daya ya taba yankewa farce,
sam baya son yaga kumba ta taru a hannun
mutum, yana mishi kazanta ba kadan ba.
"Kalli farcen ka Bajjo"
Ya fadi bayan Nawfal din ya mika mishi remote
din daya bukata
"Ni banga mai gyaran farce ba, ni kuma ban iya
yankewa ba"
Zai tuna yanda yaja karamin tsaki, yana
mamakin yanda kato kamar Nawfal zaice bai iya
yanke farcen shi ba, menene a ciki? Ka sa nail
cutter din ka datse? Shi kusan duk kayan shi
zaka samu nail cutter a ciki, in dai ya gani saiya
siya, ko a mota yana da sunfi biyar, baya so ma
ya zo ya nema ya rasa. Nawfal din ya sa yaje daki
ya dauko ya dawo
"Kai dai katon banza ne Bajjo"
Ya furta yana kama yatsan Nawfal din da yayi
dariya kawai. Ya dauka ranar ce ta farko kuma
ta karshe, sai yanzun da yake rike da na Madina,
Lubna sufyan
Hausabook.com 335
daya bayan daya haka ya kama yana yanke mata
harya gama tsaf
"Kafar fa?"
Batayi musu ba ta zare safarta guda daya tana
mika mishi kafar
"Me yasa kike rufewa?"
Ya tambaya ganin kafar tas, ga kunshin jan lalle
da tayi. Ba zai yiwu ace idanuwa shi bane kawai
suka ga kyawun kafarta, idan yana da irin
wannan kafar baiga dalilin da zaisa ya dinga
kunsheta cikin safa ba
"Bana so tayi kura ne fa, iska yana shigar mun
kuma"
Numfashi Salim ya sauke, farcen kafar bai wani
taru ba, idan na shi ko bai kai haka ba zai yanke,
amman kafar ta Madina ce, bai yarda da kanshi
cewa zai tsaya a riketa ba kawai
"Na kafar bai taru ba ai..."
Kai ta jinjina mishi tana janye kafarta ta mayar
da safar, dan yaji yana wani abu da hannun shi
da yake kaikayin son taba kafarta yaji ko
Lubna sufyan
Hausabook.com 336
laushin da yake gani a idanuwan shi zaiji shi har
a tafin shine ya sa yabi duka farcen daya yanke
mata yana tattara shi ya saka a hannun shi guda
daya ya mike ya nufi kitchen, ya kuwa yi sa'a
akwai kwandon shara a ciki, ya zuba ya karasa
sink ya wanke hannun shi, sai da ya bude fridge
ya sake shan ruwa ya dan tsaya ya mayar da
numfashi tukunna ya fito. Yanayin da yake ji ma
ba zai iya zama ba
"Tafiya zanyi"
Ya fadi da wani sanyin murya da ya sa Madina
kallon shi
"Tun yanzun?"
Ta furta, kai ya daga mata
"Baku gaisa da Daada ba"
Sai daya lumshe mata idanuwan shi yana sake
bude su, tukunna ya girgiza kai
"Ki ce ina gaishe ta"
Mikewa Madina tayi, daman tace mishi ne ba
dan ta sa rai zai amince ba, jiya ma sa'a taci bai
musa ba ya shigo suka gaisa da Daadar, tama fi
Lubna sufyan
Hausabook.com 337
alakanta yardar shi da son sake duba jikin
Daadar tunda taji ya mata wasu yan tambayoyi
kan yanda take jin jikin. Shi ba ko yaushe yake
son gaisawa da kowa ba, ko su Julde ma yana iya
sati banda
"Daddy..."
Ko
"Nanna"
Da zai furta cikin sigar gaisuwa ya wuce, wata
gaisuwa mai tsayi bata hada su ba, Khalid ma da
suke bangare daya, yana iya gaishe da shi ya
wuce batare daya amsa ba, ranakun daya amsa
din kuma idan sun sake haduwa da yamma sai
Khalid din yace zai kara gaishe da shi
"Wai ba ka gaisheni dazun ba?"
Ya kan fadi a zafafe, amman ko a jikin Khalid, da
dare ma in ba ya watsa mishi zagi ba saiya kara
gaishe da shi, baya so, ko kadan, tunda sun ga
juna ai ya wadatar, kowa ya ga lafiyar kowa,
meye na wahalar motsa labba in ba neman
surutu da sassafe ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 338
"Sai munyi waya ko?"
Madina ta bukata ganin ya shiga motar shi baice
mata komai ba, yau yan rashin surutun sun
motsa mishi, kai kawai ya daga mata yana jan
motar shi, tsaye tayi da murmushi a fuskarta
harya bace ma ganin ta. Hamman ta kenan,
kamar mai aljanu, lokaci daya suna cikin hira
zaiyi dif kamar bai taba surutu da ita ba, duk
abinda zatace da kai zai ta amsa ta, karshe ma
yace mata shi tafiya zaiyi, ko da wasa ranta bai
taba baci ba tunda ta san haka yake, shisa
yanzun ma ta koma cikin gida abinta, idan bai
kirata ba, ita zata kira shi.
Da farko tayi tunanin bugun da take ji cikin
kanta kwakwalwar tace take kokarin yaki don
samun hanyar fita daga kokon kanta bayan
shafe tsayin daren da littafi rike a hannun ta, ba
karamin mamaki tayi najin kiran assalatu a
kunnen ta ba. Dakyar ta karasa azkar tana zuwa
ta gaishe da Daada da fada mata kan ta na ciwo
zata kwanta, ta kai wasu dakika kafin ta fahimci
Lubna sufyan
Hausabook.com 339
hayaniyar ba daga cikin kanta bane ba, bugun
kofa ne da yake fitowa daga wajen dakin
"Ughhh"
Ta fitar da wani sauti daya fito daga makoshin
ta, me yasa yanzun? Duk ranaku me yasa yau?
Me yasa sanda take matukar bukatar jin shiru
don samun rama ko kadanne daga cikin baccin
da tayi sakacin rasawa a daren jiya? Hannu ta
kai gefen gadon ta in da tasan gilashinta yana
nan ta dauka ta saka a fuskarta ta batare da ta
bude idanuwanta ba, dakyar ta iya sauko da
kafafuwanta daga kan gadon tana jin kanta
kamar an dora jakar kaya saboda nauyi.
Ba karamin yaki tayi da jikin ta kafin ya yarda ta
rabashi da gadon ba, tana samu ta bude
idanuwanta ta nufi hanyar kofar da bugunta
yake ta karuwa. Sai da tayi wata hamma kamar
da bakinta zata bude kofar sannan ta mika
hannu tana murza hannun kofar tunda ba
mukulli bane a jiki. Kafafuwan shi ta fara gani,
babu takalma, sai alamar wandon farin yadin da
yake sanye da shi, ta kasan gilashin tasa hannu
tana murza idanuwanta, ta san mai kafafuwan,
Lubna sufyan
Hausabook.com 340
tana son dai tabbatar da ba bacci bane yake
sakata gane-gane.
"Hamma kafar ka kamar ta mata, zatayi kyau da
kunshi"
Maganar da ta taba fada mishi na dawo mata,
tana sakata daga kanta ta sauke shi kan fuskar
Nawfal da yake tsaye ya harde hannayen shi a
kirjin shi yana kallon ta da murmushi a fuskar
shi
"Hamma..."
Ta kira kamar wadda tayi gudu saboda
mamakin ganin shi
"Daada tace kan ki na ciwo, nace karya kike,
bacci ne bakiyi ba kin tsaya karatu"
Dariya tayi, kafin tayi murmushi mai sauti, tana
sake wata dariyar saboda ba zatace ga abinda
take ji ba, cikin su dai harda sautin bugun
zuciyarta da take jin ya karu, da yakan karu ko
da tunanin shi tayi, ko kuma taci karo da sakon
shi a wayarta kamar yanda sukan yi magana ko
da ba kullum bane tunda tayi tata wayar.
Lubna sufyan
Hausabook.com 341
"Hamma..."
Ta sake kira a karo na biyu sauran kalaman na
makale mata, ko jiya ya tambayi ya take ita da
Daada, amman baice mata zaizo ba
"Ki koma baccin ki, zan ganki ne kafin in wuce"
Yanda ta zare mishi idanuwa yasa shi girgiza kai
yana dariya
"Gida zanje in huta, daga airport nan nayo... Zan
dawo sai anjima..."
Nata kan ta jinjina mishi da murmushin da yaki
barin fuskarta har lokacin. Tana kallon shi har
ya juya, tana jin tarin maganganun da take son
fada mishi, amman ta rasa ta inda zata fara
"Hamma!"
Juyowa yayi
"Sannu da zuwa"
Dariyar shi ya sake yi, sai ta ga kamar ya kara
canzawa, kamar shekaru sun nuna a jikin shi, ya
kara yi mata girma. Ba kuma gashin daya bari a
fuskar shi bane kawai, harda wata kamala da
Lubna sufyan
Hausabook.com 342
take tare da shi ko a yanayin takun shi ba wai
iya fuskar kawai ba. Har ya fita daga falon tana
kallon shi ta kasa komawa cikin daki, sai ma
kofar da ta rike tana lilo a jikinta batare da ta
sani ba. Lokacin da ta raba jikinta da kofar
dakin Daada ta nufa tana samun ta a zaune rike
da Qur'anin ta da Hizb biyu ne.
"Daada Am"
Ta furta cike da farin cikin da take ji ya cika
zuciyar ta taf, ta karasa cikin dakin tana zama
gefen Daada hadi da dora kanta a kafadarta
kafin ta zame gabaki daya tana kwanciya a jikin
Daadar
"Hamma ya zo"
Cewar Madina tana rufe idanuwanta, dayan
hannunta Daada takai tana zare ma Madina
gilashin da yake fuskarta
"Dagani ki koma kan gado"
Batayi musu ba ta tashi tana jan jikinta zuwa
inda tasan gadon yake badan tana ganin komai
yanda ya kamata ba, tunda babu gilashinta.
Numfashi ta shaka, hancin ta na cika da kamshin
Lubna sufyan
Hausabook.com 343
da dakin Daada ne kawai yake yin irin shi, wani
dan turare ne madara da tun tashin ta tasan
Daada na amfani da shi, in ta diba ta shafa sai
taji kamshin bai mata a jikin ta ba, ta daifi son ta
shigo dakin Daada ta kwanta ta shaki kamshin
anan, ko ta kwanta a jikinta, sai taji shi ya
bambanta, har tunani take ko wasu mutanen na
da nasu kamshin ne.
Dan in dai hakane to da Salim da Daada suna da
wannan kamshin nasu na daban, ita bata da
tarar turare, kowanne iri ya sha gabanta amfani
takeyi da shi in dai taji yayi mata dadi, tana da
su kala-kala, Adee ma in dai zataje tayi mata
kunshi bayan kudin da sai sun kai ruwa rana
take karba sai ta hada mata da turaruka, Julde
kan siyo mata shima, haka Daada, Salim kan shi
ba zata kirga adadin lokuttan da ya bata kyautar
turare ba, duk kuwa da ta littafai ta shallake
kowacce kyauta da take giftawa a tsakanin su.
Ita kam tasan bata da wani tsayayyen kamshi,
zata iya jera sati kowacce rana da kalar turaren
da zata fesa, amman banda Daada da Salim,
kamshi daya sukeyi ko da yaushe, in dai bana
jikin su bane ba, to ba karamin kokarin su take
Lubna sufyan
Hausabook.com 344
gani wajen yin amfani da kalar turaren da har
ya zame musu jiki haka ba. Nawfal ba zata
tantance yana kamshi ko bayayi ba, saboda
kamshin shine karshen abinda yake zuwa mata
duk in zata gan shi, takan samu bugun zuciyar ta
daya kan karu ya koma mata dai-dai ne, zuwa
lokacin kuma sun shiga wata hirar da take saka
mata manta duk wani abu da yake wakana a
wajen abinda suke tattaunawa.
"Me kika ci?"
Madina tayi tambayar a tsakanin hammar da ta
subuce mata
"Kwai na soya na sha shayi"
Sake gyara kwanciya tayi, tasan akwai ruwan
zafi a flask tunda ita ta dafa da daddare, kuma
Julde da yazo ya kawo musu biredin da tafi so
mai kwakwa, shisa ma ta koma baccin ta bayan
tayi sallah dan tasan Daada zata sha shayi babu
wani abu da zatayi banda share-share in ta
gama baccin. Lumshe idanuwan ta tayi, Daada
na kallon ta, ko ba bacci takeyi ba yanzun da
babu makaranta sai takai karfe tara na safe bata
Lubna sufyan
Hausabook.com 345
karya ba, yau gashi goma na neman yi. Baccin
kuwa Madina ta koma dan shine a idanuwanta.
**
A gidan Daada yabar akwatin shi saboda ba zai
iya daukar kayan ba a yanda yake jin shi. Jakar
ratayawar kawai ya dauka. Kudin da ya sallami
mai mashin din daya kaishi gidan daga airport
ma a wajen Daada ya karba, haka wanda zai
kaishi Hotoro. Murmushin da yayi ma maigadi
ma yanajin yanda ya bayyana kan fuskar shi da
duk gajiyar da yake tare da ita kafin ya wuce shi
yana kara ma takun shi sauri. Harya daga hannu
zai kwankwasa kofar yaji muryar Salim cikin
kan shi
"Dole sai kun kwankwasa zaku shigo?"
Murmushi yayi yana kama hannun kofar da
tunanin watakila Salim din ma yana falon.
Tunanin shi baiyi karya ba kuwa, zaune Salim
din yake ya jingina bayan shi da kujerar, hannun
shi na rike da remote, yanda idanuwan shi suke
a lumshe yasa Nawfal tura kofar a hankali dan
yaga kamar bacci yake. A hankali ya karasa
shiga cikin dakin, farar rigar da take kan
Lubna sufyan
Hausabook.com 346
hannun kujera ta tabbatar ma da Nawfal din
Salim daga wajen aiki yake
"Ina jin idanuwan ka a fuskata"
Salim yai maganar yana sa Nawfal ja da baya
saboda ya dan tsorata shi
"Hamma mana..."
Ya furta yana saka Salim din bude idanuwan shi
daya sauke su kan Nawfal
"Sai ka gama kare mun kallo zaka wuce? Me
yasa mutum ba zaiyi bacci a nutse a falon nan
ba?"
Kallon shi Nawfal yake yana murmushi kafin ya
bude hannayen shi yana nufar inda Salim yake
zaune hadi da fadin
"Na dawo lafiya, kuma nima nayi kewar ka
Hamma"
Yanda Salim din ya zaro idanuwa yana kaucewa
ganin da gaske Nawfal rungumar shi zaiyi yasa
Nawfal din sauke hannayen shi yana kwashewa
da dariya, har kirji Salim ya dafe kamar yaga
wani babban abin tashin hankali, wucewa ciki
Lubna sufyan
Hausabook.com 347
Nawfal yayi ya karasa dakin su, komai a hargitse
yake, babu datti dai, amman ko ya rantse
bayajin zaiyi kaffara, anfi wata rabon da a gyara
gadon. Kwanciya kawai akeyi ana tashi, da zanin
gadon da bargon duk sun hade sun cakude waje
daya. Numfashi ya sauke yana zame hannun
jakar shi daga kafada ya sauke ta kasa.
Sai da ya fara rage kayan jikin shi tunda farin
yadi ne manyan kaya. Yabar singileti da gajeran
wando tukunna ya hau gyaran dakin, ya dauko
wankakken zanin gado ya shimfida, wannan din
dama wasu kayan Khalid din da yayi tunanin
masu dattine ya tattara yana saka su cikin
kwandon da ya ajiye a dakin don zuba kayan
dauda da Khalid baya amfani da shi. Har shara
ya sake ya dauki turaruka kala biyu ya fesa.
Wanka ya shiga ya fito, wata singiletin ya samu
cikin jakar shi da gajeran wando ya saka, da
yake babu kaya suna gidan Daada cikin kayan
Khalid ya samu wata bakar riga marar nauyi ya
saka a jikin shi, bai wani bi takan wando ba dan
bayajin Khalid na da wandon da zai mishi.
Yanayin jikin su ba daya bane ba, yafi Khalid
tsayi, kuma ya fishi jiki. Kafafuwan Khalid sosai
Lubna sufyan
Hausabook.com 348
suke mishi kama da sandar snooker, amman bai
fada ba saboda Khalid zai zage shi. Kitchen ya
nufa saboda yunwar da yake ji, banda shayi
baiga wani abu da zai iya ci ba, yunwar da yake
tare da ita tafi karfin shayi. Shisa ya fito falon
wajen Salim da yanzun ya kwanta kan doguwar
kujerar yana fadin
"Hamma ka bani mukullin motar ka da kudi in
fita in siyo wani abu, yunwa nake ji"
Hannu Salim yakai ya laluba kujerar da yake
kwance a kai yana mika ma Nawfal din mukullin
"Wallet dina na cikin motar, akwai kudi a ciki"
Karba Nawfal yayi
"Zan taho maka da wani abu?"
Numfashi Salim ya sauke
"Ka kyaleni Bajjo"
Juyawa Nawfal yayi yana komawa dakin su,
dakyar ya iya samun wani 3 quarter da yake
tunanin na shine ya saka ya fita. Cikin abokan da
yayi yan Najeriya acan sai yaji suna maganar
yanda suka ga komai ya canza da sukaje gida,
Lubna sufyan
Hausabook.com 349
har wasu na nuna kamar aiwatar da hidimar
yau da gobe a kasar Najeriya tana musu wahala.
Da idanuwa Nawfal yakan bi su kawai. Saboda in
yai magana tashi zata iyayin zafi, duka shekarar
su nawa a kasar wajen? Shekarun da sukayi a
Najeriya ya ninka wanda sukayi a can.
Karatu ya kai shi, yanzun kuma daya kammala
ya dawo, yana da tarin burukan da yake son
fitowa da su daga cikin kan shi, shisa ya dawo,
shisa bai bata lokaci ba duk kuwa da yanda yake
ganin son hakan a idanuwa Murjanatu. Zaman
su basu fara shi da boye-boye ba, ta sani, tun
farko ya fada mata zaman kasar waje ba nashi
bane ba, ta yarda, ta aminta da inda duk ya saka
kafafuwan shi zata bishi.
"Turai na tana tare da kai Gidado, in da duk zan
saka kafa idan taka bata biye ba zanji dadi ba,
zan fi so ace ka cire kafar ka ne a wajen kafin in
dora tawa"
Ba zai manta yanda ya riketa a jikin shi ba,
kamar yanda kalaman ta suka samu wajen zama
a zuciyar shi. Bai bata lokaci ba, duk da yana jin
shi kamar dan koyo saboda yanayin tukin nan
Lubna sufyan
Hausabook.com 350
da can ba daya bane ba, taka manyan dokokin
tuki ba wani abu bane a wajen mutane da yawa
a Najeriya balle kuma wasu kananu, ya sha zagi
yafi a kirga daga fitar shi zuwa dawowar shi,
dariya kawai suka dinga bashi. Sai da ma ya
tsaya inda yaga alamar ana saida kati ya siyi
sabon sim din MTN ya kuma siyi katin da zai
saka a ciki.
A hankali ya tura kofar dakin ya shiga, sai dai
Salim baya falon, shisa ya wuce dakin su. Zagi
zai sha idan yace yaje ya kai mishi mukullin
mota ko da kuwa ba bacci yakeyi ba. Dankali ya
siyo soyayye da gasasshen kifi sai ice cream
roba biyu, canjin da ya rage ma Salim a wallet
din gabaki daya dari takwas ne. Ba magana zaiyi
ba ya sani, ko da kudin sun fi haka, Salim din ya
koya musu kashe kudin shi kamar suna kashe
na su. Ko motar shi ka shiga, ko dakin shi,
abinda duk yai maka in kasa hannu ka dauka
Salim ba zai kalle ka ba.
Sosai yaci ya koshi, ya dauki dayar robar ice
cream din shi ya kai cikin fridge yana komawa
daki. Wayar shi ya dauka ya ciro sim din shi
yana saka MTN din, ya kumayi loading din katin,
Lubna sufyan
Hausabook.com 351
data ya siya saboda zaifi mishi sauki yayi ma
Murjanatu magana ta whatsapp, in yaso ita sai
ta kira shi daga nata bangaren. Yana budewa
kuwa sakkoninta suka fara shigo mishi, sunfi
goma, biyu daga cikine na tambayar lafiya da ko
ya sauka lafiya, sauran na yanda take kewar shi
ne. Murmushi yayi, yana amsa kowanne a ciki.
In tana haka wani sai ya dauka ita kadai take
kewar shi, idan yace mata yanda duk take ji bai
koyi rabin abinda yake ji ba sai tace zatayi mishi
gardama. Sake tura mata wani sakon yayi yana
fada mata zai kwanta, zai kuma saka wayar a
silent. Dan karta kira ta ga bai dauka ba. Dan
kan shi ya fara nauyi, kan gadon ya hau yaja
bargo yana rufe kafafuwan shi hadi da lumshe
idanuwan shi kafin bacci mai nauyi ya dauke
shi.
*
Ba sai wani ya fada mishi ba, yanayin yanda
yaga dakin tsaf ya san aikin Nawfal ne.
"Cikin satin nan fa nake son dawowa"
Nawfal din ya fada mishi
Lubna sufyan
Hausabook.com 352
"Allah ya bamu aron lokacin"
Shine amsar da ya bashi, idan ya tambaye shi
cikin satin wace rana zai iya cewa shima bai sani
ba. Kawai abinda ya sani shine cikin satin zai
dawo. Da wahala Nawfal ya tsayar maka da
lokaci, ko ya sakama abu lokaci, zai dai fadi
abinda yake hasashen zai iya faruwa. Basu kuma
sake maganar ba dan lokacin duk da zasuyi
waya ko suyi chatting sai yayi musu karanci,
zantukan su ba masu karewa bane ba. Da shi ya
wuni a wajen aiki yau, duk wani abu da za'ace
maka alfarma da kudi basa yin shi a Najeriya zai
iya karyatawa.
Dan yagani akan bautar kasar shi, Julde kawai
ya sanarwa baya son barin garin Kano, camp din
ma da ake zama shi bai zauna ba, a ASAD
pharmaceuticals ltd da yake nan Kano yayi
bautar kasar shi da bai shige watanni da
kammalawa ba, kuma sai yayi sa'ar samun
gurbin aiki tare da su, ya karba tunda albashin
babu laifi yana da kyau. Ba nan yake hari ba,
asibitin Aminu Kano yake so, zai kuma nema da
zarar ya kammala digiri din shi ta biyu da yake
jiran a fara siyar da form ya nema.
Lubna sufyan
Hausabook.com 353
Tunda yana hangen kacokan abincin shi a bokon
yake gara ya zage dantse ya nema da kyau, kafin
ya sauke numfashin da ya shaka an kwankwasa
kofar
"Shigo"
Ya furta yana kwance agogon da yake daure a
tsintsiyar hannun shi
"Kabani charger din ka Khalid, na bar tawa a
asibiti"
Jikin bango inda socket yake Khalid ya karasa
yana ciro cajar, shisa yake da guda uku, daya a
mota, daya a gida dayar kuma a office din shi
dan gudun samun irin wannan matsalar tunda
ya san halin shi da mantuwa. Abu muhimmi ma
mantawa yake balle kuma wata cajar wayar da
in ba kiran shi akayi ba saiya wuni baibi takanta
ba
"Dole sai kayi zanzaro?"
Salim ya tambaya da murmushi a idanuwan shi
duk da yanata kokarin ganin bai karasa kan
labban shi ba, kugun shi Khalid ya kalla kafin ya
daga kai ya kalli Salim
Lubna sufyan
Hausabook.com 354
"Me zanzaro na yayi?"
Kai Salim ya girgiza, idan yayi magana dariya
zaiyi, kwanaki yaga Lukman na kallon wani
cartoon a bangaren Saratu, ta gefen ido yaga
giccin wani a ciki sai da ya dawo baya ya kara
kallo da kyau, ya kwana biyu ko shi kadai yake
zaune sai yayi dariya saboda kamar sun kalli
kugu da kafafuwan Khalid ne kafin suyi zanen.
Har yanayin belt din da yake da yakinin sai da
Khalid ya kara huda a jiki sannan ya zauna. Duk
gidan babu siriri irin Khalid, ya gama
makarantar amman yaki yin kumari.
Cajar ya karba yana share kallon rashin
fahimtar da Khalid yake mishi, har ya juya ya
dawo
"Randa duk ka zo asibitin mu, in dai da wannan
zanzaron ne, kar ka cewa kowa gidan mu daya
Khalid, dan Allah kace kawai kana nemana"
Bude baki Khalid yayi, kafin yace wani abu
Salim yaja kofar, numfashi yaja ya fitar yana
jinjina kai
"Bakomai, Allah na ganin ka Hamma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 355
Ya furta a hankali yana kwance belt din ya cire
shi hadi da zaro rigarshi waje. Salim baya bude
bakin shi ya fadi maganar da zaka so kaji,
yanzun da hirar arziki ce da wahala in ba zai
zage shi ba yace ya saka shi magana. Amman da
yake ci masa mutunci yayi niyyar yi ya bude
baki ya fadi abinda babu wanda ya tambaye shi.
Har yayi wanka ya fito yana tunanin yanda duk
shekarar babu wanda yayi mishi irin zagin da
Salim yayi mishi. Masallaci ya fita yayo sallar
Magriba ya dawo.
Inda Nawfal yaje yake tunani, ko gidan Daada
zai kwana ne? Ya tambayi kan shi kafin ya dauki
wayar shi da nufin kiran Madina yaji ko Nawfal
din yana can sai gashi ya turo kofar da sallama,
kafa ma ya saka, hannuwan shi rike suke da
ledoji
"Madina zan kira yanzun inji ko kana gidan
Daada"
Kai Nawfal ya girgiza mishi yana zare takalman
shi a gefe ya sake amfani da kafar shi ya tura
kofar. Kasa ya zauna kan kafet yana ajiye ledojin
Lubna sufyan
Hausabook.com 356
da Khalid ya kawo hannu da nufin dauka Nawfal
din ya janye gefe da sauri
"Ba hali me kyau bane wannan Hamma... Daga
ajiye abu"
Kafar shi Khalid din ya saka yana harbin Nawfal
a baya kafin ya sake kai hannu yaja ledar
"Hamma mana!"
Ko inda yake Khalid bai kalla ba
"Ka aike ni ne?"
Robobine na take away da zafin su rau na kuwa,
fito da su Khalid ya shiga yi
"Gidan Adee kaje"
Ya fadi yana saka Nawfal din kallon shi
"Robobin gidan ta ne wannan, dan ita kadai
naga tana amfani da irin su"
Kai kawai Nawfal ya jinjina
"Allah ya yafe maka halin nan da ka kwaso"
Lubna sufyan
Hausabook.com 357
Jin Khalid din bai kula shi ba sai ma roba daya
daya bude yasa shi dorawa da
"Bakin halin da ka koya nake nufi"
Kafar dai Khalid ya sake sawa yana kai mishi
harbin daya kauce wannan karin yana dariya.
Yayi kewar su, yayi kewar gida da dukkan
zuciyar shi. Zama haka a daki daya da Khalid
kawai na kara tuna mishi da duk wani dalili da
yake da shi na dawowa gida, duk wani dalili da
babu inda zaije ya kira gida sai Najeriya. Yana
gama baccin shi Adee ya fara kira, ita kadai ya
fadama yana airport, dan sunyi hira ma har sai
da ya shiga jirgi. Mashin tace yahau suka hadu a
hanya dan ta fito karbar ma mijinta wani sako
da aka aika mishi daga Abuja.
Har miyar da zata mishi wajen kwana hudu
Adee tayi mishi, da farfesun kifi mai yawa.
Takarcen da ta hado mishi tsayawa yayi kawai
yana kallon ta
"Kafin matar ka ta dawo ne..."
Ta fadi tana dariya, murmushi kawai ya iya yi
mata, kuma ta dawo da shi, danma sai da ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 358
tsaya a hanya yayi sallah a wani masallaci tunda
ta san yanda baya son rasa sallar a cikin jam'i in
ba da wani babban dalili ba. Adee bata shiga
gida ba, saboda shine kuma, tare da Adee ba
saiya furta abubuwa da yawa ba, ba sai yace
mata bai shiga bangaren Saratu ba, ta sani. Idan
suka shiga tare dole zaiji kamar bai kyauta ba,
shisa taki shiga dan ta kara mishi lokacin da
yake bukata.
"Kai ba zaka ci bane ba?"
Khalid ya bukata yana katse ma Nawfal tunanin
da yakeyi
"Bangane bana ci ba? In zo da abu kana mun
wannan tambayar?"
Zaman shi Khalid ya gyara yana jinjina kai hadi
da tsoma hannu cikin robar farfesun kifin daya
bude yana fadin
"Okay..."
Ganin da gaske yake yasa Nawfal din mikewa.
Gudun kar suyi bari yasa Khalid sauke robar
kasa suka ci tare kafin su fita sallar isha'i su
dawo.
Lubna sufyan
Hausabook.com 359
"Bari inga me aka dafa"
Cewar Khalid, har Nawfal ya jinjina mishi kai zai
wuce bangaren su sai kuma ya fasa
"Muje nima ban shiga ba"
Sai da Khalid yayi mishi kallon da yake fassara
ka tabbata yaga ya da dan daga mishi kai
tukunna ya shiga gaba shikuma Nawfal na biye
da shi har bangaren Saratu da suka shiga tare da
yin sallamar da ta amsa, yanayin fuskarta na
sauyawa lokacin da ta dora idanuwanta kan
Nawfal. Zaune take kan kujera da dan karamin
kwano a hannun ta da farfesun naman rago ne
ta zubo, tama tsame duk naman, romon ne take
dan diba da cokali tana sha.
"Nanna..."
Nawfal ya furta, Khalid na karbewa da
"Sannu da gida"
Ya wuce hanyar kitchen da sauri, idon dai
Saratu ta kafa mishi cike da tambayoyin da ya
rasa wanne zai fara amsawa duk da bata furta su
ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 360
"Da zun na zo, ina wuni"
Ya ce cikin sanyin murya
"Lafiya lau"
Ta amsa a takaici tana dauke idanuwan ta daga
kan shi alamar ta gama bashi iya lokacin da take
tunanin zata iya. Juyawa yayi da nufin barin
dakin, zuciyar shi yake jin babu dadi, ita kadai
ta tsane shi, duk duniya ita kadai ta tsane shi
kuma bai san dalili ba, tunanin duniya yayi ko
zai tuna wani abu daya taba yi mata banda zama
karkashin kulawar mijin ta da Kawun shi ne,
yana da hakkin da zai rike shi ko da ba ita yake
aure ba. Me yayi mata da zafi haka?
Numfashin kirki ma bayajin yana shaka in tana
waje saboda gudun kar sautin shi ya takura
mata, yana da rai amman idan Saratu na nan
kokarin gani yake ya zama gawar da ba zata iya
gani ba, duk dan ya gujema bacin ranta. Ya gaji,
bai san yanda ya gaji ba sai yau din nan. Shisa ya
koma yana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 18