yin aikinta akan
makusancin ka ba, amman in zaka iya bayajin
shi kam zai bar ko tsinke ya soki Khalid. Sai da
Salim ya kamashi shima ya mikar
"Ku taho ku koma mota..."
Cewar Salim yana jan rigar Nawfal din, Julde ya
kama hannun Khalid, bayan suka shiga su biyun.
Julde ya rufe bangaren Khalid yana daga kan shi
yayi nasarar saukewa akan Mero da hasken
Lubna sufyan
Hausabook.com 389
fitilar wata mota ya haska mishi fuskarta dai-dai
lokacin da ta shiga gaban wata mota tana rufe
murfin tare da bude wani abu a cikin kirjin
Julde da kafafuwan shi suka fara daukar shi
"Mero... Mero Na"
Ya furta a kasan numfashi
"Daddy... Ina zaka je kuma?"
Salim ya tambaya, amman ko jinshi Julde baiyi
ba, mutane yake turewa yana ratsa tsakanin
motocin da suke wajen, kafin ma ya tsallaka har
anja motar anyi gaba, wani mashin ya dafa yana
mayar da numfashi, shekaru goma sha sai yau
ya dora idanuwan shi akanta, kafin ya maida
numfashin da yake fatan zai dan nutsar da
bugun zuciyar shi yaji an dafa shi
"Daddy... Lafiya kuwa?"
Salim ya tambaya yana ganin fuskar Julden ta
kara mishi haske kamar babu jini a jikinta
"Lafiya?"
Ya sake tambaya, kai Julde kawai ya daga mishi
Lubna sufyan
Hausabook.com 390
"Mu tafi gida kawai, gobe na dawo in duba motar
Khalid da safe..."
Kan dai Julde ya sake daga mishi, bai yarda da
muryar shi ba shisa bai amsa ba, haka suka
karasa, Salim ya bude mishi gaban motar ya
shiga. Zuciyar shi kamar kara bugawa take a
cikin kirjin shi.
Ashe zai sake ganin Mero?
Ko dai alama ce kaddara take nuna mishi?
"Inajin kamar don kai kawai aka halitta mun
zuciya a kirjina, ko dan kai ta fara numfasawa?
Wanne irin so nake maka dana watsar da
maganar kowa Julde?"
Da idanuwa Saratu take bin shi ba tun safiyar
ranar ba, tun sati biyu da suka wuce saboda
tambaya babu irin wadda batayi mishi ba akan
me yake damun shi yana amfani da damar
wajen nuna mata cewa da gaske bata da wani
muhimmanci a wajen shi. A tsayin shekarun
auren su zata kirga adadin lokuttan da yayi
rashin lafiya har ya kwanta, a cikin adadin
Lubna sufyan
Hausabook.com 391
zatace sau daya ya taba wadda ta kai shi da
kwanaki a kwance, wannan kuma rashin lafiya
ce da take son shafewa a kundin tarihi idan har
tana da halin haka.
Sai kuma satikan nan da suka wuce da alamu
duka suka nuna cewa ba ciwo yake ba, ya dai
koma kamar wani gunki-gunki ne, abinci haka
zai ta wasa da cokali a ciki, a yinin rana baifi ya
saka ruwan shayi da yar wainar kwai a cikin shi
ba, satin farko ya jera kwanaki hudu yana fita
tunda sassafe sai yammaci liqis zai dawo, kafin
daga baya ya koma rabuwa da kan gadon dakin
shi ma sai yaji su Khalid a falon ne zata ga yayi
ta. Suna kuma fita zai koma ya sake bin gadon ya
kwanta. Har daki take bin shi da abincin safe,
rana da na dare. Yau na safen da na ranar duka
haka ta zo ta dauke ta sake fita da su, babu
alamar da ta nuna ya ko bude balle ya ci.
Rashin muhimmanci da take da shi a wajen
Julde ba sabon abu bane, abune da lokaci bai sa
ta daina jin ciwon shi ba, wannan karin dai
tunanin halin da yake ciki shiya danne mata
ciwon da take ji. Ta na son shi, ta na son Julde
fiye da yanda kalamai zasuyi mata adalci wajen
Lubna sufyan
Hausabook.com 392
misaltawa, saboda ko wulakancin shi na yau da
kullum bai dakushe tasirin soyayyar shi a
zuciyar ta ba. Na dole sun dawo wuni cikin dakin
kamar marassa gaskiya, bai kore ta ba, yanda
yake nunawa ma kamar bai san tana cikin dakin
ba tunda ko inda take baya kallo.
Ta kai zuciyar ta nesa dai wajen ganin bata yi
komai daya wuce taya shi zama a cikin dakin ba.
Tana kallon shi bayan la'asar ya shiga bayi, tana
nan zaune ya fito, idanuwan ta suka fara sauka
kan fuskar shi da ta manta rabon da ta ganta
babu gashi, a kwanakin nan ma ta cika sosai
saboda bai damu da yunwar cikin shi ba balle
wata sumar fuska, yanzun ya kwashe komai, ko
fuskar Lukman akwai gashin baki daya fara
fitowa luf da shi, har tana tsokanar shi a kai ma.
Fuskar Julde da bayan kwai basu da bambanci.
Haka kawai sai yanayin ya hasko mata wani
hoto da yasa zuciyar ta bugawa kamar tana
neman hanyar fita daga cikin kirjin ta.
Tabbas shekaru ba karya bane ba, don sun nuna
kan su a tare da Julden, bata san ko idanuwanta
bane suka rage wannan shekarun akan fuskar
shi suna dai-daita mata fuskar da hoton da take
Lubna sufyan
Hausabook.com 393
da shi a cikin kanta. Bambancin ba a zanen
fuskar yake ba, a sarkar da babu ita yanzun a
wuyan shi ce, kayan fulanin da yake sakawa a
wancen lokacin, sai kuma askin kan shi da yake
kasa sosai, sabanin wancen lokacin da ya tara
gashin, bayan kadai ake ragewa an tado gaban
yayi tozo irin na samarin fulani da suke ji da kan
su a wancen lokacin. Julden ta, Julden da
zuciyarta ta zaba tun kafin ma tayi wayon sanin
haka.
Mata da yawa na son maza masu kasumba, maza
da yawa sukan ce cikar kamala ta da namiji
kenan, musamman magidanci kamar Julde, in ba
dalili na aikin kaki da kan hana ma wasu mazan
yin hakan ba, banda Saratu, a yau, a yanzun
kuma ban da ita
"Kayi kyau"
Kalmomin biyu da tayi nufin furtawa a zuciyarta
suka kubce mata suna kuma saka Julde sauke
idanuwan shi da yanayin da yake ciki bai sa
farin su canzawa ba, kyallin na shigar mata wani
waje da bata san da shi a zuciyar ta ba, har yana
Lubna sufyan
Hausabook.com 394
sata gasgata maganar cewa so baya tsufa da
masu azancin magana suke yawan fada
"Da ka aske sumar sai kayi kyau"
Ta furta muryarta na sauke kasa tunda kalaman
farko suka subuce sai suka bata kwarin gwiwar
furta sauran. Har lokacin dai kallon ta yake yi,
tun kafin ya san menene soyayya, tun kafin
Mero yake ganin soyayyar shi a idanuwan
Saratu, a irin wannan lokacin a baya da take fito
mishi da asalin kaunar da take mishi ya sha
tambayar kan shi dalilin da yasa ya kasa mayar
mata ko da kadan ne daga cikin tarin soyayyar
da ya gani, kuma ya san tana mishi. Watakila da
ta rage mishi radadin rashin Mero da yake fama
da shi.
Da bai gan ta ba, da bai sake ganin ta ba da bata
fama mishi tsohon ciwon da yake riritawa ba,
kamar mahaukaci haka ya dinga zagaye
unguwar da ya ganta yana tambayar duk wani
wanda zai tsaya ya saurare shi ko ya ganta ta
hanyar zayyana mishi kamannin ta, a idanuwan
mutane mabanbanta yaga mamakin da suke da
ya kasance cikin shiga ta kamala, ko kadan
Lubna sufyan
Hausabook.com 395
alamu basu nuna cewa yana dauke da cutar
rangwamen hankali ba, amman daga ya
bude bakin shi sai kalaman shi su sha bamban
da kamammin shi. Ziyara ta zo, ya san iya
wannan in ba kuma dalili ya raba auren da tayi a
Kaduna ba kamar yanda yake fata.
Har yanzun, yana kuma jin har abada Mero zata
kasance rike da kaso mafi girma na zuciyar shi
da duka walwalar shi. Baiyi karya ba da ya taba
ce mata
"Ina jin kamar ban san farin ciki ba sai da kika
shigo rayuwa ta Mero"
Akan ta ya fara sanin menene asalin farin ciki
kafin ya samu su Salim da suka karasa cika
mishi abinda ya rage na daga cikin farin cikin. A
yanzun kuma duk wata yar walwala da yake yi a
duniya su ne sanadi, su kadai yake kallo ya
samu nutsuwa. Ko sauran matan da yake bibiya
baya samun nutsuwar da yake nema a tare da
su, kamar akwai wani duhu da yake mamaye da
shi ya hana mishi sukuni.
"Ko kana sha'awar cin wani abu?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 396
Maganar Saratu ta kutsa ta cikin tunanin shi
"Idan anyi sallah ki kira su Khalid sai muci
gabaki daya"
Yana kallon murmushin da tayi tana daga kai
hadi da mikewa ta fice daga dakin, da zai iya da
ya so ta, ko kadan da ya so matar nan. Amman
ba zai iya ba, lokaci dai ya koya mishi sabo da
ita, amman babu soyayyar ta ko daya a cikin
zuciyar shi, akwai dai jin ko na rana daya ya
kamata yayi mata godiya, da ta bashi su Salim,
da ta ke tare da shi tana kula da gidan shi duk
fitowar rana da faduwar ta. Ta cancanci ko da
iya wannan jinjinawar ne.
Komai da sanyi-sanyi yake tayin shi, sanda ya
gama shiryawa cikin wani farin yadi da ya karbi
jikin shi har ana kiran magriba, fita masallaci
yayi, bai hadu da kowa ba wajen dawowa sai
Khalid da suka taho tare, Nawfal daman ya saba
ya zauna masallaci bayan Magriba wasu
ranakun ma har sai anyi isha'i yake dawowa. In
kuma bai tsaya ba to sai ya gama duka azkar din
shi, Khalid ya sha zama tare da shi sai yaga ya
samu waje ya jingina bayan shi da bangon
Lubna sufyan
Hausabook.com 397
masallacin, kamar akwai wata nutsuwa ta daban
da sai a cikin masallacin ya ke samun ta.
"Ku zo muci abinci, ka fada ma su Bajjo"
Julde ya cewa Khalid daya daga mishi kai
"Yanzun kuwa... Me Nanna ta dafa?"
Kai Julde ya girgiza mishi
"Ni ma ban sani ba fa..."
Yana ba Khalid din dariya kafin su rabu kowa ya
wuce bangaren shi. Sanda Julde ya shiga har
Saratu ta shirya teburin cin abincin mai
mazaunin mutum takwas. Kujera yaja ya zauna.
Ya kusan mintina goma kafin Khalid da Nawfal
su shigo da sallamar da ko amsa musu Julde
baiyi ba suka cigaba da maganar da sukeyi
"Ni fa bana son wannan tattare-tattaren da kake
mun... Jiya ba akan gado na ajiye takardar ba?
Saboda idan na zo in dauka, yanzun duk ka hade
su waje daya..."
Kallon shi Nawfal yakeyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 398
"Kan gado wajen ajiye takarda ne Hamma? Kan
gado fa? Meye amfanin teburin dakin?"
Kafin Khalid daya daga ido a zafafe ya amsa,
Salim ya rike wuyan kowannen su da hannun
shi, yana saka su fadin
"Hamma mana..."
A tare
"Tun kafin in shigo nake jin hayaniyar ku...sai
kace kaji"
Nawfal ya fara zamewa sannan Khalid, babu
shiri kowa ya samu kujera ya zauna, Khalid na
sa kafa cikin kokarin ture kujerar Nawfal daya
zauna kusa da shi
"Daddy kai ma Hamma magana"
Kallon su Julde yakeyi fuskar shi dauke da
murmushi, yanajin wani abu daya kulle mishi
kirji yana sassautawa
"Kai da baka ma jin yunwa? Me ka zo yi?"
Khalid din ya amsa
"Idan banzo ba waye zai takura maka?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 399
Wannan karin Khalid din ne ya kalli Julde
"Kana jin shi ko Daddy? Kana jin me yake cewa"
Khalid ya karasa yana kaima Nawfal dukan daya
kauce yana dariya
"Har yanzun kun kasa wuce shekara sha biyu"
Lukman daya karaso wajen ya fadi cikin
harshen fulatanci yana tsayawa kan kujerar da
Nawfal yake hadi da fadin
"Ka koma can Hamma"
Akwai wani yanayi tattare da Lukman da yake
saka kowa yi mishi abinda yake so, ko sanyin
halin shine ko kuma kwarjini ne daya ke
yalwace saman fuskar shi duk da karancin
shekarun shi. Tashin Nawfal yayi, Lukman ya ja
kujerar yana zama a tsakiyar Khalid din da
Nawfal kafin ya gaishe da Salim da Daddy
"Lukman ba'a ganin ka sam"
Nawfal ya fadi, har mantawa yake Lukman yana
gidan, sai ya ga giccin shi
"Ina nan Hamma"
Lubna sufyan
Hausabook.com 400
Ya amsa a takaice yana mikewa dan yaga alamar
kamar ba yunwa suke ji ba, shi ko abincin rana
baici ba, cake ne kwara daya yaci a makaranta.
Bubbude warmers din yayi, shinkafa ce da
miyar kaji, sai kamshi yake tashi, in dai girki ne
Allah ya hore ma Saratu, gashi tana son yin shi,
ko wani gidan taje aka bata abinda bata sani ba
bata girman kai take tambayar sunan shi da
kuma yanda akeyi, hakan ne ya sa ta kara
gogewa da abincin gayu kala-kala. Lukman ya
zuba ma kowa yana kallon Nawfal daya girgiza
mishi kai a hankali. Zai so yaci abinci a cikin su,
sai dai ko kifi aka saka ba nama ba a abincin
haramiyar shine tunda ya san akwai yaji.
Numfashin da ya shaka yaji yaki kaiwa in da ya
kamata da zuwan Saratu wajen, yana kuma jin
illar hakan a muryar shi lokacin daya furta
"Nanna..."
Cikin sigar gaisuwa. Bata kalle shi ba, amman ta
amsa da
"Bajjo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 401
Salim da yake kusa da Julde ya mike ta zauna a
kujerar shikuma ya zauna a ta kusa da ita
"Na bar wayata a daki, za'a iya kirana"
Yace yana mikewa batare daya kalli kowa ba
balle yaga yanda suka san karya yake, suka san
uzuri ne dan kawai ya bar wajen tunda Saratu ta
zo, babu kuma wanda yayi yunkurin hana shi,
akwai abubuwa da yawa da lokaci yake koya
maka ciki kuwa harda kiyaye halayen
makusancin ka. Yanda duk Saratu da Nawfal
zasuyi kokarin boye rashin kaunar da yake
tsakanin su idan wani yana nan, duk su Khalid
din na fahimta, kamar yanda suka san daga
Saratun har Nawfal sun san biye musu kawai
sukeyi. Fitar Nawfal tayi dai-dai da dagowar kan
Salim yana sauke idanuwan shi cikin na Khalid
da suke shimfide da tuhuma, shakku da alamar
tarin tambayoyi.
Baya so, tun shekaranjiya Khalid yake bin shi da
idanuwa haka, har yau ya so kauce ma dawowa
gidan ya kwana. Ocean Palace guest Inn ne
karshen in da yai tsammanin wani wanda ya san
shi zai gan shi balle kuma Khalid
Lubna sufyan
Hausabook.com 402
"Nagan ka Hamma... Na ganka yau"
Khalid din ya fadi, ba shi bane karo na farko da
wani a cikin shi ko Nawfal suka ce sun ganshi,
sai dai a shekaranjiyan kawai sai yaji zuciyar shi
tayo tsalle zuwa makoshin shi da ya bushe
lokaci daya yana kuma neman yawun da zai
samu ya jiqa shi ya rasa
"Nagan ka"
Khalid din ya sake maimaitawa muryar shi
dauke da wani abu da Salim bai taba tunanin zai
gifta a tsakanin su ba
"Kila ya kamata in nuna kamar ban gan ka ba,
kamar banga yarinyar da ka hada da jikin ka ba
Hamma, amman ba zan iya ba, ban san ya zanki
maka magana ba. Kace mun iya abinda nagani
ne kawai...dan Allah kace mun iya abinda nagani
ne kawai bai kai inda tunani ya nufa ba..."
Duk kalma daya da Khalid din zai furta wani irin
abune yake lullube Salim, ko dai haka kunyar da
yaji mutane na fada take shisa ya kasa daga
idanuwa ya kalli Khalid, a karo na farko a
rayuwar shi da yake son kasa ta bude ya shige
Lubna sufyan
Hausabook.com 403
ciki akan ya fuskanci Khalid a yanzun. Rabon da
yaji kamar abinda yake bashi da kyau har ya
manta sai a lokacin. Yana jin numfashin da
Khalid ya ja ya fitar
"Hamma..."
Ya kira zuciyar shi a shimfide cikin yanayin
yanda ya kira sunan Salim din, bai daga kai ba,
kasa yake kallo, haka Khalid din bai sake furta
komai ba ya juya kawai. Amman tun
shekaranjiya din yake bin shi da irin wannan
kallon tuhumar duk haduwar da zasuyi, banda
gaisuwa wata kalma bata gifta a tsakanin su ba
sai yau din nan, shima ya san saboda su Nawfal
suna wajen ne. Ya sa shi yanajin babu dadi tun
shekaranjiya, abinci ma ya daina gane
dandanon shi saboda taraddadin da ya kasa
fassara kona menene takamaimai.
Yanda Salim baiyi tsammanin ganin Khalid din
ba haka shima. Dan dakyar ma ya gane wajen da
kwatance da komai. Wani abokin aikin shine
kirista dan kabilar Igala yake aure a cikin satin,
to abokan shi da suka zo daga garin su sai suka
sauka a wannan Guest Inn din. Akwai takardun
Lubna sufyan
Hausabook.com 404
daya manta bai bari ba a wajen aiki kafin ya
dauki gajeran hutun, sune ya roki Khalid da
zaije dasu hotel din da yaje ya karba. Saboda
nisan wajen ma yana tafiya yana jan karamin
tsaki harya karasa, kawai dan dai Michael din
yana da kirki, bashi da matsala sam, amman
Khalid na daya daga cikin mutanen da kunya
bata cika saka su yin abinda zasu takura ba.
Ya kira Micheal din kuma yace mishi baima
karaso wajen ba, shine abinda ya saka shi zama
cikin mota in da yayi parking yana jira, kallekalle yake yanda ake shige da fice, mata da maza
a hade. Waje irin haka ya kamata ace ya zama
wajen da uzuri zai iya kawo kowa, amman ya
kasa kauda zargin da yake ma matan da yake ta
gani suna shige da fice daga cikin hotel din,
watakila tare da mazajen su suke, watakila sako
suka zo karba kamar yanda yayi, ko wani uzurin
mai tsafta, amman bata gari sun riga sun fesa
ma waje irin wannan ruwan da har abada
jirwayen shi ba zai taba wankewa ba.
Idanuwan shi da yake ta yawata wa yana kallekalle ya sauke kan wata jar mota da baiga
lambar ba, amman sak irin ta Salim, sai dai baya
Lubna sufyan
Hausabook.com 405
tunanin akwai abinda zai kawo Salim wajen nan,
watakila ma yana asibiti ko gida a wannan
lokacin. Kafin Salim din ya fito yana karyata
tunanin Khalid da ya kama murfin mota zai
bude da nufin fita ya karasa wajen Salim din,
yarinyar da yaga ta sakala hannunta a kugun
Salim na saka duk wani abu da yake kirjin shi
amsawa cikin yanayi marar dadin misaltawa.
Dakyar ya iya runtsa idanuwan shi yana sake
bude su dai-dai lokacin da Salim ya juyo da
yarinyar da duka alamu suka nuna bambancin
addini da yare a tsakanin su,Khalid na sake
runtsa idanuwan shi babu shiri
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya iya furtawa saboda ba zaiga hoton da baisan
yanda zai fara goge shi daga cikin kan shi ba,
jikin shi ko ina bari yake saboda tashin hankali.
Wacce irin bakar rana ce wannan yaci karo da
ita? Me zai gani? Salim? Hamman shi? Hamman
shi da kimar shi take kamar jirgin sama a wajen
shi har sai ya daga kai yake iya hango nisanta,
me yasa ya zo wajen nan? Me yasa kimar nan
zata ruguzo a saman kan shi kamar daman bata
Lubna sufyan
Hausabook.com 406
da nauyin rike kanta a saman shi? Me yasa Salim
ma zai karya mishi zuciya haka?
"Kar kayi saurin yanke hukunci"
Wata murya da bata da kuzari ta karfafe shi,
bayajin wani lokaci mai tsayi ya wuce, amman ji
yayi kamar zamani ne ya zo ya wuce yana nan
zaune saboda tashin hankali, sanda ya daga kai
baiga yarinyar ba, baiga Salim ba sai motar shi
da yake ja yana fita daga wajen. Ko ringing din
wayar shi Khalid baiji ba, Allah ne ya taimaka
Micheal din ya hango shi zaune cikin mota, idan
yace ga yaren da suka gaisa ciki zaiyi karya, ya
karbi file din dai, ko sallamar kirki baya tunanin
yayi da Micheal balle ya tambaye shi ya shiryeshiryen bikin shi suke tafiya. Duka wannan
abubuwane da muhimmanci yayi baya yana
tazara mai nisa da abinda Khalid din yake ji.
Da sanyin da jikin shi yayi yake tuki har gida. So
kawai yake ya shiga ya tambayi Salim dan ya
karyata mishi abinda ya gani, dan ya tabbatar
ma da tunanin shi abinda ya gani a wajen Guest
Inn din ne kawai. Amman sai shirun Khalid din
ya karfafa tunanin shi yana ruguza wani
Lubna sufyan
Hausabook.com 407
bangare na zuciyar shi. Saura wa kuma ya rage
yayi disappointing din shi haka? Sosai zuciyar
shi ta sosu, ba farin cikin duniya kawai Salim
yake wasa da shi ba, har lahirar shi ma lilo
takeyi amman yake rayuwa kullum kamar babu
mala'iku har biyu a kowanne gefen shi, kamar
baisan suna rubuta duk wani motsin shi ba.
Rashin tsoro irin na dan adam abune mai ban
al'ajabi, ko wani abin Khalid yayi da yasan babu
kyau sai yazo kwanciya yaji kirjin shi na bugawa
cike da taraddadi, kan shi na wankewa yana
barin tunani kwara daya tak, zai iya runtae
idanuwan shi na har abada, baccin da zaiyi da
nufin ya wayi gari zai iya bude idanuwan shi a
cikin kabari. Ta ya mutane masu tarin zunnubai
suke rayuwar yau da kullum kamar ba zasu
hadu da Allah ba? Abin da al'ajabi, ba kadan ba.
Laifin na Salim ne amman shi ya kasa bacci duk
tsayin daren, ga zuciyar shi da take zafi.
Kwanakin nan biyu haka yake yin su a daddafe
kawai, ko da sukai waya da Nawfal
shekaranjiyan wajen tara sai da ya tambaye shi
me yake damun shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 408
"Gajiya ce kawai"
Amman ya san Nawfal bai yarda ba shisa ya
dawo garin jiya. Yanayin yanda yake ta tsokanar
shi yana sanar mishi da cewa ko meye yake
damun shi in dai yana son su tattauna Nawfal
din a shirye yake da ya saurare shi, in kuma
yana ganin zai iya shawo kan abin shi kadai ma
Nawfal din ba zai matsa ba. Tsintar kan shi yayi
da godewa Allah da Nawfal ya kasance jinin shi,
mutum daya kuma da yake da yakini mai karfi
akan cewa ba zai taba karya mishi zuciya kamar
yanda kowa yake ta zabar yi ba.
Ganin Salim din na ta wasa da cokalin shi cikin
abinci yasa Khalid ture na shi plate din, daman
ba wai yana jin wata yunwa bane ba
"Har kayi me? Shisa kake ta kara ramewa
kullum"
Julde ya fadi, murmushin karfin hali Khalid yayi,
kafin ya amsa Lukman ya riga shi da fadin
"Meye babu a fuskar ka Daddy?"
Saboda tun dazun yake ganin kamar akwai
abinda ya kamata ace akwai a fuskar Julden,
Lubna sufyan
Hausabook.com 409
hakan yasa daga Khalid har Salim kallon Julde
kafin Khalid ya kwashe da dariya
"Inalillahi... Daddy waye yai maka wannan
yankar kaunar?"
Murmushi Julde yayi, bai san dalili ba, amman ji
yayi kamar idan ya aske gashin fuskar zai rage
nauyin da kirjin shi yayi, kamar ita kanta sumar
na da wani nauyi na daban da bai taba sani ba,
banda iska da yake ji tana shigar mishi fuska ta
ko ina babu abinda cire gashin yayi mishi
"Ni na aske abu na, furfura ta fara cika shi, shine
na aske sai baki ya fito"
Wannan karin har Salim sai da yayi dariya
"Nanna kina ganin shi ya aske?"
Khalid ya tambaya, murmushi Saratu tayi, bata
cika saka musu baki a irin wannan lokacin ba,
saboda a cikin shine take samun ganin dariyar
Julde, ta kuma ji zolayar shi da bai taba
gwadawa a kanta ba, sai taga kamar wani ne
daban ba mijin da ta aura ba, ba mijin da take
zaune da shi ba kuma. Ko dan wannan ba mijin
Lubna sufyan
Hausabook.com 410
ta bane ba, mahaifi ne tare da yaran shi, ubane
da kaunar yayan shi take a bayyane.
"Ko da ya aske din dai babu wanda zai nuna
mishi kyau a cikin ku"
Lukman ne ya fitar da wani sauti a kasan
makoshin shi da ya sake saka Khalid fashewa da
dariya
"Son kai dai Nanna"
Cewar Salim
"Son Daddy dai zaka ce"
Khalid ya amsa suna hada ido, yanayin da yake
tsakanin su na sake giftawa kamar labulen da su
kadai suke ganin shi. Kamar yanayin ya ba
Khalid damar mikewa dai-dai lokacin da suka
fara jiyo kiran sallar isha'i
"A gajiye nake ni kam, ina dawowa sallah zan
kwanta. Sai da safen ku"
Cewar Khalid din yana dan amsa tambayar
Nanna da take mishi na ko karfe nawa zai fita da
safe kafin ya juya yana barin dakin. Sai dai bai
Lubna sufyan
Hausabook.com 411
koyi minti biyu ba yaji takun tafiya a bayan shi
da yasa shi juyawa
"Khalid..."
Salim ya furta sauran kalaman da bai gama
hadawa a cikin kan shi ba suna makalewa, wani
abu ya kamata yace, amman shi din ba mai
yawan magana bane tun da can, balle kuma
magana irin wannan da bai taba tunanin zata
hadasu da Khalid ba. Murmushin da bai kai
cikin idanuwan shi ba Khalid yayi
"Bani zaka yiwa bayani ba Hamma, ba fahimta
ko yafiya ta zaka nema ba, bani da iko akan
anjiman ka balle har a tsallaka lahirar
ka...kawai kabari, ko menene dalilin ka bashi da
tushe, ka daina, ka roki Allah ya yafe maka kafin
lokaci yayi maka karanci..."
Idan ya fito da sanyin jiki, kalaman Khalid sun
sa yaji kamar kashin gwiwar shi ya sulale zuwa
wani waje da bai sani ba
"Zanje sallah..."
Khalid din ya furta yana sake juyawa yabar
Salim a tsaye. Ya so ya shiga bangaren su ya sake
Lubna sufyan
Hausabook.com 412
daura alwala, amman yana gudun kar Salim din
ya sake bin shi, shisa ya fice daga gidan. A
masallaci yayi alwalar, ana idarwa ya gama
lazumin bayan sallah ya daga hannuwan shi
sama sai kanshi yayi wani irin wayam, ga tarin
bukatu a zuciyar shi amman kwakwalwar shi
taki bashi hadin kai. Ya dauki lokaci da
hannayen shi a sama, zuciyar shi a bude cike da
yakini da kuma sallamawa har sai da yaji wani
sanyi da tsoron Allah ya ratsa sassan jikin shi
tukunna ya mike.
Da ya koma gida kai tsaye dakin su ya wuce, ya
samu Nawfal zaune kan kujerar teburin daya
dora hannayen shi yana latsa waya da kofin da
Khalid ya san shayi ne a ciki. In zai farkawa
biyar zai iya ganin Nawfal din a zaune kamar ba
dare ba
"Wai kai ba zakayi bacci bane ka huta ma ran
ka?"
Ya tambaye shi kwanaki hudu bayan ya zo
"Bana ji ne Hamma, bambanci lokacin nan yana
ta bani wahala... Gara in dan rage wani abin da
safe na rama In shaa Allah"
Lubna sufyan
Hausabook.com 413
Amman hakan baya hana shi yi mishi magana
idan ya farka ya ga dare ya raba. Ko ba zai bacci
ba dai ya kwanta kwakwalwar shi ta dan samu
hutu. Zai so ya watsa ruwa amman kasala yake
ji, shisa ya rage kayan jikin shi yana samun Tshirt marar nauyi ya dora akan singlet din shi,
sai gajeran wando yabi lafiyar gadon da ya sha
gyara sai kamshi ke tashi. Shi kanshi dakin yafi
mishi dadi idan Nawfal yana nan, matar shi dai
ta huta, Khalid din ya sani. Tsantsainin Nawfal
ba zai barshi ya jira sai tayi gyaran gida ba, tana
ma iyayi ya sake maimaitawa, dan duk yanda
zakayi shara sai kaga ya kara yin wata.
Addu'ar bacci yayi, yana runtsa idanuwan shi, a
hankali yake motsa labban shi yana fara karanta
ayoyin da suke cikin Suratul-Mulk dan neman
saukin kwanciyar kabari, baya taba mantawa
tunda ya mallaki hankalin shi ya kuma ci karo
da muhimmancin hakan, jarabawar duniya ma
neman hanyoyin samun saukin ta yake, balle
kuma samun lahira da komai ya zo mana a
bayyane. Daya dire cikon ayar karshe harya juya
baya sai kuma ya sake juyowa yana bude
Lubna sufyan
Hausabook.com 414
idanuwan shi akan Nawfal da yake zaune yana
danna wayar shi har lokacin
"Bajjo..."
Ya kira da sanyin murya, yana kasa tsayawa ma
Nawfal din ya amsa shi dan harya dan juyo da
kai
"Dole ne sai yara sun biya zunuban iyayen su?
Kana ganin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 18