ka karo uku ka
ajiye mu zama mu hudu, zamu isheka, mun
isheka Julde, dan Allah..."
Murmushin da baka raba fuskar shi da shi yayi
mata, ko ranshi a bace yake kuwa zaiyi
murmushi
"Ajiye mata hudu ba zai hanani hangen wasu ba
Saratu, ke dinma ya na kare dake? Aure, yarana
kawai da nake kallo suke hanani dana sanin
zaman aure dake, ko dan irin wannan surutan
da kike yawan yi mun. Zan sake maimaita miki
in ba zaki iya zama dani ba furtawa kawai
zakiyi...kiyi harkarki inyi tawa, zaki iya nemar
mun shiriya idan kina da wannan lokacin, in
baki dashi kibar ni da halina..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 28
Ba dan tana da wani ilimin addini ba, sallah da
tsarki ma yanda zatayi su a tsarin addini a gidan
Radio ta koya. Anan taji kalar kuskuren da take
tafkawa a rayuwarta, amman zata iya cewa
jahilci na daya daga cikin babbar cutar da take
damun Julde. Watakila da yayi makaranta, ta
boko ko ta addini zai rage wasu abubuwan.
Yanzun ma lokaci bai kure mishi ba idan har
yayi niyya, tunda ita ma takan saurari kasakasai da ta siyo na wa'azi kala-kala kuma tana
karuwa. Shisa halayen shi suka hadu suna mata
ciwo biyu yanzun, kishin shi da kuma matsayin
abinda yakeyi ga makomar goben yaran su.
Komawa tayi ta kwanta, bata koyi kokarin share
kwallar da take zubo mata ba. Sosai kirjinta
yake zafi, musamman da zuciyarta ta shiga
hasaso mata hotunan inda Julde yake da abinda
yakeyi. Idanuwanta taji sun bushe rayau, ko
alamun bacci babu. Tana jin hawayenta tun suna
zuba har suka daina, banda ajiyar zuciya babu
abinda takeyi, ko juya kwanciya batayi ba, ta dai
ja jikinta sosai ta dunkule waje daya ko zata
samu saukin zafin da kirjinta yakeyi. Ba duba
agogo takeyi ba balle ta san ko karfe nawa,
Lubna sufyan
Hausabook.com 29
kawai dai taga daren yayi mata wani irin tsayi
ne. Kiran sallar asuba kawai take saurare taji an
turo kofar.
Tana jin kai kawon shi, tasan kayan jikin shi
yake ragewa. Bata dai motsa ba, kwan dakin
daya kunna kafin ya fita yaje ya kashe ya dawo
yana hawa gadon. Jin da tayi ya rikota yana
juyawa da ita ta fuskance shi ya sa ta fara
kiciniyar kwacewa, sai dai karfin su sam ba iri
daya bace ba, ko sirantaka irin ta yawancin
fulani Julde ba shida ita, ba zaka kira shi namiji
mai jiki ba, amman dogone na misali, ko ina a
jikin shi bai nuna rama ba.
"Kina son gwada karfi dani Saratu, in kin ganni a
irin yanayin nan ki daina mun gardama kar inji
miki ciwo wata rana"
Wasu hawayen ne masu zafi taji sun cika mata
ido, da daudar zinar daya kwaso yake neman
hada jiki da ita, ko wankan tsarki baiyi ba,
lokacin da taji yanda zata tsarkake jikinta tayi
kokarin ganin shima ya sani, kwanaki ta jera
kullum sai ta karanta mishi yanda zai tsarkake
najasar da yake yawo da ita, bai nuna mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 30
alamar ya dauka ba, amman yaji ta, kuma tana
fatan ya dauka din.
"Dan Allah ka kyaleni..."
Ta furta a raunane, ta san halin shi, abinda yayi
niyya ba zai fasa ba, kuka takeyi sosai, kukan ta
bai karu ba sai da bayan ya gama abinda yayi
niyya ya juya mata baya cikin wani irin yanayi
da ya fito da tsantsar kunar rai ya furta
"Babu kamar Mero, har yanzun banji irin Mero
ba"
Kamar ita tayi sanadi ko ta zama dalilin da ya
rasa Mero kuma ya kasa samun madadinta ba
har yanzun. Kukanta kara mishi kunar rai
yakeyi. Mata uku ita cikon ta hudu a dare daya
amman ko kusa da natsuwar da yake samu da
Mero basu kusanta ba balle su cike mishi ramin
da ta bari. Akan yaran shi yasan menene
soyayya, akan Nawfal yasan asalin kauna da
dukkan zuciyar shi. Mace, ita din a wajen shi
kamar riga ce da zai saka wadda yake so don
biyan bukatar shi ya cire ya sauya a lokacin da
yayi niyya. Me yasa Mero ta kasa barin ran shi?
Zuciyar shi babu wajen kaunar wata mace
Lubna sufyan
Hausabook.com 31
banda Daada, amman yana jin wani rami a cikin
kirjin shi inda baisan Mero ta zauna ba sai da
tabar shi.
"Baka taba sona ba Julde, da akwai soyayyata a
ranka ko yaya ne ba zaka zubar mun da mutunci
har haka ba, ba zaka mayar dani abin nunawa a
dangi ba..."
Maganar Mero ta dawo mishi tana saka shi
runtsa idanuwan shi yana hango fuskarta,
idanuwanta, jan bakin da baka raba labbanta da
shi. Ita da kanta ta fada mishi baya son ta, me
yasa zata manne mishi har haka? Mata nawa ya
sani kafin ita? Mata nawa ya sani bayan ita, me
yasa ta fita daban? Me take da shi da ya kasa
samu tare da sauran? Kullum, tun bayan ita
kullum saiya nemi gamsuwar da yake samu da
ita a tare da mata daban-daban amman ya kasa
samu. Baya bibiyar mata da yawa haka kafin
Mero, ta sake bude mishi sabon shafin da babu
kalaman da zasu iya fasaltawa.
Bai bude idanuwan shi ba har bacci ya dauke shi
cike da mafarkin Mero, ya kuma bude su da
wayewar gari cike da tunaninta. Da yake Juma'a
Lubna sufyan
Hausabook.com 32
ce shi yake kai yaran makaranta in ba wani
babban uzuri ba, a gaggauce yayi wanka ya
shirya sannan yayi sallar asubar da ba kullum
ya damu daya sameta a cikin jam'i ba. Duk tare
suka karya yana hira da yaran kamar bashi da
wata matsala in har yana ganin su a kusa da shi.
Salim ne dan shi na farko, Fadila da itace ta biyu
kuma tana makarantar kwana ta Science and
Technical da take nan garin Kano, Khalid sai
Lukman.
Suna gamawa ya saka su a gaba suna fita tare,
daya sauke sune ma Khalid yace mishi
"Daddy idan na dawo zanje gidan Daada acan
zamuyi Weekend tare da Bajjo..."
Khalid din ya karasa yana kallon Julde da yake
girgiza kai
"Har kwana biyu zaku je kuyi, ka dai je idan na
dawo daga kasuwa da dare in biyo in dauke ku...
Shima Nawfal din zan hadu da shi daya tafi bai
fada mun ba"
Gardama ba halin Khalid bace ba, duk a cikin
yaran shi kadaine ba zai ja magana sau biyu da
Lubna sufyan
Hausabook.com 33
babba ba. Hakan yasa shi jinjina kai kawai yayi
ma Julden sallama yana bin bayan yan uwan shi
ya shige cikin makaranta. Julde kuma yaja
motar shi yana nufar kasuwa, zuciyar shi tayi
mishi nauyi fiye da kowanne lokaci.
*
Yanda yake cin abincin Daada take kallo, ya
tattara hankalin shi kamar bai taba yin wani
abu mai muhimmanci kamar wannan ba.
Tausayin shine cike da zuciyar ta, daren jiya da
ta zubo mishi taliya da miyar kifin da tayi ta
zallar tumatiri da albasa taga ya kalleta
"Tumatir ne kawai da albasa Bajjo"
Ta fadi tana kiran shi da sunan da ta makala
mishi kasancewar shi da daya tilo a wajen
mahaifin shi. Tana dadewa bata kira shi da
Nawfal ba. Tana gani ya saka cokali ya fara dibar
miyar da kifin yana kaiwa bakin shi, saida ya
sauke numfashi tukunna ya fara cin abincin. Yau
ma haka, kwano ta samu daban tana zuba mishi
miyar da tayi saboda shi kawai.
"Daada abincin nan yayi mun dadi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 34
Cewar Nawfal yana jin kamar ya samu waje ya
adana dandanon abincin ya dinga daukowa yana
tunawa a ranakun da zaici mai da yaji ko ya sha
shayi saboda Nanna ba zatayi abincin da zai iya
ci ba. Ya dade idan ya kalleta yana so ya
tambayeta laifin shi, yana so yaji me ya taba yi
mata mai zafi da ta dauki karan tsana ta dora
mishi ba.
"Yarana da gidan uban sune ma abinda na dafa
shi suke ci, ba zaka sakani girki biyu saboda
baka cin yaji ba wallahi, ba zan iya wannan
jidalin ba"
Ta kan yawaita fada mishi, ko a makaranta
Nawfal Bukar yake amfani da shi ba Isiyaku ba.
Ya san bashi bane baban shi ko bata tuna mishi
ba, amman shi din yake ma kaunar da ya kamata
yayi wa baban shi da bai san komai game dashi
ba bayan suna. Sai dai abu na farko daya fara
koya bayan magana shine yin shiru, akan
abubuwa da yawa, musamman abubuwan da
suka fi karfin fahimtar shi, da kuma wanda suke
damun shi. Shiru yafi komai saukin yi, furta
wasu abubuwan baya kawo gyaran su, ya taba
Lubna sufyan
Hausabook.com 35
furtawa Julde cewa Nanna tace gidan ba gidan
uban shi bane ba.
Fadan da sukayi a gaban idanuwan shi harya
mutu ba zai manta ba, yana da tabon dukan da
Saratu tayi mishi a bayan shi har gobe. Shiru yafi
komai sauki a wajen shi, yanzun ya kara
fahimtar duk abinda ake so yaji za'a iya fada
mishi ba saiya tambaya ba, abinda yake son ji
kuwa koya tambaya idan ba'a son fada mishi ba
zaiji ba.
"Kar dai ka fado daga kujerar nan wajen santi"
Daada ta fadi tana mishi dariya
"Ba dai zai hanani yabon girkin nan ba dan yayi
mun dadi... Idan zan tafi kika dibar mun miyar
nan zata dade bata lalace ba?"
Kallon shi Daada tayi
"Zata iya kwana biyu dai tunda ba sake dafawa
zakayi ba, ko akwai fridge a dakin ku?"
Kai ya daga mata saboda ya cika bakin shi da
shinkafa
Lubna sufyan
Hausabook.com 36
"To bari sai ka karo kayan miya da kifin in maka
da yawa, idan kaje saika saka cikin fridge ka
dinga diba"
Murmushi yayi, matsayin Daada daban yake a
wajen shi, ko ganinta yayi sai yaji wani sauki a
cikin ran shi. Da duk wani abu da zatayi kuma
da yanda take faranta mishi. Mikewa tayi tana
shiga daki ta fito da hijabi a hannunta
"Gara inje barkar nan sai ma in biya in taho da
Madina..."
Cewar Daada tana saka hijabin ta
"Kibari zanje in dauko ta"
Kai ta girgiza mishi
"Ba nisa da inda zanje... Sai na dawo"
Kai Nawfal ya daga
"Allah ya tsare. A dawo lafiya"
Daada ta amsa tana ficewa daga dakin. Abincin
shi ya gama ci ya dauke kwanonin ya kai
kitchen, ya dawo ya zauna yaji sallamar Khalid
daya amsa, uniform din da yake jikin Khalid din
Lubna sufyan
Hausabook.com 37
na tabbatar mishi daga makaranta kai tsaye nan
din ya nufo
"Da baka jirani mun taho tare ba gashi na zo ai"
Dariya Nawfal yayi
"Ka kyauta. Daman bance ba zaka zo ba ai,
kawai jiyan na so tahowa..."
Takalma Khalid ya cire yana sake yin sallama ya
shiga cikin falon, jakar shi ya fara saukewa dan
a cikin ya zubo duk wani abu da yake tunanin
zai bukata, yaji me Julde yace, amman yasan
wahalar dai yazo gidan Daada. Idan ta saka baki
dole yabar su su kwana biyu. Fada ne Nanna
zatayi idan ya koma, to ko bai zo ba Nannar shi
ba zata rasa dalilin yin fada ba, shisa bai koma
ta gidan ba yayi tahowar shi, zaice mata Daddy
ne yabar shi.
"Ina Daada?"
Ya tambaya
"Wai zatayi barka sai ta taho da Madina daga
makaranta kuma..."
Kai Khalid ya jinjina yana mikewa
Lubna sufyan
Hausabook.com 38
"Ni yunwa nake ji"
Kitchen ya wuce ya zuba abinci iya wanda yake
tunanin zai iya cinyewa yana hadowa da wani
filet din daban ya dawo falon, kan kafet ya zauna
ya ajiye filattan a gaban shi yana janyi jakar shi
ya bude. Mangwaro ne manya guda biyu ya
dauko
"Mangwaron ne a jaka Hamma?"
Nawfal ya fadi yana dorawa da
"Ko dan meye ba za'a samu a jakar ka ba"
Dariya kawai Khalid yayi, inda sabo ya saba jin
suna mishi wannan surutun. Kawai yafi yarda da
ya saka duk wani abu da yake tunanin zai iya
bukata a cikin jakar shi ta makaranta. Har
paracetamol zaka samu cikin jakar, inka
tambaya zaice maka
"Idan naji kaina yana ciwo fa? Tunda ba sanar
dani zaiyi kafin ya fara ba"
Akwai ranar da suke dawowa daga islamiyya
takalman Salim suka tsinke. Khalid ya zage
aljihun gaban jakar islamiyyar shi ya zaro
Lubna sufyan
Hausabook.com 39
takalma silifas yana mikawa Salim din yayi gaba
abin shi. Su duka binshi sukayi da kallo na wasu
dakika kafin su kwashe da dariya. Wata rana
dan tsokana ko sabulu ne ya kare musu a
bandaki zakaji suna
"A duba jakar Khalid ba za'a rasa ba"
Shiru yake ya kyale su kamar yanda yayi ma
Nawfal din yanzun. Abincin shi ya gama ci ya
tashi da filattan yana zuwa ya wanke
mangwaron, a fridge ya saka saboda Nawfal ya
siyo daman, ya kuma san ba zai sha ba sai yayi
sanyi ko yaya ne, idan ma yayankawa akayi zai
dauki na shi ya saka a fridge. Yanda Nawfal baya
mura har mamaki abin yake ba Khalid, idan ya
sha sanyin da Nawfal yake sha na rana daya a
sati saiya kwanta gadon asibiti. Da ya fito ma bai
zauna ba, dakin da suka saba sauka ya nufa,
wanka yayi ya fito ya dawo falon daga shi sai
gajeran wando
"Geez Hamma..."
Nawfal ya fadi yana kare idanuwan shi, kallon
kan shi Khalid yayi, yanda Nawfal din yayi wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 40
zai iya zaton babu kaya Khalid ya fito, karamin
tsaki yaja
"Kasan shekara bata fi daya ba a tsakanin mu
ko? Ba zaka daina ce mun Hamman nan kana
dora mun girma ba"
Batare da Nawfal ya sauke hannun shi daga kare
idanuwan shi da yayi ba yace
"Ka dai girmeni, zan daina in ka daina ce mun
Bajjo"
Wucewa kawai Khalid yayi abin shi. Mikewa
shima Nawfal din yayi, sai da ya kara watsa
ruwa, lokacin daya fito har Khalid ya gama
shirin shi ya fita. Shima shiryawa yayi cikin farin
yadi harda hula bula ya saka kamar takamin shi
daya dauko. Kafin ma ya fito yaji dawowar su
Daada saboda rakadin Madina da take kwala
mishi kira, sanda ya fito Khalid na fadin
"Lallai Madina, kamar baki ganni ba ko?"
Ko kallon shi batayi ba ta ruga da gudu tana
fadawa jikin Nawfal hadi da zagaya hannuwanta
jikin kafafun shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 41
"Hamma na dauka ka tafi kabarni"
Kanta ya shafa
"Nace miki ina nan har ki dawo makaranta ai...
Masallaci dai zamu tafi ni da Hamma yanzun mu
dawo, me zan siyo miki?"
Daga kai tayi tana kallon fuskar shi
"Biskit"
Khalid da yake zaune yace
"Ni ina da biskit din ai, ba zan baki ba tunda
baki kulani ba"
Juyawa tayi ta kalli Khalid
"Hamma na zai siyo mun ai dai, ko Hamma?"
Kai Nawfal ya jinjina yana dariya
"Ki je ki cire uniform, Daada tayi abinci mai
dadi"
Murmushinta ne ya fadada
"Tuwo ta dafa?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 42
Wannan karin har Khalid dariya yayi da Madina
bata ga dalilin su nayin dariya ba. Nawfal yace
anyi abinci mai dadi, shisa tayi tunanin tuwo ne
"Shinkafa"
Lokaci daya fara'ar fuskarta ta dishe tana raba
jikinta da Nawfal din
"Shinkafa kuma"
Ta furta ranta a bace tana sake saka su dariya.
Daki ta wuce harda jan kafafuwa a dole ranta ya
baci da aka dafa shinkafa ba tuwo ba.
"Daada zama dake yarinyar nan kaf ta kwashe
halin tsofaffi, ace ga shinkafa amman tuwo ne a
ranta"
Khalid yace yana dariya
"Ku da bakuyi halin tsofaffin ba ai sai kuyita
fama da shinkafar ku, amman ni tuwo zan mana
anjima"
Mikewa Khalid yayi
"Tafdin, aci tuwo lafiya..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 43
Dan shi baya so, tuwo da danwake na cikin
abincin da yunwar da zata saka shi cinsu ba
karama bace ba. Sallama suka yiwa Daada suna
fita masallaci.
"Adee..."
Ya kira ta da sunan da Khalid ya saka mata tun
lokacin baya iya kiran sunan ta, maimakon
Fadila din sai ya gajarce shi zuwa Adee da kowa
yake kiranta da shi yanzun
"Ke bakya jin rana?"
Kai ta girgiza mishi, duk rashin magana irin ta
Nawfal bai kai Adee ba. Dan ta ita duniya bata
tashi ba, komai da sanyi-sanyi takeyin shi.
Kusan ita ta kwaso jikin fulanin. Yanzun haka
idan kaganta ita da Nawfal din babu wanda zaice
itace babba, kanta da wahala idan ya kai kafadar
shi, bata da tsayi kuma bata da jiki. Sai hasken
fatar da kusan gadon shi sukayi. A gajiye take
jinta, ta rasa inda Daddy ya tsaya da yau baizo
daukar su ba. Ta riga da ta saba da anyi hutu ta
fito a bakin gate take samun motar shi yana
jiran ta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 44
"Yau Daddy ya dade..."
Tayi maganar cike da kosawa. Nawfal bai amsa
ta ba, baisan me zaice mata ba. Inda yana da zabi
zai zauna a makaranta abin shi. Duk satin
duniya sai Daddy yazo ya gansu. Wasu satikan
da Khalid yake zuwa. Sai dai a wani bangaren
idan ya tuna zai ga Daada sai yaji komawa gida
ba abu bane mai muni kamar yanda zuciyar shi
take fadi. Sati ukune kawai hutun nasu, idan ya
rike numfashin shi kafin ya sauke zaiga
kwanakin sun wuce kamar ba'ayi su ba. Zai
kokarin gujema Nanna a satikan.
"Daddy muna ta jiran ka"
Muryar Adee ta katse mishi tunanin da yake,
yana daga kai ya kalli Daddy da yake mishi
murmushin da yake mayar mishi. Sai yaji kamar
anfi sati rabon da yaga Daddyn saboda yanda
yayi kewar shi
"Ba kun gujeni kun zabi boarding ba yaran
nan?"
Dariya sukayi gabaki dayan su. In da zasu biye
Julde sam ba zasu hada hanya da makarantar
Lubna sufyan
Hausabook.com 45
kwana ba. Ya fiso ya dawo gida ya gansu kafin ya
kwanta, idan ya tashi da safe ma ya gansu kafin
ya fita. Saboda su baya tafiya ta wuce kwana
biyu, kewar yaran shi zata fara tambayar shi. Sai
dai a lokaci daya kuma bashida zuciyar hana su
abinda yaga muraran suna so. Da zai iya da ba
zasu zo makarantar kwana ba, musamman
Nawfal da baya kaunar yaga yayi mishi nisa. Su
Adee yaran shine, jinin shine, daga jikin shi suka
fita. Ba zai karya ba suna da matsayin da za'a kai
ruwa rana kafin wani ya taka shi a zuciyar shi.
Amman Nawfal, matsayin Nawfal abune da ba
zai iya furtawa ba, babu kalaman da zai iya
amfani da su ya misalta yanda yake jin Nawfal
gab da zuciyar shi.
"Amana ta ne Julde, yaron nan amanata ne"
Abinda Daada ta dinga jaddada mishi, abinda
yake so ya kalli ba ita ba har kowa yanzun yace
"Nawfal amanata ne, ni ya kamata Bukar ya ba
amana..."
Saboda Nawfal ya fito daga jikin bukar ne kawai,
amman dukkan wata kauna da uba zai yiwa dan
Lubna sufyan
Hausabook.com 46
shi itace yake yiwa Nawfal. Kuma yana godewa
Allah idan yaga irin murmushin nan a fuskar
Nawfal. Idan yaga yanda Nawfal yake nuna mishi
ko duniya zata hade waje daya tare da mutanen
cikinta in dai zata sake budewa to zai riko
hannun shi a matsayin Uba.
Soyayyar da take tsakanin su mai girma ce
Sai dai rubutacciyar kaddarar da take tsakanin
su tana son danne girman soyayyar
"Bajjo jiba idanuwan ka, kana ma cin abinci?"
Dariya Nawfal yayi me sauti
"Baka ga yanda Adee ta koma ba"
Kallon su Adee tayi
"Rabon da in koma wani abu anfi shekara uku,
ina nan yanda nake... Da gaske idanuwan ka sun
rame"
Akwatin shi daya tashi daga kai yake kokarin
dauka kafin Julde ya karasa ya karba, baiyi
musu ba ya sakar mishi. Ko siyayya ya fita dasu
shi yake rike ledojin, duk yanda zasuyi su karba
zai ce
Lubna sufyan
Hausabook.com 47
"Yaushe hannuwan ku zasu iya daukar wannan
kayan. Da nauyi sosai"
Da akwatin Adee ya hada ya saka su bayan
motar
"Yanayin abincin ka ya sa bana son ka da
makarantar kwana Nawfal, nasan wahala zaka
sha"
Gaban mota Nawfal ya bude ya shiga. Adee ta
hau baya. Daddy ya zagaya ya zauna mazaunin
direba ya rufe murfin. Har ya tayar da motar ya
juya yana mitar yanda Nawfal din baya cin
abinci duk ya rame. Murmushi kawai Nawfal
yayi
"Ina ci fa Daddy, dan baka gani na kullum ne
shisa..."
Kai Julde yake girgizawa, ko satin daya fita da
yazo ganin su bai ga yayi zuru-zuru haka ba.
Shiru kawai Nawfal yayi, dan baisan me zaice ba.
Julde baisan cewa yafi koshi a makaranta fiye da
gida ba. Tunda yana da zabin na yaci abinda aka
dafa ko akasin haka. Idan shinkafa da miya ne,
ya amshi fara yana da kifin gwangwani zai juye a
Lubna sufyan
Hausabook.com 48
ciki yaci abin shi, wata rana zaici snacks. A gida
bashi da wannan zabin, akwai kifin gwangwani
da Daddy kan ce saboda shi yake siyowa. Kamar
kuraye haka su Khalid suke akan nama, shine
kawai bayacin nama Kwata-kwata.
Ba allergy bane ba, kawai bayajin zai iya cin
nama tun yana da karancin shekarun shi. Da
yagan shi a cikin miya ma hankalin shi tashi
yake, daga kaza har sauran nau'in nama. Baisan
a shekarun yarintar da ba zai iya tunawa ba ko
yaci, iya wanda zai tuna kawo yanzun baya hada
hanya da duk wani abu nama. Amman kifin nan
bai isa ya taba ba. Idan danyene aka kawo dan
ayi miya. Nanna zata sarrafa shi yanda zai zama
haramiyar shi. Shisa bai taba saka rai a duk
wani abu da saiya fito ta hannunta sannan ya iso
wajen shi ba.
Idan Adee tazo hutu yana jin dadi, yana cin
abinci da miya, da kanta take shiga kitchen tayi
mishi miya ta kuma juye a rubber ta kai mishi
dakin shi.
"Me yasa kike haka Nanna?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 49
Shine tambayar Adee duk idan Nanna tayi
kokarin hanata. Wasu ranakun harda duka
amman ko bandaki Nanna ta shiga sai tasan
yanda tayi ta kaima Nawfal din wani abu da zaiji
dadin shi. Kifin gwangwani kuwa ita da Khalid
suna diba su kai mishi ya ajiye a dakin shi,
Khalid da dai-dai zai dauka. Adee zata iya
daukar kwalin gabaki daya, wata rana nata na
makaranta randa ta dawo hutu take zuwa ta kai
mishi. Kamar bata ci kwata-kwata tana tarawa
ne don shi. Kananun abubuwa irin wannan yasa
yake jinta har ran shi.
"Ka daina jira sai Nanna ta baka abu, idan
kagani kana so ka dauka ka tafi abinka"
Ta kan fada mishi wasu lokuttan idan ta kai
mishi wani abin. Sai dai yayi dariya, baya son
tashin hankali sam, duk wani abu da zaiyi ya
gujema fadan Nanna zaiyi, wani lokacin zai
rantse ganin shi kawai harzuka matar yakeyi. In
ba Daddy yana nan ba baya shiga bangaren ta.
Ko yunwa zata kusan halaka shi daya leko ta
window yaga tana falo saiya koma, in Khalid
yana nan zai mishi magana ya zubo mishi abinci.
Lubna sufyan
Hausabook.com 50
Idan baya nan kuma zaici duk abinda yake da
shi a bangaren shi.
Yanzun ma da suka karasa akwatin shi yaja
zuwa zai nufi na shi bangaren
"Kamar jira kake Nawfal? Ba zaka shiga kaga
Nannar taka ba?"
Murmushi yayi
"Daddy nagaji, zan watsa ruwa tukunna..."
Kai kawai Julde ya daga ya rufe bayan motar
yana daukar akawatin Adee da tayi saurin
kamawa tana fadin
"Bajjo zaka ba, akwai wasu kayan shi a ciki, idan
ya kwashe naje in dauka"
Ta karasa maganar tana kallon Nawfal da fuskar
shi take dauke da alamar tambaya. Kai ta dan
daga mishi, cikin sanyin jiki ya karaso yana jan
akwatin nata ya hada da nashi ya nufi bangaren
shi. Ita da Daddy suka wuce cikin gidan tana
bashi labarin da bashi da kan gado dan kar ya
tambayeta wanne kayan Nawfal ne a akwatin ta.
*
Lubna sufyan
Hausabook.com 51
"Takardun meye wannan?"
Saratu ta tambaya tana rarraba takardun a
tsakanin hannuwanta, a karo na babu adadi
tana jin takaicin rashin ilimi, daya daga cikin
rashin gatan da maraici yayi mata. Duk da boko
ce karshen abinda aka damu dashi a inda ta
tashi, amman ko bakomai an sa taje makarantar
allo, babu wanda ya damu da yanda rayuwarta
zata kasance.
"Takardun filayen Bajjo ne za'a siyar da wasu a
sai mishi gida"
Wani abu taji ya taso da ba zata ce ga daga inda
yake ba, amman dacin shi har akan harshen ta.
Filaye Julde yace, hakan na nufin ba daya ba ba
biyu ba tunda yana kiran wasu daga ciki za'a
siyar a sai mishi gida.
"Yana da dukiyar shi Saratu, Nawfal na da
dukiyar da tunanin ki ba zai taba hangowa ba.
Ba taimaka mishi nake ba dan ina biya mishi
kudinn makaranta, ganin dama ta ne kawai..."
Kalaman Julde suka dawo mata wani lokaci can
baya da tayi tsegumi akan yanda zaman Nawfal
Lubna sufyan
Hausabook.com 52
din yake karin nauyi akan shi. Ba zata daina
wahalar da kwakwalwar ta wajen tunanin inda
Bukar ya samu arziki har haka ba. Bukar fa,
Bukar dai daya bar kauyen su da sunan zuwa
neman ilimi. Tsoron kar tunanin ta yayi karadin
da wani zaiji shisa take tausar shi, amman akwai
ayar tambaya mai girma akan wannan kudin da
Bukar yabar wa Nawfal kamar yanda akwai
babbar tambayar da kowa yaki yarda ya furta
akan asalin haihuwar Nawfal.
"Dukiyar Nawfal bata karewa ne? Har nawa
yake da..."
Sauran maganganun suka koma mata saboda
yanayin juyawar da Julde yayi yana kallon ta
"Meye matsalar ki da dukiyar shi? Sanin yawan
ta amfanin me zaiyi miki?"
Kauda kai tayi gefe, abinda take ji yana kara
ninkuwa, wannan dukiyar da yake kira Nawfal
na da ita da su Salim take hangota, duk wani jin
dadi da yake gidan duniya rayuwar yaranta take
hangowa a ciki.
Lubna sufyan
Hausabook.com 53
"Su Khalid ma ya kamata ace suna da gidajen su
yanzun tunda kana da halin"
Karamin tsaki Julde ya ja kafin ya taka ya fisge
takardun da suke hannunta yana mayarwa cikin
jakar shi. Bai san me yasa daya dawo hannunta
kan jakar shi yake fara sauka ba, sai kuma ta
dame shi da tambaye-tambayen da bayaso kan
duk wata takarda da zata gani kamar ya aiketa.
"Duk takardar da zaki gani in ba zaki iya
karantawa kiji ko ta mecece ba karki sake
damuna da tambaya"
Maganganun shi sunyi mata zafi ba dan kadan
ba, duk da ba yau bane rana ta farko da yake
amfani da duk damar da zai samu na goranta
mata rashin ilimi kamar laifin nata ne. Karatun
hausar da ya koya daga bayane da dan kalaman
turanci daya tsinta akan titi suke kara bashi
damar zaginta haka.
"Ka sama mun makaranta ko ta yaki da jahilci
ce..."
Ta furta cikin wata irin sanyin murya. Sosai
Julde ya kalleta wannan karin kafin ya kwashe
Lubna sufyan
Hausabook.com 54
da dariya yana girgiza kai kawai. Har ranshi
dariya ta bashi. Duk tsayin shekarun nan batayi
tunanin shiga makaranta ba sai yanzun? Saboda
tana son saka ma shige da ficen shi idanuwa fiye
da yanda takeyi yanzun. Takardun shi ya mayar
tsaf ya gyara ya karasa yana samarwa jakar
waje ya ajiye. Fita yayi daga dakin baccin nasu
zuwa falo yana jin motsin Adee a kitchen, hakan
yasa shi tunkarar kitchen din ya kuwa ganta
tana wanke-wanke.
"Sannu da aiki..."
Da murmushi a fuskarta ta juyo
"Daddy Am... Ba wani aiki bane ba fa"
Kai ya jinjina, komai ma in dai ya danganci
hidimar cikin gida amsa daya Adee zata baka,
dan wajenta ba aiki bane ba, har mamakin
kokarinta yakeyi a kankantar da take da shi,
gashi sanyin halinta baisa tana da sanyin jiki ba
"Ni ma zan leka Daada ne"
Wannan karin fuskarta cike da roko tace
"Dan Allah zanje... Saura kadan in karasa..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 55
Dan jim Julde yayi sannan ya amsa
"Bari to in duba su Khalid, nasan zasuje suma
sai su shirya duk mu fita gabaki daya"
Murmushi tayi har
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 18