da wani yanayi a
shimfide da ita kadai zata iya fassara shi. Ko
takalma bai cire ba ya karasa cikin dakin, itama
mikewa tayi yana samunta a tsaye, batare da
tunanin komai ba ya zagaya hannuwan shi yana
riketa a jikin shi
"Ina kaunar ki Daada, ban taba fada miki ba ko?
Yau dai na fada, nayi kewar ki da yawa... Ba
kadan ba fa, da yawa sosai har bansan ya zanyi
in fada ba"
Dariya tayi, hawayenta na samun damar
zubowa, yayi girma saboda ba zaka kirata gajera
kai tsaye ba, amman kanta da kadan ya karasa
kirjin Nawfal din, sake riketa yayi kamar zai
cike gurbin kewarta da yayi na shekaru biyu
"Kashin tsufa Bajjo, karka karyani"
Dariya sukayi a tare yana sakinta dakyar, dan
har lokacin wata irin kewarta yakeyi kamar
bata tsaye a gaban shi
"Ina Madina?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 165
Ya tambaya yana kallon cikin dakin da bai canza
mishi ba sam
"Tana dakin ta da littafi, in dai da littafi a
hannun ta bata ji bata gani"
Dariya ya sake yi yana zame jakar shi daga
kafada ya ajiye akan kujera, sai lokacin kuma ya
kula da takalman da suke kafar shi, dan murza
goshin shi yayi, yana rankwafawa ya zare
takalman ya dauke su ya mayar bakin kofa, da
hannu ya nuna inda yake tunanin dakin Madina
ne cikin alamar neman tabbaci, kai Daada ta
daga mishi, kai tsaye ya nufi bakin kofar yana
kwankwasawa, jin shiru ya saka shi sake
Kwankwasawa da karfin wannan karin, yanda
ya kasa kunnen shi yasa shi jin takun tafiyar ta,
shekaru biyu kamar wasa.
Zuciyar shi bata doka ba sai da yaga ta murza
kofar alamun budewa zatayi, idan yace yanayin
da yake ciki yana da fassara zaiyi karya.
Numfashin shi ne ya dan tsaya na dakika kafin
yaja iskar da itama baiji inda ta tafi ba bayan
Madina ta bude kofar, wandone a jikinta ta
nannade shi har kusan gwiwarta, sai rigar sanyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 166
marar nauyi, mai hade da hula da ake kira da
hoodie a turance, dogon hannu ne shima ta ja
shi kadan, hular nada zaren da ta kama ta kulle
shi dan hular ta zauna mata a kai sosai, sai
gilashin ta da ya rufe rabin fuskarta.
Ko ya hasaso yanda Madina ta koma a shekaru
biyu rak yanzun daya ganta tsaye a gaban shi
komai ya goge, su duka kallon juna suke, ita
tana mamakin yanda akayi ta gan shi a kofar
dakinta, karatu take na wani littafin kimiyya da
Salim ya siyo mata, da highlighter a hannunta
tana shaida a duk wajajen da take da tarin
tambayoyin da idan yazo zata tsare shi ya amsa
mata taji an kwankwasa dakin, zaton ta Daada
ce zata tambayeta wani abin da ta ajiye ta rasa
inda ta kai shi. A nisantaccen mafarki bata
hango kasancewar Nawfal cikin gidan ba, shisa
ganin shi ya zama kamar an kwada mata
guduma a tsakiyar fuska.
"Madina"
Ya kira, muryar shi na dira cikin kunnuwan ta,
tana nan yanda take, muryar shi, sam bata canza
Lubna sufyan
Hausabook.com 167
ba duk da ta dade bata jita ba, shi dinma banda
tsayi bata jin ya canza
"Madina..."
Ya sake kira ganin kamar ta kasa yarda shi
dinne a tsaye, dariya yayi mai sauti yana kai
hannun shi ya taba goshin ta da tayi kokarin
karewa tana murmushi
"Kin canza"
Ya furta saboda ya kasa rikewa a cikin shi, ta
canza ba kadan ba, wani irin canji da bai taba
tunani ba
"Hamma... Da gaske kaine?"
Tace tana kasa daina murmushi, kai Nawfal ya
daga mata shima ya kasa daina murmushi, ganin
yana kara takowa cikin kokarin hade space din
da yake tsakanin su yasa ta daga hannun ta tana
matsawa, kai take girgiza mishi, duka alamu sun
nuna rungumarta yake sonyi, shi din dan
uwanta ne, duk da na rana daya Daada bata taba
mata bayanin dangantar da take tsakanin su ba.
Ta san shi din baya cikin jerin mazan da suka
halarta su rungumeta, tana zuwa islamiyya, tana
Lubna sufyan
Hausabook.com 168
kuma iya kokarin ta na ganin bata tsallake wasu
layuka da zasu iya wasa da lahirarta ba.
Babban abinda take tsoro bai wuce kwanciyar
kabari ba, lahira na ba Madina tsoro fiye da
zaton mai zato, ko mutuwa taji anyi duk yinin
ranar bata da sukuni, musamman idan a cikin
unguwar sune, sai ta kasa cire tunanin yanda
mala'ikan mutuwa ya kasance unguwa daya da
ita, amman ba wajenta yazo ba, tuni dai yayi
mata na zuwan shi babu sanarwa.
"Madina..."
Nawfal ya kira wannan karin yana jan sunan
nata, dariya tayi, mamaki yake ba kadan ba, har
tayi girma haka, girman da take kokarin jan layi
a tsakanin su. Hango ranar daya bar kasar
yakeyi, yanda dakyar ya bambare Madina daga
jikin shi, dakyar ma ta bar shi ya tafi, amman
yanzun har tayi girman da take ganin ta wuce ya
rungumeta, shekaru biyu suna da nisa ne har
haka? Yayi tambayar cikin kan shi yana neman
amsa duk a waje daya.
"Fito to... Nayi kewar ki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 169
Dariya tayi sosai
"Ni ma haka, baka kira sai nayi bacci"
Kallon ta yayi
"Ke kuma ba zaki jira ni ba"
Dariyar dai ta sake yi, har lokacin ta kasa yarda
shine a gabanta, wani irin yanayi take ji har
jikinta na daukar dumi saboda murna. Tare
suka jera zuwa falon, sam ya kasa daina kallon
ta, sosai ta canza mishi kamar ba Madinar da ya
sani ba, dariyar ta ce kawai bata canza ba, har
yanzun idan tayi dariya duka idanuwanta sai
sun rufe, sai su kansu idanuwan, basu kara
girma ba. Kallon ta kawai na saka shi jin lallai
yazo gida. Wani numfashi da baisan yana rike da
shi ba ya sauke bayan ya zauna
"Daada baki ce mun zai zo ba"
Kallon shi Daada tayi
"Nima ban san zai zo ba Madina, yanda kika gan
shi haka nagan shi"
Kai Madina ta jinjina tana murmushi
Lubna sufyan
Hausabook.com 170
"In kawo maka ruwa?"
Ta tambaya saboda ta ma rasa abinda ya kamata
tayi, kai Nawfal ya daga mata badon yana jin
kishin ruwa ba, shima zuciyar shi ta cika taf da
farin ciki. Yana son ganin Adee da Daddy,
amman anya kuwa zai iya barin gidan Daada a
yau? So yake ya kwana suna labari, in sun gaji
suyi shiru su zauna tare da juna kawai, wannan
yanayin na yau yana son ya adana shi a wajaje
fiye da zuciyar shi yanda in ya tafi zai dinga
ziyartar wajajen suna saka shi nishadi. Ruwan
kuwa ta kawo mishi a kofi ya karba
"Abinci fa?"
Kai ya girgiza mata yana saka dayan hannun shi
ya bubbuga gefen shi kan kujera
"Ki zauna muyi labari... Nayi kewar ku da
yawa..."
Zaman kuwa tayi, Daada na bin su da kallo
zuciyar ta cike da farin cikin, tsoron da take
kwana da shi tana tashi yana barinta da ganin
Nawfal din. Idanuwanta ne kawai akan su,
tunaninta yayi nisa, ba zatace ga abinda suke
Lubna sufyan
Hausabook.com 171
fada ba, amman dariya sukeyi, sosai dariya suke
kamar basu da wata damuwa a fadin duniya
Haka take son ganin su
Tare da juna
Cikin farin ciki
Haka take fatan rayuwar su ta kasance
Sai dai kaddara ta riga fata.
"Adee..."
Nawfal ya furta bayan sun shigo dakin ita da
Khalid suna gaisawa da Daada,wata irin kewar
ta na tsirga mishi, dariyar da takeyi bai hanata
hararar shi ba
"Bawani nan..."
Murmushi yakeyi yana mika mata hannun shi
daga inda yake zaune, karasawa tayi ta kama
tana zama gefen shi kafin ta zare hannun nata
tana daka mishi duka.
"Ouchhh... Adeee"
Lubna sufyan
Hausabook.com 172
Ya fadi yana murza wajen dan yaji zafi sosai
"Ka zo ba zaka iya kirana ba Nawfal, ba sai kazo
inda nake ba in ganka..."
Har lokacin murza wajen yakeyi
"Saboda ke fa na zo, yanzun nake so in kira inji
ko kin dawo..."
Tabe baki Adee tayi, Nawfal na gyara zaman shi
kan kujerar yanda zai fuskance ta, fuskarta
fayau take babu kwalliya, amman sai yaga har
wani kyalli-kyalli takeyi mishi
"Kinyi kyau sosai"
Murmushi tayi, kowa haka yake ce mata tun
bayan sati daya da fara mata gyaran jikin da
bata san nawa Nanna ta kashe a kai ba. Kuma
itama tana jin santsin da fatarta tayi, daman
fuskarta tunda can babu kurji ko daya, tana dai
gani a fuskokin mutane, ita wannan zumuncin
ne bai taba tsallakowa kanta ba.
"Nagode"
Lubna sufyan
Hausabook.com 173
Ta fadi, kai ya jinjina mata yana sata girgiza
mishi nata, ita ba dan yace tayi kyau take mishi
godiya ba
"Ina nufin nagode da kazo..."
Wani sauti Khalid ya fito dashi daga kasan
makoshin shi yana dorawa da
"Karku fara dan Allah..."
Cikin yanayin da yasa su yin dariya
"Daada ina Madina?"
Cewar Adee
"Sallah ta shiga daki tayi. Na san yanzun zaki ga
ta fito"
Ai kam Daada na rufe bakinta Madina tana
fitowa daga daki
"Adda..."
Ta kira tana karasowa ta zauna daga gefen Adee
"Hamma ina wuni"
Ta gaishe da Khalid da yake daddana wayar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 174
"Lafiya kalau Madina... Kwana biyu"
Kallon shi tayi
"Ina cewa Hamma ya gaishe ka fa"
Shima nashi idon ya raba da waya yana kallon ta
cike da alamar tambaya
"Wanne Hamman?"
Murmushi tayi
"Hamma Salim, ko shekaranjiya na ce ya gaishe
ka, kullum ma idan mun hadu ina cewa ta gaishe
ka"
Wannan karin Adee ta kama Madina tana juyo
da ita dan su fuskanci juna
"Hamma Salim naji kince Madina... Hamman
mu... Salim na mu wanda duka muka sani?"
Yanayin da yake fuskokin su ne ya ba Madina
dariya, yi suke kamar abune da ko a mafarki
basu hango zai faru ba, kai ta jinjina
"Hamma Salim kike gani? Kina magana da shi,
shima yayi magana da ke?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 175
Kai ta sake jinjina ma Adee, Khalid da ya ajiye
wayar shi kan hannun kujera fuskar shi dauke
da tsantsar mamaki yace
"Ya sunan bokon ki Madina?"
Har Daada sai da tayi dariya
"Da gaske nakeyi... Tafdin... Hamma fa... Bajjo
kana jin ikon Allah"
Kai Nawfal ya jinjina musu, dan shi ya gama
nashi mamakin tun kafin su zo
"Har daga makaranta yana dauko ta ya dawo da
ita gida wasu ranakun..."
Sai da yaga hankulan Adee da Khalid sun koma
kan shi tukunna ya dora da
"Suna labari da juna har suzo gida... More like
Madina tana labari da shi kuma bai taba sauke
ta a hanya ba"
Baki Adee ta rike
"Ashe zanyi tsahon ran da zan ga ranar nan...
Madina anya ke mutum ce?"
Dariya suke bata sosai ma
Lubna sufyan
Hausabook.com 176
"Yanzun idan ya shigo fa?"
Daada ta fadi tana saka wani shiru ya ratsa
dakin, Khalid na daukar wayar shi daya ajiye,
Nawfal ya koma cikin kujera ya zauna. Adee ma
gyara nata zaman tayi tana kallon Madina
"Maganar kunshin, gobe idan Allah ya kaimu ne
fa..."
Kai Madina ta jinjina mata
"Ban manta ba, wajen karfa tara In shaa Allah
zan taho sai in fara ma wanda suke nan kafin
sauran su zo..."
Ganin sabuwar hira zasu dasa yasa Daada cewa
"Abinci fa?"
Adee ta fara amsawa
"Ni dai ina ci, sau daya naci abinci duk yau
wallahi, cikina sai kullewa yake tun dazun"
Abincin kuwa Madina ta tashi ta zuba musu
banda Nawfal da ya shiga kitchen din da kan shi
yana dafa ruwan zafi ya hada shayi, kankara ya
dauka a fridge ya fasa ya zuba cikin kofin yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 177
karasa cika shi taf ya dauko ya fito. Banda Daada
babu wanda yayi mishi magana tunda duk ba
bakon abu bane a wajen su. Musamman Khalid
da ba zaice ga rana daya da yaga Nawfal yasha
shayi mai zafi ba. Sam baya so, suna nan suna
hira Julde ya shigo ya same su, shima abincin
aka zubo mishi suna dasa sabuwar hira kamar
lokacin gari ya waye musu ba dare bane ba.
Shikam Julde hankalin shi yana kan Adee da su
Khalid suka saka a gaba da tsokana. Haka yake
son ganin su kullum, yaran shi, farin cikin shi.
Yanda maganar auren ta ya tafar mishi batare
da wata matsala ba abune da zai jima yana
nutsar da shi duk idan ya tuna. Akan ce mutane
na daya daga cikin Rahmar da Allah zai maka,
bai kara yarda ba sai akan bikin nan na Adee,
yanda abokan arziki suka mishi tsaye ta yanda
wani dan uwa na shi bai taba mishi ba tunda
yake. Daga tambayar auren har daurin shi da ya
wakilta abokin shi ya kuma karba. Tabbas yaga
halaccin mutane, a tare da dangin mijin Adee
kuma yaga wautar mutane ta yarda da wani
kamar yanda suka yarda da shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 178
Dan shi bai basu wannan yardar ba, kaunar da
yake ma Adee tasa sai da yayi cikakken bincike
a kan su kafin ya amince. Ba zai dauki yar shi ya
kai inda wata matsala zata biyo baya ba. Sauran
maza ne, yana da tabbacin babu wani abu da zai
taba su da zasu kasa dauka. Adee ce yake son
karewa da dukkan kumajin shi. Kuma hankalin
shi ya kwanta da kalar mijin da zata aura.
"Karfe goma da wani abu, in dai ba anan zaku
kwana ba ya kamata ace kun tashi kun kama
hanyar gida yanzun"
Julde ya fadi yana kallon agogo, sake shigewa
cikin kujera Nawfal yayi yana dauke idon shi
daga cikin na Khalid da yake kallon shi
"Da gaske Bajjo?"
Adee ta fadi bayan ta mike
"Gobe da safe zan taho, sai mu taho da Madina..."
Yace yana kin hada ido da su, su yake son gani
daman, kuma ya gan su, ko da can kalar baccin
da yakeyi a gidan Daada ya sha bamban da na ko
ina, bacci yake batare da tunanin komai ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 179
Yana son ko da na yau ne kawai kar ya hadu da
Nanna.
"Muje Khalid, Allah ya kaimu goben. Daddy sai
da safe"
Adee ta fadi tana kallon su Daada
"Daada sai Allah ya kaimu... Madina ina jiran ki"
Kanta da yayi mata nauyi Madina ta jinjina,
bacci takeji ba dan kadan ba, ba zata tuna ranar
karshe da tayi wannan daren ba. Julde ma
mikewa yayi
"Nima ai tafiyar zanyi"
Dan tunda aka fara hidimar bikin ya tattara ya
koma hotel da zama, har fada sukayi da Saratu
kan hakan
"Daman kofa kake nema, in ba haka ba ko
bangaren su Khalid ai zaka iya komawa"
Shine abinda ta fadi da ko amsa bata samu ba,
saboda ba sai da biki ba, idan yaga dama zai iya
kwanakin shi a hotel tunda ba zamanta yakeyi
ba. Sai da Nawfal yaga Julde ya mike tukunna ya
raba nashi jikin da kujera, tare duk suka fita,
Lubna sufyan
Hausabook.com 180
Daada iya bakin kofar daki ta raka su, Nawfal ne
ya fita har kofar gida. Sai da su Khalid suka fara
sannan Julde ya kalli Nawfal
"Menene? Me kake son fada mun?"
Da mamaki Nawfal yake kallon shi, murmushi
Julde yayi
"Na sanka Bajjo, kana ta kallo na da na shigo, na
san akwai abinda kake son fada mun..."
Murmushi Nawfal yayi, shisa a duniyar shi
gabaki daya babu kamar su, sune kawai suke
kula da kananun abubuwa haka a tare da shi
"Zai iya jira Daddy, abinda nake so in fada maka
din... Zai jira sai an gama hidimar Adee..."
Numfashi Julde ya sauke
"Ka tabbata?"
Ya tambaya a idanuwan Nawfal din yaga ko
wacce irin magana ce ba ta rashin dadi bace ba,
babu damuwa ko daya a tattare da yaron na shi
"Daddy... Allah da gaske"
Murmushin dai Julde ya karayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 181
"To shikenan. Ka koma ciki, sai da safe"
Kiyawa Nawfal yayi, sai da yaga tafiyar Julden
tukunna ya koma yana mayar da kofar gidan ya
kulle hadi sa sauke wani numfashi da baisan
yana rike da shi ba. Kamar yanda ya fada ne,
tashi maganar zata iya jira har a gama bikin
Adee.
*
A tsaye ta fito ta same shi, ya mika mata hannu
ya karbi jakar da take rike da ita, batayi musu
ba ta mika mishi tana rugawa ta shiga kitchen,
numfashi kawai Nawfal ya sauke, ya kai minti
talatin yana jiranta, sai yanzun ya gane me yasa
Daada tace mishi
"In dai Madina ce da ka samu waje ka zauna..."
Ko Salim ya kai minti sha biyar yana tsaye kofar
gida, dan da tace ma Nawfal shi zai zo ya
dauketa bai yarda ba har sai da yaga zuwan na
shi, ita take kara bata lokaci shi gaban shi yake
faduwa saboda Salim ne, Salim ne a waje yana
jiran su. Zai fara tsayawa a cikin soron gidan
Daada, idan yaji Salim din baiyi fada ba saiya
Lubna sufyan
Hausabook.com 182
fita, dan bai shirya a sauke mishi hayaniya da
sanyin safiya ba. Ba zaice ga abinda ta kara
tsayawa yi ba, amman a tsakanin kitchen da
kuma dakinta sai da ta kara bata kusan mintina
goma. Sannan ta sake komawa kitchen tana
dauko wata karamar roba mai murfi ta fito.
Kai kawai Nawfal ya girgiza yana sata yin dariya
"Daada... Mun wuce"
Ta furta saboda Daada ta koma daki, daga can
tayi musu Allah ya tsare tana fada musu su ja
mata gidan idan sun fita. Daga baya Nawfal ya
tsaya dan ya hango Salim ya jingina kanshi da
kujerar motar da alamar ya gaji da jira, yana
kallo Madina ta bude gaban motar, sai da yaji
gaban shi ya fadi, musamman da Salim din ya
dago yana kallon ta a kasalance.
"Oh goodness"
Nawfal yace yana matsawa baya, jira kawai yake
yaji Salim din ya fara fada, amman ga mamakin
shi zama ya gyara yana tashin motar, juyowa
Madina tayi
"Hamma ka taho"
Lubna sufyan
Hausabook.com 183
Kai ya daga mata yana takawa, kafin tayi wani
motsi ya bude bayan motar ya shiga yana mayar
da murfin ya rufe, dan babu wanda zai saka shi
zama gaban motar Salim, yana kallo Madinar ta
shiga ta zauna ta rufo kofar. Sai da Salim ya fita
da motar tukunna ta fara korar shirun da fadin
"Doya da kwai na soya, ga naka na dibo maka..."
Dan kallon ta Salim yayi yana mayar da hankalin
shi kan tukin da yake yi
"Shisa kika bata mun lokaci?"
Kai ta girgiza tana dariya
"A'a Allah, inata sauri fa, ko Hamma?"
Ta karasa maganar tana dan juyawa ta kalli
Nawfal da ya sadda kan shi kasa, wannan
labarin ba dashi za'ayi ba. Baya son ta fara
tsoma shi ciki. Baisan me yake faruwa ba ko
yanda akayi ta sa bakin Salim ya bude, ko yanda
maganar ta bata mishi hayaniya cikin kunnuwa,
amman shi yasan yana bude idon shi zaice yana
ihu. Hirar Madina ta cigaba da yiwa Salim da
yake amsata dai-dai. Suna karasawa cikin gida
Nawfal na budewa ya fice daga cikin motar, yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 184
sane da ko gaisawa basuyi da Salim ba, amman
Salim ne in zaku hadu ka wuce ya wuce yafi mai
wata gaisuwa da zakayi mishi.
Madina ma bai mata sallama ba ya wuce abin
shi. Murfin motar ta kama da nufin fita itama
Salim yace
"Ina zaki?"
Kallon shi Madina tayi
"Su Adda na ta jira na nasan"
Dan daga kafadun shi yayi
"Nima na jira ki ai, ina doyar?"
Inda ta ajiye ta dauko robar tana mika mishi
"Allah suna ta jira, karfe tara nace musu...na san
zan kai dare kilan ban gama ba, zan ara wayar
Adda in kiraka idan na gama"
Ta karasa maganar tana bude murfin motar ta
fice kafin ma yace wani abu, baya ta sake
budewa ta dauki jakarta da Nawfal yabar mata.
Sannan ta wuce cikin gidan, numfashi Salim ya
sauke yana juyawa ya ga har ta bace ma ganin
Lubna sufyan
Hausabook.com 185
shi, yanda gajerun kafafuwanta suke da sauri
har mamaki yake bashi. Haka kawai yaji ganin
tan da yayi ya mishi kadan, ko hirarta baiji da
kyau ba. Sake kunna motar yayi yaja ta yana
kara ficewa daga gidan dan ba zai zauna ba,
hayaniyar tayi yawa. Gara yaje ya samu wani
hotel din ya kira wata ko zata taya shi ya rabu
da yanayin kewar Madina da ya dabaibaye shi.
Ita kuwa cikin gidan ta wuce, tana shiga cikin
falon da sallama, Saratu ta fara gani da ta amsa
sallamar da fara'a a fuskarta. Ko a cikin yaran
idan taji ana cewa Salim baya son mutane abin
baya bata mamaki, itama din ba wai mutane sun
dameta bane ba, kafin jinin ku ya hadu akwai
aiki. Idan wani ya ce mata me yasa take son
Madina zata karyata, amman yarinyar ta shiga
ranta tun ba yanzun ba, bata san me yasa bata
zuwa gidan ba, lokaci zuwa lokaci tunanin ta
yakan fado mata. Banda su Salim babu wani da
zataji alkhairi zai shiga tsakanin shi da Julde da
zataji ranta bai mata bakikirin ba sai Madina.
Tana kaunar yarinyar, irin kaunar nan da bata
da dalili. Share muryar da taji a cikin kanta tana
tambayar ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 186
"Anya kuwa? Kin tabbata babu wani dalili?
Kaunar da kike mata bata da alaka da Yelwa?"
Tana kokarin dishe sautin muryar da yiwa
Madina magana
"Madina ana ganin ki daman? Adee ta jawo
mana ke ko?"
Dariya Madina tayi
"Nanna... Makaranta fa. Ina kwana... Ya hidima?"
Murmushin ta Saratu ta kara fadadawa, duk da
yanayin muryar Madina din na son daukar
tunanin ta zuwa abubuwan da ta zabi ta adana
"Alhamdulillah...suna ciki suna jiran ki, amman
da kin fara cin wani abu, an kawo waina yanzun
nan"
Kai Madina take girgizawa
"Sai dai anjima Nanna, doya naci wallahi"
Dan har bayan wuyanta take jin ruwan shayi na
taso mata, wani irin koshi tayi na ban mamaki
"To shikenan..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 187
Har Madina ta wuce ta dan juyo
"Daada tace a gaishe ki"
Fara'arta dake fuskar Saratu sai da ta dan ragu,
kai ta jinjina kafin dakyar ta iya cewa
"Tana lafiya?"
Da murmushi Madina ta amsata tana juyawa,
karancin shekarun ta bai hanata fahimtar babu
wani shiri mai karfi tsakanin Daada din da
Saratu ba, kawai wasu tambayoyin bata san ta
inda zata fara su ba, wasu tambayoyin tsoron
amsar su na sakata sake adana su a cikin kanta.
Amman kam tana da tarin tambayoyi, masu
yawan gaske
"Sai yanzun? Karfe tara fa mukayi dake"
Muryar Adee ta katse mata tunaninta
"Afuwan Adda, inata hidima ne ashe lokaci yana
tafiya"
Cewar Madina tana ajiye jakar hannunta a kasa
dan duka kayan lallen suna ciki, tsugunnawa
tayi ta kwance takalman da suke kafarta da sam
Lubna sufyan
Hausabook.com 188
sai lokacin ta tuna bata cire su ba. Kafin ta dago
har Adee ta daukar mata jakar
"Ki kawo Adda"
Harararta Adee tayi
"Ni dai muje, ki dauko takalmin ki kafin a dinga
bi takan shi ana wucewa"
Juyawa kuwa tayi tana daukar takalman nata ta
rike su a hannu tabi bayan Adee har zuwa
dakinta da alamu suka nuna duk an kwashe
kayan ciki an bar gado kawai, dan dakin yayi fili
sosai. Yan matane kusan su sha biyar, in dai
kallo ne Madina ta saba da shi tunda inta fita har
ta dawo bata cin karo da mace mai kalar shigar
ta. Yau ma riga da wando ne, wandon na jeans
ne baki, kamar ko yaushe ta nannade kafafuwan
har kusan kwaurinta sai safa baka a kafarta.
Akwai farar riga kal daga ciki, ta dauki mai
dogon hannu ta dora a kai, tana jan hannun
baya, sai yar karamar hijab da ta saka.
Ko gilashin fuskarta abin kallo ne, waje ta samu
gefe ta zauna tana karbar jakarta a hannun Adee
bayan tace ma yan matan da suke cikin dakin
Lubna sufyan
Hausabook.com 189
"Sannun ku"
Rigar saman yellow ce, ita babu yanda za'ayi ta
bata ta da lalle, amman tabbas a cikin yan matan
nan ko wajen wucewa ne wata na iya shafar ta.
Kunshin gidan biki ba bakonta bane ba. Shisa ta
mike tsaf tana cire rigar tabar farar da tayi
zanzaro da ita, ganin tana neman inda zata ajiye
yasa Adee karba, saida ta ninketa sannan ta fice
da rigar tana barin Madina da ta zauna zata fara
hada lallen ta.
*
Sai wajen tara da rabi tukunna ta samu suka
barta, shima dan Salim da yake ta kiran wayar
Adee ne, ita nata kunshin sai washegari ma da
sassafe idan Madina din tazo ita zata fara yiwa
tunda ranar ne ya kama alhamis kuma shine
za'a fara bikin gadan-gadan, za'ayi kamu. Sai dai
kowa yazo ya ga kunshin wasu sai yace shima
za'ayi mishi, duk ta bar su a zuwan washegari
idan ta gama yiwa Adee duk sai ta samu tayi
musu. Nanna ta so ta kwana anan din tace mata
tabar Daada ita kadai. Tunda take a rayuwarta
Lubna sufyan
Hausabook.com 190
bata taba kwana wani waje banda gida ba, bata
ma jin zata iya kwana wani wajen.
Wata babbar leda Nanna ta cika mata da
kayayyakin da batasan ko meye a ciki ba. Adee
ta rike ledar tana rakata har wajen motar Salim
din sannan ta bata kayayyakin tana mata godiya
sukayi sallama, bayan motar Salim ta bude ta
saka kayan ta rufe tana kowama ta bude gaban
motar da kamar jira Salim yake ta zauna
"Ke ba zaki iya ce musu dare yayi ba? Ba zaki ce
kin gaji kina so ki tafi gida ba, ko baiwar su ce
ke?"
Saboda yanayin ta kawai ya nuna a gajiye take,
ko wayar farko daya kira wajen karfe bakwai
aka bata yanayin muryarta akwai gajiya
"Mutanen suna da yawa ne Hamma, shisa na
tsaya na kara rarragewa, kanata kira da na kara
yiwa ko mutum biyar ne kafin mu tafi tunda kai
zaka mayar dani gida"
Kallon ta yakeyi kawai, itama kallon shi tayi,
yanayin fuskar shi na sata kai hannu ta gyara
gilashin ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 191
"Dan Allah kar kamun fada Hamma, nagaji sosai
Allah, kaji..."
Numfashi kawai ya sauke, ba fada bane baya son
yi mata, surutun ne ba zai iya ba. Yana kallo ta
rufo murfin motar tana yarfe hannun ta na
dama tana mikar da shi kafin ta sake yarfe shi,
tsintsiyar hannun take ji kamar bata tare da
hannun ta saboda yanda yayi mata sanyi, kafin
tayi wani motsi sai ganin hannun tayi cikin na
Salim ya rike shi yana gyara zaman shi ya saka
dayan hannun shi yana murza mata dai-dai
tsintsiyar hannun, kafin ya bude daga gaban
motar yana dauko wani abu cikin yar roba, sai
da ya dangwalo taji yajin abin har cikin
idanuwanta, murza mata yayi sosai a gabaki
daya hannun nata har yatsu sannan ya sakar
mata hannu.
Man ya rufe ya mayar inda ya dauko, wuyan shi
yana yawan rikewa idan yayi zaman karatu
shisa baka raba shi da irin wannan magungunan
na shafawa, sai daya tayar da motar sannan yace
mata
"Saura ki murza idon ki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 192
Dan yasan abinda zata iya ne, murmushi kawai
tayi tana jinta wani iri, ko dan yau dinne ranar
farko da hannun shi ya taba nata. A kasan
zuciyar ta take jin rashin kyautuwar da yake
cikin hakan duk da Salim din Yaya ne a wajen ta,
amman ba muharramin ta bane ba.
"Kishirwa nake ji Allah"
Ta fadi tunda zasu fito taso ta cewa Adee zata
sha ruwa sai ga Nanna kuma, sai ta manta
"Akwai ruwa ki dudduba"
Salim ya furta yana jin muryar shi ta fito a bude.
Sake rike matukin motar yayi gam ko zai samu
zuciyar shi ta natsu waje daya. Mata ne kalar
duk da yaso zai samu, daga lokacin daya fara
binsu zuwa yanzun ba zai kirga hannuwan da ya
murza ba. Ko yau hannun mata biyu ne suka
shiga cikin na shi, zuciyar shi batayi tsalle irin
haka ba. Baiji kamar yana murza wani abu a
cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 18