Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ji shi ba. Ga yadda take jin gurin da yake a tsuke tunda aka yi mata ɗinkin ƴar sha biyar yanzu ya buɗe hayam shi ne abinda yake ƙara ba ta tsoro. Fitsarin da ya matseta har tana jin kamar za ta sake shi kan gadon yasa dole ta ƙara motsawa da ƙarfi "Wasssshhhhh! Wayyo Allah na zafiiiii.." Ta ja kalmar zafin ta sauke shi da wani irin huci mai ƙarfi da gurgani kamar matar da naƙuda fara kankama mata. Izuwa yanzu kukan ma ya ƙi zuwa, sai zare ido take yi kamar ƙwai a ledar biredi, lokaci ɗaya kuma tana haɗawa da cije laɓɓa saboda tsananin raɗaɗin da take ji, duk da fankar sama na ɗakin a kunne yake ta haɗa zufa tai kashirɓin. Babu yadda ta iya, tana ƙarasawa gefen gadon da ta kasa sauka da ƙafafunta sai kawai tayi shahadar ƙuda ta faɗa ƙasa, daɓas haka tayi zaman ƴan bori. Kasusuwan mazaunanta suka daki dandaryar tiles, wani marayan ihu ta ƙara sakewa a karo na ba adadi. Ta ɗauki sakanni tana sauke numfashi sannan ta lallaɓa a hankali da rarrafe ɗaya biyu har Allah ya taimaketa ta ƙarasa banɗaki. Sai a lokacin magana mai harshen damon da nurse ɗin da tayi mata ɗinki ya dawo mata daram a zuciyarta, kamar a lokacin take faɗa mata. "Kika ce inyi miki ɗinki ki koma kamar yarinya ƴar sha biyar?" Sai da ta kaɗa idanu tayi fari da yalwataccen murmushi a fuskarta ta amsa da eh! "Shi kenan! Tunda kin biya ni wadataccen kuɗi zanyi miki aiki har ma fiye da yadda kike tsammani. Amma fa ki sani, shi tsukewar gaban mace ya koma kamar ta budurwa idan tantanin budurci ya tafi a karo na farko ya tafi kenan har abada. Ban ce baza ki tsuke ba, za ki tsuke tsam, don fatar ciki da ta waje duk zan haɗa in ɗinke miki tsaf! Amma kar ki ce ban faɗa miki ba, duk sadda Oga ya kawo kai zai shige gurin ba ƙaramin azaba za ki ɗanɗana ba. Amma idan Allah ya taimake ki kika sami mai haƙuri zai ta lallaɓawa yana bi a hankali har ya samu nasarar shiga, duk da haka dai za ki sha wahala, amma ba sosai ba. Idan kuwa kika samu jarumin maza mara haƙuri... Hmmm! Wallahi sai ya miki fata-fata, duk wani ɗinki da muka yi miki zai kekketa shi..." "Aunty Nurse, kar ki wani damu. Ke dai kiyi aikinki yadda na ce. Daman a cikin yaƙin ƙwato ma kai daraja ta musamman dole sai an sha wahala. A mai haƙuri ko mare haƙuri na tarar da Aban twince zan jure ƙwarai don in ƙara samun tambarin jarumar mata a zuciyarsa. Idan komai ya kammala nasan ba ƙaramin tarairaya da gata zan gani a wannan dare ba, saboda ya tarar da ni a yadda bai taɓa tsammani ba" Wasu zafafan hawaye ne suka sake silalo mata da zuwa ƙarshen tunaninta. Kamar wacce ta haihu, haka tai ta tara ruwa mai zafin gaske tana shiga ciki, duk azaba haka ta jure. Fiye da sau takwas tana canza ruwan kafin Allah yasa ta fara jin dama-dama. Ta gwada miƙewA tsaye taga ta miƙe, ta gwada tafiya taga tana yi a hankali, duk da ƙafafunta a tattale suke kamar ta ɗan shayi ai babu laifi, matar da a ɗazu ta kasa tafiya, yanzu da take yi ko a bobbotsere ne ai ta gode Allah. Balle ma tana saka ran yinin da za tayi yau tana shiga ruwan zafi zuwa dare komai na jikinta zai koma yadda yake. Idan yaso ma a sake zagaye na biyu. Yo miye a ciki? Wannan ai shi ne auren. Gara ta lallaɓa ta koyi juriya, so take su gogu ita da Aban Twince, su murzu sosai a cikin kwanaki ukunta na amarci. Tunda wancan ƴar buƙulun ta ƙi ƙara musu kwanaki. *** Lamo yayi akan katifa kamar mai zazzaɓi, saboda tsabar damuwa da tunanin da yayi masa yawa ya kasa janyo filo a gefensa ya ɗora kai. Hannayensa biyu yayi matashin kai da su, ƙwayoyin idanunsa na kallon sama, a kallon farko sai ayi tsammanin ƙirga layin PPC da aka sa a saman ɗakin yake yi, amma ba haka bane, tsananin nisa a cikin tunani ne. Surar jikin Fatima kamar hoton da aka maƙala a duk inda ya juya idanunsa, sam ta ƙi ɓace masa a cikinsu. Mamaki yake yi, mamaki mai tsanani ƙwarai. Wai don Allah me ya shiga cikin nutsuwa, hankali, da idanunsa har ya kasa gano ramar Fatima? Yadda yake gogagge kuma wayayyen matashi ai ya kamata ko a ido ya iya banbance kayan kanti da na shago. Bazai manta wani abokinshi Sunusi da yayi aure shekaru uku baya ba. Ya auro wata yarinya a ƙauye ramammiya sosai, saboda ramewarta shi yayi tsammanin sikila ce. Tunda Sunusin ya tabbatar mishi ba sikila bace haka yanayin jikinta yake ya tasa shi gaba da tsokana da dariyar mugunta. Minti ɗaya biyu sai ya kalli Sunusin yana ƙyalƙyala dariya ya ce "Kai kuwa Sunusi don Allah me ka gani a jikin wannan lamba One ɗin? Kana ganin mace ko a cikin kaya ba tsoka ba alamar tsoka ina ga ta tsaya zir a gabanka? Ƙarmanjola kenan" Sai ya sake kwashewa da mahaukaciyar dariya ya cigaba da nuna Sunusin da yatsa, a lokuta da dama har ƙwalla yake yi saboda dariyar mugunta. Ashe shi ma yana da rabon auren irin wannan matar a rayuwarsa? Ku gane Shi fa ba ramammiyar mace ne ba ya so ba, amma a gaskiya ba ya son macen da ramarta ya cika yawa sosai ɗinnan. "Fatima kin ha'ince ni." Ya sake faɗa a karo na biyu zuciyarsa na ƙara ƙuntata. Wani abu ne ya faru a yanzu da ko a cikin tarihinsa na baya bazai ce da wayonsa ga sadda abin ya faru ba, wannan abu ba komai bane face fitowar wasu ƴan ƙananun ƙwallah a idanunsa. Ya runtse idanunsa da ƙarfi, ƙwallar suka gangara gefe da gefe har cikin kunnuwansa, zuciyarsa cike da addu'ar Allah yasa barci ya ɗauke shi ko zai samu sauƙin tunanin da yake yi, barcin bai zo ba ya ji ladanin unguwarsu ya kwaɗa kiran sallar farko. **** Ko da ake cewa ba'a iya barci a daren da aka tabbatar miji yana can zai haɗa shimfiɗa da wata macen ita kam yau an samu akasin lissafi a kanta. Tunda suka fice da zantukan rainin wayonsu suka barta cikin ƙunci, tai takwa-takwa da fuska za ta fara hawaye da sauri ta haɗiye kukan. 'Kukan me za kiyi kuma Fareeda? Bayan aikin gama ya riga ya gama?' Ƙoƙarin tattare tunaninsu tayi ta ajiye a gefe ɗaya. Taje ta rufe ƙofar falonta, ta dawo ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala, tana ji ya dawo yana ƙwanƙwasa ƙofa taba banza ajiyarshi. Ta shimfiɗa dadduma tayi shafa'i da wutiri. *_Ya ke ƴar'uwa mai karatun wannan labari, ina baki shawarar ki saki kowa ki kama Allah. Kar ki kuskura ki manta da Allah a lokacin farin ciki ko ƙunci. Shi fa Ubangiji ako da yaushe ƙofofin rahamarsa a buɗe yake, jira yake kawai bawa ya roƙa da ikhlasi ya amsa masa. A duk sa'adda kika dogara da Allah mafificin dogaro na haƙiƙa kuma da zuciya ɗaya tsarkakakkiya tabbas addu'arki za ta dinga amsuwa kamar yankar wuƙa. Idan kuma ba abin alkairi bane kike roƙa Allah zai sanyaya miki zuciya, ya cire miki damuwa da son ganin biyan buƙatar da gaugawa, a sannu a hankali sai ya canza miki da mafi alkhairi. Ko da duk duniya maƙiyanki ne aduk lokacin da suka nufo ki da yaƙi Ubangiji shi zai tare miki. Ko ba'a so ana ji ana gani za kiyi ta cigaba, a rasa ta yadda aka yi duk wani mugun abu baya samunki. Dogaro ga Allah yayi ƴan'uwa, ku gwada za kuga alkhairi._* A wannan dare bayan ta idar da shafa'i da wuturi, ta ɗauki lokaci tana istigfari, hailala, tasbihi da godiya ga Allah kan ni'imomin da yayi mata. Abu uku ta daɗe tana roƙa, abu na farko ta samu nannauyan barci a wannan dare, na biyu Allah ya cire mata damuwar Mukhtar na can kwance da tare da Fatima. Na uku ta roƙi Allah yasa duk ni'imar da Mukhtar zai ɗanɗana a jikin Fatima kar ya ɗanɗani ko kwatan wanda yake ɗanɗana a jikinta. Bayan ta gama addu'o'in ta bi lafiyar gado, ta kwanta ta tasa ƴaƴanta a gaba ta rungume su. Tana hammar barci ta janyo wayarta ta kunna ƙira'ar Sudais cikin suratul Baƙara, ta daidaita ƙarar wayar baiyi yawa ba baiyi kaɗan ba ta aje wayar, ta lumshe idanunta tana sauke numfashi cikin nutsuwa. Wani nannauyan barci ne yayi awon gaba da ita irin wanda ta daɗe rabon da tayi irinsa. Fitsari bai tashe ta ba, ƴaƴanta biyu da Hajiya ta ce ta dinga saka su fitsari cikin dare basu tashe ta ba, kuma basuyi fitsarin kwancen ba. Duk ƙara irinna alarm ɗin wayarta da yake bugawa ƙarfe huɗu na dare sam bata farka ba. Ta farka ne a daidai lokacin da Ladan ya tada iƙamar sallar asubah. Cikin nutsuwa ta farka da salati a bakinta, da farko kamar a mafarki take ji an tayar da sallah, sai da ta ƙara saurarawa sosai sai taji da gaske fa sallah ake yi. Sai ta miƙe a firgice tana taɓa wandunan yaran, ko da taji basu tsula ba ajiyar zuciya ta sauke. Ta ɗauke su ɗaya bayan ɗaya takai su bayi suka yi fitsari, bayan ta sake kwantar da su ta koma bayi ta ɗauro alwala. Zuciyarta sakayau, babu nauyi balle damuwa ko kaɗan, ta ma manta da Mukhtar balle wata Fatima karan kaɗa miya. Cikin nutsuwa ta gabatar da sallar raka'a tanilfijr sannan ta gabatar da sallar asubah! Bayan gama tasbihi tayi azkhar, ta ɗauki lokaci mai tsawo tana karatun Alƙur'ani mai girma, har gari yayi haske sosai bata kammala ba, kwatsam taji ana ƙwanƙwasa mata ƙofar falo. Sai da ta kai aya sannan ta miƙe a nutse da hijabin jikinta taje ta buɗe ƙofar. Yana shigowa da wani irin zafin nama ya kai mata wawuyar runguma. Kasancewar tana ankare da shi, matuƙar ƙoƙari tayi gurin gocewa ya rungumi iska. Cikin wayancewa da ƙwarewa a iya basarwa ta ja da baya a tsorace, ta zazzaro idanu waje, hannayenta biyu dafe da ƙirji ta ce "Oga Lafiya?" "Lafiya ƙalau" Ya amsa da wata shaƙaƙƙiyar murya. Kafin ta ce komai ya sake cewa "Miye haka? ina ƙoƙarin riƙe ki kin wani zille" "Da alwata ta." Ta faɗa kai tsaye. "Me ya haɗa riƙe kin da zanyi da alwalarki...?" "Oga mana, ka san kai ɗin fa ba dama ne. Alwalata zai iya karyewa daga riƙon da kake mishi kallon ba wani abu bane" Ta ƙarasa haɗe da kashe mishi ido ɗaya. "Ina kwana Angon Fatima? Ina fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya kai da amaryarka?" Da murmushi sosai a fuskarta ta gaishe shi, har tana ɗan duƙawa a ƙasa. Ya buɗe baki zaiyi magana buff aka buɗo ƙofar falon, a tare su biyun suka kai idanunsu kan ƙofa, wa za su gani? Fatima ce tsaye ta riƙe ƙugunta da hannu biyu. Ta sha kwalliya sosai, ta fito a amaryar turawa sak! Domin kuwa ta tsuke ne cikin wani matsattsan wando wanda da kaɗan ya ɗara gwuiwarta da ƴar fingilar riga. Ta yi amfani da kayayyakin cikonta gaban da bayan sun taso ɗam-ɗam gwanin ban sha'awa. Lokaci ɗaya Mukhtar ya fara harhaɗe girar sama da ƙasa zai ɓalle tsiya, daman kwana yayi da masifaffen haushinta a ransa. Lura da hakan da tayi cikin kissa da iya ƙwarewa a ladabi ba don Allah ba sai don tura ma wata haushi da saurin gaske ta zube a gabansa gwuiyawunta a ƙasa. Kamar an buɗe famfo sai ga hawaye shar! shar!! Bakinta na rawa ta ce "Allah ya baka haƙuri Haskenah. Don Allah don Annabi kayi haƙuri, Allah ya huci zuciyarka. Yunwa, yunwa ce ta fito da ni har linzamin tunanina ya ƙwace na faɗo muku kai tsaye ba tare da sallama ba. Haskenah, ɗan abinda na ci jiya da daddare duk ya gama tsiyayewa..." "Ke dallah saurara min kina ta wani zuba shaaaa kamar kanyar da ba zaƙi. Kije ɓangarenki ki dafa ruwan zafi, zan taho miki da kayan tea da biredi." Yayi maganar a gundure, fuskarnan a ɗaure tamau. Cikin nutsuwa Fareeda ta juya zuwa cikin ɗakinta, kwatsam ta tsinkayi muryar Fatima a raunane tana cewa "Ko za ka yi ma Aunty Fareeda magana ta sammin ruwan zafi..." "Saboda me? ita ɗin baiwarki ce?" Ya jefa mata tambayoyin cikin tsawa. Sai da ta sunkuyar da kanta ƙasa, a yanayi na muzanci da jin kunya ta ce "Dama... dama... dama... ba ni da gas ne. Ban samu sararin sayen gas ba, abin girki da gawayi na zo da shi kuma babu gawayi." Mukhtar da ya tsani tsaki a yanzu ƙarfi da yaji yawan tsakin na nema ya aure shi. Wani dogon tsaki yaja ya galla mata harara, ko kaɗan kwalliyarta bata burge shi ba, domin ya ga gaskiyar abinda ake rufewa wannan kwalliya duk bula ce. Fareeda na gaf da shigewa cikin ɗakinta ya kira sunanta a tausashe. A hankali ta juyo ta zuba manyan idanunta cikin nasa. Ƙoƙarin tausasa maganar da zaiyi yayi, ba don komai ba sai don kar Fareeda ta ji babu daɗi. "Ko kina da ruwan zafi a flask ki sammata? kin ji ba ta da gas sai abin girkin gawayi..." "Idan ka fita ƙofar gida, nan ɓangarenmu gida na huɗu a hannunka na hagu suna sayar da gawayi. Suna ƙulla na hamsin da ɗari, kwatan buhu, rabin buhu, buhu guda zuwa buhu ashirin duk suna sayarwa. Ka siyo mata gawayin kawai. Ni wallahi shigowarka ce ta fito da ni falo, karatun Alƙur'ani nake yi. Don Allah kar ka tilastani ba ta ruwan zafi alhalin ba hakkina bane." Cikin ɗakinta ta shige ta barsu a gurin. Mukhtar da Fatima suka rakata da idanu har ta ɓace ma ganinsu. Fareeda ce tayi maganar, amma Allah ya sani haushin Fatima ya ƙara ji a zuciyarsa. Tana tsugunen nan yayi mata wata muguwar damƙa a kafaɗarta ɗaya ya miƙar da ita tsaye, kafin ta gama daidaita tsayuwa ya finciketa da ƙarfi suka fice daga falon, tana wash-wash saboda ciwon da yaji mata amma bai saurara mata ba sai da suke je falonta, ya watangarar da ita ta tafi taga-taga za ta ci da baki da saurin gaske ta dafe hannun kujera, idanunta a warwaje saboda bala'in tsoron da ta ji. *Zee Maman Mujaheed mai sayar da ingantaccen maganin sanyi za ta sauƙaƙa kuɗin sayen maganin don faranta zukatan kwastomominta👇🏽* Promo! Promo!! Promo!!! A baya tana sayar da maganin 4k ne. A yanzu ta sauƙaƙa shi zuwa 2k. Za ta rufe wannan garaɓasar ne a cikin sati ɗaya kacal! Ƴar'uwa me kike jira? Maganin nata ya samu shaidar aiki ingantacce kuma da gaugawa ake ganin biyan buƙata in sha Allah. Idan kina fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin ina mai baki shawara kiyi gaugawar siyan maganin Zee Maman Mujaheed👇🏽 Ciwon gabobi, ciwon mara, fitar farin ruwa, kaikayi gaba, rashin Sha'awa, rashin kuzari gare ki ko ga namiji, rashin ni'ima, rashin haihuwa, kurajen jiki ko na gaba, jin Zafi yayin saduwa. Maganinta cikin sauƙi kuma a gaggauce yake magance duk waɗannan matsalolin. Ki tura kudin maganin ta wannan account ɗin da ke ƙasa, sai ki tura mata shaidar biya da garin da kike ta lambar wayarta👉🏽0 816 285 9027 Ga kuma acc ɗinta👇🏽 3968303018 Zainab Shu aibu Fcmb *Jinjina ga makaranta labarin Rabon Ayi aduk inda kuke a faɗin duniya🥰🥰🥰 ina maraba da gyara, sharhi, ƙorafi ko shawarwari ta whatsapp a lambar wayata👉🏽 07039080978. Masu sayen data ma su tuntuɓeni ta kan lambar, idan kuma ba ni a online ku kira ni kai tsaye ta wannan lambar 09077591726. Son ƙauna😘😘😘😘* *RABON AYI* *©️Fareeda Abdallah* _*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_ _*19*_ Ya daɗe tsaye yana sauke zafafan numfashi a tsakiyar falon. Idan ya kalleta, sai ya kalli cikin falon ya sake kallon irin kujeru da labulayen da ta zuba, waɗanda ko makaho ya laluba ya san ba masu tsada bane. Da sassarfa ya taka ya shige kicin ɗin, wani jiri da ya nemi kayar da shi da saurin gaske ya rirriƙe Cabinet da hannu bibiyu, yana ta sauke numfashi sama-sama. Ƴan kayayyakin kicin ɗin da ta zo dasu duka-duka ga su nan babu yawa, idan aka tattara su duka baza su cika buhun suger ba, idan kuwa sun cika baza su taɓa fin buhun suger ba. Kuloli masu sauƙin kuɗi guda biyu, sai farantan cin abinci dozen ɗaya, kwandon kifa wanke wanke, kwandon tsane shinkafa, tukwanen tower guda uku, jug da ƙananun kofunansa, tarkacen cokula da ludaya, bahon wanka babba da ƙarami, bokiti guda biyu, sai wasu manya kofuna na ɗidan ruwa, ga abin girkin gawayi nan babba da ƙarami ajiye a gefe guda. Ko flask Allah baisa idanunshi sunyi katarin hangowa ba. Da wani irin sanyin jiki da na gwuiwa ya fice daga kicin ɗin ya koma falo. Tana tsugune a inda ya barta, irin yadda take zare idanu ya tabbatar mishi a bala'in tsorace take, kamar ya ce kyat! ta zura da gudu. Kujerar da ke kusa da ita ya laluna ya zauna a hankali, yayi tagumi da hannu bibiyu yana kallonta. Can dai ya buɗe baki daƙyar, muryarsa na fita a hankali ya ce "Fatima!!! me yasa kika yi min ƙarya?" "Banyi maka ƙarya ba! Wallahi banyi maka ƙarya ba!! Na rantse da Allah banyi maka ƙarya ba!!! Haskenah don girman Allah kayi haƙuri..." Ta jero maganganun cikin sauri tare da saukar wasu zafafan hawaye a idanunta. Laɓɓan bakinta sai rawa suke yi saboda tsananin tashin hankali. Kallonta yake yi, mamakinta yake yi da har ta iya rantsewa da girman Allah bata yi mishi ƙarya ba. Ya sauke ajiyar zuciya, ya gyara zama ta hanyar miƙar da ƙafafunsa, ya kalleta, ko kaɗan kukan da take yi bata bashi tausayi ba. "Satin da ya wuce, ina gurin aiki kika kira ni da zancen ga ki a kasuwan barci. Da na tambaye ki me kika je yi kika ce min dubu ɗari uku ne kika je rage siyayyar kayan kicin, ga shi kinyi siyayyar kuɗin hannunki sun ƙare gaba ɗaya babu kuɗin da za ki biya me motar da zai ɗaukar miki kaya. A take na tura miki da dubu goma kuɗin mota. Anyi haka ko ba'a yi ba?" Hawayenta ne suka ƙara ƙarfin sauka, a kasalance ta zame daga tsugune ta zauna a ƙasa. Ta saukar da idanunta ƙasa sosai ta amsa da "Anyi haka! Kayi hakuri, dubu hamsin ne naje siyayyar da su ba dubu ɗari uku ba. Tabbas anan na faɗa maka ba daidai ba..." "Kin kuma yi min ƙarya ta hanyar kwaɗaita min za ki sai mana kayan ɗaki masu ƙoluluwar tsada. Tsakani da Allah ni kuma na saka rai, saboda ɗabi'a ce irinta ɗanAdam duk sa'adda aka ce za'a yi mishi wani abu dole ya saka rai. Sai yanzu kawai na ganki da waɗannan sakarkarun kayayyakin da a kallonsu kawai za'a gane na hannu ne. Saboda Allah Kin san ba ki da kuɗin sayen kaya masu tsada me yasa kika ce min za ki siya?" Lallai baki shi ke yanka wuya, a wannan gaɓar ta kasa magana, ina ma ƙasa za ta tsage ta shige don kunya?. A zuciyarta ta tsine ma yar mijinta da ta sa aka raba gado kuma aka hana ta kason ƴaƴanta ya fi sau ashirin. Da ta rasa abinda za ta ce don kare kanta sai kawai ta ƙara ƙarfin kukanta, daga sharɓen hawaye zuwa jan shessheƙa da jiniyar kuka ƙasa ƙasa. "Kinga, Fatima ni ba na son ƙarya. A rayuwata na tsani ƙarya, na tsani maƙaryaci. Sam Fareeda ba ta min ƙarya, za ta faɗa min gaskiya ko da ɗacin gaskiyar zai sa in kwana in yini in ɗauki tsawon sati biyu ina mata masifa. Haka kuma na tsani yaudara da munafunci. Waɗannan munanan halayen guda uku wallahi na tsane su, na tsani masu yin su. Kin ga daga fara tafiyarmu da har yau bamu yi wata biyu ba, kinyi min ƙarya ta hanyar kayan ɗaki, abinda kika ce za ki zo da su ba su na gani ba. Kin yaudare ni ta hanyar yin ciko na abubuwan da ko kusa ba ki da su. Fisabilillahi me yasa za kiyi haka? Da kika ga da gaske aure za muyi me yasa ko sau uku ne baki fito babu kayan ciko don in ɗan fahimci yadda kike kamar 1 a cikin riga ba? Bazan ɓoye miki ba. Wallahi raina yayi bala'in ɓaci kan wannan yaudarar da kika yi min. Ki auna lamarin ke a karan kanki, da ace ni ne nayi miki ƙaryar ina da wani abu sai da muka yi aure kika tarar ba haka ba fa? Wannan yaudarar da kika yi min da zan kai zancen kotu tsaf alƙali zai raba aurenmu, saboda nayi hidimar mallakar wayar Samsung ne na tsinci waya rakani banɗaki a cikin kwalin Samsung ɗin da aka bani. Alƙali zai tilasta ki duk da wani abu ya shiga tsakaninmu zai sa ki biyani kaf abinda na kashe na hidimar auren ki..." "Kayi hakuri! Don Allah kayi haƙuri. Kar ka kai ni kotu, don Allah kar ka bayar da dama a raba aurenmu. Mukhtar wallahi tallahi ina son ka, irin tsananin soyayyar da babu wata ƴa mace da ta taɓa gwada maka irinsa, ka bani dama ko ɗan yaya ne, wallahi zan yi maka biyayya kamar baiwa da ubangidanta! Duk abinda kake so zan so shi ko da zuciyata ba ta so. Don Allah kar ka sake ni. Bazan sake yi maka ƙarya ko yaudara ba, nayi maka alƙawarin wannan." Ta ƙarasa maganganun tana rusa kuka gwanin ban tausayi, zuciyarta sai wani irin bugawa take yi fafafat! Kalmar rabuwa tsakaninta da Mukhtar kalma ce da ko a mugun mafarki ba ta fatan ya taɓa wanzuwa. Idan ya sake ta ina za ta jefa kanta? Magauta za suyi mata dararraku ba dariya ba. Ko a gurin Fareeda da mutanenta ai ta shiga uku, ƙaryarta ta ƙare. "Hmmm! Allah yasa hakan! Ni dai na faɗa miki ki kiyaye. Kin ganni nan ba ni da haƙuri ko ƙanƙani, ɓarna dubu gyara dubu. Kamar kunama nake a taɓa ni ko da kuskure ne aji ɗau! Idan kina son zamanmu ya ɗore lafiya ki kiyaye duk abinda zai janyo mana saɓani." Yana gama faɗin haka ya miƙe tsam ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, har ya kusa bakin ƙofar sai ya dawo ya tsaya daidai ƙafafunta, ya nuna mazaunanta da ƙirjinta da yatsarsa manuniya. "Sannan cikon da kike yi anan da can kar ki kuskura ki ƙara yi min amfani da su a gidannan. Ki tsaya a iya halittar da Allah ya baki. Kashaidi na ƙarshe da zanyi miki akan ciko kenan. Na hana daga yanzu, ba na so, ruwanki ne ki nemi magungunan da za su sa ki ɗanyi kumari, ruwanki ne ki tsaya a bushe. Ciko dai na hana daga yanzu. Ke ni ko sha ka fashe za ki nema can matsalarki, ni dai kar ki kuskura ki ƙara yi min kwalliya da kayan da ba naki ba. Na faɗa miki!!" Bai jira ko za ta ce wani abu ba ya fice daga ɗakin. Ya so yaje ɗakinshi na ɓangaren Fareeda yayi wanka, amma haka nan ya haƙura. Ya shiga motarshi ya fice daga gidan. Ƴan kuɗaɗen da suka rage masa a cikin acc ya cire ya shiga kasuwa, dangin kayan abinci ya loda babu laifi, duk wani abu da yasan mace za ta nema wajen yin girki ya saye shi. Sai da ya gama siyayya tsaf sannan ya sai ma Fatima ƙaramin gas, 6kg. Ya sai mata ƙaramin flask, yaja motarsa zuwa gida. Bayan ya ajiye motar ɓangaren Fareeda ya wuce. Ya tarar da ita cikin ƴaƴanta sun sha kwalliya gwanin ban sha'awa. Suna zaune akan teburin cin abinci suna karyawa, dankalin turawa ne da soyayyen ƙwai, ga kofin tea a gaban ko wannensu. A gefe guda kuma ga faranti nan shaƙe da dubulan da alkali, irin yadda suka yi kyau a ido kawai sun isa bayyana irin daɗin da za suyi a baki. Da sauri yaran

Chapter 13 of 26