kuma fara bata taimakon da take
bukata, saboda Salim din, shi baibi sauran
likitocin ba sai da ya tsaya aka binciko file din
Daada tunda nan asibitin take zuwa duk idan
bata da lafiya.
Da kanshi ya bude yana bincika record dinta
kafin ya bisu dakin, har an saka mata ruwa an
mata allurar jini, wata Nurse tace mishi an dauki
jininta don a gudanar da gwaji, tambayoyi ya
shiga yi ma likitan daya duba Daada din suna
magana cikin harshen da in ba fannin aikin su
ka karanta ba sai sun fassara maka zaka gane
me suke cewa. Tare suka fito da likitan, shi yana
wucewa, Salim kuma yana kallon inda Madina
take tsaye ta jingina bayanta da bangon wajen,
ko takalma bata da shi, safa ce a kafarta, dan dai
tana da kauri, sai kayan baccin da ko shi ya saka
tsayin wandon ne kawai zai mishi kadan. Dan
murmushi yayi yana karasawa ya taba
kafadarta.
Da sauri ta kalle shi
"Hamma? Me yake damun ta?"
Kai Salim ya girgiza mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 306
"Komai zaiyi dai-dai"
Ganin yanda take kallon shi ya sa shi dorawa da
"In shaa Allah"
Kai ta jinjina badan ta yarda ba
"Ki shiga ki zauna da ita, zan kira Nanna in fada
mata"
Kan dai ta sake jinjina mishi, murmushin karin
kwarin gwiwa yayi mata, baya son yanda tayi
sanyi, sai da ta tura kofar dakin da Daadan take
ta shiga tukunna ya sauke numfashi. Ya kanji
Julde yace Daada bata da lafiya, ko kuma ya biya
ya kai mata magungunan ta, wasu lokuttan ma
tare suke zuwa su duba ta, amman yaune ranar
farko da yasan tana dauke da ciwon zuciya,
saboda bai taba tambayar Julde me yake damun
Daada ba, yanzun ma a file din ta ya gani, jininta
ma yakan hau ya sauka, amman baya irin hawan
da za'ace yana barazana da rayuwar ta, ciwon
zuciyar ne dai.
Da alama Madina ma bata sani ba, kuma ba zai
zama na farko da zai fada mata ba. Lambar Julde
ya fara kira sai yaji ta a kashe, hannu ya kai yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 307
murza goshin shi, yana da round din da zaiyi, ba
yanda za'ayi ya zauna da Madina, kuma ba zai
yiwu abarta ita kadai ba. Baya son wayar ta
tashi Saratu, Khalid ya kira, bugu biyu ya daga
"Hamma, lafiya dai ko?"
Yanayin muryar Khalid din ya sa Salim fadin
"Uban me kakeyi ba kai bacci ba har uku na
dare?"
Yanajin yanda Khalid ya sauke mishi numfashi a
kunnen shi, abinda ya tsana, shisa in zai waya
yawanci yake sakata a speaker ya ajiye a kasa,
ya rasa dalilin da zaisa anna waya ana
numfarfashi da wasu kananun nishi da yake
bakanta mishi rai
"Kira na kayi kaji ido na biyu ko akwai abinda
zaka fada mun?"
Cewar Khalid din
"Daada bata da lafiya, gata a asibitin mu, ka
fadawa Nanna, bana so in tasheta da waya"
Yana jin motsi alamar Khalid din ya tashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 308
"Subhanallah, tun yaushe?"
Kashe wayar Salim yayi, saboda zai iya watsama
Khalid din zagi, yana da tambaye-tambaye
marassa amfani, a aljihu ma ya saka wayar, yana
barin bangaren gabaki daya zuwa inda ofishin
shi yake.
*
"Daga jikin wa ka baro ka taho?"
Cewar Saratu bayan Julde ya shigo dakin tana
binshi da wani mugun kallo, bacci takeyi taji ana
kwankwasa dakinta, dakyar ta rabu da gado
tana zuwa ta bude
"Nanna..."
Khalid ya kira yana dorawa da
"Daada ce bata da lafiya, tana asibiti, yanzun
Hamma ya kira yake fadamun"
Dan dakuna fuska tayi, kafin ta jinjina ma Khalid
kai tana juyawa batare da tace komai ba
"Bari in sakko dogon wando in dauko id card
dina sai in zo mu tafi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 309
Har ranta batayi niyyar zuwa ba, rashin lafiyar
Daada ba matsalarta bace ba saboda dalilai
masu yawa, amman akwai halayenta da bata
cika son yaran nata suna gani ba, musamman
Khalid, shisa ma ta daga mishi kai kawai,
kayanta ta sake itama, suna hanya tana hamma
saboda baccin da ko awa batayi da samun shi ba.
Fadan da sukayi da Julde kafin ya fita ya sa taita
juyi a gado ranta na mata zafi
"Bunsuru kika taba kirana Saratu, ko kin
manta? Ban canza ba har yanzun, bunsurun ne,
ki daina yin kamar baki san abinda zan fita yi
ba"
Duk tashin hankalin da tayi bayan nan ko inda
take bai kalla ba, tasani, ta fi kowa sanin me
yake fita yi duk daren da zai shirya tsaf ya fice,
tana kauda kaine yanda ta saba, tana kuma
amaye abinda take ji idan yazo mata wuya.
Kamar yanda tayi jiya, sai dai ko yaushe ita ce
take faduwa kasa warwas, dan fada da Julde
babu riba a cikin shi, ko tace bata samun riba a
fada da shi. Sai ya tabbatar ya nuna mata bata da
muhimmanci a rayuwar shi, zaman da takeyi da
shi zabinta ne, in ta barshi babu abinda zai
Lubna sufyan
Hausabook.com 310
canza. Hakan yafi mata ciwo fiye da neman
matan shi, ba zatayi karya ba, zata so ko kadan
ne ta samu wani muhimmanci a rayuwar shi.
Don shi yana da shi a tata rayuwar, akan ce
wasu mazan na duba darajar 'ya'ya, to a
idanuwan Julde bata taba cin darajar yaran su
ba, zaka rantse da Allah shi yayi dakon cikin su,
nakuda da rainon su
"Saratu"
Julde ya kira cike da kashedi yana kallon Daada
da take kwance, da alama bacci takeyi, sanin
cewa bai daina halin shi ba shine karshen
abinda zai so taji
"Meye? Baka so ta sani? Baka so taji babu abinda
ya canza daga mugun halin ka?"
Runtsa idanuwan shi Julde yayi yana sake bude
su akan Daada, ko motsi baiga tayi ba. Likitanta
daya gani kafin ya shigo ya fada mishi ciwon
zuciyarta ne, amman babu wata matsala in dai
ta samu hutu kwana biyu, a kuma tabbatar babu
wani abu daya faru da zai daga mata hankali, in
dai an kiyaye wannan zata samu sauki. Wannan
Lubna sufyan
Hausabook.com 311
maganar da Saratu take son ya biye mata suyi na
cikin abinda zai daga hankalin Daada. Shisa yaja
kujera ya zauna yana yin shiru ya kyale ta. Yana
jin yanda take watsa mishi wani irin kallo, kafin
ta ja tsaki tana mikewa ta fice daga dakin.
Daman ko bai zo ba, ita gida zata tafi, bata da
dalilin zama asibiti, ta dai cewa Madina zata
zauna ne dan taje gida ta watsa ruwa ta sake
kaya ta kuma dauko musu abinda suke bukata.
Salim ne ya tafi ya kaita tunda gari ya waye. Da
kanta ta kira Adee ta fada mata, saboda tasan
zata kawo abincin kari
"Saboda Yelwa kawai"
Ta fadi cikin ranta bayan ta rufo musu kofar. Ko
Daada ba darajar Julde take ci ba a wajenta,
saboda Yelwa ne, in har mutunci zai shiga
tsakanin su bayan tarin kiyayyar da ta nuna
mata to saboda Yelwa ne. Julde kuwa numfashi
ya sake saukewa yana kallon Daada, wayar shi a
kashe take, cikin mota ma yabar ta, sanda ya fito
bayan asuba ya zo ya kunna ya ga sakon Khalid,
kai tsaye asibitin yayo, sai dai da nisa daga inda
yake, tunda yafi zuwa hotels din wajen gari, inda
Lubna sufyan
Hausabook.com 312
kafin ya hadu da wanda ya sani za'a dauki
lokaci, ko gidan gonar da yayi shi don wannan
dalilin kawai ba don komai ba.
Kafin yayi wani tunani an turo dakin da sallama
"Daddy..."
Salim ya fadi cikin gaisuwa, Adee da ta shigo
bayan shi da murmushi a fuskarta ta gaishe da
shi itama, kallon ta Salim yayi, suna hanyar
gidan Daada wayar Salim ta shiga vibrating,
dagawa yayi ganin Nawfal ne ya sa shi kai wayar
kunnen shi
"Na kira Hamma Khalid bai daga ba, me ya sami
Daada? Yace mun bata da lafiya tana asibiti, me
suka ce yana damun ta? Ya jikin ta?"
Yanda yayi duka tambayoyin a numfashi daya
yasa Salim fadin
"Da sauki"
Cikin taushin murya yana dorawa da
"Zazzabi ne kawai, da sauki kuma sun riketa ne
dan ta huta sosai"
Lubna sufyan
Hausabook.com 313
Duk da baiga Nawfal ba yasan ya ciza gefen
leben shi na kasa yanda yakan yi duk idan yana
cikin damuwa
"Dan Allah Hamma ka fadamun gaskiya, ya take?
Boye mun ba zaiyi amfani ba, is not like zan iya
tahowa yanzun-yanzun, kawai ina bukatar in
san halin da take ciki"
Bai fada mishi dukkan gaskiya ba, amman da
sauki, zazzabin ya sauka, da kan shi ya duba
kafin su taho, kuma jininta lafiya kalau, bai hau
ba
"Ga Madina..."
Salim ya fadi yana mika mata wayar, saboda
baisan me zai fada Nawfal ya yarda da shi ba
"Madina"
Muryar Nawfal ta daki kunnen ta tana sakata jin
wani abu ya tsirga mata
"Hamma"
Cikin wani irin yanayi Nawfal yace
Lubna sufyan
Hausabook.com 314
"Ya take Madina? Ki fada mun? Ke nasan ba zaki
mun karya ba"
Numfashi ta sauke
"Da sauki, bata kara yin amai ba, tana ta bacci
ne, gani ma Hamma zai kaini gida in watsa ruwa
in dauko mana su kafet haka..."
Tana jin ajiyar zuciyar da Nawfal ya sauke yana
ma Allah godiya cikin harshen fulatancin
"Ban san ya zanyi ba in wani abu ya same ta, ban
sani ba...na kusa dawowa gabaki daya in shaa
Allah, saura yan watanni, ba zan kara nisa ba
idan na dawo..."
Madina bata jin ko ya dawo zata daina jin yanda
yayi mata nisa
"Idan ta tashi ki kirani, tana tashi Madina"
Kai ta jinjina
"Zan kira ka Hamma..."
Kamar ba zata sake cewa komai ba tace
"Ka yarda dani, da sauki, da sauki sosai"
Lubna sufyan
Hausabook.com 315
Yanda ta karasa maganar ne ya kasa barin
kunnen Salim, kulawar da take cikin muryarta
yaji ta sa kirjin shi ya matse, sai kuma yanda ta
mika mishi wayar tana fadin
"Hamma ya cika saka damuwa a ran shi"
Tana saka shi dana sanin bata wayar da yayi,
har ya jirata bai daina jin wani zafi-zafi a kirjin
shi ba, yanzun ma da yake kallon ta yana jin
yanayin na karuwa ne, akan me zata sauke
murya da yawa haka, shi bai taba ma jin ta
sauke mishi murya cikin kulawa yanda ta sauke
ma Nawfal ba, wayar shi da yaji tana zuu cikin
aljihun shi ya zaro ya duba
"Hamma ne?"
Madina ta tambaya, shi dinne, baisan me yasa ya
girgiza mata kai yana juyawa ya fice daga dakin
kafin ya daga wayar ba
"Hamma ta tashi?"
Nawfal ya tambaya daga dayan bangaren
"Yanzun muka dawo Bajjo, bacci takeyi, tana
tashi ni da kaina zan kira ka"
Lubna sufyan
Hausabook.com 316
Yana jin Nawfal din ya sauke numfashi cike da
damuwa
"Bacci takeyi, bacci take Bajjo, na taba maka
karya?"
Cewar Salim yana jin yanda baya son damuwar
Nawfal din da yake karanta ta cikin wayar
"Zan kara kira"
Kawai Nawfal yace yana kashe wayar. Dakin
Salim ya koma, camera din wayar shi ya shiga
yana kashe hasken sannan ya dauki Daada
hotuna guda biyu, batare da tunanin komai ba
ya bude whatsapp din shi yana tura ma Nawfal
"Kagani, da sauki, kuma kaci abinci"
Ya rubuta a kasan hotunan yana sauka daga
whatsapp din bayan yaga shigar sakon na shi ya
mayar da wayar a aljihu, bashi da matsala da
kula da Nawfal, kawai baya son Madina tayi ne,
ko kadan baya so, bai taba sanin baya so ba sai
yau.
Lubna sufyan
Hausabook.com 317
Sake runtsa idanuwan ta tayi a karo na babu
adadi, saboda duk lokacin da zata bude
idanuwan sai ta dinga jinta a wata duniya
tsakanin rayuwa da wani abu da ba zata iya kira
da mutuwa ba tunda bata san yanda take ba. Ko
wacce gaba ta jikinta ciwo takeyi, ga kirjin ta da
yayi nauyi tamkar an dora wani irin dutse a
saman shi
"Daga jikin wa ka baro ka taho?"
Kunnuwan ta sun jiye mata wannan kalaman,
idan ba karya suka isarwa kwakwalwar ta ba
tabbas muryar ta Saratu ce, a tsayin shekarun
nan duk wasu kalamanta na rashin kirki ta koyi
takaita su ne akan Julde kawai, shisa zuciyar
Daada take hasasa mata cewa wannan karin ma
da Julden take, wani irin hijabi taji ya gifta
tsakanin ta da zantukan su Saratun shisa ta
hakura tana barin duhun da ya janyeta yin
nasara.
"Daada ga Hamma can ana dukan shi a gonar
mai saje, kiyi sauri kizo, kiyi sauri kar su illata
shi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 318
Yelwa ta sauke kowacce kalma a tsakanin
numfashin da take kokawa da shi cikin alamun
gudu tayi, a cikin harshen fulatanci, murfin
tukunyar tuwon da Daada ta gama tuqawa ta
dauka tana rufewa, kafin ta daga idanuwanta
tana sauke su kan Yelwa cike da nutsuwar da
zakayi mamakin ta a tattare da mahaifiyar da
aka zo ma da sakon ana dukan danta. Sai dai
bashi bane karo na farko, ba kuma na biyu bane
ba, idan Daada zata runtsa idanuwan ta, lokutta
irin wannan zasu bace a tunanin ta, ba zata iya
lissafa adadin su ba saboda yawaitar faruwar su
"Daada ki ta so"
Yelwa ta sake fadi a kagauce, murmushi Daada
tayi, murmushin da taji ya fito daga tsakankanin
zuciyar ta inda yake yawaita yi mata ciwo da
labarai irin wa'annan
"Me zan musu Yelwa? Zan iya hana su dukan shi
ne?"
Kai Yelwa ta girgiza cikin alamar rashin yarda,
daga inda Daada take zaune tana ganin kyallin
hawayen da yake cike da idanuwan Yelwar,
kafin ta kai hannu tana daukar muciyar da take
Lubna sufyan
Hausabook.com 319
a jingine da bango, ko gama bushewa daga
wankin da Daada tayi mata ba tayi ba
"Ba zasu kashe shi ba, ba zan bari su kashe shi
ba Daada"
Yelwa ta karashe maganar tana kai dayan
hannunta ta dauke hawayen da take jin alamun
zubowar shi tana juyawa
"Allah ya tsine miki albarka idan kika saka kafa
kika fita daga cikin gidan nan"
Ta tsinkayo muryar Datti a masife da ta saka
kafafuwanta tsayawa cak
"Kin jini ko Yelwa? Allah ya tsine miki albarka
idan kika fita daga gidan nan"
Juyawa tayi tana fara sauke idanuwan ta kan
butar da take hannun shi, daga bandaki ya fito.
Yana gidan kenan? Dariya Yelwa tayi me sauti
"Ki bari su kashe shi, Allah ya basu sa'a su kashe
shi"
Wannan karin hawayen Yelwa zubowa su kayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 320
"Asarar tawa ce ni kadai idan sun kashe shi na
sani..."
Ta ce tana sake kai hannu ta share kuncin ta,
tana kara ba wasu hawayen damar zubowa,
kafin ta janye idanuwan ta daga na Datti tana
sauke su cikin na Daada
"Muna da junan mu, ni da shi, ki fada mishi
Daada, ya kara tsinuwar shi akan jerin na
baya..."
Yelwa ta karashe tana juyawa ta nufi hanyar da
zata fitar da ita daga cikin gidan, sautin
tsinuwar da Datti yake jera mata nayi mata
rakiya
"Daada..."
Ta tsinkayi muryar Yelwa na mata kutse cikin
duhun da ya janyeta
"Daada!"
Ta sake jin muryar
"Ki barta tayi baccin ta"
Lubna sufyan
Hausabook.com 321
Ta tsinkayi wata murya da take son gane
madaukin ta
"Idan naga ta bude idanuwan ta ko kadan ne zan
samu natsuwa Hamma...Daada!"
Sai dai a karo na farko ta raina karfin ta, saboda
yanda take kokawa da fatar da take lullube da
idanuwan ta cikin kokarin bude su. Hannun da
taji kan nata ya kara mata karfin gwiwa, dakyar
ta iya bude rabi tana ganin dishi-dishi, ta mayar
ta rufe, tana sake kokartawa wannan karin dan
gabaki dayan shi ta bude shi
"Madina"
Ta fadi cikin zuciyar ta, ganin gilashin da yake
fuskar ta, ba Yelwa bace ba, Madina ce, tunani
ne ya dibeta zuwa baya, babu wani abu. Tabaro
wannan rayuwar, tayi nisa da ita. Inda take
yanzun ba can bane ba, tana tare da Madina,
tana tare da sanyin idaniyar ta, tana tare da
yarinyar da ta saukaka ciwon da yake cikin
kirjin ta
"Daada..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 322
Madina ta fadi da murmushin nan nata da yake
sanyaya wajaje da dama a tare da Daadar
"An mata allurar bacci ne fa, me yasa bakya jin
magana ne?"
Salim yace yana jin muryar shi ta fito da wani
irin sanyi da baiyi tsammani ba, fada yaso yayi
mata, a fadace ya jera kalaman cikin kan shi, a
tsakanin ratsowa ta cikin kan zuwa makoshin
shi suka sanyaya haka, tafi minti sha biyar tana
son tashin Daadar yana hanata, har bakin shi ya
fara nauyi da yanda take ta saka shi yawan
magana. Rigar ta da shi kan shi ta mishi yawa ya
kama ta baya yana janyo ta baya kamar ya jawo
ledar da babu komai, kafin tayi wata garda ya sa
kafar shi ya jayo kujera yana fisgarta ya zaunar
a kai.
Bayan yatsun shi biyu da manuniyar da na
tsakiyar ya hade waje daya yayi amfani da su
yana kai mata duka a goshin ta har saida ta
runtsa idanuwan ta dan taji zafi sosai tana fadin
"Ouchhh Hamma..."
Hadi da murza wajen tana turo labba
Lubna sufyan
Hausabook.com 323
"Ki zauna nan, nagaji da magana"
Bakin dai ta sake turowa har lokacin tana murza
goshin ta, Daada ta kalla, ta sake mayar da
idanuwan ta rufe, yanayin yanda take numfashi
na nuna alamar bacci ya sake dauke ta, agogon
da yake daure a hannun shi Salim ya duba, sam
bai san lokaci ya ja haka ba, shisa yaji kan shi
yayi nauyi. Bacci ne sosai a idanuwan shi, gashi
aikin dare yake da shi yau ma, mikewa yayi
"Zanje gida in watsa ruwa in dan kwanta, ki
kirani idan akwai wani abu, anjima zan dawo"
Kai Madina ta jinjina mishi, tun dazun yake ta
hamma, da tace yaje yayi bacci kai ya girgiza
mata, itama bata son zama ita kadai, taji dadi da
Adee ta zo, amman bata wuce awa biyu ba tace
zata koma dan ta dake dora musu abincin da
zata kawo da daddare, zasu sake dawowa da
mijinta. Julde ma kiran da ake ta mishi a waya
yasa Salim ya lallaba shi ya tafi bayan ya
tabbatar mishi da cewa babu komai, bacci
Daadar takeyi saboda ana so ta huta sosai.
"Ka siyo mun awara idan zaka dawo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 324
Numfashi Salim ya fitar
"Ina zan ga awara?"
Shagwabe fuska tayi
"Akan titi fa, ko ina zaka ga ana soyawa, ba mun
taba siya ba rannan?"
Kai Salim ya girgiza
"Rannan din kinsan wacce hanya ce? Kibari idan
muka fita tare"
Yanda tayi da fuska tana kai hannu ta sake tura
gilashin ta sai yaji gwiwoyin shi sun yi sanyi,
kananun abubuwa haka zatayi duk sai yaji ta
kashe mishi jiki
"Fine, idan nagani"
Murmushin nan ya samu da takanyi da dukkan
hakoranta, tana saka shi mayar mata da martani
"Ina kudin da Daddy ya baki?"
Hannu ta fara kaiwa aljihun wandon da yake
jikinta, tana saka shi girgiza mata kai
Lubna sufyan
Hausabook.com 325
"Ba sai kin dauko ba, idan kina son wani abu ki
fita ki siya, inda muka siyo ruwa dazun, zaki
gane ko?"
Kai Madina ta daga mishi kafin ya sake
numfasawa
"Ki kula kina ji? Ba zan dade ba"
Kan dai ta sake daga mishi, ji yake kamar karya
tafi ya barta, amman ko baya bukatar hutu yana
son watsa ruwa ya sako kaya. Dakyar ya iya jan
kafafuwan shi yana fita daga dakin. Gyara
zamanta Madina ta karayi akan kujerar tana
jingina sosai, ita ma baccin ne a idanuwanta. Ta
kusan mintina biyar a haka kafin ta ja kujerar
har kusa da gadon Daada, kanta ta dora akan
gadon daga gefe tana runtsa idanuwanta
"Allah ya baki lafiya Daada... Allah ya baki
lafiya"
Ta furta cikin ranta, addu'a ce da tun da suka
shigo asibitin ta dan samu nutsuwa take ta
furtawa cikin zuciyar ta. Sanin ba bangaren
hannun da ake karawa Daada ruwa bane ya sa
ta lalubo shi tana dumtsawa cikin nata, akwai
Lubna sufyan
Hausabook.com 326
wajaje da dama da ko da wasa ba zata bari
tunani ya dauketa ya kaita ba, cikin su har da
rasa Daada. Shisa ta sauke numfashi mai nauyin
gaske tana sake runtsa idanuwan ta cike da
neman baccin da yake cike da su.
*
Yau kwanaki biyu kenan da sallamar Daada
daga asibiti, ta ji sauki sosai, sai yawan baccin
da takeyi da kuma rashin karfin jiki da ba za'a
rasa wanda ya warke ciwo da shi ba, tunda
lafiya ce kadai abinda yake kwace maka a yan
mintina, amman dawowar ta sai ta dauki
lokacin da baka ma yi tunani ba. Madina ta ji
dadin kasancewar lokacin cikin hutun da suka
samu na tsakanin Waec da Neco. Ko da ace babu
hutu ba zata iya tafiya ko ina tabar Daada ba,
shisa duk nacin ta da makaranta ta hakura da
islamiyya sai ta ga Daada na hidimarta kamar ko
da yaushe.
Da wuri ta gama miyar ta da ta sha naman kaza,
Julde ya zo ya kawo musu cefane jiya. Ya karo
musu kajin da suna da saura a fridge tun
wancen karin, farar shinkafa ta dafa, ta fita da
Lubna sufyan
Hausabook.com 327
kanta tana samun yaro ta aika ya siyo mata
salak da tumatir ta yayyanka, kafin sha biyu
harta gama gyara ko ina tsaf. Ko da ta idar da
sallar azahar ma ta tashi Daada tayi itama, ta
samu ta bata abincin da ta dan ci kadan,
magungunan rana ta bata sannan ta sake
komawa bacci.
Matar da tayi wa alkawarin kunshi tun satin
daya fita ce ta zo, ko da tayi mata ya mai jiki
Madina batayi mamaki ba sam. Ta san matar ta
shiga makota ne ake fada mata, Daada mai
mutane, yanda aka dinga zuwa asibitin dubata
har mamaki ya dinga bawa Madina, wasu ma ita
bata san su ba, duk yawanci basu zo hannu biyu
ba, wata mata da kallo daya zakayi mata ka
fahimci halin rashin da take ciki dan rake ne ta
zo da shi a bakar leda irin wanda ake siyarwa a
datse, yanayin karfin halin ta sai da ya taba
Madina ba kadan ba.
Kirki abune da ba sai mai hali ba, kowa ma zai
iya kamantawa in dai akwai shi a zuciya. Matar
ma da ta zo kunshin harda lemon zaki da ayaba
ta riko
Lubna sufyan
Hausabook.com 328
"Munyi waya da Maman Anisa take fadamun an
sallame ku"
Godiya sosai Madina tayi mata, kunyar matar ta
sata hada lallen tunda baki ne take so, ta zana
mata a bayan hannu da tafuka, basu wani dauki
lokaci ba, yana shan iska tace zata tafi gidan
Maman Anisan ya karasa bushewa acan sai ta
wanke. Yanda duk tayi da Madina kin karbar
kudin kunshin tayi, ko dan alkawarin da tayi ma
matar ta saba mata ba zata karba ba. Haka
sukayi sallama suna ma juna godiyar karamcin
daya gifta tsakanin su, Madina ta tattara kayan
kunshin ta tana nade tabarmar ta koma cikin
daki. Ganin hudu harda minti biyu ya sa ta nufi
dakin ta ta shiga bandaki dan gabatar da
uzurinta ta fito bayan ta dauro alwala. Sanda ta
shiga dakin Daada ta sameta harta tashi tana
sallah.
A gefe ta raba itama tana fara gabatar da tata
sallar, ta idar tana dorawa da azkar din
yammaci kafin ta jero tarin bukatunta
"Ya jikin Daada? Ko kina marmarin cin wani
abin in dafa miki?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 329
Kai Daada ta girgiza mata
"Alhamdulillah, da sauki sosai"
Hannu Madina ta kai tana taba kuncin Daada
"Babu zazzabin fa, na ce miki yayi sauki"
Daada ta fadi da dan murmushi
"Allah ya karo miki lafiya Daada Am... Kinga
wata tazo kunshi ta kawo miki lemo da ayaba da
yawa, yar uwar Maman Anisa ce..."
Kai Daada ta jinjina
"Allah ya saka mata da alkhairi, nagode sosai
kuwa"
Suna da sauran fruits da Julde ya kawo, wannan
dinma duk a fridge ta hada ta samar musu wajen
zama
"Ko in kara kawo miki ruwa?"
Kai Daada ta girgiza, babu wani abu da take
bukata, matsawa kusa da ita Madina tayi yanda
zata iya dora kanta a jikin damtsen hannun
Daadar tana jingina da ita sosai
Lubna sufyan
Hausabook.com 330
"Karasa ni zakiyi daga farfadowa ta?"
Dariya Madina tayi saboda tana jin zolayar da
take cikin muryar Daadar
"Idan na karasa ki in zauna da wa? Hutawa
kawai nake danyi, kwana biyu banji dumin ki
haka ba"
Dan kallon ta Daada tayi
"Kaji karya fa, ina ce ko a asibiti a bayana kike
kwanciya"
Dariya Madina tayi, jiyama a bayan Daadar tayi
bacci, lokutta da dama tafi son jinta makale a
jikin Daada, ta zagaya hannunta a cikinta tana
saka nata hannun cikin na Daada ta hada yatsun
su waje daya. Wasu ranakun ma ko baccin rana
a jikin Daada takeyi. Karar wayarta da ta bari a
falo ya sata raba jikin ta da na Daada, saboda
tasan babu wanda zai kirata in ba Salim ba, har
yanzun babu wanda ya san tana da waya, bata
samu nutsuwar da zata kikkira mutane da ita
ba.
"Hamma..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 331
Ta furta bayan ta daga wayar ta kai kunnen ta
"Ina kofar gida, yunwa nake ji, me kika dafa?"
Murmushi tayi, yana tuna mata da ita ma bata ci
abincin ba
"Ka shigo sai muci, nima banci abinci ba"
Bai amsata ba ya kashe wayar, ta sauke ta daga
kunnenta tana ajiyewa akan kujera, dakin
Daada ta koma
"Hamma ne ya zo..."
Kai kawai Daada ta daga mata batare da tace
komai ba, Madinar ma juyawa tayi, tana shiga
kitchen taji sallamar da Salim yayi, daga kitchen
din ta amsa shi. Tana zubo abincin a plates guda
biyu ta fara kawowa sannan ta hado musu miyar
a kwano daya tana sake kawowa, ta samu wani
waje ta zubo salak din da kayan hadi. Kafin ma
ta dauko ruwa ta dawo Salim harya sakko kasa
yaja na shi plate din ya fara ci, tun safe rabon
cikin shi da wani abu, shima shayine ya sha dan
Saratu na mishi fadan cewa ba inda zai fita bai
saka wani abu a cikin shi ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 332
"Baka zama kaci abinci ko Hamma?"
Madina ta fadi tana kallon yanda idanuwan shi
sukayi zuru-zuru, ya wuce ace yunwar yini daya
ce
"Gashi ina ci yanzun"
Ya amsa, kai kawai ta girgiza, in dai akan abinci
ne Salim din kamar karamin yaro haka yake,
wata rana idan ya zo sai ta zuba mishi ya tafi da
shi, ko ta tsare shi ya ci, sai yace mata aiki ya
mishi yawa, ko yunwar ma baiji ba. Ya rigata
cinye abincin shi, harya koma plate din ta suka
cinye tare
"Ina karo maka?"
Kai ya girgiza mata, ita ce ma ya kamata ta kara,
ya san Madina kamar yanda ta san shi, idan tana
so ta karo ba zata jira ya fada mata ba. Cikin ta
na daya daga cikin abinda bata wasa da shi ko
kadan. Kwanonin ta tattara tana mayarwa
kitchen ta dawo ta zauna, yatsun ta ya bi da
kallo
"Kunshi kikayi ko?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 333
Ya furta yana jan jikin shi kusa da ita ya kamo
hannun ta, bakin da yatsun ukku sukayi har ya
fara ragewa dan zaman asibitin da sukayi
"Wata mata nayi wa dazun..."
Kai kawai ya girgiza
"Kina bata hannun ki, na ce ki dinga saka safar
hannu"
Dakuna fuska tayi
"Ni wani iri fa, bayamun dadi shisa"
Jujjuya hannun nata yakeyi cikin na shi
"Jibu farcen ki"
Dayan hannun ya dago tana dubawa, shima duk
ya taru
"Daada ce take yanke mun, ban iya ba da reza"
Kai kawai Salim ya girgiza yana mikewa. Yana
jinta tana binshi da idanuwa, baifi mintina hudu
ba ya dawo yana zama in da ya tashi. Hannun ta
na dama ya kamo
"Waye yace da reza zaki yanke?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 334
Karamin yatsanta ya fara kamawa sannan ta
kula da nail cutter din da yake rike da shi.
Tunda yake mutum
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 18