heart burn"
Lubna sufyan
Hausabook.com 136
Shima kwara hudu yaci ya kara shan ruwan da
yake hannun shi. Yana kallo ta kulle sauran da
alama itama ta isheta
"Zan tafi, yanzun za'a kira sallah"
Salim yayi maganar yana mika hannun shi
bayan motar ya dauko wata bakar leda yana
dorawa akan jikinta
"Komai kika ce kina karantawa, bana karanta
duk wani abu da bai shafi karatuna ba, sune
suka mun kyau a ido"
Bude ledar Madina tayi tana lekawa, sai da ta
gyara zaman gilashinta sannan ta kalle shi da
wani yanayi a fuskarta da ya saka zuciyar shi
daukar dumi, idan litatttafai zasu bayyana
wannan yanayin a fuskarta duk zuwan da zaiyi
zai kawo mata ko dan ya gani
"Nagode Hamma, kasan duk na karanta na
dakina, maimaita wasu nakeyi. Daddy yace zai
kawo mun amman bai zo ba jiya... Nagode sosai
sosai"
Murmushi kawai ya iya mata yana kallo ta sa
hannu ta zaro littafi daya tana shafa shi a gefen
Lubna sufyan
Hausabook.com 137
fuskarta kamar akwai wani abu a tare da littafin
da ita kadai ce take gani, dayan hannunta ta sa
tana bude murfin motar ta fita, harta kai kofar
gida ta dawo tana daukar ledar awarar ta hadi
da fadin
"Sai anjima...Allah ya tsare maka hanya"
Bata jira amsar shi ba ta sake juyawa, murfin
motar ma sai shi ya rufe abin shi, hankalinta
gabaki daya yayi kan litattafan. Da murmushi a
fuskar shi ya kunna motar da yayi dai-dai da
kiran sallar Magriba da akayi. Yana hanya ana
tayi a masallatan da yake wucewa, banda sallar
asuba da itama dan Khalid na tashin shi baya
kowacce sallah a cikin jam'i. Baisan lokacin da
hakan ya fara ba, rana daya ya wayi gari za'a
kira sallah yana kwance bai mike ba duk da
wani duhu da yake ji yana karuwa a zuciyar shi.
Wata rana yana aji haka zaiga mutane na fita
dan gabatar da sallar su, ko ya fita yana komawa
mota ya zauna har sai an idar.
Sai ya hada azahar da la'asar yayi su a lokaci
daya. Ko yanzun daya karasa gida ya ajiye motar
shi ya nufi bangaren su ya bude ya shiga a falo
Lubna sufyan
Hausabook.com 138
ya zauna yana sauke numfashin gajiya, saida ya
huta ya mike ya shiga kitchen tunda Adee tana
nan yasan abincin shi an kawo ba sai yaje ya
zubo ba. Ai kam an kawo din, shinkafa da wake
da miyar kifi. Daga Magriba har isha'i sai karfe
tara na dare ya hada yayi su, ya sake yin wanka
yana shirya jikin shi cikin kananun kayan da
sukai matukar karbar shi sannan ya sake ficewa
daga gidan.
*
Adee da take tsaye a gaban shi ta daga kai cikin
alamun son ganin fuskar shi sosai yake kallo
"Dan Allah Hamma, kaji, dan Allah ka danyi
fara'a idan zaku gaisa, a tsorace yake wallahi"
Murmushin da zuwa yanzun zaice Madina tafi
kowa gani yayi mata
"Good...gara da yake a tsorace"
Kallon shi Adee tayi kamar zatayi kuka. Sau
wajen hudu Salim din yana wuce ta tare da
Ahmad, cikon na biyar ne tana komawa ta
ganshi zaune a falon Nanna, sai da zuciyarta ta
buga
Lubna sufyan
Hausabook.com 139
"Waye shi? Ban taba haduwa da yan ajin ku fiye
da sau biyu a cikin wata daya ba"
Bawai bata so ta fada musu bane ba, ta rasa ta
inda zata fara tun satin daya fita da Ahmad din
ya matsa mata da yana son ya gaisa da Julde, ko
kuma tayi magana da shi a saka musu rana yana
son ko gaisuwa ce azo ayi, shine namiji babba a
gidan su, kuma kamar yanda Hajiyar shi take
cewa babu wani abu da yake jira yayi aure sai
lokaci, yana da muhalli, dan kasuwa ne da yake
harkokin shi a tsakanin Dubai da kuma nan
Kano, suna da shaguna a cikin kantin kwari,
inda yake mallakin shine, bai kuma boye mata
matakin karatun shi daya tsaya a diploma ba
tunda gabaki daya harkar karuwanci ce abinda
suka saka a gaba. Diploma din ma yayine kawai
dan ra'ayin dan samun karatun boko da abokin
shi ya kwadaita mishi.
Da ta fadawa Nanna ta samu Julde da maganar
saiya wakilta Salim da yayi bincike kafin a sati
dayan da ya sakama su Ahmad na turo manyan
shi. A tsorace Adee take dan har ranta tana son
Ahmad, irin soyayyar da bata hango kanta a ciki
ba, yana da duk wata nagarta da cikar halittar
Lubna sufyan
Hausabook.com 140
da kowacce mace zata yaba da ita. Sai dai a irin
bincike na aure haka ake binciko halayen
mutum da wasu kan toshe kunnuwan su tare da
rufe idanuwa wajen kin yarda, sai binciken yayi
hannun riga da halayen da kai aka nuna maka.
Ga Salim din yace mata
"Ina son magana da Ahmad, ki kira mun shi"
Batare da yayi mata wani karin bayani ba,
tsoron ta shiya kara tsorata Ahmad din. Da yazo
din ma ya kirata ya sanar da ita yazo tana jin
yanda muryar shi take rawa
"Tunda azahar nake addu'a Adee, idan Yayan ki
yace ban mishi ba fa? Ya zan da tarin soyayyar
da nake miki?"
Kasa bashi wani kwarin gwiwa tayi saboda
itama a tsoracen take. Dariya Salim yake sonyi
amman ya danne yana kama hannunta ya
janyeta gefe yana fita. Kaf unguwar su Ahmad
harma kasuwar su daya shiga babu mutum daya
bayar da shaidar banza akan Ahmad, asalima
tarin nagarta da alkhairin shi suke fadi. Idan
Salim ya kalli Fadila baya ganin shekarunta, yar
Lubna sufyan
Hausabook.com 141
kanwar shi yake gani, yar mitsitsiyar yarinyar
da zaiyi komai dan kareta daga duk wata
hatsaniya ta duniya. Dan baya hango aure a
cikin jerin abubuwan da yake da niyyar yi a
rayuwar shi baya nufin baya son yaga wani yayi.
Musamman kanwar shi da duk idan yaga wani
da namiji a kusa da ita sai zuciyar shi tayi tsalle
zuwa wuyan shi. Tsallen da bai taba hana shi bin
kannen wasu ba, zuwa yanzun ya daina jin
girman laifukan shi, baya hango kowa sai
nishadin da zai samu na dan kankanin lokaci. Ya
dai ji dadi har kasan ran shi da yaga zata nutsu
waje daya, ya sake jin dadin samun Ahmad da
nagartar da bashi da ita. Har hamdala ya tsinci
kan shi dayi da jarabtar su ba zata taba Adee ba
don ita dinma mutuniyar kirki ce. Ko yanda
suka gaisa da Ahmad yasan a tsorace yake
"Idan nace in ka ci amanarta Allah zai kamaka
kamar ina fada maka abinda ka sani ne. Ga
kanwata na Ahmad, dani zaka fara haduwa idan
hawaye ya zuba daga idanuwanta saboda kai"
Kai Ahmad ya jinjina mishi yana hadiye wani
abu da yayi mishi tsaye a wuya. Murmushin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 142
Salim din yayi mishi ma kara tsorata shi yayi,
idan yana tsaye da Adee sai ya ganshi babba,
amman yanzun a gaban Salim saiya raina
girman shi.
"Allah ya tabbatar muku da alkhairi"
Salim ya sake fadi yana mika ma Ahmad din
hannu cikin alamar sallama sannan ya nufi
bangaren su. Itama Adee data fito bata wani
dade ba saboda tasan Julde na gab da dawowa.
Ai kam ko mintina goma batayi ba tsakani ya
dawo
"Daddy..."
Ta furta cikin sigar sannu da zuwa tana mikewa
dan ta karbi ledojin da suke hannun shi
"Adee, sannu da kokari"
Cewar Julde yana mika mata ledojin dai-dai
shigowar Khalid
"Daddy sannu da zuwa, yanzun naji motar ka"
Hararar shi Adee tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 143
"Shisa ka shigo kenan...to sai ka juya ai tunda ka
mishi sannu, bai kawo tsarabar komai ba"
Dariya Khalid yayi yana shiga cikin dakin sosai
hadi da kaima daya daga cikin ledojin da tayi
saurin janyewa wawura
"Daddy..."
Adee ta kira
"A'a kunga yanzun na dawo ko? Kaina ba zaiyi
ciwo ba tunda kamar kaji haka kuke"
Julde yayi maganar yana raba su ya wuce, a
gajiye yake jin shi sosai. Dakin su ya wuce yana
samun Saratu a kwance, tun daren jiya da tace
tana son magana da shi yasa kai ya fice bai
saurareta ba take shan kamshi har yau da safe
ma da zai fita. Bata gaban shine, in dai zai dawo
ya samu daya daga cikin yaran shi to hankalin
shi ya gama kwanciya, wucewa yayi ya watsa
ruwa ya fito yana neman wani yadi marar nauyi
ya saka a jikin shi
"Tun jiya nace maka ina so zamuyi magana kaqi
saurarena"
Lubna sufyan
Hausabook.com 144
Alamar ciwon kai da yake ji ya sashi zama gefen
gadon wajen kafafuwanta da ta tashi zaune ta
mike akan gadon
"Ina jinki"
Ya furta
"Akan maganar auren Adee ne, idan suka bukaci
ganin dangin mahaifinta fa?"
Wani irin tsalle zuciyar shi tayi har saida kirjin
shi ya amsa. Badan ya shafe wani abu dangi daga
babin rayuwar shi ba, a'a, bukatar su a cikar
neman aure ne ya manta, wani abu da yake
neman taso mishi ya danne
"Zan san yanda zanyi"
Ya furta yana mikewa, bin shi da kallo saratu
tayi
"Julde kana ganin komai zai tafi dai-dai? Kana
ganin laifukanka ba zasu taba yaran mu ba?"
Iskar da ya shaka dakyar ta wuce mishi yana fito
da ita a wahalce, baisan me yasa take son
hautsina mishi duniyar daya dauki lokaci yana
dai-daitawa ba, amman daya kalleta babu komai
Lubna sufyan
Hausabook.com 145
akan fuskarta sai tarin damuwa, damuwar da
tunda zancen auren Adee ya taso ta danne mata
zuciya. Akwai sirrikan su da auren nan zai iya
bankadowa, abinda tafi tsoron fitowar shi fiye
da laifukan Julde da zai iya taba musu yara.
"Nace miki zan san yanda zanyi"
Ya maimaita yanajin yanda muryar shi take
rawa. Kafin tace wani abu ya fice daga dakin,
duk surutan da su Adee sukeyi iya kunnuwan
shi yake tsayawa, baya kaiwa kwakwalar shi
balle ya fahimta, abincin ci kawai yake badan
yana gane dandanon shi ba, har Adee saida ta
taba shi
"Lafiya dai ko Daddy? Fuskarka kamar babu
jini"
Dan murmushin karfin hali yayi mata
"Kaina ke ciwo ga shi akwai gajiya a tare da ni"
Sannu sukayi mishi dukkan su, Adee ta tashi ta
dauko paracetamol ta balli guda biyu ta bashi,
karba yayi ya sha badan zai mishi maganin
matsalar shi da ta girmi duk wata kwayar
magani ta bature ba, sai dan damuwar da yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 146
gani a fuskokin yaran, har yayi musu sai da safe
suna bin shi da sannu. Daki ya koma, Saratu na
inda ya barta, zagayawa yayi yahau gadon ya
kwanta yana juya mata baya. Har alamun
zazzabi saida yaji ya rufe shi. Yau fiye da
kowanne lokaci yake jin kewar Mero, yana da
yakinin ba zata rasa kalaman da zata fada mishi
da zai kwantar mishi da hankali ba, ko jinta a
kusa dashi da kamshin nan nata ya isa yasa
hankalin shi ya kwanta.
Lumshe idanuwan shi yayi ko da hoton ta ne ya
gani a zuciyar shi, amman sai hoton yazo mishi
tare da kalamanta
"Yanda kayi mun rami a zuciya, in Allah ya
yarda duk lokacin da kake tunanin hankalin ka
ya kwanta sai Allah ya aiko abinda zai birkita
maka komai Julde..."
Babu shiri ya bude idanuwan shi. Zuciyar shi na
ciwon daya dauka lokaci ya saba masa da
radadin shi. Mero ce mutum ta biyu da take da
muhimmanci a rayuwar shi da ta jefe shi da
kalamai masu zafi irin haka, rashin sa'ar shi mai
girma ne, batun yanzun ya san haka ba, shisa
Lubna sufyan
Hausabook.com 147
tunda ya samu su Salim kacokan duk wata
addu'a da zaiyi, duk ma wani aikin kirki da zaiyi
da niyyar Allah kar yasa rashin sa'ar da yazo
duniya da shi karya taba su. Tambayar Saratu ta
tokare mishi kahon zuciya.
Anya laifukan shi ba zasu taba yaran su ba?
Tambaya ce mai nauyin da shi kadai yasan shi,
laifuka tace, laifukan shi idan zaiyi waiwaye
masu yawan gaske ne, ko daya daga ciki za'a
dauka ya isa ya tsaida duk wani jin dadi da yake
gani a fuskokin yaran shi. Har Saratu ta mike ta
kashe musu fitilar dakin bai ko motsa ba, wani
irin tsoro ne yake ratsa dukkan sassan jikin shi,
kome zai same shi in dai zai tsallake su Adee
mai sauki ne. Bacci a daren ranar barawo ne ya
sace shi cike da mafarkin rayuwar da zaiyi
komai dan ganin ya shafe babinta.
Sai dai wasu shafukan na kaddara suna da
zumunci, ko baka waiwaye su ba sai sun sake
kawo maka ziyara.
A cikin kunnen shi aka bude kofar dakin duk da
baccin da yake mai nauyi ne, kuma da alamu a
hankali aka so budewa. Tunda satin bikin Adee
Lubna sufyan
Hausabook.com 148
ya kama baya samun wadataccen bacci, baisan
me akeyi a harabar gidan ba, amman yana jin
kai kawon mutanen da ba zaice duk daga ina
Nannar su ta samo su ba. In har suna da wasu
dangi da suka hada jini dasu a garin Kano daga
Daada sai Madina ya sani. Ko da wasa bai taba
jin daga Daddy har Nanna sunyi zancen wani
dangin su bayan Daada ba. Bai san ko su Khalid
ba, amman shi bai taba tambaya ba, ya yarda
cewar idan akwai dangin daya kamata su sani
za'a nuna musu su.
A ranshi dai yaga kamar wata uku da aka saka
bikin Adee yayi kusa, amman Julde na da halin
da zaiyi mata komai, watakila shisa basu jashi
da nisa ba. Watannin ma sauri sukayi mishi
matuka. Yau dai ya daya rage saura kwanaki
biyu daurin aure, ya hada yar jakar shi, zai kama
hotel ne har sai an gama hidimar bikin gabaki
daya kafin hayaniya ta haukata shi. Karar
haduwar takalmi da tayals din dakin kamar
sukuwar doki ta sa shi jan wani dogon tsaki
"Ubanka kakeyi da baka wuce ba har yanzun
Khalid?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 149
Salim ya fadi yana jin kanshi kamar ba zai bude
ba, kamar ma jan kafa Khalid din ya sakeyi
saboda ya mayar dashi sa'an shi, bude idanuwan
shi yayi yana sauke su cikin na Nawfal daya
kwashe da dariya
"Bajjo"
Salim ya fadi cike da kashedin da bai boye
murnar shi ba. Ya dauka Khalid ne, ko da wasa
baiyi tsammanin zuwan Nawfal din ba
"Normal mutane ko basu rugo sun tarbeni ba
zasu tashi zaune daga kwanciyar su suyi mun
sannu da zuwa"
Cewar Nawfal yana murmushi
"Da dariya a muryar su"
Juyawa Salim yayi, yafi son kwanciya akan
kujera fiye da yanda yake son kwanciya akan
gado. Bai kuma san dalili ba, amman in har yana
gida da rana kuma ko da daddare ma zaka gan
shi kwance a falo kan kujera
"Hamma..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 150
Nawfal ya kira da karfi yana saka Salim jin
kamar ya saka lasifika ne
"Kayi na bakunta Bajjo...karka kara"
Dariya Nawfal din yayi, tunda ya hau jirgi yake
jin shi sama-sama, daya sauka airport ya samu
taxi zuwa gida zuciyar shi dokawa takeyi ba
kadan ba. Kan shi tsaye bangaren su ya wuce,
ranar da aka sa ranar Adee ta kira shi, su tsakar
dare ne ma
"Bacci kake ko? Ban tsaya kirga awanni ba yau,
sai da naji muryarka na tuna tsakar dare ne"
Tashi zaune yayi, banda Adee a gabaki daya
rayuwar shi babu wanda yake kiran shi a
lokacin da baya daga waya ya dauka, ko da
Daddy ne, kusan zaice saboda Adee ne baya saka
wayar shi a silent in ba yana cikin aji ba. Shima
daya fito yaga kiranta yake bin bayan shi
"Kace zaka zo bikina Bajjo, idan ba zan takura
ka da yawa ba"
Shine rokon da tayi mishi
"Zan zo Adee, In shaa Allah zan zo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 151
Duk da ba saboda bikinta kawai yazo ba, bikin
natane ya karfafa dayan dalilin na shi. Filon
kujera da yaji an jefe shi da shi yasa shi rike
bayan kan shi
"Kofato ne a kafarka wai?"
Dariya Nawfal yayi, da gaske ya dawo gida. Sai
ma daya tura kofar dakin su yana jin kamshin
turarukan Khalid sun daki hancin shi, kafin ya
hade tunanin shi waje daya yaji Salim ya watsa
mishi zagi. Da gangan da yazo tura kofar ya buga
ta, mukulli yabi da shi kar Salim din ya same shi
cikin dakin, jakar shi ya fara saukewa yana jan
karamin akwatin shi ya ajiye gefe daya. Sai da ya
shiga wanka ya fito sannan ya bude dakin,
akwatin shi ya janyo ya dauki wata farar riga da
wani wando fari iya gwiwa ya saka. Shima
baccin ne a idon shi saboda jikin shi ya saba da
bambanci lokaci. Kwanciya yayi abin shi.
Cikin bacci yaji kamar ana jijjiga shi, inda yake
jin hannun ya kama ya ture yana juya kwanciya
"Bajjo... Bajjo... Dalla ka tashi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 152
Khalid ya fadi muryar shi cike da farin ciki yana
sake jijjiga Nawfal din daya daga idanuwan shi
dakyar
"Ka barni inyi bacci Hamma..."
Ya furta yana shirin gyara kwanciya Khalid din
yana kai hannu ya janye filon da kan Nawfal
yake kai
"Tashi zakayi muyi labari"
Wani irin numfashi Nawfal ya sauke
"Kayi missing dina na sani, amman ina nan, ba
yau zan tafi ba ko wani abu, ka kyaleni inyi bacci
na"
Baki Khalid ya bude zai magana Nawfal ya tashi
zaune da sauri yana katse shi da
"Kana da kati a wayar ka? Ara mun..."
Fuskar Khalid dauke da alamun mamaki ya zaro
wayar shi kirar Nokia yana mika ma Nawfal din
da ya karba yana mika hannu ya dauko tashi
wayar, kallon shi Khalid yakeyi yana dannedanne da alamar sako yake turawa. Yana
gamawa ya mika ma Khalid wayar
Lubna sufyan
Hausabook.com 153
"Nagode"
Yayi maganar hamma na kwace mishi saboda
baccin da yake idon shi
"Ka kwanta, zan fita ne nima, Nanna ta aikeni"
Da wani yanayi a fuskar Nawfal yace
"Shine ka tashe ni?"
Dariya kawai Khalid yayi ya mike yana ficewa
daga dakin. Kasa komawa baccin yayi, kamar
cikin shi jira kawai yakeyi ya farka ya cigaba da
tunasar da shi yunwar da yake dawainiya da ita
da ta saka shi mikewa zaune babu shiri yana
saukowa daga kan gadon gabaki daya. Rigar
jikin shi ya kalla, duk ta yamutse saboda baccin
da yayi da ita a jikin shi, cire ta yake kokarin yi
yaji ana kwankwasa dakin
"Come in"
Ya furta yana karasa cire rigar dai-dai lokacin
da Salim ya turo kofar yana runtse idon shi
"Ewwwww, Bajjo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 154
Dariya Nawfal yayi dan yanda Salim din yayi
wani zaiyi zaton babu kayane a jikin shi gabaki
daya
"Ka sa kaya, idanuwa na"
Cewar Salim da har lokacin idanuwan nashi
suke a runtse, rigar daya cire ya mayar a jikin
shi yana dariya, a hankali Salim ya dan bude
idon shi daya kafin ya bude su gabaki daya yana
mika ma Nawfal ledar da sai lokacin ya kula da
tana hannun shi, karba yayi cike da mamaki
"Kifi da dankali na siyo... Bakomai kake ci ba,
akwai kayan tea a kitchen"
Kai kawai Nawfal ya iya jinjinawa saboda wani
abu da yaji ya mishi tsaye a zuciya
"Idan baka ci...."
Da sauri Nawfal yake girgiza mishi kai
"Zanci, ina ci... Miyetti"
Kallon shi kawai Salim yayi, kafin kaji fulatanci
a bakin shi zaka dade, Julde yana musu, Nanna
ma lokutta da dama shisa duk suke ji, amman
Lubna sufyan
Hausabook.com 155
kana iya ma Nawfal magana ya mayar maka da
hausa.
"Kar inji motsin ka"
Hannu Nawfal ya daga yana ma Salim din alamar
salute hadi da jinjina kan shi. Sai da ya fice daga
dakin sannan ya samu waje nan kasa kan kafet
ya zauna ya bude ledar. Harda ice cream har
roba biyu, wani irin numfashi ya sauke
"Allah ya biya maka bukatunka Hamma"
Ya furta a hankali saboda har ranshi yaji dadin
ice cream din fiye ma da kifi da dankalin. Shi ya
fara sha tukunna ya ci sauran, yana cikin shan
dayar robar Khalid ya shigo da sallamar da kafin
ya amsa ya mika mishi wayar shi
"An maka text"
Karba Nawfal yayi da sauri yana duba wayar
yaga Khalid bai bude text din ba, sai da ya dan
sake kallon shi yaga waje ya samu ya zauna yana
jan ledar da take gaban Nawfal din da kifin da
ko rabi bai ci ba, sake mayar da hankalin shi
yayi kan wayar yana karanta text din, replying
yayi yana ajiye wayar da kamar haka take jira ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 156
fara ruri, kamar ba zai daga ba, Khalid yake
kallo da yake cin kifin shi hankali a kwance,
daukar wayar yayi yana daga kiran hadi da
karawa a kunnen shi, numfashin da bai san yana
rike da shi ba ya sauke
"Jaan..."
Ya kira cikin wani irin sauke murya da yasa
Khalid daga kai ya kalle shi fuskar shi dauke da
alamar tambaya
"Wanne zan fara amsawa yanzun? Bakomai fa,
na danyi bacci ne"
Ya amsa kafin yayi jim yana sake fadin
"Um um, ina zaune, naci abinci, muna tare da
Hamma Khalid"
Murmushi yayi yana mika ma Khalid din waya
"Ana son magana da kai"
Yanayin fuskar Khalid din na saka shi yin yar
dariya, karbar wayar Khalid yayi ya kara a
kunnen shi hadi da yin sallama
"Kullum sai naji labarin ka"
Lubna sufyan
Hausabook.com 157
Aka furta daga dayan bangaren bayan amsa
sallamar shi, cikin wata murya mai sanyin
gaske, idanuwan Khalid na kan Nawfal yace
"Abin mamaki ganin yanda ni banji naki labarin
ba"
Zunguri Nawfal ya kai mishi
"Hamma"
Ya kira a hankali, kafadu Khalid ya dan daga,
yarinyar da har lokacin bai san sunanta ba tayi
dariya mai sanyin sauti kamar muryar ta
"Sunana Murjanatu. Yar asalin Nigeria, garin
Adamawa, an haifeni a New York, I'm your
brother's girlfriend"
Ta karasa maganar cikin harshen turanci,
yanayin yanda ta ajiye kowacce kalma na sake
tabbatar wa da Khalid din da gasken tashin
turai ce, sai dai kalamanta na karshe sun saka
shi rasa abinda zai fada ko abinda ya kamata ya
fada, har Nawfal ya miko hannu ya zare wayar
daga kunnen shi bai ce komai ba
"Hello..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 158
Nawfal yace yana dorawa da
"Ina da tambayoyi da tarin bayanai da zanyi,
muyi magana anjima?"
Kai ya jinjina yana sauke wayar daga kunnen shi
yana kallon Khalid
"Ban tabbatar ba shisa ban fada maka ba, da na
tabbatar kuma bansan ta inda zan fara ba...
Kawai ya faru ne"
Numfashi Khalid yaja yana fitarwa a hankali,
soyayya abune da yake hange da nisan gaske a
rayuwar shi, duka shekarar shi ta uku yake a
jami'a, yana son tsayawa da kafafuwan shi,
tsayuwar da idan wata ta jingina da shi ba zasu
fadi ba su dukan su.
"Kace wani abu dan Allah"
Nawfal ya fadi yana kallon Khalid din,
Murjanatu ce abu na farko da yaji baya bukatar
amincewar kowa a kai, amman yana son goyon
bayan Khalid, ko yaya ne yana son Khalid ya
kara mishi karfin gwiwa
"Ban san me zance ba ne ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 159
Khalid ya furta cikin sanyin murya yana dorawa
da
"Da gaske na rasa abinda zance, na san abune da
zai faru wata rana, amman yanzun baiyi sauri
ba?"
Kafadu Nawfal ya dan daga mishi cikin rashin
tabbas, mutane na tsoron abubuwa
mabanbanta, kananu da manya, duka biyun ne
suka hade mishi waje daya, babban tsoron shi
bai wuce kasancewa shi kadai a filin duniyar shi
duk kuwa da rashin girman ta, yana da su ya
sani, amman ba zai kira su nashi shi kadai ba,
Nanna ta sha jaddada mishi ita da duka ahalinta
ba nashi bane ba, rabasun da takeyi da shi ba
zabinta bane ba, dole akayi mata. Yana son ya
samu wani abu da zai kira nashi.
"Nawfal..."
Khalid ya kira yana saka shi sauke numfashi
"Ban sani ba Hamma, watakila yayi sauri, kawai
ya faru ne..."
Baki Khalid ya bude zaiyi magana aka
kwankwasa dakin
Lubna sufyan
Hausabook.com 160
"Waye? Shigo?"
Cewar Khalid bayan an sake kwankwasa dakin a
karo na biyu
"Nanna tace ka fita da motar ta a duba za'ayi abu
da ita yau"
Kai Khalid ya jinjina
"Ka karbo mun mukullin..."
Sanin halin Lukman ya sa shi mikewa ya bude
kofar yana kiran Lukman da har ya kusa kofar
da zata fitar dashi daga bangaren nasu
"Yanzun fa, ka dawo yanzun ka kawo mun"
Juyawa kawai Lukman yayi cikin sanyin yanayin
shi da baisa tafiyar shi ta kasance ta malalata ba.
Yana da kazarniya sosai, kawai hayaniya ce
bayayi, dan ta Lukman duniyar bata tashi ba,
babu wanda zaice ya taba ganin ran yaron a
bace, ko a ranakun da babu makaranta ba
kullum kake ganin shi ba. Komawa cikin dakin
yayi, kallon ledar kifin da yake ci yayi cikin wani
yanayi da yasa Nawfal fadin
Lubna sufyan
Hausabook.com 161
"Ka sa a fridge mana, in ka dawo sai kaci a
nutse..."
Dan jim Khalid yayi
"Bafa harshen kowa bane irin naka...zaiyi sanyi,
bari dai in kai Kitchen kawai. Muyi magana idan
na dawo?"
Ya karasa yana tsugunna ya tattara ledar kifin
"Ni ma zanje wajen Daada, na so inga Adee, naga
kaman akwai mutane da yawa a bangaren"
Kai Khalid yake girgiza mishi tunda ya kira
sunan Adee din
"Bata gidan ma, ni na kaisu wajen gyaran gashi
ne ko meye ita da kawayenta tun dazun, tace in
sun gama zata kira ni...ka shirya, bari in bi
Lukman in karbo mukullin sai in sauke ka"
Khalid ya fadi yana fita daga dakin da ledar kifin
shi a hannu. Shima tashi yayi yana hada duk
wani abu da yake son tafiya da shi gidan Daada
din a jakar shi ta goyo, dan sai da Khalid ya dan
jira shi da ya dawo, ko rigar da yaso ya sake bai
samu ya saken ba suka fita.
Lubna sufyan
Hausabook.com 162
**
Daga bakin titi Khalid ya sauke shi saboda
motar nata rirrikewa, da kafafuwan shi ya taka
ya karasa shiga, yana hango gidan yana jin
zuciyar shi na tsalle har cikin tafukan kafafuwan
shi, dan duk wani taku da zaiyi sai ya kara
gudun zuciyar shi. Bai san yayi kewar Daada har
haka ba sai da ya taka soron gidan yaji tsalletsalle da zuciyar shi takeyi, rabon da ya ji shi
kamar yaro dan shekara uku da yake dokin
ganin wani nashi haka harya manta. Kamar ya
karasa da gudu ya shiga cikin gidan haka yake
jin shi
"Daada...Daada Am..."
Shine abinda ya iya furtawa a madadin sallama,
sunan na fitowa daga wani lungu na zuciyar shi
inda yake jin kewar Daada kamar yasa ihu
"Daada..."
Ya kara kira yana jin kafafuwan shi sun gaji,
kamar dakin nata ya kara nisa. Daada da take
daki a zaune, hankalinta yana kan labaran da
take kallo a talabijin dinta ta jiyo muryar shi a
Lubna sufyan
Hausabook.com 163
kiran farko da yayi mata, kira na biyu ne
yanayin yanda ya furta "Daada Am" din ya saka
taji kamar ruhinta ne yake shirin kubcewa daga
gangar jikinta saboda yanda muryar ta dake ta
"Bukar..."
Ta furta da wani irin yanayi mai wahalar
fassarawa tana dafa kujera ta mike dakyar, kira
na ukku ne ya mayar da ita ya zaunar tana wani
irin maida numfashi, zuciya kenan, babu abinda
ya kaita wahala a kaf halitta ta tsarin jikin dan
adam, da bata yaudare su haka ba. Kafin tunanin
ta ya tsawaita Nawfal ya karasa bakin kofar inda
yayi tsaye kamar yana son daukar sababbin
hotunanta ne cikin kan shi ya adana a kusa da
tsofaffin da yake da su
"Daada..."
Ya sake kira cike da tsantsar kaunar ta, ya
manta yanda ita kadai take saka shi yaji abinda
yake ji haka, yanda matsayinta ba zai taba
haduwa da na kowa ba a wajen shi
"Bajjo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 164
Ita ma ta kira shi, sai dai nata idanuwan ba
kaunar jikan nata bane da kewar shi kawai,
harda hawaye taf a cikin su
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 18