titi
yana kallon ta
"Shine abinda ya fara zuwa kai na..."
Ya fadi yana maida hankalin shi kan titi, wata
irin dariya Madina ta kwashe da ita
"Da gaske Hamma?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 223
Ta tambaya, kafadu yadan daga yana rausayar
mata da kai
"Kinki mun hira... Bansan me zance ba"
Yayi maganar da dukkan gaskiyar shi, hannu
takai ta gyara gilashin fuskarta tana sauke
numfashi, har lokacin da murmushi a fuskarta.
Kawai ba zatace ga asalin abinda yake damunta
ba duk satin. Ta san zazzabi, da shine zata gane,
babu inda take ji yana mata ciwo, kawai tana jin
kamar dai akwai wani abu da babu a cikin
rayuwarta a satin.
"Bajjo zaiyi aure"
Daada ta fada mata, ta zabi ta fada mata lokacin
da ta cika bakinta da ruwa tana shirin hadiye
wa, ta kuwa sarke tana tarin da ta kusan shafe
mintina biyar bai tsagaita mata ba, idanuwanta
duk sun tara hawayen wahala
"Cikin satin nan idan Allah ya bamu aron rai"
Daadar ta sake fadi, ko da taso yin wata tambaya
bata san ta inda zata fara ba, tambayoyin nata
da yawa, wata na danne wata haka suka dinga
tasowa cikin kanta. A lokaci daya kuma tana
Lubna sufyan
Hausabook.com 224
nemar ma maganar wajen zama a tare da ita
cike da son gane me hakan yake nufi da tata
rayuwar ko wata dangantaka da take tsakanin
auren na shi da ita. Shisa sai komai yayi mata
yawa, abu dayane take jin zata iya cewa, kamar
Nawfal din bai kyauta mata ba, kamar daga
bakin shi ya kamata ta fara ji. Kamar ya kamata
ace tasan maganar.
"Kunyi shakuwar da zai gaya miki zaiyi aure
ne?"
Wata murya ta tambayeta, ta so tayi gardama,
taso ta zayyano ma muryar shekarunta na
kuruciya, lokuttan da Nawfal yake daukota akan
bayan shi daga makarantar islamiyyar su zuwa
gida kamar bata da wani nauyi, lokuttan da take
jiran zuwan shi dan ta zayyana mishi duk wasu
kananun bukatunta ya kuma cire kudin shi ya
biya mata su. Sai ta tuna da shekaru biyun da
suka ja layi a tsakanin su, abubuwa da yawa
zasu iya fara a cikin awanni biyu, balle a tsallaka
awannin da suke cikin ranakun da suka shude
tare da shekara biyu.
"Ma shaa Allah. Allah ya tabbatar da alkhairi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 225
Tace maimakon furta ko da daya daga cikin
tambayoyin da take da su ne. Hidimar da ta fito
da ita ta cigaba dayi, ba dai tasan dalilin Daada
na binta da wani irin kallo mai cike da ma'anoni
ba. Ba zatace tausayawa kawai ta gani a cikin
kallon ba, kamar Daada na son sanar da ita
auren Nawfal din yana da alaka da rayuwarta
ne, ta kasa fahimtar kalaman da Daada ta zabi
tabar su cikin idanuwanta maimakon ta furta
mata su. A ranar da ta shiga dakin ta, bayan ta
zauna ta dauki agogon Nawfal kamar yanda
sabonta yake sai ta tsinci kanta da saukowa
daga kan gado tana neman waje ta jefa agogon a
ciki.
Har yau da take zaune a cikin motar Salim da
yazo daukarta zuwa restaurant din da suka
yanke hukunci zuwa yasu-yasu dan gudanar da
yar walima ta taya Nawfal din murnar auren shi
da aka daura a safiyar Asabar din ba zatace ga
dalilinta na adana agogon ba. Hannun Salim da
taji a gefen kuncinta na sata saurin janye jikinta
kamar wadda wuta ta taba, sake mika hannun
shi yayi kamar bai ga yanda ta hade da murfin
motar ba, ji yayi babu zazzabi a jikinta. Sannan
Lubna sufyan
Hausabook.com 226
ya janye hannun shi yana gyara zaman shi yana
fadin
"Shirun ki yayi mun yawa"
Numfashi ta sake saukewa a karo na biyu
"Banda labari ne fa... Yau zan missing karatu a
islamiyya, bana fashi in ba rashin lafiya ba sai
bikin Adee, zasu ga banje ba yau ma kuma ban
fada ba"
Kai ya jinjina
"Zasu dake ki ne?"
Saboda tunanin wani zai taba lafiyarta na sa
jikin shi daukar dumi da wani yanayi na bacin
rai
"A'a, ba su cika dukan fashi ba inba kana yawan
yi ba"
Duk da haka hankalin shi yaki kwanciya
"Kin tabbata?"
Yayi tambayar cikin harshen turanci
"Na tabbata"
Lubna sufyan
Hausabook.com 227
Ta bashi amsa cikin harshen itama, yana shan
wata kwana ya dan rage gudu alamar yana son
samun damar da zai tsallaka titi ne, tana kuma
iya ganin sunan restaurant din Tasty Corner. Sai
da ya tsallaka ya samu waje yayi ajiye motar
yana kashewa tukunna take kara ganin kyawun
restaurant din tun kafin ma su shiga. Da yake
banda makaranta babu inda take zuwa, sai nan
cikin unguwar su, sai kuma gidan Julde da shima
tana dadewa bataje ba, a garin Kano tsaf zaka
siyar da ita. Babu inda ta sani, yanzun ne ma da
Salim ke yawon dauko ta daga makaranta yakan
biya wani wajen yayi mata siyayya, har wani
wajen saida litattafai sukaje da bata san a ina
bane ba, amman yayi mata kyau matuka.
Da kan shi ya zagaya ya bude mata murfin motar
ta fito. Sai lokacin ya kalli kayan jikinta, jeans ne
baki, kamar yanda ta saba ta nannade shi har
kwaurinta ya dan fito, sai fararen kambas,
rigace ta sanyi mai dogon hannun da taja baya,
itama farace kamar hijabin kanta. Ta dora wata
farar hular sanyi a saman kanta. Murmushi yayi
yana tsayawa a gabanta yana kara mamakin
gajartar Madina, da kadan kanta ya wuce cikin
Lubna sufyan
Hausabook.com 228
shi, kama hular yayi yana cire ta daga kanta ya
duba kamar mai son gano wani abu a jiki.
Murmushin dai ya kasa barin fuskar shi har
lokacin, gyara hular yayi a cikin hannun shi
yana dorawa saman kanta kafin ya gyara mata
ita saman kanta, ganin yanda take kallon shi
yasa shi amfani da dan yatsa ya tura mata
gilashin da yasan gab take da dago nata hannun
ta gyara mishi zama.
"You look like a Mug"
Salim yace muryar shi dauke da wani irin yanayi
da yake jin fitowar shi daga zuciyar shi, kai
Madina take girgiza mishi tana kokarin danne
dariyar da take son yi saboda hada tsayinta da
kofi da yayi
"Ba zaka fara kirana da Mug ba Hamma"
Girar shi daya ya daga mata
"Gargadi ne?"
Kai ta girgiza da sauri tana saka shi lumshe
idanuwan shi yana bude su a kanta
"Mug it's then... Muje"
Lubna sufyan
Hausabook.com 229
Juyawa tayi kuwa, wani murmushin na kara
kwace ma Salim, da gaske tayi kama da yan
kofinan nan masu kyau da ake zuba coffee a ciki,
masu murfin da marassa murfi, amman masu
kyan cikin haka yake ganin tsayinta a gaban shi
"Mug"
Ya furta dai-dai kunnuwan shi da murmushi a
labban shi, har takai kofar wajen ta juyo tana
kallon shi da tunanin abinda ya tsayar da shi,
taku biyar yayi ya karasa inda take suna shiga
tare, can wani teburi da yake karshen wajen ya
hango su Khalid, sai kuma hannuwan Adee duka
biyun da take daga musu kamar yace bai gansu
ba. Baima san me yasa mijinta yabar ta fitowa ba
duka sati daya da aure, dariya take tana sake
daga musu hannuwa, dakuwa Salim yayi mata
daga inda yake yana kallo ta sake kwashewa da
dariya kamar wadda ya bawa kyauta.
Suna karasawa tana tashi daga wajen da take
zaune ta kama hannun Salim din da yake
kokarin kwacewa yana daure fuska
"Wallahi nayi kewar ku sosai"
Lubna sufyan
Hausabook.com 230
Ji tayi kamar tayi waya bakwai bata gansu ba
"Sakeni dalla"
Tabe baki Adee tayi, matsalar Salim ba'a mishi
gwaninta, tana zame hannuwanta daga nashi ya
daga ya dillar mata bakin da ta tabe mishi
"Dan kinyi aure zaki mun rashin kunya"
Dafe labbanta tayi babu shiri
"Ouchh... Hamma"
Kallon da yayi mata yasa ta koma ta zauna,
kujera yaja shima ya zauna yana dan kara janta
gaba, kafin ya kalli agogon hannun shi
"Minti talatin..."
Ya fadi yana kallon su, yana da hidimar da zaiyi,
ko bashi da ita baida hirar da zaiyi da su,
hayaniyar zata dame shi. Gara yaci abinci ya
barsu suyi hirar su cikin nutsuwa. Kallon juna
Khalid da Nawfal sukayi, dan sunyi gulmar shi,
babu ma wanda ya kawo zaiyi minti talatin din
duk a cikin su
Lubna sufyan
Hausabook.com 231
"Ni nace maka Hamma ba zai minti biyar a
wajen nan ba"
Cewar Khalid
"In za'a iya mishi takeaway din duk abinda yake
so a kasa da minti biyar ba zai kai ba"
Nawfal ya kara, basu taba tunanin zai zauna a
waje irin haka yaci abinci ba
"Nasan kunyi gulmata"
Ya fadi kasan makoshi yana duba menu din da
waiter din wajen ya kawo mishi bayan ya dan
daga hannu cikin alamar kira, dankali da kaza
ya zaba sai bakin lemo yana kallon Madina da
tunda ta zauna idanuwanta na kan Nawfal, bata
ganshi ba tun da akayi mata zancen bikin, bai
kwana a gidan Daada ba, sanda yazo tana
makaranta sai dai inta dawo Daada tace mata
Nawfal ya zo. Yanzun da ta ganshi kawai sai take
jin kamar abin wasanta da ta dade tare da shine
aka fisge daga hannun ta.
Kai tsaye ba zatace ranta ya baci ba, amman
kuma bata farin cikin da kwacen, wani yanayi ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 232
a tsakanin abu biyun da bata san wacce kalma
zatayi amfani da ita wajen fassara shi ba
"Madina..."
Salim ya kira a hankali yana dan daga mata
Menu din da yake hannun shi bayan ta kalle shi
"Abinda duk aka baka"
Ta ce cikin sanyin murya, su Nawfal ya kalla,
kowa ya fara jero abinda za'a kawo mishi
"Madina yaushe zaki zo gidana? Kinsan ina fushi
daman, baki je kaini ba, na kula ai"
Murmushi Madina tayi, har ranta tayi niyyar
zuwa kai Adee din tunda harda Daada, a wajen
motocin daukar amaryar taji an riko mata
hannu ana janta, kafafuwan shi ta fara kallo ta
gane waye
"Hamma..."
Ta kira, bai amsata ba ya cigaba da janta har
suka inda motar shi take ya bude murfin yana
sakin hannunta, yanayin fuskar shi yasa ta shiga
batare da tayi musu ba, ya ja motar da bai tsayar
ba sai a kofar gidan Daada, nan sukayi zaman su
Lubna sufyan
Hausabook.com 233
a ciki suna hira, ko tace tana mishi surutun da
yake amsawa dai-dai. Har fita suka kara yi ya
siyo musu tsire mai yawa da lemo.
"Zan zo, Hamma zai kawo ni. Kibari kunshin ki
ya karasa gogewa, sai ki kira Daada kinga idan
nazo sai in miki sabo"
Kai Adee ta jinjina
"Kin kusa ki wanke laifin ki"
Yar dariya tayi tana kallon Nawfal
"Hamma Ango"
Hararta yayi
"Yanzun ne zaki kula ni? Bana so"
Hannuwanta ta hade waje daya cikin ban hakuri
"Ance angwaye basa fushi fa ko Hamma Khalid?"
Dariya Khalid yayi
"Ni zan shiga fadan ku? Ku shirya ku ware ni
yanda kuka saba? Babu ruwana, sai dai babban
Yayaa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 234
Ya karasa maganar cikin sigar tsokana. Wani
kallon kashedi Salim ya watsa mishi yana saka
shi gyara murya
"Idan na taso saina mare ka"
Salim ya fadi yana sa Adee kwashewa da dariya
"Me nayi ni kuma?"
Ko da ba'a fara kawo musu abincin su ba yasan
ba amsa zai samu ba. Hira ce ta barke tsakanin
Nawfal, Khalid da Adee, Salim abincin shi yake ci
duk da maganganun su da yake ji har cikin
kwakwalwar shi, Madina ma abincin take ci tana
tsintar dankalin dai-dai. Salim na kallonta ta
gefen idanuwan shi, dan ture plate din shi yayi
yana jan nata bai damu da kallon mamakin da
take mishi ba, wuka ya dauka yana yayyanka
mata cinya guda biyu kanana yanda zata iya
dauka kafin ya tura mata plate din batare da
yace komai ba yaci gaba da cin abincin shi.
Lemon da yake gabanta ma shi ya bude yana
zuba mata a kofi ya tura mata kusa da ita. Da ya
gama cin nashi abincin ma ita yake kallo. Lokaci
zuwa lokaci takan dago su hada ido, ta saba ciye-
Lubna sufyan
Hausabook.com 235
ciye a gaban shi, tasan dai idan ta ajiye cokalin
magana zai mata tunda ba wani ci tayi ba, ita
kuma tana turawa ne badan tana gane
dandanon abincin a bakinta ba, sai da taci kusan
rabin naman da yayayyanka mata tukunna ta
ajiye cokalin a ciki tana dan ture plate din.
Ganin girar da Salim ya daga mata cike da
alamar tambaya ya sata fadin
"Na koshi Allah, tuwo Daada tayi mana"
Baice komai ba ya mike yana karasawa inda zai
biya kudin ya kuma bama Madina damar yi
musu sallama, idan yabarta zasu mayar da ita
gida ya sani, bai san ko tana so ta zauna ba, ba
tambayar ta zaiyi ba. Yanda suka zo tare haka
zasu koma tare, saboda hakan yake jinyi badon
yana da wani kwakkwaran dalili ba.
"Allah yasa alkhairi Hamma, Allah ya kawo
zuri'a dayyi ba"
Madina ta fadi tana rasa dalilin da yasa take jin
wani iri
"Zan zo anjima"
Lubna sufyan
Hausabook.com 236
Nawfal ya amsa, kai ta jinjina mishi tana
mikewa, Khalid ne ya kalle ta da fadin
"Ki bari mu tafi gabaki daya mana, ba sai mu
sauke ki ba"
Kai ta girgiza mishi
"Hamma zai ce a'a"
Dakuna mata fuska Khalid yayi
"Ka kyaleta Khalid, kiyi tafiyar ki Madina, saina
kira Daada..."
Numfashi ta dan sauke bata ma amsa ba ta juya
"Kai ina ruwan ka? Baka ga tare suka zo ba?"
Ruwa Nawfal ya kurba ya hadiye sannan yace
"Ni kadai naga Hamma ya yankawa Madina
nama?"
Dariya Khalid yayi
"Wallahi kiris in shake da taliya... Anya
Hamma?"
Kai Adee ta girgiza
Lubna sufyan
Hausabook.com 237
"Kuna da bala'in gulma yaran nan, ina ruwan
ku? Sai na fada mishi"
A tare suka kalle ta, dan kasa tayi da murya
kamar tana tsoron Salim din zaiji ta
"Amman da gaske me yake faruwa ne?"
Kallon 'maganar da nakeyi kenan ai' Khalid yayi.
Hirar suka dan karayi kafin su saki zancen suna
kama wani tunda sun san koma menene ba zai
wuce su ba, suna zaune zai zagayo kowa ma ya
gani.
*
"Yanzun wanne mai hankali ne ya dauki yarinya
yaba Bajjo?"
Saratu ta fada tana tabe baki
"Mai irin hankalin wanda ya daukeki ya bani"
Julde ya amsa ta, amsar kuma tayi mata zafi
"Ubana kenan?"
Bai ce komai ba, sakon ya isa baya bukatar jan
magana kuma
Lubna sufyan
Hausabook.com 238
"Idan wulakanci abinyi ne ka cigaba da
wulakantani Julde, Allah ya baka sa'a, hirar
arziki ma ba zan taba samu inyi da kai ba saika
gasa mun magana"
Shirun dai shi ya kara yi mata yana cigaba da
neman kayan da yake son sakewa dan ya fita
yabar mata gidan ma gabaki daya, a gajiye ya
dawo daga Abuja tunda acan ya kwana aka
daura aure da safe ya tsaya wata hidima da ta
shafi kasuwan cin shi tukunna ya juyo
"Kuma sanda na aure ka aika girmi Bajjo,
shekarar ka wajen ashirin da biyar"
Gani tayi da gaske bashi da niyyar amsata, wasu
hawaye taji masu zafi sun taru cikin
idanuwanta. Duk kawayen ta haka suke cewa
tayi sa'a, mijinta ga arziki ga kyau
"Ko yanzun mijinki yaso zai auri budurwa
wallahi da zata bi kyawun shi"
Wata kawarta ta taba fada, dan yanzun ma sun
raba jaha, daina sakar mata fuska tayi tun da
aurenta ya mutu, saboda matar ba karamar
gogaggiya bace ba. Ko da aurenta ma duk yanda
Lubna sufyan
Hausabook.com 239
kuke karka fara yaba kyawun mijinta yanzun
zata daina sauke girarta a gabanka. Wani irin
kishin shi takeyi na ban mamaki, shisa duk idan
taga zai fita haka take jin kamar baza'a waye
safiyar ranar da ita ba saboda bacin rai. Da
mutanen da suke mata kallon tana zaune a
wannan tankamemen gidan tana kuma auren
namiji kamar Bajjo sun san me take hadiya da ta
daina basu sha'awa.
Ita a bakin yaran da ta haifa da cikinta ma bata ji
zancen cewa Nawfal zaiyi aure ba. Yara kamar
ba daga jikinta suka fito ba, yanda suke nanike
ma Nawfal din yana bata takaici. Sai jiya da
Julden zai tafi Abuja yace mata
"Gobe da safe za'a daura auren Bajjo"
Tambayar duk da tayi mishi kuma bata samu
amsa ba. Haka ya tsallake ta ya wuce, son da
take mishine abinda ya sata yi mishi addu'ar
dawowa lafiya. Sai Adee ta kira, itace take fada
mata kowa zai aura da inda suka hadu. Duk da
bangare mafi rinjaye a zuciyarta na tare da
bakin cikin kalar matar da ya samu, sauran
karamin kashin yaji dadi da kuma fatan su
Lubna sufyan
Hausabook.com 240
karata can, ta rike shi karya dawo. Kar ya sake
waiwayo su, inda yake ya zauna kamar Bukari,
danma yanzun zamani ya canza ko ba'a ga
fuskar juna ba za'aji muryoyi, da tace aji shi dif,
ayi zaman makokin da babu gawa idan anyi
cigiya an gaji.
Ya zamana sunan shi ma zaiyi ma kowa nauyin
ambato kamar yanda na mahaifin shi yayi.
Wannan shine fatanta, Nawfal yayi ma rayuwar
ta da ta ahalinta nisa
Wannan karin ma kaddara ce ta riga fata
Kaddarar da take bibbiyar mutanen da ta kira
ahalin ta da Nawfal din da ta zabi ta ware a cikin
su
Bata sani ba
Bata san shi din haske bane a tare da su
Bata san shi zai zame musu katanga a lokacin da
tarihi ya maimaita kan shi ba
"Sai da safe"
Julde ya fadi yana nufar kofa, hannu tasa tana
share hawayen da ya zubo mata. Yana fita yaja
Lubna sufyan
Hausabook.com 241
mata kofar, a jagule yake jin zuciyar shi harya
fice daga gidan, inda ya tsaya ya siyi lemon zaki
yaji wani yace
"Mero!"
Sai da zuciyar shi ta nemi fitowa daga kirjin shi
saboda tsallen da yaji tayi, da sauri ya waiga
yana ganin yarinyar da bata wuce sa'ar Adeen
shi ba da take tattare kwanoninta da alama
abinci ta gama siyarwa a wajen, lumshe
idanuwan shi yayi ya bude su
"Maigida ga canjin ka"
Mai lemon ya fadi, karba Julde yayi ya karasa
motar shi ya zauna a ciki yana dora kanshi da
abin tukin, har lokacin numfashi yake fitarwa
cikin kokarin dai-dai ta bugun da zuciyar shi
"Naji maganganu kala-kala akan ka, wanda duk
yake tunanin ya isa dani yace mun kar in aure
ka... Ya zanyi da zuciyata Julde? Ya zan fito musu
da ita su fahimci hakuri da kai baya cikin zabin
da nake da shi?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 242
Kalaman Mero suka dawo mishi kamar tana
cikin motar a tare da shi, sake runtsa idanuwan
shi yayi
"Na yadda kowanne rai da nashi kaddarar, kai
ne kaddara ta Julde..."
Ya rasa yanda lokaci zai zama mai adalci kuma
marar adalci a lokaci daya, yanda yake wucewa
batare da ya jira kowa ba shine babban adalcin
shi, amman yanda idan ya wuce baya dawowa
kowa a wajen Julde hakan rashin adalci ne, ya
zaiyi da kadan daga cikin kurakuren da yake jin
zaiso ya sake samun aron lokaci dan ya sauya
zabukan da yayi? Yau bama wani waje yake son
komawa ba, rana daya ce, dakika ne kayadaddu
a cikin ranar da zai sauya amsar da ya bama
Mero, so yake ya kalleta ya fada mata ita ce
kaddarar shi bashi bane kaddararta.
"Mero tayi aure"
Labarin ya riske shi shekaru hudu bayan
rabuwar su, labarin da saida yayi yar karamar
jinya a kan shi, hangota da wani, hango rayuwar
da tayi da shi tana yinta tare da wani ba zai
daina kassara zuciyar shi ba. Shi kadai yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 243
dawainiya da ita a ran shi, ita ta shafe babin shi
daga rayuwarta harta bude wani sabon shafin
tare da wani. Bai tambayi a ina ko wa ta aura ba,
abubuwan da yake gujema cikin sanin masu
yawa ne. Da duk rana da yanda yake jin
kusancin ta a zuciyar shi yana kuma jin nisanta
da rayuwar shi
Da ya san kaddara ta adana musu shafin sake
haduwa a titi daya da ya sauya tunani
In da yasan haduwar da zasu sake yi da Mero
zata tono mishi abubuwan da za'a hada da
rayuwar shi ta baya da ta yanzun a waje daya
daya duba zabukan da yake da su
Dago kan shi yayi yana sauke wani irin
numfashi ya tayar da motar fitilar ta na haske
wajen har yana shirin kashe mishi idanuwan
daya dan jima da su a runtse, sai da yasa hannu
ya murza idanun, duk da haka ji yake hasken
kamar yayi mishi yawa
Da yasan duhun da yake bibiyar shi watakila da
ya nemi duk wani haske da zai iya kafin lokaci
ya kure mishi
Lubna sufyan
Hausabook.com 244
Kaddara
Kaddarar dai...
Ya baro tushen shi saboda ita
Tana biye da shi har wajen da yake tunanin ya
boye mata
Bai san ko ya kamata ace yana jin shi wani iri
tun safiyar ranar ba, da Julde ya kira shi yace an
daura ma baiji wani abu ba. Wasu kance sunji su
kamar suna yawo kan gajimare saboda farin
cikin an daura musu aure. Shi baiji duk wannan
ba, farin ciki, yana cikin shi tunda ya samu
goyon bayan su Julde akan auren, na rana daya
bai taba jin ba zai samu Murjanatu ba, sai dai in
rashin tabbas na rayuwa, mutuwa ta raba
tsakanin su. Shi da ita din basu fara soyayya
lokaci daya ba, daya ganta in da ance zaiji wani
abu a kanta, ko zai kirata matar shi wata rana
zaiyi mamaki.
"Ka zauna mun a waje"
Lubna sufyan
Hausabook.com 245
Shine maganar farko da tayi mishi a coffee shop
din daya shiga cikin harshen turanci , an kuma
hado mishi irin yanda yake so da kankaru a ciki.
Ya zabi teburin ne saboda yana can lungu, kuma
mai kujera biyu ne da ba lallai inka zauna kaga
wani ya zo ya zauna kusa da kai ba. Harya hango
yanda Coffee shop din zai zamana wajen zuwan
shi duk rana. Yanda take kallon shi haka shima
ya daga kai ya saka nashi idanuwan cikin nata,
da yake lokaci ne na sanyi, shigar sanyi ce a
jikinta, iya abinda yake gani na daga fuskarta ya
gane ita din me kyau ce, kyau irin wanda zaka
gani a kallo daya.
"Banga sunan kowa a wajen ba kafin in zauna"
Hannuwanta da babu safa ta murza kamar sun
daskare mata
"I'm a regular a wajen nan. Kowa zai fada maka
corner dina ce nan"
Ta karashe maganar da hausa wannan karin
dan yayi mata kama da bahaushe
"Kaga karfin hali"
Lubna sufyan
Hausabook.com 246
Ya fadi da fulatanci a muryar da yayi tunanin
dai-dai kunnen shi ta tsaya
"Ba karfin hali bane ba, gaskiya ce"
Ta amsa shi da fulatancin tana ganin mamakin
daya bayyana akan fuskar shi, dayar kujerar
taja ta zauna
"Bafullatana ce ni, tunda kaji nayi hausa bai
kamata kayi mamaki dan nayi yare na ba"
Dariya yayi, ba dan akwai abin nishadi a muryar
ta ba, sai kwarin gwiwar ta da yanda take mishi
magana kamar ta dade da sanin shi. Kamar ta
san cewa ita da shi din ranar ne labarin su ya
fara, sai da aka kawo mata abinda tayi order
harda cookies ya gani sannan ta sake ce mishi
"Murjanatu Faruk"
Kai ya jinjina mata
"Nawfal Bukar"
Ba zaice sunyi hira ba, ta dai riga shi tashi daga
wajen dan lokaci zuwa lokaci tana duba agogon
da yake wajen, yanayin ta ya nuna cikin sauri
take.
Lubna sufyan
Hausabook.com 247
"Next time ka nemi wajen ka, this is my spot"
Dariya kawai yayi, kafin ma ya amsata tabar
wajen. Ko da ya tafi ba zaice yayi tunanin ta ba,
daga ranar ma zuwa safiya ko sau daya bata
fado a ran shi ba. Watakila duk littafine da finafinai ke zuzuta wannan kalar soyayyar. Sai ace
idanuwa sun sarke cikin na juna shikenan har
soyayya ta kullu, ko an gogi juna jiki da ruhi sun
girgiza. Watakila kuma kaddara ta hada hanyar
shi da Murjanatu ne dan su kafa tarihin da zai
karyata wannan kalar soyayyar. Sunyi haduwa
wajen goma bayan nan, ta shigo Coffee house
din shi zai fita, ya shigo ita zata fita, banda
gaisuwa babu wani abu da yake hada su.
Maganar su ta fara tsayine randa ta same shi
zaune da sketch book dinshi yana nazarin wasu
zanunnuka
"Kai Artist ne?"
Ta tambaya, zai tuna ya girgiza mata kai, kamar
ba zai ce mata komai ba kafin ya amsa
"I'm a furniture designer, ko ince abinda nake
karanta kenan"
Lubna sufyan
Hausabook.com 248
Gabaki daya hirar su akan abinda yake
karantawa ne har suka rabu. Zaice ita ta fara
neman shakuwa da shi, ta fara neman alakar su
ta wuce haduwa a Coffee Shop din bayan ta
gayyace shi wani furniture showcase da za'ayi a
cewarta baban dan ajin su ne a wajen ko wani
bayani da ba zaice ya fahimta ba gabaki daya, an
gayyace ta, ita kuma ta gayyace shi. Ya amsa ta
da cewar zaije ta rubuta mishi lambar ta a
takarda tana ajiye mishi sukai sallama.
Ranar ta bude musu sabon shafi, dan duk wani
yunkuri da zaiyi sai ya gan su a tare a wani
wajen, sai yaji kamar dama can ya santa ne,
babu wata bakuntar juna a tare da su. Kamar
yanda a cikin duk wata dariya da zasuyi ya fara
jin ba ita bace ta karshe. A cikin shekara daya
sunyi wani irin sabo da kalamai zasuyi karanci
wajen fassara shi, dan a gidan su Murjanatu
babu wanda bai san shi ba, har idan an nemeta
ba'a samu ba, yana cikin jerin abokanta da
Mamanta ko babanta zasu fara kira suji ko suna
tare ko kuma ta fada mishi inda taje.
Rana daya ya tashi da safe yaji baya son hango
tana da kayadadden lokaci a rayuwar shi, baya
Lubna sufyan
Hausabook.com 249
son hango wasu ranaku a cikin rayuwar shi da
babu ita a cikin su
"Ina son kasancewa da ke, fiye da abokanta"
Ya fada mata batare da shakku ba, ta dauki
mintina biyar, har saida shirunta ya fara tsoro ta
shi kafin ta dago tana saka hannuwa ta dauke
kwallar dake cikin idanuwanta
"Na dauka ba zaka taba tambaya ta ba"
Tayi maganar muryarta na rawa
"Ka san tun yaushe nake son ka"
Kai ya girgiza mata, jin tayi shiru na sa shi fadin
"Wannan na da muhimmanci ne yanzun?"
Dariya tayi mai sauti
"Babu, kana jin yanda nake ji, shine a saman
komai"
Daga nan suka fara, bai san a inda zasu tsaya ba.
Ya dai san zai karasa sauran rayuwar shi tare da
ita yana mata godiyar yanda ta yarda da shi da
zuciyarta, da farin cikinta harda abubuwan da
tasan shi kan shi bashida tabbaci akan su.
Lubna sufyan
Hausabook.com 250
"Zan sauke ka gidan Daada ko in wuce?"
Khalid daya turo dakin ya fadi yana katse mishi
tunanin da yakeyi
"Hamma mana, ba zaka dinga kwankwasa daki
ba zaka shigo"
Dan karamin tsaki Khalid
"Har wanka na maka Bajjo"
Dafe kai Nawfal yayi yana fadin
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Kafin ya dago ya kalli Khalid din
"Zan wuce wallahi ina da abinyi..."
Mikewa Nawfal yayi
"Da zan kara watsa ruwa ne"
Ganin yanda Khalid yaja kofar ya rufe yasa shi
karasawa wajen kofar da gudu yana budewa
"Yi hakuri ka jirani in dauko jakata"
Dariya yayi ganin hararar da Khalid ya watsa
mishi. Anan cikin falon Khalid yake tsaye yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 251
jiran shi dan baiji shigowar Salim ba sai ture
shin da yayi yana furta
"Tashi dalla"
Sake matsawa Khalid din yayi, dan Salim ya
tsani ka tsaya akan hanya, ya dan fara rage
saurin hannu da ya mare shi, ko kuma sun fara
girma ne a idanuwan shi, Khalid din ba zaice
wanne bane a cikin biyun, dakin shi Salim ya
wuce yana rufo kofar, dai-dai lokacin da Nawfal
ya fito yana janyo tasu kofar dakin
"Uban
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 18