canza cewa ita din
jinin shi bace ko da bata da gadon shi'
"Madina"
Kawai ya iya sake furtawa a karo na biyu yana
son ya rungumeta a jikin shi, dan hakan ne
hanyar lallashin da ya fara zuwa kan shi, sai dai
kafin yayi wani yunkuri ta bude fuskarta tana
kallon shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 279
"Ya zan koma baya Hamma? Ya zan koma
lokacin da banga takardar nan ba? Ya zan koma
in mayar da ita in jira sai lokacin da Daada ta ga
ya kamata in sani ta fada mun da kan ta?"
Sosai take kallon shi tana son ya taimaka mata
ko zata daina jin wani abu na budewa a cikin
kirjinta, ko tarin tambayoyin da suke mata yawo
zasu daina, idan tace bata tunanin su waye
iyayen ta zatayi karya, a duk wani PTA meeting
na makaranta sukan fado mata, a lokuttan da
za'a bayar da wata takarda da sunan iyaye su
saka hannu sai Julde ne zai saka mata tunanin
me ya faru da su kan zo mata. Bata tambaya
bane saboda tasan idan lokacin ta sani yayi za'a
sanar da ita.
Ko da wasa bata hango sanin zai iya zo mata da
hargitsi irin wannan ba, idan Yelwa mahaifiyar
ta ce tana ina? Ba rasuwa tayi ba kenan? Kamar
yanda tunanin ta ya sha ba ta, shisa Daada bata
maganar ta, zafin rashin ne yake taba ta har
zuwa yanzun. Wanne son kaine tayi a karo na
farko idan tsallakewa ta barta ne na biyu? Da
sauri ta fisge takardar dake hannun Salim tana
sake duba wani layi da sai yanzun ma'anar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 280
take bude mata, yanda ta dago ta kalli Salim ne
ya tabbatar mishi da sai yanzun ta gane, ta gani
amman sai yanzun ta gane, takardar ya karba ya
ninke yana kamo hannunta ya saka a ciki
"Koma menene, ina nan, kina jina, ina nan tare
dake"
Kai take daga mishi tana jin hawayen da suka
cika idanuwanta suna zubowa
"Kin gani, babu yanda zaki goge ganin da kikayi,
idan nace miki komai ba zai canza ba zanyi miki
karya"
Kamar yanda baima san me yake ce mata ba,
kalamai yake nema, kalaman da zasu tausasa
abinda yake tunanin tana ji a zuciyar ta, shisa ya
kama dayan hannun nata yana rike shi da nashi,
kamar hakan zaisa damuwarta ta koma jikin shi,
zuwa lokacin kuka takeyi marar sauti, amman
duka jikinta bari yake saboda tashin hankali,
bata da gadon babanta, idan bata da gadon shi
hakan na nufin ita din ba ta hanyar daya kamata
aka same ta ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 281
"Kana jinta... Ban.. Banda gadon Baba na, kaji me
tace Hamma"
Ta san sunan shi Kabir, tunda da shi take amfani
a makaranta, hakan ne ma ya sa ta gane ba Julde
bane baban ta, ita da Nawfal ta san bashi ya
haife su ba, shi yana amfani da Bukar ita tana
amfani da Kabir. Kwance seatbelt din shi Salim
yayi yana gyara zaman shi yanda zai rike
hannuwan ta sosai, so yake ya hadata da jikin
shi
"Madina ce"
Zuciyar shi ta fada mishi kamar harda gargadi a
cikin yanda tayi maganar
"Lallashin ta zanyi"
Ya amsa zuciyar tashi a hankali, sai dai anya zai
tsaya iya lallashi? Ba tun yau yake son jinta a
jikin shi ba, ba tun yau suke zama a mota yake
duk wani kokari da zai iya na ganin ko da
hannunta ne bai rike ba. Ko mace ya raba da
kirjin shi zai fara tunanin yanda zai kasance
idan Madina ce, ya rasa lokacin da hakan ya
fara, kawai tsintar kan shi yayi a tsakiya, ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 282
kuma rasa yanda zai ya fita. Yanzun ma da
hannun ta yake cikin na shi yana jin dumin shi
har kasan ran shi. Idan ya rike ta a jikin shi ba
zai taba tsayawa a lallashi ba ya sani.
"Baki sani ba Madina, karki fassara duk abinda
kika gani a cikin rubutun nan, zai iya nufin
komai, kar mu ce zamu bashi fassara daya,
umm?"
Ya karasa yana dan jan hannun ta da take
kokarin zamewa, bai kokarin hanata ba,
hawayenta ta goge tana jinjina mishi kai, so take
ta yarda da shi, kalaman shi su zame mata igiyar
da zata kama dan jinta take cikin wani irin rami,
ko bata fito ba, ya zamana tana rike da igiyar,
hakan zaisa taji kamar tana da zabi a fitowa
daga ramin.
"Ki mayar da takardar nan inda kika dauka, ki
jira Daada, ki jira ta fada miki da kanta"
Kai take jinjina mishi, yana ganin yanda
kalaman shi suke zauna mata
"Kirjina yana mun ciwo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 283
Ta fadi wasu sababbin hawayen na zubo mata,
sosai yarintar da take tare da Madinar ta
bayyana a yanayin yanda tayi maganar da kukan
daya kwace mata bayan hakan, lumshe
idanuwan shi Salim yayi yana sake bude su a
kanta
"Kukan ne bana so ai, zai bari idan kika daina..."
Hannu tasa ta goge hawayen ta, kara matsawa
Salim yayi yana kama hannun nata yayi amfani
da shi wajen kara goge mata fuskarta, tsoron ya
kai nashi jikin kuncinta kai tsaye yakeyi
"Idon zai kara kankancewa, ki rufa mana asiri
Madina"
Dariya tayi mai sauti, duk da ta sake hadowa da
wani kukan, shima dariyar karfin hali yayi,
gabaki daya wani iri yake jin shi
"Kin ci abinci?"
Ya tambaya bayan ya koma ya gyara zaman shi
akan kujerar, kai ta daga mishi
"Tun dazun"
Lubna sufyan
Hausabook.com 284
Duk da bata gane kan abincin ba taci, saboda
bata so Daada tayi mata magana, ko ta
tambayeta mai yasa bata ci abinci ba. Yanda
Madina take kallon shi yasa shi fadin
"Kina son wani abin muje mu siyo?"
Kai ta girgiza mishi
"Littafi?"
Dariya tayi
"Da gaske nake yi"
Kai ta girgiza mishi
"I will be fine..."
Ta fadi da wani irin sanyin murya duk da bata
jin zatayi dai-dai din
"Karki yi mun karya, bana so, kar ki fara boye
mun kina jina?"
Da sauri ta daga mishi kai
"Dare yana yi, ki koma gida, da safe zan zo in
kaiki makaranta In shaa Allah..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 285
Murfin motar ta bude ta sauke kafafuwan ta a
waje
"Mug"
Ya kira, juyawa tayi da murmushi a fuskar ta,
haka yake son gani, murmushin nan, ko kadan
bayason yaga fuskarta babu shi
"Komai zaiyi dai-dai, kina jina, ko babu su, kina
da mu, mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai
ne, kar tunanin su ya dame ki da yawa"
Numfashi ta sauke
"Mu kadai ne daman, tuntuni mu kadai ne"
Ta maimaita cikin kanta, kalaman na zauna
mata, tunda ta bude ido su kadai din ta gani, ita
da Daada, kafin ta ga su Daddy, su kadai ne
kamar yanda Salim ya fada, daga Yelwa har
Kabir basa nan, basa tare da ita tun daga farko,
ganin takardar nan ba zai kawo su ba in har
suna raye, shekaru sha shida suke da shi su zo
inda take, duk basu zo ba. Ba zasu dame ta da
yawa ba, ba zata basu wannan muhimmanci ba,
watakila a gaba, amman yanzun bata jin zasu
same shi. Kamar Salim yaji tunanin da take yi
Lubna sufyan
Hausabook.com 286
"I love you"
Kalaman suka subuce suna komawa cikin
kunnen shi da wani yanayi da ba zai misaltu ba,
tunda yake, ko da wasa, ko a mafarki bai taba
furta su ba, babu wanda ya taba furtawa, duk da
su Adee na yawan fada mishi, amman bai taba
mayar musu ba, idan basu gane yana son su a
kananun abubuwan da yake musu ba, to baya jin
dan ya fada zai canza wani abu, sai gasu yau
kalaman sun subuce mishi kamar bashi da iko
da su. Dariya Madina tayi tana kallon fuskar shi
"Nawa yafi yawa, nagode Hamma"
Ya kasa ko motsin kirki sai ta fita harta rufe
mishi murfin motar, ba shiri ya zare seatbelt din
yana fitowa, harta shiga gida, da kusan gudu ya
bita yana kiran sunan ta, da mamaki ta juyo,
numfashi ya sauke yana kai hannu ya yamutsa
sumar da yake askewa kasa sosai, amman yanda
take a nannade duk da bamai yawa bace zai sa
kagane ya hada jini da fulani.
"Ki fada in ji"
Lubna sufyan
Hausabook.com 287
Ya tsinci kan shi da fadi, yana so yaji ta furta
kalaman ko zai samu saukin cewa shi sun kubce
mishi, yana so yaji ta furta dan ta nuna mishi
itama a wajen ta suna da saukin fita kamar a
wajen su Khalid, kalaman basu da nauyin da
yake jin sun mishi
"I need to hear you say them Mug"
Ya fadi yana saka idanuwan shi cikin nata, ita
kuma da mamaki take kallon shi, saboda tana
tunanin meye yake so ta fada din
"Mug..."
Ya kira wannan karin muryar shi na fitowa a
kagauce, numfashi ta ja
"Oh..."
Tana tuna me ya fada a karshe
"Mi yedi ma Hamma Am, ina son ka"
Numfashin da bai san yana rike da shi ba ya saki
yana jinjina kai, kafin ta sake fadin wani abu
harya juya. Motar shi ya koma ya kunna yana
janta ya fita daga unguwar, yakan ja gilasan ne
ya rufe saiya kunna AC din ciki saboda ya rage
Lubna sufyan
Hausabook.com 288
ma kan shi hayaniyar kan hanyar. Amman yau
iskar da take cikin motar yake jin tayi mishi
kadan, shisa ya sauke gilasan gabaki dayan su,
yana shakar iskar da ta shigo, tana fifita mishi
wajajen da baima san yayi zufa ba.
Ba gida yayi niyyar nufa ba, shisa da ya gan shi
bakin gate, yaga an bude mishi yasan Allah ne
kawai ya kawo shi lafiya, hankalin shi gabaki
daya baya jikin shi, shiga yayi da motar ciki, kila
idan ya watsa ruwa ya dawo dai-dai. Sai dai yana
fitowa daga motar yana cin karo da Julde cikin
wata shadda mai maiko da ta karbi jikin shi.
Shisa duk yanda za'ace yana da kyau baya
mamaki, in har yayi rabin kyawun Julde to
tabbas za'a kira shi me kyau, ko shi da kan shi
ma zai ga kyawun na shi.
Har yanzun hasken fitilar kyawun Julde zai
dishe na shi duk da bambancin shekarun da
yake tsakanin su
"Daddy..."
Salim ya kira yana dorawa da gaisuwar da Julde
ya amsa fuskar shi dauke da murmushi
Lubna sufyan
Hausabook.com 289
"Ya makarantar? Har an dawo?"
Kai Salim ya jinjina
"Zan sake fita, ina so in dan watsa ruwa ne"
Da murmushi a fuskar Julde har lokacin yace
"Allah ya taimaka yayi jagora. A dinga kula dai"
A cikin zuciya Salim ya amsa addu'ar Julden
yana wucewa, har yayi gaba ya juyo
"Daddy"
Ya kira yana sa Julde juyowa shima ya kalle shi,
dan har ya bude murfin mota
"Wacece Yelwa?"
Ya jefi Julde da tambayar da yaji kamar fadowar
gini, babu shiri ya nemi majingini da motar da
yake tsaye a jiki, saida ya tabbata muryar shi ba
zatayi rawa ba tukunna ya amsa da
"Kanwata ce"
Kai Salim din ya jinjina, haka kawai ya tsinci kan
shi da son sani, ko iya hakane, alakar da take
tsakanin shi da Madina, ya san yar uwar shi ce,
Lubna sufyan
Hausabook.com 290
amman yau yana son sanin me suka hada.
Juyawa yayi, Julde na bin bayan shi da kallo har
ya bace mishi, tambayar ta dake shi, a ina yaji
sunan Yelwa? A ina Salim yaji sunan da yake da
tabbacin ko Saratu ba zatayi kuskuren furtawa a
gaban yaran ba. Ba zama sukayi sukai shawara
ba, basa bukatar sanin ya kamata su kare yaran
daga abinda ya rabo su da asalin su.
Sai dai wasu sirrikan basa binnuwa
Wasu sirri kan ko ba'a tono su ba sai sun
bayyana kan su.
Da yawa zasu ce tana jin ranar ne daban saboda
ta kasance daya daga cikin ranakun da ya
kamata ace suna da muhimmanci a tare da ita,
tunda a yau din ta kammala jarabawar aji
shidda da ake kira da WAEC. Sai dai ita din ba
kamar kowa bace ba, yanda ta ga yan ajin su na
murna da rawar kafa tunda ma suka shiga aji
shiddan sai ya dinga bata mamaki, zaka rantse
da sun gama sakandire shikenan sun rabu da
karatu har abada, bayan tana jin tarin burikan
da kowanne a cikin su yake lissafawa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 291
"Ke ba zakiyi su calender din da naga Adee tayi
da suka gama makaranta ba?"
Salim ya tambayeta, dan shima yaga da yawa
matan ajinsu sunyi a wancen lokacin, tunda duk
sun bashi, wasu a ciki yana da tabbacin sun
bashi fiye da abinda suka rarraba, da yake
shima jeka ka dawo yayi, kuma Julde ya bashi
mota tun yana aji biyar, da ba da ita yaje ba,
bashida inda zai zuba kayayyakin da aka dinga
bashi
"Um um fa, ni babu abinda zanyi..."
Dan ba burgeta sukeyi ba, bata da wata kawa da
zata nuna ta kira da tata a cikin ajin gabaki
daya. Sai dai tace abokan karatu, zasu gaisa dai,
sunma fi kulata idan an bada wani aiki mai
wahala da suka kasa fahimta suna son ta
taimaka musu. Shisa yau ana gama jarabawa ta
fito, taji dadin samun Salim yana jiran ta, sai
hade fuska yake sanda ta shiga motar, ta kuma
san baya rasa nasaba da hayaniyar da ta karade
wajen da zaice mata yana jinta har cikin
kwakwalwar shi.
"Mug..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 292
Ya kira, murmushi tayi mishi, bakar rigace a
jikin shi, kamar yanda tunda ya fara aiki yake
cikin su, sai ya dora farar rigar da zata nuna
maka alamar likita ne a sama, yanzun take kara
ganin dalilin da yasa wasu a ajin su suke
tambayarta meye hadinta da Salim, yana da
kyau, yana da kyawun da ba saika kalle shi sau
biyu ba zaka gane hakan. Musamman yanzun da
ya ajiye gashi kwance luf a fuskar shi, saiya kara
wani irin kyau da Madina ta san ba ita kadai
take ganin shi ba. Kaf gidan su babu mai kyawun
shi, shine ya biyo Julde sak, sai dai takan ga
idanuwan Saratu a cikin na shi.
"Hamma Am, yau fuskar ka ta mun wani iri"
Numfashi ya sauke yana murza mukullin motar,
kamar ba zai amsa ba dan har yaja motar ma
sun fara tafiya
"Nagaji ne, na kwana a wajen aiki, tunda safe ina
can kuma...sai yanzun na taho"
Har ta daina tambayar shi akan maganar
shifting da tasan anayi a asibiti, wasu suyi aikin
safe, wasu na rana, wasu na dare, tunda ya fara
zuwa asibiti ta kula rabin rayuwar shi acan yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 293
yinta, kamar bashi da wani abu a yanzun da yafi
majinyatan asibitin da yake aiki muhimmanci.
Kuma kusan hakanne, tunda yana jin kamar
yana wani abu da rayuwar shi wanda ya kamata,
kamar da duk wata dakika da zaiyi wajen
taimakon tarin marassa lafiyan da ke asibitin da
yanda daudar zunuban shi take dan ragewa, duk
da a satikan yana jin da ya rage daudar daya
sake maye gurbin ta da matan da yake bi.
"Ki dauki gifts dinki a baya"
Salim ya fadi bayan ya tsayar da motar kofar
gidan Daada, duk hirar da ta dinga mishi da um
yake binta, yar maganar ma bata samu ba,
kamar yanda yace mata a gajiye take duk wata
alama ta nuna a gajiyen yake.
"Kasan ina son ka ko?"
Ta fadi tana murmushi, idanuwan shi kawai
Salim ya saka cikin nata, shi ya fara cewa yana
son ta, sau daya ne, bai kara ba har yau. Sai dai
ya bude mata hanyar fada mishi tana son shi
duk lokacin da zai mata wani abu da taji dadi.
Bai sake fadi bane saboda ya ga soyayyar da
yake nufi da wadda take nufi tayi hannun riga.
Lubna sufyan
Hausabook.com 294
Sai dai baya nufin soyayyar ta bata nukurkusar
shi, bayajin ta har kasan ran shi, ya sha farkawa
cikin dare ya duba zuciyar shi yaga itace dalilin
tashin na shi. Bai kara sanin da gaske soyayyar
da yake mata take ba sai lokuttan da ya samu
kofar rungumar ta a jikin shi yaki yin hakan.
"Madina ce"
Shine abinda zuciyar shi ta gaya mishi, a
lokuttan ne kuma yaga yanda yake da zabi a
rayuwar da ya daukar ma kan shi, idan yana son
jinta a jikin shi da duka rayuwar shi amman ya
iya rike kan shi, me yasa yake kasa rike kan shi
akan sauran matan? Ya dauki tunanin ne yayi
kasa dashi yasa wani abu mai nauyin gaske ya
danne shi, Madina tana nan, babu inda taje,
babu inda zataje, zai kara jira, zai tabbatar
zuciyar ta na in da tashi take kafin bakin shi ya
kara furta mata kalaman yana son ta.
"Ledoji biyu ne Hamma"
Batare da ya juya ba ya amsa ta
"Duka zaki dauka"
Lubna sufyan
Hausabook.com 295
Da ta dauka din ma, bayan addu'a sai da ta kara
cewa tana son shi, baice komai ba yaja motar shi
yana ficewa daga lungun. Ita kuma gida ta shiga
da sallama tana kiran Daada tun kafin ta karasa
cikin dakin
"Daada..."
Ta kara fadi ganin ta a kwance kan doguwar
kujera, takalmanta ta cire tana takawa har inda
Daadar take, sai da ta ajiye ledojin hannunta a
kasa tukunna ta kai hannu daya ta taba jikin
Daada, har lokacin akwai zazzabi, mai zafi ma
"Daada zazzabin nan har yanzun?"
Madina tace cike da damuwa, murnar da ta
shigo da ita na dishewa
"Da sauki, dazun ya sauka ma, dawowa dai ya
kara yi kuma na sha magani"
Bata yarda ba, tasan Daada da karfin hali
"Ko dai in kira Daddy?"
Da sauri Daada ta girgiza mata kai
Lubna sufyan
Hausabook.com 296
"Ki kyale shi, da sauki har abincin da kika dafa
na dan ci fa"
Numfashi Madina ta sauke, da yake sai karfe sha
daya take da jarabawar ranar, tana tashi da
asuba ta shiga kitchen, sai da ta dafa farar
shinkafa, suna da miyar kifi a fridge, dumamata
kawai tayi. Ta gyara ko ina tsaf tukunna ta fita,
dan ko lafiyar Daada kalau ma, da daddare take
wanke-wanke, sai ta share ko ina take tafiya
makaranta, girki kawai Daadar takan yi musu
kafin ta dawo daga makaranta, da ta gane yin
miya da yawa ta saka a fridge ma sai dai ta dafa
musu ko shinkafa ko taliya.
"Me kika samo haka?"
Daada ta tambaya tana son canza akalar zancen
"Hamma ne ya bani... Bari in watsa ruwa in sake
kaya"
Kai kawai Daada ta jinjina mata, wankan kuwa
tayi ta fito, wando ne daya dan wuce gwiwarta
yana da madauri daga kasan, sai riga ta kusan
kamo tsayin wandon, ta saka bakar safa
doguwa. Hulace a hannun ta tana rike da ita, kan
Lubna sufyan
Hausabook.com 297
kujera ta zauna tana kwance abin da ta daure
gashinta dashi dan ta gyara kan duk ya cakude
mata, kallon ta Daada takeyi, da gaskw gashi
rabo ne, waye zaice Madina zatayi gashi? Babu
kitso a kanta saboda ta tsani kitso, sai sun kai
ruwa rana take zuwa ayi mata, shima guda biyu
ne ko hudu. Duk idan tayi biyun nan tana kama
jelunan dan ta nannade su sai wani abu ya soki
zuciyar Daada.
Yanzun ma yanda take tattara gashin bayan ta
warware shi tana kokarin gyarawa sai da taji
zuciyarta ta matse, bata yi kama da Yelwa ba, sai
dai ko jini, Yelwa na da kyau kamar mahaifinta
da sauran yan uwanta da suke biyo shi, duk da
itama Daadar fulani ce gaba da baya, ba zatace
gashi ya saka Yelwa a tsakiya ba, tunda bata da
wadatar shi, amman mahaifinta na da shi, a
nannade ma. Na Yelwa ya sauka har kan gadon
bayanta, gashi da santsi, kamar yanda na
Madina yake yanzun, bambancin kawai shine
Yelwa na son gayu, tana kuma ji da gashin ta,
Madina bata damu da shi ba
"Badon kar Allah ya kamani ba ko Daada? Da
nayi aski, ko rabine dana yanke"
Lubna sufyan
Hausabook.com 298
Ta kan fada kusan duk lokacin da zata taje kan
ko inta dawo kitso, gashin bai dameta ba, yanda
zata kama shi ta nannade ta daure ta saka hula,
ba zaka tana sanin tana da gashi ba sam-sam.
"Kinki zuwa kiyi kitso ko?"
Lokaci daya yanayin fuskar Madinar ya canza,
bakinta ta turo gaba, tana kai hannu ta gyara
zaman gilashin ta, bata ko amsa Daada ba ta
janyo ledojin da ta ajiye, da alamar dayan
litattafai ne a ciki. Tana kuwa budewa taga sune
har guda goma, murmushine ya kwace mata
batare ma da ta sani ba tana fadin
"Allah ne kawai zai biya ka Hamma"
Har ranta taji dadin kyautar, batajin akwai wani
abu da zakayi mata kyauta da shi da zai faranta
ranta kamar littafi. Ko damuwar Yelwa da ta
kasa cirewa a ranta, dan duk yanda ta so ta ture
tunanin iyayen nata can kasan ranta sai ta kasa,
tana zaune zata ji sun fado mata. Idan abin ya
isheta zata dauki littafi, babu wani tunani da
yake rage mata banda kalmomin da suke yawo a
idanuwanta duk idan ta dauki littafi. Ko rike
littafin tayi a hannunta sai taji farin ciki. Dayar
Lubna sufyan
Hausabook.com 299
ledar ta jawo tana budewa, wannan karin ihun
da tayi sai da Daada ta dan runtsa idanuwan ta.
Waya, waya ce a kwalinta. Ta kasa daina ihun
murna
"Waya Daada.. Waya..."
Take fadi kamar zata fasa dakin da karajin ta,
tama kasa nutsuwa ta bude wayar da kyau,
zuciyarta har makoshin ta saboda murnar da
takeyi, dakyar ta iya samun nutsuwar dubawa
taga Itel ce da sukayiwa laqabi da vision. Ta taba
ganin wata itel a hannun Samira yar islamiyyar
su, da yake yarinyar bata gajiya da nuna cewa
babanta mai hali ne, duk tsanani irin na
makarantar sai da ta zo da waya a boye, yana ta
nunama kawayenta, wayar tayi ma Madina
kyau, dan wata taji tana cewa
"Itel ce, irin ta Yayana sak"
Tunda daga nesa take hangen su, waya na
burgeta, ko dan ma ta dinga daukar hotunan
lallen ta, tana yawan jin ana zancen manhajar
Instagram inda zaka iya dora hotuna irin
wa'annan, ita duk a cikin kafofin sada zumunta
Lubna sufyan
Hausabook.com 300
nan ne take zumudin budewa. Saboda jin yanda
Instagram yake ne yasa ta dan kulla abota da
Nafi'un ajin su, shi yayi mata bayanin komai, har
tana ganin ta gama fahimtar yanda manhajar
take, waya ce kawai ta rage mata. Inda tace
Julde ya sai mata, zai sai mata, amman tunda bai
dauka ya bata da kanshi ba, tana da yakinin
yana ganin lokacin da zata rike ne baiyi ba.
Gashi Salim ya bata, sai da tazo budewa ta kula
da an ma bude wayar, dan babu ledar sabuntar
nan, kwalin kawai ta cire, aikuwan an bude dan
har pouch an saka mata baki, wayar tayi mata
kyau matuka, fara ce.
"Daada kingani"
Ta fadi cike da farin cikin da yasa Daada
murmushi, karbar wayar tayi tana dubawa
"Ma shaa Allah. Allah yasa alkhairi yabar
zumunci..."
Farin ciki baibar Madina ta amsa Daada ba,
wayar kawai ta karba tana kunnawa, cike take
da caji, Salim kuma har sim ya saka mata, sa da
ta gama kawowa ne taga kusan komai ma ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 301
saita mata shi, dan har email ma taga ya bude
mata, yar takarda ta kula da ita a cikin kwalin
wayar ta dauko tana warwarewa, aikuwa email
dinne da kuma password din shi ya rubuta
mata, shafa rubutun tayi cike da farin ciki, tana
tunanin yanda wannan cakudin rubutun da
likitoci suke da shi na Salim ya bambanta, yana
da rubutu mai matukar kyau.
Duba contact dinta tayi, ya saka mata lambar
shi, ta Khalid, Adee, Julde, sai lambar Nawfal.
Duka da sunayen su yayi saving, sakewa tayi
tana gyarawa zuwa yanda take so, ta shi lambar
ta saka "Hamma Am" a jiki. Murmushi yaki barin
fuskar ta, earpiece din wayar da cajar ta dauko
tana gyara kwalin ta rufe ta mayar cikin ledar ta
kulle, murna fal cikinta ta dauka da ledar
litattafan ta kai daki ta ajiye su kan gadon ta
sannan ta dawo tana nufar kitchen, abinci ta
zubo ta dawo ta zauna suka fara hira da Daada,
duka yau hirar akan wayar tane da abinda
zatayi da wayar.
*
Lubna sufyan
Hausabook.com 302
Ta dauka bambancin ranar zai kare ne da
kyautar da ta samu daga wajen Salim, da kuma
wayar da sukayi, duk da sukanyi a land-line din
Daada, amman sai take jin wannan din ta sha
bamban, sanda duk ta so magana da shi zata iya,
flashing kawai zatayi mishi ta san zai kirata. Har
ta fara bacci, wajen karfe goma da rabi ta farka,
sai ta sauko daga kan gado ta nufi dakin Daada,
ba bakonta bane ba, ba kuma ranar bace ta
farko da ta saba barin dakinta taje bayan Daada
ta kwanta, wasu lokuttan ma cikin bacci takeyin
hakan, sai da asuba take sanin ta koma dakin.
Karfe daya da kusan rabi taji Daada tana zare
jikinta daga rikon da tayi mata, saukarta daga
kan gadon yayi dai-dai da bude idon da Madina
tayi tana juyawa, wani yunkurin amai da Daada
tayi yasa Madina dirowa daga gadon tana jin ta
wartsake gabaki daya, bandakin ta shiga, da
yake da wuta kwan a kunne yake, amai Daada
takeyi kamar zata zazzage hanjin cikinta, banda
sannu babu abinda Madina takeyi mata. Ita ta
taimaka mata ta wanke fuskarta ta kuskure
bakinta suka fito, zazzabi ne a jikin Daada
Lubna sufyan
Hausabook.com 303
kamar wuta, cikin kasa da minti talatin harta
fara fita daga hayyacinta saboda zafin zazzabi.
Madina bata san hawayen ta zai iya yin nisa ba
sai yau, banda bari babu abinda jikinta yakeyi,
musamman da ta jijjiga Daada tana kiran
sunanta taga ko jinta batayi, dakyar ta samu ta
sauketa daga jikinta, dakinta ta nufa tana dauko
wayarta ta kunna, sai take ganin ta dade bata
gama lodin ba, tana karasawa lambar Salim ta
lalubo tana kiran shi, tana jin bugun wayar na
daidaituwa da na zuciyarta, sai dai harta yanke
bai dauka ba, sai da tayi mishi kira hudu, ana
biyar ya daga yana fadin
"Mug...lafiya?"
Numfashinta na wani irin sama, muryarta na
sarkewa saboda nauyin da harshenta yayi tace
"Da... Daada bata da lafiya... Hamma, Daada..."
Ta karasa a wahalce
"Ki nutsu, ki tuna abinda na fada miki na
taimakon gaggawa, kina jina? You can do this,
kije wajen ta, yanzun zan taho"
Lubna sufyan
Hausabook.com 304
Kai Madina take dagawa tana fita daga dakin,
wayar ta ajiye a gefe tana karasawa wajen
Daada da sauri ganin tana yunkurin amai, juyata
tayi kan hannunta kamar yanda ya sha fada
mata, saboda a rigingine Daada take, zata iya
shakewa idan tayi amai a haka, sai zazzabin
jikinta yayi yawa, bandaki ta nufa tana zubo
ruwa a bokiti ta dauko towel ta zo tana
tsomawa, idan ta matse sai ta goge ma Daada
duk inda ta samu a jikinta. Bata san iya tsayin
lokacin da suka dauka, ko inda ta samo
nutsuwar da ta samu ba.
Da Salim ya kira wayarta ma, da kanta ta dauki
mukulli taje ta bude mishi gidan suka koma ciki
tare, batayi mamakin yanda ya kama Daada
yana dagata ya saba a kafadar shi ba, ko nishi
bata ji yayi ba, hijabin Daada ta daukar mata,
tana komawa dakinta ta saka karamin hijabi
itama. A kofar gida ta samu Salim, shiya karbi
mukullin yana rufe gidan, baya ta shiga kusa da
Daada tana kama hannunta ta rike, Salim ya
zagaya mazaunin direba yaja motar. Asibitin
Aminu Kano inda can yake aiki suka nufa, babu
wani bata lokaci aka samarwa Daada daki ita
Lubna sufyan
Hausabook.com 305
kadai aka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 18