kirjin shi ba.
"Madina ce, Madina... Madina ce"
Lubna sufyan
Hausabook.com 193
Shine abinda yake fadi cikin kanshi, ko bai duba
komai ba zai duba karancin shekarun ta. Gudun
motar ya kara ko zasu karasa da wuri
"Hamma gudu kakeyi yau, sosai"
Ta furta muryarta na dan rawa saboda bata son
gudu a abin hawa ko kadan, hankalinta tashi
yakeyi, yanayin yanda sautin muryarta ya fito
yasa shi rage gudun motar, badon tsoron ta ba
sai dan nutsuwar shi da take neman rabuwa da
jikin shi. Bai taba jin dadin hango kwanar gidan
Daada irin yau ba, hannuwan shi har rawa
sukeyi da ya sauke ta kofar gidan, tsaye yayi ta
bude bayan motar ta dauki kayanta, sai da safen
da tayi mishi ma da kai ya amsa mata ita. Sai da
yaga shigar ta gida tukunna ya ja motar yayi
kwana yana hawan titi da wani irin yanayi da
bashi da kalaman da zai fassara shi.
"Gashi nan Daada, ya fadi me yake ce mun a
gabanki kiji, watakila ke kina da kalaman da
zaki fada mishi ya fahimci wannan bashi bane
lokacin da ya dace..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 194
Julde ya karasa maganar yana kallon Nawfal da
yake zaune cikin kujerar da take kallon tashi da
yanayin babu abinda zai canza ra'ayina kwance
cikin idanuwan shi. Taurin kai ba bakon abu
bane ba, asalima in za'a koma wasu shekaru
baya, tabbas da yawan mutane zasu iya cewa ko
kafar shi Nawfal bai kama a taurin kai ba, in
harya saka ma ranshi yin abu to babu wanda ya
isa ya sauya mishi ra'ayi
"Idan kuskure ne kubarni, kuskure na ne, ni
zanyi dana sani akan duk abinda zai biyo baya.
Kunyi naku bangaren, kun fada mun gaskiya
nine dai ban dauka ba"
Yakan fada duk idan an nemi hana shi abinda
yayi niyya, shima din idan yana dan ganin kanka
da gashi. Sai dai yau a karo na farko baya son
ace taurin kai a ahalin sune, kar ace wannan
ra'ayin rikau din jini yake bi. Saboda Nawfal ya
dauko mishi abinda bai taba hangowa ba ko a
tunani balle kuma yasan yanda zai shiryama
daukar shi
"Aure nake sonyi Daddy, ina so a daura kafin in
koma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 195
Kalaman Nawfal din suka dake shi kamar wanda
babbar mota tayi sama da shi tana sauke shi da
wani irin yanayi da bayajin akwai kalaman da
zasu kwatanta shi. Kallon Nawfal yayi yana so
yaga ko zolayar shi yake, sai yaga wani yanayi
shimfide cikin idanuwan Nawfal din kafin ya
dora zancen shi da
"Tun a waya zan fada maka, sai na bari tunda
zan zo bikin Adee, da na zo din ma ina neman ta
inda zan fara fada maka ne..."
Yar dariya ce da Julde ba zaice ga ta inda ta fito
ba ta kubce mishi, sosai yake kallon Nawfal
"Shaye-shaye ka fara Bajjo?"
Idanuwan shi Nawfal ya saka cikin na Julde yana
fadin
"Daddy..."
Wani numfashi Julde yaja yana saukewa, kwatakwata ya rasa inda zai ajiye kalaman Nawfal
balle yayi tunani akan su harya sami kalaman
furtawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 196
"Daddy karka ce inje inyi tunani, kar kace in
sake dubawa, ko kace shekaru na sunyi
karanci..."
Cewar Nawfal din shima yana fitar da numfashi
kafin ya dora da
"Watakila duk hakane, amman ina son ta, ko
yanzun, ko nan da wasu shekaru babu abinda
zai canza, me yasa zamu jira wasu shekaru in
muna da wannan tabbacin?"
Kallon shi kawai Julde yake, cikin tashin hankali
yace
"Baka da hankali ko Bajjo? Aure? Kasan meye
aure? Yaushe ka fara karatun? Duka nawa kake
da zaka rungumo maganar aure? Da me zaka
rike ta? A ina zaka ajiye ta? Ko soyayyar ce ta
hana kai da ita yin wannan tunanin?"
Kai Nawfal yake girgiza mishi, ya bude baki zaiyi
bayani Julde ya katse shi
"Waye zai dauki yarinya ya baka? Kana fadamun
kafin ka koma kake son a daura aure? Sati biyu
kace zakayi, yau kwanan ka shidda, a cikin
sauran kwanakin za'ayi maganar aure har a
Lubna sufyan
Hausabook.com 197
daura... Kaga Bajjo baka taba batamun rai ba kar
yau ya zama na farko"
Julde ya karasa maganar yana ma Nawfal din
wani irin kallo mai cike da tarin ma'anoni.
Saboda tun tasowar Nawfal yana da manyance,
yaune rana ta farko daya fara ganin haukan
yaron, rashin hankali na sa'annin shi da
kuruciya duk Nawfal baiyi ba, duk da a baya
yana danganta hakan da rashin iyayen shi a
kusa, duk da yana iya kokarin ganin ya bashi
duk wata kulawa da zai bukata gwargwadon
yanda lokaci ya ara musu
"Zasu bani, sunce zasu bani, kawai zaka ga
Kawunta da yake Abuja ne, saboda suna son
sanin ina da dangi a Nigeria, ba wani abu za'a
kai ba banda sadaki..."
Kallon da Julde yayi mishi wannan karin na
kashedi ne
"Bajjo.."
Haka ma yanda ya kira sunan shi da bai hana shi
cigaba da magana ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 198
"Ina aiki, kudin bamai yawa bane ba, saboda
yanayin karatu ba wasu awanni nakeyi ba,
itama kuma tanayi, duka karatu muke, zamu
gina kalar rayuwar da muke so a tare... Daddy
kar kace banda hankali, karka ja layi akan
abinda addini bai haramta mun ba"
Mikewa Julde yayi
"Daddy..."
Nawfal ya kira muryar shi na karyewa
"Ka taso muje"
Yanda yayi maganar ne yasa Nawfal din bai
mishi musu ba ya bi bayan shi, babu wanda yake
magana a motar har suka karasa gidan Daada,
ko da ma suka shiga banda sallama babu abinda
Nawfal ya kara cewa ya nemi kujera mai zaman
mutum daya ya zauna. Yana kallon yanda Julde
ya amsa tambayar
"Julde, lafiya dai ko?"
Da Daada tayi mishi, da kuma yanda ta kalle shi
bayan Julde ya gama magana.
Lubna sufyan
Hausabook.com 199
"Idan kaga ban aure ka ba, matsalar daga
bangaren ka ne. Zasu tambayeni idan ina son ka,
idan aure ne abinda nake sonyi a yanzun, zasu
bani shawara bayan jin amsata, daga karshe
zabi na zasuyi amfani da shi. Haka rayuwar
ahalina take, shekaru na sha takwas, sun yarda
ina da 'yan cin da hankalin sanin me ya dace da
ni"
Maganganun Murjanatu suka dawo mishi, da
gaske matsalar daga bangaren shi ne, shakkun
da yake cikin idanuwan Julde kawai ya isa ya
tabbatar mishi da haka, bai kuma son kalmomin
da zaiyi amfani da su wajen gamsar da shi ba.
Bayan tsayawa da kafafuwan shi, aure ne abu na
biyu a cikin jerin abubuwan da yake son yi,
saboda yana son samun nashi ahalin, wanda duk
ruwa duk rana yasan zasu kasance da shi. Ta ina
zai fara fadawa Juldea da Daada cewa babban
tsoron shi a duniya shine kadaici. Shine ranar da
duk zai neme su a duniyar shi ya rasa?
Yanda duk yake son ace ya kira su da nashi shi
kadai kaunar su rabata yake da sauran mutane,
yana son abinda zai kira na shi, yana bukatar a
kaunace shi, kaunar da ba zaiji tsoron rabata da
Lubna sufyan
Hausabook.com 200
kowa ba balle har azo a ture shi daga dan inda
yake a tsugunne.
"Idan na tambayeka me ka dawo yi zakace mun
bikin Adee, kana da naci Nawfal, bana kaunar
ganin ka kusa da ahalina, in zan iya rabasu da
kai ba karamin dadi zanji ba, amman ba zan
taba daina kokarin hakan ba..."
Maganganun Saratu ne suka kara mishi karfin
gwiwar tunkarar Julde da tun bayan bikin Adee
yake juyayin yanda zai same shi. Yanda duk
yake kaunar su yana da tabbacin soyayyar da
take tsakanin su da Saratu ta girmi wannan,
kauna ce da ba zai kwatanta dorata a sikeli da
tashi ba sam
"Aure zanyi Daada..."
Yayi maganar muryar shi na fitowa da wani irin
sanyi yana sa Daada jin kamar ya juye mata
bokitin ruwan kankara kafin wani irin zafi ya
maye gurbin sanyin da ya ratsa ta, jikinta gabaki
daya ya dauki dumi, zuciyarta na soma wani irin
tsalle-tsalle kamar tana neman sabon wajen
zama a sauran jikinta, yanayin bugawar da take
Lubna sufyan
Hausabook.com 201
har cikin idanuwanta da take kallon Nawfal da
su take jin karfin shi
"Kema kina tunanin banda hankalin ko Daada?
Wannan ba shi bane lokacin daya kamata in zo
da maganar aure ba..."
Nawfal ya fadi yana dora da
"Dan Allah idan kina da dalili ya sha bamban
dana Daddy..."
Kallon shi dai takeyi zuciyarta na cigaba da
dokawa kamar zata fito waje, dalilinta ko daya
bashida alaka da duka tunanin su, dalilinta bata
san ta inda zata fara furta shi ba
"Kina jin shi ko Daada, kice wani abu"
Julde ya fadi yana kallonta, da idanuwan shi
yake rokonta da ta taimaka mishi don yanayin
Nawfal din kawai ya tabbatar mishi da cewa
bawai ya fada mishi bane saboda yana neman
izini, goyon baya yake so kawai, amman ko bai
amince ba da wahala idan maganar auren nan
ba zata zama abu na farko da zai haddasa wata
tsaga a alakar su ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 202
"Yarinyar yar ina ce?"
Daada ta tambaya tana saka Nawfal sauke wani
numfashi da baisan yana rike da shi ba
"Murjanatu... Sunan ta Murjanatu, duka iyayenta
suna zaune ne acan kasar da nake karatu,
amman asalin su yan garin Adamawa ne, dangin
su da yawa suna can, wasu suna zaune a Abuja,
suma aikine ya kai babanta can, yayyen ta guda
biyu duk suna nan Abuja suma...ni ba zama
zanyi acan ba Daada, zan dawo, zamu dawo tare
idan muka gama karatun mu"
Ya karasa maganar yana kallon Julde da har
lokacin akwai shakku cikin idanuwan shi
"Daada kiyi magana da yaron nan, da gaske fa
yakeyi..."
Baki Daada ta bude sallamar Madina ta katse
mata maganar ta, Nawfal ne ya amsa
"Hamma... Daddy"
Cewar Madina cikin sigar gaisuwa
"Zafi nake ji wallahi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 203
Ta furta tana wucewa nufar hanyar dakinta, sai
lokacin suka ga Salim da yayi sallama cikin
budaddiyar muryar shi, daga makaranta ya
wuce yaje ya dauko Madina saboda tunaninta ya
hana shi sukuni har a aji, motar shi ta fara
tsaitsayawa, dakyar ya iya samun waje gefen titi
yayi parking dinta ya kira mai mishi gyara. Sai
da yazo ya bashi mukullin tukunna suka tako
shi da Madina tunda sun kusa gida, tun a hanya
take ce mishi zafi take ji tana shiga gida zata
fara watsa ruwa kafin tayi shirin islamiyya.
Motar Daddy daya gani ne a wannan lokacin a
gidan Daada yasa shi yanken hukuncin shiga
dan yaga ko lafiya, in yaso sai su wuce da Daddy
ko bai mayar da shi makaranta ba ya rage mishi
hanya.
Kallon su yayi yana zare takalman shi hadi da
shiga cikin dakin, yanayin su bai nuna kome
suke tattaunawa mai dadi bane ba
"Ina wuni"
Ya furta kamar wanda akayiwa dole yana kallon
Daada
"Daddy..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 204
Ya kira, duk yanayin da Nawfal yake ciki bai
hana shi kallon Salim ba, daga shi har Madina
suna son kiran sunan mutum a maimakon
gaisuwa. Sai dai kafin Daddy yayi magana Salim
din ya juya, baya son hayaniya. Yana da tabbacin
kome suke tattaunawa bai shafe shi ba, baya son
sani balle kuma suyi tunanin saka shi ciki.
"Ina zaka je?"
Julde ya tambaya, dan juyawa Salim yayi yana
amsawa da
"Naga kuna magana ne..."
Kamar hakan kawai hujja ce da zai bar musu
gidan
"Ka dawo ka zauna ayi maganar da kai"
Dan runtsa idanuwan shi yayi yana bude su,
dole dai sai sun tsoma shi cikin zancen nan da ya
san bai shafe shi ba ko kadan. A nutse ya taka
yana samun hannun kujera ya zauna a kai
"Aure Nawfal yake son yi, so yake a daura kafin
ya koma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 205
Kallon Nawfal din Salim yayi, sai dai a nashi
idanuwan babu komai sai mamaki, saboda aure
baya cikin tsarin abubuwan da yake hango
rayuwar shi da shi, hayaniyar nan ba zai iya ba.
Amman hakan baya nufin dan wani yana so yayi
sai ace kar yayi. Adee ma gashi nan tayi, kuma
har ran shi yayi farin ciki da auren nata
"Kana ganin auren ne abinda kake son yi a
wannan matakin na rayuwar ka?"
Salim ya tambaya, kai Nawfal ya jinjina mishi
"Karka amsa ni idan kana da shakku, ka
tabbata?"
Kai Nawfal ya sake dagawa, girar da Salim ya
daga mishi yasa shi cewa
"Ban fada ma Daddy ba sai da na tabbata,
shekara daya ina neman tabbaci a kowacce
rana..."
Mikewa Salim yayi ya kalli Daddy
"Nanna tace sanda kukayi aure da kadan ka
girmi Bajjo, karkayi amfani da shekarun shi a
Lubna sufyan
Hausabook.com 206
matsayin hujja Daddy, in baka da dalili mai karfi
karku hana shi..."
Numfasawa yayi saboda kan shi harya fara
sarawa da maganar da yake yi
"Ku barshi yayi auren shi..."
Wanda duk yazo da maganar aure a cikin
kannan nashi zasu samu dukkan goyon bayan
shi, zaiyi duk wani abu da zai iya wajen ganin
basu fada irin rayuwar da yake ciki ba
"Aure zai hanaka biye-biye, zai nutsar da kai
waje daya"
Haka yaji wani a ajin su ya fada. Yana da yakinin
Nawfal na da dalili mai karfi da yasa yake sonyin
aure a wannan matakin na rayuwar shi, kasar
yabari don karatu, Allah kadai yasan kalar
mutanen da suke zagaye da rayuwar shi
"Ka tabbata bakayi dana sanin zabin nan ba
Bajjo"
Ya fadi yana saka Nawfal din yin murmushi
"Hamma..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 207
Hannu ya daga mishi, shi duk irin wannan
abubuwan baya son su
"I love you"
Nawfal ya fadi yana fadada murmushin shi ganin
yanda Salim din ya bata fuska yana taku biyu da
nufin karasawa kan kujerar da Nawfal yake
yana saka shi mikewa babu shiri, kallon shi
Salim yayi cike da kashedi yana ficewa juyawa
ya fice daga dakin.
Kamar bai fadu maganganun da zasu canza
komai ba
Maganganun da zasu zama silar faruwar komai
Kwallar da Daada taji ta fara tarar mata cikin
idanuwa tayi saurin saka hannuwa ta dauke su
kafin ma wani ya kula. Shikenan abinda ta gina a
cikin zuciyarta ya rushe, hangenta ya datse
lokaci daya. Wata ta maye wajen da take fatan
Madina ce zata zauna a wajen. Yanda kaddara
take wasan kura da rayuwar su a kowanne juye
na karya mata zuciya. Ba dan kar tayi sabo ba da
ta tambayi dalilin da yasa ko sau daya rayuwa
ba zata tafi kan tsarinta ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 208
"Hamma ma yace karku ce a'a, kaji Daddy, dan
Allah karka ce a'a..."
Nawfal ya katse ma Daada tunanin da take yana
sata kallon Julde da fuskar shi take dauke da
yanayin rasa tudun dafawa
"Daada..."
Ya soma ta girgiza mishi kai
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, kaje kaga
dangin yarinyar kafin ka yanke wani hukunci..."
Murmushin da Nawfal yayi bayan ya dawo inda
yake ya zauna na saka zuciyar Daada kara
tsinkewa saboda kamannin shi da Bukar da
suka kara fitowa fili. Kafin wani ya sake cewa
wani abu Madina da ta fito cikin shigar
islamiyya ta riga su da fadin
"Hamma kana nan har in dawo amman ko?"
Kai Nawfal ya girgiza mata
"Zamu dan fita da Hamma anjima, kilan in dawo
dai, me zaki ajiye mun?"
Dariya tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 209
"Zan dafa maka kifi"
Kai Nawfal ya jinjina
"Zan dawo"
Dunkule hannunta tayi tana daga mishi babban
dan yatsan ta alamar hakan yayi mata
"Daddy na tafi...Daada sai na dawo"
Binta da kallo Daada tayi, Julde ne ma ya iya
cewa
"A dawo lafiya"
Wani abune Daada taji yayi mata tsaye a
kirjinta, lokaci daya duk wani tunani da takeyi
akan goben Madina ya sauya. Ta ina zata fara
yanzun?
"Daada yanzun duka Nawfal nawa yake?"
Julde yace cikin nauyin murya, ko shi da Salim
yake magana akan auren wuri da yayi, bawai
zabi aka bashi ba a lokacin, kawai hadasu akayi
da Saratu
"Zamanin mu da nasu ba daya bane ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 210
Murmushi Daada tayi kirjinta yayi mata nauyi,
hakan yasa Nawfal mikewa yana nufar dakin
daya kan kwana ciki duk idan yazo gidan dan ya
basu damar yin magana
"Shisa zaka barshi yayi auren shi, zamanin ba
daya bane ba...kar kaja maganar nan da shi
Julde...ka kyale shi tunda ba wani abu marar
kyau bane ya dauko"
Wani irin numfashi Julde ya sauke, ranshi a
jagule yake jin shi, a saman bukatar ta da
fatanta kasancewar Bajjo a cikin su yafi
muhimmanci, hana shi aure don bukatar ranta
ta cika ba zai zama sanadin da zata rasa shi
gabaki daya ba. Idan har jinin Datti ne yake
yawo a jikin Nawfal to tasan wannan maganar
auren ba izinin su yake nema ba, goyon bayan su
kawai yake bukata, ko sun yarda ko basu yarda
ba bazai canza komai ba.
"Karka ja maganar nan da shi..."
Ta kara jaddadawa, yanayin muryarta nasa
wani abu tsirgama Julde saboda yasan inda
tunaninta yake son kaita
Lubna sufyan
Hausabook.com 211
"Ai shikenan..."
Ya furta yana sauke ajiyar zuciya
"Amman ba zai zauna kasar nan ba, yana gama
makarantar nan dawowa zaiyi"
Dan murmushin karfin hali Daada tayi
"Daman yace ba zama zaiyi ba"
Sai dai ita kanta ta maimaita kalaman ne ba dan
ta aminta da su gabaki daya ba
"Zan dawo Daada"
Taji wannan kalaman har sun isheta a tsayin
rayuwar ta, sai dai a duk mutanen da suka furta
mata su Nawfal ne na farko daya fara cikawa,
shakkun da take da shi kan kalaman ya dade da
kafa rassa a cikin zuciyarta, dan ya dawo yanzun
baya nufin in ya koma zai sake dawowa, wannan
ma tagan shi akan Yelwa. Da zatayi fata ne, fatan
kar ya zamana Nawfal bai cika alkawarin shi na
zai dawo ba. Sai dai numfashi kawai ta sauke.
Kowanne rai da nashi kaddarar, yau ma ta sake
ganin wannan kaddarar da take tunanin ta shiga
tsakanin Nawfal da Madina kamar yanda tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 212
fata, shisa ba zata sake wani fatan ba a yanzun,
idan kaddarar Nawfal ta hada da dawowa zai
dawo, idan bata hada ba sai dai ta sake
rungumar kaddara a duk yanda tazo mata a
karo na ba adadi kenan. Fatanta bashi da tasirin
canza komai.
**
Wayar shi Nawfal ya mika mishi, karba Khalid
din yayi
"Na fara gajiya fa...ni bana ma amfani da wayata
yanda nake so saboda kun isheni kai da ita...ka
siyi layi Malan"
Dariya Nawfal yayi
"Kai Hamma, yaushe muke isarka din? In ba irin
wannan lokacin ba ai bama waya... Layin zai
zama asara tunda ba dadewa zanyi ba. Haka
zakayi ta hakuri da mu"
Kai kawai Khalid yake girgiza, ya kalli inda ya
ajiye kayan wankin da aka kawo mishi da
yamma
Lubna sufyan
Hausabook.com 213
"Na kwashe na shirya maka duka wardrobe
dinne ma"
Kallon shi Khalid yayi, yana sake kallon yanda
dakin ya samu kulawa ta daban tun zuwan
Nawfal din, bawai shara bace bayayi, yana share
dakin kusan kullum, kawai dai bashida lokacin
mayar da wasu abubuwan wajen daya dauke su.
Nawfal kuma ya kasance cikin jerin mutanen da
suke son ganin komai a tsare, har litattafan shi
idan ka duba jakar shi ta makaranta a wani irin
tsare suke, bi da bi. Inda yake ajiye fensiran shi
da biro ma daban ne. Ko yaya ka taba mishi kaya
yana dawowa wajen zai nufa ya gyara abin shi
yanda yake son ganin shi.
Wajen wardrobe din Khalid ya karasa ya bude
yana ganin yanda Nawfal ya shirya komai, harta
kananun wandunan shi layi daban ya saka su.
Sai yaji kamar ace karya taba kayan, ya hargitsa
shirin nan
"Aure zanyi Hamma"
Nawfal ya fada cikin sanyin murya, wardrobe
din Khalid ya rufe
Lubna sufyan
Hausabook.com 214
"Na sani, kowa ma ai aure zaiyi idan lokaci yayi,
ko dan kayi budurwa sai ba zamu huta ba?"
Kallon shi Nawfal yayi
"Aure zanyi Hamma..."
Ya sake maimaitawa yana sa Khalid kallon shi
"Ina nufin kafin in koma za'a daura, aure zanyi
kafin in koma"
Sosai Khalid yake kallon shi wannan karin
"Nasan ya kamata in fada maka tunda na dawo,
amman nabari ne in fadama Daddy tukunna, shi
ya kamata ya fara sani kafin kowa"
Kai Khalid ya jinjina
"Allah ya sa alkhairi"
Ya furta yana rasa abinda yayi niyyar yi kafin
Nawfal din ya sauke mishi wannan zancen
saman kai
"Hamma..."
Nawfal ya kira, amman hankalin Khalid din yaki
komawa kan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 215
"Hamma mana..."
Waje Khalid ya samu gefen gadon ya zauna yana
daukar wasu dakika kafin ya daga kai ya kalli
Nawfal
"Me yasa? Ka fahimtar dani yanda zangane"
Saboda har a ranshi yana son gane dalilin da
zaisa Nawfal yanke wannan babban hukuncin da
yake ganin baiyi hankalin da zaiyi shi ba, duk da
tsiran da yake tsakanin su bawani mai yawa
bane ba. Yayi girman da yasan duk inda za'ayi
magana ta aure ba karamin abu bane ba.
"Ni kadai ne Hamma, tun banda hankalin
mutanen daya kamata su tsaya tare dani suka
fara watsar dani, ina da ku na sani, ina jin kamar
bai kamata ba da nace maka ni kadai ne..."
Kallon shin dai Khalid yakeyi
"Ina kaunar ku, ina kaunar ku fiye da yanda zan
fada, nasan kuna kaunata, da yawa, ba zan kira
ku nawa ni kadai ba, ba zan kiraka nawa ni
kadai ba, ina rabaka da mutane da yawa a
yanzun, lokaci zaizo da zan sake rabaka da
wata... Ina son abinda zan kira nawa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 216
Wani sauti ne ya kwace ma Khalid din da yake
tsakanin dariya da wani yanayi da bashi da suna
"Ita din ba zaka rabata da wani ba?"
Ya tambaya yana jin wani abu ya tokare mishi
makoshi
"Ba kaman ku ba..."
Kokarin hadiye abin da yake a makoshin shi
Khalid yakeyi, maganganun Nawfal sun mishi
zafin da ya kasa fahimtar su
"Tana da iyaye da yan uwan da ta taso da kaunar
su kafin taka, ka fadamun bambancin da yake
tsakanin ta da mu... Kana so ka fadamun mu ba
zamu taba zama naka kai kadai ba, amman ita
zata iya zama? Mu muna da wani lokaci na barin
rayuwar ka... Ko dan kaine kasa lokacin barin
mu saboda ka samu wadda zaka kira taka?"
Tunda ya fara magana Nawfal yake girgiza mishi
kai
"Idan baka fahimce ni ba babu wanda zai
fahimce ni Hamma, dan Allah karka fassara
Lubna sufyan
Hausabook.com 217
kalamai na idan baka fahimta ba, karkayi mun
haka"
Nawfal ya karasa muryar shi na karyewa
"Ka fahimtar dani Bajjo..."
Numfashi Nawfal ya sauke zuciyar shi na rawa
"Idan baka so zan hakura, zan bar maganar
nan... "
Dan tunda ya yanke hukunci bai dauka akwai
wani dalili da wani zai bashi ya sauya mishi
ra'ayi ba. Yasan Khalid na da muhimmanci a
wajen shi, bai taba tsayawa ya auna girman
muhimmancin ba sai yanzun, da a karo na farko
tun haduwar shi da Murjanatu yaji zai iya
barinta idan har zata zama silar samun matsala
tsakanin shi da Khalid din
"Babu wani abu a yar duniyar nan tawa da yake
da muhimmancin alakar da take tsakanin mu"
Cewar Nawfal yana saka Khalid jin kafafuwan
shi sunyi sanyin da in ba'a zaune yake ba zasu
kasa daukar shi, yaja iska ta bakin shi yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 218
fitarwa yafi a kirga kafin ya samu natsuwar
fadin
"Ka kalleni Bajjo, lokaci daya nake da shi na
barin rayuwar ka, lokacin da ba rayuwar ka
bace kawai abinda zan bari, duniyar ce gabaki
daya...ba kai kadai bane ba, duk tunanin da yake
fada maka haka ka karya tashi, idan kana jin
baka da kowa kana da ni, kana jina ko?"
Kai kawai Nawfal ya iya daga mishi
"Idan aure ne zabin da kayi ni banda matsala da
hakan, kawai ina so kasan ba abu bane da zaka
zaba yanzun ka canza anjima, rayuwar yarinyar
mutane ce akan layi Nawfal"
Khalid ya karasa da kiran asalin sunan shi dan
ya san maganar da yake na da muhimmanci
"Bana jin zan iya ba mai shekarun ka 'ya ta
Bajjo, ba kuma zan daina ganin wautar mutumin
nan ba...kadaici kowa yakan ji shi lokaci zuwa
lokaci, karya zama dalilin da kawai zaka aure ta,
ka hanga shekaru masu zuwa, a cikin shekarun
ka duba hali na rashin tabbas, hali na rashin
lafiya, ka duba yiwuwar jin dadi da rashin shi,
Lubna sufyan
Hausabook.com 219
kana ganin kanka a tare da ita a duka
yanayoyin?"
Numfashi Nawfal ya sauke, kalaman Khalid din
na ratsa zuciyar shi
"Idan ka shiga cikin auren ba zaka iya fita da
saurin da ka shige shi ba... Ba zaka iya ba...Bajjo
wasan nan ba da rayuwarka kawai zakayi shi ba
harda ta Murjanatu da duka ahalinta... Karka
fara abinda ba zaka iya karasawa ba..."
Cikin idanuwa Nawfal ya kalli Khalid din
"Ina son ta"
Ya amsa
"Soyayya kawai tayi kadan"
Idan Nawfal bai sani ba, shiya sani, wasu zasu
karyata ana ganin soyayya kwance a idanuwan
mutane, idan baiga soyayyar Julde a idanuwan
Saratu ba shima zai iya karyatawa, amman bata
hana su samun matsalar da suke tunanin baya
kula ba, suna fada ko da baisan me yake hada su
ba, sosai suke yawan yin fada yana kula da
Lubna sufyan
Hausabook.com 220
hakan. Da soyayya ta isa da wadda Nannar shi
take ma Daddy ta hana musu samun matsala
"Bansan sauran abubuwan ba Hamma, amman
zamu neme su a tare, shine kawai alkawarin da
zan iya a yanzun..."
Kai Khalid ya jinjina
"Aure zakayi Bajjo, aure zakayi"
Khalid yake fadi wata dariyar mamaki da tsoron
wannan babban matakin da rayuwa ta kawo dan
uwan shi na kwace mishi, shima dariya Nawfal
yayi, tsoron da yake gani a fuskar Khalid din na
taba shi, a karo na farko shima matakin na bashi
tsoro, sai dai tare da tsoron babu shakku ko
kadan
Rai da kaddara
Murjanatu na daya daga cikin kaddarorin shi
Tana daya daga cikin hasken da zai yaye wani
bangare na duhun da yake bibiyar rayuwar shi
yana jiran cikar lokaci.
Lubna sufyan
Hausabook.com 221
Shiru bai taba mishi yawa ba, lokutta da yawa
ma yana jin yayi mishi kadan, ko shi kadai ne
zaune a bangaren su cikin gida, sai ya dinga jin
hayaniya a cikin shirun dakin, karar agogo,
fanka ko AC din cikin dakin, ko wani kwaro da
ba zaice ga inda yake ba, hakan kawai na hana
shi sukuni, shisa ya siyi abin toshe kunne, yana
da su wajen kala hudu, su kansu basa taimaka
mishi, idan yasa duk kananun hayaniyar sai ta
daina isa cikin kunnuwan shi, sai kuma ya dinga
jin surutun da yake wanzuwa tsakanin
kwakwalwar shi da zuciyar shi.
Yana rasa a cikin mutane shi din wanne iri ne?
Ya kanyi tunanin ko irin shi guda nawa ne, ko ya
suke ji da hayaniyar da take cikin yau da
kullum? Musamman idan ya hasaso kasancewar
su cikin halin rashi, babu wadatar da zasu samu
wajen kebewa su kadai. Amman yau shirun da
yake cikin motar yayi mishi yawa, ba dan
gilasan suna kulle ba, idan shi kadaine zai dinga
jin karar sauran motoci harda ma kukan tashi
motar. Sai dai duk lokacin da zai zamana shi da
Madina ne a zaune cikin mota, ko kuma tana
gefen shi baya jin kowacce irin hayaniya.
Lubna sufyan
Hausabook.com 222
Asalima banda muryarta da dariyarta babu
wani abu da yake isowa kunnen shi, ko bata
magana kamar ganinta na saka komai yin shiru
ne. Sai dai yau shirun nata yayi mishi yawa,
tunda ta fito ta gaishe da shi ta koma cikin mota
ta kwanta kamar marar lafiya, har suka fita daga
layin suka hau titi ko motsi baiga tayi ba, lokaci
zuwa lokaci yana kallonta. Matsalar bai iya hira
ba, bai taba fara hira da wani ba, ko a cikin yan
gidan su kuwa, banda gaisuwa sai dai in kaine
ka tambaye shi wani abin, ya rasa me ya kamata
yace mata.
"Lokacin damuna ne ake noma tumatiri ko?"
Tambayar ta kubce mishi tana saka Madina juyo
da kanta tana kallon shi na wasu dakika cike da
mamaki, shima dan raba idon shi yayi daga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 18