Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
buɗewa yayi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya zage ya gyara ɗakin ƙal. Sai da ya gamsu ɗakin yayi yadda yake so sannan ya fice zuwa ɓangaren Fatima. Ko da ya shiga tana zaune akan kujera. Ta yi wankanta har da kwalliya a fuskarta. Kallo ɗaya yai mata ya ɗauke, ko sannun da take mishi bai amsa ba. Ɗakin barcinta ya shige, ita dai tana zaune sai ganinsa tayi yana fitowa da suturunsa da yake cikin akwatinta. Gabanta ne ya faɗi, da saurin gaske ta miƙe tsaye hannayenta dafe da ƙirji. Bai ko kalleta ba ya fice da kayan a hannunsa, da saurin gaske ta bi bayansa ta leƙa, a zatonta ɗakin Fareeda zai kai kayan, sai taga ya nufi ɗakin baƙi da su. Daƙyar ta iya komawa mazauninta ta zauna a lokacin da yake daf da dawowa cikin ɗakin, haka ta dinga raka shi da idanu har ya gama kwashe suturunsa tas da duk wasu muhimman kayansa da suke cikin ɗakinta ya mayar ɗakin baƙi. Sau takwas tana yunƙurin yi mishi magana sai ta rasa ta inda za ta fara, har yayi fita na ƙarshe da tunda ya fita bai dawo ba. *Kuyi haƙuri. Labari ya taho gangara in Allah ya yarda.* Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya da yanmata albishir gareku BONONZA; BONONZA;BONONZA; Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB 08162859027 *RABON AYI* *32* *©Fareeda Abdallah* *_Ƴar'uwa ki tuna, kafin saukar da ko wace irin cuta, sai da aka saukar da maganinta. Don kinyi magani da yawa baki dace ba ba shi zai sa ki yanke tsammani daga samun waraka ba. Ki gwada maganin da muke karɓa ma al'ummar Annabi SAW, wata ƙila warakarki a wannan maganin yake baki sani ba. Haihuwa kike nema? Baki taɓa yi bane ko kuwa jinkiri ne kike samu tsakanin haihuwar? Sanadiyyar planning ne kika samu jinkirin ko kuwa sanyi ne yake damunki ko haka kawai? Matsalar rashin haihuwar daga mijinki yake? Muna da ingantaccen magani garanti wanda aka gwada muka tabbatar da aikinsa, in Allah ya yarda ko me ya shafi mahaifar mace da mararta wanda ya hana ta haihuwa in dai tayi amfani da saiwoyin maganinmu za ta samu biyan buƙata da yaddar Allah. Matsalar mace ko namiji 2k ne.* *Akwai ƙullin maganin da muke sayar da shi 500, in dai matsala ta shafi nonon mace da yaddar Allah za ki samu waraka. Mai ciki, mai shayarwa, mare shayarwa duk za su iya amfani da wannan magani. Ko da matsalar ciwon daji ne da ya shafi nono in sha Allah za ki sami waraka sanadiyyar amfani da wannan magani. Akwai garin maganin sanyi da za ki haɗa a cikin yaji, shi ma 500. Akwai ingantaccen maganin sanyi da za ki saya muku ke da Oga, 2k ne. In Allah ya yarda za ki sha mamakin yadda lafiya zai wadace ku ke da Oga, za ki ga yadda za ku dawo kamar sabbin amaren da suke mararin junansu😍.* *Akwai ingantaccen haɗin magani na gyaran nono wanda ni Fareeda Abdallah nake sayarwa, bokiti 1litter 2500, ƴar'uwa in dai za ki juri dama kunun garin maganin safe da dare, za kiga yadda ba cikowar nono kaɗai ba, hatta fatar jikinki sai ta canza, za kiyi kuɓul-kuɓul😍, sa'annan ni'ima bazai taɓa yanke miki ba in Allah ya yarda saboda irin haɗe-haɗen da ke cikin wannan magani. Ga duk mai buƙatar ɗaya daga cikin maganinnan da gaske ta tuntuɓeni ta whatsapp a 07039080978, idan kira ne a kira ni ta 09077591726. Don Allah ƴan'uwa🙏🏽🙏🏽🙏🏽idan ba da gaske kike yi ba kar mu ɓata ma juna lokaci.* Tun da yabar ɗakinta a yammacinnan bata ƙara ganinsa ba, har aka wayi gari. Ta leƙa tsakar gida ta windonta ya fi sau goma ko za ta ga giftawar Mukhtar, amma ko alamarsa bata gani ba. Ranta ne ya ƙara ɓaci. Minti ɗaya biyu sai ta ɗaga hannu ta shafi lafaffen cikinta. Ita kaɗai take sakin murmushi akai-akai idan ta tuno tana ɗauke da cikin Haskenta. A jiya da lamura suka ɗakko kwaɓe mata har suka ziyarci gidan Maman Murad zuciyarta cike take da nadama mai tarin yawa. Amma bayan tabbatuwar ciki a jikinta daga bakin da bazai mata ƙarya ba sai duk wani ɓurɓushin nadamar da ta fara yi ya kau. Ta san zama tsakaninta da Mukhtar a yanzu ba alfarma bace, dolen dole ne. Ga ta ɗauke da gudajin jininsa me zai sa shi sakinta? Ita fa ta riga ta san tun da Fareeda ta haifi ƴaƴa biyu wataƙila ita da ƴan uku za ta fara a gidan. "Hehehehe! Shagali! Wa ka ganni da ƴaƴa uku rigis a gidannan? Hmmm! Na rantse da girman Allah Fareeda za ki gane shayi ruwa ne." Ta faɗa a fili tana dariya irinna bosawa. Agogo ta kalla taga ƙarfe bakwai da kwata na safe. Tsam ta miƙe tsaye ta shige cikin ɗakinta, doguwar rigar barcin da yake jikinta ta cire, ta ɗauki wata ɓingilar riga da gajeren wando ta saka. Ta ɗauki Hijabi iya gwuiwa ta saka. Gaban madubi ta ƙarasa ta ɗan goga powder a fuskarta ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin. Ɗakin baƙi inda Mukhtar yayi ƙaura ta nufa, tafiyarta lafiyar Allah take yi a tsakar gidan. Amma tana isa ƙofar ɗakin tasa hannuwa biyu ta dafe mararta, ta duƙe ƙasa kaɗan, ta takwarkwashe fuska sosai, tsawon minti ɗaya tana matse-matsen idanu daƙyar ta samu nasarar matso hawaye daga cikinsu. Nishi ta fara sas-saukewa sauri-sauri. Daƙyar tasa ƙafa ta tura ƙofar, ta faɗa cikin ɗakin a galabaice. Bawan Allah Mukhtar yana kwance akan darduma a tsakar ɗakin. Ga Alƙur'ani da casbaha ajiye a gefe ɗaya, daga irin kwanciyar da yayi za'a gane irin barcin nan ne da ba'a shirya mishi ba ya samu nasarar ɗauke shi. _'Wani abu da Mukhtar ya daɗe baiyi ba shi ne tashi a tsakiyar dare yayi sallah. Ko a can baya a mafiyawancin lokuta yana ji da zarar ƙarfe huɗu da rabi na dare yayi Fareeda za ta raba jikinta da nashi, ta shige bayi ta ɗauro alwala ta fara nafila, shi kam sai dai ya gyara kwanciya._ _A daren jiya bayan shafe awoyi cikin tunani kyakkyawan alwala ya ɗauro ya fara jero nafilfili. Zuciyarsa cike da tunanin rahamar Ubangiji ga bayinsa. Shi Ubangiji mai gafara ne mai jin ƙai, duk yawan saɓon bawa sai dai in bai nemi gafara ba, abinda kawai ake so shi ne bawa yayi tuba cikakkiya da niyyar bazai ƙara komawa ga irin laifin da yake aikatawa ba._ _Bayan cikakkun awoyi uku da suka shafe shi da Ibrahim suna tattake guri akan matsalolinsa. Ibrahim ɗin ya sake jaddada masa kacokan abubuwan da suke faruwa da shi a yanzu na rashin daɗi shi ke da kaso tamanin bisa ɗari na faruwar komai. Ya kuma jaddada masa matuƙar bai ɗauki hanyar gyara ba tabbas bai ga komai ba, ya shirya ganin taɓarɓarewar al'amura ninkin ba ninkin na yanzu da yake gani._ _A matsalarshi da Fareeda baya da yanzu, shi ne ya taka muhimmiyar rawa gurin ɓata komai. A tsakaninsa da Fatima tun farkon fari ba haka ya kamata su faro tafiyar ba._ _Da yake a shirye yake da karɓar gyara ta ko wane ɓangare. Bai kawo suka ko ƙoƙarin kare kansa ba, da hannu bibiyu ya karɓi laifukansa, sannan ya buɗe kunnuwa sosai yana karɓan shawarwari daga bakin Ibrahim da yake kallon mace a matsayin wata sassauƙar aba wajen tafiyarwa. Daga ƙarshe ya ƙarƙare da ce ma Mukhtar ɗin_ _"Ban ce maka babu hatsabibai kuma shaiɗanun mata ba. Waɗanda idan bawa za ka zame musu wajen hidimtawa da tarairaya baza su taɓa yi maka da daɗi wajen zamantakewa ba. Akwai irinsu da yawa, waɗanda kamar ƙuli-ƙuli suke gurin rashin gane gabansu. Amma ni abinda na yarda da shi shi ne kaso tamanin cikin ɗari na matan da muke aure rashin fahimtarsu ke sa muke fuskantar matsala da su."_ _Ya ɗauki aniyar gyara ta ɓangaren Fareeda da Fatima. Amma Fatima ta yi mishi laifukan da baya jin zai iya ƙyale ta taci bulus ba tare da ya ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki da zai sa ta gane lallai tayi ba daidai ba. Tsakani da Allah cikin da aka ce mishi tana ɗauke da shi ko kusa baiyi murna da samunshi ba. Da irin waɗannan halaye na Fatima ta ina mutum mai cikakken hankali zai so haɗa zuria da ita?_ _To amma ya ya iya? Rabo ya rantse tsakaninshi da ita. RABON AYI aure ta samu ciki da shi Mukhtar yasa komai ya faru a baya. Lallai wannan shi ake ce ma ƙaddara ta riga fata. Tsakani da Allah ta gama sire masa a cikin zuciya, gaba ɗaya maa jikinsa ne yayi wani irin sanyi da al'amarin rayuwar duniyar. Yana tare da matarsa suna zaune lami lafiya ƙaddara da rashin jin magana irinta Fareeda da rashin haƙuri irin nashi suka ja mishi gora wajen ɗakko ma kanshi ƙajaga. Ko da ya idar da sallah a cikin addu'o'inshi sai da ya saka Fatima, babbar addu'arshi gare ta shi ne Allah ya shirye ta, Ubangiji ya cire mata ƙyashi, hassada, baƙin ciki, ƙarya, munafurci, rashin yin abu don Allah da duk wasu miyagun halaye da take da su. Matar da kuke shirin haɗa zuri'a da ita ko ɗan yaya ne dole ka dinga saka ta cikin addu'o'inka._ _Fareeda kam bayan addu'ar Allah ya huci zuciyarta kan fushin da take yi da shi, ya daɗe yana addu'ar Allah ya kawar da shaiɗanin da yake tsakaninsu. Ubangiji ya ƙara musu danƙon ƙauna da soyayya, Allah ya raya musu zuria ya kuma sauketa lafiya. Ya ƙarƙare da roƙon Allah yasa yadda take uwargidanshi anan duniya ta zama uwargidansa a aljannah._ _Ga kanshi kuma sosai ya ɗauki tsawon awanni yana addu'ar Allah ya sassauta mishi zafin zuciya, kishi, rashin haƙurin da yake ɗawainiya da shi. Ya roƙi Allah ya yaye mishi duk wani hali nashi da yake taka rawa gurin samun matsaloli tsakaninsa da iyalansa. Bai samu nutsuwa ba sai da aka kira sallar assalatu. Ya sallaci raka'atanil fijr a gida sannan ya fice zuwa masallaci. Bayan an idar ne ya dawo gida yayi azkhar, ya cigaba da karatun Alƙur'ani. Jin barci na neman fin ƙarfinsa ne yasa shi ajiye Alƙur'ani da casbahan ya kishingide nan kan dadduma. Shi ne har Fatima ta shiga ɗakin bai sani ba._ Ganin yana barci yasa ta miƙe tsaye daga duƙewar da tayi, harara ta maka masa. A zuciyarta take ayyana yau fa cikon kwana ɗayan girkinta ne, amma maimakon su kwana suna rungumemeniya yana shafa cikinta shi ne ya wulaƙantar mata da kwanan ba tare da ta mori abinta ba. "Ai wallahi baka ci bulus ba, za ka biya bashi in dai Fatima ce. A yanzu ne zan fito maka da asalin wacece ni tunda mun riga mun ƙarasa haɗewa. Yo me ya rage? Jinina da naka sun gauraya wajen samar da gudajin jinainai da za su zamo rayayyu nan gaba kaɗan ai dole in dama kunu na yadda nake so." Tayi maganar ƙasa-ƙasa ta yadda ita kaɗai take jin abinta, laɓɓanta da ke motsi ne kawai za su saka a fahimci maganar ciki take yi. A ɗan fusace ta ɗauki Alƙur'ani da carbin ta ajiye gefe ɗaya, hijabin jikinta ta cire ta hurga kan katifa, ta ɗaga vest ɗin jikinta zuwa sama sosai sannan ta raɓa ta bayansa ta kwanta haɗe da ruƙunƙume shi tana aikin goga mishi ƙirjinta. Nishi take yi a wahalce kamar wacce take cikin wani matsanancin ciwo. Idan ba sani aka yi bama yadda take goga mishi ƙirjin za'a zaci irin bugun ciwon nan ne take juye-juye ba tare da saninta ba. Kamar a mafarki yake jin nishinta, da yake da riga a jikinsa bai farga da abinda take masa a bayansa ba sai daga baya. Ko da ya tabbatar ba mafarki yake yi ba a firgice ya buɗe idanunsa. Da saurin gaske ya janye jikinsa daga nata ya miƙe zaune fuskarsa a tamke tamau. "Miye kike yi haka? Me ya kawo ki nan?" A maimakon ta amsa tambayoyinsa ko kuma ta faɗi wani abu daban kawai sai ta saka kuka. Tasa hannu biyu ta dafe saitin mararta ta cigaba da juyi tana hawaye da shessheƙa. "Kin ga, idan baza kiyi magana ba salin-alin ki tashi ki fice min daga nan." Yayi maganar cikin dakiya da ɗaurewar fuska. "Has...Aban twince cikina... marata.... bayana ciwo... zan mutu.... wallahi jiya kwana nayi banyi barci ba... har wasiyya na rubuta na aje maka a gefen gad..." "Kina jin irin ciwukan da kika lissafa ne har kika samu damar rubuta wasiyya?" Ya katseta da tambayar, a zuciyarsa yake girmama ƙwarewarta a wajen sharara ƙarya. Ɗif tayi bata amsa ba, can kuma sai ta cigaba da jan shessheƙa. "Tashi ki zauna" Ya bata umarni. A sakalce ta miƙe ta zauna tana mutsutsuke idanu da tura baki. Har ta fara jan hanci za ta cigaba da kuka ya daka mata tsawa a dole ta haɗiye kukanta. "Fatima? Wai ke wace irin macece? Yanzu don Allah bayan abinda ya faru jiya har kin samu ƙwarin gwuiwar da za ki iya fuskanta ta da wasu ƙarerayi naki?" "To ba tun jiya Hajiya ta ce kayi haƙuri ba..." "Banyi haƙurin ba. Ke saurareni kiji da kunnen basira." Ya miƙe tsaye daga ƙasa ya koma kan katifa ya zauna, har lokacin fuskarnan ba wasa. "Ke bakiyi mamaki da duk irin abinda ya faru jiya me yasa ban sake ki ba?" Wani irin rugurgujewa ƙirjinta yayi ya buga daram. A tsorace ta zaro idanu tana kallonsa, ta kasa cewa komai. "Hmmm! Bari kiji, ni a tsarina ko? Duk rashin haƙuri irin nawa saki shi ne mataki na ƙarshe da zan bi da mace wajen ladaftarwa. Akwai matakai iri-iri da ya kamata abi kafin rabuwar aure, tunda dai ke mayya ce na kaiki gidanku kin ƙi zama, to ki cigaba da zama anan ɗin. Amma na rantse da Allah na ƙaurace miki kenan har zuwa sa'adda ni a karan kaina zan gamsu da gyaruwar halayenki. Bazan hana ki ci da sha, sutura, gurin kwana da nema miki lafiya ba, hakkinki ne tunda ban sake ki ba. Amma mu'amala da miji, kulawa, soyayya, tarairaya sai dai ki gani a maƙwafta. Idan kin so ki hankalta Fatima, idan baki so ba kar Allah yasa ki hankalta ki gyara halayenki. Abu ɗaya da zan tabbatar miki shi ne daga wannan matakin idan baki gyara ba za mu kai iyaka ne tsakanina da ke. Tashi ki fitar min a ɗaki, kuma daga yau duk abinda kike buƙata ki aika min saƙo ta waya ne, kar ki sake takowa cikin ɗakinnan, idan ba haka ba Wallahi zan shayar da ke mamaki mai girman gaske. Kuma ki saka a zuciyarki ni Mukhtar na jefa ki a cikin layin maƙaryata, daga yanzu har zuwa sadda zan gamsu kin gyara halaye ko baki gyara ba Allah ɗaya kawai za ki ce min in yarda dake. Tashi ki fita tun kafin ki hassalani" Haka ta miƙe jiki ba ƙwari za ta fita a ɗakin. Maganganunsa sun daki jikinta ba kaɗan ba. "Haka za ki fita tsirara? Ko da yake je ki, daman akwai ƙarancin abinnan, fita a yadda kike so." A kasale ta juya ta ɗauki hijabinta da ke ajiye kusa da shi ta saka, ta fita a ɗakin ba tare da ko kallonsa ta sake yi ba. Tana tafe tana haɗa hanya har ta ƙarasa falonta, nan kan kujera ta zube tana hawaye, ta buɗe baki za ta kwarma ihu sai muryar Mukhtar ta ji a gefenta yana cewa "Duk da nasan ƙarya kika sharara min cewa kin kwana cikin ciwo. Ga dubu biyar nan ki tafi asibiti, na baki kuɗinnan ne kawai don kar Allah ya tuhumeni kin ce ba ki da lafiya ban kula da ke ba." Bai jira ta karɓi kuɗin ba ya ajiye a gefenta ya fice daga ɗakin yana jan tsaki ƙasa-ƙasa. ***** Da matuƙar mamaki ta buɗe baki, sai kuma tayi dariya tana kallon Kamalu da ya kasa haɗa idanu da ita. "Ɗan ƙanina, wai duka-duka yaushe maganar tayi ƙarfi ne har aka shirya maganar aure a gaggauce haka ban sani ba? Na zaci iyayen Jamilar sun ce sai tayi shekara uku a jami'a sannan za'ayi maganar aure?" Wanda ta kira Kamalu dai ba baka sai kunne, ƙara sunkwui da kanshi ƙasa yayi cikin kunya yana murmushi. "Fitsararre, ai dole kaji kunya mana tunda a gaban Fareeda ne. Wallahi a gidan in kika ga yadda ya tasa mu gaba da fitsara iri-iri za ki sha mamaki. Da fa Honey cewa yayi mu bari gobe lahadi mu shiga kasuwa haɗo lefen, amma da ya taso mu gaba da naci har da ƴar ƙwallarsa ai babu shiri muka fito a gatse-gatsen ranar nan. Allah yasa dai bamu takura miki ba Fareeda, duk mun sanki da sanin kyawawan kaya kalar ƴan birni shi yasa muka ce tsinke baza mu siya na lefennan ba sai kina gurin..." "Au! Wai yanzu kina nufin kasuwa za mu shiga Aunty Kareema?" "Eh mana babbar Yayata. Don Allah kar ki ce baza ki samu zuwa ba. Ya Mukhtar don Allah kasa baki, Wallahi tun da aka saka bikinnan kullum sai Jamcy ta jaddada min in tabbatar an zuba mata zaɓaɓɓun kayayyaki kuma masu tsada a cikin lefenta." Ya ƙarasa maganar yana kallon Mukhtar da Fareeda a marairaice. Shi dai Ibrahim ɗan dariya kawai yayi yana kallon ƙanin nasa. Hmmm! Ta yaro kyau take ba ta ƙarko, bai san a cikin rayuwar auren kashi saba'in da biyar na zamantakewar haƙuri ne jagoranta ba. Mukhtar a tausashe ya matsa kusa da Fareeda yana rarrashinta da tausasan kalamai kan ta daure su shiga kasuwar. "Ba sai kun jigata kanku wajen gama haɗa kayayyakin ayau ba. Abinda baku siya ba gobe ku leƙa ku ƙaro, jibi haka, har dai ku gama siyan duk abinda ake buƙata." "Ni fa ban ce bazan je ba Abee. Tunani nake yi, da mu wahalar da kanmu wajen shiga kasuwa me zai hana Ya Ibrahim ya faɗi iya adadin kuɗin da yake so mu haɗa komai na lefennan, yanzunnan zan kira *Hds jawellerys and more* mu tura musu kuɗaɗen su haɗa mana duk abinda muke buƙata..." *"Hds jawellerys and more?* Su wanene kuma haka?" Su ukun suka haɗa baki gurin tambayar Fareeda da mamaki a fuskokinsu. "Hds jawelleries and more business name ɗinsu ne. Kawai abinda za mu yi yanzu shi ne za mu kira Sister Hadiza mace mai haba-haba da iya tarbar jama'a a fili da cikin waya kan lambarta 08144965394. A garin kano suke, adireshin babban shagonsu suna nan kan titin gwarzo unguwar kabuga bayan gidan man AYM SHAFA..." "Haba Fareeda, duk shagunan da suke nan kaduna sai mun tsallaka kano?" Kareema tayi maganar tana ɗan ɓata fuska. "Ke kam Aunty Karima kin cika gajen haƙuri. Ki bari in kaiki mana. Kin tuna kayan da nasa da yamma nayi fitan bikin amaryar Abee da su? Har kina tambayata inda na siya lace da atamfar da sarƙa da ƴankunne haɗe da warwaraye masu kyau na ce miki Aunty Binto ce tayi min siyayyar? To ai a gurinsu ta siya min. Muna daga nan za mu aika mata da kuɗi gobe zuwa jibi da sassafe saƙonninmu za su iske mu har nan kaduna. Kuma ko rantsuwa nayi babu kaffara za kuyi mamakin irin haɗaɗɗun kayayyakin da za zuba mana a cikin akwatunan. Ke ni fa na huda ne naga jini, in kunji ana faɗin garanti trust kuma sayen na gari don mayar da kuɗi gida to kayan *Hds jawelleries and more ne*. Kuma ƙarin armashi shi ne idan da kanmu muke so mu zaɓa yanzunnan muna kiranta za ta antayo mana da hotunan sabbin yayi na kayyaki mu zaɓa mu darje. Suna da group a whatsapp da suke tallata hajojinsu👉🏽 https://chat.whatsapp.com/LpxLzmsKFFfBatQoY8q1jA Ke ko ruɗewa kikai wajen zaɓin kala da kin tura mata hoton kalar fatarki za ta zaɓa miki atamfa, ko lashi, ko material, ko shadda, ko abaya wanda zai shiga da ke sosai da sosai, duk inda kika shiga da suturan da kika siya gurinsu ayita kallonki ana tunanin ina kika sai wannan ɗanɗasheshen zanin..." "Taɓɗijan! Ni kam na ga gurin zuwa haɗo lefen Sweet Jamcy my heart. Yaya Ibrahim kawai a kira Hds jawelleries and more su haɗa min lefen amaryata." Ango Kamal ya faɗa cikin karaɗin murna. Nan dai dukkansu suka haɗu kan shawarar a kira Sister Hadiza 08144965394, sun san halin Fareeda ƙwarai. In dai ta yaba da abu, to tabbas wannan abu fa yayi ne ɗari bisa ɗari. *_Lissafin rayuwa a wannan lokaci da muke ciki🥰_* Sunana Rumanatu Bashir Abubakar. Ƴar'uwata ko ban faɗa ba kin san rayuwar duniyar kullum ƙara sauyawa take yi. Matuƙar kina so al'amuran cefane a gidanki ya tafi dai-dai sai da lissafi, tsari, da bin hanyoyin da za ki mallaki duk abinda kike so cikin sauƙi ba tare da kin ɗaga hankalin maigida ba. Duk wacce ta gane sirrin rayuwar idan an ciza sai a hura, sai kuma aɗan dakata aga sakamakon da hakan zai haifar. Da fatan Ubangiji Allah ya shige mana gaba a dukkan al'amura. (Ameen) Azumi na ta ƙaratowa, a yanzu haka da nake wannan maganar saura bai fi kwanaki hamsin da wani abu ba. Wane tanadi kike yi don mallakar kayayyakin da za su ƙayata girke-girkenki na azumi? Ko kuwa jira kike sai azumin ya zo kaya sun ninka farashi a kasuwa kizo groups kina surutun ƴan kasuwa Allah ya musu kaza da kaza? Bari in sake faɗa muku ko mu so ko mu ƙi komai yanzu sai da tsumi da tanadi. Kin ga ƴar'uwata. Muna sayar da dankalin turawa, fruits, vegetables akan farashi mai rahusa. A jos muke da zama, amma idan kika ce kina son kayanmu duk jihar da kike za mu aika miki da shi cikin ƙanƙanin lokaci. Malam bahaushe ya ce mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka. Haka zalika Hajiyoyi manyan mata idan kuka bi wannan tsarin da zanyi magana akai da zaran azumi ya zo za ki karɓi dankalin turawa, fruits, vegetables kamar kyauta aka baki👌🏽🥰. Ko maigida yaga kaya turus an aiko miki da shi ba tare da kin caje shi maƙudan kuɗi a lokaci ɗaya ba za ki bani labarin yadda zai kwashe kwanaki talatin cif na azumi yana zunduma miki albarka❤️🥰. Kamar gonar auduga haka za ki dinga ganin talatin da biyunnan a waje ko wane lokaci. Yo taya bazai miki dariya ba bayan shi a ganinshi ya tsinci dami a kala? Yana miki kallon biri kina mishi na ayaba ba tare da sanin a jikinshi kika tatsi kuɗaɗen da kika zuba a asusunmu don mallakar kayan buƙatar yau da kullum ba😂 Wannan tsarin da nake muku magana akai adashi ne za ki zuba, akwai ɗan kullum akwai na duk sati😍 amma idan lokacin kwasa yayi za ki kwashi Irish, fruits, vegetables👌🏽. A taƙaice dai Iya kuɗinki iya shagalinki Hajiyata😍💃🏽 Waɗanda suke buƙatar yin adashi da gaske domin samun cikakken bayanin yadda tsarin zubin yake ku tuntuɓeni akan lambar wayata 👉🏽 wa.me/2348065530483 *_RABON AYI_* *©️Fareeda Abdallah* *33* *Ƴan'uwa da gaskiyar Mal Bahaushe da ya ce komai yayi farko tabbas zaiyi ƙarshe. A labarin RABON AYI mun taho gangara. Ku adana lambobina guda biyu domin siyan DATA na ko wane irin layin waya. Da sauran kayayyakin da muke saidawa don taimaka ma Al'ummar Annabi Muhammad SAW. 09077591726, 07039080978* Ƴar'uwa kina fama da matsalar rashin haihuwa ko dogon jinkiri? ko kuma matsalar daga mijinki yake? Muna bayar da magani da yaddar Allah. 2k matsalar mace, 2k matsalar miji. Sanyi ne matsalarki? Irin infection ɗinnan mai sa zubar ruwa, bushewa, ƙaiƙayi, ƙuraje? Muna da kalolin maganin sanyi masu kyau in sha Allah, waɗanda

Chapter 24 of 26