanunta ta dawo da su kan Mukhtar ta ƙara rage muryarta ta ce
"Idan akwai abinda ya fusatar da kai a maganganu na Allah ya huci zuciyarka Abee"
Ta kira shi da yadda su Sayyid suke kiranshi, bata bashi damar cewa wani abu ba ta cigaba da magana.
"Idan kuma Kwana casa'in ɗin da na ƙara muku sunyi kaɗan ne to na ƙara muku wasu kwana casa'in ɗin, kaga wata shida kenan. Idan su ɗin ma sun muku kaɗan ba laifi ku ƙara wasu kwana casa'in ɗin akai, daga haka..."
Wani irin wawan damƙa da ya kai ma kafaɗarta na hagu yasa ta katse maganar da take haɗe da cewa
"Ahhhhhhh! Wayyo Allah Hannuna... Wash za ka murƙusa ni."
Sai ga wasu zafafan hawaye sun silalo daga idanuwanta.
A gaggauce ya sake ta haɗe da ja baya. Cikin fushi ya nuna ta da yatsarsa manuniya
"Ki kiyaye ni Fareeda. Ni ba sa'an wasanki bane, kar ki kuskura ki ce za kiyi wasa da ni ko kuma ki nemi raina min hankali. Wallahi tallahi baki isa ba, ba'a son kwanakin. Saboda Allah da Annabi ni ne kike kyauta da ni kamar wani tsohon kaya Fareeda? Ni? Ni kike ma haka?"
Yayi mata tambayoyin bakinsa na ɗan rawa-rawa.
Ya ƙara murtuke fuska yana sake ɗaga murya cikin bala'i da masifa ya cigaba da cewa
"Ke in banda rashin hankali da ƙuruciya ina kika taɓa jin an ƙara ma miji da kishiya kwana casa'in? Na yi magana kuma kin sake ƙara mana wasu casa'in ɗin, ke gwana har da sake ƙara wasu kwana casa'in ɗin. Haba Fareeda? Ba kya so na ne? Ko kuwa kishi na ne ba kya yi?"
Yai mata tambayoyin yana zazzaro idanu waje don tsananin ɓacin rai da takaicin da ƙari kwanakin suka cusa masa.
Ita dai har lokacin hawaye take yi, Allah ya sani sosai ta ji zafin riƙon da yayi mata. Ita ba ta son irin wannan, ita ƙashinta ba irin ƙauƙau ɗinnan bane da take jure wahala. Har yanzu zafi take ji a inda ya riƙe mata.
A hankali ta ɗago fuskarta da sukai kace kace da hawaye ta ce
"Ni ce ba ni da hankali ko Mukhtar? Ni ɗin ce dai mare hankali don na yi muku abinda kuka nema. Na gode Mukhtar, ga mai hankali nan a kusa da kai ka tattara ta ku fice min daga ɗaki. Ke kuma"
Ta mayar da idanunta kan Fatima, ta nuna ta da yatsa manuniya, cikin ɓacin rai ta cigaba da cewa
"Ba dai Mukhtar bane? Ga ki ga shi nan! Kin dai ji da kunnenki na ƙara muku kwana casa'in kan casa'in bisa wasu casa'in ɗin ko? To don Allah ki tarkata shi ki riƙe a gurinki. Amarcin da kika ce me kukai a cikin kwanaki uku ina so kije kiyi ta sharɓan romonsa har nan da shekara guda mu ga tsiyar da za ki tsinta a cikinshi..."
"Fareeda"
Mukhtar ya katse ta da kiran sunanta a haukace cikin tsawa.
Idanunsa sun kaɗa sunyi jajur ya fara kora mata kashaidi bayan ya shata rantsuwa
"Wallahi Tallahi in kika sake cewa kin bada kwanakinki ga Fatima sai nayi mugun saɓa miki anan gurin.
Ke daga yau ma na soke batun wani kyautar kwana ko me zai je ya zo a gidannan. Babu wata mace da ta isa ta ce za tayi kyauta da kwanakinta ga abokiyar zamanta.
Ni ne maigida, sai na so za'a aikata min duk irin waɗannan abubuwan a gidannan! To ba na so!! Na ce ba na so!!!"
Ya ƙarasa cikin tsawa da tartsatsi.
A fusace ya ja musu tsaki ya kaɗa kai ya shige cikin ɗakinsa na nan ɓangaren Fareeda.
Fatima ta raka shi da idanu. Zuciyarta damƙam da mamaki da tsoro. Abin har ya kai a ƙara musu irin waɗannan magagan kwanaki masu yawa ya ƙi karɓa? To saboda me? Bayan duk irin maƙudan kuɗaɗen da ta kashe gurin magungunan mata da magungunan mallaka a ina ne aka samu matsala? Lallai ya kamata ta koma baya a hankali tayi karatun ta nutsu ta gano inda ta kuskure tayi gaggawar gyarawa...'
Dogon tsakin da taji saukarsa a kunnuwanta yasa tayi gaggawar dawowa cikin hayyacinta, sai ganin Fareeda tayi ta balla mata harara da manyan idanunta ta wuce tana gaf da shigewa cikin ɗakinta.
Ita kuwa tana zaune, kamar wacce aka dasa ta a gurin, ta kasa motsawa balle har ta tashi ta fice zuwa ɓangarenta. A madadin zaman banza da tunani ma sai ta fara ƙare ma falon kallo.
Lallai dole Mukhtar ya raina mata ajawali. Ba wasu sababbin kaya Fareeda ta zuba a falon ba fa, amma saboda tun farkon sayen kayan an zuba manyan kuɗaɗe ne ba tare da ƙyashi ba an sai na gari don mayar da kuɗi gida shi yasa har yanzu kayan ƙal suke.
Ga Fareeda kamar mayya take gurin tsafta, duk iya hangenta bata hangi wani ɗan datti da za taga cikashin falon ba.
"Gaskiya da sake! Ya zama dole in shiga in fita in nemo kuɗaɗe in gyara ɗakunana."
Tayi maganar a fili, zuciyarta cike da ƙyashin kyawun ɓangaren Fareeda.
Kwatsam sai ga Mukhtar ya fito daga ɗakinsa zuwa cikin falon kamar wanda aka jefo shi. Ganin Fatima a zaune kuma babu Farida yasa shi yin turus yana kallonta da mamaki.
"Zaman me kike yi anan?"
Sai da tayi fari da idanunta sannan ta ƙanƙance murya ta ce
"Ai na zaci ka shiga ciki ka fito mu tafi ne? Haskenah ko ka ƙi karɓar mana kwanakin da ta ƙara mana har yanzu magrib da zan fita a girki baiyi ba. Gurina ya kamata a ce..."
"Girko! Fatima na ce Girko!! Za ki ɓace min da gani ko sai na ja ki a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 26