hakoranta suka bayyana
kafin ta juya kamar tana son kara sauri wajen
ganin ta gama da wuri. Ficewa yayi daga
bangaren nasu gabaki daya yana nufar nasu
Khalid. Hannun kofar ya kama ya murza yana
shiga da sallamar da Nawfal ne ya koya mishi
yinta a ko ina zai shiga
"Daddy baka yi mun sallama ba ka shigo"
Ya kan fadi har saida ya saba da yin sallamar da
a baya bata dame shi ba, kai tsaye yakan tura
kofa ya shiga waje. Yanzun kam a kasuwa ko
shagon wasu zai shiga da yake a bude sai yayi
sallama, yana ganin yanda hakan ke siya mishi
kima a idanuwan mutane da yawa. Ba kowa a
falon sai Salim da ya kara shigewa cikin kujera
kamar yana son hadewa da ita, tv nata aiki
amman babu sauti hakanne ma yasa Julde jin
sallamar shi da Salim ya amsa can kasan
makoshi. Idan wani da baisan yaron ba yagani
zai dauki hakan a matsayin rashin girmamawa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 56
Kuma a wajen Salim ba haka bane ba, yawancin
maganar shi duk daga kasan makoshi take fita
da yanayin kamar an mishi dole dauke a fuskar
shi.
"Daddy..."
Nawfal daya fito daga dakin baccin shi jin
sallamar Daddy ya kira yana dorawa da
"Ina kwana"
Murmushi Julde yayi
"Lafiya kalau, kun tashi lafiya ko?"
Kai Nawfal ya jinjina
"Ina Khalid? Ku shirya muje gidan Daada,
amman ba kwana zakuyi ba"
Dakuna fuska Nawfal yayi
"Da ma ina so inje fa Daddy, munyi maganar
zuwan da Adee"
Kai Julde yake girgizawa
"Kwana daya to, dan Allah, gobe idan ka dawo
kasuwa saika biyo ka dauke mu"
Lubna sufyan
Hausabook.com 57
Numfashi Julde ya sauke yana dai-dai da lokacin
da Salim ya fitar da wani sauti dake nuna alamar
hirar su ta takura shi yana kara shigewa cikin
kujera. Murmushi kawai Julde yayi
"Ku shirya to"
Sai da Nawfal ya jinjina mishi kai tukunna ya
juya yana fita hadi da ja musu kofar. Nawfal
kallon Salim yayi, baisan lokacin daya yanke
hukunci dawowa bangaren da kwana da yini ba.
Shima tunda yazo hutun nan yagan shi, kafin
kaji hirar Salim zaka dade, zai iya tashi da safe
baice wa kowa komai ba, ko hanya ta hadaku
wucewa zakaga yayi kokarin ganin ya kauce
karma iskar da kuka kwaso ta hadu da ta juna,
magana ma idan yanayi kamar bakin shi cike
yake da harshe saboda yanda take fitowa.
Nawfal zai iya cewa duk da Salim na cikin
mutane shi kadai yake rayuwar shi, ko kasa shi
cikin harkar ka da wahalar gaske ya shiga. Duk
wani abu da zaisa ayi rikici Nawfal na guje
mishi, shisa tunda ya dawo yaga Salim a
bangaren da yake kira nashi ya daina zaman
falo sam, akwai tv a dakin shi idan kallo yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 58
son yi, shima zai saka sautin dai-dai kunnen
shine kafin Salim yazo ya kwankwasa mishi
yana fadin
"Ka rage volume din TV dinka Bajjo yana shigar
mun kwakwalwa"
Duk wani surutu ma shigar ma Salim
kwakwalwa yake kamar kunnen shi yafi na
kowa ji
"Anya Hamma Salim ba vampire bane ba?"
Khalid ya taba tambaya bayan ya baro dakin shi
a bangaren Nanna ya same su a falon da tazarar
shi take wajen taku goma harma da wani dan
sirqakon lungu a tsakani yana watsa musu wani
irin kallo
"Me yasa ba zakuyi magana irin ta mutane ba?
Ta ya mutum zaiyi bacci kun cika gida da ihu?"
Hada idanuwa kawai sukayi shi da Khalid suka
mike suna barin bangaren gabaki daya. A cikin
su babu wanda zaice ga rana daya da Salim ya
taba lafiyar jikin su, amman akwai marin da
yayi wa Adee kan tana wanke-wanke tana kida
da cokula a cewar shi. Amman dukkan su suna
Lubna sufyan
Hausabook.com 59
shakkar Salim din. Nawfal ya juya zai koma inda
ya shigo Khalid ya bankado kofar yana fadin
"Wai kasan wa nagani ku..."
Maganar ta koma mishi saboda idanuwan shi da
suka sauka cikin na Salim da ya dage girar shi
duka biyun, ko dan girar Salim kusan kullum a
sama take, kamar baya sauke ta, hannuwa
Khalid ya daga cikin ban hakuri yana motsa
labban shi batare da yayi maganar da sauti ba
yace
"Yi hakuri"
Yana takawa a hankali ya karasa inda Nawfal
yake ya tura kafadar shi suna nufar dakin baccin
Nawfal din da kamar jira yake Khalid ya tura
kofar dariya ta kubuce mishi
"Ban san vampire na zaune a dakin ba ai"
Khalid ya fadi da alamar dariya a muryar shi,
har mamakin ji irin na Salim sukeyi
"Daddy yace mu shirya zamu je gidan Daada"
Nawfal ya fadi har lokacin da alamar dariya a
muryar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 60
"Ni ai nayi wanka..."
Kai Nawfal ya jinjina
"Nima nayi wanka, ban dai ci komai bane ba...
Zan karya a gidan Daada kawai"
Da gabaki dayan su suke karyawa a bangaren
Nanna din, yanzun tunda kowa ya fara girma sai
suke zaben lokacin yin karin idan ba ranakun
makaranta da Julde ba zai bar su fita basu saka
wani abu a cikin su ba ko yaya ne kuwa. Nawfal
yana da kayan Tea din shi, akwatin da Adee ta
bashi nata harda katon gwangwanin madara da
bata fasa ba sai na Milo karami, da kifin wajen
gwangwani ashirin. To kuma ma ya ga Salim ya
sake kwaso wasu kayan tea din ya ajiye a
kitchen din bangaren nasu, da kofuna da yawa
ma da kananun kayan amfani, ya ga har gas din
kitchen din an hada.
"To mu jira Daddy ya fito sai mu wuce..."
Cewar Khalid yana dorawa da
"Nasan da Adee zamu je, Lukman dai ba zai bar
Nannar shi yaje wani waje ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 61
Murmushi Nawfal yayi
"Auta kam babu inda za shi"
Suna nan zaune suna hira, ta window din dakin
Nawfal da yake ta waje yake suka hango Daddy,
kusan a tare suka mike suna fita
"'Hamma sai mun dawo"
Khalid ya fadi, hannu Salim din ya daga yana
musu alamar su fita. Dariya sukayi a tare suna
ficewa, daman dan neman tsokana yasa Khalid
yima Salim din magana. Har wajen motar Daddy
suka karasa kusan a tare da Adee da take sanye
da riga da wandon da zaka iya gani saboda
hijabinta iya gwiwa ya tsaya, ta rataya jaka a
gefe sai robar take away a hannunta.
"Dare yayi sanda na gama jiya..."
Ta furta tana mikama Nawfal robar da ya karba
yana jinta da sanyi alamar a fridge ta kwana,
dubawa yayi ta kasan robar yana ganin farfesun
kifi ne ko miyar kifi, ba zai iya ganewa ba, ya dai
san taliya aka dafa jiya da dare da miyar kifin da
yasan ba zai iya ci ba dan yaga Khalid da ita,
Lubna sufyan
Hausabook.com 62
sanda ya shiga bangaren ma dan su gaisa da
Daddy ne.
"Meye kika bashi ni baki bani ba"
Cewar Khalid da ko inda yake Adee bata kalla
ba. Yanzun da suka kara hankali Nawfal yasan
Adee dare take bi idan Nanna tayi bacci ta dafa
mishi abu irin haka. Hannun shi na dama da
baya rike da robar da ta bashi ya dora akan
kirjin shi inda yafi tunani zuciyar shi take dan
nan yaji ya dauki dumi sannan ya daga hannun
yana nuna Adee da tayi murmushi, yasan ta
fahimta, bashi da kalamai in dai akan kulawarta
ne, amman tana da waje mai girma a zuciyar shi,
Allah yake roko daya bashi aron rayuwa mai
tsayi a tare da Adee dan ya kwatanta biyan ta
duka kirkin da takeyi mishi.
Su baya suka shiga shi da Khalid ita tana
shiga gidan gaba. Har lokacin da murmushi a
fuskar ta
Bata san duka labarin Nawfal ba
Amman tana hasaso rayuwar ta babu Daddy da
Nanna
Lubna sufyan
Hausabook.com 63
Tana hango dararen kadaicin da take tunanin
yana fama da shi
Ita din ko kusa da matsayi na uwa ba zata hango
ba balle ta taka
Amman in dai tana numfashi zata sama ma
Nawfal duk wani sauki da yake a karkashin ikon
ta
In dai har yaya mace na zama mahaifiyar da
mutane ke fada zata zamewa Nawfal.
Idan yaji ana cewa lokaci na gudu ada sai yayi ta
mamaki, saboda shi sam baya ganin gudun
lokaci. Musamman idan yana gida, yini daya sai
ya zame mishi kamar yini biyu. Amman wannan
karin zai saka baki idan ana maganar gudu na
lokaci, saboda da gaske kamar idanuwan shi ya
rufe a aji hudu ya bude su ya ganshi yana zana
jarabawar gama sakandire ta aji shidda da ake
kira da WAEC. Randa suka zana ta karshe sai
yake jin abin kamar a mafarki, har Julde yaje ya
dauko su bai dana jin shi kamar a mafarki yake
yawo ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 64
Sai dai ya koma kirga kwanakin da suka rage
mishi a cikin gidan. Adee ta samu gurbin karatu
a jami'ar Wudil, nisa ta sake yi musu.
"Ga BUK, me yasa sai Wudil? Quantity Survey
din ne basu da shi a BUK?"
Ya tambayeta, bai taba zuwa Wudil ba, amman
yasan kauye ce, kuma yaji wani a ajin su yana
magana cewa babu mata da yawa a makarantar,
duk wani abu da zata takura baya son shi sam.
Murmushi kawai tayi
"Ka ce mun BUK zaka je kaima Bajjo, in har can
din zaka sai in hakura da Wudil..."
Shirun da yayi murmushin Adee kawai hakan ya
fadada
"Idan kana gida zan dinga kokarin dawowa
weekend In shaa Allah"
Bai dai sake cewa komai ba, burin shi mai girma
ne, bai kai da furtawa ba. Amman nisan da zaiyi
wa gida da sunan karatu ba zai tsaya
makarantun da suka sani ba. Ya fi kowa jin
rashin Adee a cikin gidan, dan ma yanzun Julde
kudin kashewa yake basu kusan kullum, ba zaici
Lubna sufyan
Hausabook.com 65
yana da matsalar abinci ba. Mai dadine kamar
wanda Adee zata tsaya ta dafa mishi sai dai yaje
gidan Daada yake samu. Islamiyya da ya koma
yanzun bashi da lokaci mai yawa na zuwa gidan.
Yanzun ma daya taso masallaci ya wuce yayi
zaman shi yana nazarin darussan da akayi na
ranar har sai da yayi sallar Magriba da Isha'i
tukunna ya dawo gidan.
"Ina kaje tun dazun?"
Khalid da yake kwance cikin kujera ya tambaya
"In da ka aikeni"
Ya amsa yana wucewa, dakin su ya nufa ya ajiye
jakar makarantar shi, ruwa ya watsa ya sake
kaya sannan ya sake fitowa yana nufa kitchen,
fridge ya bude yana ganin robobin ice cream din
shi har biyu inda ya bar su tun daren jiya. Guda
daya ya fiddo yana mayar da fridge din ya rufe
ya karasa ya dauki cokulla har biyu ya dauraye
su, yana daukar wani plate shima ya dauraye ya
taka zuwa falon, teburin da ke tsakiyar dakin
yaja zuwa kusa da kujerar da zai zauna ya ajiye
plate din ya dora cokullan a sama yana ajiye
robar ice cream din shi a gefe.
Lubna sufyan
Hausabook.com 66
Sake komawa daki yayi ya dauko kifin
gwangwani guda biyu tukunna ya samu waje ya
zauna. Gabaki daya Khalid hankalin shi ya
mayar kan Nawfal da yake bude kifin harya juye
shi cikin plate, gani yayi ya bude robar ice
cream din ya saka cokali a ciki, tashi zaune
Khalid yayi
"Jikin ka na shan wahala a hannun ka Bajjo, kifi
da ice cream?"
In dai akan zabin abinci ne ya saba da surutun
Khalid din, bude baki Khalid yayi zai sake
magana shigowar Salim ta saka shi ya mayar ya
rufe
"Na dauka ba'a hada kifi da madara"
Salim yayi maganar cikin sigar da bata bukatar
amsa kamar yanda ya saba, kana iya amsa shi
yayi maka kallon "Da kaina nake magana, me
yasa kake amsawa?". Kowa a gidan ya koyi zama
da Salim, duk da haka kafadu Nawfal ya daga
"Har yanzun ban ci da yawan da zai mun illa
bane ina jin"
Lubna sufyan
Hausabook.com 67
Dan ba zaice ga ranar da yake hada shayi kuma
da madara yaci da kifi ba. Kai Salim ya girgiza
yana wucewa abin shi
"Da gaske abin nan dadi yake maka?"
Hararar Khalid yayi yana cigaba da cin kifin shi
hankali kwance. Yana gama cinye kifin ya mike
ya dauke plate din ya kai kitchen, yana dawowa
ya hangi Khalid da robar ice cream din shi ya
dibo a cokali yana shirin kaiwa baki, da gudu ya
karasa amman har Khalid ya kai cokalin cikin
bakin shi
"Ewww...Hamma...kace mun shine cokalin
farko..."
Wuyan shi Khalid ya rike da alamu ke nuna
dakyar ice cream din ya wuce ta cikin shi, fuskar
shi a hade take gabaki dayanta, harya ciro
cokalin kokarin tattara sauran dandanon ice
cream din daya rage a bakin shi yakeyi amman
ya kasa, hannu kawai ya iya dagawa Nawfal da
ya dakuna fuska yana jujjuya robar hannun shi
kamar zata sanar mishi idan Khalid din ya sha
abinda yake cikinta fiye da sau daya. Kurkuro
Lubna sufyan
Hausabook.com 68
bakin shi Khalid yayi amman bai daina jin
dandanon ba
"Nawfal meye a robar nan?"
Asalin sunan shi da Khalid ya sa Nawfal din
amsawa da
"Ice cream"
Yana dorawa da
"Sau daya ka sha?"
Babu abinda ya tsana irin kurbi in kurba da abu
a cikin kofi, ko kuma yana shan ice cream, ko
yana cin wani abu kazo ka dauki cokalin ka ci da
shi ka mayar a ciki, saiya ga kamar da sauran
yawu a jiki ka mayar mishi. Idan Khalid na son
ya bar mishi abu haka yake masa wannan rashin
kirkin
"Wanne irin ice cream ne wannan?"
Numfashi Nawfal ya sauke
"Chocolate mint... Me ya faru?"
Kai Khalid yake girgizawa, komai na Nawfal ya
fita daban, kamar kullum dalilin da zai sake
Lubna sufyan
Hausabook.com 69
banbanta da mutane yake nema. Kamar McLean
yayi kankara haka ice cream din yake
"Sau daya na sha, na farko kuma na karshe da
yardar Allah"
Khalid yace muryar shi na fitowa a gajiye.
Dariya Nawfal yayi
"Me ya samu ice cream din? Me ya faru? Ba dai
zaka ce babu dadi ba"
Wani irin kallo Khalid yake mishi
"Akwai dadi, a sha lafiya"
Da murmushi a fuskar Nawfal ya nufi kitchen
dan ya dauko wani cokalin, daga can dakin su ya
wuce ba sai Salim ya dawo falon ya kore su ba.
Ko da Salim ba zai fito ba lokacin baccin shi yayi,
kome zaiyi da wuri yake yi ya gama, karfe tara
idanuwan shi sun fara nauyi, har mamakin
Khalid da zai iya kai karfe daya na dare zaune
yana kallo yakeyi, kuma washegari ya tashi su
tafi sallar asuba kamar lafiyar shi kalau. Shi
kanshi zaiyi kamar an dora dutse, bacci na da
muhimmanci a wajen Nawfal.
Lubna sufyan
Hausabook.com 70
**
"Daada..."
Ya kira muryar shi can kasan makoshi, hannu
tasa tana share hawayen da suka kasa daina
zuba daga idanuwanta, ya dauka da Julde zaifi
samun matsala, sai dai soyayyar da ke tsakanin
su da take tasiri akan Julde ko yaushe ita tayi
nasara. Nawfal na ganin yanda tafiyar shi wani
gari da sunan karatu ne karshen abinda Julden
yake so balle kuma ace wata kasa.
"Cikin kudina, kai da Daada kunce ina da kudi,
in dai zasu isa..."
Julde bai barshi ya karasa ba, da wani nauyi a
muryar shi yace
"Me yasa kake tunanin kudi ne matsala ta da
tafiyar ka? Bajjo ina da kudin da zan fitar da ku
dukan ku karatu kasar waje, ba kudin bane
matsalata, nisan ka, nisan da zakayi ne
damuwata"
To ga damuwa fiye da wadda ya gani a tattare da
Julde nan shimfide kan fuskar Daada, kukan da
takeyi gabaki daya ya kashe mishi jiki, zuciyar
Lubna sufyan
Hausabook.com 71
shi daya ke tunanin ba mai raunanata kan
tafiyar ce yake ji tana mishi rawa
"Daada..."
Ya sake kira kamar hakan zai isar da sakon da
baisan ta inda zai fara fada mata shi ba. Yana
bukatar tafiyar, jin shi yake kamar yana cikin
wata yar karamar kwalba, watakila tafiyar ta
fito da shi daga cikinta, duniyar shi yar karama
ce, haka ma mutanen da suke cikinta. Ba
fadadata yake son yi ba, asalima yana jin wajen
mutum daya ya rage mishi, daya cike shikenan.
Yana dai son tafiya saboda da dalilai da ba zai
iya rabawa da kowa ba.
"Daada makaranta ce kawai fa, zan dawo... Ki
daina yi kamar na tafi kenan"
Kai ta jinjina, zuciyarta na wani irin ciwo, tafiya
ta rabata da mutane da yawa, tafiya tayi mata
sanadin abubuwa da ba zasu lissafu ba. Idan
tace ko sunan tafiya bata son ji wasu zasuyi
mamaki, amman dalilanta masu karfine. Shi da
Madina ne mutane biyu rak da suka rage mata
da take jin in dai tana numfashi ba zata bar wani
abu ya rabata da su ba. Ko da yace makarantar
Lubna sufyan
Hausabook.com 72
kwana zai tafi hankalinta ya tashi, sai da Julde
ya fada mata makarantar a cikin garin Kano ne,
duk da haka sai da taji duk satin duniya Julden
na zuwa ya dubasu.
Amman baccin kirki batayi duk asabar din
duniya sai Julde ya biyo ya sanar mata da cewa
Nawfal din na lafiya take samu nutsuwa. Yanzun
kuma yazo mata da zancen tafiya wata kasar
amurka, yana tuna mata abubuwan da ba
mantawa tayi ba, amman ta samu waje ta adana
su idan ba ranaku irin yau ba basa kwacema
adaninta sai ta basu damar hakan.
"Dan Allah Daada... Kina daga mun hankali"
Hannu tasa tana sake dauke kwallar da ta taru
cikin idanuwan ta
"Naji tafiya da sunan karatu Bajjo, tafiyar da
batayi mun dadi ba, naji tafiya da dalili da tafiya
babu dalili, duka basuyi mun dadi ba..."
Kai yake girgizawa tunda ta fara magana, ga
wani abu daya taso daga zuciyar shi yana tokare
mishi makoshi
Lubna sufyan
Hausabook.com 73
"Karki hada mu, ko a tunanin ki karki hada mu,
ba zan sake cewa daga jikin shi na fito ba.
Amman ni daban ne, ni bashi bane ba, ba zan
watsar da ku kamar baku da muhimmanci a
rayuwata ba, karatu zan tafi, karatu zanyi in
dawo Daada... Zan dawo"
Ya karasa cikin dishewar murya, ba zai ce ga
ranar karshe da yayi kuka ba, amman yanzun
alamun shi yake ji. Ya san zafin da Daada take ji,
amman baya son inda tunaninta yake son
daukarta ya kaita balle ta ja shi su tafi tare.
Shafine daya dade da rufewa. Abinda ya wuce ko
kayi tunani a kai ba zai canza komai ba, shisa
yake zabar barin shi inda yake, a matsayin
abinda ya wuce.
"Zan dawo Daada... Ni bashi bane"
Ya sake fadi, murmushi tayi mai sauti duk da
kukan da take ta kokarin tsayarwa. Yanda
Nawfal yake jaddada bambanci da yake tsakanin
su da Bukar na karya mata zuciya. Kila tsayin
shekaru yasa shi manta muryar Bukar da take ji
a cikin tashi muryar, duk idan zai shigo gidan da
sallama sai zuciyarta ta doka a cikin kirjinta, ko
Lubna sufyan
Hausabook.com 74
shigowa yayi fuskar Bukar take gani, ko a dabi'a
bambanci da yake tsakanin su ba mai yawa bane
ba. Ba ta da karfin fada mishi haka, ko tana da
shi ma ta ina zata fara?
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi"
Ta furta tana saka Nawfal sauke numfashin da
yake rike da shi
"Duk karshen shekara fa anan zanyi shi In shaa
Allah..."
Kai Daada ta jinjina, zuciyarta taki natsuwa da
tafiyar, in da zai hakura zata fi son haka. Da tana
jin ta isa ta hana shi tafiyar zata hana ko dan
gudun da takeyi na kar tarihi ya maimaita kan
shi.
"Daada"
Nawfal ya kira, baya son yanayin da yake cikin
idanuwan ta da kan fuskarta
"Ina Madina? Ba tace anyi hutun islamiyya ba?
Ina taje?"
Ya tambaya cikin son sauya maganar gabaki
dayan ta, fuskarta Daada ta goge sosai, dan har
Lubna sufyan
Hausabook.com 75
gefen zaninta ta kama tayi amfani da shi. Sai da
tayi gyaran murya sannan ta amsa Nawfal din
"Nan bayan gida suke taron suna gobe idan
Allah ya kaimu, shine taje tayi musu kunshi, tun
jiya ma take tayi"
Dan dakuna fuska yayi
"Kin sansu ne Daada, kince jiya ma taje fa"
Kai ta jinjina mishi
"Bata nisa ai, suma dan ana mutunci da sai dai
su same ta a gida....baki ma nake gudu, kowa
zancen kunshin ta da kuma karancin shekaru
yakeyi"
Numfashi Nawfal ya sauke, dole za'ayi magana,
idan har kalar zanukan da yake gani tanayi ne a
littafi, tun ba yanzun bama idan yazo ya same ta
tana aikin da aka basu a makaranta, littafin duk
da zai dauka ba zaka rasa yar flower da ta zana a
jiki ba. Idan yace
"Madina ana ina kika ga wannan zanen?"
Zata amsa shi da
Lubna sufyan
Hausabook.com 76
"Ba ko ina fa, kawai na zana ne"
Yanzun da ta dan fara hankali ne take ware
litattafan da take zanen a ciki daban dana
makaranta. Yanzun gashi alamu sun nuna
kunshi zai iya zame mata sana'a. Kawai baya son
ta da zuwa wani waje da sunan kunshi ne, kowa
yazo gida ya same ta. Kasa hakuri yayi sai da
yayi wa Daada mitar
"Bajjo nace maka dan makota ne kawai shisa
taje, karka isheni dan Allah... Ka fita ka tambaya
gidan su Salaha, ka kirata ka rabu dani"
Shiru yayi yana gyara zaman shi a kujera, zai dai
jira tazo ya ganta sai ya tafi. Alawoyin daya siyo
da hannun shi yake son ya bata, ba kwana zaiyi
ba, yanda yake lallaba Julde ba zai sake
tambayar shi wani abu ba har yabar kasar, ciki
kuwa harda kwana gidan Daada.
"Rochester institute of technology"
Sunan makarantar ya fado mishi a rai yana saka
shi sake sauke numfashi a karo na ba adadi tun
wayewar garin. Wani yanayi yake ji tunda ya ga
hotunan makarantar a Café din da yaje domin
Lubna sufyan
Hausabook.com 77
yin binciken makarantar da zatayi dai-dai da
ra'ayin shi, daga hotunan yake jin kamar wani
abu mai girma da ya wuce karatu zai faru da shi
a kasar New York da take yankin amurka, a
cikin makarantar da sunan ta kawai ya sa
murmushi kwace mishi.
*
"Sai yanzun kake dawowo Julde? Karfe biyu uku
saura? Ka kasa yima kanka fada, idan anyi maka
ba zaka saurara ba"
Muryar Saratu ta daki kunnuwan shi, da alama a
hanyar da zata hadaka da dakin baccin su take
tsaye, sake rakubewa yayi jikin bangon kitchen
din yana dana sanin shigowar da yayi. Wani irin
kunnuwa gare shi da komin baccin da yakeyi
takun tafiya idan akayi kusa da kofar dakin shi
saiya bude ido. Ko dakin da yake kusa da nashi
da Lukman ne a ciki yasha shiga da dare ya
watsa mishi zagi saboda yana buga kofar
bandakin da yake cikin dakin idan ya farka zai
shiga.
Fadan su Julde da tun bashi da hankalin gane
inda ya dosa ya sha tashin shi cikin dare. Daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 78
fara hankalin gane yawancin maganganun su
saiya ke tsintar kan shi da kallon Julde da wasu
irin idanuwa na daban, yana kuma cika da
mamaki ko da yaushe na yanda yake Daddyn su
a gaban su, yake cikin rigar mutunci da kamala
idan yana gaban su, amman sai ya cire ta ya
yarda daga yayi tunanin sun dauke idanuwan su
daga kan shi. Mutuncin da suke tunanin yana da
shi, mutuncin da suke ganin zasu daki kirji a kai
a waje shine yake zubarwa da duk rana.
"Meye a jikin matan nan da kake bi da ni na
rasa?"
Maganganun Saratu kenan da suka kasa gogewa
daga cikin kunnuwan Salim
"Idan na miki bayani ba zaki gane ba, idan ba
kafafuwan ki kika saka a takalmana ba..."
Shine amsar da Julde ya bata wani dare da ba zai
tuna a cikin wacce shekara ko wata yake ba,
amman dare ne a cikin dubban darare da ba zai
taba mantawa da shi ba. Saboda dare ne da
wayewar garin shi ta zo mishi da wani sabon
al'amari. Yana son Daddy, soyayya da ba zai taba
iya kwatanta yawanta ba, shisa yake so ya
Lubna sufyan
Hausabook.com 79
fahimce shi, fahimtar da yake kiran Saratu ta
kasa mishi ita, tabbas ba zata iya saka
kafafuwanta a takalman Julde ba, amman shi zai
iya. Ba shi da kyawun sauran yaran gidan, akan
ce Khalid duk yafi su kyau. Shima ya yarda,
amman ya fi kowa hasken fata, sannan kuma
dogo ne, irin dogayen da ko a cikin masu tsayi
sai ka dade baka gan su ba.
Kuma da yake da tsayi shi din ba siriri bane,
dirarren namiji ne da tun yana sakandire yake
kula da yanda yan mata suke son magana da shi,
hayaniyar da baya so take saka shi share su.
Amman tunda ya samu gurbin karatu a jami'ar
Bayaro bangaren likitanci sai hakan ya kara
haska shi a idanuwan mutane da yawa, baya
mu'amala da kowa a ajin, sallama ce take
rabasu, amman tun sakamon jarabawar su ta
farko da aka kafe ya zamana shine a saman
kowa wajen samun maki yasa mutane suka kara
sanin shi.
Yanda duk yakan so zamewa sai sun saka shi
yayi musu bitar wasu cikin darussan da sukan
yi, musamman ma wa'anda suka hada da lissafi.
Mata bashi yake kula su ba, sune suke kula shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 80
Ranar farko da yayi watsi da duk wani gargadi
da zuciyar shi take mishi akan abinda ya
kudurci yi tun safiyar da zai fita bayan yace wa
Saratu
"Zan kwana a makaranta yau Nanna, akwai
abubuwan da zanyi"
Bai san ya akayi bata ji muryar shi na rawa ba,
da kuma tsoron da yake shimfide a cikin
idanuwan shi, watakila da ta tambaye shi
menene abinda zaiyi a makaranta a ranar daya
canza komai, amman bata tambaya ba
"Allah ya tsare, kar dai ka zauna da yunwa"
Shine amsar daya samu, daya hadu da Khalid ma
a hanyar fitar shi, gefe Khalid din ya rabe ko
magana baiyi mishi ba. Shidin ba ma'abocin
ciye-ciye a waje bane ba, ko zai yini a makaranta
ruwane zai siya yayi ta sha. Ko yana gida idan
zaiyi kyakkyawan karin safe zai iya kaiwa dare
bai sake saka komai a cikin shi ba
"Dogaye da cikin zani aka sansu, amman kalli
dan abincin da ka zubo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 81
Julde kan tsokane shi, wani lokacin har Saratu
na shiga
"Kuma fa tun abincin safe banga ya kara cin
komai ba, da abinci ke saka jiki yaron nan tsayin
nan ma ba zaiyi ba"
Murmushi yakan yi ya wuce su, tunda da
wahalar gaske kaga ya zauna anci abinci dashi
gabaki daya, baya son yin zagi a gaban su Julde,
to kuma ko Lukman saiya saka shi yayi magana
saboda yanda yake tauna abinci kamar yana cin
karfe. Duk kudin da Julde zai bashi na kashewa
da kuma na hidimar makaranta bai cika amfani
da su ba. Idan Adee tazo gidan yafi kashe kudin
shi, tunda in taga zai fita ba zata rasa cewa ya
siyo mata wani abin ba.
Wata yarinya yar asalin garin Kaduna, kabilar
Bajju ce ta manne mishi, yana aji biyu tana aji
hudu ko a lokacin, ta sha kai tsaye ta fito mishi
da asalin abinda take so daga wajen shi, tunda
tasan ko hauka take soyayya a tsakanin su ba
zata yiwuwa ba, idan nashi addinin ya amince
mishi auren mabiyiya wani addinin, ita nata ba
zasu amince ba, kuma ga bambanci shekaru a
Lubna sufyan
Hausabook.com 82
tsakanin su. Shisa itace zabin farko da yake da
shi. Harya gama darasin shi karfe shidda na
yamma yana jin shi kamar akan allurai, karfe
tara na dare suka yi da ita.
A masallacin makaranta yayi sallar isha'i, da
suka hada idanuwa da dalibin da yayi musu
limancin da sauri ya sauke nashi, saboda ya
tsargu, sai yaga kamar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 18