Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels *RABON AYI* *©️FAREEDA ABDALLAH* *_BABI NA ƊAYA_* "Wayyiiiihuhuhuuuuu... jama'a ku saurara, kowacce ƴar abu kaza-kazan uba ta tsaya cak a inda take! an sace jakar uwar amarya cike taf da maƙudan kuɗaɗe..." Ta jiyo wata murya mai tsananin taratsi da hargagi daga can cikin ɗakin uwar bikin tana faɗin haka, a daidai lokacin da ta ɗaga cinyar kaza ta nufi bakinta da nufin yi mata wani yaga na wulaƙanci, irinna an daɗe ba'a gamu ba. Ƙirjinta ne ya yanke ya faɗi rugugum! ta ɗaga idanu a tsorace ta kalli Fatima, akayi arashi suka haɗa idanu. Amma ita saɓanin Fareeda da ta ƙame da cinyar kaza a hannu baki buɗe, ita tauna take yi, hankalinta kwance kamar tsumma a randa, ga faskeken rabin ƙirjin kaza nan a hannunta ta kusa cinyewa. Muƙut ta haɗiyi wani kakkauran miyau da ta ji yana barazanar yaga mata maƙogwaro, ɗauke kai tayi daga kan Fatima ta waiga gefe kusa da ita, sai taga jakarta tana ajiye inda ta barta. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, jikinta a sanyaye kamar wacce aka naɗawa na jaki ta aje naman hannunta cikin soyayyiyar shinkafar da aka shaƙo mata cikin faranti. Lumshe idanu tayi, ta girgiza kai, ta fara maganar zuci. 'Yau babu sa'a, daga zama da niyyar ɓarje gumi sai ace anyi sata? Sawuna a likkafa gara in tattara tsumman rayuwata in san inda dare yayi min, tun kafin wata tsautsayin ta rutsa da ni in shiga uku.' Hannu tasa ta ɗauki jakarta ta maƙala a kafaɗa, ta kalli Fatima da maɗaukakin mamaki a fuskarta, ganin har lokacin cin naman take yi a nutse, bisa ga dukkan alamu hankalinta a kwance yake, har wani ƙara balance tayi a cikin kujera don taji daɗin loda abinci, kamar bata ji satar da aka ce anyi daga can cikin ɗaki ba. Wani kakkausan kallo ta watsa mata, ta yunƙura za ta miƙe tsaye daga zaunen da take sai ta ji caraf Fatima ta dafe hannunta. "Ferry?" Ta kira sunanta da mamaki a muryarta. "Ina za ki? baki ci komai ba fa, ko naman ma baki ci ba, kuma kin san dai bamu daɗe da zuwa ba, ko Jiddah bamu gani munyi mata Allah ya sanya alkhairi ba balle har mu fara tunanin tafiya a daidai lokacin da ake tsaka da shagali." Ta ƙarasa maganar da murya ƙasa-ƙasa yadda babu mai jin abinda ta ce, in dai ba a kusa da mu sosai ake ba. Kafin ta ce uffan wata kakkauran mata mai ƙiba ta fito daga cikin ɗakin uwar amarya gudu-gudu sauri-sauri, ta nufi babban ƙofar falon da ake shiga da fita ta rufe, ta ƙara da murza key ta datse ƙofar ɓam. Ta zare makullin, ba tare da kunyar kowa ba ta janyo wawakeken wuyan rigarta yayi ƙasa-ƙasa har ana hangen tudun ƙirjinta ta jefa ɗan makullin a cikin rigar mama. Ta juyo tana kallon cincirindon matan da suke zaune rukuni-rukuni a makeken falon, fuskarta ɗauke da wani mummunan murmushin da ya fi kama da na rainin wayau, sai wani irin numfarfashi take saukewa kamar wacce tayi tseren gudu. Ta fara magana da garjejen muryarta mai kama da na magidanci. "Sas-sannunku fa, kuyi haƙuri don Allah, kar ku tashi hankulanku!! Abu ne kamar wasa ƙaramar magana tana neman zama babba! Kun dai ji anyi shelar sata ko? To wallahi ta tabbata! da gaske anyi satar, Kamar ɓatan dabo Ƙasa ko sama mun nemi jakar Hajiya Mariya yanzunnan akan gado mun rasa, abu kamar layar zana ƙad-da-bus jaka ta ɓace ɓat! Ba zarginku muke ba fa, Don Allah ku kwantar da hankalinku kamar tsumma a randa. Yanayi ne na rayuwar duniyar da ta canza, kun san mutane ba gaskiya... inji bahaushe yakan faɗi kai dai ga mutum, sanin zuciyarsa sai Allah..." "Aunty Kubura menene haka? me nake gani haka? me nake ji haka? ya kike ta wani lallaminsu kina basu hakuri? Sata ne dai an riga anyi kuma na tabbata kwarankwatsa dubu a cikinsu ne akwai ɓarauniyar nan. Duk inda jakar nan take na tabbata bata bar cikin falon nan ba, don ƙasa da minti bakwai da suka gabata jakar tana kan gado a ajiye. Don haka wallahi tallahi yau in za a kwana a yini sai sun fito da jakar nan sannan ko wacce za ta fita daga nan! Caje ne daga sama har ƙasa sai munyi in ta kama daga nan har caji ofis sai mun je!" Idanu warwaje Fareeda take kallon wata figaggiyar matashiyar mata da ta fito daga cikin ɗaki tana faɗin haka cikin fushi da masifa, bakinta har yana kumfa da tartsatsin miyau saboda bala'i. A tsorace ta sake mayar da idanu kan Fatima da har lokacin hannunta ke damƙe da na ta, da rawar murya mai cike da tsoro tayi ƙasa ƙasa da murya ta raɗa mata "Fatee na shiga uku na lalace! Wallahi Mukhtar bai barni ba na fito gidan bikinnan, yau idan suka riƙe mu anan ina zan saka kaina?...!" Kafin Fatima ta ce wani abu ɗaya daga cikin hamshaƙan matan da suke zaune a can wani ɓangare na falon ta miƙe tsaye a fusace ta kalli tsigaggiyar nan ta fara maida mata martanin maganganunta cikin fushi "Wai wane irin zancen banza kuke yi haka? ku kalle mu dakyau ku gani, kusan duk cikar mu babu wata wulaƙantacciya mai wulaƙantaccen sutura balle har ku maƙala mana satar ƴan kuɗin da kila ma ba wasu masu yawa bane." _A ɗarare Fareeda ta kalli kayan jikinta, inda Allah ya taimaketa zaninta na ƙasan akwati ne a jikinta, Chiganvy Gold, atamfar da daƙyar da jiɓin goshi ta mallaketa, tsabar ta so siyanta bazata iya ƙayyade kwanaki nawa tayi tana ƙwangen kuɗin cefane da na karyawa kafin ta tara kuɗin siyanta ba. Naira dubu goma sha uku cif haka ta caskewa Hajiyar Barrister kafin ta samu nasarar mallakar atamfar, ta ƙara tara asusun dubu huɗu cif ta ba Yayanta Musty don yayi mata ɗinkin kece raini na fita ko wane irin muhimmin taro._ Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke, ta mayar da hankali kan matar nan inda ta ji ta ci gaba da cewa "Mun ci, mun sha, mun rufa mun tada kai balle har ayi tunanin za mu gani mu ɗauka. To Satar me za ayi? ina ƙudan yake balle romonsa? in dai da gaske ne ma anyi satar to kuwa na tabbata ko rantsuwa nayi babu kaffara ƴar iskar ɓarauniyar baza ta wuce a cikin ku ƴan'uwanta na jiki-jiki da kuka maƙale kuna zaune a cikin uwarɗakinta ba..." Maganar da tayi sai ya zama kamar mabuɗin bakin ko wace mace da take zaune a falon, nan take aka fara cece-kuce da ƙananan maganganu, aka fara zage-zage da wannan figaggiyar matar, kamar za aba hammata iska. Tana masifa ana maida mata martani, ko wacce mace na ƙoƙarin kore gaskiyar zancen anyi satar balle har a maƙalawa ɗaya daga cikinmu mazauna falon. Fatee ta gallah ma Fareeda harara, ta fusge hannunta da ta riƙe, cikin fushi da ƙarfin hali ta fara magana da faɗa-faɗa. "Ke dallah banza ki nutsu ki kwantar da hankalinki, to miye don ba'a barki ba kika fito? kanki farau satar fita? da wannan mutsu-mutsu da zare-zaren idon da kike yi ai sai ki zama abar zargi a cikin mat..." Wani mahaukacin ƙaƙƙarfar ihu mai cike da amo da amsa kuwwa da aka ƙwallah daga cikin ɗakin uwar bikin yasa kusan duk mazauna falon suka miƙe tsaye a tsorace, tsit kake ji ! duk hayaniyar mata ya tsaya cak kamar ɗaukewar ruwan sama. Hankalinsu bai ƙara mugun tashi da ɗugunzuma ba sai da wannan ƙatuwar da aka kira da Aunty Kubura ta fara jero sallallami tana tafa hannaye, fuskarta bayyane da matsanancin tashin hankali, da saurin murya mai ɗauke da damuwa ta ci gaba da magana "Shi ke nan! Ta faru ta ƙare anyiwa mai dami ɗaya sata. Abinda muke ta gudu da alamun shi ne ya faru. Mugayen aljanun da suka yi dafifi a jikin Aunty Adama ƙanwar Hajiya Mariya sun tashi. Wallahi duk wacce tasan ta ɗauki jakar nan ina bata shawara ta fito salin-alin sawunta a likkafa tun kafin a fito da ita a tozarce a wulaƙance. Don wallahi aljanunta ƴan fallasa ne, kuma duka suke yi, idan suka zuciya babu ruwansu da mai gaskiya da mare gaskiya, kan mai uwa da wabi suke yi da wacce ta ji da wacce bata gani ba su naɗi fata" Kayan cikin Fareeda ne suka tattaru suka cure guri ɗaya, lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa kamar ana kaɗa mata ganga, hanjin cikinta sai mazari suke yi kamar ana tsakiyar hunturu. A ƙanƙanin lokaci idanunta suka cicciko da hawaye, bayan wasu daƙiƙu sai ga hawayen sun zubo shar... Ta kalli Fatima ita ma ta kalle ta, a wannan gaɓar ƙuru-ƙuru ta hangi matsanancin tausayinta a idanun Fatiɓa, domin ta san Mugun tsoron aljanu ne da Fareeda. Ta tsani aljanu, ta tsani tashin aljanu a gabanta, tun tana ƴar ƙanƙanuwar yarinya duk idan taji labarin wata wacce ta sani tana da aljanu ta rabu da mace kenan haihata-haihata. Ko a cikin dangi ne takan guje ta faufau balle kuma a cikin ƙawaye ko kuma ƴan ajinsu, a islamiyarsu ta canza aji fiye da sau goma saboda tsoron tashin aljanu. Kafin wata a cikinsu tayi wani yunƙuri don motsawa ko cewa wani abu sai suka fara jin buge-buge daga cikin ɗakin kamar ana watsi da kayayyaki, ko kuma ana mugun dambatuwa. Can kuma sai suka ji an sake yanka ƙaƙƙarfar ihu a karo na biyu, aka buɗe ƙofar ɗakin buf sai ga wata gajeriyar mace mai kama da wada wacce da alama ita ce Aunty Adaman ta fito falon a guje daga cikin ɗakin. Daga ita sai shimi a jikinta, ƴan uwanta har da uwar bikin suna biye da ita da gudu suna yunƙurin riƙeta, fuskokinsu cike da maɗaukakin damuwa suna cewa "A tara jama'a... ku tare mana ita. Taimako jama'a ku riƙeta kar ta futa waje, yunƙurin guduwa da ita suke yi ako wane lokaci." Abin mamaki da tsoro Aunty Adama tana zuwa kusa da ƙafafun Fareeda ta zube ƙasa yaraf kamar an taɗiyeta, takai wa ƙafafunta wani mugun damƙa da wawaso da yasa tayi taga-taga kamar za ta faɗi amma ta tsaya daƙyar bayan ta damƙi ƙugun Fatima da take kusa da ita, Aunty Adama kuwa ta riƙe ƙafafunta tamau. Tsananin tsoro da firgici yasa Fareeda ƙamewa a tsaye tana jan numfashi daƙyar, kamar wata mutum-mutumi, ta kasa ƙwaƙƙwaran motsawa ta kasa numfashi mai ƙarfi, gani take da tayi wani ƙwaƙƙwaran yunƙuri za'a zare mata rai. Sama-sama take jiyo ringing ɗin waya a cikin jakarta da ke kafaɗa tana rera waƙar "Fareeda gimbiya... fareedah kin zama sarauniyar mata..." Waƙar da idan ta ji ta tabbatar mijinta Mukhtar ne yake kira... 'Na shiga uku!!!' Ta faɗi hakan a zuciyarta, wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata kamar an buɗe famfo. A Fusge kamar daga can nesa taji muryar wata mata tana cewa "Baiwar Allah ki nutsu, ki kwantar da hankalinki. Da alama aljanunta suna son ki ne..." Ƙaƙƙarfar kukan da Fareeda ta buɗe baki ta fashe da shi yasa mai maganar ta kasa aje numfashin maganarta daidai. 'So dai? aljanun ne suke so na? A duniya in rasa suwa za su so ni sai aljanu? ni kam yau wace irin mummunan baƙar rana ce a gare ni?' _'Fareeda kar ki tafi gidan bikinnan, in dai ni mijinki ne kuma na isa da ke ban baki izinin ki tafi gidan bikinnan b..._' _'Haba Baby haba haba don Allah? me yasa kake irin haka ne wai? Jiddah ce fa za tayi aure ba wata ƙawata can nesa ba. Fisabilillahi duk yadda muke da Jiddah ace bikinta ya zo bazan samu halarta ba? haba! ai duniya ma sai ta zage ni, ka tuna yadda tayi uwa tayi makarɓiya a bikinmu..._ _Ni na sata dole tayi? na dai faɗa miki kar ki fita ko ina, gobe zan dawo. Idan kuwa kika fita wallahi tallahi duk abinda nayi miki ke kika jawo wa kanki. Domin a wannan karon zan ɗauki mummunan mataki a kanki. Ƙit ya katse wayar ba tare da ya sake sauraren abinda zan sake ce ba._ A cikin ɗan taƙaitaccen lokaci taƙaddamar da muka kwasa da mijina Mukhtar a ɗazu da safe ya faɗo min arai, da yake ni ɗin mai kunnen ƙashi ce tsautsayi da rabon ayi yasa nayi fatali da hanawarsa, kashedinsa, rantsuwarsa nayi fitowata bayan ƙawata Fatima ta shirya ta biyo min har gida da direbanta. "Baiwar Allah kiyi haƙuri, kibar kuka, yanzunnan za mu ɓamɓare hannuwanta daga jikin ƙafafunki, ki nutsu, kiyi hakuri babu abinda za tayi miki." Ɗaya daga cikin ƴan uwan Aunty Adama ta faɗa ma Fareeda haka, da sassanyar murya mai ɗauke da alamun rarrashi don kwantar mata da hankali. Sannan ta kalli matan da suke tsattsaye cirko-cirko a falon ta buɗe murya ta ce "Ina Hafizai mahaddata Alƙur'ani? ku marmatso kusa da ni kuyi aikin lada" Sai tayi zaman dirshan a gabanta tayi basmala da zazzaƙar murya ta fara rero karatu cikin suratul-baƙarah. Tsoro ne ko kuwa rashin iya karatun ne oho! a cikinsu babu wacce ta tayata karatun, sai zazzaƙar muryarta ne ya ci gaba da ratsa dodon kunnuwansu cikin wani daddaɗan sauti da iya ba ko wace kalma haƙƙinta. Bata yi mintuna bakwai cikakku tana karatun ba Fareeda ta ji hannuwan da sukayi ram da ƙafafunta sunyi sanyi laƙwas, motsawa tayi ta ji za ta iya janye ƙafafunta ai a saba'in ta matsa can gefe guda tana zazzare idanu kamar wacce tayi ƙarya a gaban sarki, sai kallon Adama take yi da wani irin kallo mai bayyana tsananin tsana da ƙyama, a zuciyarta babu abinda take ja mata sai Allah ya isa na firgici da tashin hankalin da ta ƙara jefata a ciki, a daidai wannan lokacin ta tabbata da za a auna jininta za aga yayi mugun hawa. "Alhamdulillahi! Yau an taki sa'a, sun jirge da gaugawa." Uwar bikin ta faɗi haka fuskarta na bayyana matsanancin farin ciki, wani abu a cikin kwalba mai kama da magani ta miƙawa wacce tayi karatun tana faɗin "Ungo nan Aliyah, yi sauri ki shafa mata a goshi, idan tayi barci ta tashi za ki ganta garas kamar ba ita ba." Ana gama shafa mata suka yi kama-kama suka kaita cikin ɗaki, sannan suka dawo cikin falon. Umarnin zama suka mana sannan wannan wacce tayi Ruƙya ta fara mana nasiha tana janyo ayoyi da hadithai, a ƙarshe ta dire da haɗamu da girman Allah da na ma'aiki kan duk wacce ta ɗauki jakar nan ta dawo da shi cikin mutunci da lalama ba tare da anyi tsiya-tsiya ba. Hajiya Mariya ta ƙara da cewa "Ni wallahi ba kuɗin jakar ne ma yafi damuna ba, akwai muhimman takardun His Excellency a cikin jakar! I'm sorry to say idan ba'a ga jakar nan ba gaskiya daga nan sai dai a kwashe mu zuwa station din gidan gayu..." Da rarrafe Fareeda ta ƙarasa gabanta saboda tsananin tashin hankali "Hajiya... don ya rasulillahi ki rufa min asiri... kin sanni tun ba yau ba wallahi bazan taɓa ganin abin wani in ɗauka ba. Ki min rai ki sallameni in koma gida, bikinnan ba da izinin mijina na taho ba, ga shi yayi min saƙo yana hanyar shigowa kaduna. Idan ya dawo ya tarar bani a gida na mutu kawai, na tabbata a zafin rai da rashin hakuri irinna Mukhtar igiyoyin aurena da suke hannunshi tsaf zai tsittsinka su..." "Kiyi haƙuri Fareeda, a al'amarin sata irin wannan kowa ma abin zargi ne, kinga har ƙannaina ban cire su a cikin ɓarayin ba." Tsabar tashin hankali yasa ban ankara da waya take dannawa a hannunta ba sai da naji tana cewa "Hello... Inspecter..." *_Ƴan'uwa barkanmu da Yamma. Kun tuna wannan labarin? yanzu na shirya mishi tsaf, za mu cigaba in Allah ya yarda. Ƴan kasuwa masu buƙatar a tallata musu kayan sana'arsu cikin farashi mai rahusa su tuntuɓeni ta private ta wannan lambar 07039080978._* *RABON AYI* *©️Fareeda Abdallah* _*Littafin TUBALIN TOKA ya zama complete Document. Ga duk wacce take buƙata akan N400 ta tura kuɗin ta 5407827015, Farida Abdullahi, FCMB. Sai ta tura shaidar biya ta lambata 07039080978*_ _*2*_ "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku!!!" Fareeda ta faɗi haka idanunta a warwaje, hannu bibiyu ta ɗora akai wasu sabbin hawaye suka sake ɓalle mata. Babu abinda take hangowa a idanuwanta da ji a kunnuwanta sai masifar da Mukhtar zai sauke mata, ba shi da haƙuri ko kaɗan. Balaƴaƴƴe ne na bugawa a jarida idan aka yi kuskuren shiga gonarsa, ba shi da uzuri ko misƙala zarrah. Har wani kirari yake yi wa kansa cewar "Ni fa kamar kunama nake, a taɓa ni aji ɗau." Da waɗannan tunanin da suka yiwa zuciyarta ƙawanya yasa ta fara jan wani irin numfarfashi sama-sama, kamar mai cutar athma. Hankalinta yayi gaba saboda tsananin ɗimuwa da fargaba haɗe da tashin hankali, duk hayaniya da surutan da mazauna falon suke yi sam hankalinta ba shi a kansu. Tana cikin wannan mawuyacin halin jiniyar ƴan sanda ya karaɗe unguwar, kasancewar unguwar ta masu kuɗi ce babu hayaniya sosai sai suke jin jiniyar ƴan sandan yana tashi tamkar a cikin gidan. "Alhamdulillahi, ga ƴan sanda nan sun iso." Uwar biki Hajiya Mariya ta faɗi haka da fuska kadaran kadahan, duk hasashen mutum bazai taɓa gane farin ciki take ciki ko akasinsa ba. Nan take waɗanda suke zaune suna ganin abin kamar wasa duk suka miƙe tsaye, hankula ya ƙara tashi, nan take ƙaton falon ya ruɗe da surutai haɗe da cece-kuce. Ƙarara ake jingina rashin kyautawa ga Hajiya Mariya da daga taron arziki ya koma na tsiya da rashin mutunci. Wata Aminiyar Hajiyar da ta sha kwalliya cikin wani danƙareren leshi da gwala-gwalai wuya da hannu ne ta taka ta matsa kusa da Hajiyar, ta fara magana fuskarta na bayyana matsanancin ɓacin rai. "Yanzu ke Hajiya Mariya kina ganin wannan mutunci ne? Da girmanmu da arzikinmu daga zuwa miki taron Allah ya sanya alkhairi sai ki haɗa mu da ƴansanda? wannan ai tozarci ne da wulaƙanci. Tunda haka ne ni na ɗauki lamunin kuɗin, ki ƙiyasta nawa ne a cikin jakarki in Allah ya yarda biya bazai gagar..." "Dakata Hajiya Balaraba, dakata dan Allah. Kar ki nemi ki faɗa min baƙar magana, kin sanni sarai bakina ba ya haila." Uwar biki ta katse ta tana harhaɗe girar sama da ƙasa. Ta miƙe tsaye ta riƙe ƙuƙuminta kamar wata ƙaramar yarinya, ta ƙanƙance idanunta suna kallon juna ta fara magana cikin fushi da fusata. "Tun farko na faɗa ba kuɗin cikin jakar ne damuwata ba. A can cikin jakar akwai muhimman takardun His excellency, ko yanzu da wacce ta ɗauki jakar za ta fito min da takardun na rantse da girman Allah zan iya bar mata kuɗaɗen ciki duk yawansu." Da faɗin wannan magana sai aka fara kallon kallo a tsakanin mata, ko wacce a zaƙe take ta ga ta inda takardun cikin jaka zai ɓullo, wace jajurtacciyar ɓarauniya ce za ta iya fitowa tsakiyar cincirindon matannan ta kawo takardu tunda anyi alƙawarin bar mata kuɗaɗen cikin jakar? "Ƴan'uwana mata don Allah don darajar fiyayyen halitta muji tsoron Allah, duk wacce ta san ta ɗauki jakarnan ta fito da shi. Don Allah, ta rufa mana asiri mu koma gidan mazajenmu lafiya." Malama Aliyah mai ruƙya ta faɗi maganganun fuskarta na bayyana matsanancin tashin hankali da damuwa. Bayan maganar da tayi har aka kwashi daƙiƙu sittin babu wacce ta motsa, izuwa wannan lokacin kuma ƴan sanda sun shigo cikin gidan har sun adana motocinsu, mata a cikin ƴan sandan ne suka matsa ƙofar babban falon suka fara bubbuga ƙofar da ƙarfi. "Ai shi kenan! Tunda duk haka kuke so bari in basu dama suyi aikinsu, mu tafi caji ofis ɗin kawai. Acan ko ma wacece ɓarauniyar za tayi bayani idan ta ji matsa." Tana gama faɗin haka bata saurari magiyar da aka fara yi mata ba ta nufi ƙofar fita daga cikin falon da niyyar buɗewa, a kulle ta ga ƙofar, kuma babu ɗan mabuɗi a jikin ƙofar. Ɓangaren da ƴan'uwanta suke tsaye cirko-cirko hannuwa naɗe a ƙirji alamun tashin hankali ƙarara a fuskokinsu ta kalla. Da cusasshiyar murya ta ce "Ina ɗan makullin ƙofar nan?" Cikin sanyin jiki Aunty Kubura ta zura hannunta a rigar mama ta ciro makullin ta miƙa mata. Yamutsa fuska tayi, a ƙyamace ta kalli makullin sannan ta kalli fuskar Kubura da take miƙa mata makullin. "Wani irin iskanci da ƙazanta ne za ki wani cusa min key ɗin ƙofa a rigar nono? ki tabbatar bayan kwaranyewar wannan al'amarin kin wanke min makulli tsaf sannan ki mayar min da shi jikin ƙofa." "To Hajiya, kiyi haƙuri." Ta bada haƙurin cikin ƙanƙan da kai. Ƙasa-ƙasa ta ja tsaki, ta harareta, sannan ta bata umarnin buɗe ƙofar. Tana murza makulli ta buɗe tiƙa-tiƙan ƴan sanda mata su takwas suka shigo cikin falon fuskokinsu a ɗaure, sai zare-zaren idanu suke yi kamar za su ci babu. A hannayensu riƙe da ƙananun bindigu. Cikin girmamawa suka kai gaisuwa ga Hajiya, ta amsa musu a gadarance. "Ga su nan, dambu da taliya na juya sun ƙi fito min da jakata, idan aka kwashe su zuwa caji ofis ko ma wacece ɓarauniyar za tayi bayani." Duk da a cikin matan gurin akwai masu dakakkiyar zuciya ƴan rajin rigima ubanwa ta kashe irinsu Fatima, da yawansu jikinsu yayi sanyi. Zuwa wannan lokacin ba Fareeda ba ce kaɗai mai kuka da hannayenta

Chapter 1 of 26