Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kawai tai tayi da kuɗaɗe ba tare da tunanin irin wannan lokacin zai iya zuwa ba. "Na amince" Ta amsa a raunane. Ko minti biyar ba'ayi ba da yake yana acc ɗinta taji wayarta yayi ƙaran shigowar saƙo, tana dubawa taga ɗari da ashirin ɗin ne ya turo mata. Tsananin farin ciki yasa ita kaɗai ta fara ƙyalƙyala dariya, kamar wata sabuwar kamu. Tana wannan dariyar taji kamar ana ƙwanƙwasa mata ƙofar falo. Ajiye wayar tayi a kusa da ita ta ƙara saurarawa da kyau, sai taji tabbas ƙwanƙwasawar ake yi. Agogon fuskar wayar ta kallah taga ƙarfe takwas da minti arba'in da bakwai na safe. Hijabi ne a jikinta, sai ƙarfe takwas ta samu sararin gabatar da sallar asubah tun da ta idar shi ne bata cire ba ta zauna kiran lauya. Har za ta fita sai tayi tunanin idan ba Mukhtar ba wa zai ƙwanƙwasa mata ƙofa da safennan? Hijabin ta cire ta aje a gefen gado, ta cire zanin da ta ɗora kan rigar barcin jikinta tayi sallah ta ajiye. Ta sake kallon rigar barcin jikinta, shara shara take ana ganin komai na jikinta. Murmushi ta saki ta nufi ƙofar falon ta buɗe tana ta wani gantsare - gantsare. Suna haɗa idanu ta sakar mishi lallausan murmushi, da wani irin salon rangwaɗa ta gantsare sannan ta duƙa a gabanshi kamar za tayi ruku'u, ƴan mamunanta suka fito sosai ta gaban rigarta ta ƙale mishi idanu ɗaya haɗe da cewa "Haskenah! Barka da asubah hasken zuciyar Fatima. Ina fatan ka tashi cikin aminci da ƙoshin lafiya?" Ƴaƴansa da ke tsaye gefensa yayi saurin mayar da su baya haɗe da cewa "Miye haka kike yi? Dallah ki miƙe tsaye bakya ganina tare da yara ne?" Ya ƙarasa maganar haɗe da ɗaure fuska tamau. A saɓule ta miƙe tsaye tana tura baki. "Fareeda ba ta da lafiya. Za mu tafi asibiti yanzu..." "Allah ya sauwaƙe" Ta katse shi tare da mayar da ƙofar falon za ta rufe. Hannunshi ɗaya yasa ya danne ƙofar "Za mu bar yara a hannunki ne..." "Yara kuma?" Tayi mishi tambayar tana yamutsa fuska. Allah ya sani ta tsani wahalar ƴaƴa, nata ƴaƴan ma ƙannenta ke ɗawainiya da su, shi yasa babu wani shaƙuwa mai girma tsakaninta da yaran har aka raba su. Ganin wani mugun kallo da ya aika mata yasa tayi saurin cewa "Shi kenan! Ba damuwa. Kai kuzo mu shiga ciki" Ta miƙa hannu da nufin janyo Shahid da tun ɗazu take kallon yadda yake leƙota daga bayan Uban. Aikuwa a tsorace yaron ya fashe da ihun kuka yana ƙamƙame ƙafafun uban. Sayyid ganin ɗan'uwanshi na kuka shi ma ya fashe da kuka yana rirriƙe ɗan'uwansa. "Daman ba kiyi niyyar riƙe su ba." Yayi ƙwafa, sannan yaja hannun ƴaƴansa a fusace suka bar gurin. Cikin rashin damuwa ta mayar da ƙofar ta kulle. "Ai kam dai banyi niyya ba. Haka kawai ina zaƙin amarcina na samu an raba ni da nawa yaran za ka fara haɗa ni da wata wahalar? Bazan ɗauka ba. Ba ni na ɗora mata ciwo ba don haka ko za ta mutu taji da ƴaƴanta." Taja dogon tsaki sannan ta shige cikin ɗakinta. Wayarta ta ɗauka ta duba lafiyar kuɗinta tana sakin murmushi. Nan gefen gado ta zauna ta fara kasafta yadda za ta bi da kuɗin daki-daki gurin magance matsalolin da take ganin su suka sa Mukhtar yake mata gani-gani. Mintuna goma tsakani taji ficewar motar Mukhtar. Cikin gyatsine ta ce "A gayas, Umma ta gaida Assha." ***** Ko da suka isa asibiti babu ɓata lokaci aka bata gado saboda yadda ta galabaita sosai. Bayan duk wasu gwaje-gwaje, Likita ya tabbatar musu tana da ƙaramin ciki na wata biyu, sai kuma tyohoid ɗan kaɗan a jikinta. Saboda tsananin murnar jin tana da ciki bakin Mukhtar ya ƙi rufuwa. Sai rungume su Shahid yake yi kamar wasu manyan yara yana basu labarin Ammee za ta haifa musu ƙani. Suna so? Ɗaga kai suka yi suna dariya ganin yadda yake dariya amma ba don sun fahimci abinda yake nufi ba. Su da suka bar gida tun safe ba'a sallamesu sai da yamma liƙis. Ruwa leda biyu aka ƙara mata, kuma likita ya ce a barta ta huta ta hanyar samun wadataccen barci cikin nutsuwa. Ita kuma Fatima wannan yinin asibiti da suka yi abin yayi mata daidai. Akwai wani yaro a maƙwaftansu da ta sani kafinta ne, tun safen ta kira shi yaje gidanta. Ko da ta nuna mishi kujeru da shimfiɗar gadonta tana tambayarshi nawa za ta kashe gurin gyara su zama lafiyayyu? Domin kujerun har yadinsu take so a canza. Kasancewar yaron yana da tsoron Allah kuma akwai zaman amana kai tsaye ya ce mata in dai za ta ji shawararshi ta canza kujerun kawai, saboda ruɓaɓɓun katakai ne aka lulluɓe su da katifa da yadi. "Aunty Fatima ko kin gyara waɗannan sake ɓallewa za suyi. Amma idan za'a sami dubu tamanin a hannunki akwai wasu lafiyayyun kujeru a ƙasa da sai a kwashe waɗannan a kawo miki waɗancan." Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tana jinjina shawarar da ya bata. Ta marairaice sosai tana kallon yaron mai suna Khalipha ta ce "Wannan harka taimaka min za kayi Khalipha. Ka ga waɗannan ruɓaɓɓun kujerun wallahi a dubu tamanin da biyar suke a hannuna. Asabe Dillaliya cutata tayi, Allah zai min sakayya tsakanina da ita. Ka taimaka don girman Allah in baka cikon dubu hamsin ka kwashe wannan ka kawo min waɗancan..." "Ina.. Ai hamsin baza ta yi ba Aunty Fati." Taja yaja dai daƙyar ya karɓi dubu saba'in. Ta bashi dubu biyar kuɗin wasu sabbin shimfiɗun gado da zai kawo mata. Sai dubu biyar kuɗin motar da za'a kwaso kayan. Yana fita bai ci awa biyu ba sai ga sababbin kujeru masu kyau daidai gwargwado ya kawo mata. Cikin ƙanƙanin lokaci aka kwashe tsoffin kujerun da shimfiɗun gadon aka zuba mata sababbi. Sai ga guri ya fara fitowa tsaf. Bakin Fatima har kunne saboda tsananin farin ciki da jin daɗi, ita kaɗai sai safa da marwa take yi tsakanin uwarɗaki da falo tana ƙyalƙyala dariya. Idan ta gaji da zurga-zurgar sai ta daka tsalle ta haye kan kujera tana sauke ajiyar zuciya, kujeru daƙauƙau, duk tsallen da tai tayi a kansu ko motsi basu yi ba. "Saura labulaye." Ta faɗa a fili tana kallon yadda ko kusa kalar kujerun basu shiga da labulayen ba. Cikin ɗaki ta shige da sauri ta ɗauko wayarta, lambar wata tsohuwar ƙawarta Jamila da take aure kusa da kasuwar barci ta lalubo ta danna mata kira. Sun taɓa magana da Jamilar ta tabbatar mata ana samun labulai masu kyau kuma cikin sauƙi a gwanjo, waɗanda idan ba ke kika faɗi cewa gwanjo bane za'a rantse da Allah sababbi ne. Bayan gaisuwa Jamilar ta tabbatar mata in dai da kuɗi a ƙasa to akwai kaya. Nan take ta ɗauki hotunan kalar kujerun ta tura mata, ta tura mata kuɗi dubu ashirin. Itama nan Jamilar bata ɓata cikakkun awa uku ba sai gata niƙi-niƙi da labulai. Kuma babu ƙarya sunyi kyau, sunyi kalar kujerunta. Sai dai a yamutse suke sosai. Dubu biyu ta ba Jamilar da take kamar mayya gurin son kuɗi jikinta na rawa ta koma gida ta goge labulayen tas ta sake kawo mata. Kafin ta bar gidan sai da ta taimaka suka maƙala labulayen. Sai ga guri ya sake fitowa gwanin ban kyau, ɗakin Amarya ya fito shar! Saboda tsananin Murna ita kaɗai sai wani hura hanci take yi tana jin kanta a sama. Duk da ɗakin Fareeda ya fi nata kyau amma itama baza a raina mata ba. "Hmmm! Wai dan ma babu kafet, dining table, da kayan kallo kenan. Ai wallahi da ɗakina sai ya yaga ma nata a kyau! Amma babu damuwa kan tafe kan isa dai." Ta faɗa a fili tana sake hango yadda tsarin falon Fareeda yake a idanuwanta. Sai kuma taja tsaki, lokaci ɗaya ƙunci ya mamaye farin cikin da take yi tunano har yanzu fa Fareeda ta kere mata. ***** "Amma dai kin tabbatar yanzu bakya jin ciwon komai?" Ya tambayeta cikin kulawa a hanyarsu ta komawa gida. Hannunsa ɗaya na kan sikiyari yana tuƙi, ɗayan hannun kuma na riƙe da nata yana ɗan murzawa a hankali. Kafin ta amsa sai da tayi murmushi, zuciyarta cike da jin daɗin wani kulawa ta musamman da ya ƙara ninka ma wanda yake mata a baya da jin zancen tana da juna biyu. "Alhamdulillah! Ba na jin ciwon komai Habeebee. Na ji sauƙi sosai." "Madallah! Haka nake son ji. Bari mu biya in muku takeaway, yadda baki da lafiyar nan bai kamata da mun je gida ki shiga kicin ba..." "A'a! Don Allah ka barshi. Akwai ragowar abincin jiya babu abinda yayi. Kuma na ga ka aje nama a firij sai in haɗa in ɗunɗuma, zai ishe mu a wadace. Amarya ce dai ina roƙon alfarma ka ce mata tayi girkinta na dare, gobe da rana idan na dafa sabo sai in bata." "Ba damuwa, Allah ya ƙara miki lafiya." "Ameen" Su Sayyid suka haɗa baki gurin amsa addu'ar! A tare iyayen suka saki murmushi. Suna isa gida bayan ya taimaka mata zuwa ɓangarenta kai tsaye ya fice zuwa gurin Fatima. Ko da ya shiga falon ko kusa hankalinshi bai kai kan gagarumin canjin da aka samu a kayan ɗakin ba. "Kin ji mu shiru ko? Jikin nata ne sai a hankali..." "Allah sarki! Sannunku da dawowa." Ta faɗa da wani irin yanayi da ƙarara yake nuna mishi rashin damuwarta kan ciwon Fareeda. Sai yayi turus a tsaye ya dafa hannun kujera yana kallonta, ta ci kwalliya sosai cikin wata doguwar riga ƴar kanti. "Muje ki duba jikinta ko...?" "Kwance take ranga-ranga ne? Ina kallonku ta window fa da ƙafafunta ta shige ɓangarenta. Tunda jikin ba tsanani yayi ba ko zuwa sati mai zuwa ne idan bata warke ba sai in leƙa ta." Saboda tsananin takaici da baƙin ciki, tsawon minti biyu yana kallon ƙasa. Ya ma kasa kallonta, ya kasa buɗe baki yayi magana. Idan ya buɗe baki a yadda yake jin zuciyarsa lallai zai iya ɗuɗɗura mata ashar. Sai kawai ya kaɗa kai ya juya zai fice daga cikin ɗakin. "Haskenah, baka ga na yi canjin kayan ɗaki bane?" Ta faɗa ganin yana gaf da ficewa ba tare da ya yaba ƙoƙarin da tayi gurin kashe maƙudan kuɗaɗe a gyaran ɗakin ba. A ɗaiɗaice ya kalleta yana taɓe baki, ta wani tsuke cikin kayan da ya ƙara bayyana ramarta a fili tunda babu ciko. Ya kalli falon nata a wulaƙance, ya sake taɓe baki don ya cusa mata haushi "Ummm na gani. Ba laifi. Duk da haka dai da kaɗan kwaɗo ya ɗara gaya. Ni dai har yanzu ko kusa banga royal chairs da gadajen da aka yi ƙaryar za'a cika min ɗakuna da su ba." Ya fice yana jin sauƙi-sauƙin takaicin maganar da ta yaɓa masa kan ciwon Fareeda. Ko babu komai dai ya ɗan rama. ***** A wannan dare, haka dai aka sake maimaita abin yau da safe. Sai bayan gama zafafan wasanni a tsakaninsu da ya yi yunƙurin shiga gonarsa sai ta kwanta likif, izuwa yanzu lamarin ya daina ba shi mamaki. Sai dai tsoro. Ita kuwa Fareeda kawar da damuwar komai tayi tasha barcinta hankali kwance. Shi kuwa yana rungume da ita a ƙirjinsa yana karanta wasiƙar jaki. *_Ƴar'uwa me kike jira? Na ce kin siya kuwa? Jibi ne fa idan Allah ya kaimu ranar Alhamis Promon maganin infection na Zee Maman Mujaheed zai zo ƙarshe. Idan baki mallaki naki ba ina tabbatar miki kiyi gaugawar taɓo ta ta whatsapp kiyi odar naki. Maganin zai kawar miki da duk wata damuwa ne ya ƙara armashin harka tsakaninki da Maigida ran gida. Zai kankaro miki mutunci da daraja fiye da yadda kike tsammani😍😍😍😘👇🏽_* Promo! Promo!! Promo!!! A baya tana sayar da maganin 4k ne. A yanzu ta sauƙaƙa shi zuwa 2k. Za ta rufe wannan garaɓasar ne a cikin sati ɗaya kacal! Ƴar'uwa me kike jira? Maganin nata ya samu shaidar aiki ingantacce kuma da gaugawa ake ganin biyan buƙata in sha Allah. Idan kina fama da ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin ina mai baki shawara kiyi gaugawar siyan maganin Zee Maman Mujaheed👇🏽 Ciwon gabobi, ciwon mara, fitar farin ruwa, kaikayi gaba, rashin Sha'awa, rashin kuzari gare ki ko ga namiji, rashin ni'ima, rashin haihuwa, kurajen jiki ko na gaba, jin Zafi yayin saduwa. Maganinta cikin sauƙi kuma a gaggauce yake magance duk waɗannan matsalolin. Ki tura kudin maganin ta wannan account ɗin da ke ƙasa, sai ki tura mata shaidar biya da garin da kike ta lambar wayarta👉🏽0 816 285 9027 Ga kuma acc ɗinta👇🏽 3968303018 Zainab Shu aibu Fcmb *RABON AYI* *©Fareeda Abdallah* _*22*_ *Ku zo ku sayi data a gurina sai ku cigaba da karatu💃🏽💃🏽👇🏽😘😘* _Ki tura kuɗin tsarin datar da kike so a wannan acc ɗin 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ki tuntuɓeni ta whatsapp akan 07039080978, idan ba ni a online ki kira ni ta 09077591726. In sha Allah cikin daƙiƙu ƙalilan datar da kika siya zai sauka a wayarki👌🏽_ *MTN data price👇🏽* 500 MB 👉🏽 N150 1GB 👉🏽 N280 2GB 👉🏽 N550 3GB 👉🏽 N800 4GB 👉🏽 N1100 5GB 👉🏽 N1350 6GB 👉🏽 N1600 10GB👉🏽 N2500 *AIRTEL data price👇🏽* 300MB 👉🏽 120 500MB 👉🏽 150 1GB 👉🏽 N300 2GB 👉🏽 N600 5GB 👉🏽 N1350 10GB 👉🏽 N2500 20GB 👉🏽 N5000 *GLO data price👇🏽* 1GB 👉🏽 N500 2.9GB 👉🏽 N1000 4.1GB 👉🏽 N1500 5.8GB 👉🏽 N1950 *9MOBILE data price👇🏽* 500MB 👉🏽 N500 1.5GB 👉🏽 N1000 2GB 👉🏽 N1250 3GB 👉🏽 N1600 4.5GB 👉🏽 N2000 *_Na mu ba irin na su bane shi yasa farashin daban yake da nasu😉😉_* Washe gari Fareeda ta tashi lafiya ƙalau, babu wani ciwo ko ƙanƙani da take ji a jikinta. Amma saboda ɗoki da zakwaɗin cikin jikinta da Mukhtar yake yi haka ya dinga tarairayarta, duk inda ta saka ƙafa yana biye da ita. Duk aikin da ta kamo haka yake saka hannu ya tayata suyi su gama. Ba yadda baiyi da ita ba kan ta zauna ta huta ta ce a'a! Ita baza ta iya kwanciya ba tare da ta gyara ɗakunanta ba. Ya ce ta barshi yayi aikin, nan ma ta ce a'a! Baza ta iya zama tana kallonshi shi kaɗai yana aiki ba. Wannan shi ne dalilin da yasa ya saka sauƙaƙan kaya marasa nauyi ya dinga taimaka mata. A yinin wannan rana, sun sabunta soyayyarsu fiye da yadda ake zato. Minti ɗaya biyu zai kalleta da faffaɗan murmushi a fuskarsa ya ce "Ina son ki Fareeda." Idan ya faɗi haka wani irin girma kanta yake yi kamar zai fi ƙarfin gangar jikinta, zuciyarta ta cika ta tumbata da matsanancin farin ciki, har takan manta yanzu ba ita kaɗai ce da shi ba. A yangace cike da ƙasaita take mayar mishi da martanin murmushinsa. "Nima ina son ka Uban ƴaƴana." "Allah ya barmu tare" "Ameen thumma Ameen" Suke haɗa baki su biyun gurin amsa kyakkyawar addu'ar da yayi musu. Sai su ƙara musayar murmushi sannan su cigaba da aikin da yake gabansu. Irin kalaman soyayyar da ya dinga faɗa mata a wannan rana, kamar lokacin da ta samu cikin farko ne, tana Amarya. Suna bala'in mararin juna tun gishiri bai fara sauka daga kan kaza ba. Da an ɗauki ƴan mintuna zai riƙo ta zuwa jikinsa, cikin salon soyayya yake shafa lafaffen cikinta da in banda likita ya tabbatar tana da ciki babu wanda zai ce akwai ajiyar ɗa a ciki saboda shafewarsa. "Baki gaji ba Matata? Ba na so ku wahala ke da Babys ɗina..." Ta zazzaro idanu a tsorace ta ce "Babys ɗin har guda nawa Habeebee?" "Uku mana! Wancan karon kin bani biyu rayayyu kuma lafiyayyu yanzu ba sai ki bani uku ba?" Ya raɗa mata a kunne, har lokacin yana shafa cikinta. "Ban yarda ba, ni dai gaskiya ban yarda ba Habeebee. Haihuwa wahala, ko ɗaya Allah ya bani Allah ya saka mishi ko mata albarka." Kukan shagwaɓa ta sakar mishi bayan gama maganar tana bubbuga ƙafafunta a ƙasa. Ƙara riƙeta yayi sosai a jikinsa yana dariya yayi sama da hannayensa yana lalubeta kamar yana mata cakulkuli. Daƙyar ta iya ƙwace jikinta ta matsa gefe itama tana dariya. Ko da ta gama abinci ta zuba na Fatima wadatacce a kula shi da kansa ya ɗauka ya miƙa mata. Ya tarar da ita bakinnan a gaba don har lokacin bata manta maganar da ya yaɓa mata jiya ba. Kuma da safe ko sararin leƙawa ya duba yadda ta tashi baiyi ba, ta leƙa ta window fiye da sau talatin da tunanin ko ya fita ne sai taga motarsa na ajiye a tsakar gida. Saboda wannan baƙin cikin da ƙyar ta iya buɗe baki ta gaishe shi. Ya amsa hankalinshi kwance ba tare da ya bi ta kan ɗaure fuskar da take yi ba. Ya kai mazaunai zai zauna kenan kan ɗaya daga cikin kujerunta ta kalle shi da salon saƙa magana ta ce "Ai na zaci ba ka lafiya ne. Tun safe nayi ta zuba idon ka shigo mu gaisa baka shigo ba, har na fara tunanin ko idan ba ranar girkin mace bane baza ka dinga leƙawa da safe kaga lafiyarta ba" Zaman da yayi niyyar yi ne ya fasa, ya tsaya a tsaye. "Amma dai kin san Fareeda ba ta da lafiya?" Yayi mata tambayar idanunshi na cikin nata. "Haka ka ce min dai." Ta amsa bayan ta kawar da idanunta daga gare shi. Da mamaki sosai a fuskarsa ya ce "Haka na ce miki? Ƙarya nayi kenan?" Shiru tayi bata amsa ba, sai ƙara tamke fuska da tayi tana hararar inda take kallo. Shirunta shi ya fara fusata shi, da ɓacin rai ya kira sunanta. "Fatima?" "Na'am" Ta amsa a ɗaiɗaice bayan ta taɓe baki. "Wai me kike nema da ni ne tun jiya a gidannan?" Yayi mata tambayar cikin tsawa-tsawa. Runtse idanu tayi tana ƙoƙarin danne ɓacin ranta. Ta buɗe idanun bayan ta kalato hawaye ƙarfi da yaji ta kalle shi a raunane, da rawar murya ta ce "Kayi haƙuri Haskenah! Allah ya huci zuciyarka. Ni ba nufi na in ɓata maka rai ba." Kaɗa kai kawai yayi ya fice daga ɗakin, zuciyarsa cike da baƙin ciki. Ƙoƙarin watsar da tunanin komai yayi gaf da zai shiga ɓangaren Fareeda don kar ta karanci damuwa a fuskarsa itama ta shiga damuwa. Cikin walwala da farin ciki suka ci abinci su da ƴaƴansu. Kamar a film, haka sukai ta ba juna da salon ƙauna har suka ƙoshi. Shi da yaran suka tattara farantan abincin zuwa kicin ita kuma tana zaune kan kujera a falo tana hutawa. Ko da Magrib tayi sun rabu ne cikin farin ciki. Ita da yaran sai bye bye suke mishi kamar wanda zaiyi tafiya. Duk da bata furta ba, yana hango kewa mai girma a cikin idanunta. Har ya fita sai ya dawo, kai tsaye inda take ya ƙarasa yaɗan riƙo ta kaɗan saboda idanun yaran ya ce. "Ko in zauna sai zuwa anjima? sai in bata uzurin baki da lafiya..." Da sauri ta katse shi da cewar "A'a! Haba dai! Abinda bazan so ayi min ba bazan taɓa ba da damar ayi ma wata ba. Je ka Habeebee, Allah ya bamu alkhairi. Bayan ma kamar anjima ne kwanaki biyun za suzo su wuce..." "Ai zan ma dinga shigowa duba lafiyarki da ta yara." "To babu damuwa! Sai da safe." Ta sakar mishi murmushi ta riƙe hannunshi cikin nata ta raka shi har ƙofar falon. Fuskarta ya riƙe cikin hannayensa ya sumbace a laɓɓa. Ya shafo cikinta, ya tsugunar da fuskarsa saitin cikin ya sumbaceta, ya riƙo hannunta na dama ya sumbaceta. Ya sake mata sallama ya nufi ɓangaren Fatima zuciyarsa tumbatse da kewar Fareeda da komai nata. A kasalance yake yafiya, yana yi yana tsayawa sai ya waiga ya kalli Fareeda da har lokacin take tsaye tana kallonsa, fuskarta da murmushi, hannunta ɗaya a sama alamar bye. Duk wannan abu da yake faruwa kan idanun Fatima da tun da ya rage sha biyar a kira Magrib take ta safa da marwa tsakanin window da tsakar falon. Ta sha kwalliya sosai kamar wacce take shirin zuwa dinner. Leƙe take yi taga ta ina Mukhtar ɗin zai fito, kuma da wani yanayi zai fito, farin ciki ko akasin haka? Idan ta gaji da tsayuwa a window sai taja dogon tsaki, ta sake kallon agogo zuciyarta cike da matsanancin baƙin ciki da ɓacin rai. A fili take surutan cewa "Tun yanzu shegiyar nan za ta fara gwada min bariki ta hanyar mini ƙwangen lokacin barin miji ya dawo gurina? Wallahi sai na ci ubanta, zan nuna mata bata isa ba. Wato za ta nuna min ta fi ni sanin daɗin miji ko? Ni rannan ai ba haka na mata ba, tun la'asar ma da ya bar nan bai dawo ba sai da daddare da ya kawo min wata wulaƙantacciyar kaza." Tayi ƙwafa mai ƙarfi, ta cije gefen laɓɓa tana girgiza kai. "Daga ke har Mukhtar ɗin zan nuna muku ku ƙananun ƙwari ne. Na fi ku sanin duniya da ajujuwan cikinta na kissa da makirci" A haukace ta shige uwarɗakinta ta ƙara janyo jarkar da aka cika mata shi taf da tsumin ƴar gata, ta ɗaɗɗaka sosai kafin ta mayar da jarkar inda ta ɗauko. Kicin ta wuce ta ɗauko kofi da madara ta sake dama kalolin magungunan mata masu yawa ta shanye. Gyatsa mai ƙarfi ta saki saboda yadda cikinta ya cika sosai da magungunan da tun ukun rana take sha. Ta sha alwashin yau sai ta saka Mukhtar ihu a kan gado, sai ga shi yana neman ɓata mata lissafin da ta yini tana yi a ƙwaƙwalwarta. Ko da ta koma falon a wannan karon ba a window ta tsaya ba, ƙofar falon ta buɗe tana leƙen ɓangaren Fareeda kwatsam sai taga fitowarsu, kamar wacce aka dasa tana tsaye ta kasa motsawa daga gurin har Mukhtar ya gama sumbace sumbacensa ya kamo hanyar ɓangarenta. "Auchhhhh" Ta faɗa tana dafe goshinta bayan ya turo ƙofar ba tare da sanin tana tsaye a gurin ba ya buga mata a goshi. "Subhanallahi, na buge ki ko? Me kike yi a bakin ƙofa?" Ya tambayeta cikin kulawa bayan ya janyo ta jikinsa yana mulmula mata goshin. "Na zo rufe ƙofar ne." Ta amsa daƙyar cikin jin zafi, sosai ta bugu a goshin, hankalinta yayi nisa sosai har bata san ya iso bakin ƙofar ba da tuni ta kauce. "Yi haƙuri. Sannu! Hankalina yayi gaba ban lura da ke a gurin ba." Sosai ya mulmula mata goshin yana jera mata sannu kafin ya sake ta ya shige banɗaki don ɗauro alwalar sallar magrib. Ita kuma kicin ta shige ta fara fito mishi da kayan abinci tana jerawa a tsakar ɗakin. Har yayi mata sallama zai fita masallaci ta nuna mishi kular da Fareeda ta zuba mata abincin rana ta ce "Ga abincin ƴan can ɓangaren fa. Ko za ka miƙa musu kafin ka wuce?" "Ok!" Ya amsa a taƙaice. Har ya ɗauka zai fita jin kular babu nauyi sosai sai ya buɗe. Ƙanƙance idanu yayi yana kallonta bayan ya ga abincin can ƙasa, shinkafa ce da miya tayi, kuma miyar ƴar ɗugul akan shinkafar "Miye haka Fatima? Wannan abincin ai ko su Sayyid bazai ƙosar ba balle ace har da mamansu. Kuma saboda Allah sai ki zuba musu miyar akan shinkafa? Idan ba yanzu za su ci ba fa?" Narai narai tayi da fuskarta cikin sallamawa ta ce "Ayya Haskenah, don Allah kayi haƙuri. Na san Fareeda bata cika cin abinci da yawa ba shi yasa ban cika musu ba, kuma daman ƴar kaɗan na dafa saboda kar inyi ɓarna. Amma zan kiyaye gaba in sha Allahu. Kayi haƙuri." Bai ce komai ba. Inda ta jera nasu abincin ya nufa ya, ko da ya buɗe babbar kular sai yaga ta shaƙe musu taf da farar shinkafa. Ta miyar ma ta zuba a wadace ga mai nan nasha-nasha a sama. Ajiye wanda ta zuba ma Fareeda yayi ya ɗauki wanda ta zuba musu ya nufi ƙofa zai fita da su. "Zan kai musu wannan. Ke sai ki ci wancan, ko ban samu ba babu damuwa sai in sha tea." Ya fice da kulolin a hannunsa, ya barta daskare akan kujera baki buɗe. Ranta a ɓace, zuciyarta a ƙuntace. Tsabar baƙin ciki da takaici bata san sa'adda ta lailayo wani ƙatoton ashariya

Chapter 16 of 26