me yasa zaku dinga jan kofa kamar zaku
rabata da mazaunin ta? Me yasa ba zaku rufe a
hankali ba?"
Salim ya leko yana fadi a masife, har kanshi
saida ya sara da yanda yaji karar rufe kofar da
Nawfal yayi. Ko inda Salim din yake babu wanda
ya kalla a cikin su, sauri ma sukayi suna fita
daga dakin, Khalid ne karshe, yana sane ya buga
kofar da zai rufe
"Khalid!"
Yaji muryar Salim din, sauri suka kara suna
dariya, yasan koya dawo ba zai mishi magana ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 252
tunda ba son surutu yake ba. Zai dinga binshi da
harara ne, ba ma zai zauna a falon ba sam, dakin
shi zai shige yana dawowa, Nafwal zai kwana
gidan Daada.
*
Gabaki daya hankalin ta yana kan littafin da
take karantawa, novel ne na James Hadley Chase
mai suna (A coffin from hong kong). Abincin da
ta zuba har yayi sanyi saboda gabaki daya bata
san abinda yake faruwa a wajen duniyarta ba.
Tana son litattafan mutumin, har mamakin irin
fasahar da yake da shi takeyi. Guda goma Salim
ya kawo mata a lokaci daya, kamar tayi me dan
murna ranar. Cancana su takeyi, bata karantawa
sai ranakun karshen mako, ta dauki guda daya
ta karanta a ranaku biyun.
Yanzun ma Daada ta daina mata magana kan
karatu, a cewar ta
"Bakina ya gaji da surutu Madina, in shaa Allah
ba zan kuma ba, in dai akan wannan litattafan
ne, ace abinci ma ba zaka natsu kaci shi ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 253
Tana kuma kokarin kyautata maganar tata, idan
Madina ta kula da ita ne, sai ta ajiye ta dan kara
tsakurar abincin ta mayar ta ajiye. To yau tunda
Salim ya dawo da ita daga restaurant din can,
sallah ce kawai abinda yake tashin ta daga inda
take. Littafin saiya rage mata yanayin da ta
shigo gidan da shi, yanzun ma isha'i take jira a
kira tana da alwala in tayi ta shige dakinta. Shisa
sam bata ji shigowar Nawfal ba, balle sallamar
shi. Sai hannun shi da ya sa yana yin kasa da
littafin nata ta gani, a hankali ta dago suna hada
idanuwa ta cikin gilashin ta
"Hamma..."
Ta kira da sanyin muryar da Nawfal yaji yayi
mishi tsaye, littafin ya zare daga hannunta, babu
gardama ta sakar mishi, duba sunan yayi
"Da dadi?"
Ya tambaya, ta jinjina mishi kai
"Sosai ma... Bansan zaka zo ba. Me zaka ci?"
Dan jim yayi
"Ki bani shayi kawai, bana jin yunwa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 254
Mikewa Madina tayi tana shiga kitchen din, ta
san yanda yake son shayin shi, babu bata lokaci
ta hado mishi, kafin ta gama tana jin muryoyin
su shida Daada data fito daga daki, tana fitowa
ta mika mishi
"Ka sha ko sikarin yayi maka kadan"
Karba yayi yana sake juyawa da cokalin da yake
cikin kofin kafin ya kurba
"Ki karamun Milo kawai ko cokali daya"
Cewar Nawfal yana mika mata kofin shayin.
Karo mishi tayi ta dawo tana bashi, ta dauki
plate din abincin da tasan ba ci zatayi ba ta
mayar da shi kitchen, sanda ta dawo ana kiran
sallar isha'i, shisa bata zauna ba ta nufi dakin ta.
Nawfal ma mikewar yayi, ya shiga kitchen ya
bude fridge ya saka kofin shayin yana fita
masallaci. Sanda ya dawo babu kowa a dakin,
kan kujerar da land-line din Daada take gefe a
ajiye ya zauna yana janyowa, lambar Murjanatu
ya kira tana dagawa yace ta kira shi, saboda
yasan zaifi sauki daga can akan ya kirata daga
nan din
Lubna sufyan
Hausabook.com 255
"Jaan..."
Ya kira yana jin yanda yayi kewar ta
"Ina missing din ka sosai"
Murmushi yayi
"Kan ki kawai kika sani"
Yana jin dariyar ta cikin kunnen shi, sautin na
nutsar mishi da zuciya yana saka shi sake
shigewa cikin kujerar
"Na kira Hamma yace mun kana gidan Daada,
nace ba kai nake nema ba na kira ne in gaishe
shi..."
Wannan karin shi yayi dariyar
"Bai yarda ba ai, yace yaji dadi dana kira saboda
yana so yayi magana da ni daman. Yan uwan
suna son ka Gidado"
Ta karasa da sunan da takan kira shi a lokaci
irin wannan, idan tana jin tsokana zata kira shi
da Bajjo tun ranar da taji Khalid ya kira shi da
hakan.
"Na sani, na san hakan Jaan"
Lubna sufyan
Hausabook.com 256
Nawfal yayi maganar batare da shakkun komai
ba, yana da cikakkiyar yarda akan soyayyar da
take tsakanin shi da yan uwan shi
"Hamma yace in kula da kai, yace kar in cutar da
kai, zai bada shaida ba zaka taba yin abinda zai
basu kunya ba..."
Wani abu Nawfal yaji ya tsaya mishi a kirji,
Khalid, Khalid daban ne a wajen shi.
"Zan so ace nayi recording din kiran kaji
kalaman shi idan ka dawo, ban rike gabaki daya
ba saboda ina ta share hawaye, ya karya mun
zuciya da yawa"
Dariya Nawfal yayi, shima tashi zuciyar rawa
yaji tana yi
"Ke komai abin kuka ne ai"
Yanayin yanda yayi maganar yasa Madina da ta
fito juyawa zata koma dan tasan dawa yake
magana, ta kuma san yana bukatar kasancewa
shi kadai dan ya sake da matar shi, amman sai
taga yana daga mata hannu cikin nuni da ta
karasa inda yake din
Lubna sufyan
Hausabook.com 257
"Jaan ga Madina zaku gaisa"
Ya fadi yana kallon Madina da take kokarin
ware mishi kananun idanuwan ta, nunin dai ya
sake mata da hannu yana kiranta, dakyar ta
karasa ta karbi wayar tana furta
"Hello..."
Cikin yar karamar murya
"Madina, ya kike?"
Murjanatu ta fadi ta dayan bangaren, yanayin
hausarta kawai ya isa bama Madina tabbacin
yar gayu ce, dan yanda ta ajiye kowacce kalma
harda sunan Madina din cikin ba kowanne
harafi hakkin shi zai tabbatar maka da hakan,
ga muryarta ma
"Alhamdulillah, ya kike kema? Ya aiki?"
Dariya Murjanatu tayi
"Lafiya kalau, aiki da karatu duka. Ya naki?"
Saida Madina ta gyara gilashin ta sannan ta
amsa tana sauke numfashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 258
"Ban sanki ba, amman na san Hamma, in ya
yarda kin zama matar shi, muma mun yarda da
kasancewar ki a cikin mu. Dan Allah ki kula da
shi"
Maganganun suka kubcewa Madina batare da
tayi wani tunani ba
"In shaa Allah, shima kice ya kula dani, ku daina
son kai haka"
Kai Madina ta jinjina tana murmushin da
batasan me yasa yake bude wani abu a kirjinta
ba
"Zan fada mishi shima.. Mungode sosai"
Ta amsa tana mika ma Nawfal wayar batare da
ta jira amsar Murjanatu ba, shima bata bari sun
hada ido ba, dan haka kawai take jin idanuwan
shi na shiga cikin nata zata iyayin kuka. Gashi
suna daki daya amman tana jin yayi mata wani
irin nisa. Karasawa tayi kan kujera ta dauki
littafin ta sannan ta wuce daki tana maido kofar
ta rufe a hankali.
*
Lubna sufyan
Hausabook.com 259
Wannan karin jirgin shi na karfe hudu ne, tunda
safe yaje gidan Daada sukayi sallama, abinda
yake gudun saida ya faru, tana ta kuka kamar
wanda zaiki dawowa, dan wannan karin duk
yanda yace mata zai dawo yana ganin rashin
yarda shimfide akan fuskarta. Haka ya dawo
duk ta kashe mishi jiki, bacci yayi zuwa azahar,
yana tashi ya fara shisshirya kayan shi ya watsa
ruwa, ya sake kaya kenan yana taje sumar kan
shi aka kwankwasa dakin
"Shigo"
Ya fadi dan a tunanin shi ma Lukman ne, sai
yaga Salim daya shigo dakin gabaki daya yana
mayar da kofar ya rufe. Lokacin Nawfal yaga yar
jakar da take hannun Salim din, mika mishi yayi,
da mamaki yasa hannu ya karba
"Na matar ka ne, ka kira mun ita"
Murmushi Nawfal yayi yana kallon Salim din,
kafin ya ajiye jakar a gefen shi, wayar Khalid na
wajen shi, dan haka ya mike yana duddubata
akan gadon ya dauko. Babu bata lokaci ya kira
Murjanatu da yasan tana tare da wayar dan yace
zai kirata kafin ya fita daga gidan
Lubna sufyan
Hausabook.com 260
"Harka gama shiryawa?"
Ta fadi bayan ta daga
"Zaku gaisa da Hamma Salim ne, ina kanyi"
Nawfal ya fadi yanajin yanda harshen shi yayi
nauyi a gaban Salim din, wani abu kamar kunya
na son lullube shi, mika mishi wayar yayi ya
koma ya zauna, yana jin suka gaisa kafin Salim
din ya dora da
"Bajjo yace miki bana magana da yawa ko?"
Baisan me Murjanatu tace ma Salim din ba,
amman yasa yayi dan murmushi
"Nasiha ya kamata in miki, amman banda wasu
kalamai masu yawa. Bajjo bashi da matsala,
shine mutum daya marar matsala dana sani, ba
don yana kanina ba. Yana da karancin shekaru
amman ba yaro bane ba, yana da hankalin da zai
rike ki da kyau. Karki cutar da shi, shine kawai
abinda zan fada miki, ba kashe di bane ba, roko
ne, kece zaki zama mutum ta farko dana roka
alfarma, ki rike mun kanina da kyau"
Lubna sufyan
Hausabook.com 261
Salim ya karasa cikin sauke muryar da Nawfal
bai taba ji a tare da shi ba
"Allah ya sa muku albarka a zaman ku ya
tabbatar muku da alkhairi"
Saida ta amsa tukunna ya mika ma Nawfal
wayar yana ficewa daga dakin. Da dukkan
zuciyar shi yake addu'a tun da aka fara maganar
auren, addu'ar da rabon daya zauna yayi irinta
harya manta. Saboda hayaniyar dayake gani a
cikin auren Julde da Saratu baya son ta kasance
a tare da Nawfal, rayuwa da tayi kason tashin
hankali a faranti Nawfal baiyi hankalin da zai
dauka ba, miko mishi kason shi tayi da kanta ya
karba saboda bashi da wani zabi. Baisan duka
labarin Nawfal ba, amman yasan me yake
faruwa da shi a zaman da yake a cikin gidan su,
idan shine bashi da yakinin zuciyar shi zata
dauka.
Shisa ya roki Murjanatu, idan bata samar mishi
da nutsuwa ba baisan me zai faru da yaron ba.
Yanata tunanin kyautar da zai basu, sai
shekaranjiya yaga wani bracelet na azurfa a
hannun wata yarinya a makaranta, yayi mishi
Lubna sufyan
Hausabook.com 262
kyau shisa ya tambayeta inda ta siya, tace mishi
yayanta ne yake siyarwa, basu rabu ba saida ta
kira masa shi sukayi magana ya fadi abinda
yake so a rubuta a jiki, da yake aikin cikin
saurine sai da ya kara mishi kudi, an kuma yi
masa shi yanda yake so. Dakin shi ya wuce yana
daura alwalar la'asar, raka Nawfal airport ne
abinda ya dawo da shi daga gidan.
Nawfal kuwa inda Salim yabar shi nan ya zauna,
ya rasa inda zai sa zuciyar shi ya rage emotions
din da yake ji. Dakyar ya iya yin alwala ya fita
masallaci. A sujjadar shi, a karo na farko ya roki
Allah da karya ba Saratu nasarar raba shi da yan
uwan shi, yaranta ne ya sani, amman Allah yake
roko daya saka mata salama a zuciyarta ta
taimaka mishi ta raba su tare da shi, karta raba
su, kome take mishi yana yafe mata, in tayi
wannan ba zai iya ba, ba zai taba yafe mata ba
saboda suna da muhimmanci na gaske a
rayuwar shi.
Har kasan ran shi yaji sanyi daya ga bangaren
Saratu a kulle, da alama bata nan, har sauri yake
wajen dauko jakar shi dan subar gidan kafin ta
dawo, duka haduwa biyu sukayi tunda ya dawo
Lubna sufyan
Hausabook.com 263
kasar, bayason suyi ta uku, baya son ya tafi da
wasu cikin maganganun da yasan dole saita fada
masa su. Ai kuwa har Khalid ya zo ya shigo
motar, Salim ma ya fito bata dawo ba, ajiyar
zuciya ya sauke har Khalid na kallon shi.
Da yake babu wani isasshen lokaci kusan a
gaggauce suke sallamar
"Baka dai manta komai ba ko?"
Julde yake tambaya
"Babu abinda na manta Daddy, kayan babu
yawa ai"
Kai Julde yake jinjinawa
"Na kara maka kudi, in dai kana bukatar wani
abin ka kirani kana ji ko?"
Sau hudu yana kara mishi kudi kenan, saboda
gani yake kamar zasuyi mishi kadan, baya so
yaje yana manejin komai ga yarinyar mutane,
yanda danginta suka karamma shi a Abuja ba
zai so ace Nawfal baya rike musu yarinya da
kyau ba, babanta ma kusan sau hudu suna
gaisawa, uku daga ciki duk shi ya kira Julden,
Lubna sufyan
Hausabook.com 264
basu da matsala ko kadan ya kula, mutane ne su
masu karamci da saukin kai, duk kuwa da tarin
arzikin da yaga Allah ya wadata su da shi, bai
saka musu girman kyau da kyamar mutane ba,
ko Kawun Murjanatun yaga yanda yake faran
faran da ma'aikatan gidan na shi kamar wasu
abokan shi.
"Daddy kudin ai yayi yawa, da gaske ba wani
abu nake siye ba, kuma nace maka ina aiki"
Kallon shi Julde yayi
"Ka tsayar da hankalin ka kan karatun ka, da
zaka ajiye wannan aikin ma zaifi"
Dariya kawai Nawfal yayi, yanda duk zai ma
Julden bayani yasan ba zai yarda ba, tsadar
rayuwa acan kawai in baka da lafiya ne, ganin
likita da magungunan su akwai tsada sai kuma
kudin haya, amman abinci kowanne mazaunin
New York ko wanda ya taba kai ziyara zai fada
maka babu tsadar kayan ciye-ciye. Karasawa
yayi kawai yana hugging din Khalid da Julde, bai
ma fara nufar Salim ba. Shi din dai ya kara so ya
karbi akwatin Nawfal din yana dan yin gaba,
Lubna sufyan
Hausabook.com 265
sallama ya sake yi wa su Khalid ya karasa inda
Salim din yake
"Ka kula musu da yarinya Bajjo, kai kace zaka
aure ta. Karka bani kunya"
Murmushi Nawfal yayi
"Ita rokonta naji kayi Hamma"
Babu wasa a fuskar Salim yace
"Kai kashedi ne nake maka"
Hannu Nawfal ya daga cikin alamar salute yana
saka Salim din girgiza kai kawai ya mika mishi
akwatin shi ya juya
"'Hamma..."
Ya kira, juyawa Salim yayi, hannu Nawfal yasa
akan kirjin shi inda yake tunanin zuciyar shi
take yana ganin Salim din ya sake bata rai
"Nagode"
Ya fadi a hankali, yasan baiji sautin muryar shi
ba, amman ya karanci godiyar akan labban shi.
Bai daiyi magana ba kamar yanda yayi
tsammani ya sake juyawa. Salim yana da
Lubna sufyan
Hausabook.com 266
wahalar fahimta, kullum nuna musu yake
rayuwar shi yasa a gaba, bai damu da harkar
kowa ba, amman a cikin kananun shiga
harkokin su da yakeyi yana nuna musu cewa
yana tare da su duk runtsi, zasu kuma iya
jingina da shi a duk lokacin da bukatar hakan ta
taso, amman su tsaya da nasu kafafuwan shine
abinda zaifi son gani
"Allah ya kula da kai Hamma Am"
Nawfal yayi addu'ar cikin zuciyar shi, yana
sauke numfashi, inda wani zaigani zaiyi tunanin
Nawfal ya leka wasu a cikin shafukan da
kaddara ta tanadarwa Salim
Kamar yaga yanda yake bukatar addu'ar
Kamar yasan kurar da take tunkaro rayuwar shi
bata wasa bace ba
Kan wayar Madina ta maida mazaunin shi tana
mikewa, dakinta ta wuce tana sauko karamar
hijab, riga da wando ne a jikinta, rigar sai a saka
irinta su hudu kafin su cikata, takalman kafarta
wasu manya ne da Daada bata san inda ita da
Lubna sufyan
Hausabook.com 267
Julde suka nemo su ba, amman masu gashine,
kamar ma kan kaza-kaza take gani daga
karshen takalman dan harda yan idanuwa daga
jiki, da tayi magana randa ta fara ganin Madina
na yawo da su a cikin gida dariya tayi
"Guda biyu ne, in dauko miki dayan Daada, zaki
ji dadin shi, ga laushi, kuma yana da dumi"
Kai ta girgiza
"Allah ya tsare ni, ke dai kiyita fama"
Ai kam kamar ta dauki shawararta, in dai tana
cikin daki to da wahala kaga kafafuwanta babu
su, ga safa ga wannan takalman.
"Zan ga Hamma a waje"
Ta fadi tana kama hanya batare ma da ta jira
amsar da Daadar zata bata ba. Da ido kawai
Daada ta bi Madina harta fice. Bata son kawo
komai a ranta akan Madinar da Salim, amman
kullum sai yazo, shi yake zuwa ya dauko ta daga
makaranta, kuma da yamma idan bai zo ba to
dai-dai irin lokacin nan zaka gan shi. Da yawan
lokutta takan dawo da ledoji yayo mata siyayya,
tayi fata kala-kala a baya da bai kasance ba, ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 268
zatayi wani akan Madina da Salim ba, koma
menene yau da gobe zata nuna.
Madina da ta fita motar Salim ta bude ta shiga
tana mayar da murfin ta rufe hadi da sauke
numfashi, jikinta har bari yakeyi. Bata taba
tunanin zata iya boyewa Daada halin da take
ciki ba sai yau, saboda wani abu da zaisa tayi
hakan bai taba faruwa ba. Asalima bata san ta
kwana da wani abu a ranta ba sai bayan auren
Nawfal, haka kawai zata nemi bacci a lokacin da
ta saba yin shi ta rasa saboda yanda tunanin shi
yake damunta, da yawan ranaku takan labe
bakin kofa a dai-dai lokacin da yake kiran
Daada taji ringing din wayar sannan ta koma ta
kwanta.
Zuciyar ta kan raya mata ta fita ta karbi wayar
su gaisa, amman sai kafafuwan ta su kasa fitar
da ita, tana daukar abin zaiyi sauki lokacin da
awanni suka shude a cikin ranaku, amman a
hankali wannan ranakun suka dinga tafiya da
satikan da suke cikar watanni har shekarar da
take ganin kamar ta rufe ido ne ta bude. Yanayin
bai barta ba, amman ta saba da shi, ta dai kasa
samun amsar dalilin da yasa take jin nisan da
Lubna sufyan
Hausabook.com 269
yake tsakanin su ya ninka na da. A gefe daya
kuma Salim ya zame mata wani bango da take
jingine da shi batare da fargabar komai ba.
Duk sanda take da wata bukata sai ta ga Salim
tsaye a gabanta yana kallon ta kamar in har
yana tare da ita babu wani abu da zatayi kukan
rashin shi, tasha tsinto kalmomi biyu a litattafai
'comfort zone' tare da Salim take ganin asalin
ma'anar kalaman, dan kamar shi din da
matsayin shi a rayuwar ta bature ya kalla ya
kirki kalaman. Shisa yau da ya zama rana ta
farko da tashin hankali ya fara yiwa rayuwarta
sallama ya zama mutum na farko da take son
rugawa wajen shi.
Safiyar ranar alhamis din tazo mata a birkice
tun bayan zuwanta makaranta suka kuma juyo
sakamon rasuwar Malami a makarantar, ba
bangaren ta yake koyarwa ba, amman mutuwar
ta daketa, sai take ta ganin fuskar shi, ta daiji
dadi daya kasance musulmi saboda ko bakomai
mutanen da zasu roka mishi gafara a wajen
Allah kuma addu'ar ta same shi suna da yawa, a
cikin su harda ita kuwa. Da yake ta saba tsara
Lubna sufyan
Hausabook.com 270
ranarta, sai lokacin ya zame mata wani abu da
bata san me zatayi da shi ba.
Shisa ta tsiri yin kwalema, share nan, goge can,
lokacin da taje dakin Daada ta sameta ta gama
shiri wai zataje jaje nan makota in da yaro ya sa
kafa cikin tuwon da aka kwashe a kwano ya
kone. Bayan ta Madina tabi tana kulle gidan,
tasan gidan da Daada take magana, akwai
mahaifiyar maigidan da take zaune tare da su,
kusan kawaye ne ita da Daada din, Madina tasan
in ta shiga zasu zauna ne suna ta hira, gara ta
kulle gidan kafin wani ya fado mata.
"Ko da ba zan dade ba kece fa, zan ga yanda
zakiyi da tsoron nan in kikayi aure"
Daada ta fadi cike da zolayar da ta saba yi mata
duk sanda zata fita. Dariya kawai tayi, tsoro ai
halal ne ko a musulunci babu inda ta ga an
haramta shi har yanzun da take zuwa Islamiyya.
Bata san ko a gaba ba, in ba nan gidan su ba,
batajin akwai gidan da zataje abarta ita kadai a
ciki ta zauna. Tunda Allah yayi mata tsoro, sai ta
ga kamar wani zai shigo ya yankata kafin tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 271
ihun da za'a aji har a kawo mata dauki. Ko da ta
koma dakin Daada ta nufa tana cigaba da aikinta
"Yanzun ji tarkacen da yake dakin nan, amman
na dakina take gani"
Madina take tsegumi tana janyo wata tsohuwar
butar tangaran mai murfi, bambanci dakin
Daada da nata bata ganin yana da wani yawa,
kawai ita Daada komai a kammale yake, ita
kuma nata a barbaje suke. Zama tayi tana bude
butar dan ganin meye Daada ta ajiye a ciki,
zazzage butar tayi a kasa tana murmushi ganin
harda wasu kudin karfe irin na da, ta dauka ta
duba, da wani hoton fasfot, duk da babu kala a
jikin shi kuma ya tsufa sosai bai hanata ganin
kamannin mutumin da na Julde ba, wata irin
kama ta ban mamaki.
Ajiyewa tayi a gefe tana daukar wata takarda da
saboda tsufan da tayi har ta fara ja, ga wani
maikon ajiya da yake jiki kamar an tsoma cikin
mai an fiddo. Zaman gilashin ta da ta gyara baisa
ta ganin rubutun da kyau ba bayan ta bude
takardar, tashi tayi tana sake kunna dayan
kwan dakin dan ta ga haske sosai:
Lubna sufyan
Hausabook.com 272
Daada,
Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina.
Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da
bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya
ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata
mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a
cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata
ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare
sauran kwanakin ta a duniya tana biyan
zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan
baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai
canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da
gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a
ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba.
Yelwa.
Ta karasa karanta suna da ya zama karshen
rubutun da yake jikin takardar, a karo na farko
tana tabbatar da yaren hausa bashi bane asalin
ta saboda yanda rubutun da akayi a cikin
harshen ya birkita mata kwakwalwa yana sa ta
kasa fahimtar shi kai tsaye, sake karantawa tayi,
wannan karin a zaune, zaman da bata san
lokacin da tayi shi ba, kamar yanda har zuwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 273
yanzun ba zata ce ga adadin yanda rubutun da
yake jikin takardar da zata zama mafarin
budewar abinda aka dade ana boye mata ba ya
dawo mata. Ta haddace kowacce kalma, ta dai
rasa ma'aunin dora nauyin da sukayi mata.
Da rarrafe ta karasa ta kwashe kayan da ta
zazzago tana mayar da su cikin butar banda
takardar da ta ninke. Butar ma mayar da ita tayi
inda ta dauko, har ta karasa share dakin, ta
koma nata ta bude littafi ta saka wasikar ba zata
ce ga abinda take ji ba, ko me tunaninta yake so
da ita ba, saboda yaki daukarta ya kaita ko ina.
Murmushi take tana jin kamar ba fuskarta ba,
amsa hirar Daada take tana rasa daga inda
kalaman suke fito mata, duk idan sautin
muryarta ya koma cikin kunnuwan ta sai tayi
mamakin yanda bai fito da alamar tambayar da
tafi kowacce yi mata yawo cikin kai ba
"Wacece Yelwa?"
Kusan har ihun wata murya take ji cikin kanta
da wannan tambayar, amman yanda akayi bata
sakko daga kan nata zuwa makoshinta ba abin
mamaki ne. Har girki tayi, duk wani abu daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 274
kamata ace tayi saida ta gudanar yau, wajen
karfe biyu da rabi wayar dakin Daadar ta hau
ruri, da yake Daada ce a kusa ita ta amsa tana
yin jim hadi da fadin
"Lafiya kalau Salim, gata nan a kusa ma"
Ta karasa tana mika ma Madina kan telfon din
"Mug..."
Salim ya kira ta dayan bangaren, muryar shi da
taji, da yanda ya kira sunan daya makala mata
kamar yasan tana boye wani abu yasa taji
gwiwoyin ta sunyi sanyi, zuciyarta ta karye
"Hamma"
Ta amsa tana yin gyaran murya jin maganar ta
fito daga kasan makoshin ta
"Kana makarantar mu ko? Banyi tunanin kiran
ka ba sam, kayi hakuri"
Tana jin yanda ya sauke numfashi a kunnen ta
"Zanyi abu yanzun, ban san lokacin da zan gama
ba, amman zan zo in ganki"
Kai ta jinjina kamar yana ganin ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 275
"Allah ya taimaka, sai kazo"
Ta san ba wani abu zai sake cewa ba shisa ta
mika ma Daada kan telfon din da ta mayar
mazaunin shi. Yanda zuciyarta ke karyewa ne
yasa ta mikewa tabar falon. Kwanciya tayi har
la'asar. Da ta fito taji ko Daada na marmarin
wani abin ta dafa mata tace mata a'a daki ta
sake komawa. Ba zatace ga abinda take ji ba,
lokacine dai yaki yi mata sauri har zuwa yanzun
da take cikin motar Salim inda ta hada kanta da
gaban motar tana sauke numfashi. Wasu
abubuwa da bata san suna daure a jikinta ba
take jin suna kwancewa a hankali yanzun.
"Madina..."
Salim ya kira ganin yanayin ta. Ta kasa dagowa,
numfashin ta da take jin daidaton shi ya kwace
mata take son nutsarwa
"Madina"
Salim ya sake kira yana jin zuciyar shi na
dokawa, bai taba ganin ta yanda yake ganin ta
yanzun ba, tunda rana da ya kira yaji kamar
yanayin muryata ya canza, baisan yanda zai
Lubna sufyan
Hausabook.com 276
tambayeta ba shisa yayi shiru, amman tana
rashin tun lokacin, kawai akwai abinda yake
dubawa ne saboda jarabawar shi ta karshe da
take gabatowa. Danma yajin aikin da akayi ta
fama da shi, da sun manta da gama wannan
wahalar. Hannun shi ya kai yana dan bubbuga
kafadar ta
"Hey Mug"
Ya fadi cikin wani irin sauke murya da baisan ya
iya ba, lallashi ba sabon shi bane ba, ko su
Khalid idan yaga alamar wani abu na damun su,
karshen abinda yakeyi shine ya fita ya siyo
musu wani abu da yake tunanin suna so yazo ya
basu, in a falo suke ya zauna da su har sai sun
tashi sun bashi waje, idan a dakin sune zai ta
tsayuwa har saiya tabbatar idan ya tafin babu
abinda zai same su, ko a fuskar su yaga alamar
suna son ya tafin. Ko Saratu da ya sha shiga
bangaren su ya jiyo sautin kukanta duk da kofa
a kulle take bai taba kwatanta shiga ba.
Zai tsaya daga inda yake zuciyar shi na wani irin
ciwo da ba zai fassaru ba har saiya daina jiyo
sautin kukan nata sannan zai tafi. Shisa yanzun
Lubna sufyan
Hausabook.com 277
yake addu'a ba kuka Madina zatayi ba, tunda
baisan yanda zaiyi da ita ba, zai sake magana ta
dago tana gyara zamanta, da yake ya kunna
fitilar cikin motar yana ganin fuskarta fayau,
babu alamar kuka tayi, yana dai so yaga
idanuwanta ne yau, shisa ya mika hannu yana
zare gilashin dake fuskarta, sai idanuwan nata
suka kankance mishi, kamar ta cikin gilashin
sun fi haka girma.
"Idanuwa ne haka Madina?"
Sai da murmushi ya kwace mata duk kuwa
yanda take jin zuciyar ta, Salim na da wannan
tasirin a tare da ita, hannu ta mika tana karbar
gilashin ta
"Bana gani da kyau Hamma"
Ta fadi tana mayarwa ta gyara mishi zama,
takardar da take hannunta ta mika mishi, da
mamaki ya karba yana warware wa, kallon
Madina yayi ta dan daga mishi kai cikin alamar
ya karanta, bai kuwa yi musu ba ya karanta din
kafin ya raba idon shi da takardar yana kallon
Madina da ta dan daga mishi kafadu
Lubna sufyan
Hausabook.com 278
"Mama na ce ko?"
Tayi tambayar da taji tsoron furtawa har a cikin
kanta tun safe, Salim na ganin firgicin da yake
cikin idanuwan ta
"Madina..."
Ya kira da wani yanayi da yasa ta kai hannuwa
tana rufe fuskarta hadi da furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Shi kan shi kalaman cikin wasikar ne suke mishi
yawo, yana harhada ma'anar su. Baije islamiyya
kamar yanda su Khalid suka ba, tunda har
yanzun yaga Khalid na zuwa, amman yayi zuwan
da ya fahimci kalaman Yelwa a cikin wasikar
'...Yanayin haihuwar ta ba zai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 18